Ticker

6/recent/ticker-posts

Dacewar Wasu Diyoyin Wakokin Baka Da Nassoshin Addini Wajen Kyautata Mu’amala Tsakanin Al’umma

Citation: Muhammad ADAMU PhD & Ahmed Sulaiman BAFFA (2025). Dacewar Wasu Ɗiyoyin Waƙoƙin Baka Da Nassoshin Addini, Wajen Kyautata Mu’amala Tsakanin Al’umma. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 13, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

DACEWAR WASU ƊIYOYIN WAƘOƘIN BAKA DA NASSOSHIN ADDINI, WAJEN KYAUTATA MU’AMALA TSAKANIN AL’UMMA

NA

MUHAMMAD ADAMU PH.D

AHMED SULAIMAN BAFFA

Tsakure

Halin da al’umma ta tsinci kanta a ciki a yau, wani yanayi ne da gurɓacewar mu’amala tsakanin al’umma ke neman ya zama ruwan dare gama duniya. Wannan ya sa dole a lalumo dukkan wata hanya da za ta taimaka wajen ingatawa tare da kyautata mu’amala a tsakanin jama’a. Nazartar wasu ɗiyoyin waƙoƙin makaɗa zai taimaka wajen samar da ingantacciyar mu’amala a tsakanin al’umma. Saboda haka a wannan takarda an ƙudiri a niyyar zaƙulo wasu ɗiyoyin waƙoƙi da suke nusarwa da jawo hankulan jama’a, daga fitattun makaɗa daban-daban domin a nazarce su a mahanga ta ilmi, tare da nuna inda suka dace da nassi. Daga cikin abubuwan da wannan takarda ta fito da su, sun haɗa da: haƙuri da gaskiya da taimakon jama’a da haɗin kai da nuni kan ɗabi’u da halayen da ma’aurata za su lizimta da son juna da kuma sauran abubuwa da kan iya biyo baya. Wannan takarda ta ƙunshi hujjoji daga alƙur’ani da Hadisai da kuma matanin waƙoƙin makaɗan Hausa. An yi amfani da Alƙur’ani da Hadisai da littattafan masana da wasu muƙalu da takardu da suke da alaƙa, wajen samun bayanai da aka yi amfani da sako su cikin wannan aikin. Wannan aikin an ɗora shi ne kan hanyar da Abba da Zulyadaini (2001) suka kawo a littafinsu Nazari Kan Waƙar Baka Ta Hausa. Sannan a aikin an gano cewa mawaƙan baka kan sako ɗiyoyi masu ɗauke da haƙuri da yin ko faɗan gaskiya da nuna yadda mutane suke haɗa kansu da nuni da ɗabi’u kyawawa da ma yadda ma’aurata suke wajen son juna.

1.0 Gabatarwa

Al'ummar Hausawa, al'umma ce da suka yi riƙo da addinin Musulunci, kuma ya zama tsarin rayuwarsu. Wannnan ya sa suke girmama sha'anin addini. Suna ƙoƙarin kiyaye umarnin Allah da Manzonsa da ƙin abin da ya saɓa wa addninsu. Wannan ya sa ba a bar mawaƙan baka a baya ba, wajen amfani da wasu kalamai a ciki ɗiyoyin waƙoƙinsu waɗanda in an nazarce su suna da dacewarsu da wasu nassoshin addini wajen kyautata mu’amala a tsakanin al’umma. Mawaƙan suna ƙarfafa imanin al'umma, tare da wayar musu da kai wajen nuna musu muhimmancin mu’amala a bisa tsari na addini. An lura cewa, mawaƙan baka na yin wasu zantuka cikin hikima da jawo hankali a waƙoƙin nasu, waɗanda ke ɗauke da bayanai na ɓangarorin addinin Musulunci daban-daban. Waɗannan su suke ba da gagarumar gudummawa wajen kira kan halaye da ɗabi’u na kyautata mu’amala a tsakanin al’umma. Abubuwan nan sun haɗa da: haƙuri da gaskiya da adalci da taimakon al’umma da ƙarfafawa wajen neman na halak da mutunta juna da son juna da girmama na gaba da tausayin na ƙasa da mutunta aure. A takardar an yi ƙoƙari inda aka yi amfani da ayoyi da hadisai tare da kawo ɗiyoyin waƙoƙin wasu makaɗan baka da suka dace da waɗannan nassoshi.

2.0 Bitar Ayyukan Da Suka Gabata

A wannan wuri an yi amfani da bibiyan ayyukan da wasu suka yi domin fito da ma’anar waƙa da nassi da addini da kuma mu’amala.

2.1 Ma'anar Waƙar

Abba da Zulyadaini (2000:2), sun bayyana ma'anar waƙar baka da cewa “Ita ce wata tsararriyar magana cikin hikima da fasaha da aka ƙirƙira aka rera ta daki-daki (tare da taimakon amsa amon a wani lokaci), kuma ta kasance tana ɗauke da salon burgewa a bisa wata ƙa'ida ta musamman domin isar da saƙo”.

Gusau (2008:188), ya ce a taƙaice “Waƙar baka wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa'idojin shiryawa da daidaitawa, a rera cikin sautin murya da amsa-amon kari da amshi da kiɗa”.

Ɗangambo (2007:6), ya ce “Waƙa wani saƙo ne da ake gina shi kan wata tsararriyar ƙa'ida ta baiti, ɗango, kari, amsa-amo, da sauran ƙa'idojin da suka daidaita kalmomi, zabensu da sa su cikin sigogi da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba”.

2.2 Ma’anar Nassi

Kalmar ‘Nassi’, kalma ce ta Larabci wadda ta bayyana cikin lafazin da aka yi amfani da ita (Almu’ujam Alwast, 2008:579). Kalmar nassi tana nufin ayoyin Alƙur’ani ko Hadisi. A wata ma’anar ya kira shi da matani (CNHN, 2006:358).

2.3 Ma’anar Addini

 Fatima da Hadiza (2020:342), sun bayyana addini da cewa "Addini kamar addinin Musulunci hanya ce ta gudanar da bautar Allah bisa dokoki da matakai waɗanda Allah ya shimfiɗa wa mabiya ko masu imani. Waɗannan matakai kuwa sun haɗa da yin imani da Allah da Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama da kiyaye ayyukan ibada kamar salla da azumi da sauransu.

2.4 Ma’anar Mu’amala

Kalmar mu’amala tana nufin “gudanar da wata harka tsakaninka da wani mutum” (CNHN, 2006:309). Wannan yana nuni da cewa mu’amala aba ce da mutum ɗaya ba zai gudanar da ita ba, sai da wani. Mutum baya rayuwa shi kaɗai sai da mutane, wannan ya lizimci gudanuwar harkoki tsakaninsa da jama’a, wannan shi ke nufi da mu’amala.

3.0 Dacewar Wasu Ɗiyoyin waƙa da Nassi Wajen Inganta Mu’amala Tsakanin Al’umma

A nan sama an bada ma’anar mu’amala da cewa, ita ce gudanar da wata harka tsakanin wani da wani ko da wasu, to lallai akwai buƙatar kyautata wannan alaƙa. Irin wannan alaƙa ba za ta inganta ba sai an haɗa da haƙuri da gaskiya da riƙon amana da kyautata wa juna. Allah da Manzonsa sun faɗakar game da kyautata mu’amala. A wannan fage ba a bar mawaƙan baka a baya ba, su ma sun bada tasu gudummawar kamar yadda takardar ta bayyana.

3.1 Haƙuri

Haƙuri kalma ce da take nufin juriya kan wani abu na ɓacin rai ko masifa ko makamancinsu (CNHN, 2006:190). Hausawa na yi masa kirari da ‘Haƙuri maganin zaman duniya’. Haƙuri abu ne da yake da muhimmanci wajen ingantuwar mu’amala. Allah ya yi umarni da a yi shi haƙuri ya fi dacewa. “Ya ku waɗanda suka yi imani, ku yi haƙuri, ku dage cikin haƙuri, ku yi zaman dako, ku ji tsoron Allah tabbas za ku rabauta” (Sura-3:200). Sannan ya yi bushara ga masu haƙuri. “Lallai za mu jarrabe ku da wani abu na tsoro, da yunwa, da tawayar dukiya, da rasa rayuka, da tawayar ’ya’yan itatuwa, kuma ka yi wa masu haƙuri albishir” (sura-2:150).

Manzon Allah (S.A.W.) ya faɗi muhimmancin haƙuri, “Abin mamaki ga al’amarin mumini, lalle dukkan al’amarinsa alheri ne, haka ba ya ga kowa sai mumini. Idan farin ciki ya same shi sai ya gode sai ya zama alheri gare shi. Idan cuta ya same shi sai ya yi haƙuri sai ya zama alheri gare shi. (Riyadu Assalihina, Babi:3 Hadisa:29).

Alhaji Adamu Ɗanmaraya Jos, a waƙarsa ta ‘Haƙuri’, ya jawo hankali mutane kan muhimmancin yin haƙuri. Ga abin da yake cewa:

In an haƙuri malam,

Ka ga komai zai daidai,

Komai zai gyaru,

Haƙuri abin Manzon Allah,

Mai haƙuri shi yad dace,

Marar haƙuri kuma ya taɓe.

 (Waƙar Haƙuri)

Ɗanmaraya ya nuna muhimmancin haƙuri wajen daidaituwa da gyaruwar kowane al’amari, tare da tabbatar da dacewa ga mai haƙuri da kuma taɓewa ga marar haƙuri. Kamar yadda Allah ya yi umarni da yin haƙuri, kuma ya ce, ya yi wa masu haƙuri albishir. Sannan Annabi S.A.W. ya bayyana cewa ‘haƙuri ya jawo alheri ga mumini’.

Sannan a wani ɗa na wannan waƙa ya ci gaba inda ya jawo hankulan jama’a game da muhimmancin haƙuri da alfanunsa ga rayuwar jama’a, inda yake cewa:

Ko mutum ya cuce ka,

In kai haƙuri ka ga sakayya,

Ko mutum ya zage ka,

In kai haƙuri ka ga sakayya,

Ko mutum ya ɓace ka,

In kai haƙuri ka ga sakayya,

Haƙuri ba ya ɓaci tun da Allah ya so shi,

Haƙuri ba ya ɓaci tunda Annabi ya yi shi,

Haƙuri ba ya ɓaci, haƙuri abin Manzon Allah.

 (Waƙar Haƙuri)

A wannan ɗa mawaƙin ya sake nuna da jaddada muhimmancin haƙuri, ta hanyar nuna juriya da dauriya kan yin haƙuri game da duk abin da wani zai maka. A ƙarshe za a ga cewa ya nuna sakayyar nan daga Allah ce. Ya bayyana haƙuri a matsayin abin da Allah yake son ɗan’Adam ya yi, sannan Manzon Allah ma ya ayyana haka daga gefensa, kuma ya yi umarni da a yi hakan.

3.2 Gaskiya

Gaskiya kalma ce da ke nufin nuna ko faɗar abu ko aikata abu a ainihin yadda yake babu ƙari ko ragi (CNHN, 2006:160). Yin gaskiya a tsakanin al’umma babbar hanya ce ta kawo zaman lafiya da inganta mu’amala a tsakanin al’umma. Dan haka Allah (SWT) ya yi umurni da a yi ta, inda yake cewa: “Ya Dawuda lalle mun sanya ka kalifa a bayan ƙasa, ka yi hukunci tsakanin mutane da gaskiya, kada ka bi son rai har ya ɓatar da kai daga tafarkin Allah. Lalle waɗanda suke ɓata daga tafarkin Allah suna da azaba mai tsanani saboda abin da suka yi na mantawa da ranar hisabi” (Sura-Sad, aya-26). Sannan ya sake cewa: “ Ya ku waɗanda suka yi imani, ku kasance tare da masu gaskiya” (Sura-Tauba, aya-119).

Manzon Allah (SAW) ya yi magana kan muhimmancin yin gaskiya, ya ce: “Lallai gaskiya yana shiryarwa zuwa ga ɗa’a, kuma lallai ɗa’a yana shiryarwa zuwa ga Aljanna, sannan mutum ba zai gushe ba yana yin gaskiya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai gaskiya ne. Kuma lallai ƙarya yana shiryarwa zuwa ga fajirci, sannan fajirci yana shiryarwa zuwa ga wuta” (Riyadu Assalihina, babi-4, Hadisi-56).

A cikin waƙar Alhaji Mamman Shata waƙarsa ta ‘Ibrahim Badamasi Babangida’ ya fito muhimmancin yin gaskiya da alfanunta a wajen inganta mu’amala tsakanin al’umma, kamar haka:

Kui maza kui shirin gaskiya,

Bai son shirin ƙarya,

Janaral na Mairo giwa,

Ya kori mai danniya,

Ya kori mai murɗiya

Janaral na Mairo giwa.

 (Waƙar Ibrahim Badamasi Babangida)

Alhaji Mamman Shata ya gargaɗi al’umma da su yi maza su yi shirin gaskiya, sannan cikin ɗa da ke sama, ya nuna shugaba Babangida bai son mai shirin ƙarya ko danniya ko murɗaya. Idan an lura za a ga yadda Allah ya umarci Annabinsa Dauda da tsayar da gaskiya sanna kuma ya nuna yana tare da masu gaskiya, Manzonsa ya nuna cewa gaskiya tana shiryarwa ga ɗa’a, ɗa’a tana kai mutum aljanna.

Haka shi ma Aliyu Gadanga Gusau a waƙarsa ta ‘Kadi Ɗahiru Muhammad Gusau’ da ya yi nuna kan muhimmancin yin gaskiya wajen tafiyar da al’umarar al’umma a ɓangaren mu’amala a tsakaninsu, inda yake cewa:

J. Zanka kula da halin mutane,

A. Ka san mutum yau bai da arha,

J. Shi ba cin hanci yakai ba,

A. Mai gaskiya duk baitsare shi,

J. Kanda shi yanke ma shari'a,

Sai ya karanta ma hadisai.

 (Waƙar Kadi Ɗahiru Muhammad Gusauƙ

Mawaƙi Gadanga Gusau ya bi Ƙadi Muhammad Gusau kan yin gaskiya da adalci wajen yanke hukunci a tsakanin al’umma. Bayan ya ja hankalinsa kan kula da haƙƙin jama’a, sai ya bayyana shi a matsayin mai gaskiya wanda bay a cin hanci. Kuma sabo da ƙoƙarinsa wajen yin gaskiya baya yanke hukunci sai ya karanta ma Hadisi. Wannan ya nuna ƙoƙarin mawaƙan baka wajen inganta mu’amala tsakanin jama ta hanyar dacewa da nassi.

Shi ma Sarkin Taushi Salihu Jankiɗi a waƙarsa ta ‘Sardaunan Sakkwato Alhaji Amadu Bello’ ya ja hankali game gaskiya musamman cikia alkawari, inda yake cewa:

J/Sarkin Gwamba munai maka murna,

A/Alƙawari ka san kaya ne,

Batun nan da ka hwaɗi ka isai.

 (Waƙar Sardaunan Sakkwato Alhaji Amadu Bello)

Bayan Sarkin Taushi ya taya Sarkin Gwandu murnar samun nasara, sai ya ci gaba da jawo hankalinsa game da cika alkawari. A nan ya nuna wa Sarki muhimmancin yin gaskiya musamman ga shugabanni wajen cika alkawarin da suka ɗauka wa talakawansu. Wanna babu shakka hanya ce ta kyautata mu’amala tsakanin jagorori da mabiyansu, kuma da wannan ne Allah ya umurci Annabi Dauda A. S.

 3.3 Haƙƙin Ma’aurata:

Haƙƙi yana nufin abun da mutum ya cancanta (CNHN, 190). Bayar da haƙƙi ga mai shi, musamman tsakani ma’urata, yana daga cikin hanyoyin kawo zaman lafiya da kyautata mu’amala a tsakanin al’umma, wannan ya sa Allah S.W.A. ya yi umarni da a yi aure kuma a kula da haƙƙoƙa, “ Kuma ku aurar da gwagwaren cikinku da waɗanda suka isa aure maza daga cikin bayinku, da bayinku mata. In sun kasance matalauta Allah zai wadata su daga falalarsa, kuma Allah mai ji ne masani” (Ƙura’an 24:32). Ya yi kira gamr da haƙƙi inda ya ce: “ Mata suna da haƙƙi a kan mazajensu, kwatankwacin irin haƙƙin da ke kan na mazajensu’ (Ƙur’an 2:228).

Manzon Allah ya nuna wajabcin ba da haƙƙi “Lallai kuna da haƙƙi a kan matanku, kuma lallai matanku na da haƙƙi a kanku” (Minhaji Musulim:337, Hadith:1851).

Alhaji Dr Mamman Shata Katsina a waƙarsa ta ‘Jega’ ya jawo hankalin mata das u yi aure, sannan su kula da haƙƙin aure kamar haka:

Ku wa Allah ku bi aure mata,

Ku bar ma batun Malam Ɗanmani,

Tsoho mai zancen banza,

Ku wa Allah ku bi aure mata.

Don ni na ce maku duk ku yi aure,

Allah ba ku miji kui aure,

Ɗan mani ya ce maku kak ku yi aure,

Ku tsar ma batun sha,

Faɗa ma wadda ba ta da aure,

Allah ya ba ta miji ta yi aure,

Wadda take gida na mijinta,

Ta wa Allah ta bi aure daidai,

Ku wa Allah ku bi aure mata.

Kai aljannar mace ɗakin mijnta,

Don Allah ku bi aure mata,

Ku wa Allah ku bi aure mata.

 (Waƙar Jega)

Mawaƙi Mamman Shata ya ƙarfafa maganar yin aure, inda ya haɗa mata da Allah domin su yi aure, ya musu fatan samun miji a kan lokaci. Sannan ya musu gargaɗi kar su yarda da mai hana su yin aure. A bayanin nasa ya yi kira ga mata masu aure das u ji tsoron Allah su yi biyayya ga mazajensu. Daga ƙarshe ya nuna samun Aljannah ga ‘ya mace yana ƙarƙashin aure. Wannan ya bayyana ƙoƙarin mawaƙin wajen gyara ma’amalar ma’aurata, kamar yadda Allah da Manzonsa suka yi umarni.

Haka shi ma Alhaji Ɗanmaraya Jos, a waƙarsa ta ‘Gargaɗi ga Ma’aurata’ ya jawo hankali ma’aurata kan abubuwan da za su wanzar da kyakkyawan mu’amala a tsakaninsu inda yake cewa:

Dubban jama'a sun tabbata,

Maigida kai zan maka gargaɗi,

Kai ma wannan matarka ce,

Ruwan wanka ita za ta kai,

Ta lura da yara ƙanƙana,

Sharar ɗaki ita za ta yi,

Ta tuƙa abinci ka zo ka ci,

In kai baƙi ta kula da su,

Shin malam ko boyinka ne,

A wata nawa za ka biya shi ne.

To don haka nan daɗa kun jiya,

Mata ku riƙe aure da kyau,

To maza ku riƙe aure dakyau,

A cikin ko maza ma har da ni.

(Waƙar Gargaɗi ga Ma’aurata)

Ɗanmaraya ya ja hankalin ma’aurata kan kulawa da haƙƙin junansu. Mawaƙin ya yi kira ga mazaje da kyautata wa matansu, sadoda hidimar da matan ke musu, kamar kai musu rowan wanka da sharer gida da kula da yara ƙanana da dafa abinci da sauransu. A ƙarshe ya jawo hankalin maza da mata cewa su riƙe aure da kyau. Waɗannan ɗiyoyin sun yi nuni kan yadda mawaƙan baka ke wayar wa al’umma kai wajen kyautata mu’amala a tsakaninsu bisa dacewa da nassi.

3.4 Kyautata Wa Al’umma:

Kyautata wa al’umma yana nufin yi musu abin da zai faranta musu rai ko, taimaka musu wajen biya musu buƙatun da suke ci musu tuwo a ƙwarya. Hakan yana da tasiri wajen inganta mu’amala tsakanin al’umma. Allah y ace: “ Har abada ba za ku samu yardarm Allah da rahamarsa ba har sai kun ciyar da abun da kuke so” (Ƙur’an:2 :92). Sannan ya ce: “Ya ku waɗanda suka yi imani ku ciyar da tsarkakan abun da kuka samu, sannan kuma daga abin da muka fitar muku daga cikin ƙasa”, (Ƙur’an:2:267).

Hadisin Abu Ɗalha Allah ya ƙara yarda a gare shi, Manzon rahama ya yi bayanin hakan cikin Hadisai ingantattu, (Rayadu Assalihina:110).

Aliyu Ɗandawo a waƙarsa ta ‘Arɗon Shuni Muhammad’ ya yabi Arɗon Shuni Muhammad bisa wannan aiki inda yake cewa:

yay yi ma rabon duniya,

A/ Ya ko tsare tattalin lahira,

Don yai Ishirinya,

Arɗo ya yi Risala,

Baba ya tsare makoma.

Samu ka samu uban 'yanruwa,

Shi yat tsare tattalin shekara dut,

Hid da dame ɗari tara na zakka,

Kuma ya yi kai ɗari tara na kono.

(Waƙar Arɗon Shuni Muhammad)

Bayan mawaƙi Aliyu Ɗandawo ya bayyana irin baiwar da Allah ya yi wa Arɗon Shuni Muhammadu, sai ya ambaci yadda yake ƙoƙarin tattalin lahira, wajen neman ilmin shari’a, inda ya nuna ya karanta littattafai da dama kamar Ishiriniya da Risala. Daga ƙarshe ya ambaci yadda yake cire haƙƙin talakawa ta hanyar fitar da zakka da ta kai dame ɗari tara, da kai ɗari tara na ƙono. Irin waɗannan zakka hanyoyi ne na taimako da kyautata wa al’umma da ke inganta mu’amala tsakanini al’umma. Wannan ya tabbatar da gudummawar mawaƙan baka wajen ƙarfafa kyakkyawar mua’amala a tsakanin al’umma wadda ta dace da nassi.

Haka kuma Alhaji Ɗanmaraya Jos a waƙarsa ta ‘Mai Akwai da Babu’ ya ja hankalin mawadata da su agaza wa masu ƙananan ƙarfi, inda ya ce:

Kai mai akwai ka gane,

In muddin kana da shi ne,

Burinka shirya hairi,

Kai taimako ga kowa,

Ka agaza wa kowa,

Ka kyautata wa kowa,

Ran komawa ga Allah,

Wallahi ka ji daɗi,

Bayanka sun ji daɗi,

In muddin kana da shi ne,

Burinka dai ka ɓata,

Ba ka taimako ga kowa,

Burinka cin mutunci,

Ko burinka cin amana,

Malam akwan a tashi,

Gidaje gami da mota,

Sannan gami da mata,

'Ya'ya su zo ƙare,

Mata su zo su ƙare,

Mota su zo su ƙare,

Ka ga ran komawa ga Allah.

(Waƙar Mai Akwai da Babu)

MawaƙƊanmaraya ya jawo hankalin jama’a musamman masu hanu da shuni, da su kyautata wa marasa ƙarfi. Inda ya yi amfani da kalmomin agazawa da kyautatawa da taimakawa ga kowa. Sannan ya nuna yin hakan zai sa mutum ya ji daɗi duniya da lahira, kuma bayansa ma za su ji daɗi. Ya ci gaba da bayyana haɗarin rashin taimakon, inda ya nuna gidaje da mototi da mata da mutum ya tara, za su ƙare. Da wannan za a ga yadda mawaƙan baka ke bin sahun nassi wajen kyautata alaƙa tsakanin al’umma a cikin waƙoƙinsu.

Haka shi ma Abdurrahaman Sarkin Kotso a waƙarsa ta ‘Sarkin Kano Muhammadu Sunusi (1954-1963)’ ya faɗakar game da kyautata wa al’umma, inda ya ce:

Gabas da yamma, kudu da arewa,

Mulkin Muhammadu yai mana daɗi,

Domin ya gyara mutane,

Jamaa'ar birni da ta ƙauye,

Ko'ina begen ka ake yi,

Da sarakunan addini,,

Kwaikwayon mulkinka suke yi

Sir Sunusi Sarkin yaƙi,

Zakin daga na Asabe.

(waƙar Sarkin Kano Muhammadu Sunusi)

A wannan ɗan waƙa Sarkin Kotso ya bayyana hanyoyi da dama na kyautata wa al’umma waɗanda za su ƙara ƙarfafa kyautatuwar alaƙa ta mu’amala tsakanin al’umma da shugabanninsu. Domin mawaƙin ya nuna goyon bayansa da nuna jin daɗinsa game da mulki da jagoranci Muhammadu Sunusi. Ya kuma nuna yadda mutanen birni da ƙauye ke bege da nuna ƙauna a gare shi, saboda gyaran da yake. Wannan kira ne ga sauran shugabanni da su yi koyi da halin na kirki.

Mawaƙi Abdurrahaman Sarkin Kotso ya ci gaba da zayyana irin waɗannan halaye na kyautata wa talakawa, inda ya ce:

Zamanin Mamman na Abashe,

Wajen ilmi ko'ina mun ƙaru,

Ga makarantu an yi fiyayyu,

Ga siniya faramare na nan,

Furobishal sakandare na nan,

Ga makarantun mata na nan,

Ilmi yau ya kai ga kwaleji,

Sir Bayaro Kwaleji ta nan,,

Makaranta babba a Nauzan,

Dukka ƙasashe babu.

(waƙar Sarkin Kano Muhammadu Sunusi)

Waƙin ya nuna taiman talaka ya haɗa da a samar masu ilmi mai amfani kamar, yadda Muhammadu Sunusi ya yi makarantu daban-daban kuma, a mataki daban-daban. Wannan kira ne ga dukkan shugabanni da jagori da su tsayu wajen inganta ayyukan al’ummarsu. Don haka mawaƙan baka nahausa suna ƙoƙari wajen ganin an kyautata mu’amala tsakanin al’umma, kamar yadda addini ya tanada.

3.5 Dogaro da Kai

Dogaro da kais hi ne neman halak, kauce wa son banza da mutuwar zuciya wajen neman abun da za a rayu das hi. Wannan yana daga cikin muhimman al’amura da suke inganta mu’amala a tsakanin al’umma. Wannan ya sa Allah ya ce: “ A yayin da aka idar da sallah, to ku watsu cikin gari, ku nema daga falalar Allah kuma ku ambaci Allah Ambato mai yawa tsammanin za ku rabauta”, (Ƙur’an: Juma’a:10) .

Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “ Ɗayanku ya ɗauki igiyoyinsa ya zo da dami na itace da gadon bayansa ya sayar Allah ya rufa masa asiri da shi, shi ya fi alheri da ya roƙi mutane ko sun ba shi, ko sun hana shi”, (Riyadu Assalihina:79 Hadisi:548)

Alhaji Ɗanmaraya Jos a waƙarsa ta ‘Lebura’ ya nuna muhimmanci neman halak, inda yake cewa:

Don haka nan mutanenmu,

Ku ɗaukaki leurorinmu,

Kar ku tabbata ba su aikin nan,

Kai lebura ko waliyyi ne,

Aiki da yake na lada ne,

Ba dan ƙarfin Bature ba,

Da don ƙarfin Bature ne,

Da lebura bai yi aiki ba.

(Waƙar Lebura)

Cikin hikima Ɗanmaraya ya nuna muhimmancin neman halak, ta hanyar kira ga mutane da su daraja lebura, su ɗaukaka shi. Sannan ya yi kira a tabbatar an ba su cikakkiyar mutuntawa da za ta ba su dama su gudanar da aikinsu. Sannan ya ambaci mai neman halak da cewa waliyyi ne, wannada yake aikin taimakon al’umma. Da wannan za a ga gummawar mawaƙan baka wajen ƙarfafa masu neman halak.

Dr. Mamman Shata Katsina a waƙarsa ta ‘Kai ‘Yan Yara Gumina Nake Ci’ ya yi jan hankali kan neman halak kamar haka:

Masu zuwa ofis ku yi ofis,

Masu zuwa gona ku yi gona,

Lebura kan hanya ka yi aiki,

A yau kowanne guminai yake ci,

Kai ‘yan yara gumina nake ci

(Waƙar Kai ‘Yan Yara Gumina Nake Ci)

Mawaƙin ya yi kira game da masu zuwa ofis das u tafi wajen aiki a kan lokaci, sannan masu zuwa gona su ma, su tafi gona. Bayan haka ya kira lebura ya tafi gurin aiki. Wannan ya bayyana yadda mawaƙan baka ke ƙarfafa jama’a wajen neman halak

3.6 Haɗin Kan Al’umma

Haɗin kai tsakanin al’umma ya nufin yin abu tare, da manufa ɗaya don cin nasa ta gaba ɗaya. Kuma yana matuƙar taimakawa wajen samar da zaman lafiya tsakanin jama’a. Haɗin kai kuma ba ya samuwa sai an kawar da bambancin da ke tsakanin jama’a na launin fata, da bambancin harshe, sannan a mutunta juna. Saboda muhimmancinsa, Allah S.W.T. yake cewa; “ Ku yi riƙo da igiyar Allah gaba ɗaya kar ku rarraba. Ku tuna ni’imar da Allah ya yi a gare ku domin kun kasance masu gaba da juna, ya haɗa tsakanin zukatanku, kuka wayi gari da ni’imar Allah kuka zama ‘yan’uwan juna. Kun kasance a gaɓar ramin wata, Allah ya tseratar da ku daga gare ta. Haka Allah yake bayyana ayoyinsa a gare ku tsammanin ko za ku shiryu”, (Ƙur’an:3, aya:103).

Sannan ya ce: “Lallai mun halicce ku daga namiji guda da mace guda, sannan muka sanya ku yanki-yanki da kuma ƙabilu domin ku san junanku. Lallai wanda ya mafifi ci a cikinku shi ne, wanda ya fi tsoron Allah”. (Ƙur’ani: Hujurat:13),

Ɗanmaraya Jos a waƙarsa ta ‘Mai Akwai da Babu’ ya yi jan hankali kan haɗin kai, inda yake cewa:

Allah Huwallazina

Allah Huwallazina

Ya yi Larabawa,

Ya yi Ingilishi,

Yay yi mutan Amerka,

Ya yi Indiyawa,

Allah Huwallazina,

Yai haka domin mu gane juna.

In ba ku ɗan misali,

Shi Allah Huwallazina,

Allah ya yi Ghana,

Yai Ethopia ai,

Yai Nijeriyarmu mu ma,

Ga shi duk baƙaƙe,

Wani bai jin batun waɗansu,

Allah Huwallazina,

Yai haka domin mu gane juna.

(Waƙar Mai Akwai da Babu)

A wannan ɗiyoyin waƙar mawaƙƊanmaraya, ya nuna Alla ɗaya ne ya halicci; Larabawa da Turawa da Indiyawa da Amurkawa da mutanen Ghana da Najeriya da Ethopia, don haka ɗaya muke ba bambanci. Wannan yana nufin mu haɗa kai, mu daina ganin bambancin launin fata ko gurin zama, ko harshe.

Har yanzu mawaƙin a waƙarsa ta ‘Ishara’ ya kawo bayanai musu maka da wannan cikin wasu ɗiyoyin waƙar, kamar haka:

Wani Allah sarkin iko,

Wani yai makaranta Malam,

Da yai makaranta tasa,

Da farko in ka gane,

Ya yi sakandare Malam,

Ya yi midil ya ƙare,

Ya je har Unibasti,

Ya ziyarci Amirka da Rasha,

Duk naman ilmi yakkai shi,

Ya dawo gida ya zauna,

To sannan wani ba shi da biro,

To, duk Allah na ƙaunar ku,

Tun da shi yai wannan,

Sannan Allah shi yai wancan,

Allah ya san wannan,

Sannan Allah ya san wancan,

To, duka Allah na ƙaunar ku,

Duka ku duk ba bambanci.

(Waƙar Ishara)

A wannan ɗan waƙar, mawaƙin kira ya yi game da haɗin kai ta hanyar nuna duk ilimin da Allah ya ba ka, da yawan sanin duniyarka, da wayewarka, kar ka wulaƙanta wanda bai yi ilmi ba. Saboda kowa da abin da Allah ya zaɓa masa wanda ya dace das hi. Ya kuma yi bayanin kasancewar su ɗaya a wajen Allah. Manufar Ɗanmaraya a wannan ɗan waƙa shi ne, mu haɗa kai, mu so junanmu, kar bambancin ɗaukakar ilmi ko dukiya ko wayewa ko wani ci gaba da mutum ya samu ya sa mu ga fifiko a tsakaninmu.

3.7 Son Juna

Son juna yana nufin ƙauna da shaƙuwa da mutunta juna, sha’ani ne na fatan samun ci gaba ga ɗan’uwanka da ƙin duk wani abu mammuna ya same shi. Son juna yana kyautata mu’amala tsakanin al’umma, don haka Allah yana cewa: “Waɗanda suka zauna a gida kafin su, suna son wanda ya yi hijira zuwa gare su”, (Hashari : 9). Haka kuma Ƙur’ani sura (Alfatahi) aya ta 29, Lallai Muhammadu Manzon Allah ne, waɗanda suke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu tsananin so ne a tsakaninsu”, (Alfatahi :29).

Allah ya ce: “ Soyayyarsa ta wajaba ga suke son juna don ni, da waɗanda suke zama domin ni da waɗanda suke ziyartar juna domin ni, da waɗanda suke kyauta domin ni’. (Riyadu Assalihina shafi: 412, Hadisi: 388).

Alhaji Ɗanmaraya Jos a waƙarsa ta ‘Mu So Al'adu’ ya bayyana muhimmancin son juna kamar haka:

To jama'a mu so junanmu,

Dukkanmu 'yan'uwan juna ne,

Al'amarinmu ba bambanci,

Ubangiji ya ƙara zumunci,

'Yan'uwa baƙaƙen fata,

Za ni ba ku bayani,

Mu so gida daɗa kun ji,

Kowa ya bar gida kai Malam

Na tabbata gida ya bar shi.

(Waƙar Mu So Al'adu)

MawaƙƊanmaraya Jos ya yi kira ga jama’a da mu so junammu, ya kuma bayyana cewa dukkanmu ‘yan’uwan juna ne. Ya ci gaba da bayyana matsayin wajen rashin bambanci, domin dukkanmu daga Adamu muke, Adamu kuma daga ƙasa. Mawaƙin ya yi kira da mu riƙe zumunci kuma ya yi addu’a domin, zumunci yaƙaru a tsakaninmu. Daga ƙarshe ya ƙara jawo hankalinmu da mu so na gida wato, baƙaƙen fata. Ya bayyana a fili ƙoƙarin mawaƙan baka kan ingata mu’amala tsakanin al’umma kamar yadda nassoshin addini suka yi umurni.

4.0 Kammalawa:

Wannan takarda ta tattaro manyan batutuwa da suka danganci kyautata mu’amala a tsakanin al’umma, ta hanyar amfani da nassoshin Alƙur’ani mai girma da Hadisan Manzon Allah S.A.W da kuma matanoni na ɗiyoyin waƙoƙin baka. An rattaba ayoyi da Hadisai da suka ja hankali da faɗakarwa a kan inganta mu’amala, sannan aka nuna dacewar su matanonin waƙoƙin wajen ƙarfafawa kan kyautata halaye da ɗabi’u masu kyau a tsakanin al’umma.

Sannan an lura cewa, mawaƙan bakan sun yi amfani da tasirin haƙuri da yin gaskiya da dogaro da kai da kyautata wa al’umma da haɗin kai da son juna da kiyaye haƙƙi tsakanin ma’aurata wajen inganta mu’amala a tsakanin al’umma, da takardar ta mai da hakali gare su. Waɗannan abubuwa da aka duba an alaƙanta su da nassoshi da suka dace da su waje jan hankalin jama.

Wannan binciken hanya ce da ta taimaka kan fannin ilimi, domin takarda ce mai amfani da za ta bada haske ga masu yin bincike kan irin wannan aiki ko makamancinsa da zai zama abin dogaro a gare su nan gaba

Manazarta

Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000) Nazari Kan Waƙar Baka Ta Hausa. Zaria: Gaskiya Corporation Limited.

Ali, Y. (1975) Translation and Commentary of the Holy Ƙur’an. Great Britain: Pitman Press, Bath.

Altine, H. (1983) “Aliyu Ɗandawo Da Waƙoƙinsa”. Kundin Digiri na Farko, Sakkwato: Jami’ar Usman Ɗanfodiyo.

Asimina, S. M. S. (1989) Attauhidu Walfiƙhu Wat-tajwid Lil-Faslir Rabi’u Al-Ibtida’iyyat. Mahfulzatil-Wizaratil Ma’arif. Saudi Arabiyya.

Bunza, U. A. (2001) “Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu: Tauhidi A Bakin Makaɗan Bakan Hausa”. Kundin Digiri na Farko, Sakkwato: Jami’ar Usman Ɗanfodiyo.

Bunza, U. A. (2013) “Wa’azi A Bakin Gambo Dogo Mai Kalangu”. Cikin Mujallar Makaɗi A Mahangar Manazarta. Jerin takardun da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani kan Tubar Muahammadu Gambo Mai Kalangu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usman Ɗanfodiyo.

CNHN Jami’ar Bayero Kano (2006) Ƙamusun Hausa. Zariya: Ahmadu Bello University Press Limited.

Ɗangambo, A. (2007) Daurayar Gadon Feɗe Waƙa. Kano: Amana Publishers.

Gumi, A. M. (1980) Fassarar Ma’anonin Al-Ƙur’ani Mai Tsarki Zuwa Hausa. Lebanon: Dar al Ma’aref

Gumel, M. A. (1992) “Tarbiyya Da Dangoginta A Waƙoƙin Makaɗan Baka Na Hausa”. Kundin Digirina Farko, Jami’ar Bayero, Kano.

Gusau, S. M. (2008) Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu Da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publisher Limited.

Gusau, S. M. (2014) Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i na Biyu. Kano: Centurey Research an Publishing Limited Nigeriya.

Gusau, S. M. (2018) Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i na Uku: Kano: Centurey Research and Publishing Limited Nigeriya.

Gusau, S. M. (2009) Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Baka na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited Nigeriya.

Gusau, S. M. (2020) Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i na Biyar: Kano: Century Research and Publishing Limited Nigeriya.

Gusau, S. M. (1993) Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kaduna: Fisbas Media Serɓices.

Gusau, S.M. (1996) Makaɗa Da Mawaƙa Na Hausa. Kaduna: Fisbas Media Serɓices.

Sharif, Y. A. (2014) Riyad As-salihin.Lebanon. Dar El-fikr Poblishers, Distributors Beirut

 Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC)

Post a Comment

0 Comments