Citation: Adamu, A. I. and Adamu, F. U. (2025). “Nazarin Dabarar Mutuntarwa a wasu Waƙoƙin Siyasa na Hausa.” in Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 03, No. 02, Pp. 167 – 174. www.doi.org/10.36349/djhs.2025.v03i02.021.
NAZARIN DABARAR
MUTUNTARWA A WASU WAƘOƘIN SIYASA NA HAUSA
A’ishatu Isma’il
Adamu
Sashen Koyar da
Hausa, Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, Kumbotso, Kano
and
Fatima Uba Adamu
Kwalejin Ilimi da
Share Fagen Shiga Jami’a, Kano
Tsakure:
Wannan takarda mai takenNazarin
Dabarar Mutuntarwa a wasu waƙoƙin siyasa na Hausa,n rubuta ta ne da
niyyar fito da ire-iren hikimomi da basirar da mawallafan siyasa suke amfani da
su ta hanyar ɗaukar
abin da ba mutum ba su mayar da shi mutum domin su isar da saƙonsu
ga jama’a ta hanyar
hikima a cikin waƙoƙinsu na siyasa. A nazarin an yi amfani da waƙoƙi a ƙalla
guda goma sha biyu na mawallafa daban-daban waɗanda
suka yi amfani da wannan dabarar a cikin waƙoƙin. An ɗora
wannan takarda bisa hanyar nazari wadda Ɗangambo (2007) ya assasa a littafinsa na Ɗaurayar
Gadon Feɗe Waƙa. An
yi amfani da dabaru da hanyoyin wajen gudanar da wannan nazari waɗanda suka haɗa da samo waƙoƙin
daga hannun wasu mawallafan, an kuma samu waƙoƙin daga wasu kundayen bincike na ilimi a
matakai daban-daban a kuma rubuce. A nazarin an gano mawallafan sun yi amfani
da wannan dabarar ta hanyar yin amfani da wasu siffofi da darajoji da halaye da
sauransu da mutum kaɗai
aka sani da su a laƙaba wa wanda ba mutum ba ya zama mutum, domin su isar da saƙo ga
masu saurare ko karatu a cikin waƙoƙinsu. Haka kuma an yi nasarar fito da
ire-iren misalai na dabarar mutuntarwa ta hali da mutuntarwa ta siffa da
mutuntarwa ta daraja tare da yi musu sharhi. Har ila yau kuma, ana kyautata
zaton wannan nazarin zai zama jagora a kan abin da ya shafi dabarun jawo
hankali musamman na mutuntarwa a waƙoƙin siyasa a fannin adabin Hausa. Haka
kuma nazarin ya zamto jagora ga manazarta da ɗalibai
a ɓangaren rubutattun
waƙoƙi
musamman na siyasa a fannin adabin Hausa.
Muhimman Kalmomi:
Mutuntarwa, waƙoƙin siyasa, mawallafa
Gabatarwa
Dabarun jawo hankali dabaru ne da mawallafa suke
amfani da su domin su isar da saƙonsu a cikin waƙa ta hanyar
jawo hankulan jama’a zuwa ga manufa. Dabarar mutuntarwa na ɗaya daga
cikin dabarun da mawallafan ke amfani da ita a cikin waƙa ta hanyar
sarrafa hikimominsu da basirar da Allah Ya hore musu, su isar da saƙo ga masu karatu. Mawallafan sukan yi amfani da hikimarsu ta hanyar mayar
da abin da ba mutum ba ya zama mutum, sukan yi amfani da wasu halaye ko
darajoji ko siffofi da sauransu da mutum kaɗai aka sani da su a laƙaba wa wani abu marar rai da masu rai cikin azanci a waƙa, a kuma isar da saƙo cikin armashi.A wannan nazari an yi amfani da waƙoƙi na mawallafa daban-daban a waƙoƙin siyasa waɗanda aka fito
da misalansu tare da yi musu sharhi aƙalla daga waƙoƙin mawallafa guda goma sha biyu (12).
An duba wasu makusantan ayyuka waɗanda suke da alaƙa da
wannan nazari musamman ayyukan Birniwa (1987) da Ɗangambo
(2007) da Auta (2008) da Bunza (2009) da Adamu (2012) da Yahaya (2016) da
Abubakar (2017) da Bunguɗu (2017) da Bunza da Bunza (2018) da Adamu (2021)
dukkansu sun yi amfani da wannan dabarar a cikin ayyukansu, inda suka duba
dukkan sauran salon dabaru, wannan nazari kuwa ya bambanta da nasu, inda aka
duba dabara guda ɗaya ta mutuntarwa a kuma waƙoƙi daban-daban na mawallafa
daban-daban na siyasa, saɓanin nasu ayyukan.
Mutuntarwa
Masana da
manazarta sun bayyana mutuntarwa da cewa:
Mawaƙa kan yi amfani da wannan dabara
ne ta hanyar ɗaukar waɗansu halaye ko siffofi na bil-adama sannan sai a lanƙaya su ga wani abu wanda ba
mutum ba (Abba & Zulyadaini, 2000:122).
Mutuntarwa na
nufin mawaƙi ya ɗauki wasu halaye ko siffofi ko darajoji dasauransu da mutum
ne kawai aka sani da su, a laƙaba
wa wani abu marar rai ko dabba, ko tsuntsu ko ƙwaro da sauransu. Mutuntarwa ita ce mai da abin da ba mutum
ba ya zama mutum (Ɗangambo,
2007:45-46).
Ana yin mutuntarwa
ce ta hanyar samar da wani abu da ba mutum ba, a mayar da shi mutum ta fuskar
yi masa sunan mutane; ba shi darajar mutane ta magana ko hankali da sauransu,
sa masa rigar mutunci ta fuskar tafiya ko kuka ko dariya, ga su nan dai, ba shi
aiki irin na mutane kamar nema ko sarauta ko saye da sayarwa da makamantansu.
(Bunza; 2009:395)
“Jinsarwa da ake ɗora wa abin da ba mutum ba wata halayya ko darajar mutum”.
(Yahaya; 2016:102)
Mutuntarwa ita ce
a inda mawaƙi zai yi
amfani da fasaharsa a cikin waƙa
ya mayar da wani abu marar rai ko mai rai wanda ba mutum ba ya zama mutum ta
hanyar alaƙanta shi
da halaye da ɗabi'u irin na mutane. (Bunguɗu; 2017:98).
Mutuntarwa na
nufin a ɗauki wasu halaye ko darajoji da
sifofi da Ɗan’adamkawai
ya keɓanta da su a ɗora wa wani abu da ba Ɗan’adam
ba ya zama mutum (Adamu, 2021:120).
A taƙaice, a wannan nazari za a iya
kallon mutuntarwa da cewa, mutuntarwa ita ce a ɗauki
wasu siffofi da halaye da darajoji na mutum a laƙabawa abin da ba mutum ba, ya zama mutum.
Dabarun Gudanar
da Bincike
Kowane bincike na
ilimi akwai dabaru da hanyoyin da mai nazari ke bi wajen gudanar da shi. An ɗora wannan nazari bisa mazhabar Ɗangambo (2007) ta Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa.
Dabaru da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da wannan nazari sun haɗa da samo matanin waƙoƙin kai tsaye a hannun wasu
marubutan, an kuma samu wasu a cikin kundayen domin samun sauƙin nazari. An kuma karanta waƙoƙin an fito da baituka da sharhi kan layukan da aka sami
dabarar mutuntarwa.
Dabarar
Mutuntarwa a Waƙoƙin Siyasa
A wannan muhalli
an kawo misalai na dabarar mutuntarwa daga wasu waƙoƙi na mawallafa daban-daban na siyasa, inda aka kawo ire-iren
mutuntarwa kamar haka:
Mutuntarwa ta hali
da mutuntarwa siffa da mutuntarwa ta daraja.
Mutuntarwar
Siffa
A wannan muhalli,
an kawo misalan mutuntarwa ta siffa.
Siffa tana nufin
kama ko hanyar bayyana kamannin abu. (CNHN; 2006: 395).
Ga misalin wani
baiti, a waƙar PDP
farar uwa ta Misbahu Sale Ganuwa.
Aikin more rayuwar
al’ummarta
PDP ta ce akwai
shi a tsarinta
Jin daɗin al’umma shi ne burinta
Don haka dole ne ta tashi ta inganta, iye
(Musbahu Sale
Ganuwa, waƙar “PDP
farar uwa” bt: 10)
A wannan baitin
mawallafin ya yi amfani da wannan dabarar inda ya ɗauki wani abu da aka san mutum ne kawai ya keɓanta da shi ya ɗora wa jam’iyyar PDP inda ya
nuna jam’iyyar ta yi magana ta ce, wanda a zahiri ba a san wani abu da yin
magana ba, ballantana sunan jam’iyya ko alama ta jam’iyya. A nan ya yi amfani
da dabara ne don ya nuna irin ci gaba da irin daɗin
da za ta kawo wa al’umma.
Mawallafin waƙar “A mai da ruwa rijiya”,
Yahuza Sa’id Shinkafi, shi ma ya yi amfani da wannan dabarar kamar haka:
Daɗa PDP ta mutu wa zai mata likkafani
Ɗan MAS ne rayuwarta a Zamfara ke
ba ni
Sannan muke
tallata ta Kabiru Kilasik da ni
Yau mun koma gun
Yarima ba za mu ƙi babanmu
ba
(Yahuza Sa’id Shinkafi, waƙar “A mai da ruwa rijiya” bt:7)
A wannan baitin
mawallafin ya yi amfani da wannan dabarar, inda ya ɗauki wani abu da aka san mutum kaɗai ake yi wa sutura bayan ya mutu, wato likkafani, ita ce
suturar da ake saka wa mutum bayan ya mutu a saka shi a cikin ƙabari. A nan ya nuna jam’iyyar
adawa ta mutu murus, tun da ana neman wanda zai mata sutura, don haka a nan ya
nuna jam’iyyar adawa ba mai yinta.
A baiti na 15 a waƙar dai sai ya cigaba da faɗin:
Ciwon ajali in ya zo mun tabbata ba magani
PDP ta ƙanjame
ta kamu da ɗan zamani
To don haka ni na fita don ba ki macewa da ni
Tun da dai har MAS ya fita ba za ki bakwai
shida ba.
(Yahuza Sa’id Shinkafi, waƙar “A mai da ruwa rijiya” bt:15)
A nan mawallafin
ya ɗauki wani abu da aka san mutum
ne yake kamuwa da shi, wato ciwon ƙanjamau
ko sida, inda ya ɗauka ya ɗora wa jam’iyyar hamayya ya nuna cewa ta mutu, wato wani
zazzafan ciwo ne da yake kama mutum, wanda idan mutum ya kamu da shi sai dai
mutuwa, don haka ya ɗauki ciwon ya alaƙanta jam’iyyar adawa da shi don
ya nuna ta mutu, al’umma kuma ba su yin ta.
Haka ma a waƙar Garba Gashuwa ta “Mai
Dumi-Dumi”, ya yi amfani da irin wannan dabarar ta mutuntarwa mai nuna sifa, ga
yadda yace:
ANPP tana faɗa mana,
Kan noman rani da
damina,
Ta rarraba taki a
ko ina,
Ta gargaɗi masu yin kwana-kwana,
Da hakkin jama’a
su hau dumi-dumi.
(Garba Gashuwa, Waƙar “Mai Dumi-Dumi” bt: 14)
Mawallafin a nan
ya yi amfani da wannan dabarar ta mutuntarwa inda ya dauki wani abu da aka san
mutum ne kawai ya keɓanta da shi ya ɗora wa jam’iyyar ANPP, inda ya nuna jam’iyyar ta yi magana,
tana faɗa mana, wanda a zahirin gaskiya ba a
san wani abu dayin magana basai mutum, balantana sunan jam’iyya ko alamarta.
Don haka a nan ya yi amfani da wannan dabarar ne ta mutuntarwa don ya nuna irin
ci gaban da jam’iyyar zata kawo ga al’umma.
A waƙar Garba Gashuwa “Munafurcin
Karen Ruwa”, ya kuma yin amfani da wannan dabarar ta mutuntarwa mai nuna sifa,
inda yake cewa:
APP ta tashi tai kira,
Ta ko kira birni
da karkara,
Maza mu game kai
ban da yaudara,
Kar ka shigo mana
mai katoɓara,
Ka ya mutsa
al’umma gaba ɗaya.
(Garba Gashuwa, Waƙar “Munafurcin Karen Ruwa” bt:3)
A wannan baitin
ma, mawallafin ya yi amfani da irin wannan dababrar ta mutuntarwa inda ya kuma
nuna APP ta yi magana, wadda siffa ce ta Ɗan’adam
inda yake nuna ta yi kira. A nan ya yi amfani da dabarar ne don ya nuna
haɗin kai na ‘ya’yan jam’iyyar da
kuma nesanta ‘yan jam’iyyar adawa zuwa ga jam’iyyarsu.
Mutuntarwar Ta
Hali
A wannan muhalli
an kawo misalan mutuntarwa ta hali.
Hali yana nufin ɗabi’a musamman ta mutum (CNHN; 2006:191). Misali:
APC munafukar
jam’iyya ce
Ƙarya yaudara cikinta sukai
kwance
Shi kau cin amana
sam ba a zance
Ha’inci gurinsu
shi ko aƙida ce,
iye
(Musbahu Sale
Ganuwa, waƙar “PDP
farar uwa” bt: 20)
Haka ma a wannan
baitin mawallafin ya kawo irin wannan dabarar inda ya ɗauki wani hali da aka san mutum ne yake da shi, wato
munafurci, inda ya ɗauka ya ɗora wa abokiyar jam’iyyarsu ta adawa, wato ya kira ta da
munafuka. Ma’ana ya kira jam’iyyar da haka ne domin ‘yan cikinta suna munana wa
al’umma, inda suke nuna za su yi musu ayyuka, amma sai su noƙe, su ƙi cika alƙawarin da suka ɗauka. A nan ya zama akwai yaudara da ƙarya ta munafurci, don haka ya
kira ta da munafuka.
Shi ma Muhammad
Ali Gyaranya a waƙarsa ta
“Nijeriya a yau”, ya kawo irin wannan dabarar ta mutuntarwa kamar haka:
Al’ummar ƙasata ina ta kiran ku,
PDP ce take kishin
ku,
Ku zo ku bi ta za
ta kare haƙƙinku,
Dan manufarta alhairi ne.
(Muhammad Ali
Gyaranya, waƙar
“Nijeriya a yau” bt: 46)
Mawallafin, a nan
ya mutuntar da jam’iyyar PDP inda ya ɗauki wani hali da aka san mutum
ne yake da shi, ya ɗora wa jam’iyyarsu. A nan yana
kira ga al’umma da a zo a bi jam’iyyarsu ta PDP, inda yake nuna irin
manufofinta na alheri da kuma ci gaban da za ta kawo wa al’umma don ta kare haƙƙin kowa.
Haka ma a waƙar Lawan Inusa Gwarzo mai suna
“PDP Jam’iyyata”, ya yi amfani da wannan dabarar ta mutuntarwa, ga yadda yake
cewa:
PDP mai kyan nufi
che,
Du mai bin ta fa
ya yi dache,
Dan kuwa mai kyan tarbiya che,
Mai bin hanyar
gangara che,
Zuwa alkhairi ba
shari ba
(Lawan Inusa
Gwarzo, Waƙar “PDP
Jam’iyyata” bt:28)
A nan mawallafin
ya yi amfani da wannan dabarar ta mutuntarwa, inda ya ɗauki wani hali da aka san ɗan’adam
ne kaɗai yake da shi ya laƙaba wa jam’iyyar PDP inda ya
kira ta da mai kyan nufi da tarbiya, wato mutum aka sani da
wannan siffa. A nan yana tallata jam’iyyarsa ne ta wannan hanya domin ya nuna
wa al’umma irin nagartarta cikin hikima don ya isar da saƙonsa.
Mutuntarwa Ta
Daraja
A wannan muhalli
kuma an kawo misalan mutuntarwa ta daraja. Daraja tana nufin ɗaukaka ta muƙami
musamman ga mutum ko ɗaukaka ta kuɗi ga wani abu kamar zinariya ko girmamawa misali bin wani
(CNHN; 2006:97). Misali:
PDP uwa ce ta
jam’iyyarmu ita ya fito,
Jam’iyyar talakawa
wadda ta zamo sha ambato,
Me nufin khairi
gun mu ce da kyakkyawan zato,
Ba nufin rushe
rayuwar talaka tai ba.
(Musbahu Sale
Ganuwa, waƙar,
“Watan Bakwai” bt. 15)
A wannan baitin
mawallafin ya mutuntar da jam’iyyar PDP inda ya ɗauki
daraja ta uwa ya ba ta. A nan yana nuna irin darajar da jam’iyyarsu take da ita
ta kulawa da ‘ya’yan cikinta da kuma kyautata musu.
A waƙarsa ta “PDP Farar uwa”
mawallafin dai ya yi amfani da wannan dabarar ta mutuntarwar daraja, ga yadda
ya kawo a baitin:
Waƙata
a nan nake son tsaida ta
PDP farar uwa ne sunanta
Farko ta zamo akwai wasu danginta
Sai mun rushe jam’iyyar merger kwata iye.
(Musbahu Sale Ganuwa, waƙar “PDP Farar Uwa”, bt: 39)
Idan aka kalli
wannan baitin za a ga mawallafin ya yi amfani da wannan dabarar, inda ya ɗauki jam’iyyar PDP ya mutuntar da ita, ya mayar da ita
“uwa”, wato uwar ma fara. Ma’ana a nan yana nuna kulawa da darajar jam’iyyar
take da wajen kulawa da hidima da ɗaukar ɗawainiya sosai da take yi wa magoya bayanta, don haka ta
amsa sunanta na “farar uwa” yana kuma daɗa nuna darajarta da nuna
fifikonta a wajen al’umma fiye da abokiyar adawa inda yake ganin ta zo ƙarshe sai sun rushe ta, saboda
kulawa da hidimar tasu jam’iyyar a wajen al’umma.
Haka shi ma
mawallafin waƙar “Ku
Casu”, ya yi amfani da wannan dabarar, inda yake cewa:
PDP uwa babu zobe
Ko babu a yau ai
da gobe
Ko yanzu za a yi
zaɓe
Mu ne za mu ka da
su zaɓe
Har tsoho su je
sui ta dambe lallai
(Shu’aibu Usman
Maikokara, waƙar “Ku
casu” bt: 30).
Idan aka kalli
wannan baitin ma mawallafin wannan waƙar
ya yi amfani da wannan dabarar inda ya mutuntar da jam’iyyar PDP ya mayar da
ita uwa wadda babu zobe, wato uwa wadda bata taɓa
yin kyauta da wani abu ta kuma koma ta kwace. Wato dai ita ce wacce take haifar
ɗa kuma ba ta haifar sa ta ce ba
ta haifa ba, sannan kuma ba ta yi wa ɗa kyauta ta ce ta ƙwace. A nan ya ɗauki hali da daraja ta uwa ya ɗora
mata saboda irin hidima da ɗaukar nauyi da kulawa da za ta
yi wa al’umma wadda babu tauye wani abu, za ta bayar da cikakkiyar kulawa ta
komai da komai.
Haka shi ma
mawallafin waƙar “Sai
Musa”, ya yi amfani da wannan dabarar ta mutuntarwar daraja, inda yake faɗin:
PDP babbar uwa ce
jam’iyar maza da mata,
Sannan uwa ce maba
da mama dan ba ta ƙin duk ɗiyanta,
Kuma ta kula da haƙi na kowa dukka jihohinta sun
banbanta,
Domin ta bai wa ɗiyanta ‘yanci PDP tai mana daidai.
(Shehu Galan, waƙar “Sai Musa” bt: 17)
A wannan baitin
mawallafin ya ɗauki daraja ta girma ya mutuntar
da jam’iyyar PDP da “uwa”, uwar ma kuma babba wadda ta haɗa komai da komai wajen kulawa da cikkaken ɗaukar nauyi da ɗawainiya da ta yi ga kowa a duk
jihohin ƙasar nan,
wato ta kula da duk magoya bayanta a duk faɗin
ƙasar nan don haka ya kuma
mutuntar da ita da “uwa maba da mama”, wato mai cikakkiyar kulawa da hidima da ɗaukar nauyin al’umma, wato magoya bayanta.
Haka shi ma mawallafin waƙar “Ba Na
Shakka”, ya yi amfani da wannan dabarar ta mutuntarwar daraja, inda yake cewa:
'Yan Kudu har Arewa mun zaɓi farar uwa,
Peoples Party ƙasarmu bana ta zamo ƙoƙuwa,
Yau kaf Najeriya mu ta haɗa ba ta garkuwa,
Ita ce jirgin fitar shiga bana a
haye ruwa,
APP is the best head of Nigeria.
(Aminu Ibrahim Ɗandago, Waƙar “Ba Na Shakka”, bt:14)
A nan mawallafin ya ɗauki daraja da siffa ta uwa ya mutuntar da jam’iyyar APP
a matsayin wadda suka zaɓa. Wato ya ba ta daraja ta uwa, ya kuma siffanta da
“fara”. Farar uwa dai, wato mai kulawa da ‘ya’yanta da ɗaukan
dukkan nauyin ɗawainiyarsu da kuma son ci gabansu. To haka ma jam’iyyar
za ta kula da ‘ya’yan cikinta wato mai kulawa da ‘ya’yan cikinta, wato magoya
bayanta.
A baiti na 15 ya kuma faɗin:
Hausawa mun rabauta tun da ana so a ga,
Mun samu abinci ga kuɗi da baraden shiga,
Ba mai mana yatsina da yanga yau ga da ga,
Mun samu uwa da za mu nuna mu yi
burga,
A dukkanin duniya a gan mu muna dariya.
(Aminu Ibrahim Ɗandago,
Waƙar “Ba Na Shakka”, bt:15)
A wannan baitin, mawallafin ya sake mutuntar da jam’iyyar da “uwa” a
matsayin wadda za a ji daɗi da ita, inda ya kwatanta ta da darajar uwa a matsayin
wadda za su yi alfahari da ita na irin ɗawainiyar
da uwa za ta yi wa ‘ya’yanta.
A dai waƙar ya ƙara da cewa:
Farin al’amari a inda duk
yake malam shigo,
Tutarmu ku duba wadda babanmu ya tattago,
Shi da abokan zubinsa naku na san ba rago,
Na yarda na bi ka tun da babu gara
ba zago,
APP ce ƙasa ta
cancanta sarauniya.
(Aminu Ibrahim Ɗandago, Waƙar “Ba Na Shakka”, bt:28)
A nan mawallafin ya mutuntar da jam’iyyar APP inda ya kwatanta ta da
“sarauniya”, wato mai mulki wadda ya kamata al’umma su zaɓa
dangane da iya mulkinta.
Shu’aibu Usman Maikokara shi ma a tasa waƙar “Jiki Magayi”, ya yi amfani da wannan dabarar ta
mutuntarwa inda yace:
Jam’iyr PDP uwa
ma ba da mama
Ga shi ta bar
mulki duk ƙasarmu
ta suma
Duk masoyin maja
gabanmu ya zama kurma
Da suna zaga
guri-guri suna gulma
Yanzu ta ƙare jam’iyarmu tai musu ƙofi.
(Shu’aibu Usman
Maikokara, waƙar “Jiki
Magayi” bt na 9).
A wannan baitin
mawallafin ya ɗauki daraja ta uwa ya
mutuntar da jam’iyyarsa ta PDP. Wato ya ba ta daraja ta uwa, wato mai
kulawa da ‘ya’yanta da dukkan nauyin ɗawainiyarsu da kuma son
cigabansu. To haka ma jam’iyyar ta kula da ‘ya’yam cikinta, wato magoya bayanta
a lokacin da ta yi mulki, saɓanin jam’iyyar adawa a wannan
lokaci da ba ta taɓuka komai. Haka ma a ɗango na biyu ya kawo mutuntarwa inda yake nuna cewa ƙasarmu ta suma saboda ba jam’iyyarsa ce ta PDP
ke mulki ba, don haka a nan yake nuna ana cikin wahala a ƙasa. Ya kuma cigaba a ɗango na uku, inda ya ƙara
kawo wata mutuntarwa yana nuna jam’iyyarsu ta maja ta zama kurma. Ma’ana basa
son su ji abin da jam’iyyar adawa ke yi. Saboda ba jam’iyyarsu ce PDP take
mulki ba.
A waɗannan baitoci da aka kawo an ga yadda ake ɗaukar wani abu wanda aka san mutum ne kawai ke da shi a ɗora wa wani abu daban da ba mutum ba, a nuna mutum ne shi,
wato a mutuntar da shi.
Kammalawa
Kamar yadda bayanai suka gabata a wannann nazari, an yi nazarin dabarar
mutuntarwa a wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin siyasa na Hausa. An ga yadda mawallafa suka yi amfani da hikimarsu da
basirarsu wajen isar da saƙonsu
ta hanyar yin amfani da dabarar mutuntarwa daga cikin ire-iren dabarun da suka
yi amfani da su na dabarun salon jawo hankali wadda suke ɗaukar
abin da ba mutum ba su mayar da shi mutum ta ɗaukar
wasu darajoji ko halaye ko siffa wadda mutum ne kaɗai ya
keɓanta da su, su laƙabawa
wani abu da ba mutum ba. A nazarin an yi nasarar gano dabarar mutuntarwa
nazarin kuma ya gano mawallafan sun yi amfani da wannan dabarar domin su jawo
hankulan jama’a zuwa ga manufa da kuma nuna gwanintar harshe. Gudunmawar da
binciken ya bayar kuma ya zama jagora ga ɗalibai da manazarta wajen ƙara ba da haske akan yadda za a nazarci dabarar mutuntarwa a waƙoƙin siyasa.
Manazarta
Abba M. da
Zulyadaini, B. (2000). Nazari Kan Waƙar Baka ta Hausa. Zaria: Gaskiya Corporation.
Abubakar, U.S.
(2017) “Nazari da Sharhin Rubutattun Waƙoƙin Siyasa na Musa Yunusa Saye”.
Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero.
Adamu, A. I.
(2012) “Salo da Sarrafa Harshe a Cikin Wasu Waƙoƙin
Jam’iyyun ANPP da PDP a Jihohin Kano da Jigawa”. Kundin Digiri na Biyu. Kano
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Adamu, A. I.
(2021) “Dabarun Jawo Hankali a Wasu Waƙoƙin Siyasa a Jihohin Kano da
Katsina da Zamfara, Daga 2007 Zuwa 2018”. Kundin Digiri na Uku Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Auta, A. L. (2008)
“Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Faɗakarwa a Ƙarni
na Ashirin”. Kundin Digiri na Uku. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya.
Jami’ar Bayero.
Birniwa, H. A.
(1987) “Conservatism and Dissent: A Comaparative Study of NPC/NPN and NEPU/PRP
Hausa Political Verse From Circa 1946-1983”.
Kundin Digiri na Uku. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo.
Bunguɗu, A. I. (2017) “Tarken Rubutattun Waƙoƙin Siyasa na Kabiru Yahaya Kilasik” Kundin Digiri na Uku.
Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya”. Jami’ar Bayero.
Bunza A.M (2009). Narambaɗa Lagos: Ibrash Islamic
Publication Centre.
Bunza, U.A da
Bunza D.B (2018) “Jinsarwa a Alƙalamin
Ibrahim Aminu Ɗandago.
Tsokaci daga Waƙar Gudumar
Dukan Telu. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC),
Vol. 6. Department of African
Langugaes and Linguistics, Yobe State University
CNHN (2006) Ƙamusun Hausa. Kano: Jami’ar Bayero.
Ɗangambo, A. (2007) Ɗaurayar Gadon Feɗe
Waƙa” (Sabon tsari), Kaduna: Amana Publishers
Limited.
Yahya, A. B.
(2016) Salo Asirin Waƙa. Sabon
Bugu Sokoto: Guaranty Printers.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.