Citation: Dr. Aminu IBRAHIM, Dr. Salima Sulaiman ISAH & Fadeelatu Malam SUNUSI (2025). Amfani Da Turare Da Kayan Ƙamshi A Rayuwar Matan Hausawa. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 13, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
AMFANI DA TURARE DA KAYAN ƘAMSHI A RAYUWAR MATAN HAUSAWA
NA
DR. AMINU IBRAHIM
DR. SALIMA SULAIMAN ISAH
FADEELATU MALAM SUNUSI
Tsakure
Turare da kayan ƙamshi wasu muhimman abubuwa ne waɗanda
matan Hausawa suka ɗauke su da matuƙar muhimmanci da daraja, kuma suke yin amfani da su tun lokaci mai tsawo da
ya gabata. Manufar wannan bincike ita ce bayyana yadda mata suke yin amfani da
turare a gargajiyance, da kuma yadda suke yin amfani da turare a zamanance har
ya zama hanyoyin ci gaba a cikin rayuwar matan Hausawa. A cikin hanyoyin
gudanar da bincike, an yi amfani da hanyar karantawa daga rubutattatun bayanai
na magabata da kuma ganawa ta gaba da gaba da waɗanda
suke da alaƙa da
wannan aiki, domin samun ingatattun bayanai. Haka kuma, an ɗora
wannan bincike a bisa Ra’in Buƙatun Ɗan’adam (Theory of Human Need), wanda Abraham Maslow ya assasa a shekarar
(1908 Sh.1970). Bincike ya fito da matsayin turare ga matan Hausa da kuma yadda
matan Hausawa suke yin amfani da turare wajen ni’imta jikinsu da kuma samar
da ƙamshi
ga muhalli. Har wa yau, binciken ya gano yadda tsofafin turaruka da kuma
sababbi suka ba da gudummuwa wajen biyan buƙatu na warkarwa ga matan Hausawa.
Muhimman kalmomi- turare, kayan ƙamshi,
mata, Hausawa, magani.
1.0 Gabatarwa
Turare na ɗaya
daga cikin muhimman abubuwan da kowace al’umma ta duniya ke yin amfani da shi,
a wasu lokuta na musammaman, domin samun natsuwa da tsaftace jiki da muhalli da
kuma gyaran zamantakewa a tsakanin ma’aurata. Yana da wuya a iya cewa ga
lokacin da aka fara amfani da turare, saboda ba a gani a rubuce ba, sai dai a
yi hasashen hakan. Don haka, turare abu ne mai dogon zamani da ya ɗauki
shekaru aru-aru ana amfani da shi. Wannan bincike ne da za a nazarci al’ada da
yadda ake yin amfani da turare a cikin al’ummar Hausawa, tare da binciko irin
tasirin da zamani ya yi a kansa. A zamantakewar Hausawa suna yin amfani da
turaruka wajen yin ibadunsu ko a gidajensu da kuma waɗanda
suka haɗa da na magani domin kore cuta, kuma idan an yi nasara ana samun jin daɗi da
kwanciyar hankali, sannan ta ɓangaren bikin aure ma ana amfani da nau’o’in
turaruka masu ƙamshi musamman ma a
wannan zamani. Sannan ana yin amfani da turare da kayan ƙamshi a matakai da kuma wasu lokuta na musamman, don haka turare abu ne mai
taka muhimmiyar rawa a cikin zamantakewar Hausawa.
2.0 Asalin Kalmar Turare
Kalmar turare Bahaushiyar kalma ce, ba
aro ta aka yi ba, saboda Bahaushe yana da turare tun kafin ya haɗu da
Larabawa da kuma Turawa ko kuma sauran ƙabilu. Don haka, Bahaushiyar kalma ce. Bahaushe yana yin turare, kuma ana
amfani da shi tun tuni. Akwai turaren tashi bi ƙato, kuma ana wankan amarya da turare, kuma ana yi wa ‘ya’yan manyan
sarakuna da limamai asiri da turare. Akwai wata dabba mai suna mazurun Juda
wadda Hausawa suke yin turare da kasinta. Wannan dabba a ƙasar Hausa take. Don haka turare al‘adar Bahaushe ce. Kafin Barebari su
zo ƙasar Hausa, akwai Hausawa a cikin duniya.
Turare ya zamanto sana’a a da can kuma saboda bokayen ƙasar Hausa tun da har zuwa yanzu suna amfani da turare wajen kiran wasu
iskoki don biyan wasu buƙatu. (Hira da Farfesa
A.M Bumza) [1].
2.1 Ma’anar Turare
Masana da manazarta da dama sun yi ƙoƙarin bayyana ma’anar turare. Irin waɗannan
masana sun bambanta ne ta fuskar yadda suka jeranta tunani ko sarrafa kalmomin
da suka yi amfani da su, domin ƙulla
zaren ma’anonin da suka kawo dangane da turare. Sai dai daga ƙarshe, sun tattaru ne a kan manufa ɗaya
wadda suka bayyana ta kamar haka.
Sa’id da wasu,
(2006 Sh. 446) da Manzur (1920 Sh. 58) da Skinner (1999 Sh.126) da Muhammadu
(2011Sh. 650) sun bayyana turare da cewa: wani ruwa ne da ake matsawa daga
ganye ko wani sashi na bishiya, a sa a kwalabe. Ana shafawa a jiki ko a tufa,
saboda ƙamshinsa. Ƙwaro ko itace mai ƙamshi wanda ake ƙonawa don hayaƙinsa ya sa wuri ƙamshi. Itace ko ciyawa da ake
zubawa a garwashin wuta ana shaƙar hayaƙin don magani.
Ta la’akari da
bayanan da masana suka bayar, kenan a iya cewa turare wani ruwa ne mai ƙamshi wanda ake samu ta hanyar
harhaɗa nau’o’in tsirrai ko wasu dabbobin da Allah ya halitta
wanda babu wayau ko wata dabara ta ɗan’adam.
2.2 Yadda ake
Samar da Turare a Taƙaice
Turare ya samu ne daga itatuwa da tsirrai da
furanni da ‘ya’yan bishiya, da kuma sassan jikin wasu dabbobi. Akwai wasu
itatuwa da ke samar da sinadarin ƙamshi
tun daga furensu da suke fitowa har ya zuwa wasu sassa na jikinsu, kuma ƙamshin nasu kan bambanta daga wannan zuwa wancan. Ta hanyar sarrafa waɗannan
furanni ne ko ganye ake samar da turare na ruwa da na mai. Shi kuma
turaren ƙonawa ana samun sa ne ta
hanyar itace masu ƙamshi, amma sai aƙara masu sinadarai ta yadda idan an ƙona hayaƙin za ya samar da ƙamshi mai daɗi. Bugu da ƙari, akan samar da wani
nau’in turaren mai daga wata dabba mai dangantaka da mage, wadda ake kira magen
juda. Ita wannan dabba ta ƙasar Hausa ce, (Hira da
Dakta S.M Kudan)[2].
3.0 Turare a Wurin
Matan Hausawa
Matan Hausawa mata ne da za a iya kalon su ta
fuska biyu duba da yadda zamantakewarsu take. Da farko, akwai ‘yan asalin ƙasar Hausa, waɗanda iyayensu da kakanninsu a nan aka haife su, kuma suna
tafiyar da tsarin al’adunsu da ɗabi’unsu da adabinsu da magana da harshensu,
kamar yadda al’ada ta tanadar. Na biyu kuwa su ne, waɗanda
aka auro su, ko kuma wani dalili ya sa suka zo ƙasar Hausa suka zama Hausawa ta yadda al’adunsu da ɗabi’unsu
da harshensu duk suka koma na Hausawa. Mata Hausawa suna ɗaukar
turare a matsayin wani makami, wanda suke yaƙin duk wata ƙazanta da shi, wato abu
ne mai matuƙar daraja da muhimmanci a cikin rayuwarsu.
Saboda duk yadda mace take, dole ne sai ta buƙaci turare domin tafiyar da harkokin rayuwarta. Turare yana sawa mace ta
samu daraja da girma da ɗaukaka da kuma lafiya a cikin rayuwarta. Don
haka turare a warin matan Hausawa ya kasu kashi–kashi. Akwai wanda za a yi
amfani da shi wajen tsaftar jiki. Wani kuma wurin gyaran muhalli, wani kuma don
samun lafiya da dai sauransu, (Hira da Kabir Ɗanasabe).[3]
3.1 Rukunnan Mata Masu Amfani da Turare
Rukuni na nufin ɓangare
ko sashe (Sa’id da wasu, 2006 Sh.376). Akwai rukunin matan Hausawa waɗanda
suke yin amfani da turare a zamantakewarsu, saboda wasu dalilai da suka keɓanta
da su. Duk inda mace take an san ta da ado da kwalliya. Sannan sanya turare a
wajen matan Hausawa sababben abu ne, sai dai kowane rukuni da irin nau’in da
yake amfani da shi.
3.1.1 ‘Yan Mata
Rukuni ne na mata waɗanda
shekarunsu suka fara daga goma zuwa goma sha biyar. ‘Yan mata sukan yi kwalliya
su shafa nau’in turaren da suke buƙata, domin ƙara ma kwalliyarsu armashi. Ire-iren turarukan sun haɗa da:
Aminami da rose da biza. Rukunin yara ƙanana rukuni ne da yake farawa daga shekara ɗaya
zuwa goma. Ana yi masu amfani da turarukan da ba su da ƙarfi sosai, ire-iren turarukan sun haɗa da: Habiba Hafsat da nuril. Rukunin budurwa
na farawa daga shekara sha biyar zuwa ashirin. Budurwai suna sanya kowanne irin
turare wanda ake yayi mai matuƙar ƙamshi. Turaren shi ne yake fito da kwalliyarsu. Idan budurwa ta yi kwalliya
ta wuce ba ta sanya turare ba, yawanci ba a sanin ta wuce. Amma idan ta sanya
turare daga ta doso duk wanda yake wurin sai ya ɗaga
kai ya kalleta saboda wannnan ƙamshin
turaren, ire-iren turarukan sun haɗa da: Madarar Yobe da rakkan da burhan da sweet
baby da black ss da cool weather da touch me da
dai makamantansu. Su waɗannan turarukan da aka ambata su ne turarukan da ‘yan
mata ke amfani da su na yayi. Dalilin da ya bambanta turaren ‘yan mata da
sauran rukunin mata shi ne, su ‘yan mata basu damu da turaruka masu tsada ba.
Sun fi mayar da hankali ga turarukan da ake yayi masu ƙarfin ƙamshi ko masu
sanyin ƙamshi, kowacce budurwa da irin wanda take
ra’ayi in dai na yayi ne, sun fi son ƙawayesu ko samari su fara jin ƙamshin
turaren daga garesu. Wannan dalilin ne yasa turaren ‘yan mata ya bambanta da na
sauran rukunin mata. (Hira da Abdullahi Yakubu Darma).[4]
3.1.2 Matan Aure
Sa’id da wasu, (2006 Sh. 22) sun ba da
ma’anar aure da cewa, dangantaka tsakanin namiji da mace ta hanyar shari’a.
Matan aure suna sanya turare, domin su burge mazajensu na aure. Bayan nan kuma,
turarukan da matan aure suke yin amfani da su ya danganta ne daga matsayin
matan ko kuma ikonsu da kuma ƙarfinsu. Saboda turaren
mataki -mataki ne akwai na matan sarakuna da matan masu kuɗi da
kuma na matan talakawa. Ire-iren turarukan da matan Hausawa suke yin amfani da
su a wancen lokacin sun haɗa da: Turare Sarkin Kano, wanana turare ne na ƙasar Hausa mai laushin ƙamshi da tsada haka
kuma, ba ko’ina ake sayar da shi ba, mafi yawan matan gidan sarauta sun fi yin
amfani da shi. Turare mai kofi na ƙasar
Hausa ne, yana da sanyin ƙamshi da tsada ana sayar
da shi a manyan shaguna waɗanda sunansu ya yi fice a gari. Matan masu kuɗi sun
fi yin amfani da shi. Turare alwalar uwarɗiya na ƙasar Hausa ne, yana da kaifin ƙamshi.
Ana samunsa a ƙananan shaguna yana da
sauƙin kuɗi matan talakawa sun fi yin amfani da shi, da
dai makamantansu. Amma a wannan zamani, matan Hausawa sun sami sababbin
turaruka sakamakon cuɗanya da suka yi da baƙin al’ummomi na kusa da na nesa. Waɗannan turaruka sun zama na matan Hausawa. Ire-iren
turarukan sun haɗa da: humra fara ko baƙa ko ruwan ƙasa. Nau’o’in humra kuɗi-kuɗi ne, idan an yi amfani da manyan turaruka wajen yin ta
za a sayar da tsada, idan kuma ƙananan
turaruka aka yi amfani da su za a sayar da arha, iya kuɗinka
iya shagalinka. Sai kuma wasu daga cikin nau’o’in madarar turare masu ƙamshi. Kamar narsis da amrish da royal oud waɗannan
kuma sun danganci matan sarakuna. Haka kuma, akwai turare lailatul-sahara
da munjid da makamantansu. Su kuma sun danganci matan masu kuɗi.
Bugu da ƙari, akwai turaruka irin
su kafi-kafi da alliƙa
da sauransu, su kuma sun danganci matan talakawa.
Saboda haka, dalilin da ya bambanta turaren
matan aure da sauran rukunin mata shi ne, saboda yawanci matan aure sun fi yin
amfani da turare a gidajensu. Idan aka shiga gidan sarauta za a ji ƙamshin turarensu ya bambanta da na gidan masu hali, haka kuma, na gidan
masu hali ya bambanta da na gidan talakawa Hakan ne ya sa matan aure ba su damu
da yin amfani da turaruka barkatai ba, haka kuma yin amfani da turare ga matan
aure ya taallaƙa ne a bisa son ra’ayin
mazajensu saboda su kaɗai ne za su yaba masu, ko da akwai turaren da suke buƙata, dole ne su yi haƙuri su so wanda yake
burge mazajen nasu. Idan kuma mijin ɗan baruwana ne, to za ta yi amfani da
turaruka masu sanyin ƙamshi, waɗanda
ba za su damu hanci ba kamar nau’in humra, da makamantansu. Sabo da haka,
wannan ne ya bambanta turarukan matan aure da na sauran rukunin mata. (Hira da
Malama Samira Kano)[5].
3.1.3 Amare
Amare jam’i ne na amarya. Amarya tana nufin
mace budurwa ko bazawarar da ta yi sabon aure (Sa’id da wasu, 2006 sh. 15).
Matan Hausawa sukan yi amfani da wasu hanyoyi wajen gyara jikin kowace amarya
ta hanyar yin turgeza[6].Ana tanadar lalle dakakke da wanda ba a daka
ba da turare iri-iri da farar albasa da garin magani. Za a kwaɓa
garin lalle da nau’o’in turaruka da garin magani, za a sanya ɓantalen
tsamiya da lemun tsami don ya kama fatar jikin amarya (Halima, 2018 Sh.95). Sai
a shafa wa amarya tun daga cikin gashin kanta har zuwa tafin ƙafa. Za a yi ta cuɗa ta ana mulke ta har tsawon awa ɗaya.
Bayan an gama sai a jiƙa lalle wanda ba a daka
ba a zuba ruwan jima mai ƙamshi a sanya farar
albasa da turaruka, amarya ta yi wanka da ruwan. Yanzu kuma cuɗanya
da baƙi ya kawo sauyin nau’o’in turare da
kayan ƙamshi, waɗanda
aka keɓe musamman saboda amare. Idan bikin yarinya ya matso abu na farko da za a
fara yi mata shi ne dilka.
3.1.3.1 Dilka
Dilka dai wata sabuwar hanya ce ta gyaran
jiki wadda ta samo asali daga Barebari. Ana dilka da abubuwa kamar haka,
dankalin Turawa da gyaɗa da shinkafar tuwo da kuma sawa.
Kamar yadda Mu’azu (2023 Sh. 110) ya ce,
dilka ko halawa al’ada ce ta cire ko goge duk wani gashi da yake jikin sabuwar
amarya kafin a kai ta gidan miji, yawanci akan nemi madara da turaren ƙanshi da kuma gari na magani irin na gargajiya a shafe jikin amarya da su.
Bayan kamar minti ashirin 20 zuwa talatin 30 sai a yi mata wanka. Jikinta zai
yi suɓul da santsi kamar kifi.
Bulkisu, (2015 Sh. 87) ta bayyana dilka
da cewa, wani nau’i ne na gyaran jiki wanda Hausawa ke yi lokaci zuwa lokaci,
domin su tsaftace jikinsu, su yi kyau su yi fes-fes, jikinsu ya yi luƙui-luƙui abin sha’awa.
Ita dilka haɗin ta
nau’i-nau’i ne, kowa da yadda yake yin na sa amma a ƙarshe abu ɗaya ne ake samu wato jikin amarya za ya yi kyau sosai da
laushi da silɓi, sannan za ta canza kalarta ta asali zuwa ɗorowa
mai haske shi ne dalilin da ya sanya ake cewa a kori kwailin (bleaching).
Duk inda amarya ta shiga za ta yi ƙamshi.
Abubuwan da ake buƙata wajen haɗin
dilka sun haɗa da: garin dilka da ƙwai da lalle da madara
da lemun tsami da kuka da zamantaroro da manja ko farin mai da kurkum da
nau’o’in madarar turaruka da nau’o’in garin kalɗa
i. Hanya ta
Farko
Za a haɗa garin kalɗa
adadin nau’o’in da ake buƙata sai a zuba ƙwai da turare da kurkum na gwangwani da kuma mai marar masƙi (Lotion silɓer line[7]) sai a bi jikin amarya a shafe mata duka.
ii. Hanya ta
biyu
Amarya za ta shiga hayaƙin dorrot[8], wanda aka haɗa shi
da turaruka za ta zauna a kan kujera, sai a rufe ta yadda hayaƙin ba za ya fita ba, bayan ta haɗa gumi sai a fidda ta daga hayaƙin. To a lokacin ne amarya da mai yin dilka za su sha madara saboda hayaƙin da suka shaƙa, sai dai ba a so a shaƙi hayaƙin sosai.
iii. Hanya ta
uku
Za a jiƙa dilkar da ruwan ɗumi tsawon minti sha biyar (15). Idan ta yi laushi a zuba
manja ko man gyaɗa, sannan a fasa kwai a zuba ruwan kwai wato farin nan (albumin) ba
a sanya gwaiduwar wato (yoke). Daga nan za a zuba kurkum na awo kaɗan da
garin lalle sai madarar turare, a matsa lemun tsami kaɗan.
Za a ƙara shafawa a jikin amaryar. Bayan ya bushe a
murje jikin sosai duk wata dauɗa za ta fita. Jikin zai yi laushi da sulɓi.
Asalin hasken fatar jikinta za ta fito. Kuma ta canza zuwa ɗorowa
mai haske. Ana yi wa wannan gyaran jiki kirari da akori kwailin (bleaching).
Ba a yin wanka tun daga ranar da aka fara har sai ranar da aka gama.
Dalilin da ya sa turarukan amarya suka
bambanta da kowanne rukuni mata shi ne, lokacin amarci lokaci ne na musamman da
matan Hausawa suke ɗaukar shi da matuƙar
daraja. Haka kuma, kowacce amarya ana yi mata shiri na alfahari da fita kunya
musamman ma budurwa. Ana yi mata amfani da kowanne nau’in turare mai tsada da
mai arha, masu ƙarfin ƙamshi da kuma masu sanyin ƙamshi
da masu kaifin ƙamshi, saboda tun daga
ranar da amarya ta shiga lalle ake fara yi mata amfani da turaruka har ranar buɗar
kai. Sannan kuma, kowanne mataki na cikin tsarin bukin akwai nau’in turaren da
ake yi mata amfani da shi. Don haka, wannan shi ne dalilin da ya bambanta
turarukan amarya da na sauran rukunin mata. (Hira da Zara Shuwa Arab).[9]
3.1.4 Mata Zawarawa
Zawarawa na nufin matan da aurensu nada ya
mutu kuma suna neman sake yin wani auren (Abubakar 2014 sh 515). Matan Hausawa
zawarawa suna yin amfani da turare mai ƙarfi saboda suna so duk inda suka wuce a ji ƙamshinsu. Sannan zawarawa sun fi yin amfani da turare mai tsada sosai
saboda su fita dabam da ‘yammata. Wasu zawarawa suna sanya turare domin su
burge kowa ba sai wanda yake son su ba. Su dai sun ɗauki
sanya turare tamkar farilla, saboda suna ganin babu igiyar aure a kan su. Don
haka, babu wani hukunci mai nauyi a kan sanya turaren. Yawancin turaren da suke
shafawa sun haɗa da Elope 419 da 212 da amrish da Tee da
narsis da amirul oud da sandal babba da makamantansu. Dukkansu waɗannan
turaruka ne masu kyau da kuma ƙamshi.
Sannan suna da wuyar samu idan har suka yanke daga wurin masu sayarwa.
Wani dalilin kuma da ya bambanta turaren
zawarawa da na sauran rukunin mata shi ne, galibi zawarawa sun fi yin amfani da
turare domin su janyo hankali ko ƙara
kwarjini a wajen jama’a. Don kuwa, sub a su damu da turaren da ake yayi ba, duk
tsadar turare bazawara za ta iya sayensa domin ta fita dabam da sauran mata.
(Hira da Alhaji Bishir)[10].
3.1.5 Mata Tsofaffi
Su ne mutanen da shekarunsu sun ja ƙwarai. Amma mata tsufansu na farawa ne daga shekaru hamsin (50) ko hamsin
da biyar zuwa abin da hali ya yi (Sadik, 2014 sh 213).
Matan Hausawa tsofafi suna yin amfani
da turare wanda ba ya da ƙarfi sosai. sannan babu
ruwansu da su burge kowa. Sun fi mai da hankali su sanya turare idan za su yi
ibada. Ire-iren turare da matan Hausawa tsofaffi suke shafawa sun haɗa da:
kafi –kafi da sandal da jako da tijjani bolori da dai sauransu.
Dalilin da ya bambanta turaren tsofaffi
da na sauran rukunin mata shi ne, idan mace ta tsufa babu ruwanta da ta burge
ko ta jan ra’ayin kowa ba, sannan ba kowace tsohuwa ce ke shiga jama’a ba, haka
ma ɓatan wata, don haka mu’amular su da turare ragaggiya ce. Hakan ne yasa
turarensu bai shafi zamani ko yayi ba, Wasu ba su damu da ƙamshin turare a jikinsu ba sai don yin ibada, Yawanci sun fi son su shaƙi iska mai ƙamshi don haka suke yin
amfani da turaren wuta na tsintsiyar ƙamshi, suna yin amfani da turaruka dai-dai da shekarunsu. Wanana ne dalilin
da ya bambanta turarukan tsofaffi da na sauran rukunin mata (Hira da Hassana
Lawal)[11].
3.1.6 Mata Masu Jego
Jego na nufin lokacin da mace ke goyo da
shayar da ɗan da ta haifa (Sa’id da wasu, 2006 sh. 215).
Matan Hausawa masu jego tun a da suna yin
amfani da turaren wuta saboda su kore warin jini da ƙarninsa, da kuma warkarwa daga ciwon da ta samu wajen haihuwa. Ana turara
kajiji a ɗaki domin kore ƙarnin jini. Ana haɗa
kashin awaki da turaren juda, a zuba su kan garwashi sai mai jego ta tsugunna
ta turare jikinta hakan zai taimaka mata wajen warkar da ciwon da ta ji
sanadiyar haihuwa. Har ila yau, ana haɗa kajiji da ƙarangiya a tsugunna duk wata buɗewa da mace ta yi za ta matse. Sannu a
hankali zamani ya kawo wa matan Hausawa masu jego yin amfani da turaren wuta na
tsugummo wanda ake haɗa shi kamar haka: kashin Raƙumi da itacen magarya da hawi[12] da misik[13] da ganyen magarya da garin
farce da kanumfari. Dukkan abubuwan da aka zayyano za a haɗe su
wuri ɗaya a dake su, sai a zuba ruwan turare lafinta[14], a rufe kamar kwana uku, sannan a buɗe a
zuba madarar turare da jan miski da kuma sandal[15] da dai sauransu. Za a bar shi ya yi
sati a tsume. Da mace ta haihu bayan jini ya ɗauke
mata, za ta fara yin amfani da shi har ta yada wanka.
Haka kuma, wani dalilin da ya bambanta
turaren masu jego da sauran rukunin mata shi ne, kamar yadda aka sani jego wani
abu ne na musamman wanda yake buƙatar kula. Dole ne sai
an yi taka tsan-tsan sosai wajen rabuwa da ƙazanta. Babu wani turaren shafawa da aka ware musamman saboda mata masu
jego, sai dai mace za ta iya yin amfani da turaruka masu ƙarfi saboda yanayin/hali da take ciki na ƙarni. Saboda haka, akwai buƙatar ƙamshi. Sai kuma nau’in turaren wuta wanda aka yi bayaninsu a baya da kuma
turaren wuta na ɗaki duk don saboda a gyaran muhalli kada ya yi ƙarni. Wannan ne dalilin da ya bambanta turaren mata masu jego da na sauran
rukunin mata. (Hira da Hajiya Talatu mai turare Maiduguri)[16].
3.1.7 ‘Yan Bori
Bori na nufin mutum ya fita cikin hayyacinsa
a sakamakon haɗuwa da iska domin biyan wata buƙata
ta musamman (Hira da Ibrahim Abdullahi S.S[17]) Matan Hausawa ‘yan bori suna yin amfani da
nau’ o’in turare domin kiran iskokai, kowane iska akwai irin turaren da ake yi
musu amfani da shi wajen kiran su. Sannan akwai turaren da ake haɗa
magani a kori iskan da shi idan azzalumi ne. Kowanne mai aiki da iska, akwai
irin yadda suke gudanar da ayyukansu. Waɗannan turaruka sun daɗe
a ƙasar Hausa kuma har yanzu ana yin amfani da
su, Ire-ire waɗananna turaruka sun haɗa da, mai- kai- uku/ garambasa da Binta-Sudan da mai- Aku
da mai- Kurege da Ɗan’duwala da Alƙali-goma da turaren Juda da dai sauransu (Hira da Malama Gajen Gawuna)[18]
Kamar yadda aka samu tasirin zamani na samun
sababbin turaruka a wajen matan Hausawa ta dalilin cuɗanya
da baƙi na kusa da na nesa, haka ma abun yake ga
mata ‘yan bori da masu ba da maganin iskokai. Saboda su ma iskokai suna tafiya
da zamani. Ba kowanne iska ne idan za a kira shi ake yin amfani da waɗancan
tsofafin turarukan ba. Wasu daga cikin su sai ɗan
fisa. Ire-iren waɗannan iskokai sun haɗa da
Bature ko Baturiya da Gwari da Alhaji Ibrahim da dai sauransu. Ana kiransu da
kowane irin turare na fesawa amma Baturiya ta fi son mai jar kwalba kamar fashion da
sauransu.
Wani dalili da ya bambanta turaren mata ‘yan
bori da na sauran rukunin mata shi ne, ‘yan bori suna yin amfani da turaruka a
dalilin umarnin da iskokansu suke ba su. Dole ne turaren da iska yake buƙata shi ne za su dinga shafawa, saboda samun biyan buƙata. Wasu daga cikin turarukan ma sunayen iskokan ne suke ɗauke
da shi, turaruka ne waɗanda ƙamshinsu ya bambanta da
sauran waɗanda aka sabo shaƙa. Wannan ne dalilin da
ya sa turarukan mata ‘yan bori suka bambanta da na sauran rukunin mata. (Hira
da Zuwaira Bindawa)[19].
3.2 Turare a Matsayin Magani Ko Mahaɗin
Magani a Wajen Matan Hausawa.
Danga ne da hanyar samar da waɗannan
magungunan a al’ummar ta Hausawa, hanyoyi sukan bambanta daga wuri zuwa wuri,
amma masana sun fi danganta samuwarsu da Bokaye da Malaman tsibbu da kuma
mutanen da suka shahara a wata sana’a ta gargajiya. Kamar Wanzamai, da Maƙera da masunta da dai sauransu. Irin tasirin da magani ya yi a rayuwar
Hausawa shi ya sa har kwanan gobe ba lungun da za ka shiga a ƙasar Hausa ba ka sami boka ko malaman tsibbu ba. Idan kuma aka nazarci
kasha- kashen magungunan da ya gabata za a fahimci cewa, ba ɓangaren
rayuwar da lamarin bai shafa ba, kama ga haihuwa, da aure da sana’o’in ko
hanyoyin samun abinci, da tsaro har kaiwa ga mutuwa. (Ibrahim, 2000 Sh. 18)
Mahaɗi na nufin wani abu d ake haɗa
abubuwa da shi dan su game wuri ɗaya (Sa’id da wasu, 2006 sh.318).
Duk wani abu da aka samu a magungunan
za a tarar da gargajiya ce tsan-tsarta, idan an ga irin wannan magani ko
magunguna Hausawa na amfani da su ko sun sarrafa su, su ake cewa magungunan
gargajiya na Hausawa. (Bunza, 1990 Sh. 134)
Sai’d da wasu, (2006 sh. 316) sun bayyana
ma’anar magani kamar haka, abun da ake sha ko shafawa a jiki ko ɗurawa
a jini ta hanyar yin allura dan neman samun lafiya.
Ta la’akari da bayanan da suka gabata, kenan
a iya cewa magani wata hanya ce ta yin amfani da nau’o’in abubuwa ko kuma
kiyayewa daga wasu abubuwa.
Akwai ire-iren turaruka da dama waɗanda
matan Hausawa suke yin amfani da su a matsayin magani ko mahaɗin
magani. Ire-iren waɗannan turaruka sun ƙunshi turaran wuta na hayaƙi da na ruwa da na maiƙo.
3.2.1 Turaren Warkarwa
Warkarwa na nufin taimakawa wajen warware
matsala kuɓutarwa daga abin da ya damu rai (Abubakar, 2014 Sh.483). Turarukan warkarwa
suna da yawa, amma daga ciki akwai:
3.2.1.1 Turaren Juda da Cututtukan da Yake
Warkarwa
Turaren juda,[20] turare ne na ƙasar Hausa wanda ake yin maganin cututtuka da dama da shi musamman cutar da
ta shafi fata da kuma iska. Wannan turare na mai ne kuma yana da kauri da ƙamshi. Daga cikin cututtukan da ake amfani da wannan turare, wajen haɗa
maganinsu akwai maƙero. Ana wanke maƙero har ya yi jini. Idan wurin ya sha iska sai a shafa turaren juda. Sai
kuma ƙurjin da yake fitowa a guaiwa wanda Hausawa
suke kira fitsarin gwairo shi ma ana shafa masa a jikin ƙurjin. Ta ɓangaren iska kuma idan ciwon kai na iska ne shi ma ana
shafa turaren juda da dai sauransu, (Hira da Alhaji Surajo mai Asharalle) [21].
3.2.1.2 Turaren Binta Sudan da Cututtukan da
Yake Warkarwa
Binta Sudan kala biyu ne, akwai na gida
Nijeriya da kuma wanda aka shigo da shi. Amma yanzu shi ma ya zama na ƙasar Hausa. Ana yin amfani da wannan turare ga wanda maye ya kama, ko ya
tura ma iska. Za a samu zamantaroro[22] da tazargade da ganyen magarya da
ganyen ƙaiƙayi
koma kan masheƙiya, a haɗe su
wuri ɗaya a daka su sai a zuba wannan turaren Binta sudan a riƙa turara wa wanda maye ya kama har tsawon sati biyu. Za a samu lafiya da
yardar Allah. Idan kuma mayen ya tura wa mutum iska, za a ɗebo ƙasar kasuwa da ta suri da ta gidan tururuwa, kuma a samu ciyawar ɓadda
kurwa sai a daka ta a haɗesu wuri ɗaya sannan a zuba turaren Binta sudan. Marar
lafiya za ta yi wanka da hayaƙi. (Hira da Malam
Muhammadu) [23].
3.2.1.3 Turare Jan Miski da Cututtukan da
Yake Warkarwa.
Jan miski, turare ne da ya samo asali daga
Misira amma yanzu ya zama na matan Hausawa. Matar da take fama da ciwon cikin
tsanki [24]za a rubuta mata Innahu min Sulaimaana wa
innahu Bismillahir rahmanir rahiym babu adadi (Suratul Namli: Aya ta30). Idan
an wanke sai a ɗiga jan miski kaɗan a sha za a samu lafiya. in Allah ya yarda
(Hira da Malam Muhammadu) [25].
3.2.2 Turaren Cutarwa
Wannan rukuni na magunguna ya ƙunshi waɗanda ake yi don a cutar da wani mahaluki a bisa wani dalili da mu’amula ta
haifar. (Ibrahim, 2000 Sh. 19)
3.2.2.1 Turare Wardi da Irin Cutarwar da ake
Yi da shi
Turare wardi turare ne na ƙasar Hausa wanda wasu mata suke yin amfani da shi wajan korar kishiya. Ana
samun iccen mallaka da mushen dodon koɗi da zuciyar Aku da zuciyar Kare. Za a haɗe su
wuri guda a daka, sannan a zuba turare mai Aku a jiƙa. Duk lokacin da mace za ta kama ruwa da shi za ta yi amfani. Saboda ta
janye mijin ta raba shi da sauran matansa. Za ya bar jin maganar kowa sai ita.
A ƙarshe ma ya rabu da su, (Hira da Malam
Rabi’u) [26].
3.2.2.2 Turare Ɗan goma da Irin Cutarwar da ake Yi da Shi
Matan arewa, turare ne na ƙasar Hausa wanda matan Hausawa suke yin amfani da shi wajen yi wa
kishiyoyinsu mugunta. Za a samu mushen jaɓa sabuwar mutuwa, da mushen hawainiya da idon
mujiya da tsumman ƙunzugun wadda za a yi wa
asirin, da ciyawar balasana[27]. Sannan a tona rami a binne, ana karanta
wasu surutai na surkulle. Wadda ta yi asirin, za ta nemi bi-ta-zai-zai, da
zuciyar zakara sai ta daka, ta zuba wa mijin a abinci ya ci, sannan ta ɗibi
kaɗan ta zuba turare ɗan goma, ta turara a jikinta. Da mijin ya ji ƙamshinta shike nan, daga lokacin ɗayar
matar za ta fara wari, (Hira da malam Umaru) [28].
3.2.3 Turaren Kariya
Sa’id da wasu, (2006 Sh. 235) sun bayyana
kariya da yin amfani da wani abu don kange wani abu. Kariya na nufin rigakafi a
kan abin da kake tsoron kada ya same ka, ko kiyayewa daga shiga wani hali.
Matan Hausawa suna yin amfani da nau’o’in magunguna da turaruka domin rigakafi,
ba wai sai ciwo ya dame su suke yin magani ba. Tun kafin abu ya zo ake neman
kariya, ko da ya zo, za a samu sauƙi, (Hira da Malam Rabi’u
Sada) [29].
3.2.3.1 Turare Mai Kurege da Irin Kariyar da
Yake yi
Turare mai kurege, turare ne na ƙasar Hausa wanda matan Hausawa suke yin amfani da shi wajen maganin
tsautsayi da asara. Za a shanya ganyen tattaba a ɗaki.
Bayan ya bushe, za a daka shi a haɗa da wannan turare mai kurege. Idan mace za
ta fita sai ta turare jikinta. Haka kuma ana dafa ganyen, a tace ruwan, sannan
a zuba turare, duk amfanin su ɗaya. (Hira da Bilki mai Kitso) [30].
3.2.3.2 Turare Alƙali Goma da Irin Kariyar da Yake yi
Turare alƙali goma, turare ne na ƙasar Hausa. Matan
Hausawa suke yin amfani da shi wajan maganin baki da sammu. Za a samu ganyen
magarya da ciyawar ƙaiƙayi koma kan masheƙiya da ganyen garahuni
da ƙasar maƙabarta
da ƙasar mararrabar hanya. A dake ganyayen sannan
a haɗa da wannan ƙasar sai a zuba turaren
alƙali goma. Za a yi wanka kuma a turare jiki,
(Hira da Malam Umaru). [31].
3.2.4 Turaren Biyan Buƙatar Rayuwa.
Wannan rukuni ya shafi magungunan da akan
bayar ko akan nema don biyan buƙatar rayuwa, ko taimaka
wa rayuwa ta gudana yadda ake buƙata. Misali, asirran
neman auren mace, ko mace ta so namiji, da na farin jinni, da na samun bashi da
na kiran kasuwa da neman Mulki ko ɗaukaka da na sarauta da na ilimi da dai
sauransu. (Ibrahim, 2000.Sh. 20)
Abubakar, (2014 Sh. 60) ya fasara buƙata da son abu, saboda wajibcin samunsa ko dacewarsa. Matan Hauwasa suna
yin amfani da wasu daga cikin turaruka saboda biyan buƙatar rayuwarsu. Biyan buƙarar rayuwa yana nufin
neman biyan buƙatar da mutum ya san bai
iya biya wa kansa ita ta kowace hanya. Wato ta ƙunshi duk wata buƙatar da za ta ƙara wa rayuwa armashi wadda mutum ba zai iya biya wa kansa ita ba.
3.2.4.1 Turare Kiko da Irin Biyan Buƙatar da Yake yi
Turaren kiko turare ne wanda ya samo asali
daga Indiya amma yanzu ya zama na ƙasar
Hausa. Turaren kiko[32] kala biyu ne, akwai na wuta da na ruwa.
Ana haɗa sirrika iri-iri da wannan turare. Matan da suke amfani da wannan turare
sun haɗa da, manyan mata ‘yan kasuwa da mata masu neman mulki da mata masu neman
buwaya. Kowane asiri za a haɗa akwai hanyoyin da ake bi don a samu biyan buƙata, amma duk matar da aka haɗa mata asiri da turaren kiko tabbas sai ta ba
da mamaki. (Hira da Abba Abbati) [33].
4.0 Kayan Ƙamshi da Yadda Matan Hausawa Suke Amfani da su
Kayan ƙamshi wasu sinadarai ne da ake haɗawa su ba da ƙamshi. Matan Hausawa suna yin amfani da kayan ƙamshi a jikinsu, saboda kawar da duk wani abu wanda za ya haifar da iska
marar daɗin shaƙa. Kayan ƙamshi kala- kala ne, akwai waɗanda suke gari ne, akwai kuma waɗanda
suke mai ne. Haɗuwar matan Hausawa da baƙi na kusa da na nesa ya
sanya sun ƙara samun wasu
kayan ƙamshi wanda a yanzu suka zama na matan
Hausawa. Kayan ƙamshi suna da yawa, daga
ciki akwai: lalle da misic da dai sauransu.
4.1 Lalle
Wani tsiro mai taurin saiwoyi, da ƙananan ganye, wanda mata suke dakawa suna yin ƙunshi da shi a ƙafa da hannu don ado
(Sa’id da wasu, 2006 Sh.300). Lalle yana da ƙamshi na asali mai laushi wanda mata da yawa suke jin daɗinsa,
kuma bai cika damun hanci ba, kamar wasu turaruka. Matan Hausawa sun daɗe
suna yin amfani da lalle a matsayin ɓangare na tsafta da ƙamshi a al’adance, haka yasa mata ke ci gaba da yin amfani da shi har yau.
Lalle ya zama ɗaya daga cikin kayan ƙamshi na matan Hausawa a wannan zamani, ta dalilin kwaɓa shi
da wasu tsirrai na ƙasar Hausa masu ƙamshi, da kuma nau’in turaruka na gida da wanda baƙi suka shigo da shi. Sai a shafe jiki domin samun wani nau’in ƙamshi, wanda yake ɗaukar lokaci bai fita daga jikin mace ba. Wannan ƙamshi yana rage gumin da kuma kore warin jiki da ƙara lafiyar fata. Da lalle ake amfani wajen alamta shigar da mace musamman
budurwa cikin lamarin aure, abu na farko da ake fara kawowa gidan su amarya shi
ne lalle, wasu ma dole sai an sa wa namiji lalle kafin a ɗaura
masa aure saboda muhimmancinsa a cikin al’adun aure da kuma rayuwar matan
Hausawa. (Malama Karbiya) [34].
4.2 Misik
Misik wani nau’in kayan ƙamshi ne wanda ya samo asali daga ƙasar Sin. Sai dai yanzu ya zama na matan Hausawa. Misik yana da ƙamshi sosai kuma mai ƙarfi. Yana da daɗin
shaƙa sannan kala-kala ne. Akwai fari mai kamar
ruwan madara-madara, matan Hausasawa suna yin amfani da shi wajan yin duk abin
da ya shafi turare ko kayan ƙamshi. (Hira da Ali
Zajeri) [35].
5.0 Turaruka Masu Asali da Tushe da Ƙasar Hausa
Ƙasar Hausa Allah ya azurta ta da tsirrai da
itatuwa da duwatsu Sallau (2009 Sh. 23). Don haka daga cikin itatuwan da Allah
ya albarkaci ƙasar Hausa da su, su ne
matan Hausawa suke sarrafawa domin samar da turaruka ire-iren. Waɗannan
tsirrai da itatuwa sun haɗa da Lafiya dubu da Iccen Maje da Ɗaɗɗoya da Bunsurun fadama da Kumbususu da Jema da makamantan su. Ga misalan
yadda ake haɗa wasu daga ciki kamar haka:
5.1 Lafiya Dubu
Lafiya dubu wani tsiro ne na ƙasar Hausa, yana da ƙananan ganye ga ƙamshi. Matan Hausawa suna yin amfani da shi wajen yin turare. Ana jiƙa shi da ruwa kaɗan a ajiye shi inda rana ba za ta taɓa shi
ba. Idan mace tana buƙatar yin ƙamshi sai ta tsiyayo ta shafa. Bugu da ƙari, yana yin maganin ciwon ƙafa.
(Hira da Hajiya A’isha Shakka)[36].
5.2 Iccen Maje
Wani nau’in icce ne na ƙasar Hausa wanda ake yin turaren wuta da shi. Sannan yana fitar da ƙwaro mai ƙamshi daga cikin shi
wanda ake kira ƙwaron maje. Matan
Hausawa suna ƙona shi ba ta tare da an
yi masa haɗin komai ba. Amma yanzu ana yi masa haɗi na
musamman. Za a samu bokiti mai marfi a zuba itacen maje wanda aka sassara a
ciki, sannan a zuba ruwan turare lafinta da madarar turare. Bayan nan za a zuba
garin sandal bakhur da jawil da lubban da misik, sai a rufe, bayan kwanaki kaɗan a
fara yin amfani da shi. Daga nan ya zama turaren wuta na jiƙawa. (Hira da Abba Almu)[37]
6.0 Sakamakon Bincike
Sakamako na nufin wasu abubuwa da bincike ya
gano waɗanda da can ba a gano su ba. Bincike ya gano yadda matan Hausa suke yin
amfani da turare a gargajiyance, da kuma yadda suke yin amfani da turare a
zamanance don taimakawa wajen ci gaban rayuwarsu.
Kazalika, bincike ya gano cewa matan Hausawa
sun daɗe suna yin amfani da kayan ƙamshi
a matsayin tsabta da kuma ado, sannan kuma suna bunƙasa al’adun matan Hausawa a wannan zamani.
Harwayau, binciken ya gano cewa kowanne
rukuni na matan Hausawa, akwai nau’in turarukan da suke yin amfani da su wajen
aiwatar da kwalliya da kuma magunguna domin neman biyan buƙatunsu..
7.0 Kammalawa
Wannan maƙala ta yi bayanin muhimman al’amurran da suka shafi turare da kayan ƙamshi. A cikin maƙalar an kawo tsakure na
abinda takardar ta ƙunsa sai gabatarwa,
wanda ya yi bayani a kan abin da aikin ya ƙunsa. Haka kuma an yi bayanin wasu fitattun al’amurra na bincike da suka haɗa da
hanyoyin gudanar da binciken da kuma ra’in da aka ɗora
binciken a kai da dai sauransu. Haka kuma, an yi tsokaci kan kalmar turare da
asalin samuwar turare da ma’anar turare. Kazalika, an kawo bayanin yadda turare
yake a wurin matan Hausawa. An kuma dubi rukunnan mata masu amfani da turare a
inda aka kawo bayanin na matsayin turare a fagen magani ko mahaɗin haɗa
maguguna. Har’ila yau, an yi bayanin kayan ƙamshi da yadda matan Hausawa na ƙasar
Hausa suke yin amfani da su. An kawo sakamakon bincike da kammalawa da kuma
manazarta.
Manazarta
Ado, A. (2017). Ra’o’in bincike kan
al’adun Hausawa. Kanki Classical, Enterprises.
Abubakar, A.T. (2014). Ƙamusun harshen Hausa. Northen Nigerian Publishingcompany.
Bunza, M.A (1990). Hayaƙi fidda na kogo: Nazarin siddabaru da sihirce sihircen Hausawa. Kundin
digiri na biyu. Sashen nazarin Harsunan Nigeria Jami’ar Bayero.
Bello, A.S. (2014). Dabarun gudanar
da bincike a Hausa: Unlimited Graphic. Prints.
Halima, Z. D. (2018). Zamani riga:
Nazarin tasirin zamananci a kan amaryar Baatsine a yau: Kundin digiri na biyu,
Umaru Musa Yar adua University.
Ibrahim, A.S.S. (2000). Magani da siddabaru
cikin rubutattun ƙagaggun labarun Hausawa:
Keɓaɓɓen nazarin litattafan gasar shekarar 1933 da 1978 da 1980. M.A Hausa
Culture Department of Nigerian Languages.Usman Ɗanfodiyo University.
Mu’azu, A. (2023). Baƙin a’ladu a ƙagaggun
littattafan soyayya na Hausa: Ahmadu Bello University Press Limited.
Mansur, I. (1290). Lisan Alab-ar.
Dictionary Wikipedia.
Muhammad da wasu, (2011). Tajul Arus:
Company of publication, daru sadir. Beirut.
Sa’id da wasu, (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero: Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero.
Sallau, (2009). Sana’ar wanzanci da
sauye-sauyen zamani jiya da yau: Kundin bincike wanda aka gabatar a tsangayar
fasaha da addinin Musulunci sashen koyar da Harsunan Nigeriya Jami’ar Bayero,
domin cika wani bangare na samun digiri na uku (ph. D) A fannin Hausa.
Skinner, N. (1999). Ƙamus na Turanci da Hausa. Northern Nigeria
Publication Company.
Sadik, M.A. (2014). Tasirin Zamananci a
adabin baka na Hausawa: Nazari a kan sara. Himma Journal of Contemporary Hausa
Studies Vol, 5. No. (1).
Tukur, B. (2015). Mata dangin ado: Nazari a
kan adon jikin mata jiya da yau, In Partial Fulfilment of the Reƙuirement for the Award of Masters Degree in Languages and Cultures, Ahmadu
Bello University.
hhtps://www.worldwidlife.org.
[1]Hira da aka yi da Farfesa Aliyu Muhammad
Bunza, ɗan kimanin Shekara 70 ta wayar tarho a ranar 26/5/2024.
[2] Hira da aka yi da Dr Muhammad
Mu’azu. Sa’adu Kudan, ɗan kimanin Shekara 61 ta wayar
tarho a ranar 1/9/2024.
[3] Hira da aka yi da Dr Kabir Ɗan asabe, masani a kan a bun da ya shafi
al’adun Hausawa mutimin garin Minna. Dan kimanin shekara 65 ta wayar tarho a
ranar 12/2/2024.
[4] Hira da Dr Abdullahi Yakubu
darma, ɗan Shekara 55 a gidansa da ke Rafin daɗi layin gidan Ali Guguwa a
ranar 6/7/2025.
[5] Hira da aka yi da Malama
Samira Ɗahiru, ‘yar
Shekara 49, a gidanta dake sharaɗɗa, hauren Shanu, gidan Alhaji Gwangwan, Kano a ranar
3/12/2024.
[6] Turgeza wata shafa ce da ake yi wa
amarya da kwaɓaɓɓen lalle da waɗansu nau’in turaruka masu ƙamshi, wanda ke sa amarya ta yi kyau, jikinta ya yi ja mai haske kuma duk inda za
ta shiga za a ji ƙamshinta.
[7] Wani mai ne marar maiƙo wanda ke ba fata kariya da kuma
sanya ta laushi da sheƙi da ƙamshi.
[8] Wani Iccen Magarya ne mai haske wanda ake yi wa
amarya turaren wuta na hayaƙi da shi domin hana dilkar da aka yi
mata ta fita da wuri. Sannan kuma zai riƙe dukkan turaren da aka sanya mata domin kada
ya fita da wuri.
[9] Hira da aka yi da Zara Ali Baba ‘yar
kimanin Shekara 50 a gidanta da ke Al’ansar Damaturu a ranar 5/6/2025.
[10] Hira da aka yi da Alhaji
Bishir Ƙamshi a Babbar
kasuwa (central market) Katsina layin ‘yan turare, ɗan
kimanin Shekara 55 a ranar 7/12/2024.
[11] Hira da aka yi da Hasana Lawal ‘yar
kimanin Shekara 60 a gidanta da ke unguwar rahamawa a cikin garin Katsina.
[12] Wani icce ne na ƙasar Indiya, murɗaɗɗe mai ƙamshi wanda ake yin turaren wuta da shi.
Ana haɗa shi a cikin kowane irin nau’i na Itacen turaren wuta
domin samar da wani nau’in ƙamshi. Ana yi mashi baƙar suya a sanya shi cikin Humra baƙa.
[13] Wani kayan ƙamshi ne na ƙasar Cana mai kama da dutse, yana da laushi ana daka shi a zuba cikin abubuwa da
yawa kamar, turaren wuta da Humra da kwalakca da dai Sauransu.
[14] Wani nau’in ruwa ne marar maiƙo mai ƙamshi, wani yana da sanyi wani ba ya da
shi. Akwai na Nijeriya da na Kwadebuwa da Paris, dukkansu ana yin kowace irin
Humra da su. Sannan ana yin turaren wuta na jiƙawa da su ko kuma a shafa shi haka nan
ba tare da an haɗa shi da wani abu ba.
[15] Sandal icce ne na ƙasar Indiya mai ƙamshi, ana yin turaren wuta da shi ko
turare na maiƙo mai Kauri
ko tsunkakke.
[16] Hira da aka yi da Hajiya Talatu ‘yar
kimanin Shekara 63, a gidanta da ke Gwange Zuwa da Wuri, Maiduguri a ranar
15/10/2024.
[17] Hira da Farfesa Ibrahim
Abdullahi ɗan kimanin
Shekara 55 a Jami’ar Umaru Musa ‘yar aduwa da ke Katsina a ranar 4/9/2025.
[18] Hira da aka yi da Malama Gajen
Gawuna, ‘yar kimanin Shekara 48 a gidanta da ke Ceceniya a ranar 2/11/2024.
[19] Hira da aka yi da Zuwaira Isa, ‘yar
Shekara 49 a gidanta da ke bayan gidan Audu na Malam, Bindawa, Katsina a ranar
9/12/2024.
[20] Juda dai wata dabba ce ta ƙasar Hausa mai kama da Mage amma ta fi
Mage girma, wasu suna kiranta da Magen Juda ko Mazurun Juda. Tana fitar
da kashi mai ƙamshi, tana haihuwa kamar mage. Allah ya yi
mata tsawon rai, ba ya ga turare da take fitarwa har’ila yau tana yin maganin
cututtuka da dama.
[21]Hira da aka yi da Alhaji Surajo mai
Asharalle ɗan kimanin Shekara 61 a gidansa da ke Ƙofar Ƙaura,
Katsina a ranar 20/5/2025.
[22] Wani, nau’in magani ne na ƙasar Hausa, kuma iri ne na lansir wanda
ake kwaɗawa a ci, yana da wani irin ƙamshi mai kamar kayan yaji. Ana maganin
mayu da shi da kuma maganin ƙuraje, ana daka shi a haɗa da jar kanwa a jiƙa da ruwa a shafa wa ƙurji, sannan ana daka shi a zuba acikin
fura ko nono a sha wanda ke ciki za su mutu.
[23] Hira da aka yi da Malam
Muhammadu ɗan kimanin Shekara 50 a gidansa da ke unguwar Alƙali ɗan hili Katsina a ranar
17/6/2024.
[24] Tsanki wani ciwon ciki ne wanda
iskokai ke sakar wa mace jini da kuma hana ta haihuwa.
[25] Hira da aka yi da Malam
Muhammadu, ɗan kimanin Shekara 50 a gidansa da ke unguwar Alƙali ɗan hili, Katsina, a ranar
17/6/2024.
[26] Hira da aka yi da Malam Rabi’u
Sada, ɗan kimanin Shekara 60 a gidansa da ke sabon layi Mashi, Katsina, a
ranar 1/2/2025.
[27] Wata ciyawa ce mai tauri, da
wuyar ɗiba dabbobi ma da wuya su ci irin ta.
[28] Hira da aka yi da Malam Umaru Ɗahiru, ɗan kimanin Shekara 52 a
gidansa da ke ramin gari Katsina a ranar 30/11/2024.
[29] Hira da aka yi da Malam Rabi’u
Sada ɗan kimanin Shekara 60 a gidansa da ke sabon layi Mashi, Katsina a
ranar 1/2/2025.
[30] Hira da aka yi da Bilki mai Kitso,
‘yar kimanin Shekara 74 a gidanta da ke unguwar Gabas a garin Doro Katsina a
ranar 19/12/2025.
[31] Hira da Malam Ummaru, ɗan kimanin Shekara 52 a
gidansa da ke ramin gari Katsina, a ranar 30/11/20/24.
[32] Turaren Kiko ya samo asali daga
Indiya, Kiko sunan wani Aljani ne wanda yake tun a zamanin Annabi Sulaimanu A.S
a lokacin shi ne yake riƙe da taskokin da dukiya take. Idan za
a kira shi a kwai wuridan da ake yi bayan an gama sai a turara turaren wuta
idan ya bayyana kuma za a sanya turaren ruwa. daga nan za ya ba da sharuɗɗa da dokoki idan an yi biyayya za a
samu biyan buƙata sosai.
[33] Hira da aka yi da Abba
Abbati, ɗan kimanin Shekara 73 a gidansa da ke Rafindaɗi ƙaramin
rafi, Katsina a ranar 3/6/2024.
[34] Hira da aka yi da Malama Karbiya
‘yar kimanin Shekara 60 a gidanta da ke Rafindaɗi bayan gidan Ali
Guguwa, Katsina a ranar 5/2/2025.
[35] Hira da aka yi da Ali Zajeri ɗan
kimanin Shekara 52 a wayar tarho a unguwar Bolori bypass Maiduguri a ranar
10/10/2024.
[36] Hira da aka yi da Hajiya A’isha
Shakka ‘yar kimanin Shekara 55 a gidanta da ke Rafindaɗi layin Gobirawa a ranar 5/3/2025.
[37] Hira da aka yi da Malam Abba Almu
Mai Turare, ɗan kimanin Shekara 74 a gidansa da ke Rafindaɗi kusa da tabkin Asama a ranar
5/2/2024.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.