Lantana Jafar (2023). Maraici Ko Son Zuciya? Ɗaukar Jinka (Labaran Da Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun Labarai Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2022). Kangiwa Multimedia and Communication Company LTD
MARAICI
KO SON ZUCIYA?
Na
Lantana Jafar
“Anti shan kayan maye na da matuƙar illa ga rayuwar ɗan’adam, kuma abu ne da yake zubar
da ƙima da darajar ɗan’adam. Don
Allah ko don lafiyarki da darajar ‘ya’yanki ki daina, yanzu duk cikin barikin
nan kallon rashin daraja ake yi miki. Ƙabilun
da ke ciki ma cewa suke mu ‘yan arewa dama mun fi kowace ƙabila lalacewa da iskanci da shaye-shaye
da dai zantuka munana masu ciwo gare mu.” Ta ƙare
maganar tana sunkuyar da kai.
Wadda
aka kira da Auntin ce ta ɗago idanuwanta ta sake ƙare wa kanta kallo. Daga ita sai shimi
mai ɗan ƙaramin hannu wadda tsayinta bai gama
kaiwa guiwa ba. A ce wai a haka ta kwana a waje kai ba ko ɗankwali? Wannan wacce irin rayuwa ce?’
Ta
sake duƙar da kanta ƙasa, ƙwallar
da ya taru ta gangaro bisa
kuncinta.
Shiru
ne ya ratsa na ɗan wani lokaci, sai ɗan
sautin jan numfashin da take na kuka ne yake fita.
“Idan
maganata ta ɓata miki rai ko na yi miki rashin kunya,
don Allah ki yi haƙuri.”
“Raliya!
Ko ɗaya
ba ki ɓata
min ba. Babu sanayya ko haɗuwar jini tsakanina da ke,
sai dai zama na muhalli guda da kuma kasantuwarmu ‘yan yanki guda. Duk da
gazawar shekarunki hakan bai sa kin ɗauke
idanuwanki akaina ba akan dukkannin halin da nake ciki, ba ki gujeni ko ki ƙyamaceni bisa halinaba. Kamar yadda wasu
da muka fito yanki guda suke kyarata da kuma tsangwamata. Na gode sosai da
kulawarki gareni. Har kullum ina fatan Allah ya ba ni ikon daina wannan ɗabi’a
tawa, ko nima mutane za su mu’alamalanceni yadda suke da kowa.”
“Mutum
ba ya ƙin mutum, sai dai ya ƙi halayyarsa. Idan ban takura ki ba don
Allah ina son sanin musabbabin faɗawarki
wannan halin Aunti.”
Murmushi
ne da ya fi kuka ciwo ya bayyana kan fuskarta.
“Babu
takura ko kaɗan a ciki. Kulawarki gareni kin wuce da
haka.”
Murmushi
ita ma ta yi, ta ce,
“Na
gode.”
“Rayuwar
gidanmu cike take da maraici gaba da baya. Muna ƙarƙashin kulawar mutanen da ke haya ne a
cikin gidanmu, su ke ba mu ci da sha kuma su tsawatar mana. Sai ‘yan kuɗaɗen
hayan da muke ɗaukar ɗawainiyar
kanmu dasu idan lokacin karɓa ya yi, ko kuma idan mun
samu alheri daga samarinmu. Hakan duk ta faru ne a sanadiyar watsi da
makusantan danginmu suka yi da mu. Ɗoriya
da rashin sanin takamaiman inda ragowar dangin mahaifanmu suke. Muna da tarin
burika na son yin karatu sai dai babu mai ɗaukar
nauyinmu, wanda hakan ya sa muka haƙura
wasunmu suka rungumi aure. Babban burina a baya bai wuce zama soja ba, hakan ya
sa nake yawan zuwa barikin soja wurin ƙawata
Hafsat domin mijinta ya taimaka mini na cimma muradina.
A nan
ne Allah ya haɗa ni da Mark ɗan
jihar Calaba wanda ya nuna ya na so na amma naƙi
amincewa saboda bambancin addini da ke tsakaninmu. Ya cigaba da bibiyata har
yasan komai game da ni. Akwai sanayya da shaƙuwa
tsakaninsa da mijin Hafsat, hakan har ta kai shi ga musulunta duk a sanadina.
Shiru
ta yi na ɗan lokaci kafin ta ɗora.
“Yayanmu
wanda muke ‘yan uba da shi, shi ne ya yi silar rugujewar rayuwata da bazan
daina kuka ba har in koma ga mahaliccina.
Watarana
ba kowa a gidan ya umurce ni da na share masa ɗaki,
shiga ta keda wuya ya shigo ya rufe ƙofa
da makulli hankalina ya tashi matuƙa da
na fahimci nufinsa a kaina, yana son ya yi mini fyaɗe.”
Kuka ne ya ci ƙarfinta wanda ya sa
ta sake tsagaitawa da zancenta na ɗan
lokaci. Cike da jimami Raliya ta ce, “Ya Ilahi! Wanda kuke uba ɗaya
a ce shi yake shirin ɓata miki rayuwa? Wannan
wacce irin rayuwa ce muke a cikinta?” Ta kai aya tana share hawayenta.
“Rayuwarmu
ta yau ai ba a cewa komai, sai godiyar Allah da fatan shiriya kawai.”
“Allah
ya kyauta.”
“Amin.”
Sannan ta ɗora,
“Na
yi roƙo da magiya amma ya ƙi saurara, a ƙarshe muka shiga ‘yar kokawa da shi daga
bisani ya koma duka na saboda na ƙi
amince masa, ina ji ina gani ya jona hitar ruwan zafi ya manna min a fuskana.
Wani gigitacen ihu na kurma wanda hakan ya sa mace guda da ta dawo gidan ta
garzayo don ganin abin da ke faruwa, ta yi bugun duniya ya ƙi buɗe ƙofar, hakan ya sa ta garzaya ƙofar gida neman taimako. Maza uku ta
samo suka ɓalle kofar tun da sun yi mai magiya ya ƙi ɓuɗewa.
Tunda
na samu na kuɓuta na shige ɗakin
matar gidanmu ƙarƙashin gadonta mai rumfa. Da aka tambaye
shi me ya faru sai cewa ya yi wai ina yawan tara samari a kofar gida ya sha yi
mini faɗa na
ƙi dainawa, ni ina ganin na fi kowa kyau
da farin jini to bari ya lalata fuskar tawa sai yaga da wane kyawun za a riƙa biyo ni.
Wannan
shi ne silar da na gudu daga gidan, na koma cikin barikin soji da zama a gidan ƙawata Hafsat. Idan dare ya yi sai in
tafi ɗakin
su Tosi makwabtan ta in kwana. A hankali soyayya da shaƙuwa ta shiga tsakanina da Mark wanda
yanzu ya koma Ibrahim. An sha fama kafin ‘yan’uwa su amince da aurenmu
kasancewar shi tubabbe watarana komai na iya faruwa.
Tun a farkon aurenmu na fara fuskantar matsala, duka da
rashin yadda, ban isa in yi hulɗa da mutane ba. haka na haƙura na zauna tunda yana ɗaukar ɗawainiyata kuma ba
ni da matsalar kuɗi har ina taimakawa yan’uwana, a haka har muka haifi ya’yanmu
uku maza biyu mace ɗaya ita ce ƙarama.
Watarana
wata harkar kasuwanci ta fito na sayan hannun jari, ya tattara kuɗaɗe
masu yawa ya saya mana har da yara.
Rana
ɗaya
aka neme su aka rasa, wannan abu ya samu cikin ruɗani
da tashin hankali. Wannan dalilin ya sa ya nemi posting zuwa garinsu Calaba. Ba
ni da zaɓi
haka na bi shi saboda yarana. Ko sallamar arziƙi
ban yi da yan’uwana ba.
Bayan
komawarmu garin sai matsaloli suka ƙara
yawa ciki harda shaye-shaye na giya da neman mata da ya fara, ga tsana da nake
fuskanta daga ‘yan’uwansa da mahaifiyarsa da ke yawan kawo mana ziyara
akai-akai.
Ya gaza
yarda da ƙaddarar da ta faɗo
mana, a haka ya ci gaba da shan barasa a cewarsa tana rage masa damuwa, idan na
yi masa nasihar haƙuri
da yarda da ƙaddara, da illar da
kayan maye ke yi sai ya ce ya kasa jure asarar da ya yi ne, in ci gaba da taya shi
da addu’a.
Kwanaki na tafiya, al’amura na ta faruwa, duniyar tayi
mini zafi, abin da za mu ci ma watarana gagararmu yake yi. Albashinsa a kayan
maye da mata yake tafiya, danginsa kuma su taru su yi ta tsangwamata kan na yi
kane-kane kan dukiyarsa, na hana ya riƙa yi musu abin arziƙi. Haka na cigaba da haƙuri saboda ‘ya’yana, wasu lokutan ida ya dawo a bige ya
kamani da duka wani sa’in har korata yake ya rufe ƙofa idan na shiga ɗakin makwabta, nan ma wata fitinar
ce.
Wani lokaci sai dai in tafi maƙotan block ɗinmu gurin wata yar garinsu Rofen, itama soja ce watarana
da tashin hankalin yayi yawa ya watsomin kayana Rofen ta tausaya mini sosai, ta
kwashe kaya na zuwa gidanta ta ce zata bani kuɗin mota in koma
gaban iyayena wulaƙancin ya yi yawa. Na
sanar mata ni marainiyace iyayena sun rasu ‘ya’yana sune gatana ba zan iya
tafiya in barsu ba.
Da
ta ga kukan da nake yi yayi yawa ta ɗauko
wasu ƙwayoyi wanda ban sansu ba ta miƙa mini.Ta ce in sha zan samu sauƙin damuwar da nake ciki. Haka na ƙarɓa ba
tare da wani tunani ba na sha jimawa kaɗan
na fara ji na wani iri can sai jiri-jiri da aka jima amai ya biyo baya, da ya ɗan
lafa ne ta ce kada in damu dan ban saba ba ne.
Washegari yazo ya yi mini ɗadin baki akan
yarana, kin san yadda soyayyar uwa take akan ‘ya’yanta haka na haƙura na koma ɗakina. Tun daga wannan rana idan raina ya ɓaci
sai in tafi gurin Rofen ta bani ƙwayar
na sha. A hankali har ya shiga jikina idan ban sha ba, ba na jin daɗi. Da
na ƙara wayewa a harkar sai na fara haɗawa
da wasu masu ƙarfi.
A
hankali na fara janye jiki daga mutane ban cika son yin magana ba idan zaki
tuna. Lokacin da kuka dawo nan barikin aka ce miki ga ‘yarArewa, da murna kika
zo ke a dole kin samu ‘yar’uwa. Amma ba ki samu wata fuskar da zaki ji daɗin
mu’amala da ni ba. A haka kika yi ta jure wa halina.
Yarana
ma na daina ba su cikakkiyar kulawa; ba na kula da addinina ballantana in kula
da na ‘ya’yana da mijina, a haka shima ya daina sallar kwata-kwata ni kuma
ranar da naga dama inyi na saka yara su yi. Dama aikin gida tuni na sakar musu
su suke komai na kula da kansu idan babansu baya duty shi zai yi.
A hankali ya fara gajiya da halina yayi duka da surutu
har ya gaji waɗanda muke mutunci dasu musamman musulmai ‘yan Arewa idan
suka yi nasihar sai dai ince naji zan daina a lokacin gani nake sun takura wa
rayuwata, sai na daina kula su ko da sun yi mini magana. Da
haka kowa ya fita harkata, sai tsangwama da kyara. Shaƙuwa mai ƙarfi
ta ƙara shiga tsakanina da Rofen har ta fara
ja na zuwa club daga nan ta tura min ra’ayin shan barasa wanda a da idan mun je
sai dai in kallesu suna sha.
Cikin shekara ɗaya zuwa biyu na canza kamanni, gabaɗaya na lalace duk
wanda ya ganni yaga cikakkiyar ‘yar ƙwaya ga ciwo da
nake fama yau lafiya gobe babu har asibiti mijina ya kai ni akan matsalar
shaye-shaye sun riƙe ni na sati biyu babu laifi na samu
lafiya. A
yanzu haka an tura shi zuwa Port Haccourt, shi zai je can, mu kuma zamu je ƙauyensu. Kan haka muke ta faɗa
wanda ɓacin
rai ya sa ni shan kayan mayena.”
Bayan jan dogon numfashi Raliya ta ce, “Zan ji babu daɗi da za mu rabu da
ku, amma don Allah Aunty ki yi ta addu’a ki riƙe ibadarki, da sannu Ubangiji zai kawo sauƙin da canji. Sakaci da ibada da kuma addu’a ya sa komai
ke ƙara lalacewa, ki maida kulawarki da yaranki, ki kuma nemi
‘yan’uwanki.”
“In
shaa Allahu! Na gode sosai.”
Ta
ba ta zani da mayafi ta yi sallah, sannan ta nufi gidanta.
Bayan kwana biyu da faruwar haka suka tattara ya kai su ƙauyensu Ikon, shi kuma ya wuce wajen aikinsa.
Zama
ya ƙi daɗi
tsakaninta da mahaifiyarsa, a yanzu sunan mayya ne ya maye gurbin sunanta a ƙyauyen. Babu mai raɓarsu,
a cewar mahaifiyarsa da ‘yan’uwansa, ta mallakeshi ya fita daga addininsu ya
koma nata.
Wannan
yawan ɓacin
ran shi yasa ta koma halin shaye-shaye gadan-gadan. Duk da dama ba dainawa ta
yi ba amma ta rage kashi arba’in cikin ɗari.
Rigima
ce ta ɓarke
sosai wata ranar Lahadi akan sai dai ta ba ta jikokinta su tafi coci, don ba za
a raba mata jikoki da addinin iyaye da kakanni ba. Da ta faki idanuwan kowa ne
bayan an tafi shiryawa, ta kwashesu sai mashaya, nan ta sha ta yi maƙil, sai ɗaukota
aka yi zuwa gida. Bayan fitarta mijinta ya zo har ya fita ba ta sani ba, nan
suka dasa masifa ta dinga tsine mata albarka harda wasu maƙotan ta da suke taya ta.
Shi kuma da ya fita ya kira wayar ‘yar’uwarta ya kwashe
komai ya sanar mata, ya kuma ce su yi gaggawar zuwa su kwasheta, ya gaji da
zama da ‘yar maye. Da ta fara dawowa hayyacinta ne ta ga tayi kaca-kaca da
amai, hakan ya sa ta cewa ‘yar ta Mima ta ɗebo mata ruwa. Tana
zuwa kakarta ta hana, wai kada a sake a taɓa mata ruwan gida,
lokacin yayunta ba su nan, hakan ya sa ta umurci Mima da ta ɗebo a rijiya. Kafin
ta dawo ne bacci ya ɗauketa.
Cikin
bacci ta ji sauƙar
ruwan sanyi haɗe da duka a lokaci guda, a firgice ta
tashi tana faɗin “Mim...” Maganar ya maƙale sakamakon naushi mai ƙarfi da aka sake mata akan baki, ga duka
ta ko ina.
“Ku ƙyaleta haka, kada ace mun yi kisan kai,
ko yanzu ai ta ji a jikinta, ta fara gane hukuncin mai shaye-shaye.” Cewar wata
dattijuwa. “Ku barni in kasheta kamar yadda ta kashe mini jika. Idan ba iskanci
ba, babba ma ya ya ya ƙare
da jan ruwa a rijiyar garin nan balle kuma yaro, kin sa ta je ta faɗa
ciki ta mutu, gara mu kasheki kowa ma ya huta, tunda wanda ya ɗaukoki
ya ƙi rabuwa da ke.” Cewar surukarta da ta
gama fita hayyacinta da kuka da tarin takaicin abin da ya faru.
Da ƙyar ɗaya daga cikin waɗanda suka shigo, ta
janye ta zuwa tsakar gida, abin da idonta ya yi tozali da shi ya sa ta daddage
iya ƙarfinta ta kurma ihu mai firgitarwa! Duk
da ragowar mayen bai gama sakinta ba, hakan bai hanata fahimtar abin da ke
faruwa ba.
Jama’a ne suka yi dafifi tsaye suna kallo cike da alhini,
wasu daga ciki ma kuka suke yi saboda tsabar tausayi.
Jijjiga gawar yarinyar ta shiga yi cikin kuka mai tsuma
zuciyar mai sauraro tana mai kiran sunan ɗiyar ta ta, sai dai ko gezau ba ta
yi ba.
Gashin kanta aka damƙo, take aka shiga janta a ƙasa, garin kiciniyar ƙwacewa ne suka yi ido biyu da mijinta, wanda mahaifinsa
ya kirashi a waya ya sanar misa da abin da ke faruwa.
Wani
ɗaki
mara komai ya wurgata a ciki ya mai da ƙofar
ya rufe.
Ɗakin mahaifiyarsa ya nufa, jim kaɗan
ya fito rike da belt ɗinsa ta sojoji ji ka ke
gararam ƙarar rufe ƙofar.
Rufe ido ya yi ya shiga jifgarta kamar Allah ya aiko shi,
haɗawa yake da ruwan ashariya tare da naushinta da ƙafa a dukkan sassan jikinta. Cikin
tashin hankali mutane ke ta bugun ƙofar
ɗakin.
Sun yi rarrashi haɗi da ban baki kana aka samu
ya buɗe ƙofar da ƙyar.
Ko
da ya fito kulle ta ya yi a ciki ya ce baza ta fito ba.
Haka
ta cigaba da rera kuka mai ban tausayi. Da wanne zata ji? Mutuwar ‘yarta ko
kuma na dukan da suke mata kamar jaka?
Ba
ta san adadin sa’o’in da ta ɓata a cikin yanayi mai cike
da tashin hankali ba.
Bayan
shuɗewar
wasu sa’o’i. Sai ta ji an buɗe ɗakin
haske ya gauraye ko’ina, ɗago rinannun idanuwanta ta
yi masu kama da jan gauta. Ƙanin
surukinta ta gani rai a ɓace ya ce mata.
“Ki
fito mu je jana’iza.” Daga haka ya juya ba tare da ya ƙara ce mata komai ba.
Da
gudu ta taso har tana karo da bango saura kaɗan
ta faɗi ƙasa.
Haka
ta dinga kutsawa cikin mutane maza da mata,wanda dukkanninsu cikin shigar baƙaƙen
kaya. har ta isa kan gawar ‘yarta da ke kwance cikin akwatin gawa, an yi mata
kwalliya cikin kaya na ƙawa,
yayin da fulawa ke sarƙafe
a cikin hannunta.
Kukan
da take yi a wannan karon, ya bambanta da na mutuwa sai na tsantsar baƙin ciki, saboda ganin irin jana’izar da
ake shirin yiwa ‘yarta, wanda ya bambanta da na addinin Islama.
“Innalillahi
wa’inna ilaihiraji’un.” Sai a lokacin ta tuna da wannan kalmar ta neman
sassauci a wurin Ubangiji.
Ba
ta da ƙarfi ko ikon hanawa, haka tana kallo aka
turnuƙa ‘yarta a cikin rami batare da anyi
mata salla ba.
*** *** *** *** *** ****
Tun da
aka ɗauketa
aka watsa ta a ɗaki, ba wanda ya sake bi ta
kanta, sai ma sharholiyar jana’izarsu suke yi.
Cikin
haka ne Allah ya jefo mata ɗaya daga cikin maƙotansu da suke ɗan
mutunci, a nan ne ta roƙeta
aron waya ta sa lambobin ƙanwarta
ta ce ta kira za ta faɗa mata saƙo.
Ƙanwar tata ta ɗaga tare
da sallama, ta tambayi da wa take magana? “Baki sanni ba, ni maƙociyar yayarki ce Maman Mima, ita ta ce
in ƙira ki. Tana cikin mawuyacin hali na
ciwo sosai, ya kamata ki zo.”
Sai
ta miƙa mata wayar.
“Jamila
kin ƙi zuwa ko? To idan na mutu kya zo.” Daga
haka ta katse wayar.
Hankalin ta ya kai ƙololuwar tashi, ta
fara tunanin karo na uku kenan tana kiranta, ko wane irin hali gareta da har
tilon ‘yar’uwarta za tai ta kiranta ta je amma ta kasa zuwa? “Talauci.”
ta furta a hankali.
Tabbas
talauci ne ya hanata amsa kiran ‘yar’uwarta da ta kasance a cikin halin ciwo
tun bayan rashin ‘yarta da ta yi.
Hawaye
masu raɗadi
ne suka dinga kwaranyowa daga idanunta.
Ta ɗaga
idanuwanta, yayin da take ƙarewa
ɗakinta
kallo, babu wani abin kirkin da zata ɗaga
ta sayar in ka cire katifar da suke kwanciya, sai firji da take sana’a domin rufawa kanta asiri.
Ta ɗauki lokaci tana tunani ta wace hanya za ta samu kuɗin, amma ina ba ta
hango mafita ba, dole dai shawararta ya tsaya akan ta saida firjinta Allah zai
rufa mata asiri.
Bayan wasu sa’o’i mijinta ya dawo daga wurin sana’arsa,
ta yi ƙoƙarin yi masa bayanin halin da ‘yar’uwarta
ke ciki na jinya an buƙaci ta je.
“Babu
inda zaki je.” Ya katse ta.
“Don
Allah ka barni...,Ina tsoron ace mutuwa ta raba ganawarmu, domin ta faɗa mini
abin da ya ɗaga mini hankali wanda tunda nake ba ta
taɓa
furta mini ba.” Ta ƙarasa
zancen cike da tausasawa.
“Yo
Allah na tuba idan ɗan shaye-shaye ya mutu ai an
rage mugun iri ne a doron ƙasa.
Saboda haka wannan ba wani abu bane, ta yiwu ma ɗan
afe-afen ta ta yi, tunaninta ya juye, shi ya sa ta faɗa
miki ƙarya, so take hankalinki ya tashi domin
ki je.”
“Duk
lalacewar naka dai naka ne. Idan duniya zata juya mata baya, ni ina tare da
ita, ka sani jini ya fi ruwa kauri. Jinin jikinta ke yawo a jikina kamar yadda
nawa ke yawo a jikinta. Na riga na gama shiri, gobe idan Allah Ya kai mu, can
na nufa.”
“Wallahi
idan kika je ba da yawuna ba. Har wani amfani rayuwar ‘yar maye take da shi? Ta
yi ajalin ‘yarta saura naki, don haka ban amince ba.” Ya fice yana ta bambami.
Ba su yi aune ba sai ganin tsofaffin mata da ke zaman
makoki suka yi a ɗakin da surukarta, ba ɓata lokaci suka
shiga janta har waje.Ta ce ba a gidanta ba, tunda aka fara kashe ɗaya, su ma da haka
zata kashesu, sun yi bincike boka ya ce dodon maitarta ne ya cinye ɗiyar.
Haka
Ibrahim ya tattarasu suka koma cikin bariki. Tun daga wannan lokaci rayuwa ta ƙara munana a harkar shaye-shaye madadin
sauƙi, kowa ya gujeta, ‘ya’yanta mazan ma ba
sosai suke zama kusa da ita ba. Ana haka ne kuma sai ga zuwan ‘yar’uwarta
Jamila da Hauwa wanda suka sami bayanin a gurin maƙociyarta ta Calaba. Sun koka sosai ganin
irin rayuwar da ‘yar’uwarsu take ciki, hakan ya sa suka nemi Chief Imam na
barikin kan ya yi wa Ibrahim magana za su tafi da ita da yaran, bayan zuwansa
ne ya ce, ba dai ‘ya’yansa ba, sai dai su ɗauki
‘yar’uwarsu. Dole suka haƙura,
ya ba su kuɗin motar da zai kai su, domin a yanzu ya
zaƙu a tafi da ita, saboda yana tsoron ta
mutu a hannunsa ya biya diyya, tunda al’adar su ce hakan a garin.
Washegari
suka ɗauki
hanya cike da kewar yaranta. Kai tsaye Kano suka nufa gidan matar mahaifinsu da
ta baro Bauchi ta dawo garinsu bayan mutuwar babansu.
An karɓesu hannu bibbiyu babu ƙyama ko wulaƙanci da safe aka
kira wani likita ya zo gida ya dubu ta yanayin jikin nata ya sa ya ce aje ayi
mata hoton cikinta da yayi ƙwaja-ja, bayan sun
yi hoton ya duba ne ya ce su tafi babban asibitin domin sai abin da hali yayi. Ba
ta magana sai nishi da take yi sama-sama gurin da take kwance a nan take
fitsari mai kama da ruwan ganye har wani baƙi-baƙi yake yi haka bayan gidanta ma ya koma
baƙi.
Suna
isa asibiti emagency aka wuce da ita likitoci biyu ne akanta, suna mana
tambayoyi muna basu amsa. Ba mu ɓoye
masu komai ba dangane da shaye-shayenta, sun tabbatar mana da kayan mayen da
take ta’ammali da su ne suka haifar mata da matsala tana fama da cutar Cancer.
Hakan
ya taimaka wajen ruɓewar kayan cikinta. Sun yi ƙoƙarin
suga tayi magana amma sam taƙi
sai da suka goga mata dunƙulallen
hannu a ƙirji kana ta ce wash daga nan bata ƙara magana ba ruwa kawai suka jona mata
da allurai. An saka mata robar abinci ta hanci da ta fitsari, haka muka kwana
har washegari babu wani canji, sai ma sassan jikin ta da suka fara kumburi kaɗan-kaɗan
ta fara wari, cikin dare ta fara jijjiga da wani irin ƙara, allura aka yi
mata ya ɗan
lafa, haka muka yi ta fama har cikin dare sai gab da asuba ta amsa kiran
mahalicci, Allahu Akbar! Haka muka ci kukan mu har garin Allah ya waye mutanen
gida suka taho da mota muka koma gida aka
yi mata sutura. sai a lokacin yan’uwan da sukayi watsi da zumunci suka zo cike
da nadama rashin kulawar da basu bamu ba.
Sai
ana gobe ‘yan Bauchi za su koma, Jamila ke shaida masu mutuwar aurenta. Sun
jajanta mata.
Jamila
ta duƙufa wurin bincike a kan shaye-shaye da
hanyoyin magance shi.
Hauwa
takan ce “Jamila wannan babban al’amari ne domin yana buƙatar ilimi da kuɗi, ke kuma ko ɗaya
baki mallaka ba “ takan ba ta amsa da,
“Ba
sai mutum yana da ilimi zai yi wani abin kirki a rayuwa ba, irin wannan tunanin
shi ya haifar mana da koma baya a yankunanmu.
Shaye-shayen
nan da zaman banza ba ƙaramin
illa ya yiwa matasanmu ba wanda sune shugabanninmu na gobe, bai kamata mu naɗe
hannayenmu muna jiran gwamnati ko hukuma su magance
mana matsalarmu ba, matsayin muna da yanda zamu yi. Kawai abin da nasa a rai
shi ne zan iya koda kuɗi da
ilimi ko babu.”
Na
nemi shawarar ƙawata Barira da yake
tayi karatu,
fanin magunguna ta karanta ta bani goyon bayan maganar da na zo da ita.
Ta
amince mu haɗa hannu domin yaƙi da zaman banza da shaye-shaye.
Mun fara yaɗa manufarmu ta kafar sadarwa domin shi ne hanya mafi sauƙin na isar da sako ga wannan zamani, kafin wani lokaci
mun samu karɓuwa da masu son shiga cikinmu domin a tafi tare ciki
harda waɗanda suke shaye-shaye sun kasa bari mun fara tuntuɓar ƙungiyoyi masu zaman kansu wasu da kansu suke kawo mana
goron gayyata, cikin ƙanƙanin lokaci mun samu karɓuwa muna yawan
samun gayyata gurin taruka ko makarantu domin faɗakar da su tare da
nuna masu illar shaye-shaye da zaman banza. Wannan dalilin yasa gwamnati da
kanta ta nememu ta bamu office tare da gina mana Rehabilitation center inda za
a dinga aje masu lalurar shaye-shayen ana kula da lafiyar su tare da ɗora su akan magani
har Allah yasa su warke a gefe guda kuma hadda gurin koyar da sana’a idan Allah
yasa mutum ya samu lafiya sannan akwai tallafi na jari da za’a ba mutum ya
tallafi rayuwarsa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.