Citation: Gwandu, B. A. (2025). “Kalmomin Aro a Hausar Malaman Zaure: Nazarin Wasu Yankunan Sakkwato da Kabi ” in Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 03, No. 02, Pp. 120 – 127. www.doi.org/10.36349/djhs.2025.v03i02.015.
KALMOMIN ARO A HAUSAR MALAMAN ZAURE: NAZARIN WASU YANKUNAN
SAKKWATO DA KABI
Na
Buhari Atiku Gwandu
PhD Candidate, Department of Nigerian Languages, Sokoto State
University, Sokoto
Tsakure:
Wannan takarda ta yi nazarin wasu kalmomi da harshen Hausa ya ara
daga harshen Larabci, waɗanda Malaman zaure ke amfani da su a yayin karatukansu
a zaure ko majalisi a masallaci. Wannan takarda ta fito da waɗansu misalai da
aka fi yawan jin Malaman zaure ke yawan furtawa a lokacin karantarwarsu, tare
da tasirin karin harshen Yamma. Haka kuma an ɗora wannan takarda kan ra’in
hulɗa tsakanin harsuna wanda Greenberg (1962) ya yi amfani da shi. An tattara
waɗannan bayanai ta hanyar zama a majalisin karatu zaure da masallaci da
sauraren karatukan waɗansu malamai na zaure, da kuma waɗansu ayyukan da aka
wallafa masu alaƙa da wannan bincike.
Samakon nazarin ya tabbatar da cewa: (i) Ana samun aro na kaitsaye ta fuska
uku; (a) aron lafazi da ma’ana sukutum; da (b) aron lafazi ban da ma’ana da
kuma (c) aro da faɗaɗa ko karkatar da ma’ana. (ii) takardar ta lura da ana
samun tasirin shaddantawa a mafi yawan Hausar Malaman zaure na Sakkwato da
Kabi.
Gabatarwa
Malaman zaure mutane ne waɗanda suke koyar da
al’umma addinin Musulunci, musamman karatun Alƙur’ani mai girma da waɗansu ilmuka. Babban dalilin
gabatar da wannan takarda, ita ce fitowa da waɗansu kalmomi na aro da malaman
zaure ke amfani da su wajen karantarwa irin ta su da hulɗarsu da abokan
mu’amala. Wannan ya haifar da yawaitar yin amfani da wasu
kalmomin aro na harshen Larabci a zaure. Harshe yana aron kalmomi kai tsaye
daga wani harshe zuwa wani ta hanyar fassara da kwaikwayo tare da sarrafa
kalmomin. Aro na faruwa ne yayin da hulɗa da cuɗanya ta haɗa harsuna mu’amala
da juna. Ta wannan hulɗar da cuɗanya da juna za su samar ma junansu hanyar
sadarwa kowace iri. Wannan takarda za ta fito da waɗansu kalmomi da harshen
Hausa ya ara ga Larabci da yadda aron ya kasance. Domin Hausa, harshe ne wanda
ya kasance ɗaya daga cikin manyan harsuna da yake taka rawa a nahiyoyin
duniya, kuma harshe ne da masu magana da shi ƙaruwa da yaɗuwa suke. Harshen Hausa yana
cikin jerin gwanon harsuna da duniya ta lisafta na goma shɗaya (11) a duniya,
cikin harsuna 70,250, NTI (2020). Girman darajarsa da hulɗarsa ya
haifar da aron kalmomi ga harshen Larabci ta sanadiyyar cinikayya da karɓar
addinin Muslunci.
Harshe na nufin hanyar magana tsakanin
al’umma iri ɗaya (CNHN, 2006). Irin abubuwan da harshe yakan bayyana a
sarari don a fahimci mutum, shi ake kira magana ko zance (Yero, 2012). Harshe
wata baiwa ce wadda Allah ya halicci mutum da ita, domin ya bayyana tunaninsa
zuwa ga sauran ‘yan uwansa mutane ta hanyar furucin waɗansu sautukan magana
masu ma’ana da kuma amfani (Yakasai, 2012).
Aron Kalmomi a Harshe
Aron kalma ba gazawa ba ce ko kasawa ba ko
kuma cikas ba ne ga harshe da ya ari wata kalma kaitsaye ko ya ɓalli
wani ɓangare na ta, ko ya yi ma ta kwaskwarima don ta dace da furucinsa
(Umar, 2019). Kalmar ‘aro’ a rarrar kalma ce da aka aro daga harshen
Larabci, wato ‘Isti’aara, Yusti’iiru ‘Isti’aaratan’ Almu’ijamu al-Lugah.
Hausawa sun yi wa kalmar kwaskwarima ta koma aro, Daurawa (2023). Irin yadda
ma’anar ta take a harshen Larabci, su ma Hausawa haka suka ari kalmar sautin da
ma’anar sukutum. Aro na nufin karɓar wani abu don a yi amfani da shi a mayar wa
mai shi (CNHN, 2006). Aron kalma yana nufin ɗauko wata kalma
daga wani harshe zuwa wani harshe (Adamu, 2016).
A wani ƙauli kuma aro na nufin harshen da ya yi
aro yana ɗaukar wannan kalma ya cigaba da amfani da ita a mu’amalarsa ta
yau da kullum (Abubakar, 2007). Kalmomin aro su ne kalmomi ko
sassan jumla da aka ɗauko daga wani harshe domin amfani da su ga wani
harshe, (Umar, 2019).
Bayan waɗannan ma’anoni da aka hikaito
daga bakunan masana da manazarta daban-daban, an lura da cewa aro a nan, na
harshe ake nufi. Aro shi ne amfani da wata kalma ko yankin jumla ta wani harshe
domin inganta sadarwa da abinda harsunan biyu suka yi matsaya na manufa ko
ma’ana. Tarihi ya nuna dukan harsunan duniya sun samo asali ne daga
kaka ɗaya, Annabi Adamu da Hauwa’u (Alaihis salam), saboda faɗar Allah “…lalle
ne Mu, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangogi da ƙabiloli, domin ku san juna ….”, (Gumi:
Suratul Hujirat, aya ta 13). Wannan aya ta Alƙur’ani an bayyana alaƙa ta ƙut-da-ƙut da mu’amala da
hulɗar harsuna na daɗa tasiri da bunƙasuwa
da haɓakar aro a harsuna.
Dalilai da dama sun haifar da aro a
harsuna mabam-banta, don masana da manazarta sun yi ishara da tsokaci a kai,
saboda harsuna na dogaro da taimakekeniya ga junansu don samar da wadatattun
kalmomi da za a iya isar da saƙo
babu wata tantama ko tangarɗa. Daga cikin dalilan da masana ke hasashen sun
haifar da yin aro sun haɗa da:
· Alaƙar sautuka ta ƙut-da-ƙut
· Addini
· Ɓacewar tsofaffin kalmomi na asali
· Cuɗanya ko hulɗa
· Auratayya, (Junju, 1990).
Masana sun nuna wani harshe zai zo ya ari
kalma ko sashe domin waƙiltar
wani abu da babu a wancan harshen da ake hulɗa ko mu’amala da shi, don haka,
amfani da baƙin kalmomi dole ne don cike gurbin waɗanda
babu ga harshe, shi ake kira aro ga harshe. Ta haka ne Hausawa suka samu himma
wajen koyon kalmomin Larabci da kuma Hausance wasu, saboda tasirin kalmomin
Larabci a mu’amalarsu da hulɗarsu da Hausawa (Yakasai, 2012). Harshen
Larabci, harshe ne da ya fi kowane harshe matsayi da daraja a duniya, domin shi
ne ya game kowa da kowa na duniya, kuma shi ne ake amfani da shi a wurin bautar
Allah, wato baƙi ne kai ko farar fata ne kai, matsaya
guda ku ke a wurin Allah, subhanahu wa ta’ala.
Harshen Hausa harshe ne mai tafiya tare da
zamani ta fuskar addini da kimiyya da fasaha da kasuwanci da neman ilimi da
sauran fannonin rayuwar al’umma. Harshen Hausa ya ari sautukan Larabci
baki-ɗayansu ya mayar da su hanyar salon rubutunsa na Ajami. Wasu sautukan aron
kaitsaye ne, wasu kuma kwaskwarima ya yi musu don su dace da sautukansa na
Hausa da Larabci ba ya da su (Adamu, 2002).
Malamai da masana sun gabatar da ayyuka
mabambanta dangane da abin da ya shafi aro tsakanin harshen Larabci da na Hausa
kamar su Ramlat (2002) da Salama (2011) da Suleiman (2014) da Adamu (2016) da
Muhammad (2024) da makamantansu. Dukansu sun yi bayani kan alaƙa da dangantaka da abubuwan da suka haifar
da aro a tsakanin harshen Larabci da Hausa. Kuma kowanensu da abinda ya kalla
dangane da aron kalmomin Larabci zuwa harshen Hausa. Ramlat ta nazarci aron
kalmomi da ƙirar
kalma. Ita ma Salama ta yi nazarinta ne kan kalmomin da harshen Hausa ya ara.
Muhammad ma ya kawo rabe-raben aro aƙalla
uku da Malaman Zaure kan yi da makamantansu. Aron lafazi da ma’ana kaitsaye da
aron lafazi ban da ma’ana da aron lafazi da faɗaɗa ko karkatar da ma’ana
Malaman Zaure a Sakkwato da Kabi
Kalmar ‘Malamai’ jam’i ce ta Maalam ko
Mallam a matsayin tilo da Hausawa suka ara daga harshen Larabci. Malam na nufin
masanin wani ilimi na addini, ko kuma ilimin zamani a yanzu.
Ita ma kalmar ‘Zaure’ Bahaushiyar kalma ce
da ta samo asali daga harshen Hausa wadda ke nufin wani ɗaki da aka shiga
a kwanta ko a yi karatu ko wani abu makamancin haka.
Zaure na nufin ɗaki mai ƙofa biyu wanda ake fara shiga ta cikinsa
kafin a shiga cikin gida Adamu (2016).
Zaure na nufin ɗakin hayi (CNHN
2006).
Zaure a ƙasar Hausa wani ɗaki ne kewayayye mai
kama da da’ira wanda aka gina da laka mai ɗauke da itace a sama kewaye da
shi tare da hakin baibaya na bunu. Kazalika duk wani wuri da aka keɓe ana
karantar da manya ɗalibai masu neman ilimi a bakin garka ko ɗaki ko
shigifa. Amma yankin Sakkwato da Kabi, zaure shi ne wurin shiga da aka yi a
bakin garka don saukar da baƙo
ko kwanan yara ko kuma karantar da yara da manya masu karatun ilimi (Abubakar
2007).
Hanyoyin da aka yi amfani da su a wajen
tattara waɗannan bayanai na wannan takarda sun haɗa da:
1. Ziyartar
zaurukan ɗaukar ilimi na malamai. An samu halartar waɗansu zauruka na
Malamai a yayin gudanar da karatuka kamar irin su Zauren Malam Babi Gangare
Sakkwato da Malam Abubakar Gwandu Digar Agere Sakkwato da Zauren Modibbon
Gwandu B/Kebbi da Zauren Malam Walu Adarawar Borno Gwandu da Zaurukan Lungun
Malamai Gwandu.
2. Kafafen yaɗa labarai da
suka ƙunshi, kafafen yaɗa
zumunci kamar su Fesbuk (facebook) da watsaf (WhatsApp) da tit-tof (Tik-tok) da
Yutub (You tube) da Istagiram (Instagram) da makamantansu.
3. Wallafe-wallafen ayyukan
masana da manazarta da suka shafi aron kalmomin harshen Larabci da harshen
Hausa suka yi.
An zaɓi garuruwan Sakkwato da Kabi ne
domin irin alaƙa da dangantaka da ke tsakanin garuruwan
tun zamanin masu jihadi. Garuruwan biyu tankar Ɗanjumma ne da Ɗanjummai ne. Saboda Daula ɗaya ce
suka raba, Gabasci kulawar Muhammadu Bello Ɗan Sheikh Usmanu Bin Fodiyo, Yamma kuma
kulawar Sheikh Abdullahi Bin Fodiyo Gwandu. Haka kuma Malumman waɗannan
garuruwan sun yi musayar neman ilimi a tsakaninsu da junansu. Sakkwato ita ce
babbar cibiyar Daular Usmaniyya, haka nan kuma ko bayan zuwan Turawa ‘yan
mulkin mallaka Sakkwato ita ce uwa ga Kabi, Ambursa (2013). Waɗannan dalilai ne
ya sa aka zaɓi Sakkwato da Kabi ga wannan binciken. An lura da karin harshensu
iri ɗaya ne, malummansu ɗaya ne, kuma sun fi ba da ƙarfi da kulawa a ɓangaren Fiƙhu da Luggah.
Yadda Malaman Zaure Suke Amfani da
Kalmomin Aro a Kabi da Sakkwato
Masana ilimin nazarin harshe da
kimiyyarsa, sun bayyana duk harshe yana da hanyar da yake amfani da ita wajen
bayyana kalmomin da ya ara ta ba su ma’ana ta sarari da ta ɓoye (Ramlat,
2002). Saboda haka duk maganar da aka furta sai an yi nazarin ma’anarta da kuma
inda ta dosa kafin a yanke ma ta hukunci a fannin nazarin ma’ana (semantics).
Wannnan ya nuna kalmomin da harshen Hausa ya aro akwai yadda ake amfani da su,
ko dai su ɗauki ma’anar kaitsaye ko su faɗaɗa ta, ko ma su yi watsi da
ma’anar ta asali su ba da tasu ma’anar ta daban don wata manufa da
suka ɓoye ko sakaya ga wasu da ba abokan hulɗa ba. Har ila wa yau, harshen
Hausa yana aron kalmar Larabci ya ba ta ma’ana mai dangantaka da ma’anar
kaitsaye ko kuma ta karkace ma ma’anar ta asali (Salama, 2011). A
wani lokaci ma za a iya samun ma’anonin babu alaƙa ko dangantaka ta kusa ko nesa.
Baya ga la’akari da bayanan da suka gabata
a baya, kalmomin da harshen Hausa ya aro kuma yake ci gaba da aro a halin yanzu
ana kallonsu da nazarinsu ta fuska uku 3 kamar haka:
Aro na Kai Tsaye Tsakanin Malaman Zaure a
Kabi da Sakkwato
Aro na nufin ɗaukar kalma daga wani
harshe a shiga da ita cikin jerin kalmomin wani harshen a daban. Aro wata
fasaha ce da Ɗan’adam
ke amfani da ita ta hanyar ɗauko gudan kalma ko gudajen kalmomi daga wani
harshe a shigar a shigar cikin jerin kalmomin wani harshe a daban, Suleiman
(2014).
Aro na kai tsaye, wani salon aron kalma ne
da harshen Hausa ya yi na tarewar ma’anar harshen Larabci da harshen Hausa ko
ta sauti ko kuma Hausance sautin kalmar da ma’anar. Wato ma’anar fili ko sarari
daga ma’ana ta asali wadda Larabci yake amfani da ita, kana Malaman Zaure na
Kabi da Sakkwato suka Hausantar da kalmomin kamar haka:
a. Aron lafazi (sauti) sukutum da ma’anarsa
b. Aron lafazi (sauti) ban da ma’ana
c. Aron lafazi (sauti) da juyar da ma’anarsa, Muhammad (2024)
Ataƙaice dai an fahimci aro kaitsaye na nufin
yin amfani da wata kalma ta wani harshe don sauƙin isar da saƙo a tsakanin harsunan biyu da niyyar
faɗaɗawa ko bunƙasawa.
Wannan aron kalmomi ne da ke ɗauke da lafazi da sautin kalma (Hausancewa)
da ma’ana ta Larabci. Wato ma’anar da harshen Larabci ke nufi, haka su ma
Hausawa ke nufi a harshensu.
|
|
Kalmar Aro Daga harshen Larabci |
Hausantar da Kalmar a Harshen Hausa |
Ma’anar Kalmar a Harshen Hausa |
|
1 |
Yardwáá |
Yaddáá |
Aminééwââ |
|
2 |
Khasarah |
Hasaaraa |
Taasarii |
|
3 |
Al-turaab |
Turɗaa/Turɓaaya |
Ƙasa laƙai-laƙai |
|
4 |
Al-ramadwaan |
Ramalaanaa |
watan azumii |
|
5 |
Gaafilun |
Gahwalallee |
Rafkanannee |
|
6 |
Jidaal |
Jidaalii |
Faɗaa |
|
7 |
Daƙiiƙ |
Daƙiiƙii |
Bin diddigii ko naacii |
|
8 |
Ƙaimii |
Ƙaimii |
Linzaamin dookii |
|
9 |
Ƙiimatun |
Kiimaa |
Kwatantaa abu |
|
10 |
Muflis |
muhulisii |
Wanda aka rabee ma laadaa |
|
11 |
Dwaririyyu |
Laluurii |
Ƙurarren lookacii |
|
12 |
Mu’allim |
Mallaam |
Masanii |
|
13 |
Fitnatun |
hitinaa |
Taashin hankalii |
|
14 |
Al-aalah |
Aalaa |
Kayan ɗimaamaa ruuwaa |
|
15 |
Harakaat |
Harkaa |
Wasulaa |
|
16 |
Al-laun |
Launii |
Launii |
Kalmar ‘khasaarah’ an aro ta ne daga
harshen larabci, kana daga baya Malaman zaure suka Hausantar da kalmar ta koma
‘hasaaraa’, saboda Bahaushe ba ya da harafin ‘kha’ sai dai harafin ‘ha’.
Malaman Zaure sun Hausantar da kalmar ta koma ‘Hasaaraa’ saboda tsohuwar kalmar
fassararta ta nisanta.
Ita ma kalmar ‘Ramadwaan’ Balarabiyar
kalma ce da aka aro daga harshen Larabci, amma Malaman Zaure suka Hausantar da
ita ta koma ‘Ramalaana’, saboda harafin ‘dwa’ ya koma ‘la’ na da wuyar furuci
ga Bahaushe. Saboda haka Malaman Zaure suka Hausantar da kalmar ta
‘Ramalaana’
Kalmar ‘Jidaal’ ararrar kalma ce da aka
aro daga harshen Larabci, amma Malamai suka Hausantar da lafazinta da ma’anarta
a harshen Hausa ta koma ‘Jidaalii’. Bambancinsu shi ne harshen Larabci
na ɗaure hafin ƙarshe
na kalma, saboda aikin nahawu. Malaman Zaure suna yi ma mafi yawan kalmomin aro
wasli a ƙarshen kalma.
Ita ma kalmar ‘fitnatun’ aro ta aka yi ga
harshen Larabci, kana daga baya Malaman Zaure suka Hausantar da lafazinta da
ma’anarta ta koma ‘Hitinaa’. Nan ma an samu musayar harafin ‘f/p’ ya koma ‘h’ a
Hauasar Yamma. Saboda harafin kalmar na farko Balaraben harafi ne, ba Bahaushe
ba. Shi yassa Malaman Zaure suka sauya harafin na Larabci.
Duk waɗannan kalmomi da aka kawo suna nuna
yadda harshen Larabci ya yi tasiri ga harshen Hausa, domin Malaman Zaure sun
Hausance mafi yawan waɗansu kalmomin Larabci ta la’akari da tsarin lafazi
(sauti) da ma’anar kalma. Sai dai waɗansu kalmomin sun ɗan bambanta da
lafazin asali na Larabci da yadda Hausawa suka Hausantar da su. Waɗansu kalmomi
sun yi canjaras da lafazin (sauti) da ma’anar sai inda ba a rasa ɗan wani
abu ba.
Duk waɗannan kalmomi aro ne na kaitsaye da
Hausawa suka ara ba tare da an canza musu salon rubutu da ma’ana ba, saboda
tasirin harshen Larabci a wajen karatu a makarantu da mu’amala da zamantakewa
tsakanin Hausawa da Larabawa. Saboda daɗewa ana amfani da su har ma sun zama
‘yan gida wato kalmomin din-din-din na harshen Hausa.
Aron Lafazi (sauti) Ban da Ma’ana, Sai Dai
Faɗaɗa Ma’ana Tsakanin Malaman Zaure a Kabi da Sakkwato
Faɗaɗa ma’ana na nufin ƙarawa wani abu faɗi (CNHN, 2006). Faɗaɗawa
na nufi buɗe wani abu da yake tsuke ko ƙuƙunce
a cikin wani mayuwacin hali, ko yalwata wani zance ko magana ko wani wuri ko
wani abu na zahiri (Gwandu, 2021). A nazarin ma’ana kamar yadda aka gani a
baya, a kan sami yanayin da ma’anar wata magana ko kalma ta faɗaɗa ko yaɗu ko
ma ta fanɗare daga ma’anar ta asali. Wannan na faruwa ne ga ma’anar ko dai don
tsawon lokacin amfani da kalmar da ya sa ma’anarta ta gurɓata ko ta sauya, wani
lokacin ma don ma’anar ta tafi da zamani (Abubakar, 2014).
|
|
Kalmar Aro Daga Harshen Larabci |
Hausantar da Kalmar a Harshen Hausa |
Ma’anar Kalmar a Hausa da Faɗaɗa Ma’ana |
|
1 |
Farj |
Hwarji/ farji |
Gaban macee ko namijii |
|
2 |
Tasbii |
Tasbahaa |
Abinda akee ƙidan
zikirii da shii |
|
3 |
Ajamiyyun |
Ba’ajamee |
Boobaawaa |
|
4 |
Al-imam |
Liiman |
Jaagooraa |
|
5 |
Al-suurah |
Suuraa |
Alaamaa ko hootoo |
|
6 |
Haajah |
Haajaa |
Buƙaataa ko
kaayan tallaa |
|
7 |
Al-jariidah |
Jariida |
Gangaamee ko abin karantawa |
|
8 |
Al-hisaab |
Hisaabi |
Lisahi ko bin diddigi, sakamako |
|
9 |
Al-akhdwariyyu |
Ahlarii |
Mazauni gida, mahalarci |
|
10 |
Al-swahaabah |
sahabbai |
Mabiyan Annabi Muhammad |
|
11 |
Al-sheikh |
Sheehu |
Tsoho ko babban maalamii |
|
12 |
Al-zamanu |
Zaamanii |
Lookacii ko yanayii ko yanzu |
|
13 |
Lakaa’i |
Lalatattaa |
Halakakkiyaa ko karkatacciyaa |
|
14 |
Abdullah |
Audullahi |
Bawan-Allah |
Kalmar ‘Farj’ ta samo asali ne daga
harshen Larabci, amma saboda kalmar tana da nauyin faɗi ga al’adar Hausawa.
Wannan ne ya sa aka yi amfani da sunaye daban-daban don sakaya kalamar a
harshen Hausa. Hausawa na fassara wannan kalmar kamar haka; gindii ko guutsuu
ko matuucii ko gatoo ko zakarii ko kuma al’auraa da sauransu. Kana daga baya
Malaman Zaure suka sakaya kalmar da sunan ‘gaban namijii ko gaban macee.
Malaman Zaure sun yi wannan fassara ce don ɓoye ma’anonin da al’adar Hausa
ta zarga.
Kalmar ‘Tasbih’ ararrar kalmace da aka aro
daga harshen Larabawa, kuma aikatau ce. Malaman Zaure sun Hausantar da kalmar
ta koma ‘Tasbahaa’ daga tasbih ta dawo sunan abinda ake amfani da shi wurin
tasbih. Wannan ya nuna hikimar Malaman Zaure sun ƙara samar da faɗaɗuwar ma’ana daga ajin
aikatau zuwa ajin suna.
Ita ma kalmar ‘Al-ajamiyyun’ kalma ce da
ta samo asali daga harshen Larabci, kuma tana nufin duk wanda ba Balarabe ba.
Malaman Zaure sun Hausantar da kalmar ta koma ‘Ba’ajamee’. Wato an
samu ɗafa ƙeyar
da ya haifar da faɗaɗuwar kalmar, wanda kuma aka kira da sunan ‘Boobaawaa ko
Boobooniyaa’. Wato wanda ba ya jin ko iya magana da wani harshe.
Haka kuma kalmar ‘Al-suurah’ an aro ta ne
daga harshen Larabci. Ita wannan kalma tana nufin wani dunƙulallen saƙo mai ɗauke da hikimomi tare da kanun
labarai a cikinsa. Malaman Zaure sun faɗaɗa ma’anar wannan kalma kamar haka;
zatin wani abu ko ƙwangarangwal
ko hoto ko makamancin wani abu.
Bisa la’akari da misalan da suka gabata za
a fahimci Malaman Zaure na da ƙwarewa
da fasaha a wajen aron kalmomin harshen Larabci da yi musu kwaskwarimar
Hausantarsuwa. Malaman Zaure sun yi amfani da hulɗa da zamantakewa sun faɗaɗa
ma’anar kalmomin harshen Larabci. Haka kuma sun sakaya waɗansu ma’anoni da
al’adar ke zargin furtawa duk da kasancewarsu kalmomin asali na harshen Hausa.
Aron Lafazi (sauti) da Karkatar da Ma’ana
Tsakanin Malaman Zaure a Kabi da Sakkwato
Malaman zaure na aron kalma daga baya su
karkartar da ma’anarta ko faɗaɗa ta la’akari da waɗansu abubuwa da kalmar
ta ƙunsa da kuma ma’anar da suka ba ta. Wannan
yana faruwa ne ko dai don ɓadda bami ko ɓoyewa ko sakaya ma’anar.
Karkatar da ma’anar aro na nufin aron kalma daga wani harshe, sannan a karkatar
da manufarta ta asali zuwa wata manufa ta daban da ba ita ba in an fassara ko
tarjama (Ramlat, 2002). Akwai wasu kalmomin Larabci da yawa waɗanda
ma’anarsu ta bambanta da na harshen Hausa ta sanadiyyar karkatar da ma’anar
asali da aka fassara ta da ita. Mu’amalar Hausawa da Larabawa ta yi
tasiri ƙwaran gaske wajen baddala ma’anar waɗansu
kalmomin Larabci. Harshen Larabci, harshe ne mai faɗi, a kan faɗin ƙunshiyar ma’anarsa ne ma ya haifar da
Hausawa na karkatar da ma’anar waɗansu kalmomin Larabcin.
|
|
Kalmar Aro Daga Harshen Larabci |
Hausantar da Kalmar a Harshen Hausa |
Karkatar da Ma’anar Kalmar a Harshen Larabci da Faɗaɗa Ma’ana |
|
1 |
Al-daƙiiƙ |
Daƙiiƙii |
Takkwalii ko kidaahumii |
|
2 |
Zuuƙu |
Zuƙuu |
Kwaraaree ko zarceewaa |
|
3 |
Al-guluul |
guluuluu |
Suruutuu |
|
4 |
Li’iilafi-ƙuraish |
Li’iilahi-ƙuraishi |
Annaniyar koowaa ta bii shi |
|
5 |
Inkaar |
Ankara |
Luura ko guduu/sheeƙaa |
|
6 |
Haajah |
Haajaa |
Kaayan sayarwaa |
|
7 |
Al-muhaajir |
Almaajirii |
Mabaraacii |
|
8 |
Al-zakaat |
Zakkaa |
Korarree cikin dangii |
|
9 |
Albarakaat |
Albarka |
Ba a barii haka nan baa |
|
10 |
Sayaws |
sayas |
Addu’ar sayar da abin sayarwa a kasuwa |
|
11 |
Al-salaamu |
An sallama |
An bar abin sayarwar nan haka nan |
|
12 |
Al-adah |
La’adaa |
Abinda mai sayee da sayarwaa kee baa wanda yaa shiga tsakaanii |
|
12 |
Al-magrib |
Magariibaa |
Ƙasaashen yammaa |
|
13 |
Al-haal |
Alhaalii |
Sabooda ko doomin ko don |
|
14 |
Al-geb |
Gaaɓaa/gaɓaa |
Geebee ko Koogii |
Kalmar ‘Al-daƙiiƙ’ aro ta aka yi a harshen Larabci, Sannan
daga baya aka Hausance Kalmar sai ta koma ‘Daƙiiƙii’. Larabawa sun fassara ma’anar wannan
kalma da naci ko ƙwalailaicewa.
Amma Malaman Zaure sun faɗaɗa ma’anar ko karkatar da ma’anarta da fassarar
takkwali ko kidahumi, wato wanda bai gane komai a karatu ko a rayuwa.
Kalmar ‘Zuuƙuu’ ma ararriya ce daga harshen Larabci,
kuma aikatau ce. Larabawa na fassara wannan kalmar da ‘ɗanɗana’ ko ‘lasa’ ko
‘ka ji da kanka’. Malaman zaure sun ƙara ma wannan kalma gudu da faɗaɗa ko
karkatar da ma’anarta, don sun fassara ta da ‘Kwarare’ ko ‘Zarcewa’ ko ‘Zurare’
ko kuma ‘Wuce gona da iri’ da makamantansu.
Kalmar ‘Al-magrib’ ta samo asalinta ne
daga harshen Larabci, kuma tana nufin Sallar Magariba, wato bayan faɗuwar rana.
Amma su Malaman Zaure na fassara wannan kalmar da ma’anar ‘Ƙasashen Yamma’ ko ‘ wani salon rubutu da
aka gada ga Malamai’. Wannan ya nuna Malaman Zaure na ƙara faɗaɗa ma’anar kalmomin Larabci don
sadarwar yau da kullum.
Ita ma kalmar ‘Al-guluul’ Balarabiyar
kalma ce da aka aro ga harshen Larabawa mai ɗauke da ma’anar ‘Ɗaukar wani abu cikin kayan rabo, kamin a
raba’. Wato wannan abin da aka ɗauka na kayan, shi ake kira ‘guluul’.
Malaman Zaure sun ari sauti da lafazin kalmar suka faɗaɗa da karkatar da
ma’anarta kamar haka; ‘Surutu’ ko ‘Magangannun da ba su da amfani’ ko kuma
‘yasassun zanzantuka’ da makamantansu.
Kammalawa
Bayanai sun gabata masu matuƙar muhimmanci dangane da abinda ya shafi
aron kalmomi a Hausar malaman zaure a wasu ɓangarorin rayuwar al’umma.
Takardar ta bayar da haske kan yadda furucin waɗansu kalmomi ke bambanta da
juna, sanadiyyar tasirin harshen Larabci wajen koyon addinin Muslunci. Haka
zalika kuma, takardar ta yi nuni da yadda Hausawa masu alaƙa da karatun zaure ke aron kalmomi
kaitsaye da faɗaɗa ma’ana da karkatar da ma’ana.
Manazarta
Abubakar
N. (2007). Nazarin Hausar Malaman Zaure a Garin Sakkwato Kundin Digiri na Ɗaya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Abubakar
N. (2014). Malaman Zaure da Gudummuwarsu a Harshen Hausa. Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa da Ƙasa, Jami’ar Bayero, Kano
CNHN,
(2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero Kano.
Ahmadu Bello University Press Ltd.
Galadanci
M.K.M, (1992). Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare 2.
Longman Nigeria.
Greenberg
J.R. (1962). Languages of Africa. Bloomington.
Gwandu
A.B. (2021) Kalmomin Fannu na Magungunan Kyamis a Kasuwar Dodoru. Kundin Digiri
na Uku. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sokoto.
Junju
H.M. (1990). Garkuwar Hausa da Tafarkin Ci gaba. Fisbas Media
Services Publications.
N.T.I,
(2020). Course Book on Primary Education, Second Semester Year 4.
N.T.I Press
Ramlat
J.D. (2002). Morphological and Phonological Adaptation of Arabic Loan Words to
Hausa. Algaita: Journal of Current Research in Hausa, Bayero
University, (2)1.
Salama
S.I. (2011). Kalmomin Aro: Nazari a Kan Wasu Kalmomi da Hausa ta Ara Daga
Larabci. Takardar da Aka Gabatar a Taron Ƙarawa Juna Sani. Sashen Harsunan Nijeriya.
Katsina : Jami’ar Umaru Musa Yar’adua.
Umar,
M.M. (2019) Nazarin Hausar Wasu Rukunnan ‘Yan Kasuwa a Garin Sakkwato. Kundin
Digiri na Uku. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Sakkwato.
Yakasai,
A.S. (2012). Jagoran Ilimin Walwalar Harshe. Garkuwa Media Services Ltd.
Zainab
Y. (2012) Nazarin Hausar Yaron Mota a Garin Zaria. Kundin Digiri na Biyu
Jami’ar Ahmadu Bello Zaria.
Ambursa U. R, (2013).
Tarihin Shehu da Abdullahi, Ambursa Printing Press Ltd.
Muhammad A. A (2024). Muhadara: Yadda Aka Zakkah
da Waƙafi, Taron Ƙarawa Juna Sani. Ma’aikatar Lamurran Addinin
Muslunci ta Jihar Katsiona.
Adamu M. (2016). Kalma Ɗaya Ma’ana Bamban: Nazari Kan Wasu Kalmomin Aro
Daga Larabci Zuwa Hausa. Takardar da Aka Gabatar a Taron Ƙarawa Juna Sani a Jami’ar Jihar Kaduna.
Daurawa, A. I. (2023). Tafsir Suratul Fatiha, Gombe State, a Ranar
07 ga Watan Ramadwaana, Shekara ta 1444, Shekarar 2023.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.