Citation: Gwandu, B. A. (2025). “Nazarin Hausar Malaman Zaure a Jihar Sakkwato da Kabi.” in Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 03, No. 02, Pp. 138 – 143. www.doi.org/10.36349/djhs.2025.v03i02.017.
NAZARIN HAUSAR
MALAMAN ZAURE A JIHAR SAKKWATO DA KABI
Na
Buhari Aiku Gwandu
PhD Candidate,
Department of Nigerian Languages, Sokoto State University, Sokoto
Tsakure:
Masu azancin magana kan ce
‘‘Kowane tsuntsu; kukan gidansu yake yi’’. Malaman zaure mutane ne waɗanda suke koyar da al’umma
ilimin addinin Musulunci a fannoni daban-daban, domin su fahimci addini kamar
yadda ya kamata, musamman karatun Alƙur’ani
maigirma da waɗansu
ilmuka. Manufar wannan binciken ita ce nazartar kalmomi da yankin jumloli da
kuma jumlolin da malaman zaure suke amfani da su a wajen hulɗa da mu’amalarsu da ɗalibai da kuma al’umma.
Saboda maganganunsu da zantukansu na sadarwa sun bambanta da na gama-gari. An ɗora binciken bisa ra’in
Greenberg (1962) da yake cewa ‘‘Hulɗa
tsakanin harsuna, yana nufin tasirin harsuna a kan juna’’. Yakasai (2005) ya
tabbatar da wannan ra’in, a inda ya ƙara da cewa ‘‘akwai tasiri da hulɗa,
kana akwai tasiri babu hulɗa
kaitsaye’’. An yi amfani da hanyoyin tattara bayanai manya da ƙanana.
An yi amfani da hanyar zuwa da kai ya fi aike, wato ziyara a wasu Zaurukan
karatu da majalisan karatu da kuma sauraren kafafen zamani na sada zumunta. Waɗanda suka haɗa da karatukan da aka naɗa da memori (memory). Sakamakon bincike ya nuna akwai Hausar rukuni
ta malaman zaure ta kalma da yankin jumla da jumla. Misali a kalma, yankin jumla da kuma jumla. Da wannan ne
Hausawa kan ce ‘‘A san mutum a san sana’arsa ko Kowa bar gida, gida ya bar
shi”.
Gabatarwa
Karin harshe wani ɓangare ne na nazarin ilimin walwalar harshe da ya shafi
kowane harshe tare da rukunnan jama’arsa a duniya baki-ɗayanta (Abbas, 2017).
Malaman zaure su
ne masu mazauni a cikin zaurukan ɗakin bunu da shigifar laka da
kudandami da bukka da rumfa da fili fallau suna ba da ilimi (Abubakar, 2007).
Wannan ne ya sa Hausawa ke yi musu kirari da cewa ‘‘Malamai magada Annabawa da
Malamai fadawan Allah da Malamai na kusa ga Allah da Malamai tushen tarbiyya da
kuma Malamai uwayen al’umma’’. Girmansu da ƙimarsu da darajarsu da kwarjininsu da ɗaukakarsu da gogewarsu da sanin yakamatansu da kuma
mu’amalarsu ya haifar dazamansu iyaye da jagororin al’umma.
Ma’anar Harshe
Harshe na nufin
hanyar magana tsakanin al’umma iri ɗaya (CNHN, 2006).
Harshe shi ne
dillalin zuci, mai bayyana abin da zuciya take so ko ƙi. Irin abubuwan da harshe yakan
bayyana a sarari don a fahimci mutum, shi ake kira magana ko zance (Galadanci,
1992).
Da an ambaci
amfanin harshe, babban abin da zai fara faɗowa a zuciyarmu shi ne ana
amfani da shi (harshe) wajen sadarwa. Harshe ne muke cuɗanya da juna mu gane ra’ayoyin juna, mu kuma yi musayar waɗansu ra’ayoyi’’(Yunus, 2016).
Harshe shi ne
babbar hanyar sadarwa ta ɗan Adam, ta amfani da sautin
murya mai ma’ana kuma yana tafiya ne tare da waɗansu
dokoki na musamman.
Hausar Rukuni
Hausar rukuni keɓaɓɓun kalmomi da jumloli ne da wasu
nau’in mutane masu tarayya ga wani aiki ko sana’a ko kuma mu’amala da suka zaɓa ma kansu don sauƙaƙa sadarwa a tsakaninsu da juna.
Rukunin jama’a ya ƙunshi ɗaiɗaikun mutane waɗanda suka yi tarayya ta fuskar zamantakewa ko tattalin
arzikki (Yakasai, 2012).
Hausar rukuni,
wani tsararren karin harshe ne da wasu ƙungiyoyin
mutane kan ƙirƙira domin samun mafita ta
sadarwa a tsakaninsu ko shayar da kansu ƙishin
magana da harshensu, ba tare da wani wanda ba ɗan
ƙungiyar ba ya fahimci abin da
suke faɗa ba (Umar, 2019).
A taƙaice Hausar rukuni, wasu
shiryayyun kalmomi da jumloli da yankin jumloli ne da aka shirya domin waƙiltar wata ɓoyayyiyar magana ko zancen Hausa wadda ta saɓa ma maganar sarari. Hausar rukuni, Hausa ce da ke ƙunshe da kalmomin fannu waɗanda suka shafi wasu ɗaiɗaikun
mutane da suka yi tarayya a wajen sana’arsu ko matsayi ko aikace-aikacensu.
Hausar Malaman
Zaure
Hausar Malaman
zaure ita ce yin amfani da wasu kalmomi ko yankin jumloli ko jumloli na fannu
da malaman zaure ke tu’ammali da su a wajen sadarwarsu.
Malaman zaure ƙwararru ne a wajen zaɓen kalmomi ko jumla da yankin jumla don faɗaɗa ma’ana da samar da sabuwar
ma’ana bayan ta asali, (Abubakar, 2007).
Hausawa na yi wa
malamai kirari da cewa, ‘‘Malamai magada Annabawa, da Malamai fadawan Allah, da
Malamai makusanta ga Allah, da Malamai ‘yan gatan Allah, Abubakar.
Hausar zaure,
Hausa ce ta malamai da almajirai da suke karatu a zaure a gargajiyance, wadda
ta haɗa nau’o’in mutane da suka fito
lunguna da saƙunan ƙasar Hausa.
Hausar zaure,
Hausa ce mai ban mamaki da al’ajabi da yake da sakaye da kinaya a cikinta.
Hausar zaure, Hausa ce mai tafiya da ingausar harsuna, musamman tasirin harshen
Larabci.
Hausar Malaman
Zaure ta Sigar Kalma
|
|
Kalma |
Asalin Kalma da
Ma’anarta |
Sabuwar Ma’ana
ko Fɗaɗa Ma’ana |
Tsokaci |
|
1 |
Hwarga
|
Asalin kalmar
‘hwarga’ Bahaushiyar kalma ce wadda ke nufin faɗaka ko kora ko kuma lura. |
Malaman zaure
na amfani da ita a wajen yi wa ɗalibai ko almajirai faɗa kan a mayar da hankali kan abin da
aka yi na kratu, ko kuma wane ya yi zarra ya tsere ma abokin karatu. |
Wannan Kalmar
daga hwarga, hwargaga, hwargage. Tana nufin
Ankara ko tunawa ko lura, ko kuma ba da tsoro ko kora da makamantansu. |
|
2 |
Fàariyyàa ko hwàariyyàa
|
Kalmar ‘fariyya’ Balarabiyar kalma ce da aka yi wa kwaskwarima aka ɗebe wani a cikinta. Tana nufin nuna isa ko iko ko kuri ko kuma cika-gaba
ga wani abu. |
A makarantar zaure, idan an ce wane akwai fariyya gare shi, to kowa na
gudunsa a wajen ƙulla mu’amala da shi, saboda kaucewa wannan halin ko ɗabi’arsa da ke da mummunan zargi. |
Asalin wannan kalma Balarabiyar kalma ce. Tana nuna bugun gaba da wata
ni’ima da Allah ya yi ma mutum ga wanda ba ya da wannan ni’imar ko wannan
abin. |
|
3 |
Wanca’aninka ko wancaananka
|
Kalmar ‘wanca’aninka’ Bahaushiya ce, kuma tana nufin
waɗancan ko waɗannan mutane. |
Malaman zaure na amfani da wanca’aninka a madadin nuni ga wani abu ko
kuma gare ka aiki ya rage na karatun da aka yi ma. |
Wanca’aninka kalma ce tsohuwa da Malaman zaure ke amfani da ita a
lokacin karatu musamman a zaure. Wasu na kiranta wanca’aninka wasu kuma
wanca’ananka. Dukansu ma’ana ɗaya gare su. |
|
4 |
Gishirii |
Gishiri wanda ake amfani da shi wajen dafa abinci. |
Wannan kalma tana nufin mutum mai ilimin nahawu na Larabci |
Ita wannan kalma ta gishiri tana nuna cewa duk malamin da aka ce ma ba
ya da gishiri, wato yana ƙwaɓa a cikin karatunsa. |
|
5 |
Googaa |
Haɗa wani abu da wani abu a
murza ko su zoji juna |
Kirari ne ga duk malamin da ya shahara a wani fannin tsibbu ko fannoni
da yawa. Ko kuma ta aikace-aikacen ɗibbu
(tsibbo). |
Kalmar ‘goga’ kalmace mai nuna aikatau na umurni a asalinta. Amma kuma
tana ɗaukar suna ga malaman
zaure da suka yi fice ko ɗaukaka a tsibbace na ɗibbu. |
|
6 |
Dafà’ii ko Dahwa’ii |
Kalmar ‘dafa’i’ tana nufin ture abu ko kare abu |
A Hausar malaman zaure tana nufin maganin tsari na kariyar kai daga maƙiya. |
Asalin kalmar ‘daf’u’ Balarabiyar kalma ce, amma Hausawa suka Hausance
ta da ma’anarta, saboda tasirin harshen Larabci ga malaman zaure. |
|
7 |
Saƙandamii |
ƙuƙumi da ake sa wa ga mahaukaci ko kuma dabba
mai faɗa. |
Saƙandami Bahaushiyar kalma ce da malaman zaure ke faɗaɗa ma’anarta. |
Kalmar ‘saƙandami’ suna ne na wani abu. Ana amfani da shi a wajen ɗaurin mutum mahaukaci ko dabbar da ta
bijire. |
|
8 |
Buuɗejii |
Bahaushiyar kalma ce, kuma tana nufin mutum ƙato. |
A fassarar malaman zaure da suka faɗaɗa ma’anarta, tana nufin
abin da aka bauta ma kamar gunki da abin da ya yi kama da haka. |
Kalmar ‘buɗeji’ Bahaushiyar kalma ce
da ta samo asali cikin harshen Hausa, kuma tana nufin ƙaton mutum da bai da amfanin komai, wato bai
iya hanawa ko sawa. Shi buɗeji bai iya amfanar da
kanshi ballantana waninsa. |
|
9 |
Kutumaa |
Asalin Kalmar ‘kutuma’ gamin-gambiza ce tsakanin harshen Larabci da na
Hausa. Tana nufin kai ma haka |
Kalmar ‘ kutuma’ wani ɗan ƙaramin zagi ko ɓaci ne da malaman zaure ke yi ga wanda ya ɓata musu ko hasala su game da wani abu. |
A duk lokacin da malamin zaure ya faɗi ko ambaci wannan kalma an fusatar da shi ainu. Ko kuma da za ran an
ji ya furta wannan kalma hankalin waɗanda yake wa
faɗa zai dawo nan take su
aikata abin da ake son su yi ko su bari. |
|
10 |
Kiigoo |
Kalmar ‘kogo’ kalma ce da ta samo asali daga harshen Hausa. Kuma suna
ce da ake kiran mutum namiji kuma malami. |
Kigo suna ne na malamin da ya
shahara a wani fannin ilimi daga cikin fannoni. Haka kuma ana kiran
malamin da ya yi fice a wajen ba da taimakon makaranta. |
Bahaushe na girmama duk matumin da ake kira kigo, saboda ana ɗaukarsa da babban matsayi na ilimi daga
cikin fannonin ilimi. Haka kuma Bahaushe na kiran mai ba da rubutun sha da
layu da karikitan tsibbu a matsayin kigo. Kigo sai wanda ka bari don Allah. |
|
11 |
Taakìi |
Taki Bahaushiyar kalma ce da ke ɗaukar ma’anar kashin dabbobi ko yaye-yaye na ƙazanta da ake kai gona. |
Kalmar ‘taki’ ali-aƙalla tana ɗaukar ma’anoni har guda
uku a harshen Hausa. Taki wanda ake sa ma shuke-shuke. Haka kuma akwai taki
na tsakanin ƙafa-da-ƙafa ko fili (hili) da kuma taki na saduwa tsakanin namiji da mace. |
Amma dukansu ana Magana ne a nan kan tarewar namiji da mace masu aure.
Faɗar wannan kalma a
magangannun malaman azure ko hulɗarsu tana
nufin saduwa. Malaman zaure na amfani da wannan kalma ne domin kauce wa
kalaman batsa musamman malmin zaure da kowa ya san su da natsuwa da kamun
kai. |
|
12 |
Taasarii |
Kalmar ‘tasari’ Balarabiyar kalma ce da aka Hausanceta wadda ke nufin
hasara ko tutar babu. |
Malaman zaure suna amfani da wannan kalma ne a cikin karance-karancnsu
a zaure. Ita wannan kalma na nufin biyu-babu wato an rasa tsuntsu an rasa
tarko. Wannan uwa da riba duk sun noce. |
Asalin wannan kalma a Larabce ‘khasira’. Wannan ya nuna Hausawa suna da
hikima da azanci wajen sarrafa kalmomin Larabci zuwa Hausa, da kuma faɗaɗa ma’anar
Kalmar ta hanyar salon Magana ko Karin Magana. |
Hausar Malaman
Zaure ta Sigar Yankin Jumla da Jumla
|
|
Yankin Jumla ko Jumla |
YJJA |
Hausar Zaure da
da Faɗaɗa Ma’ana. |
|
1 |
Kaa ƙi duuniyàa, àmmaa gàa kaa cikintà. |
Jumlar ta nuna wani abu namiji bai son duniya ko kaɗan, amma kuma ya kasa barin duniyar. |
Malaman zaure na amfani da wannan jumla a matsayin kirari ga wani
mashahurun littafi mai suna ‘Zuhdu’. Duk wanda ba ya da alaƙa da makarantun zaure ba zai fahinci wannan
jumlar yadda ya kamata. |
|
2 |
Haƙƙìn màcee ciyârwaa |
Ita ma wannnan jumla, tana nufin daga cikin abin da ya wajaba ga wanda
ya ajiye mace ta aure, shi ne ya ciyar da ita. |
Jumlar tana da ma’ana ta ɓoye da
malaman zaure suka faɗaɗa kamar haka; idan dare ya yi a ɗaura ma ta sirdi. Saboda an biya ma ta wajibinta da rana. |
|
3 |
Baràaden alƙalumàa |
Wannnan jumla ko yankin jumla kalmomin gambiza ne ɗaya Bahaushiyar kalma ta biyu kuma
Balarabiyar kalma. Abin da za a fahimta, shi ne mallaka ta faru, wato alƙalumman nan barade ne, wato jarummai a fagen
yaƙi. |
Amma a ɓoyayyiyar ma’ana da
malaman zaure ke ba wannan jumla ko yankin jumla, shi ne ƙwararrun marubuta. Ke nan wannan ya nuna
malaman zaure suka keɓanta da wannan ma’ana ta
baɗini kuma ta fannu. |
|
4 |
Bainà yaa yi nauyii |
Jumlar ‘baina ya yi nauyi’ jumla ce bayanau wadda ma’anarta a fili ko
sarari take ga mai saurare ko mai nazarin harshen Hausa. |
Jumlar ‘baina ya yi nauyi a mahangar malaman zaure tana da ɓoyayyiyar ma’ana ta baɗini da malaman zaure ke nufinta da shi kamar
haka; wato tana nufin iyalaina sun yi min yawa ko tsatson zariyata sun fi ƙarfi na. |
|
5 |
Fìtìluu sun bicѐe |
Fitillu sun bice, jumla ce bayanau da ta bayyana abin da ke faruwa game
da fitillu sun ɗauke haskensu da suke da
shi. Saboda haka ma’ana ta fito sarari a ma’anance |
Jumlar ‘Fitillu sun bice’ na ɗauke da
ma’anoni fiye da ɗaya a Hausar malaman zaure
na Ƙasar Gwandu
kamar haka; fitillu sun bice na nufin manyan-manyan malaman addini sun rassu.
An samu wannan ma’anar ne a bakunan malaman zaure. |
|
6 |
Ràagon Maalàm |
Wannan jumla ko yankin jumla yana ɗauke da kalmomi biyu, kuma duk sunaye ne, ɗaya ta mallaki ɗaya saboda harafin mallaka
ya shiga a tsakanin suna da suna, sai ya koma malam ne ya mallaki rago. |
Ma’anar wannan jumla ta ‘Ragon malam’ tana nufin abu mai kyau kuma mai
arha kowane iri ne. Ba wai sai abin da aka faɗi sunan shi ba. Malaman zaure ne suka faɗaɗa wanna jumla har ma suka
samar da ɓoyayyiyar ma’ana. |
|
7 |
Zaman daatsàa |
Zaman datsa yankin jumla ko
jumla ce da ya ƙunshi kalmomi biyu ta farko suna da aikatau da kuma harafin nasaba. A
inda datsa ke mallake da zaman. Datsa na nufin sara wani abu a daidai gaɓa, kamar a ce datsin rake da makamancin
haka. |
Yankin jumla ko jumlar ‘zaman datsa’ yana nufin wurin zaman tattaunawa
da masu kai-ka-wo kan hanya ko an yi an ce ga mutane. Ko kuma sa ido sana’ar
banza. Kenan an samo waɗannan ma’anoni na ɓoye ga malaman zaure na ƙasar Kebbi. |
|
8 |
Raariyaa mataatar sallàah |
Wannan cikakkiyar jumla ce mai ɗauke da kalmomi uku (3) ta ɗaya suna ta
biyu bayanau ta uku suna-aikatau |
Ita wannan jumlar ta ‘Rariya matatar sallah’ tana ɗauke da ma’anar da malamai suka ba ta, wato
littafi ne mai bayanin sallah da tantance ta. An kwatanta aikin da rariya ke
yi da littafen ahlari. |
|
9 |
Googaa mài kashi da tsiinin gambaa |
Jumlar ‘goga mai kashi da tsinin gamba’ jumla bayanau ce, kuma dukansu
kalmomin Hausa ne. |
A nan kalmar ‘Goga’ suna ne na namiji jarumi, amma ana nufin
gawurtaccen malamin zaure mai kwana rubutu. Ana amfani da rubutu a halaka
mutum. |
|
10 |
Mài ‘yar kimbaa |
Jumlar ‘mai ‘yar kimba’ jumla bayanau ce mai nuna ƙarancin wani abu kimba. |
An yi ƙoƙarin sifanta
kimba da azzakarin namiji, wato ita kimba siririya ce kuma marar kauri, to
shi ma namiji marar kauri da girman azzakari ake kira haka. |
Kammalawa
Muƙala ta yi bayanin Malaman zaure
da Hausarsu ta la’akari da sigogi da ƙunshiyarsu. An yi bayanin waɗanda ake kira Malaman zaure da ayukansu ko sana’arsu ta
karantarwa. Kazalika shi ma zaure an yi bayanin abin da ake kira zaure a ƙasar Hausa da abin da ake
cikinsa. Haka kuma ita ma Hausar an kawo yadda Malaman zaure ke amfani da ita a
wajen sadarwarsu.
Daga cikin abinda
wannan mu}ala ta gano ga wannan }warya}waryar bincike sun haɗa da:-
Akwai kalmomi da
sashen jumla da jumla na Hausar Malaman Zaure a Sokoto da Kebbi; haka nan ma
akwai tasirin karin harshen Yamma a cikin Hausar Malaman Zaure na Sokoto da
Kebbi; kuma akwai gamin gambiza a wajen wannan Hausar Malaman Zaure na Sokoto
da Kebbi. Haka an gano kuma ba ko’ina aka samun Hausar Malaman Zaure ba in ban
da makarantu da bakunan Malaman Zaure.
Manazarta
Abbas N. I. (2017). Karin Harshe
na Rukuni: Nazarin Hausar Shafin Makaranta na Jaridar Aminiya. Journal of
Nigerian Languages & Folklore: Volume xxiv, 2014, Bayero University
Press.
Abubakar N. (2007) Nazarin
Hausar Malaman Zaure a Garin Sakkwato Kundin Digiri na Ɗaya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato.
CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Printed by Ahmadu Bello
University Press Ltd.
Galadanci M.K.M da Wasu, (1992).
Hausa Don Ƙananan
Makarantun Sakandare
2. Longman Nigeria.
Greenberg J.R.(1962) Languages
of Africa, Bloomington
Umar, M.M. (2019) Nazarin Hausar
Wasu Rukunnan ‘Yan Kasuwa a Garin Sakkwato. Kundin Digiri na Uku. Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo
Sakkwato.
Yakasai, S.A. (2005). Aro da Ƙirƙira: Nazarin Samuwar Sababbin Kalmomin Hausa a Jami’a da
Kuma Garin Sakkwato: Maƙalar
da Aka Gabatar a Taron {arawa Juna Sani a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya.
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Yakasai, A. S. (2012). Jagoran
Ilimin Walwalar Harshe. Sokoto: Garkuwa Media Services Ltd.
Yunus A. (2016). Harshe Mai Zayyana Hoton Mutum: Dangantakar
Hausawa da Makwabtansu Sojoji. Maƙalar
da Aka Gabatar a Taron Ƙara
wa Juna Sani a Jami’ar Kaduna, Kaduna Nijeriya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.