Citation: Bashir Aliyu TSAFE (2025). Gaisuwa Da Roƙon Iri: Nazarin Roƙo A Cikin Godiya Daga Bakin Wasu Mawaƙan Baka Na Hausa. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 13, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
GAISUWA DA ROƘON IRI: NAZARIN ROƘO A CIKIN GODIYA DAGA BAKIN
WASU MAWAƘAN BAKA NA HAUSA
NA
BASHIR ALIYU TSAFE
Tsakure
Makaɗa da mawaƙan baka na Hausa na amfani
da wasu irin dabaru da kalmomi masu ɗaukar hankali don ƙoƙarin samun wani abu daga waɗanda suka yi wa waƙar. Manufar wannan takardar
ita ce bayyana irin yadda mawaƙa ke yin godiya da wata
kyauta da aka yi masu daga bisani kuma su bijiro da wata buƙata, wannan dabarar suna
yin ta ne daidai da faɗar Allah cewa idan kuka yi
godiya zan ƙara muku. A ƙoƙarin gudanar da wannan bincike an bibiyi wasu bayanai da aka samu
a cikin wasu littafai da kuma sauran takardun ililmi da aka samu. Haka kuma an
saurari wasu daga cikin waƙoƙin baka na Hausa domin ganin aikin ya inganta. Har ila yau
an ɗora wannan aikin a kan ra’in awon baka na Hausa
saboda la’akari da aka yi cewa, abubuwan da aka kula da su a kan wannan aikin
sun haɗa da layukan ɗan waƙa da ƙulli da ƙari na nazarin waƙar baka Bahaushiya ta
hanyar duba hawa da saukar amsa amo ƙari da amfani da sassan
adabin baka da sauransu kamar yadda Gusau (2015. Shafi, sh 34-35) ya yi nuni.
Ire-iren waɗannan masana na cikin gida suka aiwatar mai
nasaba da wannan rai sun haɗa da Abdulƙadir (1975) da Ibraahim (1983) da Bichi (1975) da Gusau (1983) da
1988 da 2014). Wannan ra’i yana ganin cewa waƙoƙi rumbu ne na hikimomi waɗanda ake amfani da su yau da kullum, ake kuma bayyan irin
al’amurran da suke faruwa a cikin hikima tare da danganta su cikin hira,
daga ƙarshe suke rikiɗewa su koma ɗa na waƙa.
1.0 Gabatarwa
Waƙa tana da matuƙar muhimmanci a rayuwar
Hausawa kuma wani rukuni ne na adabin baka na Hausa. Don haka a wajen bayyana
ma’anar waƙa sai a yi ta yin
tuntuɓe. Mawaƙan baka na Hausa mutane ne
waɗanda ke da wata irin baiwa
da hikima da fasaha da basira wajen sassarƙa maganganun azanci a cikin
waƙoƙinsu kuma waƙar ta tafi, saƙon ya je inda ake so. Mawaƙan baka na Hausa na amfani
da hikima da fasahar zance, wanda hakan yake ba su damar yin amfani da dabaru
daban-daban wajen isar da saƙo.
Manufar wannan takarda ita
ce; Gano yadda mawaƙan baka na Hausa ke sarrafa kalmomi domin samun buƙatarbsa da sanin yadda suke
dabarar yin godiya kafin roƙo da kuma samar da waƙoƙin Hausa da ke ɗauke da irin wannan roƙon.
Haka kuma, a wannan maƙalar za a fito da wasu
abubuwa waɗanda mawaƙan baka na Hausa suke yi
cikin azanci su roƙi wani abu a cikin godiya, wato sun yi godiya da wata
kyauta da aka ba su, sai su biyo da roƙo. A wannan aiki za a fito da wasu muhimman abubuwa waɗanda mawaƙan baka na Hausa suke roƙon al’umma bayan nuna godiya a kan kyautar da aka yi
musu.
Haka ma za a bayyana ma’anar waƙa da kuma roƙo sai kuma abubuwan da suke
roƙo, sai misalai daga cikin
waƙoƙin daban-daban, daga ƙarshe sai sakamakon bincike
da naɗewa sai manazarta.
1.1 Fashin Baƙin Tubalan Take
A nan zan fito da wasu tubalan ne da taken ya ƙunsa da kuma bayar da
ma’anarsu a taƙaice domin sanin inda
aikin ya dosa, da kuma taimakawa
wajen taƙaituwar aikin a cure wuri
guda.
1.1.1 Ma’anar Godiya
Kalmar godiya kalma ce
wadda masana da manazarta suka tofa albarkacin bakinsu game da ita, kaɗan daga cikin irin waɗannan masana akwai:
Bunguɗu, (2023, sh 6), ya bayyana kalmar
godiya da cewa:
Godiya tana nufin nuna jin
daɗi da ake furta wasu kalmomi
a sakamakon wata kyauta ko wani aikin alheri da aka yi wa mutum.
Haka ma CNHN (2006, Shafi,169) an bayyana
ma’anar godiya da cewa:
‘’Yabawa
ko nuna murna saboda kyakkyawan abu da aka yi’’.
A wata tattaunawa da na yi da Malam Ɗahiru a gidansa a ranar
Asabar 12/8/2025 da misalin ƙarfe biyar na yamma, ya
yi bayani a kan abin da ya fahimta da godiya cewa:
“Nuna
farin ciki a zahiri a kan wani taimakon da aka yi wa wani.
Da wannan ana iya cewa:
Godiya wata hanya ce da mutum ke amfani da ita
don nuna jin daɗinsa ga wani abu da aka ba shi ko aka yi mashi
albishir.
1.1.2 Ma’anar Roƙo
Kalmar roƙo kalma ce wadda masana da
manazarta suka tofa albarkacin bakinsu a kan fito da ma’anarta. Daga cikin irin waɗannan masana akwai:
Bello S.R. (1982, shafi,7),
ya bayyana kalmar roƙo da cewa, “Roƙo yana nufin fasaha da hikimomin rayuwar
al’umma ta amfani da harshe.
Yahaya (1985) ya bayyana
cewa, “Roƙo magana ce ‘yar gajeruwa
da akan tsara cikin azanci da nuna balagar zance da ke zuwa jimla –jimla.
Dunfawa, (2004, shafi,17),
ya kalli raƙo kamar haka, “Roƙo wani ɓangare ne na ma’abanci,
wanda yake ɓangare ne na adabin baka.
Bunguɗu, (2019, shafi:5), cewa ya yi, “Roƙo shi ne neman wani abu daga wani mutum domin
biyan buƙata.
Dangane da waɗannan mabambanta ra’ayoyin
da masana suka bayar ana iya cewa, “Roƙo wata ɗabi’a ce da wasu ke yi da
nufin samun wani abu daga wajen al’umma”.
1.1.3 Ma’anar Waƙar Baka
Masana da dama sun yi
iya ƙoƙari don ganin cewar an
fitar da ma’ana ko abin da ake kira waƙar baka, misali a ra’ayin Gusau, (1993,
shXII), yana cewa, ‘’Waƙa Magana ce ta fasaha a cure wuri ɗaya a cikin tsari na
musamman.’’
Yahya, (1997, shafi, 3). Ya
bayar da ma’anar waƙa da cewa, “Magana ce da ake shisshirya kalmominta
cikin azanci ta yadda wajen.
A wata riwayar ta Gusau
(2003, shafi:XIII) cewa ya yi, Waƙar baka wani zance ne shiryayye cikin hikima
da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da
daidaituwa a rere cikin murya da amsa-amo kari da kiɗa da amshi. Daidaituwa da
aka yi wa layukan waƙa ya sa ba ta zuwa a shimfiɗe ko kuma ta zo gaba ɗaya.
Haka ma a wani aiki na
Gusau, (2011) ya bayar da ma’anar waƙar baka da cewa:
Waƙar baka fage ce wadda ake
shirya maganganu na hikima, da ake aiwatarwa a rera cikin rauji tsararre, waɗanda za su zaburar da
al’umma tare da kuma hankaltar da su dangane da tafiyar da rayuwa da za su ba
damar a cimma ganga mai inganci, waƙa bisa jimla, takan zama fitila wadda take
haskaka rayuwar jama’a. Kuma take kare rayuwar al’umma daga sallacewa.
Tahir (2011), cewa ya yi,
‘’Waƙar baka wani katafaren
tsauni ne daga cikin tsaunukan adabi da yake ɗauke da hanyoyin ci gaban
al’umma, ta fuskar al’adu da siyasa da addini da zumunci da karamci ko wani
canji da ke iya samun wannan al’umma a yau. Har ila yau wannan fage na waƙar baka fage ne da ke
tafiya da kusan kowane irin abu da ake nema dangane da al’ummar Hausawa’’.
Ɗangambo (1982, shafi, 6), ya kalli waƙa da cewa:
‘’Waƙa wani furuci (lafazi ko saƙo) ne cikin azanci da ake
aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaita kalmomi cikin wani tsari ko ƙa’ida da kuma yin amfani da
dabaru ko saƙon armashi’’.
Da waɗannan bayanai na masana ana
iya cewa:
‘’Waƙa wata dabara ce ta fitar da wasu kalmomi a
kuma saita su, a jera su, su kuma tafi daidai da fahimtar masu sauraro”.
2.1 Dalilan Da Kan Sanya Mawaƙa Yin Godiya
Akwai wasu dalilai da ke sa mawaƙa na yin godiya dangane da
abin da aka ba su domin su bayyana jin daɗi, daga cikin dalilan akwai:
· Nuna jin daɗi da kyautar da aka yi musu. Mawaƙa kan nuna jin daɗi ƙarara wato a fili ko kuma a
fakaice domin bayyana farin cikinsu, dangane da kyautar da aka ba su.
· Maimaita abin da aka ba su.
Yawan faɗin kyautar da wani ya ba su
a duk inda za su yi waƙa.
· Fatar samun wata kyautar
ko ƙarin wata kyautar da aka ba
su.
· Domin waƙarsu ta tafi daidai kuma ta
karɓu ga jama’a.
2.2 Wasu Dalilan Da Kan Sa Mawaƙa Roƙo
Akwai wasu dalilai da kan sanya mawaƙa roƙo a wajen al’umma, waɗanda suka haɗa da:
v Rashin mallakar abin da
suke roƙo a wajen al’umma. Wannan
na sanya mawaƙan baka roƙon al’umma, dalilin rashin
mallakar abin da suka roƙa, za su roƙi abin da ba su da shi, ko
kuma suna da shi amma suna neman ƙari.
v Ƙari a kan abin da suke da
shi. Sukan nemi a ba su wani abu, misali mota ko babur ko abinci ko da kuwa suna da abinci amma
suna neman ƙari ne.
v Ƙarin tallata alherin wanda
aka roƙa. Mawaƙan baka kan ƙara tallata mutum idan ya
yi masu alheri, sai su ƙara tallata abin da ya ba su.
v Dushe hasken wanda ba ya
alheri. Mawaƙa na da wata aƙida ko al’ada ta ƙoƙarin dushe hasken wanda ba ya
alheri a cikin waƙa. Hakan kan sa ake yi masu
kyauta wani lokaci ko ba a yi niya ba.
2.3 Roƙo a Cikin Godiya
Makaɗan baka na Hausa mutane ne
da Allah ya hore masu wata baiwa iri daban-daban wajen sassarƙa zance cikin hikima.
Wannan ya sa suke sarƙa manufa cikin wata manufar domin isar da wani saƙo. Hakan shi ya sa suke
jefa roƙo a cikin godiya idan suna
gudanar da waƙoƙin su. Makaɗa da dama suna amfani da
irin wannan hikima a cikin waƙoƙinsu domin sun san cewa dukkanin wanda aka yi
wa godiya a kan wata kyauta da ya yi idan aka bijiro masa da wata buƙata zai yi saboda jin daɗin godiyar da aka yi masa.
Ga misalai daga wasu ɗiyan waƙoƙi na wasu makaɗa daban-daban kamar haka:
misali a waƙar makaɗa Amali Sububu a waƙar da ya yi wa sarkin noman
garin Magaji, inda yake cewa:
Jagora : Amali kiɗi babu wanda ban yi ba,
: Na ci awaki da raguna da dawaki,
: Am ba mu dukiyar raƙumma,
: Am ba mu had da shanu,
: Saura mota a hwara sai man,
: Komi kab ba ni duk cikin ƙari ne,
Y/Amshi : Komi kab ba ni
duk cikin ƙari ne
Kay yi man
G/Waƙa : Da hanzarin noma nis san shi,
: Taho gida rana ta hwaɗi,
: Mu gaida Kartau mai gulbin hura.
(Amali
Sububu: waƙar sarkin noman Garin Magaji)
A nan makaɗa Amali Sububu yana godiya
ne a kan irin abubuwa da aka ba shi wato irin
kyautar da sarkin noma ya ba shi, yana godiya har yana zayyano abubuwan da aka ba shi, kamar awaki da
riguna da shanu, bayan ya nuna jin daɗinsa sai kuma ya biyo da
roƙo, yana
roƙon cewa ya kamata a ba shi
mota, tun da dai an ba shi raƙumma da dukiya da shanu, ya gode amma kuma yana buƙatar mota domin ya samu
abin hawa da zirga-zirga.
Haka ma a waƙar makaɗa Maidaji Sabon Birni wadda
ya yi wa Inna a wani ɗan waƙar ya yi amfani da irin wannan dabarar inda
yake cewa:
Jagora : Na za ka in yi
godiyar riga inda Inna,
Y/Amshi : To in za ki ba ni wata
amma kar ki fasa,
G/Waƙa : Kina da martabar jan
gwarzo da Yumfa,
: Giwa ta Bawa tausa gaba inda kis sa.
Jagora : Bara da niz zo kiɗi ga Inna
Y/Amshi : Ta ba ni kore,
: Koren nan da tay yi man kau ya
zo da sa’a,
: Bara da za ni Makkah can nis
sas sai ga hanya,
G/Waƙa : Kina da martabar jan
gwarzo da Yumfa,
: Giwa ta bawa tausa gaba inda
kis sa
(Maidaji Sabon Birni: waƙar Inna)
A nan makaɗa Maidaji ya nuna godiya
da irin abubuwan da Inna ta yi masa na alheri inda ya faɗi cewa ya zo ne domin ya yi godiyar riga da aka ba shi, wanda ya
cigaba da bayanin cewa bara da za shi Makkah ta ba shi kore wanda ya sayar a
hanya kuma ya ji daɗI sosai domin ya yi amfani da kuɗin ya ƙara guziri to amma ya faɗa cewar kar fa ta ji ya sayar ta hana shi wata rigar. Sai ya nuna
mata cewar yana da buƙata idan za a ƙara masa wata.
A waƙar Wazirin Anka wadda makaɗa Ƙwazo Bagega ya yi, ga abin da yake cewa a
wani ɗan waƙar:
Jagora: :Kana
gaba da maza Waziri Allah yai ma rabo,
Y/Amshi: :Kana
gaba da maza Waziri Allah yai ma rabo,
Jagora: :Ni
na ga wane ya kai kainai
Y/Amshi :
Wurin da Allah bai kai shi ba
Jagora: :Sai
godiya Wazirin Anka
Y/Amshi :Inuwa
Allah yai mai rabo
Jagora: :Ni
inai maka koke
Y/Amshi :Waziri
ni ban zo Makkah ba
Jagora: :Ni
inai maka roƙo
Y/Amshi :Waziri
ni ban zo Makkah ba.
G/Waƙa :Kana gaba da maza Waziri Allah yai ma rabo.
(Ƙwazo Bagega: waƙar Inuwa Wazirin Anka)
A waɗanan ɗiya na waƙar za a ga cewa, mawaƙin ya yi godiya ne a kan irin abubuwan da Wazirin Anka ke yi masa
na alheri, a cikin waƙar ya ambaci cewar an ba shi mashin ya hau ya je
gona an kuma ba shi abinci an ba shi kuɗi an yi mashi abubuwan
alheri da yawa, duka dai ya lissafo abubuwan da Inuwa Wazirin Anka ya yi masha,
amma yanzu koken da yake gare shi a ba shi kujerar Makkah. Ya ambata cewa ita
kawai ce abin da ya rage Inuwa ya ba shi. A nan mawaƙin ya yi amfani da dabarar nan da suke yi ta godiya sannan a
bijiro da roƙo.
Haka ma a wata waƙar da Kassu ya yi wa
‘yan Jabanda a wani wuri na ɗan waƙan ya yi amfani da irin wannan dabara ta godiya sannan roƙo ya biyo baya, Ga abin da yake cewa:
Jagora :Godiya
madalla,
:Muhammadu
Kassu ya gode ma,
:Allah ya
hi ni yabawa,
:Kai ma
Duna na gode ma,
:Sai
Kassu Labbo na Gandau,
:In nai
gangara sai sauka,
:Ciki ai
ba ɗumi nika so ba,
:Ɗumi guda nika so,
:Sai mai
ce mani Kassu ya ka amsa,
:Ku kawo,
amshi ba ta kashe ni.
(Kassu
Zurmi: waƙar ‘yan Jabanda)
A wannan ɗiyan makaɗa Kassu na nuna godiyarsa ne a kan abubuwan da sarki ya yi masa na
alheri, kuma ya jero wasu na tare da sarki ya yi masu godiya daga baya kuma ya
biyo da roƙo cewa ba ya buƙatar a dame shi da yawan
surutu shi dai abin da yake buƙata a ce Kassu zo ka amsa. Haka ma a wata waƙa ta Nadada Sabon Birni wadda ya yi wa Sarki Salihu, inda yake
cewa:
Jagora : Sarki ya ba mu Riguna,
‘Y/Amshi : Kuma ya ba mu Dawaki,
Jagora : Saura nai ya ba ni
jikka in sai gero,
G/Waƙa : Jikan Jari Ɗan Hassan Jikan Jangwarzo,
:Ko
way jaka Gardama kunya ta yaj ja.
(Nadada
Sabon Birni: waƙar Sarki Salihu)
Idan aka dubi wannan ɗan waƙa za a ga cewa, makaɗa Nadada Sabon Birni yana
gaisuwa ne da roƙon iri ga uban gidansa.
Watau yana godiya tare da miƙa wani ƙoƙon bara, domin tun farko ya
nuna godiyar sa ga sarki na irin riguna da Dawaki da ya ba shi, daga nan kuma
sai ya miƙa ƙoƙon bara a taƙaice na abin da ya rage
sarki ya ba shi ita ce yana son a ba shi kyautar jikkar kuɗi ya sayo gero. A
cikin wata waƙar da ya yi wa Sarki Salihu
ya sake yin amfani da wannan hikima ta cusa roƙo a cikin godiya, inda yake
cewa:
Jagora : In an koma jan
wani taro,
‘Y/Amshi : Ko ni mai kiɗi sai na zo,
: Amma ban zuwa huntuna,
: Sai an koma ban wata riga,
: Sai an koma ban wani doki,
Jagora : Sarki ba ni rigab
biddah,
‘Y/Amshi : In don wagga nan ta
tsuhwa,
: Sake min iri Ɗan Mamman.
(Nadada
Sabon Birni::waƙar Sarki Salihu)
Idan aka dubi wannan ɗan waƙa za a ga cewa, makaɗa Nadada yana nuna cewa taron da sarki ya tafi wanda Gwamna
ya kira a Sakkwato, makaɗa Nadada bai samu zuwa ba, amma dai ya yi wa
sarki rakiya tare da yaransa. Don haka sai ya nuna cewa, idan aka sake kiran
wani taro sai ya tafi, sai dai da sharaɗin cewa sai an sake ba shi wata riga da wani
doki da rigar Biddah, domin rigunan da aka ba shi sun tsufa, wannan dai ya nuna
cewa an taɓa ba shi, don haka ya yi
godiya kuma yana roƙon a ƙara ba shi wata, domin waccan ta tsufa. Har
wa yau a cikin wata waƙar ta makaɗa Nadada ta Sarkin Gobir Salihu ya yi amfani
da wannan hikima, inda yake cewa:
Jagora : Sarki ya riƙe ni ya ɗaukan
lamba ɗai,
‘Y/Amshi : Ya ɗaukemu don kiɗi ba don noma ba,
Jagora : To sarki zamaninka mi
ab ba mu samu ba,
‘Y/Amshi : Du wada munka so
mukai ba don ƙarhi ba,
Jagora : To babu abin da nir
rasa,
‘Y/Amshi : Ban rasa komi ba,
: Sa ƙarad da niy yi ma ab
bata ƙare ba,
: Matan nan da nis saki ban
canzo wata ba,
: Kuma ɗakin da tab bari na nan
kango nai,
Jagora : Ko matan da ag gidan
sun shiga
watsewa,
‘Y/Amshi : To daɗa na san zuwa gabas ya
kusa kamawa,
: Ba ni zama ƙasag ga ba ni da matan
aure.
G/Waƙa : Ɗan Mamman ubangijin barga
as Sarki,
: Jikan Sanda Ɗan Sabon Birni.
(Nadada
Sabon Birni: waƙar Sarkin Gobir Salihu)
Makaɗa ya yi godiya sosai ga
irin kulawar da sarki ke yi musu, ya riƙe shi lamba ɗaya, babu wanda da ke da fada kamar shi, ya faɗi cewa a zamanin sarki babu
abin da ba su samu ba ya shaida wa sarki
cewa ya fa saki matar shi kenan uwar gidan sauran kuma waɗanda ke cikin gida sun fara watsewa kuma ga sarki zai je makkah
don haka yana roƙon sarki cewa kar ya wuce sai ya auro mashi wata
mata ko kuma wadda ya saki a dawo da ita.
3.1 Sakamakon Bincike
Wannan bincke an yi nazarin wasu abubuwa ne waɗanda mawaƙan baka suke yi domin nuna godiya ga irin
abubuwan da masu gidansu suka yi musu, sannan kuma su roƙi wata buƙata da suke so a yi musu. An ga irin waɗannan ga misalan da suka gabata. Wannan ya ƙara tabbatar da cewa godiya sannan a biyo da roƙo wata hanya ce mai sauƙi da mawaƙa ke amfani da ita domin su samar wa kansu abin kalaci. Kuma da
yawa suna samun abin da suke so kai tsaye da kuma kaikaice idan an ba su sai su
yi godiya idan kuma ba a ba su ba wani lokaci su yi zambo. An gano cewa mawaƙan kan miƙa ƙoƙon barar su ne bayan sun yi godiya.
4.1 Kammalawa
Wannan takarda ta yi nazarin wasu daga cikin
halaye da mawaƙa ke yi a wajen al’umma ta amfani da fasaha da kuma ƙwarewar da Allah ya ba su wajen sarrafa harshe da sarrafa kalmomi
domin ganin daɓensu ya ji makuba. Haka kuma takardar ta yi
bayanin wasu dalilai da kan sa mawaƙa ke yin godiya da kuma
abubuwan da suka fi roƙo a wajen al’umma, sannan sai aka biyo baya da
bayanin misalan wasu waƙoƙi da suka yi godiya da
roƙon irin. Bayan wannan sai sakamakon bincike da kammalawa sai
manazartar binciken.
Manazarta
Abba, M.D. Zulyadaini, B. (2000). Nazari
Kan Waƙar Baka ta Hausa. Gaskiya Cooperation Limited.
Bunguɗu, H.U. (2015). Bara da Wasu Waƙoƙin bara a ƙasar Hausa, ƊKundin digiri na ukuɗ Jami’ar Ɗanfodiyo.
C.N.H.N. (2006) Kamusun Hausa.
Jami’ar Bayero.
Dumfawa, A.A. (2002). Waƙa a Tunanin Yara, Ɗkundin digiri na ukuɗ. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Dumfawa, A.A. (1995). Zuga a Waƙoƙin Fada. Algaita Journal of Current Research in Hausa
Studies. Department of Nigerian Languages Series 4. Bayero University Kano.
Ɗangambo, A. (1973). Shata da Waƙoƙinsa, Ɗkundin digiri na ɗayaɗ sashen Hausa, Jami’ar
Bayero.
Ɗangambo, A. (2008). Rabe–Raben Adabin
Hausa: (Sabon Tsari). Amana Publishers.
Ɗangambo, A. (2011). Waƙa da Rawar da Take Takawa a Rayuwar Hausawa. Maƙala Taron Bikin Ranar Al’adu na Hausawa da
Fulani, Katsina, F.C.E.
Garba, C.Y. (1991). Sana’o’in Gargajiya
a Ƙasar Hausa. Spectrum Books Limited.
Gusau, S.M. (1996). Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Fisba Media Services.
Gusau, S.M. (2002). Salihu Jankiɗi Sarkin Taushi. Baraka Publishers.
Gusau, S.M. (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Benchmark Publshers.
Gusau, S.M. (2008). Waƙoƙin Baka a ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu
da Sigoginsu. Benchmark Publishers.
Gusau, S.M. (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun
Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa. Century Research and Publishing.
Gusau, S.M. (2011). Adabin Hausa a Sauƙaƙe, Kano Century
Research and Pubishing.
Gusau, S.M. (2015). Mazhabobin Ra’i da
Tarke a Adabi da Al’adun Hausa. Century Research and Publishing
Limited.
Sarɓi, S.A. (2007). Nazarin
Waƙen Hausa. Samarib publishers.
Yahya, A.B (1997). Jigon Nazarin Waƙa. Fisbas, media services.
Yahya, A.B (1999). Salo Asirin Waƙa. Fisbas, media Services.
Yahya, A.B (2010). WaƘa: Ma’ana da ɗabi’a da Ginshiƙi, Maƙala da aka gabatar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari Sakkwato.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.