Citation: Bappha BABANGIDA, Mannir SHEHU &Muhammad Sani USMAN (2025). Nazarin Kan Kalmomin Lissafi: Duba Zuwa Ga Hausar Masu Sana’ar Sayar Da Shanu A Garin Azare. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 13, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
NAZARIN KAN KALMOMIN
LISSAFI: DUBA ZUWA GA HAUSAR MASU SANA’AR SAYAR DA SHANU A GARIN AZARE
NA
BAPPHA BABANGIDA
MANNIR SHEHU
MUHAMMAD SANI USMAN
Tsakure
Wannan takarda ta ƙunshi bincike a kan
sauyawar ma’anar kalmomin lisssafi a bakin masu sana’ar sayar da shanu a garin
Azare ta jihar Bauchi. A cikin wannan takarda an fito da irin kalmomin da masu
wannan sana’ar suke amfani da su, wajen lissafin kasuwancinsu. An yi amfani da
ra’in Sauyi wanda wani Bature mai suna Robins R.H (1964) ya ɗabbaƙa (Transfers of Meaning).
Sannan an bi hanyoyin da suka dace, domin neman bayanai waɗanda suka haɗa da hira/tattaunawa da
kuma lura. Takardar ta gano wasu daga cikin kalmomin lissafin da suke samun
sauyin ma’ana. Daga cikin kalmomin akwai irinsu: riɗa (ɗari), shiri (ashirin),
linta, ɗauri, kwasta (takwas), murhu (uku) da kuma ma
(goma). Sannan yawancin kalmomin an samu tasirin ɓangarorin da suka shafi
kimiyyar harshe kamar shafewa da musaya da sauransu.
1.0 Gabatarwa
Masana da manazarta
harshen Hausa da dama musamman waɗanda
suka shafin ilmin walwawalar harshe da ma’ana, sun gudanar da rubuce-rubuce
dangane da Hausar rukuni, musamman ta masu sana’a wasu daga cikinsu akwai; Yola
(2021) da Asiru (2000) da Fagge (2004) Muktar (2002) da Fage (2002) da Wurma
(2002) da Zage (2002) da Adamu (2004) da Gandu (2004) da Shafa’atu Usamatu
Mahmud (2012) da Maigari (2017) da Yakasai (2004) da Aisha Adamu Umar (2008) da
Salima Ahmad (2008) da Aujara (2012) da Yahaya (2012) da Abubakar (2023) da
Babangida (2023) da kuma Ramadan 2017. Karin harshen rukuni ya samu ne
sanadiyyar banbancin aji da matsayi ko jinsi da muƙami
ko kuma sana’o’in da ake samu a cikin zamantakewar al’umma. Kuma ƙarƙashin
wannan nau’i na karin harshe ake samun nau’o’i da dama, musamman abin da ya
shafi Hausar rukunin jama’a. Wannan takardar ta yi nazarin sauyawar ma’anar
kalmomin lissafi a Hausar masu sana’ar sayar da shanu ne amma na garin Azare.
Takardar ta yi bayani ne bisa yadda waɗannan
masu sana’a suke furta kalmominsu na lissafin kuɗi a
lokutan sana’ar su. Sa’annan kuma takardar ta yi nazarin irin kalmomin lissafin
da suke amfani da su tare da fito da ma’anar su ta asali da kuma sabuwar
ma’anar da aka samo.
1.1 Ma’anar Sauyawar Ma’ana
Babangida (2023), ya
bayyana sauyawar ma’anar kalmomi da cewa “ta shafi yadda ake samun sabbin
kalmomi a harshe, domin kai-tsaye yake shafar rayuwar al’umma. Dalili kuwa shi
ne ma’ana ita ce ginshiƙin kowane irin saƙo da ake son isarwa al’umma aba tare da samun
wata tangarɗa ko matsala ba, don haka,
ana samun sauyin ma’ana a yawancin harsuna”.
Aujaura (2023, sh. 7),
bayayana ma’anar ma’ana da cewa “nazarin ma’ana a harshe shi ne yadda za a
fahimci dangantakar kalma da abin da take nufi. A duk lokacin da aka
ambaci ɗaya daga ciki, dole ne
tunanin ɗayan ya zo zuciyar mai
magana ko mai sauraro”.
Ɗanzaki (2015:450) na da
ra’ayin cewa “sauyin ma’ana hanya ce ta sauyawar ma’anar asali ta kalma inda
ake samun sabuwar ma’ana daga tsohuwar ma’ana ta kalma”.
Aujara (2012:77) ya ƙara da cewa “sauyin ma’ana
shi ya fi tasiri cikin tsarin rayuwar harshe domin kai tsaye yake shafar
rayuwar al’umma. Saboda ma’ana ita ce ginshiƙin kowane irin saƙon da ake son isarwa”.
2.1 Hanyoyin Tattaro
Bayanai da Ra’in da aka Ɗora Aikin
Kowane bincike irin na
ilimi, ana gudanar da shi ne ta hanyar bin wasu matakai ayyanannu waɗanda zasu tabbatar da
wanzuwarsa, a kuma ɗora shi a kai (Dornyei, 2011, Muhammad,
2017). A wannan bincike an yi amfani da hanyar bincike sharhantau (ƙualitatiɓe research) wajen aiwatar
da wannan takarda da ke ƙoƙarin bayyana sauyawar ma’anonin kalmomin
lisaafi a Hausar masu sana’ar sayar da shanu a garin Azare, ta fito da ƙirƙirarrun kalmomi tare
da ƙalailaice ma’anarsu. Irin
wannan dabara masana irinsu Creswell (2009), Dornyei (2011), Taɓakoli (2012) da Muhammad
(2017) sun gudanar da mabambanta bincike ta hanyar ɗora wannan dabara
(sharhantau), sun haƙiƙance tare da turjewa a kan wannan dabara. Saboda haka,
wannan bincike an ɗora ta ne akan hanyar bincike sharhantau wajen aiwatar da
ita.
2.2 Tattaunawa
Na nufin zanatawa ko
maganganu tsakanin mai gudanar da bincike da kuma wanda ake bincike akan sa.
Hanya ce wadda ake amfani da ita wajen tambayar ma’abocin bincike yana kuma ba
da amsa akan abin da aka tambaye shi gwargwadon hali. A wannan bincike da aka
gudanar an yi amfani da wannan hanya ta tattaunawa domin neman sahihan bayanai
daga wurin nasu gudanar da wannan sana’a ta sayar da shanu a garin Azare, wadda
yayin aiwatar da wannan tattaunawa an tambayi waɗanda
binciken ya shafa akan yadda suke furta kalmominsu na lissafi, tare da sani da
dalilin da ya sa suke amfani da su. An kuma yi tambayoyin ne baki-da-baki ana
naɗa a wayar hannu daga
baya an mai da shi zuwa takarda, a wasu lokutan kuma akan rubuta da kuma naɗa a
tare, domin tabbatr da ingancin ta.
2.3 Lura
Wannan ma dabara ce ta
hanyar gudanar da bincike wadda ake yinta ta hanyar kallon ko kiyaye al’amuran
da suka shafi bincike kai-tsaye ta hanyar duban majikirta bincike nan take. A
wannan takarda an yi amfani da lura, a wasu lukuta domin fahimtar wasu kalmomin
lissafi da masu sana’ar sayar da shanu a garin Azare, suke furtawa domin sanin
ma’anoninsu.
3.1 Ra’in Bincike
Wannan bincike da aka
gudanar an ɗora shi kan ra’in Sauyin
Ma’ana (Transfers of Meaning) wanda wani Bature ɗan ƙasar Amurka mai suna Robins
R.H (1964) ya ɗabbaƙa, wanda ra’in yake bayani a kan yadda ake
samun sauye-sauye a cikin harshe waɗanda suke faruwa ta la’akari da irin ci gaban
da harshe yake samu ta ɓanagren ƙare-ƙere. Haka kuma, sauyarwar
ma’anar ta shafi yadda kalmomin harshe ne suke sauyawa da nufin samar da
sababbin ma’anoni daga wani rukuni na wata al’umma da take amafni da
harshe ɗaya. Takan samu kuma ta
hanyar ƙirƙirar kalmar da babu ita, ko
kuma faɗaɗa ma’anar kalmar daga
tsohuwar kalmar zuwa sabuwar da samar.
3.2 Dangantakar Ra’i da
Bincike
Dangantakar da ke tsakanin
wannan ra’in da bincike ita ce, binciken an gudanar da shi ne a kan nazarin
ma’ana da ƙirƙirar kalmomi, ra’in shi ma
yana magana ne a kan yadda ake samun sauyin ma’ana ta hanyar faɗaɗa da ƙirƙirar kalma, wanda Hausar
masu sana’ar sayar da shanu suna amfani da waɗannan hanyoyi.
4.0 Kalmomin Lissafi a
Hausar Masu Sana’ar Sayar da Shanu a Garin Azare
Kalmomin lissafi, kalmomi
ne da ake amfani da su domin aiwatar da kasuwanci musamman ɓangaren da shafi cinikayya
ta kuɗi. Masu sana’ar sayar da
shan u kamar sauran sana’o’i suna amfani da irin waɗannan kalmomi. Sai dai nasu
kalmomin ma’anarsu ta sha bamban da na daidaitacciyar Hausa, wasu kuma an samu
canje-canje da suka shafi kimiyyar harshe, irinsu musaya da sharewa da naso da
sauransu.
4.1 Ma’anar Lisssafi
Ƙamusun Hausa (2006, sh.
280), ya bayyana ma’anar lissafi da cewa “kalma ce da take bayani akan ƙidaya ko lissafi na adadin
wani abu, kamar kuɗi ko tufafi da sauransu.
Lissafi ya shafi yadda ake
iya auna ko mizanin abu, wanda yake iya tantance yawa ko adadin abin da ake
son ƙidaya wa. Bisa irin wannan
dalili ya sa Bahaushe kan ce mutum yana da lissafi. Wato kenan lissafi abu ne
mai kyau da yake tabbatar da gaskiya ko sahihancin abu.
4.2 Kalmomin Da
Suka Shafi Lissafin Kuɗi
Kalmomin da suka shafi
lissafin kuɗi a Hausar masu sana’ar
sayar da shanu a garin, kalmomi ne da suke zuwa a wakiltar kuɗi a Hausar yau da kullum.
Suna amfani da kalmomin ne domin karya harshe a tsakaninsu, domin wanda baya
cikinsu kar ya fahimci me suke nufi. Har ila yau, suna sadar da junansu a harƙoƙinsu na kasuwa kuma suna
fahimtar me suke faɗa. Wasu daga cikin kamomin kamar yadda suke amfani da su
ne kamar haka a jadawalin da ke biye a ƙasa:
4.3.
Lissafin Ƙananan
Kuɗi
Waɗannan kalmomi da ke ƙasa, kalmomi ne waɗanda masu sana’ar sayar da
shanu a garin Azare suke amafani da su wajen bayyana ƙananan kuɗi daga naira ɗaya zuwa naira ɗari biyar.
|
Lamba |
Ma’anar Hausar Masu Sana’ar Sayar Da
Shanu a Garin Azare |
Ma’anar Kalmomin a Daidaitacciyar
Hausa |
|
01. |
Má |
Naira goma |
|
02. |
Shíirí/ɗân-kánóo |
Naira ashirin |
|
03. |
Líntàa |
Naira talatin |
|
04. |
Yàríi/síhán |
Naira biyar |
|
05. |
Kwái |
Bakwai/naira bakwai |
|
06. |
Ráatá |
Tara/naira tara |
|
07. |
Ríɗáa-yàríi |
Naira ɗari biyar |
|
08. |
Fítá-dá- yàríi |
Naira hamsin |
|
09. |
Búutà-dá-fítá-dá-yàríi |
Naira ɗari biyu da hamsin |
|
10. |
Búutà |
Naira ɗari biyu |
|
11. |
Támáa |
Naira tamanin |
|
12. |
Cáasàa |
Naira casa’in |
|
13. |
Ríɗáa |
Naira ɗari |
|
14. |
Kwástà |
Takwas/naira takwas |
|
15. |
Dáshì |
Shida |
|
16. |
Ɗíhù |
Huɗu |
|
17. |
Múrhù |
Uku |
|
18. |
Yú |
Biyu |
A wannan waje an kawo
lissafi ne wanda ya shafi dubu-dubu, ma’ana daga kan naira dubu ɗaya zuwa sama da haka,
kamar yadda yake a ƙasa.
|
Lamba |
Sunan Kuɗi a Hausar Masu Sana’ar Sayar Da
Shanu a Garin Azare |
Ma’anar Kalmomin a Daidaitaciyar
Hausa |
|
19. |
Ɗáurí |
Naira dubu |
|
20. |
Jákà-má |
Naira dubu biyu |
|
21. |
Ríɗáa-yàríi |
Naira dubu ɗari biyar |
|
22. |
Ríɗáa-múrhù |
Naira dubu ɗari uku |
|
23. |
Dúbùu-má |
Dubu goma |
|
24. |
Dúbùu-ráatá |
Dubu tara |
|
25. |
Dúbùu-kwástà |
Dubu takwas |
|
26. |
Dúbùu-kwái |
Dubu bakwai |
|
27. |
Dúbùu-dáshì |
Dubu shida |
|
28. |
Dúbùu-ɗíhù |
Dubu huɗu |
|
29. |
Dúbùu-múrhù |
Dubu uku |
|
30. |
Dúbùu-yú |
Dubu biyu |
|
31. |
Dúbùu-támáa |
Dubu tamanin |
|
32. |
Dúbùu-búutà |
Naira dubu ɗari biyu. |
33. Jákà-má: Jaka wata aba ce da ake
amfani da ita wajen saka kaya ko wani abu domin suturta shi ma kuma bata da
wata ma’ana a Hausa, amma masu sana’ar sayar da shanu sun sauya ma’anar kalmar
da nufin naira dubu biyu domin ɓadda bami ga wanda baya cikin sana’ar.
34. Ríɗáa-yàríi: Yari wani abu ne da ya
shafi adon mata, riɗa kuwa bata da wata ma’ana. Amma masu sana’ar sayar da
shanu suka ba ta ma’ana wajen lissafinsu na kuɗi da cewa dubu ɗari biyar.
a. Dúbùu-má: Wannan kuma lissafi ne da
suke yi mai ɗauke da ma’anar naira dubu
goma, ya yin da suke yin wannan lissafi ba a fahimtar me suke nufi sai wanda
yake cikin rukuninsu.
36. Dúbùu-ráatá: Wannan ma lissafin kuɗi ne da suke nufin naira
dubu tara, wanda idan aka duba ma’anar kalmar rata tana nufin tazara da ake
samu a tsakanin wani abu. Amma suka sauya mata ma’ana ta hanyar ɗauko gabar ƙarshe ta dawo farko domin
amfaninsu.
37. Dúbùu-kwástà: Wannan kalma kuma tana
nufin naira dubu takwas a Hausar masu sana’ar sayar da shanu a ƙasar Katagum ta yadda suka
mata kwaskwarima ta hanyar ɗauko gaɓar farko ta koma ƙarshe.
38. Dáurí: Ɗauri na nufin kulle wani
abu da zare ko wata igiya, amma masu sana’ar sayar da shanu suka bata sabuwar
ma’ana da nufin lissafin kuɗi mai ɗauke da ma’anar naira dubu.
39. Dúbùu-kwái: Kwai kalma ce da bata da
wata ma’ana, amma masu sana’ar sayar da shanu suna amfani da ita wajen kiran
naira dubu bakwai a ya yin gudanar da harƙoƙin ksuwancinsu.
40. Dúbùu-dáshì: Dashi kalma ce mai ɗauke da ma’anar adashe da
ake yi ta hanyar tara kuɗin mutane a bawa wani duk sati ko wata, amma
a Hausar masu sana’ar sayar da shanu tana nufin naira dubu shida. Sun samar da
wannan kalma ce ta hanyar sauya gaɓar farko ta koma gaba domin biyan buƙatarsu ta kasuwanci. Sun
kuma ɗauko gaɓar farko ta koma gaba wato
musayar gurbi kenan.
41. Dúbùu-ɗíhù: Kalmar ɗihu kalma ce ƙirƙirarriya wanda bata da wata
ma’ana, amma masu sana’ar sayar da shanu sun bata ma’ana da nufin huɗu idan aka haɗata da dubu kuma ta koma
naira dubu huɗu ta lissafin kuɗi.
42. Dúbùu-yú: Wannan kalma ta dubu-yu,
kalma ce wacce take da ma’anar naira dubu biyu a Hausar masu sana’ar sayar da
shanu. Ya yin da suka yi amfani da dabarar shafewa domin samar da kalmar, yadda
suka shafe ‘bi’ suka bar gaɓar ‘yu’.
43. Dúbùu-támáa: Dubu lissafin kuɗi ne, tama kuwa dabarar
shafewa aka yi amfani da ita domin samar da wata kalma ta daban a Hausar masu
sana’ar sayar da shanu a ƙasar Katagum. Suna amfani da wannan kalma ce
da nufin naira dubu tamanin na lissafin kuɗin a yayin gudanar da harƙoƙin kasuwancinsu.
44. Dúbùu-búutà: Wannan kalma kuma a
Hausar masu sana’ar sayar da shanu tana nufin naira dubu ɗari biyu na lissafin kuɗi. Amma a daidaitacciyar
Hausa dubu lissafin kuɗi kamar yadda yake, yayin da buta kuma take ɗauke da ma’anar abin da ake
amfani da ita wajen alwala ko zagawa bayan gida domin wata buƙata.
45. Ráatá: Kalmar rata tana nufin
tazara da ake samu tsakanin wani abu da wani. Amma a Hausar masu sana’ar sayar
da shanu a ƙasar Katagum tana nufin
naira tara ta lissafin kuɗi.
46. báyi-tá-Állah:
Bayi-ta-Allah wata nau’in tsuntsuwa ce da ake samu a daji ko a gida wadda ake
iya cin namanta. Amma a wurin masu sana’ar sayar da shanu suna amafani da ita a
matsayin naira biyar.
47. Fítá-dá-yàríi: Wannan kalma harɗaɗɗiya ce wadda take nufin
naira hamsin a Hausar masu sana’ar sayar da shanu a ƙasar Katagum. Wadda asalin
fita tana nufin baro wani abu, yari kuma wani abin ado ne na mata.
48. Búutà: Buta kuwa wata a bace da
ake amfani da ita wajen yin alwala. Amma masu sana’ar sayar da shanu sun bata
ma’ana da nufin naira ɗari biyu na lissafin kuɗi.
4.4 Shafewa/Datsewa
Wasu kalmomin a Hausar masu
sana’ar sayar da shanu a garin Azare suna samuwa ne ta hanyar shafe wata gaɓa daga cikin wata kalma
wadda take da ma’ana a Harshen Hausa. Shafewa wata dabara ce da ake amfani da
ita domin samar da wata kalma ta hanyar datse wani ɓangaren gaɓar kalmar. Wasu daga cikin
kalmomin da masu sana’ar sayar da shanu a ƙasar Katagum suke amfani da
su waɗanda suka shafi datsewa sun
haɗa da;
49. má: A wannan lissafi an samu
datsewa ne na kalmar, asali kalmar tana nufin naira goma ne a harshen Hausa,
sai masu sana’ar sayar da shanu suka datse gaɓa ta biyu domin samar da
tasu kalmar, duk da cewa ma’anar bata canza ba.
50. gáná: A wannan kalma ta gana
wadda a Hausar masu sana’ar sayar da shanu take ɗauke da ma’anar magana. Ita
ma sun shafe gaɓar ‘ma’ ne mai ɗauke da ma’anar magana ta
koma gana a wajensu domin sadar da junansu.
51. shíirí: Asalin wannan kalma tana
nufin lissafi ne na ashirin. Har ila yau, a Hausar masu sana’ar sayar da shanu
ma’anarta tana nan sai dai sun yi amfani da dabarar shafewa ne domin samar da
tasu kalmar, ya yin da suka shafe baƙin ‘a’, ta koma shiri maimakon ashirin.
52. kwái: Masu sana’ar sayar da shanu
a ƙasar Katagum sun samar da
wannan kalma ce ta hanyar datse gaɓar farko domin samar da lissafin kuɗi na kalmar bakwai. Anan
sun shafe ‘ba’ ne daga kalmar bakwai ta koma kwai, wadda kuma suka barta da
ma’anar ta asali sai dai sun sauya mata tsari ne.
53. támáa: Kalmar tama ita
ma lissafin kuɗi ce wadda take nufin
tamanin a Hausar masu sana’ar sayar da shanu. Amma asalin kalmar sun datseta ne
ta gaba, ta hanyar shafe ɗafin ‘nin’ dake gaban kalmar wadda take ɗauke da tama da nin ta ba
da lissafin kuɗi na tamanin a Hausa, suma
a wurinsu ma’anarta ta tamanin tana nan sai dai datseta da suka yi kawai.
54. cáasàa: Ita ma kalmar casa a Hausar
masu sana’ar sayar da shanu tana nufin casa’in, wadda suka datse ɗafin ‘in’ domin samar da
sabuwar ma’ana tasu ta daban. Asalin kalmar daman casa’in ce ta lissafin kuɗi sai suka datseta daga
casa+in ta koma casa.
55. yú: Wannan kalmar
masu sana’ar sayar da shanu sun shafe gaɓa ta farko ne, wadda asalinta daga kalmar
lissafi ce mai ɗauke da ma’anar ‘biyu’ sai suka sauyata ta
hanyar datse ‘bi’ ta koma ‘yu’ da kuma zaman ma’anar a matsayin biyu na
lissafi.
4.5 Musayar Gurbi
Sani (2007) ya bayyana
musayar gurbi da cewa “lamari ne yadda sautika biyu na kalma suke musaya
muhalli a junansu ba tare da jirkita ma’anar wannan kalma ba. Ma’ana sautin
wannan wuri ke komawa, na wancan wuri kuma ya komo nan”.
Musayar gurbi na nufin
yadda ake samun sauyawar sautika ko wani baki ba tare da ma’anar kalma ta
jirkita ba. A Hausar masu sana’ar sayar da shanu a ana samun irin wannan
lamari, sai dai wanda baya cikinsu ba lalle ya fahimci abin da suke nufi ba.
Suna ɗaukar gaɓar farko su mai da ta zuwa
gaba ko ta ƙarshe ta koma ta farko, duk
suna yi ne domin samar da ma’anar kalmomin da suke amfani da su a haƙarsu ta kasuwanci.
56. ráatá: Ita ma wannan kalma an yi
amfani da musayar gurbi ne, wadda asalinta tana ɗauke da ma’anar tara ta
lissafi sai masu sana’ar sayar da shanu suka sauya fasalinta ta hanyar ɗauko gaɓar ƙarshe ta dawo farko domin
amfanin kansu. Amma ma’anarta ta na nan a matsayin tara ta lissafin kuɗi da aka santa.
Ta+ra=tara sai ta koma
ra+ta=rata
57. rídáa: Har ila yau,
wannan kalma an yi amfani da ilmin musayar gurbi ne domin samar da ita a Hausar
masu sana’ar sayar da shanu a ƙasar Katagum wadda take nufin ɗari a wajensu. Yayin da
ma’anarta ta asali tana nufin reɗe fatar wani abu kamar dabba da sauransu.
Ɗa+ri=ɗari sai ta koma ri+ɗa=riɗa
58. dáshì: Kalmar dashi ma
musayar gurbi aka samu na gaɓar ‘shi’ ta koma ƙarshe maimakon farko da
take a asalinta a daidaitacciyar Hausa. Masu sana’ar sayar da shanu suna amfani
da wannan dabara ce domin ɓadda-bami yayin gudanar da kasuwancinsu na
yau da kullum.
Shi+da=shida sai ta koma
da+shi=dashi
59. kwástà: Kwasta ma kalmar lissafin
kuɗi ce wadda take ɗauke da ma’anar takwas a
Hausar masu sana’ar sayar da shanu. An sauya gaɓar farko ‘ta’ ta koma gaba
maimakon zamanta a farko yadda take domin samar da kalma tasu mai zaman kanta a
cikin kalmomin da su ke amfani da su a yayin gudanar da sana’arsu ta sayar da
shanu.
Ta+kwas=takwas sai ta koma
kwas+ta=takwas
60. díhù: Wannan kalma
ta ɗihu ita ma an yi amfani da
ilmin musayar gurbi domin bata ma’ana a Hausar masu sana’ar sayar da shanu.
Asalin kalmar ta lissafi ce wacce take nufin huɗu, ta yadda aka sauya gaɓar farko ta ‘hu’ ta koma
gaba sannan ta biyu ‘ɗu’ aka mata musayar ‘u’ da ‘i’.
5.1 Kammalwa
Wannan takarda ta yi bayani
ne dangane da abin da shafi kalmomin lissafi a Hausar masu sana’ar sayar da
shanu a garin Azare, takardar ta gano cewa masu sana’ar sayar da shanu a garin
Azare suna amfani da wata Hausa ta musamman, wadda suke sanar da junansu yayin
gudanar da kasuwancinsu, wadda in mutum baya cikinsu ba lalle ya fahimci me
suke nu fi ba. Sannan binciken da aka gudanar ya zama jagora ga mai nazarin
harshe musamman Hausar rukuni ɓangaren walwalar harshe.
Manazarta
Abdu, A. (1991). Hausar
‘Yan Tasha. Kundin Dirigi Na Farko. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar
Bayero, Kano.
Abubakar, D. (2023).
Nazarin Jirkitawa da Harɗantawa da Ƙirƙira a kalmomin Hausar
Mahauta a garin Ɗandume Jihar Katsina. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar
da Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.
Adamu, M.Y. (2004). The Deɓelopment of Hausa
Neologism: The Role of Urban Spaces, Takardar da aka gabatar a Taron Ƙarawa Juna Ilimi a Kan
Harshe da Adabi da Al’ada. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero,
Kano.
Aisha, U. (2008). Salon Taɗin Mata Hausawa Ma’aikatan
Gwamnati a Cikin Garin Kano. Kundin Digiri Na Biyu, Sahen Koyar da Harsunan
Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.
Asiru, A. (2000). The Use
of Slangs in Kantin Kwari Market in Kano. M.A Dissertation in the Department of
Nigerian Languages, Bayero University, Kano.
Aujara, S. (2023). Nazarin
Ma’ana a Hausa. Kano: Gidan Dabino Publishers.
Aujara, S. (2012).
Sauye-sauye Tsakanin Larabci da Hausa. Kundin Digiri na Uku. Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.
Azare, Y.M (2011). Language
Diɓersity: “A Look At The Role
of Women Towards Language Deɓelopment in Hausa Socio-linguistics Setting”
6th Hausa International Comference on Hausa Culture, Language
and Literature, BUK.
Babangida, B. (2023).
Nazarin Sauyawar Ma’anar Kalmomi a Hausar Masu Sana’ar Sayar da Shanu a Ƙasar Katagum, Jihar Bauchi.
Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano.
Bello, A. (2016). Hausa
Dialect and Distinctiɓe Feature Analysis:
Phonology, Morpology, Syntaɗ and Leɗicon. Zaria: ABU Press.
Bilkisu, U. (2000). Nazari
A Kan Hau sar Mata Matasa a Cikin Kano. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Bayero, Kano.
Bunza, A.M. (2017). Dabarun
Bincike. A Nazarin Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa. Zaria:
ABU Press Limited.
Chamo, I.Y. (2011).
Language and Identity: Hausa Language of Youth Generation in Northern Nigeria.
Warsaw: Studies of the Department of African Languages and Cultures, No. 47.
Chomsky, N. (2002).
Syntactic Structures. 2nd edition. New York.
Creswell, J.W.
(2009). Educational Reaserch: Planning, Conducting, Ƙualitatiɓe and Ƙuantatitiɓe Reaserch, 4th ed.
Boston: Seasons Publishers.
CNLS, (2006). Sabon Ƙamusu na Hausa Zuwa Turanci. Kano: Jami’ar Bayero.
Dornyei, Z. (2011). Reaserch
Methods in Applied Linguistics: Ƙuantitatiɓe, Ƙualitatiɓe and Miɗ Methodologies. New York: Oɗford University Press.
Dressler, W. U. (1987)
Studies in Language Companion Series. Amsterdam/Philadephia: John B. Publishing
Company.
Fagge U.U. (1992). Tasirin
Karin Harshe na Rukuni Wajen Ƙirƙirar Sababbin Ma’anoni a Hausa. Takardar da
aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Ilimi a Sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya. Jami’ar Bayero, Kano.
Fagge, U.U. (2002).
Zaurancen Zaurawa a Birnin Kano da Kewaye. Algaita Journal of Current Research
in Hausa Studies. Vol. II. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero, Kano.
Fagge, U.U (2004). Ire-ren
Karin Harshen Hausa na Rukuni. Kano: Benchmark Publishers.
Fatima, A. (1991). Hausar
‘Yan Tasha a Kano. Kundin Digiri na Farko.Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero, Kano.
Fisher, J.L. (1958). Social
Influence on the Choice of Linguistics Ɓariants. Word, 47, 56.
Retrieɓed on 14 October, 2019 from
www.scholarsgoogle.com.
Gandu, da Wasu
(2005). Jagoran Gudanar Da Bincike A Hausa. Kano: Zage Computer Serɓices.
Hassan, S. (2018). Hausar
Fada a Masarautar Katsina. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Haiba, (2001). Hausar ‘Yan
Acaɓa a Garin Malimfashi.
Kundin Didiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Isah, I. (2012). Salon
Maganar Fursunonin Gidan Yarin Katsina: Nazari a Kan Ma’anar Kalmomi. Kundin
Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Kabiru, M. (1993). Hausar
‘Yan Daba a Kano. Kundin Digiri na Farko. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero, Kano.
Robins, R.H. (1964).
“General Linguistics: An Introductory Surɓey”. Bloomington: Indiana University.
Laboɓ, W. (1966). The Social
Stratification of English in New York. Washington DC: Center for Applied
Linguistics.
Meyerhoff, M. (2006). Introducing
Sociolinguistics. New York: Routledge Group USA
Muhammed, D. (Ed.)
(1990). Hausa Metalanguage. Ibadan: University Press Limited.
Muhammad, A. (2016). An
Introductory Research Report Format. Germany: Omniscriptum GmbH & Co
KG.
Muhammad, A.S.
(2017). Ɓariation in the Descriptiɓe Writing Skills of the
Nigerian Undergraduates. Unpublished Doctoral Thesis. Kadah, Malaysia:
University Utara.
Maigari, B.A. (2017).
Hausar ‘Yan Kasuwar Waya: Tsarinta da Ma’anoninta. Kundin Digiri na Farko.
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Kimiyyarsu, Jami’ar Jihar Bauchi, Gaɗau.
Newman, R.M. (2012). An
English-Hausa Dictionary. Lagos: Learn African Plc.
Pross, T. (2018). Leɗical Semantics. What About
Leɗical Semantics if Syntaɗ is the only Generatiɓe Component of the Grammar?
A Case Study on Word meaning German. Springer Science+Business Media B.Ɓ.
Ramadan, A.I. (2017).
Nazarin Hausar ‘Yan Gwanjo a Kasuwar Ƙofar Wambai Kano. Kundin
Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Shafa’atu, U.M (2012).
Hausar ‘Yan Sanda a Wasu Barikokinsu a Kano. Kundin Digiri na Biyu. Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Taɓokoli, H. (2012). A
Dictionary of Reaserch Methodology and Statistics in Applied Linguistics.
Iran: Rabmana Publishers.
Wurma A.G. (2002).
Semantics Changes Occuring in Hausa Language. In Algaita Journal of Current
Research in Hausa Studies. Vol.2. No.1.
Yakasai, M.G. (2004).
Yanayin Karin Harshen Sojoji a Barikoki: Nazari a kan Barikokin Bakaɓo da na Janguza. Kundin
Digiri na Biyu Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Yakasai, S.A. (2012). Jagoran
Ilmin Walwalar Harshe. Sokoto: Garkuwa Media Serɓices Limited.
Yahaya, A. (2012). Hausar
Masu Ƙwallon Ƙafa a Garin Katsina. Kundin
Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Zage, U. (2002). Karin
Harshen Tukari Mazauna Ƙasashen Larabawa. Kundin Digiri na Farko.
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.