Ticker

6/recent/ticker-posts

Salon Karin Magana A Wakokin Karni Na 21: Duba Kan Wasu Daga Cikin Makada

Citation: Muhammad ADAMU & Ahmed Sulaiman BAFFA (2025). Salon Karin Magana A Waƙoƙin Ƙarni Na 21: Duba Kan Wasu Daga Cikin Makaɗa. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 13, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

SALON KARIN MAGANA A WAƘOƘIN ƘARNI NA 21: DUBA KAN WASU DAGA CIKIN MAKAƊA

NA

MUHAMMAD ADAMU PH.D

AHMED SULAIMAN BAFFA

Tsakure

A wannan takarda an nazarci wasu karin maganganu a waƙoƙin ƙarni na ishirin da ɗaya, waɗanda suka tasirintu wajen gane irin salon da waƙoƙin ƙarni na ishirin da ɗaya suke ɗauke da shi ko tabbatuwa. A cikin aikin, an yi amfani da waƙoƙin ƙarni na ishirin da ɗaya ne kaɗai da suke ɗauke da wannan azancin magana, waɗanda aka zaƙulo su daga mawaƙa daban-daban na Arewacin Nijeriya. A binciken an yi amfani da waƙoƙin mawaƙa irin su: Nura M. Inuwa da Ali Mega da Hauwa ’Yar Filani da Dauda Kahutu Rarara da Kamilu Husaini Nguru da sauransu. Sannan an bi hanyar tattaro waƙoƙin ta amfani da wayar salula, an saurari waƙoƙin aka juya su a kan takarda, da duba littattafai da muƙalu. An ɗora wannan aiki a kan littafin ‘Salo Asirin Waƙa’ na Yahya, A. B. (2001). Binciken ya gano cewa mawaƙan wannan ƙarni, sun bi sahun waɗanda suka gabace su wajen amfani da irin wannan salo na amfani da karin magana a cikin waƙoƙinsu, ko ma a ce sun fi mawaƙan da suka gabata wajen yawan amfani da salon yayin gudanar da waƙoƙinsu. Saboda haka, sauye-sauyen da aka samu na zamani, bai iya rage wa wannan salo armashi ba a cikin waƙoƙin nasu. Don haka salon karin magana na taka muhimmiyar rawa wajen jawo hankalin masu saurare a wannan ƙarni na 21. Hakan ya nuna ƙwarewa da fasahar mawaƙan wajen sarrafa harshe, duk da cewa suna kwaikwayon salon waƙoƙin Turawa da na Indiyawa a wajen tsara waƙoƙin nasu.

1.0 Gabatawa

Kasancewar waƙa aba ce mai saurin kama zuciya da kuma isar da saƙonni masu muhimmanci ga al’umma, wannan ya sa masana da manazarta suka mayar da hankali a kanta. Tun daga ƙarni na sha bakwai (ƙ17) aka fara samun ɓirɓishin rubutattun waƙoƙi irin su; ‘Waƙar Daliyya’ da ‘Nuniyya’ da ƙasidar ‘Muzjiratul Fitiyan’ ta Wali Ɗanmarina. Sha’anin waƙa ya ci gaba da wanzuwa har ƙarni na sha takwas (ƙ18) lokacin da aka samu malamai irin su; Malam Muhammadu na Birnin Gwari wanda ya yi waƙoƙi da dama, waɗanda suka haɗa da; ‘Ma’akusa’ da ‘Billahi Arumu’. Haka kuma akwai Malam Shi’itu ɗan Abdurra’ufu wanda ya yi waƙoƙi da dama kamar; ‘Fassarar Arshada’ da ‘Waƙar Tuba’. A ƙarni na 19 (ƙ19) kuma aka samu mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo a (1754-1817) da almajiransa sun yi waƙoƙi da dama masu manufofi na addini kamar ‘Waƙar Cin Birnin Alƙalawa’ da ‘Waƙar Tsarin Mulkin Musulunci’ ta Abdullahi Fodiyo da sauransu (Yahaya, 2002:37-59). A ƙarni na ashirin (ƙ20) al’amarin waƙa ya zama muhimmi. Jigoginta suka faɗaɗa daga manufofi na addini suka haɗa da al’amuran rayuwar duniya. An yi waƙoƙi da dama kamar ‘Waƙar Zambon Ƙazama’ ta Aliyu Namangi da ‘Waƙar ‘Yar-gagara’ ta Aƙilu Aliyu da sauransu a wannan ƙarni. Sun yi fice da nuna ƙwazo wajen bayyana fasaharsu a fagen sarrfa harshe, domin sun bi sahun magabatansu mawaƙa wajen amfani da salon karin magana ta kowace fuska, irin yadda ake samu a waƙoƙin ƙarni na 17-19, ko fiye da haka. Waƙoƙin ƙarni na ashirin da ɗaya (ƙ21) su ma sun tasirintu da salon mawaƙan ƙarni na 17-20 na amfani da karin magana. Sukan sa shi ganin yadda waƙoƙin magabatan ke samun shiga wajen masu saurare, domin azancin magana na yin tasiri a zukatan mutane, ganin abubuwa ne da suke sha’awan su ji.

2.0 Bitar Ayyukan Da Suka Gabata

Waƙoƙin ƙarni na ashirin da ɗaya (ƙ21) waƙoƙi ne da suka bambanta da na lokutan baya (17-20), ta fuskokar jigogijsu da zubinsu da wasu salailansu. Wannan ya haifar da tsananin buƙatar sake nazarin su don gano abin da ke faruwa a cikinsu game da salon karin magana, saboda waƙoƙin sun zo da wasu sabbin tsari na aiwatarwa, kamar yanayin jagoranci inda ake samun jagora fiye da ɗaya, da haɗuwar maza da mata cikin jagorancin. Don haka a ka dubi yanayin salon karin magana a waƙoƙin.

2.1 Ma’anar Salo:

Kalmar salo ba baƙuwar kalma ba ce ga Bahaushe da kuma a fagen nazari. Don haka masana da kuma manazarta harshe ta fuskar adabi sun ba da gudummowa wajen bayyana ma’anar salo cikin jumloli dogaye da gajeru.

Yahya, (2016:1-3) ya bayyana ma’anar salo da: “Dabara ko hanya ko wayo” ko kuma “Salo kwalliyar magana ce mai tasiri kan mai jin ta”. Ya ci gaba da cewa a dunƙule, “Salo dabara ce ko hanya mai yin kwalliya ga abu domin abin ya kwarzanta ko ya bayyana”.

Gusau, (2003:54) cewa ya yi, “Salo wata hanya ce da ake bi a nuna gwaninta a cikin furuci ko rubutu, kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta bin yanayin harshensa, ko zaɓar abubuwan da suka dace da abin da yake son bayyanawa”.

Ɗangambo, (2007:37) ya ba da ma’anar salo da cewa, “Bisa jimla muna iya cewa salo shi ne hanyoyi ko dabarun isar da saƙo”.

Sarɓi (2007:153) yana cewa, “Dabarun jawo hankali ko hanyoyi ne da marubuta waƙoƙi suke amfani da su ta hanyar sarrafa kalmomi da maganganu domin cusa sha’awa da jin daɗi ga mai karatu ko mai sauraren waƙoƙainsu”. Irin waɗannan dabarun suna ƙarfafa wa mai karatu ko saurare guiwar kaiwa ga ƙarshen waƙa.Yin hakan kuwa shi ne zai sa mutum ya fahinci irin saƙon da ake son sadarwa zuwa ga al’umma.

Idan aka dubi diddigin yadda waɗannan masana suka ba da ma’anar salo, za a iya cewa lallai salon a nufin dabara ko hanya da kan sa hankali ya karkato har mai saura ko mai karatu ya fahimci abin da ake nufi. Alal misali, su kansu waɗannan masana da aka ambata, kowannensu ya yi amfani da salo wato dabararsa wajen ƙoƙarin gamsar da mai karatu ya fahimci ma’anar salo. Misali: Yahya, (2016:1-2) ya kwatanta salo da bin diddigin ƙuruciyar yaro a tsakaninsa da mahaifiyarsa inda takan ce da ɗanta “Kai raba ni da salo” musamman idan yaron na buƙatar wani abu. A nan ne ya nuna lallai salo shi ne dabara ko hanya wadda a cewarsa ita ce dahir. Ya ci gaba da bayaninsa cikin dabara inda, ya danganta ma’anar salo da ƙaulin Hausawa da sukan ce “Salon magana” ko “Sabulun salo”, wato magana ba wadda aka saba ji ba, ko kuma sabulu ba wanda ake saurin kawowa a zuciya ba.

2.2 Ma’anar Karin Magana

Karin magana shi azancin magana ne mai zuwa cikin wasu ‘’yan guntayen maganganu, ko zantuka da ke kasancewa cikin gaɓa-gaɓa ko gunduwa-gunduwa domin isar da saƙo na musamman. Karin magana ya kasance daga muhimman ɓangaren salon sarrafa harshe da mawaƙa ke yi wa waƙarsu ado da kwalliya da shi don jan hankalin masu sauraro da masu karatu. Don haka, masana suka duƙufa wajen bincike da bin diddiginsa a cikin zantuka da rubuce-rubucen adabi. Masana da dama sun bayyana ma’anar karin magana ta sigogi daban-daban cikin jimloli mabambanta.

Sarɓi, (2007:131) ya bayyana karin magana da cewa, “Gajeruwar jimla ce wadda ta ƙunshi ma’ana mai faɗi. Kuma ya ƙara da cewa, “Hikima ce da ta shafi fasahar dunƙule magana mai yawa wuri ɗaya”.

Karin magana wata “’yar gajeriyar jimla ce ta hikima; wadda ta ƙunshi ma’ana mai yawa in za a tsaya a yi bayaninta” (Muhammad, 2003:59).

Karin magana wata “dunƙulalliyar magana ce ta hikima ɗauke da ma’ana mai yawa wato dai, ɗabi’a ce da Hausawa ke ɓoye manufa a cikin zance” (Abba da Zulyadaini, 2000:140).

3.0 Salon Karin Magana A Waƙoƙin Ƙarni Na 21

Ana samun karin magana a cikin waƙoƙin ƙarni na 17-20, amma ba su yawaita kamar a na waoƙiƙin ƙarni na 21 ba. Lamarin amfani da karin magana ya ƙaru sosai, har ta zama fili ne da mawaƙan ƙarni na 21 ke baje kolinsu su yi ciniki kuma har su ci riba a kasuwar wannan salo. Mawaƙan ƙarni na 17-20 sun yi amfani da shi a zaman jigogi na yaɗa saƙonninsu, kasancewa waƙoƙin nasu suna, gargaɗi da nasiha da ta’aziyya da wa’azi, da yakan zama hannun-ka-mai-sanda ga al’umma. Sai dai an samu ƙaruwa da bunƙasar amfani da wannan salo a wannan ƙarni na 21 sakamakon ilimin boko da wayewar zamani, wadda ta sa samari da ’yanmata ke amfani da karin magana a matsayi birgewa ko wayewa. Haka kuma an yi sa’a mafi yawa mawaƙan matasa ne, kuma sun yi karatun boko. Shi ke nan sai faɗuwa ta yi daidai da zama. Kusan ana iya cewa a ƙarni na 21 wannan salo shi ne gwanintar harshe mafi girma da mawaƙa ke amfani da shi domin nuna gwanintar harshe. Ga misalin da aka zaɓu daga wasu matasan mawaƙan nan da aka nazarta kamar haka:

3.1 Waƙoƙin Nura M. Inuwa

Mawaƙi Nura M. Inuwa a Waƙarsa mai suna “Sannu Amarya” ga abin da ya ce:

Fitsari shi in banza ne kaza taiyi man,

To wani in yai an yaba wani duka za ya ci da’iman,

 Idan sauƙi kake so a gida ka je wuman,

 Mutum ba a iya mai gane wannan a badan,

 Makaho ba ya gane bambanci kogi da ƙar.

 (Waƙar Sannu Amarya)

ɗango na farko, mawaƙi ya yi amfani da karin magana cewa ‘In fitsari banza ne kaza ta yi man’. A ɗango na biyu kuma an samu karin magana mai cewa ‘Inda wani ya yi rawa aka yaba aka ba shi kuɗi, in wani ya yi duka zai sha’. Wannan baiti ya tabbatar da gaskiyar samuwar karin magana a cikin waƙoƙin ƙarni na 21 fiye da ƙarnukan da ke gansa, inda aka samu karin magana biyu a baiti ɗaya.

Sannan an sake fito da wani misali a waƙar Nura M. Inuwa cikin waƙarsa ta ‘Manubiya’, ya yi amfani da wannan salon ne domin jawo hankalin masu sauraronsa. Ga karin maganar da ya yi amfani da ita a cikin ɗangon waƙar tasa kamar haka:

 Rashin sani na san bai kai dare duba,

Iya biyayya na yi maka, kai ba ka kula ba,

So babu reno inda yake ba zai tsaya ba,

 Dalilin da ya sa amanar da ka ba ni na sake ta,

 (Waƙar Manubiya)

Ya sako shi ne a cikin ɗango na farko kamar yadda aka gani a nan sama. Wannan karin magana da ya yi amfani da ita a rubuce ba haka karin maganar take ba, amma saboda larurar waƙa ya sauya ya saka ta a hakan. Yadda karin maganar take asalan shi ne rashin sani ya fi dare duhu. Ataƙaice Nura ya juya maganar ne zuwa wata fuska ta daban.

A wani misali da aka fito da shi daga waƙar Nura M. Inuwa, ya yi amfani da irin wannan salon sarrafa harshe na karin magana a cikin waƙarsa ta ‘Hussuna da Huzzuna’. Ga abin da yake cewa a waƙar kamar haka:

 Hussuna ke da Huzzuna, yau guna kun zamo masoya,

Bambancinku ko suna, bai da yawa ko za a juya,

Har in babba yana da laifi yaro ma yana da ƙiwa,

 Kun samin farin ciki, ku za ku fitar da yadda zan yi,

 (Waƙar Hussuna da Huzzuna)

A wannan baiti mawaƙin ya yi ƙoƙarin nuna yadda idan babba ya so kansa, na ƙasa da shi ba zai masa yadda yake so ba. Wato ya yi amfani da karin maganar nan dake cewa “Laifin babba rowa yaro ƙi wuya”. Wannan yana koyar da darassin cewa, shi babba ya kyautatawa na ƙasa da shi ko da dattijo ne, domin yin rowa ba abu ba ne mai kyau. Mawaƙin ya yi hakan wajen yin hannunka-mai-sanda ga wani.

3.2 Waƙoƙin Ali Mega

Sannan a ɓangaren mawaƙi Ali Mega, shi ma akwai wurin da ya yi amfani da irin wannan salo na karin magana a cikin waƙarsa mai suna “To A Yi Dai Mu Gani”. Ga abin da yake cewa:

 To APC Yobe ku ji ƙarshen fa alewa ƙasa,

 Talakawa mun gane jemage fa ba ya taka ƙasa,

 Sai mun kada mazalunta domin bana ga damarmu kusa,

 Sangami bana to milki na jiha ka taka ƙasa,

 Bana to ba za mu yi ba, ɗan tamore ka tashi ba za ka ci ba.

 (Waƙar To A Yi Dai Mu Gani)

A wannan ɗango mawaƙin ya yi amfani da karin magana na ‘Ƙarshen alewa ƙasa’ ne, domin ya fito da bayani kan zalincin da azzalumai daga jam’iyyar APC ke yi wa talakawa. Ya nuna hakan ba mai ɗorewa ba ne.

Har ilau, cikin wata waƙa ya yi amfani da karin magana wajen ƙulla babban manufar ko saƙon waƙarsa. Ga abin da yake cewa:

 Masu mulkin bambanci da ƙabilanci bana za ku gani,

 Dukkan mu Musulmi ne amma kunka ware kanku tuni,

 Mu Filani kun ƙi mu kun ƙi Hausawa, to za ku gani,

 Matsayi kun ƙwace kun ci nama mu kun bar mu da jini,

 Allura ƙarfe ce a kiyaye, in an ƙi ko za a gani,

 To mu zuba mu gani mulkin nan dai ba za ku ci ba.

 (Waƙar APC Ta Yobe)

Cikin wannan baitin, mawaƙin ya yi da wasu da suka yi zalunci cikin tafiyar. Ya nuna mu su ba za su yi nasara ba, domin son kansu da yin ƙyaliya da sauran al’umma Filanai da Hausawa. Ya sako wannan karin magana ne na cewa idan fa ba su yi hankali ba, allura za ta tono garma, domin bambanci harshe da yare da jam’iyyar APC take yi a Yobe.

3.3 Waƙoƙin Hauwa ’Yar Fulani

Ita ma mawaƙiya Hauwa ‘Yar Fulani shahararriyar mawaƙiya ce a wannan ƙarni na 21. An sami wata wata da ta yi amfani da irin wannan salo a cikin waƙoƙinta. Ga misalin abin da ta ce cikin waƙarta, kamar haka:

 Ina tuya ashe ban sa albasa ba,

 Domin giwa uwar dawa ce babba,

 Bukkar daji kamar ki ba za ai ba.

 (Waƙar Yankari)

Wannan mawaƙiya ta yi amfani da karin magana a ɗango na farko mai cewa ‘An yi tuya an manta da albasa’. Domin cikin yabo da ta yi, ta manta ta yabi da kuma zuga dabbar da ta waƙe.

Baya ga wannan baiti da ke sama. An sake fito da wani baiti a wata waƙar Hauwa ’Yar Fulani da ta yi amfani da karin magana, domin jan hankalin masu saurare. Ga abin da ta ce a wannan baiti kamar haka:

 Sansanin dabbobin al’ajabi,

 Kakaninsu har iyaye tuni,

 Rayuwarsu nan suke ban da ni,

 Hawwa nake ’yar gidan fulani,

 Wata rana in shuɗe babu ni,

 In bar ’ya’ya da jikanu dausayi,

 Yau da gobe sai Allah, mabuwayi,

 Kakaninmu sun mace kan mu zo.

 (Waƙar Dabbobin Al’ajabi)

Mawaƙiyar ta yi amfani da wannan baiti ta yabi dabbobi, wanda cikin dabbobin ma waɗanda suke da abubuwan al’ajabi. Ta faɗi yadda rayuwarsu take kasancewa a inda suke, kuma ta amfani da karin maganar ‘yau da gobe ai sai Allah’. Domin yau su ne, wata rana kuma ba su ba ne.

3.4 Waƙoƙin Kamilu Husaini

Sai kuma sarkin mawaƙan jahar Yobe Kamilu Hussaini Nguru, wanda ba a bar shi a baya ba, shi ma ya yi amfani da salon karin magana a waƙarsa da ya yi ta Atiku Bagudu, inda yake cewa:

 Tabbas ka ga jaki ya yi shiru, wataƙil ya shaƙu da kaya ne,

A jihar Kebi mun samo canji,

Kowa ya ci zomo ya ci gudu, wataƙil kalmar jiya kun gane,

A jihar Kebi mun samo canji,

 Zaɓe fa su gundira sun faɗi dila ko ba ki akwai sata.

 (Waƙar Atiku Bagudu)

Kamilu Hussaini kuwa a ɗango na uku karin magana da ya yi amfani da ita wato ‘kowa ya ci zomo ya ci gudu’. Ya yabi Bagudu kan yadda yake tafiyar da al’amurarsa a kan mulki, domin ba ya ƙaƙƙautawa yin aiki sai zafin nama.

A ci gaba da fito da misalan karin magana a waƙoƙin mawaƙan ƙarni na ashirin da ɗaya, an sake ci karo da wani baiti mai ɗauke da wannan azancin maganar a wata waƙar mawaƙin nan. Domin ya yi amfani da salon ne da yake nuna yadda muhimmancin azanin magana a cikin waƙoƙinsu da ganin yadda masu saurare suke samun nishaɗi da nishaɗantarwa. Ga abin da yake cewa a baitin wannan waƙar tasa kamar haka:

 Mulkin ga idan mun kula,

Zomo ba ta zuwa kasuwa banza,

 Mu tuna fa akwai sabon zuwa.

 (Waƙar Garkuwan Matasa Brabra)

A wannan baitin mawaƙin ya jawo hankali da fakar da mutune kan yadda al’amuran mulki yake. Wato ya nuna cewa ba haka kawai ya hau kan mulki ba. Ya yi amfani da wannan karin maganar ce, domin shaida wa mahassada Allah shi yake yi sa ya zama gwamnan Jihar Yobe, ba wayonsa ba ne, kuma ba da ƙarfi ba.

3.5 Waƙoƙin Dauda Kahutu Rarara

Haka kuma Dauda Kahutu Rarara, a waƙarsa ta “Mai Malafa Ƙarya Ta Ƙure”, ya yi amfani da karin magana, kuma ga abin da ya ce:

 Mai malafa ƙarya ta ƙure,

Shure-shure fa bai hana mutuwa,

Mai malafa ƙarya ta ƙure,

 Ƙafafu gatan hannuwa.

 (Waƙar Mai Malafa Ƙarya ta Ƙure)

Dauda Kahutu Rarara a nan ya yi amfani da wannan karin magana na ‘Shure-shure ba ta hana mutuwa’ domin wayar da kan jama’a cewar za a ci nasara, ganin cewa mai malafa ba zai iya jan hankalin mutane ba, domin an riga an gane sharrukan cikin mulkinsa.

Rarara bai tsaya a nan ba, wajen amfani da irin wannan hikima ta magana a cikin waƙoƙinsa. Ya ƙara fito da wata karin magana a wata waƙarsa kamar haka:

 Yau gashi duk ’yan’uwanka suna fushinka,

 Ka saurari ƙorafi na abokanka,

 Dole masoyan ƙwarai su ji tausayinka,

 Sai ai rabo a cikin gidanka,

 Sannan ka zo a hana ka ɗauka,

 Don ka sallama waɗ an kamashon gidanka,

 Rashin jini a hana a yanka,

 Tsaya da ƙafarka Abba, kar su hana ka aiki.

 (Waƙar Tsaya Da Ƙafarka Abba)

Wannan karin magana mai habaici ce da mawaƙin ya yi amfani da ita, domin nuna wa ko kiran Abba kan yadda mutane suke kallonsa. Ya yi bayani cewa, kar ya yarda ya bar wasu su kwashe masa ƙafafu. Saboda haka, kar ya manta da ’yan’uwansa da abokansa wajen taimaka musu. Kusantaka ba zai hana su yin ƙorafi ba, sai dai ya gyara.

3.6 Waƙoƙin Nura M. Inuwa Da Adam A. Zango

A waƙar da Nura M. Inuwa da Adam A. Zango suka yi haɗaka a kai wadda suka mata laƙabi da “Maƙiya A Zango Ƙaryar Ku”. A nan sun yi amfani da karin magana kamar haka:

 Ba gudu cikin magana tasu ba batu na ciki,

Yarfe ne suke sun ce wai yana da auri saki,

Mai gida ya san inda yake yi mar zubar ɗaki,

Mu bar wannan magana sirri ba zan faɗa wa kowa ba.

 (Waƙar Maƙiya A Zango Ƙaryar Ku)

Mawaƙan sun yi amfani da wannan karin magana ‘Mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo’ ne domin nuna wa maƙiyansu har yanzu suna nan. Wannan maganar da ake zarginsa da ita ba haka ba ne, shi ya san abin da yake faruwa.

Sannan a cikin wani ɗangon waƙar sun ƙara amfani da wani karin magana kamar haka:

 Sara da sassaka ba ya hana tofuwar gamji,

Zango kai ruwa ne mai ɗauke guguwar daji,

Tunda ka riƙe Allah cikin gida da ma daji,

 Masu ƙin ka sun taɓe suna ganin ba ka kai ba.

 (Waƙar Maƙiya A Zango Ƙaryar Ku)

A cikin ɗangon da ke sama Nura ya yi anfani da karin magana na sara da ‘Sassaƙa ba ya hana gamji toho’. Wato yana nunawa mahassada cewa Adam Zango ba kanwar lasa ba ne, murucin kan dutse ne, bai fito ba sai da ya shirya. Saboda haka, ba yadda za su yi da shi sai kallo.

Bugu da ƙari, shi ma Adam A. Zango ya kawo wannan salo na karin magana cikin wannan waƙa, ga abin da yake cewa:

 Ku zo ku shaida yadda mahassada suke tonon rami,

Su ƙirƙiro sharri su manna sannan su ɗau kalami,

Don su ɓata suna nai su dai da kalami,

 Ciki da gaskiya tsini ba zai masa huda ba.

 (Waƙar Maƙiya A Zango Ƙaryar Ku)

ɗango na huɗu a wannan baiti an yi amfani da karin maganar ‘Ciki da gaskiya wuƙa ba ta huda shi’. Mawaƙin yana nufin a rayuwa mutum mai gaskiya ba zai taɓa wulakanta ba, kar a ji tsoron yin gaskiya. Ya yi amfani da shi wajen kushe mahassada, domin abu ne mara kyau.

3.7 Waƙoƙin Yahaya Bala Sauwa

Mawaƙi Yahaya Sauwa shi ma ya yi amfan da irin wannan salon sarrafa harshe a cikin waƙarsa ta “Dogaronka Allah Zaki Ɗan Zaki.” Ga abin da yake cewa:

 Abin da ka kashe baya a fatin APC, Allah kaɗai ya ke sakayya na duba,

 Ka ɓata dukiyarka da ƙarfinka sadaukarwa har yanzu ga shi ban ga alamar jinƙai ba,

 Kura da shan bugu gardi da kwashe kuɗɗin shi, mai yaudara ba zai iya halin girma ba,

 To Abu Walid ka kai dattijo, ka ba su baya ba tare da buƙatar komai ba.

 (Waƙar Dogaronka Allah)

A wannan ɗango ya yi amfani da karin maganan ne mai cewa ‘Kura da shan bugu gardi da kwashe kuɗi’. Wato ya nuna yadda gwanin nasa ya yi hidima ga jam’iyyar, amma babu wani abu na a zo a gani game da abin da jam’iyyar ta yi masa. Sannan ya kurarata maigidansa kan irin hidimar da ya yi ma jam’iyyar tasa.

A ganin cewa ya kamata ya ƙaro wani ƙarin maganar, ya kawo hakan a cikin wata waƙarsa. Inda yake cewa:

 Yunƙuro ka bar shakka Ibrahim ɗan zaki,

 Yanzu ’yan jihar Kebi na da buƙatar irinka dattijo,

 Tun da taimakon al’umma halinka ne uban Ansar,

 Haƙuri na sa a dafa dutse, sannan a sha romonsa,

 Ga Ciroma nan na Kabawa mai hanƙuri da adalci, uba.

 (Waƙar Alheri)

Galibi mawaƙa kan yi amfani da irin wannan dabara wajen ɗaukaka gwaninsu. Cikin wannan ɗango a layi na huɗu, mawaƙin ya sako wannan karin magana wajen yaba masa da irin ƙoƙarin da yake yi ga jama’arsa na taimakawa ba kama hannun yaro. Ya kuma nuna haƙurinsa cikin amfani da wannan magana ta hikima.

3.8 Waƙoƙin Ɗahiru Na Maikwari

Shi kuma Ɗahiru Na Maikwari a waƙar da ya yi wa Abu Magaji, a cikin waƙar akwai wurin da ya sako karin magana. Ga abin da yake cewa a wani ɗangon waƙa:

 Ba za ni fara tuya ba na manta da albasa,

 Kin ga amarya mai yin kyauta da mashina,

 Da Umaima kun haɗa kanku zama da lafiya.

 (Waƙar Abu Magaji)

MawaƙƊahiru ya yi amfani da wannan karin maganar na ‘An yi tuya an manta da albasa’. Shi kuma ya sako wannan maganar a cikin waƙarsa ce domin ya manta da ya yaba amarya. Shi ne ya ce, ba zan yi tuya in manta da albasa ba, a ɗango na farko na wannan baiti. Wato ya yi wannan dabarar ce ganin kar ya rasa abin da ya kamata a bashi.

Har ilau, Makwari a wata waƙarsa da ya sake sako irin wannan azancin magana, ita ce, waƙar ‘Maharba Muke’. Ga abin da ya ce:

 Zance ake gurin kyauta ka basowa,

 Faɗin jiharmu yau Magaji ya yi basowa,

 Bai handama da buri bai bai wa karuwa,

 In an ƙi ji, baba to ba a ƙi gani ba nawa,

 Wasu sun ƙi bin sa sai gashi suna cikin ruwa,

 Da na sani suke yi ya baba garkuwa,

 Kowa ɓata ta kama shi ya yi ɗimuwa,

 Ku ƙyale kurma bai iya maggana.

 (Waƙar Maharba Muke)

A nan, mawaƙin ya yi amfani da wannan Karin maganar ce wajen nuna wa maƙiya Magaji sun ɓata. Wato ya yi bayani da cewa, rashin biyayya ya sa sun rasa duk wani abin da ya tanada domin su, amma gashi sun ɓarar. Ya sako wannan dabarar ce ta nuna musu, gani ga wane….. Saboda haka, dukkanin masu son abun hannun Magaji, sai su zo a yi tafiyar da su.

3.9 Waƙoƙin Amiuu Ladan Abubakar

Aminu Ladan Abubakar da aka fi saninsa da Alan waƙa, shi ma ya sako karin magana cikin waƙarsa ta ‘An Fa Gane Wanzami’. Ga misalin ɗangon waƙar da yake cewa:

 Rama cuta ga macuci ba illa ne ba

 Kar ka juya juyayye, Alan waƙa,

 Kar ka rikita rikitacce, Alan waƙa,

 (Waƙar An Fa Gane Wanzami)

Mawaƙi Ala ya yi anfani da wannan karin magana mai cewa ‘Rama cuta ga macuci ibada ne’ domin yin wa’azi ko nasiha ga mutane. Wato idan aka yi muku laifi za ku iya ramawa, amma barinsa ya fi alheri. Allah a cikin Alƙur’ani ya faɗi hakan, sai dai cewa ya yi kar a rama shi ne mafi alheri, wato in an yi haƙuri ya fi.

Har ila yau, Aminu Ladan Abubakar a cikin waƙar nan tasa ta ‘An Fa Gane Wanzami’, an fito da wani ɗango da ya sake ƙara amfani da karin magana, domin fito da wasu abubuwa fili ga masu saurare cikin rayuwar yau da kullum. Ga abin da yake cewa:

Sara da sassaƙa ba sa hana gamji toho ba, Alan waƙa,

Kainuwa dashen Allah ba shukawar mutane ba,

Duk tsoron da Allah yake so zai tsuro, Babu tababa,

 Ba da kai ruwa gumba, Alan waƙa.

 (Waƙar An Fa Gane Wanzami)

Cikin ɗangon nan dake sama, Alan waƙa ya yi wannan karin maganar ‘Kainuwa dashen Allah ba dashen mutane ne ba’, domin nuna wa mutane a daina hassada. Abin da Allah ya bai wa mutum, kar a ce za a yi jayayya da shi. Wato hassada cta ce, domin kan kai mutum ga kushewa.

4.0 Kammalawa

Waƙa aba ce da take da tasiri a wurin jama’a ganin yadda amfaninta ke da muhimmanci cikin rayuwar yau da kullum. Wannan ya sa a koyaushe take shiga zukatan mutane, domin ire-iren saƙonni da ke tattatare da shi. Saƙon da waƙa take ɗauke da shi kan sa a fahimci inda ta dosa, kamar irin su: faɗakarwa da gargaɗi da wa’azi da nasiha da ta’aziyya da siyasa da zuga da yabo da soyayya da roƙo da sauransu. Sannan cikinsu, mawaƙan kan sako ƙananan saƙonni da suke taimakawa wajen gina babban saƙo. Cikin irin ƙananan saƙoninnan da akwai: karin magana da kirari da zambo da habaici da ba’a da tarihi da raha da sauransu. Waɗannan suna taimakawa kan tasirintuwan waƙoƙin mawaƙan, mawaƙan gargajiya da na zamani, musamman ma kamar yadda aka yi amfani da fito da karin magana a cikin waƙoƙin mawaƙan ƙarni na ashirin da ɗaya (ƙ21).

Wannan aiki da aka yi ya shafi mawaƙan zamani na ƙarni na ashirin da ɗaya (ƙ21). An gano cewa mawaƙan na yawan amfani da karin magana wajen isar da ƙananan saƙonnin waƙoƙinsu, ta bin wannan hanyar ce yake taimakawa wajen yin manyan saƙonni na yabo ko zuga ko hannunka-mai-sanda ga waɗanda ake yi waƙar domin su. Sannan mawaƙan da aka yi amfani da su sune, matasan mawaƙan nan da suka shahara wajen yin waƙoƙin soyayya na zamani waɗanda mafi akasari ake samun su cikin finafinan Hausa da waƙoƙin ta’aziyya da na sha’awa kamar na Alan waƙa da waƙoƙin siyasa da sauransu da ke fitowa a bakin irin su Kahutu Rarara. Baya ga haka, waƙoƙin da aka nazarta sun taimaka wajen nuna ire-iren karin magana da suke fito ko waɗanda mawaƙan suka yi amfani da su a cikin waƙoƙinsu.

Har wa yau, a wannan takarda an lura cewa salon da mawaƙan suka yi amfani da shi a cikin waƙoƙinsu, sun nuna salo ne mai jan hankali, salo ne mai kwaɗaitar da masu sauraro da ba za su gaji sauraron waƙoƙin nasu ba. Domin amfani da karin magana da mawaƙan sun dace ne saƙonnin da suke so su isar.

Daga ƙarshe, wannan aiki da aka yi, ya bada ƙarfin gwuiwa da ya samar wa ɗalibai da manazarta ƙarin bayani da haske kan salon nan na karin magana. Hakan ya taimaka wajen ganin yadda mawaƙa musamman na ƙarni na ashirin da ɗaya suke amfani da sarrafa basirarsu da suke sako karin maganar cikin waƙoƙinsu kuma ya tafi babu tangarɗa.

Manazarta

Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000) Nazari Kan Waƙar Baka Ta Hausa. Zaria: Gaskiya Corporation Limited.

Aliyu, S. L. (2014) “Tarihin Rayuwa da Nazarin Waƙoƙin Maryam Saleh Fantimoti” Kundin Digiri na Ɗaya, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, Jami’ar Bayero.

Atuwo, A. A. da Bunza, D. B. (2014) “Transformation of Hausa Poems in the 21 Century”. Taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa kan nazarin Hausa. Kano: Sashen Nazarin Harsunan Najerya, Jami’ar Bayero.

Auta, A. L. (2008) “Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Faɗakarwa A Ƙarni na Asirin”. Kundin Digiri na Biyu, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, Jami’ar Bayero.

Ɗangambo, A. (1980) “Hausa Wa’azi Ɓerse From CA 1800 to CA 1970: A Critical Study of Form, Content, Language and Style”. Ph.D Thesis, School of Oriental and African Studies, University of London.

Ɗan’iya, D. (1997) “Adon Harshe A Cikin Rubutaccen Adabin Hausa”. Kundin Digiri na Biyu, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, Jami’ar Bayero.

Dunfawa, A. A. (2002) “Waƙa A Tunanin Yara”. Kundin Digiri na uku, Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Dunfawa, A. A. (2014) “Makaɗan Zamani: Wani Ƙarin Kaso Na Rukunin Makaɗa”. Takarda da aka gabatar a taron ƙasa da ƙasa kan nazarin Hausa, ƙarni na 21, Kano: Jami’ar Bayero.

Garba, M. (1998) “Azancin Magana A Waƙoƙin Makaɗan Baka”. Kundin Digiri na biyu, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayaro.

Gusau, S. M. (1983) “Waƙoƙin Noma Na Baka: Yanaye-Yanayensu Da Jigoginsu Musamman A Sokoto”. Kundin Digiri na Biyu, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Gusau S. M. (2014) Waƙar Baka Bahaushiya. Kano: Bayero University, Inaugural Lecture.

Ƙanƙara, L. L. (2004) “Siddabarun Harshe, Sabuwar Hanyar Nazarin Adon Harshe A Waƙoƙin Baka na Hausa”. Kundin Digiri na Biyu, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, Jami’ar Bayero..

Mohammed, E. I. (2009) “Bunƙasa Da Ci Gaban Waƙoƙin Zamani”. Kundin Digiri na Ɗaya, Zariya: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Afirika, Jami’ar Ahmadu Bello.

Mohammed, L. A. da Wasu (2009). Mutanen Ɓoye: Nazari da Sharhin Mawaƙan Fina-finan Hausa. Kundin Digiri Na Ɗaya, Sakkwato: Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Mudi, A. (1990) “Kayan Kiɗan Hausa Na Gargajiya”. Kundin Digiri na Ɗaya, Kano: Sashen Koyar da Harsunnan Nijeriya, Jami’ar Bayaro.

Muhammad, Ɗ. (1977) “Indiɓidual Talent In The Hausa Poetic Tradition: A Study of Aƙilu Aliyu And His Art”. Kundin Digiri na Biyu, London: School of Oriental And African Studies.

Muhammad, Y. M. (2003) Adabin Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Sa’id, B. (1975) “Salon Magana”. A cikin Harsunan Nijeriya, Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Usman, B. B. (2018) “Ruwa Biyu: Sabon Zubin Waƙoƙin Ƙarni Na Ashirin Da Ɗaya” Yobe Journal of Language, Literature and Culture. Damaturu: Department of African Languages and Linguistics.

Yahya, A. B. (1984) “Matsayin Waƙoƙin Baka A Cikin Adabin Hausa”. Maƙala Wadda aka Gabatar a Makon Hausa, a Kwalejin Horar da Malamai Mata ta Larabci, Gusau.

Yahya, A. B. (1995) “Ƙawancen Jigo Tsakanin Waƙoƙin Sarauta na Baka da Rubutattu”. Takarda Wadda aka Gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Yahya, A. B. (1997) Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Serɓices.

Yahya, A. B. (2001) Salo Asirin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Serɓices.

Yahya, A. B. (2016) Salo Asirin Waƙa (Sabon Tsari). Sokoto: Guaranty Printers.

Yahaya, I. Y. (2002) Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zaria: Kamfanin Buga Littattafai Na Arewa.

Yakasai, M. G. (2014) “Nazarin Kwatancin Salo A Waƙoƙin Shaibu Abubakar Atiku Sanka Da Na Lima Muhammad”. Kundin Digiri na Biyu, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayaro.

 Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC)

Post a Comment

0 Comments