Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Kimiyyar Harshe A Cikin Azancin Hausawa: Duba A Kan Ma’ana Da Nahawu

Citation: Fauziyya Muhammad HASSAN Ph.D (2025). Nazarin Kimiyyar Harshe A Cikin Azancin Hausawa: Duba A Kan Ma’ana Da Nahawu. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 13, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

NAZARIN KIMIYYAR HARSHE A CIKIN AZANCIN HAUSAWA: DUBA A KAN MA’ANA DA NAHAWU

Na

FAUZIYYA MUHAMMAD HASSAN Ph.D

Tsakure

Wannan bincike ya duba adon harshen Hausawa daga mahangar kimiyyar harshe, musamman ta fuskar ma’ana (semantics), da kuma nahawu (syntaɗ). Adon harshe wani muhimmin ɓangare ne na al’adar Hausa wanda ke ƙunshe da hikima da tunani mai zurfi, da kuma koyarwa cikin sauƙi da nishaɗi. Manufar wannan bincike ita ce gano yadda ake gina adon harshen Hausa da kuma yadda ma’ana ke bayyana a ciki wajen sadarwa da jan hankali da koyar da ɗabi’u. Binciken ya bayyana cewa adon harshe na amfani da dabarun karya ƙa’idar nahawu da daidaituwar kalmomi domin janyo hankali da sauƙaƙa fahimta. Haka zalika, ma’anar kalmomi a cikin adon harshe tana zuwa ne fiye da zahirin abin da kalmar ke nufi a cikin jimla, lamarin da ke nuna amfani da ma’ana na al’ada da tunanin Hausawa. An kuma gano cewa tsarin nahawu a cikin adon harshe yana iya saɓawa da tsarin da aka saba da shi a cikin zance na yau da kullum, amma hakan ba ya rage ingancinsa wajen sadarwa. Binciken ya yi amfani da dabarun nazari na ilimin harshe da misalan adon harshe daban-daban domin fahimtar tsari da ma’anar su daga wallafe-wallafe da zantukan yau da kullum. A ƙarshe, binciken ya nuna cewa adon harshe wata muhimmiyar hanya ce ta adana harshe da al’ada da basirar Hausawa.

Mabuɗan takarda: Nazari, Kimiyyar Harshe, Adon harshe, Nahawu, Ma’a’ana,

1.0 Gabatarwa

Adon harshe wani muhimmin ɓangare ne na al’adar Hausawa da ke bayyana hikima da basira da tunani mai zurfi cikin kalmomi da guntayen jumloli. Hausawa na amfani da adon harshe a fannoni da dama na rayuwa domin bayar da shawara da jan hankali da nuna ƙwarewa ko kuma gargaɗi cikin salo mai jan hankali. Wannan ya sa adon harshe ke ɗaukar matsayi na musamman a matsayin wata hanyar sadarwa mai cike da fasaha da falsafa.

ɓangaren kimiyyar harshe, ana nazarin harshen mutum ta fuskar tsarin nahawu (syntaɗ), da kuma tsarin ma’ana (semantics). Wannan bincike zai dubi yadda waɗannan manyan fannoni biyu na kimiyyar harshe ke bayyana a cikin adon harshen Hausawa, tare da nazarin yadda tsarin kalmomi da jimloli da kuma rawar da suke takawa wajen gina adon harshe mai ma’ana da tasiri.

Manufar wannan bincike ita ce gano yadda adon harshe ke ƙunshe da dabarun harshen da ke inganta sadarwa da bayyana tunanin al’umma. Binciken zai amsa tambayoyin kamar haka: Ta yaya ma’anoni ke canzawa bisa ga al’ada? Kuma ta yaya tsarin jumla ke shafar fahimtar adon harshe?

Wannan bincike yana da muhimmanci domin zai taimaka wajen fahimtar dangantaka tsakanin tsarin harshe da al’ada, tare da nuna irin gudummawar da adon harshe ke bayarwa wajen kula da lafazin harshe da da kuma bayyana gwanintar harshe wajen sadarwa a tsakanin Hausawa.

2.0 Tarihin Adon harshe a Wurin Hausawa

Al'ummar Hausawa kamar sauran al'umma na duniya ta mallaki Adon harshen da take amfani da shi, wajen yin adon zantukanta, da ƙawata su cikin armashi. Adon harshe na magana na nufin "wasu 'yan guntayen maganganu ne ko zantuka da ke zuwa gaɓa-gaɓa ko gunduwa-gunduwa domin isar da wani saƙo na musamman. Sannan kuma shi wannan Adon harshe ana tsara shi da ka, a isar da shi gajama'a da ka, sannan a adana shi da ka" (Ɗangambo, 1984).

Adon harshe maganar al'ada ce ta Hausawa daɗaɗɗiya wadda ba za a iya cewa galokacin da aka fara ta ko aka ƙage ta ba. Hausawa suna aiwatar da adon harshensu ne saboda nishaɗantarwa da ban dariya da yaɗawa tare da haɓaka harshe wanda yake shi ne rumbun ajiye al'adun. Har ila yau, wannan adon harshe na Hausawa na koyar da darussan zaman duniya da ban dariya daban-daban da nasihohi da isharori da hannunka mai sanda da sauran hanyoyin faɗakarwa.

2.1 Ire-Iren Adon harshen Hausawa

Kaɗan daga cikin ire-iren Adon harshen Hausawa, za a jero tare da taƙaitaccen bayani a kansu, kamar yadda Ɗangambo (2008) ya bayyana sun haɗar da:-

-Karin magana

Salon magana

Kacici-kacici

Ƙarangiya/karya harshe

Kirari

Take

Zaurance

Habaici

zambo

Ba'a

Barkwanci

Gatse

Shaguɓe

Gugar zana

Saye/dungu

Fadanci

Santi

Waskiya

Sara da sauransu.

2.1.1 Karin Magana

Ta fuskar ma'ana, karin magana tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajarce na hikima da zalaƙa tare da bayar da ma'ana gamsasshiya, mai faɗi, maiyalwa, musamman idan aka tsaya aka yi bayani daki-daki (Junaidu da Yar'Aduwa, 2007).

Ashe kenan karin magana taƙaitacciyar magana ce 'yar ƙil wadda ta ƙunshi hikima da zantuttuka masu ma'ana.Karin magana kan danganci abubuwa da yawa kamar al'adu da tarihi dafasaha da hikimomin Hausawa kusan karin magana a iya cewa "komai da ruwanka ne” yakan yi katsalandan a duk cikin ɓangarorin rayuwa, yakan ayyana falsafar Hausawa dangane da wasu abubuwa da suka shafi rayuwa, kamar arziƙi da alheri da ilimi. Yana taimakawa ƙwarai wajen kyautata tarbiyya da yadda za a gina halaye nagari.

Karin magana yakan daidaita ɗabi'un yara ya kyautata zumunta, ga shi kuma kotun tafi-da-gidanka ne wajen bayyana matsayin abu, sannan ga taƙaita zance da ƙara masa armashi.

2.1.2 Zaurance:

Wannan ma zance ne na hikima da yawanci 'yan mata kan shirya shi cikindabara da naƙaltar harshe don isar da sako ga junansu da shigar da baminsa duhu, yarasa gane abinda ake nufi (Yahaya da wasu, 1992). Wani ƙauli kuma akan ce zaurance ƙirƙirarren harshe ne wanda matasa ke yi don ɓatar da bami.

A Wajen tsara zaurance akan jujjuya gabo bin sautikan magana ta yi musu ƙari ko sauya muhallan zamansu, kuma akan dinga aiwatar da shi ne da sauri don ƙara batar da baminsa ko don kau da jin mai naciya. Wani lokacin gaɓoɓin da ake ƙara sakaɗawa cikin tsarin jumlar da ake magana ba su ko da wata ma’ana an fi karkata ga amon ne bisa ma’ana.

Misali: -Kizo (kiwala zo)

-Zan sha ruwa (zan wala sha wala ru wala wa wala )

-Za ni kasuwa (za bani ba ka ba su bu wa)

-Na ga Musa jiya (na ruwa-ruwa ga ruwa-ruwa, mu ruwa-ruwa sa ruwa-ruwa ji ruwa-ruwa ya ruwa-ruwa)

2.1.3 Karya Harshe

Karya harshe ya danganci salon sarrafa sautika ta cakuɗa muryoyin kalmomi su dinga maimaita junansu cikin takidi don nuna gwaninta. Ko kuma a ce karya harshe zance ne mai sassarkiya, da ake shiryawa domin wasa da harshe, ko don ɓatar da mara jin harshen sosai ko don yin zolaya (Yahya da wasu,1992). Wannan nau’i na ƙarangiya ya ƙunshi gagara gwari da ingiza bami.

Misali: -Tantabara tara ƙwai tara ɗa tara

- Na bugi baƙin dokin baba da bayan hannu

2.1.4 Salon Magana

Yana koyar da wayo da kyakkyawan tunani tare da sa raha da shaƙuwa tsakanin yara. Misali: (Waƙar Salihu Jankiɗi)

Yaro in taƙamar salon magana ka ke yi,

ce tsara tsara.

Tahi tsantsamin tsantsara,

Katsantsame tsari tsab ga tsamiya.

3.0 Nazarin Karin Magana a Ma’ana da Nahawu

Adon harshe wani muhimmin ɓangare ne na harshe da ke ƙunshe da hikima da salo na musamman wajen isar da saƙonni a cikin al’adun Hausawa. Adon harshe na ƙunsar fahimta da dabarar harshe wadda ke wuce abin da kalmomi ke nunawa kai tsaye. Wannan bincike yana nazarin adon harshen Hausa ta fuskar kimiyyar harshe, musamman ta fannonin ma’ana (semantics) da nahawu (syntaɗ). Ta fuskar ma’ana, ana duba yadda adon harshe (karin magana) ke iya ɗaukar ma’ana kai tsaye ko ta nuni, wanda ke ƙara zurfafa fahimta ga mai karatu ko saurare (Abubakar, 2005). Ta fuskar nahawu kuwa, ana nazarin tsarin da kalmomi ke bi a jumla da yadda wasu karin magana ke karya ko bin ƙa’idojin nahawun Hausa (Jaggar, 2001). Nazarin yana bayyana yadda adon harshe ke ɗauke da tsari mai ƙayyadaddun ma’ana da salo, wanda ke tabbatar da cewa adon harshe ba kawai karin magana ba ne, sai dai hanya ce ta hikima da dabarar bayyana tunani da saƙonni cikin harshe.

3.1 Nazarin Karin magana Ta Fuskar Ma’ana

Nazarin ma’ana (semantics) na cikin manyan sassa na kimiyyar harshe da ke nazari akan ma’anar kalmomi, jimloli da yanayi da suke bayyana ma’ana. A cikin karin magana ko adon harshen Hausawa, ana amfani da kalmomi da jimloli ta hanyoyi da dama, inda ma’anar kalmar na iya wuce abin da take nufi kai tsaye. Wannan ya haɗa da ma’ana ta kai tsaye da ta nuni, ma’ana da ta dogara da al’ada ko mahalli, da ma’ana ta adon magana.

3.1.1 Ma’ana ta Zahiri da Ɓoyayyiyar Ma’ana

Ma’ana ta Zahiri : Ita ce ma’anar da kalmomi ke nuni da ita a fili, wato yadda suke a zahiri ba tare da buƙatar fahimtar salo ko alama ba. A cikin adon harshe, akwai karin magana da kalmomin su ke nuni da abin da ake nufi a zahiri ba tare da dogon tunani ba. Wannan na taimaka wa yara da sabbin masu karatun Hausa wajen fahimta cikin sauƙi. A cewar Abubakar (2005) “ma’anar ta zahiri a cikin karin magana na da amfani wajen isar da saƙo cikin gaggawa, musamman a lokutan da ake buƙatar fahimtar abin da ake nufi ba tare da salo ko ɓoyayyen nuni ba”. Misali:

“Ruwa baya hana shan ruwa.”

Ma’ana ta zahiri: Ko da ruwa yana da yawa ko yana tafasa ko ana ruwan sama, ba zai hana mutum sha ba.

 “bikin magaji ba ya hana na magajiya.”

Ma’ana ta zahiri: bikin da za a yi namagaji ba zai hana aiwatar da bikin magajiya ba domin itama ‘ya ce kamar yadda magaji yake ɗa (wato matsayinsu ɗaya).

Ɓoyayyiyar Ma’ana: Ita ce wadda kalmomin adon harshe ke nufi ba kai tsaye ba, sai dai ta hanyar amfani da alama ko salo ko al’ada. Yawancin karin magana a Hausa na ɗauke da wannan irin ma’ana domin adon harshe yana sarrafa hikima da salo fiye da yadda ma’anar kalmomin suke a ma’ana ta zahiri. Wannan ma’ana tana buƙatar fahimta mai zurfi da masaniyar al’adun Hausawa.

Karin magana sun fi kowane irin adon harshe ƙunshe da alamar hikima, kuma suna buƙatar fahimta bisa al’ada da harshen da ake amfani da su a ciki.

Haka kuma, Jaggar (2001) ya ƙara da cewa nau’in ma’anar da ke cikin karin magana ya fi yawa yana nuni da wancan abu da kalmar da kanta ba ta fayyace ba, yana da salo ne na hikima da falsafa.

A taƙaice a iya cewa, wasu karin magana na da ma’ana kai tsaye, amma akasari suna amfani da nuni zuwa wani hali ko saƙon da ya fi zurfi fiye da abin da aka faɗa. Misali:

 “Zomo baya ƙyale raminsa”.

Ma’ana ta zahiri: Zomo baya barin ramin da ya haƙa.

Ɓoyayyiya ma’ana: Mutum baya mantawa da asalinsa ko tushe.

“Gaba da gaba ya fi nesa da nesa”.

Ma’ana ta zahiri: Fuskantar juna na kusa ya fi nesa da rabuwa.

Ɓoyayyiyar ma’ana: Tattaunawa da fahimta tsakanin mutane ya fi zaman rashin jituwa.

“Tsuntsu baya ƙauran dare sai da dalili”.

Ma’ana ta zahiri: Tsuntsu baya barin masauki da dare haka kawai.

Ɓoyayyiyar ma’ana: Kowanne abu yana da sanadin sa, babu abu da ke faruwa haka nan.

“Mai haƙuri yakan fi mai ƙarfi”.

Ma’ana ta zahiri: Wanda ke da haƙuri na da ƙarfin zuciya fiye da mai ƙarfin jiki.

Ɓoyayyiyar ma’ana: Juriya da haƙuri sun fi hanzari da tashin hankali amfani.

“Wuta bata ci gaba sai da itace”.

Ma’ana ta zahiri: Wuta tana buƙatar itace don ta ci gaba.

Ɓoyayyiya ma’ana: Fitina ko rikici baya ci gaba sai da goyon baya.

“ Ruwa baya tsami banza”.

Ma’ana ta zahiri: Ruwa ba zai yi tsami ba sai an zuba masa wani abu.

Ɓoyayyiya ma’ana: Rashin daidaito yakan zo daga wani canji da aka haifar.

“Idan ka ci tuwo da tsakuwa, ka faɗa”.

Ma’ana ta zahiri: Idan ka ci tuwo da tsakuwa, gaya mana.

Ɓoyayyiyar ma’ana: Idan ka ci karo da matsala, ka faɗi gaskiya, kada ka ɓoye.

3.1.2 Amfani da Ƙarin Ma’ana

Karin ma’ana na nufin ma’anar da wata kalma ko jumla ke ɗauka fiye da ma’anarta ta asali ko ta ƙamus. Wannan nau’in ma’ana yana taka muhimmiyar rawa a cikin adon harshen Hausawa, inda kalmomi ko jumloli sukan ƙunshi ma’anar da ke da alaƙa da ji ko al’ada ko ra’ayi ko tarihi.

Ƙarin ma’ana na nuna yadda kalma ke iya nuni da abin da ba a faɗa kai tsaye ba, amma wanda masu al’ada ko masu amfani da harshen ke fahimta cikin sauƙi. Wannan na ƙara armashi da hikima a cikin adon harshe, musamman a ɓangaren harshen magana da adabin baka.

A dunƙule, adon harshe yana amfani da kalmomi masu ɗauke da ma’ana fiye da yadda ake ganinsu a rubuce. Wannan yana faruwa ne a lokacin da kalmomi ke samun ma’ana bisa al’ada ko ɗabi’a.

Misali:

“Ido biyu ba ya ganin kuskure”.

Ma’anar a nan ita ce: mutum da ke da ruɗani ko son zuciya ba zai iya fahimtar kuskuren kansa ba.

“Wanda bai ji bari ba, shi ne ruwa ke kaiwa bango”.

Ma’anar ba wai ruwa da bango kai tsaye ba, ana nufin wanda baya jin shawara zai shiga matsala.

3.1.3 Sakaya ma’ana (Saye)

Saye (sakaya) na nufin kiran wani abu da sunansa, ta hanyar amfani da wasu kalmomi da suke da kusancin ma’ana amma kuma sukan ɓoye hali ko yanayi na zahirin abun (Salim, 1978:92). Wani lokaci adon harshen Hausawa yana amfani da karin magana masu sakaya ma’ana, wato jumloli da ba za ka fahimce su da fassara kai tsaye ba sai da zurfin fahimta. Misali:

“Ka hura wutar da za ta ƙone ka”.

Anan ana nufin ka jawo wa kanka fitina ko masifa.

“Ka tono wuƙar yanka ka”.

Anan ana nufin ka ƙwaƙulo wa kanka abin da zai iya zama tonon asiri ko fallasa.

Hikimar Amfanin sakaya ma’ana a Harshe shi ne fadakarwa cikin ladabi, wato ana iya gargaɗi ko tuni cikin salo mai sauƙin karɓuwa, kaucewa cin mutunci ma’ana magana ta nuni da mutunci ba tare da wulaƙanci ba. A wani lokacin kuma hanyace ta isar da ma’ana mai zurfi da ƙarfafa salo da ɗabi’a, don nuna hikima da ladabi.

3.1.4 Ma’ana Bisa Mahalli

A fannin ilimin ma’ana (semantics), ana fassara bisa muhalli (conteɗtual meaning) a matsayin ma’anar da kalma ko jumla ke ɗauka bisa yanayin da aka furta ta, muhallin da aka ambata ta, ko dangantakar da take da wasu kalmomi a cikin magana. Wannan yana nufin cewa ma’anar kalma ba lalle ta kasance ɗaya ba a kowane lokaci, domin yana iya canzawa bisa ga yadda aka yi amfani da ita a cikin zance (Lyons, 1977).Misali:

A kalmar “ciki”, a ma’anar ƙamus, tana nufin wurin da abinci ke shiga ko sassan jiki na gaba.

Amma idan aka ce “Kayan ciki ba ya waƙa,” a cikin adon harshe, “ciki” yana nufin damuwa, ɓacin rai, ko sirrin zuciya. Wannan shi ne bisa muhalli, ma’ana da ta bambanta da ta kai tsaye bisa ga yadda ake amfani da kalmar.

Kalmar “gida” na iya nufin wurin zama, amma a cikin adon harshe kamar “Gida biyu ba ya hana zumunci,” tana nufin matan aure biyu. Wannan nuni ne da yadda ma’anar kalma ke sauyawa daidai da muhallin zamanta a cikin jimla.

Muhimmancin ma’ana bisa muhalli nada matuƙar amfani wajen:

i. Ƙarfafa fahimta: Yana sa a fahimci ainahin abin da kalma ke nufi a zance, musamman a harshe mai amfani da karin magana da adon harshe kamar Hausa.

ii. Guje wa ruɗani: Ana guje wa rikice-rikicen ma’ana ta hanyar duba mahallin zance da wuri.

iii. Nuna tasirin al’ada da zaman jama’a: Muhalli yana ɗauke da wasu ƙayyadaddun al’adu da ke ƙarfafa fassarar kalma (Abubakar, 2005).

A taƙaice, a cikin adon harshen Hausawa, bisa muhalli na taka muhimmiyar rawa wajen sauya ko faɗaɗa ma’anar kalmomi da jimloli. Hausawa sun ƙware wajen amfani da adon harshe don isar da saƙo ta hanyar salon nuni da sakaya ma’ana, wanda ke buƙatar duba mahalli domin fassara su daidai. Wannan yana nuna cewa, nazarin ma’ana a harshen Hausa ba zai cika ba sai an fahimci tasirin ma’ana bisa muhallin magana.

3.1.5 Ma’anar Tana Sauyawa Bisa Salo da Sauti

A fannin ilimin harshe, musamman a nazarin adon harshen Hausawa, ana cewa ma’ana tana sauyawa idan ta sauya daga ma’anarta ta ainihi zuwa wata ma’ana ta nuni ko ta salo. Wannan rikiɗewar na faruwa ne sakamakon tsarin salo (style) ko kuma tasirin sautuka (phonological aesthetics). Wato, adon harshe kan rikita ma’ana ko ya kawata ta, domin ya dace da al’ada, hikima, ko kuma ya jawo hankali cikin natsuwa.

Lyons (1977) ya bayyana cewa:

 "semantic meaning is often shaped and reshaped through

phonological and stylistic deɓices."

Haƙiƙa a nazarin adon harshe na Hausawa, ma’anar kalmomi tana canzawa (sauyawa) bisa tsarin sauti. Wannan rikiɗewar ma’ana na nuna yadda harshen Hausa ke tattare da zurfin hikima da salo mai ɗaukar hankali, wanda ke buƙatar ingantaccen fassara da zurfin fahimta ga masu nazari. Misali:

“A ɗaga sama an yi wa wadaa ƙwace”

“A ɗaga sama an yi wa wada ƙwace”

A nan idan aka duba misali na farko (karin magana) za a tarar kalmar waada a kan ta ma’anar ta ɗamfaru, kuma suna ne gama-gari; sau da yawa sunaye gama-gari wasalinsu na ƙarshe dogaye ne. Saboda haka da zarar an maida sunan na yanka to dogon waslin yana gajercewa. Wato kalmar ta kom “wada” sunan mutum na yanka.

“A zaɓa a gásà ta hana yaro suna”

“A zaɓa a gásá ta hana yaro suna”

Haka nan ma idan ka duba kalmar gásà aikatau ne ɗan aji ɗaya, karin sautin sa (sama-ƙasa), saboda haka a kan ta ma’anar karin maganar ta ɗamfaru da zarar kari sautin ya canza, babu shakka ma’anar za ta canza kamar yadda aka gani a misali na biyu da ta zo a matsayin suna.

3.1 Nazarin Adon Harshen Hausa Ta Fuskar Nahawu

Hikima da ma’ana mai zurfi, sau da yawa yana saba da ka'idojin daidaitattun nahawun Hausa (syntactic rules). Wannan rashin bin ƙa’ida ba laifi ba ne a fannin fasahar harshe, domin yana faruwa ne saboda buƙatar salo, da sauƙaƙa isar da saƙo. Irin wannan sauye-sauyen tsarin nahawu ana ɗaukar su a matsayin wani fasali na al’ada da ƙirƙra cikin magana, ba rashin ilimi ba.

Haƙiƙa a cikin nau’o’in adon harshen Hausa, akwai lokuta da yawa da ana saba wa ƙa’idojin nahawu (grammatical rules) na Hausa. Wannan saba dokar nahawu ba kuskure ba ne a nan, domin galibin irin wannan saɓa wa doka ana yin shi ne da gangan don dalilai kamar:

i. Salo.

ii. Ƙayatarwa da sauƙaƙa tunawa.

iii. Ma’ana mai zurfi ko nuni da hikima.


 

Ire- ien saɓa dokar Nahawu a cikin Adon harshe sun haɗa da:

3.1.1 Saɓa wa Tsarin Nahawu

Karya tsarin jumla (sentence structure) na ɗaya daga cikin saɓa wa tsarin nahawu a cikin adon harshe. Misalin Adon harshe:

 “Idan dutse ya motsa, ruwa ya biyo shi”.

Daidai tacciyar Hausa: Idan dutse ya motsa, ruwa zai biyo shi.

Ma’ana: Bisa daidaitaccen tsari na Nahawun Hausa, ana amfani da tsarin “zai biyo” wanda shi ne lamirin suna (LS) da lamirin lokaci (LL) da suka dace da gurbin, kasancewar an sami kalmar sharaɗi a cikin jumlar, sai aka yi amfani da “ya biyo” don samar da lafazi mai ƙarfi da salo.

3.1.2 Saɓa wa Tsarin Jumla

A nahawun Hausa, tsarin jumla yana bin ƙa’ida ta aikau (subject), aiki (ɓerb), da karɓau (object), wato SƁO (wanda yai aiki, aikin, wanda aiki ya faɗawa). Amma a cikin adon harshe (proɓerbs), wannan tsarin sau da yawa ana lalata shi ko sauya shi domin cimma wata manufa ta salo, ma’ana ko sauƙin isar da saƙo. Wannan saɓawa tsarin jumla shi ne ke ba adon harshe armashi da zurfin fasaha a magana.Misalai na Sabawa Tsarin Jumla akwai:

i. Rage ko kawar da kalmar aiki:

Misalin Adon harshe: “Mai rabo bai wahala.”

Daidaitacciyar Hausa: “Wanda yake da rabo ba zai sha wahala ba.”

→ A nan an kawar da tsari na SƁO, aka bar sassa kaɗan, don taƙaitawa.

ii. Farkon jumla ba tare da sun aikau ba:

Misalin Adon harshe: “Ƙarya gugar goro.”

Daidaitaccen jumla: “Ƙarya kamar gugar goro ce.”

→ Tsarin nahawu ya buƙaci cikakken bayani, amma an rage shi domin lafazi mai sauti da tasiri.

3.1.3 Amfani da Kalma a Wata Ma’ana

A cikin adon harshen Hausawa, ana yawan amfani da kalma ɗaya ko jumla domin nuni da wani ma’ana daban da na zahirin kalmar. Wannan salo ana kiransa da amfani da kalma a wani ma’ana, ko karkata ma’ana (semantic shift). Wannan tsari na daga cikin fasaha da ke ba wa adon harshe zurfin ma’ana da nishaɗi.

Nau’o’in amfani da kalma a wani ma’ana ya haɗa da; Tamkar ko Kama (Simile/Analogy) da Nuni (Metaphor) da Zambo (Sarcasm/Irony) da makamantansu. Misali:

“kowa ya bar gida, gida ya bar shi”

‘Gida’ yana nufin muhalli ko matsuguni, wato wurin zama da aka gina domin mutane su zauna. Amma idan aka faɗaɗa ma’anar ‘gida’ na nufin asali ko tushen wani abu, haka yana iya zama kwanciyar hankali da kariya.

3.1.4 Saɓa wa Siffar Kalma

A cikin adon harshen Hausawa, ana yawan canza ko karya dokokin ƙirƙirar kalmomi (morphology) domin cimma wata manufa ta salo, nuni, ko ƙarin ma'ana. Wannan salo ana kiransa da saɓawa siffar kalma, wato sauya tsarin daidaitattun kalmomi ko ƙara musu wani salo ko murya domin ƙarfafa tasirin maganar.

Saɓawa siffar kalma na nufin sauya tsarin ginin kalma daga yadda ya kamata a ce kalmar tana a tsarin nahawu, zuwa wata siffa daban ta salo, ko nuni. Misali:

“Mai ƙarya, ƙarya ce garkuwarsa”.

Ana amfani da kalmar “ƙarya” sau biyu a jere; ta farko a matsayin sifa, ta biyu a matsayin suna. Wannan sauyin matsayi ya saɓa da tsarin da aka saba amfani da kalmomi a cikinsa cikin dokokin nahawun harshen.

3.1.5 Rashin Cikasa Sassan Jumla

A ilimin nahawu, jumla ita ce cikakken zance mai ma’ana da ke ƙunshe da wanda yai aiki (subject) da kuma bayani ko aiki (predicate). Amma a cikin karin magana ko adon harshen Hausawa, ana iya rage ko barin wasu sassa na jumla saboda manufar salo, rage yawan magana, ƙarfafa nuni, ko jawo hankali. Wannan salo na daga cikin abin da ake kira ellipsis a ilimin nahawu.

Rashin cikakken sassan jumla yana nufin barin wasu sassa daga cikin ginshiƙin jumla (kamar aikau ko aiki), duk da haka ana iya fahimtar ma’ana daga yanayi ko al’ada.

Yahaya (2003) ya bayyana cewa, “A karin magana, rage ko barin ɓangarori na jumla wani salo ne na hikima wanda ke jawo tunani.”

Baba (2011) ya ce: “Adon harshe yakan yi amfani da barin wasu sassa na nahawu domin sauƙaƙe fahimta da haifar da tasiri.”

Kenan wannan salo yana bayyane a cikin karin maganganun da ba su da cikakken tsari na nau’in daidaitaccen jumla. Da yawa daga cikin irin waɗannan karin maganganu, nau’o’i ne na karin magana mai labari. Irin wannan karin magana ya samu ne a dalilin wani labari ko tatsuniya ko kuma a sakamakon aukuwar wani al’amari. Hassan da Yankara (2022) sun jero misalan karin maganar da suka samu asalinsu daga labari kamar haka:

“Gyaɗar dogo”

“Faɗan gwaggo a ƙofa”

“Sautun mahaukaciya”

“Adashin uwar Nuhu”

“Sanin damisar bunu”

“Jiran gawon shanu”

 Da sauransu.

A nan akwai kalmomi da ba a faɗe su gaba ɗaya ba, amma mai magana ya fahimtar da mai sauraro a cikin adon harshe, wanda ya saɓa wa tsarin jumla cikakkiya.

3.2 Me Yasa ake Wannan saɓa wa Ƙa’idoji?

Adon harshen magana na da babban matsayi a wajen al'ummar Hausawa, domin ta wajen magana ake siffanta halayyar mutum ko gane ɗabi'ar mutum tun kafin ya yiwani abu a aikace. Matsayin adon harshe a jiya tamkar matsayin sharar fage ne a ɓangaren makarantun yara dukkanin hanyoyi da ake bi domin cusawa yara kyawawan halaye da dakushe munana.

Kaɗan daga misalan matsayin Adon harshe a jiya sun haɗar da:

i. Sashen nazari ne da ke taimakawa wajen ilimantar da yara a ɓangaren al'adunsu musamman ta nusar da su lura da kyakkyawar tarbiyya.

ii. Yakan zama fage ne na shiryar da yara ga hanyoyin koyi da nagartattun ɗabi’u tare kaucewa ɓatattu. Don haka ne ya zama tamkar makaranta inda ake ɗaukar darussa.

iii. Hukuma ce ta adana tarihi da al'adun gargajiya ta yadda ba za su salwance ba domin ya zame wa yara a jini da tsoka wajen tsarin gudanar da rayuwarsu. Inda ake sanar da su tarihin al'ummomin da suka shuɗe musamman dangane da rayuwarsu da aikace-aikacensu.

iv. Zauren sulhu ne, domin yana taimakawa waje yanke hukunci da daidaita tsakanin yara ta wajcn yi musu sulhu.

v. Tsangayar ilimi ce, domin a jiya Adon harshe kan taimaka wajen ƙago da ƙirƙirosababbin kalmomi, ta haka yakan ƙara haɓaka rumbun harshe (Hassan, 2010).

Wannan ne babban dalilin da ya sanya Husawa basa la’akari da ƙa’ida ta Nazarin Kimiyyar Harshe, domin samun damar ƙarfafa sautin magana ko don ɗaukar hankali da tunani, saboda harshen adon harshe na dogara da salo, hikima da sauƙaƙe magana, ba lallai ya bi cikakken tsarin nahawu ba, a wani lokacni ana ƙetare iyakar nahawu don faɗar abin da aka ɓoye da basira.

4.0 Kammalawa

Wannan takarda mai taken “Nazarin Kimiyyar Harshe a cikin Adon harshen Hausawa: Duba a kan Ma’ana (semantic) da Nahawu (syntaɗ),” an gudanar da bincike kan yadda adon harshe (karin magana) ke ɗauke da ingantaccen tsarin harshe mai cike da hikima da fasaha. An gano cewa, ko da yake adon harshe yakan kauce daga daidaitattun dokokin nahawu da ma’ana na yau da kullum, hakan yana da nufin ƙarfafa tasirin sa da faɗaɗa ma’anoni bisa ga yanayin al’ada da fahimta da ƙwarewar masu magana.

ɓangaren nahawu (syntaɗ), an fahda makamantansu. Waɗannan sauye-sauyen ba suna nufin kuskure bane, sai dai suna nuni da ƙwarewa a salo da tsararren gini domin cimma hikima da gargaɗi domin ƙarfafa ma’ana.

ɓangaren ma’ana (semantic), adon harshe na ɗauke da ma’ana ta sarari da ta ɓoye, inda wasu kalmomi ke fitowa da ma’anoni masu zurfi da ƙarin ma’ana, ko ma dabam da yadda suke a ƙamus. Ana iya fahimtar adon harshe daidai ne idan an yi la’akari da yanayin amfani da shi, muhalli, da al’ada. Wannan ya nuna cewa adon harshe wata hanya ce ta isar da saƙonni masu nauyi cikin taƙaitattun jumloli.

ƙarshe, adon harshen Hausawa wata muhimmiyar hanya ce ta sarrafa harshe wadda ke bayyana hikima, ƙwarewa, da dabarun sadarwa na al’ummar Hausa. Wannan bincike ya tabbatar da cewa adon harshe ba wai kawai abin da ya shafi adabi da al’ada ba ne, akwai bayyana dokokin harshe da tsari da salo, da zurfin ma’ana wanda ke buƙatar fahimtar kimiyyarsa, musamman nahawu da ma’ana domin a tantance girman darajarsa da aikinsa a cikin al’umma.

Manazarta

Abubakar, M. (2005). Karin Magana da Ma’ana a Hausa. Kano: Bayero Press.

Baba, A. (2011). Nazarin Harshen Hausa. Kano: Triumph Publishing.

Ɗangambo, A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Gidan Sa'adu Zungur.

Ɗangambo, A. (2008). Rabe-Raben Adabin Hausa. Zaria: Amana publishers.

Hassan, F. M. (2010). “Tsokaci dangane da Adon harshen Hausawa Wajen Cusa Ɗa’a a Zuƙatan Yara”. Huda-Huda Journal of Languages, Vol. 3, No. 1, pg: 230-237.

Hassan, H. da Yankara, M. M. (2022). Karin Magana Mai Labari. http://www.researchgate.net

Jaggar, P. J. (2001). Hausa. Amsterdam: John Benjamins.

Junaidu, I. da Yar' aduw a, T.M. (2007). Harshe da Adabin Hausa a Kammale. lbadan:Spectrum Books Limited.

Lyons, J. (1977). Semantics (Vol. 1). Cambridge: Cambridge University Press.

Salim, B. A. (1978). Saye a Hausa. Harsunan Nijeriya ƁIII. Kano: Cibiyar Nazari Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero.

Sani, M. (2011). Ilmin Sauti da Nahawu a Hausa. Zaria: Gaskiya Corporation.

Sani, M. (2015). Ilmin Nahawun Hausa na Zamani. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Yahaya. I. Y. da wasu (1992). Darussan Hausa. Ibadan: University Press Plc.

Yusuf, B. (2014). Fasahar Magana a Adon harshen Hausawa. Kano: Benchmark Press.

 Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC)

Post a Comment

0 Comments