Citation: Dalha, I. and Mode, N. M. (2025). “Sana’ar Gyartai: Matsayinta da Makomarta a Ƙarni Na 21 (Nazari a Shekarar 2025).” in Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 03, No. 02, Pp. 175 – 183. www.doi.org/10.36349/djhs.2025.v03i02.022.
SANA’AR
GYARTAI: MATSAYINTA DA MAKOMARTA A ƘARNI NA 21 (NAZARI A
SHEKARAR 2025)
Ibrahim
Dalha
Ɗalibin PhD, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
and
Nasiru
Muhammad Mode
Cibiyar
Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Tsakure:
Sana’o’i dai
wani ɓangare ne da suke nuna fasahohi da kuma hanyoyin
dogaro da kai na al’umma. Wannan dalili ya sanya suka zama wasu hanyoyi da
suke ƙara bunƙasa tattalin arzikin al’umma. Wannan ne ya sa
suka zama sanadiyyar shaharar Hausawa a ciki da wajen ƙasar
Hausa. Muradin wannan takarda ne ta dubi sana’ar gyartai ta hanyar bayyana
matsayinta tare da fito da hasashen makomarta a wannan ƙarni
da muke ciki na ashirin da ɗaya. Duk da cewa masana
da manazarta sun gudanar da ayyuka da dama masu alaƙa
da sana’o’in Hausawa, amma wannan takarda ba ta samu zarafin riskar wani aiki
da ya tunkari sana’ar gyartai ba. Takardar ta yi ƙoƙarin
tuntuɓar
masu gudanar da sana’ar da kuma masu amfanuwa da ita, domin samun bayanai. An
yi haka ne ta hanyar ziyartar su a wurin da suke gudanar da sana’arsu. Haka
kuma, nazarin ya kai ziyarar rangadi kasuwanni da kuma wuraren da ake gudanar
da sana’ar, saboda a fahimci ta inda salka take yin tsatsa. Sakamakon da aka
gano sun haɗa da: Sana’ar gyartai ta ja baya matuƙa,
saboda yawaitar kayan amfanin gida na zamani. Rashin samun kuɗin
shiga mai gwaɓi daga sana’ar, yana daga cikin dalilin da ya sa
take samun koma baya musamman a wannan lokaci da yanayin gudanar da harkokin
rayuwa suka ƙara tsada.
Muhimman
Kalmomi: Sana’a; Gyartai
Gabatarwa
Ayyukan masana da manazarta sun tabbatar da cewa, ƙololuwar cigaban kowace
al’umma ta fuskar tattalin arziki yana da alaƙa da sana’o’insu da kuma
kasuwancinsu. Duk al’ummar da take da nakasu ta fuskar sana’o’i da kasuwanci ta
zama koma baya. Wannan dalili ya sa al’ummar da ta san darajar kanta ba ta wasa
da sana’o’in dogaro da kai komi ƙanƙantarsu. Sakamakon masaniyar da suke da ita cewa, mai
rena kaɗan yakan iya dangana da babu. Don haka suka yarda da maganar masu hikima da
suke cewa: “Ɗan ƙaramin gatarinka ya fi sari ka ba ni.” Ga al’ada, kowace sana’a ba ta
rasa wani alfanu ga al’umma. Fahimtar haka da Hausawa suka yi, shi ne ya sanya
suke ba sana’o’insu kima. Wannan kuma shi ne ya ƙara ɗaukaka Hausawa tare da kai
su wuraren da duga-dugansu ba su taka ba. Duk da shaharar da Hausawa suka yi ta
fuskar riƙo da ayyukan dogaro da kai, a yanzu cigaban fasahohin zamani ya fara yi wa
wasu sana’o’in nasu barazana. Misali, sana’o’in kaɗi da saƙa da dangoginsu sun fara ja
da baya.
Muradin wannan takarda ne ta dubi sana’ar gyartai ta
hanyar bayyana matsayinta tare da fito da hasashen makomarta a wannan ƙarni da muke ciki. Tabbas,
aikin da Sanyinnawal (2015) ya gudanar ya nuna sana’ar gyartai tana cikin
rukunin sana’o’i marasa kima na Hausawa. Shi kuwa Muhammad (2019:122) ya ambaci
gyartai a cikin rukunin sana’o’i masu wahala, amma dukkaninsu ba su faɗaɗa bayani a kanta ba. Haka
kuma, Bunza (2019) ya gudanar da bincike a kan ƙwarya da yadda ta mamaye
adabin baka na Bahaushe. Waɗannan ayyuka sun zama kamar sun kashe maciji ne ba su
sare kansa ba. Ma’ana dai, tamkar suna haska wa ɗalibai ne cewa, akwai buƙatar a gudanar da wani keɓanataccen aiki a kan sana’ar
gyartai. Domin ko ba komai, akwai buƙatar a taskance wani abu da ya shafi al’adun da
suka ɗamfaru da sana’ar gyartai, saboda gudunmawar da take bayarwa ta fuskar
gyara kayan da suka danganci ƙwarya idan sun fashe ko sun tsage.
An fara maƙalar da bayyana ma’anonin kalmomin da aka gina taken
takardar da su. An yi haka ne domin samun nagartaccen jagoranci dangane da inda
takardar ta nufa. Kalmomin da aka bayyana ma’anoninsu su ne: Sana’a da gyartai.
Sana’a
Idan aka ƙura wa kalmar sana’a ido za a fahimci cewa, tana nufin
nagartacciyar hanyar da ɗan’adam yakan bi domin dogaro da kansa, waɗanda suka haɗa da samar wa kansa abin da
zai ci ya sha tare da gudanar dukkanin buƙatun rayuwarsa. Sanin haka ya sanya Sharifai, (1990:17)
Garba, (1991:11) da Yahaya da wasu, (1992:48) da Muhammad (2021:38) da kuma
Maidabino, (2024:186) duka bayanansu suke bayyana sana’a a matsayin aikin yi
domin samun kuɗin shiga.
Gyartai
Idan aka kalli kalmar gyartai a farfajiyar nazarin
harshe, tana da fuskoki guda biyu. Na farko, takan iya tsayawa a matsayin suna
gama-gari, inda akan kira duk wani mai sana’ar ɗinke ƙwarya da dangoginta da
sunan, “gyartai”. Wani abin mamaki game da wannan kalma, idan ta zo a matsayin
suna ba ta da jam’i kamar yadda sunaye suke da shi a Hausa. An bayyana kalmar
ta fuskoki biyu kamar haka, (i) mutum mai gyaran ƙwarya. (ii) sana’ar
gyaran ƙwarya (CNHN, 2006: 185). Wannan ma’ana ta Ƙamusin Hausa ta yi daidai da
tunanin Muhammad (2019: 122) inda ya nuna sana’a ce wadda ake ɗinke ƙwarya idan ta fashe.
Kodayake, wannan takarda tana ganin bai kamata a bayyana aikin gyartai ya tsaya
a gyaran ƙwarya kaɗai ba. Sakamakon sukan ɗinke gora (gyanɗama) da ludayi da shantu da zunguru da
sauransu. Kenan kamata ya yi ma’anar sana’ar ta zama aikin ɗinke dukkanin wani abin
amfani dangin ƙwarya. Mai gudanar da sana’ar ana kiran sa da gyartai kamar yadda ake kiran
sana’ar da shi. Ga alama, maza ne suke gudanar da wannan sana’a, don haka
takardar ba ta iya gano sunan da ake kiran macen da take yin ta ba.
Hanyoyin Gudanar da Bincike
Ingancin kowane bincike yakan bayyana ne ta hanyar amfani
da nagartattun hanyoyin da aka yi amfani da su wajen tattaro bayanai. Wannan
takardar ta yi ƙoƙarin
yin amfani hanyoyin tattaro bayanai domin naƙalto abubuwan da take nema.
Daga cikin hanyoyin da aka yi amfani da su akwai: Ziyartar wuraren da masu
sana’ar gyartai suke gudanar da ayyukansu a kasuwar Kara da take Sakkwato,
domin gane wa idanu yadda ake aiwatar da ita. Haka kuma, an gudanar da hira da
masu gudanar da sana’ar tare da waɗanda sukan kawo musu ayyuka domin ji daga gare su. Bugu
da ƙari, an tuntuɓi wasu masana al’adun Hausawa domin ƙara wa katangar binciken yaɓi. Har wa yau, an dubi wasu
ayyukan magabata waɗanda suke da alaƙa da batun da ake tattaunawa a kansa domin samun hasken gudanar da wannan
bincike.
Hanyar Ɗora Aiki
Ba wani abu ne hanyar ɗora aiki ba, face yin amfani
da tafarkin magabata domin daidaita akalar bincike. Duba da cewar wannan nazari
ya karkata ne a kan nazarin sana’ar da Hausawa suke gudanarwa, shi ne ya sa
aka ɗora shi a kan tunaninsu. An yi haka ne saboda gaskata maganar Hausawa da
suke cewa: “Karen da ya yi cizo da gashinsa ake magani.” Sakamakon haka,
an ɗora wannan nazari a kan tunanin Hausawa da suke cewa: “Kowa da haɓarsa yake tagumi.” An ɗora shi a kan wannan
fahimtar ne bisa hasashen cewa, masu gudanar da sana’ar sun dogara da ita, kuma
tana biya musu buƙatunsu gwargwado. Wannan ya nuna hikimar Hausawa da sukan ce, “ƙaramin goro ya fi babban
dutse.”
Asalin Sana’ar Gyartai
Gano haƙiƙanin lokacin da aka fara sana’ar gyartai abu ne mai wahala, saboda daɗewa da aka yi ana amfani da
kayan amfanin gida dangin ƙwarya. Duk da haka, Sankalawa (2024) yana da ra’ayin
Hausawa sun samu fasahar ɗinkin ƙwarya ne daga wurin Buzaye[1]. Kodayake Bunza (2025)[2] yana ganin Hausawa ne suka fara
wannan sana’a, sauyawar yanayi ne ya jawo Buzaye suka fi su yawa a cikin masu
gudanar da ita. A tunanin wannan takarda, sana’ar feƙe ita ce ta haifi ta
gyartai. Wannan ya nuna fasahar ɗinkin ƙwarya Hausawa ne suka samar
da ita, musamman idan aka dubi waɗannan dalilai:
i. An yi hasashen cewa a faɗin Afirka garin Gummi na jihar Zamfara ne ya fi kowane
gari noman ƙwarya. Babu tantama kuwa, Gummi garin Hausawa ne da yake ƙarƙashin daular Zamfara. Shi ne
ya sa aka yi hasashen cewa, wurin da aka yi fice da noman ƙwarya nan ya kamata a samu
fasahar gyaran ta idan ta tsage ko ta fashe. Domin ko ba komai, wurin da aka
san darajar goro nan akan lulluɓa masa ganye.
ii. Bunza, (2025) ya tabbatar da cewa, ƙasar Amurka sun nuna cewa,
irin ƙwarya ya isko su shekaru dubu goma (10,000) da suka wuce. Don haka ya yi
hasashen daga Gummi ne irin ƙwarya ya bi igiyar ruwa zuwa ƙasar Amurka.
iii. Haka kuma, bayyanar ƙwarya da dangoginta a dabin Bahaushe ta tabbatar da cewa,
Hausawa sun ɗauki lokaci mai tsawo suna amfani da ita. Don haka wurin da ake amfani da
ita nan ya kamata a samu fasahar ɗinke ta idan ta fashe.
iv. Samun wasu ɓangarori na sana’ar gyartai a cikin mahaɗin maganin Bahaushe wata
hujja ce da take tabbatar da maganar masu hasashen sana’ar ta Hausawa ce.
v. Bayyanar sana’ar gyartai a cikin camfi da barkwancin Bahaushe shi ma abin
dubawa ne matuƙa, musamman ga mai laluben tushenta.
Domin laluben tushen sana’ar gyartai, an dubi wasu ɓangarori na adabi da na
al’ada saboda kasancewarsu rumbun adana fasahohin Hausawa.
Muhalin Sana’ar Gyartai a Wasu Sassan Adabi
Ɗangambo (1984:1) da Yahaya
da wasu, (1992:1) da Bunza, (2003:15) da Mustapha (2018:271) da Kumbashi,
(2018:43) duka bayanan waɗannan manazarta yana tabbatar da cewa, adabi wani ɓangare ne na fasaha da yake
nuna hoton rayuwar al’umma. Wannan takarda ta yi ƙoƙarin fito da jirwayen
sana’ar gyartai a wasu sassa na adabin baka. A wannan muhalli an waiwayi
jirwayen sana’ar gyartai a cikin sassan adabi na kirari da kuma karin magana.
Jirwayen Sana’ar Gyartai a Cikin Kirari
Ma’anonin da Ɗangambo, (1984:42) da Junaidu da ‘Yar’aduwa, (2007:89) da
Gandu, (2012:42) da Kumbashi, (2018:107) suka bayar dangane da kirari, ana iya
bayyana ma’anarsa da cewa, tsararriyar magana ce ‘yar doguwa ta hikima da akan
shirya ta musamman don kambama mutum ko wani abu. Kodayake, wani lokaci kirari
yakan ɗauki yabo ga abin da ake wa. Wani lokaci kuma yabon yakan zo da wata siga
wadda a zahiri ba ta nuna yabo. Irin wannan kirari ana yi wa ‘yan tauri da
dangoginsu. Idan aka dubi kirarin da ake yi wa ‘yan tauri cuɗanye yake da wasu abubuwa waɗanda a zahiri ba yabo ba ne.
Daga cikin kirarin da ake yi wa sana’ar gyartai akan ce:
“Gyartai, gyarta ɓari mugunyar sana’a; daga gare ki sai dai a yi sata.” Wannan kirari bai
kalli sana’ar gyartai da kima ba. Hasali ma, ya dube ta a matsayin ƙasƙantacciya. Sakamakon haka,
masu gudanar da sana’ar suka juya wannan kirari kamar haka: “Gyartai,
gyarta ɓari kyakkyawar sana’a; daga gare ki sai dai a yi samu.”
Jirwayen Sana’ar Gyartai a Cikin Karin Magana
Karin magana wani ɓangare ne da yake nuna
hikimar Hausawa inda sukan yi amfani da basirarsu su dunƙule magana mai faɗi zuwa taƙaitacciya mai ma’ana.
Bayyanar sana’ar gyartai a cikin karin magana wata alama ce da take nuna daɗewarta a ƙasar Hausa. Wasu daga cikin
karin maganar Hausawa masu alaƙa da sana’ar gyartai waɗanda suka shahara sun haɗa da:
i. Ban da tuna baya, gyartai ya ci sarauta
ii. Kada ciko ya biyo gyartai
iii. Tsiya ɗinkin ludayi
Duka waɗannan karin maganganu suna kallon gyartai a matsayin ‘yar
autan sana’ar Hausawa. An manta da cewa, lomar arziki ta fi kaɓakin tsiya.
Sana’ar Gyartai a Mahangar Al’adun Hausawa
Al’ada dai tana nufin dukkanin rayuwar ɗan’adam tun daga haihuwa har
zuwa kabarinsa (Bunza, 2006: xxxii). Duk da cewa, masana suna nazarin al’ada ta
fuskar yanayi zuwa ɓangarori guda uku. Wadda ake aiwatarwa da gaɓɓai da wadda ake furtawa da
baki da kuma wadda ake ƙudurtawa a zuci. Wannan takarda ta lalubo wasu ɓangarori na al’ada waɗanda sana’ar gyartai take da
ruwa da tsaki cikinsu.
Wasan Barkwanci
Idan aka kalli wasan barkwanci a wurin Hausawa, wata kafa
ce da take ƙara bunƙasa zaman lafiya tare da inganta danƙon zumunci. Don haka Galadanchi da wasu, (1990) suka kalle shi a matsayin: “Salon magana ne wanda mai magana kan sarrafa harshensa
ta yadda mai sauraron sa zai yi raha har ma wani lokaci ya yi dariya.” Masu sana’ar Gyartai suna wasan barkwanci da masu sayar da robobi da kuma
masu tallan rariya. Daga cikin wasannin da sukan yi wa juna akwai:
Gyartai ga mai
tallen roba: Ku ba ni irin roba na shuka.
Mai tallen rariya
ga Gyartai: Dole dai ba a yi sai da matankaɗi
Gyartai ga mai
tallan rariya: Ana yi da ƙwarya mana.
Camfi
Shaharar camfi a wurin Hausawa, shi ne ya sanya ya shiga
cikin lungu da saƙo na al’adunsu. Idan aka dubi ma’anonin da Mu’az (2005:6) da Bunza,
(2006:60) da kuma Magaji, (2020:174) suka bayar game da camfi ana iya taƙaita su ta hanayar bayyana
shi da, wani ƙagaggen bayani ne a kan wani abin da za a yi, ko kuma abin da zai faru da
ya ƙaunshi sakamakon aikin wanda yakan iya zama mai kyau ko akasin haka.
Misalin camfin da Hausawa suke gudanarwa wanda ya shafi sana’ar gyartai shi ne:
i. Shan ruwan da gyartai ya rage yana kawo arziki ƙwarai.
Hikimar da take cikin wannan camfi ita ce, Hausawa suna
koyar da tarbiyar girmama sana’ar da mutum yake gudanarwa kowace iri ce.
Sakamakon ba a san tafkin da zai makara da ruwa ba. Domin sun yarda da
cewa, ƙaramin goro ya fi babban dutse.
Mahaɗin Magani
Kowace al’umma ta duniya tana da wasu hanyoyi da take
amfani da su domin magance cututtukan da suka addabi mutane na sarari da
na ɓoye. Wasu daga cikin magungunan da ake amfani da su domin daƙushe cututtuka ana samun su
ne ta hanyar tsirrai da itatuwa da ganyaye da kuma saiwoyi da sauransu. Wasu
magungunan kuma ana samun tushensu ne daga wasu sana’o’i na al’umma. Tunanin
Hausawa ya aminta da cewa, ana haɗa wasu magunguna na biyan buƙatun zuciya da wani ɓangare na saana’ar gyartai.
Wasu daga cikinsu sun haɗa da:
i. Idan aka sha ruwan da gyartai yake jiƙa akwara tare da wasu abubuwa da ake haɗawa da su yana tsayar da
cutar juwa (hajijiya).
ii. Haka kuma, mata suna amfani da sauran ruwan da gyartai yake jiƙa akwara da shi domin yin
wasu magunguna.
Kayan Aikin Sana’ar Gyartai
Kamar kowace sana’a ta Bahaushe, ana gudanar da aikin
gyartai ta hanyar amfani da waɗannan kayan aiki:
i. Akwara/ashuta: Saiwar kaba ce da ake tonowa a ƙasa, musamman wurin da ƙasa take da laushi. Idan an
tono akan tsaga ta yadda ake buƙata sannan a shanya ta bushe, daga nan sai a naɗe a sanya a cikin kurfi. Duk
lokacin da za a fita aiki, sai a sanya mata ruwa saboda ta jiƙa ta yi laushi yadda ake buƙata.
ii. Kurfi/ɗunki: Ƙaramin ƙarfe ne siriri wanda ya ɗara allurar ɗinkin kaya yana da tsini. Ana yi
masa ƙota (ɓota) daga ƙasansa domin a samu sauƙin amfani da shi. Ana amfani da shi wajen huda ƙwaryar da ta tsage ko kuma
ta fashe domin a samu damar ɗinke ta.
iii. Gora: Wani madaidaicin mazubi ne na duma da ake fafe samansa sannan a yi
masa maɗauri a gefensa. A cikin gora ne gyartai yake zuba akwara, saboda gudun
bushewa.
iv. Jaka: Wata ƙaramar mazubin kayan aiki ce da ake ratayawa a kafaɗa. Gyartai yana amfani da
ita domin zuba kayan aiki da kuɗi, wani lokaci ma yakan zuba wani abu na ci dangin abinci
kamar ƙuli-ƙuli da alawa da sauransu.
Yanayin Yadda Ake Gudanar da Sana’ar Gyartai
Ga ala’ada, mai sana’ar gyartai yana samun jaka ya rataya
a kafaɗarsa. Yakan sanya kurfi da kuma ‘yan kuɗaɗensa a ciki (wani lokaci).
Yana tafiya riƙe da gora (kuttu) sanye da akwara a ciki. Galiban idan ya fito yakan sanya
ruwa a cikin kuttun saboda akwarar da take ciki ta jiƙu sosai ta yi laushi ta
yadda za a ji daɗin amfani da ita. Ga al’ada, mai sana’ar gyartai yana yawo ne
shiyya-shiyya, wasu kuma sukan zauna a cikin kasuwa wurin masu sayar da ƙorai ko kuma wurin masu
aikin feƙe (heƙe). Wanda yake yawo, yana tafiya yana bayyana wa al’umma cewa:
: Gyartai,
: Kowak kashe ta kawo,
: Mai hankali ta aza bisa rumfa.
: Gyartai,
: Ga mai gyartai ya zo,
: Wadda ta kashe ta
kawo.
Daga lokacin da mata suka jiyo wannan murya, sai su fito
da ƙorensu (ko wasu kayan aiki dangin ƙwarya kamar ludayi da gyanɗama) da suka fashe, domin
ya ɗunke musu. Galiban mai sana’ar yakan samu ƙarƙashin wani itace ko ƙofar wani gida mai yalwa
wanda ba zai takura ba, ya riƙa gudanar da sana’arsa. Idan ya kammala ayyukan da aka
tara masa sai ya yi gaba, sai kuma wani lokaci. Ga al’ada, gyartai yakan gyara
dukkanin nau’o’in mazubi dangin duma da ya fashe ko ya tsage. Misalin kayan da
suke gyarawa sun haɗa da: Ƙwarya da gora da gyanɗama da zunguru da sauran abubuwa da dama.
Ga tsarin sana’ar, gwargwadon girman fashewar ƙwarya shi yake nuna kuɗin da za a biya na gyaran
ta. Masu gudanar da sana’ar ba su da tsarin sarauta ko na shugabanci nasu
na ƙashin kansu; sai dai suna tafiya da tsare-tsaren ƙungiyar masu sayar da ƙwarya da na masu sana’ar feƙe a mafiya yawancin
kasuwanni[3]. Aikin gyartai dai yana cikin masu yi wa
mutane hidima idan aka kwatanta sana’ar da rukunonin sana’o’in da Alhasan da
wasu (1982: 39) suka yi.
Ɗabi’un
Masu Sana’ar Gyartai
Wasu daga cikin ɗabi’un masu sana’ar gyartai
da wannan takarda ta iya ganowa sakamakon ziyartarsu da kuma mu’amalar da aka
yi da su sun haɗa da:
i. Suna da juriyar zama babu kuɗin kashewa a tattare da su.
ii. Suna da ƙoƙarin
tattalin abin da yake hannunsu.
iii. Rashin surutu, sun fi mayar da hankali a kan ayyukansu, musamman idan suna
gudana.
iv. Rashin kasala, shi ne ya sanya suke bin shiyoyi ba tare da ƙosawa ba.
v. Sha’awar cin abincin da ba shi da nauyi
vi. Dangana da yanayin da aka samu kai[4].
Dangantakar Sana’ar Gyartai da Wasu Sana’o’i
Sana’ar gyartai tana da alaƙa walau ta kusa ko ta nesa
da wasu sana’o’in. Misali, sana’ar noma da kuma ta feƙe (heƙe) suna da alaƙa da ita. Sakamakon manoma
su ne suke noma ƙwarya da dangoginta. Idan ba su noma ƙwarya ba babu abin da masu
sana’ar heƙe da gyartai za su yi. Wannan dalili ya sa a kasuwanni ma suke bin tsarin
shugabanci guda da masu sana’ar heƙe, inda sukan zaɓi mutum guda a cikinsu ya zama shugaba.
Su kuwa masu sana’ar heƙe su ne suke yi wa ƙwarya da dangoginta zane-zanen ado na ƙawa. A ɓangare ɗaya kuma, akwai sana’o’in da
sana’ar gyartai take taimaka musu a kaikaice. Misalin irin waɗannan sana’o’i sun haɗa da, sussuka da su (makun
kifi) da sauransu. Ga alama, sana’ar ba ta samu gatan samun muƙamin sarauta kamar yadda
sauran sana’o’i irinsu fawa da su da wanzanci suka samu ba. Wannan bai rasa
nasaba da irin kallon da ake wa sana’ar na zamowarta ‘yar auta cikin sana’o’in
Hausawa.
Gudunmawar Sana’ar Gyartai ga Al’umma
Gudunmawar da sana’ar gyartai take bayarwa ga al’umma sun
haɗa da:
i. Rayar da al’adun Hausawa na dogaro da kai ta fuskar sana’a.
ii. Bunƙasa tattalin arzikin waɗanda suka rungume ta.
iii. Samar da aikin yi ga al’umma.
iv. Taimakawa ta fuskar tattalin kayan amfanin gida dangin ƙwarya waɗanda suka haɗa da, ƙoƙo da gora da masaki da
zunguru da gyanɗama da ludayi da kuma mara da sauransu.
v. Fito da ɗabi’un Hausawa na dangana da yanayin da aka samu kai.
Barazanar Zamani a kan Sana’ar Gyartai
Cigaban zamani ya yi nisa wajen yi wa sana’ar gyartai
barazana. Daga cikin abubuwan da wannan takarda ta hango a lokacin da ta kai
ziyarar rangadin bincike wurin masu gudanar da sana’ar gyartai akwai:
i. Raguwar amfani da ƙwarya, inda aka koma ta’ammali da roba.
ii. Amfani da zaren roba/ robar Bature (ramar roba) maimakon akwara.
iii. Ƙamfar masu gudanar da aikin
gyartai, saboda yanayin sana’ar a yau ba za ta iya biyan buƙatun rayuwar masu gudaar da
ita ba.
iv. Ƙamfar samun aiki, saboda
al’umma sun karkata wajen amfani da roba maimakon ƙwarya da dangoginta.
v. Cigaban zamani ya sanya masu ɗinkin roba, sun fara maye gurbin sana’ar gyartai. Hakan ya sanya suke ɗinke robar da ta tsage, kamar yadda
gyartai yakan yi wa ƙwarya[5].
Dalilan Koma Bayan Sana’ar Gyartai a Ƙarnin
da Muke Ciki
Haƙiƙa ƙarnin da muke ciki na 21 ya zo da fasahohin zamani waɗanda sukan iya zama barazana
ga wasu sana’o’in. Duk da cewa, ana ganin fasahohin a matsayin ci gaba, amma
hakan bai hana ɗaliban ilimi su dube su da idanu biyu ba. Wato, ido ɗaya ga kifi guda ga bado,
saboda ko ba komai, guntun gatarinka ya fi sari ka ba ni. Wannan takarda tana
da ra’ayin cewa, wasu daga cikin dalilan da suka jawo sana’ar gyartai take
neman salwanta sun haɗa da:
i. Koma bayan da ake samu ta fuskar noman ƙwarya saboda matsalolin
tsaro da ya riski yankunan da suka yi fice ya taimaka wajen daƙushewar wannan sana’a.
Sakamakon sai ƙwarya ta yawaita, mai sana’ar gyartai zai samu aikin yi.
ii. Ƙamfar amfani da ƙwarya da dangoginta a
matsayin muzubi, saboda ɓullar na roba.
iii. Ƙarancin kuɗin shigar da ake samu daga
sana’ar gyartai, wata barazana ce da take nuna nan gaba kaɗan za a yi bankwana da ita.
Idan aka yi la’akari da kuɗin shigar da ake samu daga gare ta, ba za a iya rayuwa a
kan sana’ar ba a yau.
iv. Yawaitar amfani da roba maimakon ƙwarya yana nuna sana’ar ta
fara ja da baya. Dalili kuwa shi ne, idan babu ƙira mai zai ci gawayi?
v. Ƙamfar saiwar kaba, saboda haɗarin da yake cikin shiga
dazuka a wannan lokaci, shi ne ya sanya ake gudanar da sana’ar da rama bature
(roba). Wannan ya sanya mafiya yawa daga cikin masu amfani da ita ba sa so,
saboda ingancinta bai kai na akwara ba.
Sakamakon Bincike
Sakamakon binciken da wannan takarda ta gano su ne:
i. Sana’ar gyartai tana ɗaya daga cikin tsofaffin sana’o’in da suka daɗe ana gudanar da su a ƙasar Hausa.
ii. Sana’ar ta samu shiga cikin adabin Bahaushe, kamar yadda take da gurbi a
wasu ɓangarori na farfajiyar al’adun Hausawa.
iii. Hausawa suna yi wa sana’ar gyartai kallon ƙaramar sana’a, wadda mai
gudanar da ita ba ya samun kuɗin shiga mai gwaɓi.
iv. Sana’ar gyartai ta fara ja da baya matuƙa, saboda yawaitar kayan
amfanin gida na zamani.
v. Rashin samun kuɗin shiga mai gwaɓin daga sana’ar, yana daga cikin dalilin da take samun koma baya musamman a
wannan lokaci da yanayin gudanar da harkokin rayuwa suka ƙara tsada.
Kammalawa
Daga abin da ya bayyana a wannan takarda, Hausawa
sun ɗauki lokaci mai sawo suna gudanar sana’ar gyartai, don haka ta shiga cikin
adabinsu da al’adunsu. Sana’ar ta bayar da gudunmawa ta fuskar tattalin wasu
daga cikin kayan aikin gidan Bahaushe, sannan kuma tana taimaka wa sana’o’in
sussuka da su (kamun kifi) a kaikaice. Duk da daɗewa da Hausawa suka yi suna
gudanar da sana’ar gyartai, tana fuskantar barazanar zamani a wannan ƙarni da muke ciki. Manyan
abubuwan da suke janyo wa sana’ar barazana a ƙarni na ashirin da ɗaya sun haɗa da, rashin samun kuɗin shiga mai yawa wanda zai
iya ɗaukar ɗawainiyar rayuwar masu gudanar da ita da ta iyalansu. Yawaitar amfani da
robobi da sauran kayan aikin gida na zamani maimakon ƙwarya da aka saba da ita a
baya, babbar barazana ce a gare ta. Haka zalika, ɓullar wasu sana’o’i da suka
fi sana’ar gyartai kawo kuɗin shiga, suna daga cikin abubuwan da suke mata barazana
a wannan ƙarni da muke ciki na ashirin da ɗaya. Duk da kallon da wasu al’umma suke
wa gyartai na ‘yar autan sana’ar Bahaushe, akwai ragowar mutanen da suke
gudanar da ita a matsayin wata hanya da take agaza wa rayuwarsu, baya ga
sana’o’in noma da kiwo da suke aiwatarwa. Wannan ya nuna irin hikimar Bahaushe
wadda ta yi daidai da tunanin magabata da ke cewa: “Kowa da haɓarsa yake tagumi,” sannan
kuma, “sana’a goma ita ce maganin mai gasa.”
Manazarta
Abdulkadir, D. (2002). “Sarrafa Kaba.” Cikin
Bichi, A. Y. , Kafin-Hausa, U. A. da Yalwa, L D.(Editoci). Studies
in Hausa Language, Literature & Culture. The Fith Hausa International
Conference, Pp. 427-442. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Alhassan, H., Musa, U.I. da Zarruƙ, R. M. (1982). Zaman
Hausawa Bugu na Biyu. Lagos: Islamic Publication Bureau.
Bunza, A. M. (2003). “Hoton Buzu a Adabin
Bahaushe.” Maƙalar da aka gabatar a taron haɗin guiwa tskanin Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato da
Jami’ar Abdulmumini, Yamai, Jamhuriyar Nijar.
Bunza, A. M. (2006). Gadon Feɗe
Al’ada. Lagos: Tiwal Publications Limited.
Bunza,
A. M. (2019). Ƙwarya a Farfajiyar Adabi da Al’adun
Bahaushe. Cikin East African Scholars Journal of
Education, Humanities and Literature, 2 (12), 720–727. ISSN 2617-443X.
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya
(2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu
Bello University Press.
Ɗangambo, A. (1984). Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga
Rayuwar Hausawa. Kano: Maɗaba’ar Triumph, Gidan Sa’adu Zungur.
Ɗangambo, A. (2008). Rabe-raben Adabin Hausa (Sabon Tsari).
Zaria: Amana Publishers Limited.
Daura, H. K. (2013). “Sana’a Sa’a: Ci Gaban
Sana’ar Noma Ta Fuskar Sarrafa Tsirrai.” Cikin Yelwa, D. L. Et al
(editoci). Ist National Conference Proceeding Pp. 846-853. Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano.Zaria: Ahmadu Bello University.
Galadanchi,
M. K. M. da Wasu, (1990). Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare Na 1. Zaria: Longman
Nigeria Ltd.
Gandu, I. M. (2012). “Matsayin Kirari Cikin
Waƙoƙin Jarumta na Muhammadu
Bawa Ɗan’anace da Ya Yi wa Shago.” Cikin Ɗunɗaye
Journal of Hausa Studies, Vol.1, No. 5, Pp.41-55. Department
of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
Garba,
C.Y. (1991). Sana’o’in Gargajiya a Ƙasar Hausa.
Kaduna: Baraka Press
and Publishers Limited.
Junaidu, I. da ‘Yar’aduwa, T. M.
(2007). Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Manayan Makarantun
Sakandare. Zaria: Spectrum Books Limited
Kumbashi, I. N. (2018). “Adabi Mabuɗin Al’ada: Tsokaci a kan
Al’adar Baƙunci a Adabin Hausa.” Kudin Digiri na Biyu. Sakkwato: Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Madabo,
M. H. (1979). Ciniki da Sana’o’i a Ƙasar Hausa. Ibadan: Printed in Great
Britain Thorbay Press Limited Rayleigh Essex.
Magaji,
A. (2020). “Camfin Hausawa a Matsayin Rigakafin Magani.” Cikin Ɗunɗaye
Journal of Hausa Studies, Vol. 2, No.3, Pp.173-182. Department
of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
Maidabino, I. B. (2024). “Nazarin Wasu Ƙananan Sana’o’i Domin
Matasan Jihar Katsina.” Cikin Himma Journal of Contemporary Hausa
Studies, Vol.9, No.1, Pp.186-196. Department of Nigerian Languages,
Umaru Musa ‘Yar’adua University, Katsina.
Mu’az, A. H. (2005). “Camfi a Cikin Akushin
Bahaushe.” Kundin Digiri na Ɗaya. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Muhammad, M. S. (2019). Sana’a Sa’a. Kaduna:
Gado da Masu Communications.
Muhammad, M. S. (2020). Bahaushiyar
Al’ada. Kano: Bayero University Press.
Muhammad, U. I. (2021). Tsakure Cikin
Al’adun Hausawa da Adabin Gargajiya. Kano: Gidan Dabino Publishers.
Mustapha, S. (2018). “Tarken Adabin Hausa
a Ƙarni na 21: Tsakanin Matarkan Gargajiya da na Zamani.” Cikin Kadaura
Journal of Hausa Multi Discipliary Studies Vol.1, No. 4. Pp.271-286. Department
of Nigerian Languages and Linguistics, Kaduna State University, Kaduna, Nigeria.
Sanyinnawal, S. I. (2015). “Jirwayen
Sana’o’in Gargajiya a Adabin Bakan Bahaushe.” Kudin Digiri na Biyu. Sakkwato:
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Sharifai, B. (1990). “Take da Kirarin
Sana’o’in Gargajiya: Nazarin Ma’anarsu da Muhimmancinsu ga Rayuwar Hausawa.”
Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Yahaya, I. Y. da Wasu (1992). Darussan
Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare Juzi’i na 1-3. Ibadan:
University Press.
Yola, M. M. (2014). “Sana’o’in Hausawa na
Gargajiya da Tasirinsu a Zamanance.” Cikin Gusau, S. M. (editoci). Garkuwan
Adabin Hausa. A Festchrift in Tribute to AbdulƘadir Ɗangambo.
Pp. 507-514. Zaria: Ahmadu Bello University Press.
Yunusa, Y. (1989). Hausa a Dunƙule. Kano: Maɗaba’ar Triumph, Gidan Sa’adu Zungur.
[1] Hira da Malam Ɗahiru Hussani Sankalawa, Malami a Kwalejin Ilimi ta Tarayya
(FCET) da ke Gusau, Jihar Zamfara. Ranar 12/11/2024 a Harabar Jami’ar Usmanu
Ɗanfodiyo, Sakkwato.
[2] Hira da Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ta wayar hannu ranar Litinin,
27/01/2025 da misalin ƙarfe 08:30 na dare.
[3] Hira da Malam Abubakar Gyartai a kasuwar Kara da ke Sakkwato ranar
30/11/2024 da misalin ƙarfe 5:00 na yamma.
[4] An samu waɗannan bayanai ne a hirar da aka gudanar da Malam
Abdullahi Usman da ke Kasuwar Kara, Sakkwato ranar 06/02/2025 da misalin ƙarfe
3:20 na yamma.
[5] An cirato waɗannan bayanai daga tattunawar da masu bincike suka haɗa a
tsakanin Malam Abubakar Muhammadu da Malam Yahaya Sanda da kuma Malam Musa
Ɗandare a garin Shuni da ke Ƙaramar Hukumar mulkin Dange, Jihar Sakkwato, ranar
10/09/2025.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.