Citation: Ayagi, J. S., Musa, I. I. and Ɗayyabu, A. (2025). “Gargaɗi a cikin Waƙar Arewa Jamhuriya ko Mulukiya: Madogara daga wasu Nassoshin Addinin Musulunci.” in Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 03, No. 02, Pp. 144 – 151. www.doi.org/10.36349/djhs.2025.v03i02.018.
GARGAƊI A CIKIN
WAƘAR AREWA
JAMHURIYA KO MULUKIYA: MADOGARA DAGA WASU NASSOSHIN ADDININ MUSULUNCI
Na
Jibrin Sani Ayagi
Da
Rabi’u Musa Kwamkwaso College of Advanced and Remedial Studies
Kano
Department of Linguistics and Nigerian Languages, Alvan Ikoku
Fed.University of Edu., Owerri, Imo State
Da
Idris Ibrahim Musa 2 and Abubakar Ɗayyabu 1
Rabi’u Musa Kwamkwaso College of Advanced and Remedial Studies
Kano
Tsakure:
Wannan takarda mai taken Gargaɗi a cikin
waƙar Arewa Jamhuriyya ko Mulukiyya: Madogara daga
wasu Nassoshin Addinin Musulunci, ta yi bayani ne a kan irin dangantakar da
take tsakanin tsoratarwa da hani da addini ya yi a kan aikata munanan ɗabi’u, da faɗakarwar
da jan kunne da marubucin waƙar ya yi
wa Hausawa na yankin Arewacin Najeriya a kan wasu ɗabi’u marasa kyau da suke aikatawa. Daga cikin
munanan ɗabi’un da binciken ya gano akwai rashin mai da
hankali wajen neman ilimi da taɓarɓarewar
tarbiya da kawalci da almubazzaranci da gulma da hassada da baƙin ciki da cin amana da camfi da ƙarya da roƙo da fariya da sauransu. Binciken ya gano cewa tabbas akwai
dangantaka mai ƙarfi
dangane da shawarar da marubucin waƙar ya ba wa ‘yan arewa a kan wasu ayyuka marasa kyau da suke
aikatawa da kuma hani da tsoratarwar da Al’ƙur’ani da Hadisai suka yi a kan aikata aiyuka marasa kyau. Wannan
waƙa da aka nazarta an same ta ne a cikin littafin
marubucin da ya kira “Waƙoƙin Sa’adu Zungur” (1968) littafi ne da
yake ƙunshe da
waƙoƙi ciki har da ita wannar waƙar. sannan aka sake rubuta ta domin yin wannan bincike. Haka kuma
an karanta ta da yawa domin ƙara fahimtar komai. An yi amfani da Ra’in fanɗarewa daga karɓaɓɓun Al’adun A’umma
(Deviance theory) aka ɗora takardar a kansa. Ra’in yana
bayani ne a kan yanayi na fanɗarewa daga al’adar da
al’umma ta saba da ita. Mutum na iya fanɗarewa ta hanyar ƙin aikata wasu al’adu ko wuce gona da iri a
wajen aikata al’adu ko ma aikata al’adun da ba su yi daidai da dokokin da
al’ummar da yake ciki ba. (Otite and Ogionwo 1981:217).
Gabatarwa
Wannan muƙalar tana
bayani ne a kan rubutacciyar waƙar Hausa
wadda Malam Ahmad Mahmud Sa’adu Zungur ya wallafa. Masana da dama sun bayyana
ma’anar rubutacciyyar waƙar Hausa
a cikin nazari kamar Ɗangambo
(2007:6) yana cewa “Rubutacciyar waƙa na nufin “wani saƙo da aka gina shi kan tsararraiyar ƙa’ida ta baiti, ɗango, rerawa, kari (bahari), amsa amo da sauran ƙa’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓensu da amfani da su cikin sigogin da ba lallai ne haka suke a
maganar baka ba”. Bayan haka, an duba wasu nazarce-nazarcen
masana da manazarta a kan rubutattun waƙoƙin Hausa
na mabambantan marubuta da dama ta sigogi daban-daban. Bello (2002:276) ya
nazarci rubutattun waƙoƙin Hausa ta hanyar fito da tasirin da harshen
Larabci ya yi a kan rubutattun waƙoƙin Hausa.
Shi ma Umar (2002:165) ya nazarci rubutacciyar waƙar Malam Aliyu Namangi inda ya nazarci kwalliya da ma’ana tare da
saƙon da ke cikin waƙoƙinsa da
suka shafi addini. Har ila yau Aliyu (2011:113) ya yi nazari a kan manufar waƙa a siyasa. A nasa binciken ya nuna yadda
rubutatun waƙoƙin siyasa suka haifar da ire-iren jigogi
mabambanta a cikin waƙoƙin siyasa na Hausa. Haka kuma Hussaini
(2024:299) ya nazarci rubutattun waƙoƙin Hausa
a inda ya nazarci salon amfani da nassi a rubutattun waƙoƙin Hausa misalai daga wasu waƙoƙin
gwagwarmaya. Wannan ne ya bayar da damar yin wannan binciken, ganin yadda
masana da manazarta suke ta nazarin rubutattun waƙoƙin Hausa,
amma ba a samu wani nazari wanda ya bibiyi waƙar ‘Arewa Jamhuriya ko Mulukiya ta Malam Sa’adu Zungur ya fito da
irin dangantakar da ke tsakanin al’adun Hausawa da na addinin Musulunci da
ya sarrafa a ƙananan
manufofin cikin waƙar, ta
hanyar bincike na ilimi domin daɗa fito da
saƙonnin cikin waƙar a fili ba. Shi ya sa ake son cike wannan giɓin da daɗa samar da abin da bitar bicike ba ta samar ba,
da kuma daɗa tabbatar da zalaƙar mawaƙin ta
hanyar binciken ilimi.
Taƙaitaccen
Tarihin Malam Sa’adu Zungur
An haifi Malam Ahmad Mahmud Sa’adu Zungur a cikin garin Bauchi a
cikin shekara ta 1914. Ya yi karatun Muhammadiyya. da na littattafai a garin
nasu. Ya yi karatunsa na Firamare a garin Bauchi/ Bayan nan, ya halarci
makarantar kwaleji ta Yaba da ke garin Legas a shekara ta 1934. Ya zama Malami
a wata makaranta a garin Zariya, bayan ya dawo daga garin Legas. Ya kafa
wata ƙungiya
mai suna Zariya friendly society tare da Malam Abubakar Imam da wasu abokansa
na wancan lokacin. Wannan ƙungiyar
da suka kafa, daga baya ta zama kamar ƙungiyar siyasa a yankin. Ta sha suka daga wajen wasu sarakunan
lokacin. (Ahmad 1968:2).
A shekara ta 1942, ya sake dawowa garin Bauchi inda ya cigaba da
harkar karantarwa. Bayan haɗuwa da suka yi da Malam Aminu Kano da Muhammad
Baba Halla na yin gwagwarmaya na yadda ake mulkin a yankin Arewa na wancan
lokacin, Malam Sa’adu Zungur Ya kasance sakatare na jam’iyyar
NCNC a shekara ta 1948. Ya yi rubuce-rubuce da dama a fannin adabin Hausa. Wasu
daga cikin waƙoƙin da ya rubuta sun haɗa da waƙar Maraba
Da Soja da Waƙar Bidi’a
da Waƙar ‘Yan
baka da ita wannan waƙar da ake
nazari, wato Arewa JUmhuriya Ko Mulukiya da sauransu. Ya kasance abin koyi ga
marubuta adabin Hausa kamar irinsu Malam Abubakar Ladan Zariya da sauran
marubuta. Ya rasu a shekara ta 1958 a cikin garin Bauchi. (Ahmad: 1968:2).
Wannan waƙa da aka
nazarta an same ta ne a cikin littafin marubucin da ya kira “Waƙoƙin Sa’adu Zungur” (1963). Littafi ne da yake ƙunshe da waƙoƙi guda huɗu ciki har da ita wannar waƙar, sai aka sake rubuta ta domin yin wannan bincike. Haka kuma an
karanta ta da yawa domin ƙara
fahimtar komai.
Babban jigon wannan waƙa shi ne faɗakarwa a kan kaucewa da daina wasu munanan ɗabi’u da
mutanen Arewa suke aikatawa da kuma yi musu gargaɗi a kan
makomar yankin kamar yadda marubucin ya tabbatar a wannan baitin:
Matuƙar yaranmu suna bara,
Allah ba ku mu samu abin
miya.
A gidan birni da na ƙauyuka,
Da cikin makarantun
tsangaya.
Sun yafu da fatar
bunsuru,
Babu shakka sai mun
sha wuya.
Wannan ya tabbatar gaba ɗayan
manufar da ya gina waƙar a
kanta dai shi ne faɗakarwa da yin gargaɗi a kan makomar yankin Arewa. Marubucin ya yi
amfani da wasu ƙananan
manufofi da dama waɗanda kuma su ne suka haɗu suka tabbatar da jigon waƙar.
Addinin Musulunci, kasancewarsa addinin gaskiya, ya shiga saƙo da lungu cikin al’adu da ɗabi’un al’ummar
Hausawa. Ba kasafai ake iya rarrabe da yawa
daga cikin al’adu da ɗabi’un
Hausawa da na addinin ba. Marubucin a cikin waƙar ya faɗakar, ya kuma tsawatar da ‘yan arewa
a kan wasu munanan ɗabi’u da suke aikatawa, da su nutsu, su daina tun
kafin yankin nasu ya lalace. A sabo da haka ne, ya ƙarfafi wannan magana da marubucin ya yi a kan al’ummar Arewa ta
hanyar hani da tsawatarwa. Wannan takarda ta yi
bayani ne a kan irin dangantakar da ke tsakanin tsoratarwa da hani da addini ya
yi a kan aikata munanan ɗabi’u, sannan da faɗakarwar
da jan kunne da marubucin waƙar ya yi
wa ‘yan Arewa a kan wasu ɗabi’u marasa
kyau da suke aikatawa. .
Dangantakar Al’adun Hausawa da na Addini a cikin waƙar Arewa Jamhuriyya ko Mulukiyya
-Dangantaka na nufin “’yan uwantaka” (CNHN: 2006:95).
-Ɗabi’a na
nufin ‘halim mutum ko al’adarsa’ (CNHN: 2006:116).
Gargaɗi shi ne “kashedi
ko horo” (CNHN: 2006:159).
-Faɗakarwa ita ce zaburar
da faɗakar da a sa mutum ya fahimta, a sanya mutum ya
gano wani abu na haƙiƙa wanda aka rigaya aka mance (Bargery 1934:288).
Kamar yadda maubucin ya bayyana cewa ‘yan Arewa ya kamata su farka
ganin irin matsalolin da ke tattare da yankin , shi ne ya gargaɗe su da su shiga taitayinsu, domin su daina. Wannan
gargaɗi da faɗakarwa da
marubucin ya yi, sai ya yi daidai da tsoratarwa da hani da addinin Musulunci ya
yi a kan aikata munanan ayyuka. Kusan dukkan matsalolin da marubucin ya bayyana
a cikin waƙar tun a
wancan lokacin game da ‘yan Arewa, yana kusan daidai da halin da yankin ya
tsinci kansa a ciki a yau. Matsalolin da malamin ya kawo sun haɗa da jahilci da karuwanci da bara da cin amana. Misali ya yi
Magana a kan halin ko in kula na rashin neman ilimi da ‘yan arewa
ba sa yi da rashin nuna hikima wajen zamantakewar rayuwa da kuma riƙon sakainar kashi da suke yi wa addinin
musulunci. Wannan ya sa abokanan zaman mu ‘yan kudu, suke yi mana kallon
wawaye.
Jahilci
Jahilci shi ne rashin sani ko kuma rashin iya karatu da rubutu
(CNHN 2006:211)
Akwai wasu karin maganar Hausawa da suka yi nuni a kan illolin
jahilci domin a zaburar da jama’a su shiga neman ilimi, su kuma yaƙi jahilcin. Misali, jailci ya fi hauka wuyar
magani da kuma wanda ake cewa ƙaramin sani ƙuƙumi, sai kuma mai nuna fa’idar ilimi da yake
cewa, ilimi, gishirin zaman duniya. Malam Sa’adu Zungur ya yi amfani da
hikimarsa ya faɗakarda al’ummar
Arewa kan illolin jahilci a cikin wasu baitukan waƙarsa kamar haka:
4. Jahilci ya ci lakarmu
duk,
Ya sa mana sarƙa har wuya.
5. Ya sa mana ankwa hannuwa,
Ya ɗaure ƙafarmu da tsarkiya.
6. Bakunanmu ya sa
takukumi,
Ba zalaƙa sai sharholiya.
7. Ya Allah kai mana agaji,
Don mu kauce kunyar duniya.
8. Ilimi mai amfani duka,
Inda addinmu ya rataya.
9. In fa addinmu ya
raunana,
Babu alheri nan duniya.
10. Mu dai ilimi muka
tambaya,
Ko a London ko a Arabiya.
Addinin musulunci, ya kwaɗaitar a
kan neman ilimi da kuma yaƙar
jahilci. Misali Allah ya ce “Ka ce shin waɗanda suke da ilimi da waɗanda ba
su da ilimi za su kasance daidai ?” (Alƙur’ani 39:9) (Muhammad 2021:231)
Sannan Annabi (SAW) ya ce “Neman ilimi wajibi ne ga kowane
Musulmi” Ibn Majah, Hadisi na 224
A wani hadisin Annabi (SAW) ya ce “ Duk wanda ya bi hanya
domin neman ilimi, Allah zai sauƙaƙa masa hanya zuwa Aljanna” ( Muslim Hadisi na 2699).
Idan aka yi la’akari da waɗannan
nassoshi sun nuna abin da Malam Sa’adu
Zungur ya yi gargaɗi kansa, daidai yake da yadda addinin Musulunci
ya nuna. Ba a son Musulmi ya zauna da jahilci domin zai iya auka kansa cikin
fitina mai girma kamar yadda yau yankin Areawa yake ciki.
Karuwanci
Karuwanci shi ne zaman mace maras miji da saduwa da maza don neman
kuɗi (CNHN 2006:236). Karuwanci yana ɗaya daga
cikin muhimman matsalolin da Sa’adu Zungur ya gargaɗi al’ummar Arewa a kansa. Karuwanci yake haifar da
samuwar wani rukuni na mutane marasa kunya a cikin gari kamar ɗan daudu
da magajiya da samari masu ruwan kuɗi da maroƙa da gidajen barasa. Idan waɗannan abubuwa suna cikin Arewa, babu shakka ɓacin rai
da damuwa ba zai bar mu ba, sannan zancen jagoranci ƙasa, sai dai mu ga ana yi. Ga abin da Malam Sa’adu yake cewa a
cikin waɗannan baitoci:
11.Matuƙar arewa da karuwai,
Wallahi za mu ji kunyar
duniya.
12. Matuƙar ‘yan iska na gari,
Ɗan daudu da shi da magajiya.
13. Da samari masu ruwan kuɗi,
Ga maroƙa can a gidan giya.
14. Babu shakka ‘yan kudu
za su hau,
Dokin mulkin Najeriya.
A shekarun baya da suka wuce, karuwai ba mutanen gari ba ne, baƙi ne suke zuwa, su kama wuri a sabon gari, wato
inda ƙabilu baƙi suke zaune, can waɗanda suke lalata da su suke zuwa. Yanzu lamarin sai ya canza salo,
ya zama ‘ya’yan gari
daga gidajen iyayensu, suke zuwa wurare daban-daban ake yin lalata da su, kuma
su dawo gidajen iyayen nasu, a wasu lokutan ma da sanin iyayen nasu.
Akwai ayoyin Alƙur’ani da
hadisan Annabi (SAW) masu yawa da suka yi tir da al’amarin zina. An yi hani
Musulmi ko namiji ko mace da kada ya kusantar zina. Allah ya ce “kuma
kada ku kusanci zina. Lallai ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga
zama hanya” Sura isra’I aya 32. Annabi SAW yana cewa “
Mazinaci ba zai yi zina ba a lokacin da yake mumini ba….Muslim ne ya
rawaito. Hadisi na 2342.
A yau tare da dukkan nassoshin Alƙur’ani da hadisai na Annabi (SAW), ‘yan iska sun yi yawa a yankin Arewa.
Wannan ba ya rasa nasaba da sakacin iyaye na halin ko in kula a kan ‘ya’yansu
da sakacin hukumomin Arewa da sauran al’umma baki ɗaya. Sanadiyar haka, a Arewa aka sami yara matasa masu yawa masu ƙwacen waya da garkuwa da mutane da shaye-shaye da harkar daba da
sace-sace wanda hakan ya janyo rasa rayuka da dama da koma baya ga yankunan
Arewa. Annabi (SAW) yana cewa “Dukkaninku masu kiwo ne kuma kowa sai an
tambaye ku abin da aka ba ku kiwo” Muslim ne ya rawaito Sahih Muslim.
Hadisi na 2134
Kawalci ya zama ruwan dare game duniya a ma fi yawan yankuna na
Arewa. Kawali shi ne mutumin da yake haɗa mace da
namiji ko namiji da namiji don su yi aikin assha. (CNHN 2006:241) ‘yan
siyasa da masu kuɗi da masu riƙe da madafun iko, suna amfani da kawalai su kawo musu yara maza da
mata su lalata, wanda wannan shi ma naƙasu ne ga yankin Arewa. Allah yana cewa “ Ku yi
temakekeniya wajen aikin alhairi da kuma aikin tsoran Allah, kada ku yi
taimakekeniya a cikin aikin saɓo da kuma
aikin ƙetare iyaka” Ma’ida: Aya ta 2. Annabi (SAW) yana cewa “Wanda yake nuni
a kan aikin alhairi kamar ya aikata ne haka wanda yake nuni ga aikin sharri shi
ma wannan kamar ya aikata ne” Tirmizi Sunan Tirmizi, hadisi na 34.
Daga nan, sai magana a kan almubazzaranci wato ɓarnar dukiya (CNHN 2006:15) Mafi yawan
masu hannu da shunin yankin Arewa ba su
cika yin taimako ta hanyar samar da abin yi ga masu rauni da
talakawa da yara da suka kammala karatu ko ɗaukar nauyin su yi karatu ko
taimakon ‘yan uwa da sauransu. Baya ga haka, a wasu
lokutan, sukan yi abin da ba shi da muhimmanci sosai domin neman suna ko neman
burgewa. Hakan ya sa ɓarna da matsaloli sun yi yawa a yankin. Allah
yana cewa a cikin suratul Isra’I “kada ka
yi almubazzaranci, lallai masu almubazzaranci sun kasance ‘yan uwan shaiɗan ne” Aya ta 26
Annabi SAW ya yi hani a kan almubazzaranci ko da yana
gaban ƙorama ne
mai gudana to kada ya yi almubazzaranci” Buhari, hadisi na 2345
Ga matsalar roƙo wanda
yake nufin neman kyauta daga wani (CNHN 2006:374) Yankin Arewa, kusan ya fi na
ko’ina yankin ƙasar
Nijeriya matsalar roƙo. Roƙo a al’ummar Arewa ta zama ruwan dare da ya game
duniya. Manya da yara, maza da kuma mata. Wannan abu ya sa wasu mutane da yawa
zuciyarsu ta mutu, sun rasa wadatar zuci da tawakkali. A Masallaci roƙo, a kasuwa roƙo, a kan hanya roƙo ba ga
yara ba, ba kuma ga manya ba. Wannan kaɗai ta isa
ta zama babbar masifar da Arewa za ta shiga halin ni ‘ya su.
Annabi SAW yana cewa “Dayanku ba zai gushe ba yana roƙo, har sai ya gamu da Allah Maɗaukakin Sarki babu gutsiran nama a fuskarsa” Buhari da Muslim suka rawaito. Sahih Muslim,
hadisi na 275
Bara
Bara na nufin neman sadaka daga wurin mutane (CNHN 2006:37. Bara
na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka
dabaibaye yankin Arewa. Wasu daga cikin mutanen Arewa sun mayar da bara wani
abu na addini wanda ya sa suke tura yaransu ƙanana
zuwa wasu garuruwa da sunan karatu ba tare da guzuri ba. Waɗannan yara sai ya zama sukan ware da bara gida-gida, wasu kuma su
tsinci kansu a sace-sace da sauran miyagun ayyuka. Haka kuma bara ya haddasa
faruwar wasu matsaloli a cikin yankin Arewa da suka haɗa da yawaitar masakai da malaman duba da tsafi da camfe-camfe da
alfahari da girman kai da ƙarya da kuma rashin sada zumunci a tsakanin ‘yan
uwa da maƙota.
Malam Zungur ya ambaci waɗannan matsaloli kamar haka::
1. Matuƙar
yaranmu suna bara,
Allah ba ku mu samu abin
miya.
2. A gidan birni da na ƙauyuka,
Da cikin makarantun
tsangaya.
3. Sun yafu da fatar bunsuru,
Babu shakka sai mun sha
wuya.
4. Matuƙar da
masakai barkatai,
Da makaho ko da makauniya.
5. Birni ƙauye da
garuruwa,
Duk suna yawo Najeriya.
6. Kai bahaushe ba shi da zuciya,
Za ya sha kunya nan duniya.
7. In ko in kudu sun ka hau,
Babu sauran daɗi daɗa kowa zai sha wuya.
Bara ita ce neman sadaka daga wurin mutane (CNHN: 2006:37) A nan
marubucin yana so ya bayyana illar tura yara da iyaye suke yi da sunan karatu
daga ƙarshe su
yaran su ɓuge da yin barace-barace da sauran abubuwa na ƙasƙanci a
wuraren da aka tura su karatun. Wannan nau’i na bara ya canza salo, ma fi ya
yawan makafi da guragu ko kutare da suke yankin Arewa zuciyoyisu sun mutu.
Nakasa ba ta kai a yi bara basai su fara, Mata tsofaffi daga karkara su ma bara
daga nan har kudancin ƙasar,
wani lokacin a kan yi amfani da su wajen tsafi ko kuma a kashe su idan
rigimar ƙabilanci
ta ɓarke ko wasu dalilai mabambamta. Haka kuma, a
cikin al’ummar mu da yawa daga cikinmu zuciaya ta mutu,
za ka ga mutum da ƙarfinsa amma yana bara a masallatai da kasuwanni
da wuraren shaƙatawa da
sauransu, tabbas ba ƙaramin ƙasƙanci ba ne ga yankin mu arewa ba, Musulunci ya tsawatar a kan
illar yin bara, Misali Annabi SAW yana cewa “Ya fi kyau ga mutum ya saɓi gatari, ya hau kan dutse ya yi wo itace, ya ɗauka ya
sayar, da ya tsaya wajen mutane ya roƙe su sun bashi ko sun hana shi.Muslim (1425/2004: 1042) Babin ƙin roƙon Mutane.A wani hadisin yana cewa” ɗayanku ba zai gushe ba yana roƙo, har sai ya gamu da Allah maɗaukakin sarki babu gutsiran nama a fuskarsa.Buhari da Muslim suka rawaito
Wata matsalar kuma ita ce ta yawaitai malaman duba a yankin na
Arewa, ya yi sanadiyar ko ya haifar da tsafe-tsafe da camfe-camfe a yankin, shi
ma wannan babbar matsala ce a yankin, musammaan wajen rashin dogaro da Allah.
Hadisin Anas Annabi SAW yana cewa” Babu kamuwa da cuta, haka nan babu
camfi a cikin musulunci. Wato wani ya shafawa wani cuta. Kakkyawar fata
yana ƙayatar da
ni. Sai sahabbai suka tambaya menene kyakkkyawan fata? Sai ya ce kyakkyawar
Magana” Buhari da Muslumu suka
rawaito. A wani hadisin Annabi SAW yana cewa” ku kiyayi abubuwa guda bakwai
masu hallakarwa. Sai sahabbabi suka tambayi Annabi ko menesu? Sai ya ce Na
farko shirka da Allah, da kuma tsafi da kashe ran da Allah ya haramta a kashe
ta da cin riba da cin dukiyar maraya da juya baya a ranar gumurzu da yi wa
mumina katangaggiya rafkananniya daga aikata alfasha yi mata ƙazafi. Buhari da Muslumi suka rawaito hadisi na 3452
Dangane da malamin duba kuwa, Annabi SAW ya ce “Duk wanda
ya je wajen malamin duba kuma ya gasgata shi a kan abin da yake faɗa, haƙiƙa ya kaficewa abin da aka saukarwa Annabi
Muhammad. Muslumu ne ya rawaito
(Sahih Muslim:342)
Rashin Zumunta
Zumnta tana nufin kyakkyawar dangantaka ta jinni ko ta aure ko
kuma ta abota tsakanin mutum da mutum (CNHN 2006:496). Zumunta na ɗaya daga cikin muhimman abubuwa da ba a son mutane su yanke.
Zumunta a ƙafa take in ji Bahaushe. A al’ummar Hausawa ana
son mutane su riƙa
ziyartar juna, suna duba lafiyar junansu. Haka kuma, zumunta tana ƙara danƙon so da ƙauna da
tausaya wa juna. Idan mutane suka daina ziyartar junansu domin zumnuci, suka
yanke ta, al’amurransu za su lalace, ƙiyayya ta ƙaru
tsakaninsu. Malam Sa’adu Zungur ya gargaɗi al’ummar
Arewa kan sakaci da suka yi suka kashe zumunta da take tsakaninsu. Ga abin da
yake cewa da kuma abin da hakan ya haddasa
1. Arewa zumunta ta mutu,
Sai nishaɗi sai sharholiya.
2. Sai alfahari da yawan kwafe,
Girman kai sai ƙwambom tsiya.
3. Camfe-camfe da tsubace-tsubbace,
Malaman ƙarya ‘yan damfara.
Sai ƙarya sai
kwambon tsiya, Sai hula mai annakiyada.Matsalar rashin sada zumunci a tsakanin
‘yan uwa da maƙota, ya
zama ruwan dare a cikin al’ummar Arewa, abin da ya haifar da rashin tausayi da
taimakon junaAnnabi (SAW) yana cewa” Duk wanda yake so a yalwata masa a cikin
arzikinsa, a jinkirta masa a cikin gurbinsa, ya sadar da zumuncinsa. Buhari da
Muslim. Buhari: 2211
Wasu matsaloli da suke tare da rashin sada zumunta su ne alfahari
da girman kai da kuma ƙarya
kamar yadda marubucin ya bayyana a cikin waƙar. Dukkan waɗannan abubuwa da aka ambata, Musulunci ya
tsawatar da waɗanda suke aikata su. Misali, Annabi (SAW) yana
cewa “Abubuwa guda huɗu duk wanda ya kasance a cikinsu, to tabbas ya kasance tataccen
munafiki. Wanda kuma yake da wata ɗabi’a daga
cikinsu, ya kasance yana da wata ɗabi’a ta
munafunci. Na farko idan ya yi zance sai ya yi ƙarya, idan aka amince masa sai ya yi ha’inci,
idan ya yi alƙawari sai
ya yi yaudara, idan aka yi husuma da shi, sai ya yi fajirci. Bauhari da Muslim ne suka rawaito. (Sahih
Buhari: 3452).
Dangane da girman kai kuwa, Annabi SAW yana cewa” Duk wanda ya
kasance a zuciyarsa akwai misalin ƙwayar zarra na girman kai, ba zai shiga Ajanna
ba. Sai wani mutun yake cewa, ya Rasulillahi aiko mutum yakan so tufafinsa mai
kyau da takalminsa ma mai kyau, sai Annabi ya ce Allah kyakkyawa ne, kuma yana
son abu mai kyau. Girman kai shi ne ƙin gaskiya da raina mutane” Buhari da Muslim.
(Sahih Buhari : 2312)
Cin Amana
Cin amana a wannan takarda yana nufin ka yarda da mutum ta hanyar
ba shi ko faɗa masa wani abu na sirri, amma ya karya. Cin
amana abu ne mai muni a zamantakewar jama’a, kuma
mai haddasa rashin jituwa da naƙasa
cigaban ƙasa.
Malam Sa’adu Zungur domin ya ƙara fito da jigonsa na faɗakarwa da
gargaɗi ga aikata munanan aiyuka da ‘yan Arewa
suke aikatawa, ya ƙara fito da mummunan ɗabi’ar nan ta cin amana abin da yake haddasa ayyukan
riya da ƙarya da yawan rantse-rantse da zalunci da zamba
da kuma gulma. Misali kamar yadda ya ambata a cikin waƙarsa:
1. Cin amana kuma da yawan riya,
Ga hula mai anakiya.
2. Babu mai aiki bisa hankali,
Da basira don ya ga
gaskiya.
3. Rantse-rantse da Allah yai yawa,
Ga ƙarya ga zambar tsiya.
4. Sai kinibibi sai kwarmato,
Ga gulma da son ƙullalliya.
Tun a wancan lokacin, cin amana ya zama ruwan dare a tsakanini
al’ummar yankin Arewa, wannan ne ya sa marubucin yake gargaɗinsu da su daina saboda ba ɗabi’a ce mai
kyau ba. Annabi SAW yana cewa “Alamomin munafukai uku ne idan ya yi
zance sai ya yi ƙarya,
idan ya yi alƙawari sai
ya saɓa, idan aka amince masa sai ya yi ha’inci” Buhari da Muslimu ne suka rawaito. Buhari:1234.
A wani hadisin Annabi SAW yana cewa “Dukkaninku masu kiyo ne kuma kowa
sai an tambaye shi abin da aka ba shi kiwo” Buhari da Muslim. Buhari:354.
Haka kuma, cin amana tana haifar da riya wato yin abu ba domin
Allah ba, sai domin a yabi mutum. Annabi (SAW) yana cewa” Ma fi tsoron
abin da na ke jin tsoro ga al’ummata shi ne ƙaramar shirka. Sahabbai suka ce mene ƙaramar shirka ya Rasulilla? Sai Annabi yace
riya” Imam Ahmad da Imam Tirmizi
suka rawaito. Littafin Tirmizi 234
Bayan wannan kuma sai yawan rantse-rantse da babu gaira, babu
dalili da kuma yawan ƙarya a
kowane lokaci. Allah ya ce “Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, wulaƙantacce” (Suratul Ƙalam aya
ta 10). Annabi (SAW) yana cewa “ Mutum uku Allah ba zai magana da su ba
ranar ƙiyama, ba
zai kalle su ba kuma ba zai tsarkake su ba kuma suna da azaba mai raɗaɗi. Annabi SAW ya maimaita haka sau uku, Sai Abu
Zarril Gifari ya ce su wanene waɗannan ya
Rasulillahi? Sai Annabii SAW ya ce mai jan tufafinsa a ƙasa da mai yin gori da kuma mai ɗaga farashin kadararsa ta hanyar rantse-rantse. Muslim da Tirmizi
da Nisa’I sun rwaito wannan hadisi. Muslim:432.
Baya ga haka da yawa daga cikin mutanen Arewa, sun lalace wajen
yin ha’inci da zamba da zalunci. Annabi (SAW) yana cewa” Duk wanda yake mana
zamba to ba ya daga cikinmu” Muslimu ne ya rawaito. Muslim:233
Sannan, ya yi musu gargaɗi wajen
haɗa husuma a tsakanin al’ummaa.
Babu mai son haɗa rigima saboda son zuciya, sai shaiɗani A wani hadisin yana cewa “
“Ku kiyayi son kanku, domin shi ne ya halakar da waɗanda suka zo gabaninku “. Muslim ne rawaito (Muslim : 2984)
Babin haramcin zalunci.
Kammalawa
Daga ƙarshe
babban jigon wannan waƙa mai
suna ‘Arewa Jumhuriyya ko Mulukiyya ta Sa’adu Zungur shi ne faɗakarwa. Takardar ta yi tsokaci ne a kan irin dangantakar da ke
tsakanin tsoratarwa da hani da addini ya yi a kan aikata munanan ɗabi’u, da faɗakarwar
da jan kunne da marubucin waƙar ya yi wa Hausawa na yankin Arewacin Najeriya a kan wasu ɗabi’u marasa kyau da suke aikatawa. Daga cikin
munanan ɗabi’un da binciken ya gano akwai rashin mai da
hankali wajen neman ilimi da taɓarɓarewar
tarbiya da kawalci da almubazzaranci da gulma da
hassada da baƙin ciki
da cin amana da camfi da ƙarya da
roƙo da fariya da sauransu. Wannan dalili ne ya sa
marubucin waƙar ya faɗakar da ‘yan Arewa tare da jan kunne ta lisssafo
irin illolin da suke tattare cikin halin da suka tsinci kansu tun a wancan
lokacin, wato kamar ma dai a wannan lokacin ya wallafa waƙar
Manazarta
Abdulƙadir, Ɗ.
(1979) Zaɓaɓɓun waƙoƙi na da da na yanzu. Kano Thomas Nelson Nigeria Limited
Aliyu, I. F. (2011) Manufar Waƙa a Siyasa: Ire-iren Jigogin Waƙoƙin Siyasa na Hausa. Algaita Journal of Current Research in Hausa
Studies, Depatment of Nierian Languages and Linguistics Bayero University,
Kano.
Bargery, G. P. (1934) Hausa- English Dictionary
and English-Hausa Vocabulary. London. Oɗford
University press.
Muhammad, S.U.R. (2021) Fayyataccen
Bayani na Ma’anoni da Shiriyar Alƙur’ani Ɗab’I na 1-6. kano. Markaz Imam Buhari
Bello, S. (2002) Tasirin Larabci a kan
Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Hausa language. Literature and
Culture. The fifth Hausa International Conference. Centre For the Study of
Nigerian Languages, Bayero University. Kano.
C.N.H.N. (2006) Ƙamusun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press. CSLN kuma. Ba haka aka
rubuta cikin takarda ba. Bah aka yake ba. A ƙara dubawa
C.S.N.L. (1977) Sabon ƙamus na Hausa zuwa Turanci. Ibadan University Press PLC CSNL a duba
bayanan sama
Ɗangambo, A. (2007) Ɗaurayar Gadon Feɗe waƙa [sabon
tsari] KanoK.D.G.
Publishers
Gusau, S. M. (1983) Waƙoƙin Noma na Baka: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Algaita
Journal of current Research in Hausa. Deparment of Nigerian Languages. Bayero
University Kano. Vol. 1, No 1
Otite, O. and Ogionwo, W. (1981) An Introduction
to Sociological Studies. New York: noatrand
Husaini, H. (2024) Salon Amfani da Nassi a Waƙoƙin Hausa: Misalai daga wasu Waƙoƙin
Gwagwarmaya. Festschrift in Honour of Professor Salisu Ishaƙ Ja’afar (1964-2022) Department of African Languages, College of
Humanities, Alƙalam
Uniersity, Katsina.
Newman, R. M. (1997) An English Hausa
Dictionary. Lagos: Nelag Press Ltd.
Newman. P. and Roɗana, M.
N. (2020) Hausa Dictionary (Ƙamusun
Hausa) Kano, Bayrro University Press, Main Library Building.
Umar, A. (2002) Metaphor, Meaning and Message in
the Religious Poetry of Aliyu Namangi. Hausa language. Literature and
Culture. The fifth Hausa International Conference. Centre For the Study of
Nigerian Languages, Bayero University. Kano.
Yahaya, A. B. (1997) Jigon nazarin waƙa. Kaduna. Fisbas Media Services.
Bargery, G. P. (1934) Hausa- English Dictionary
and English-Hausa Vocabulary. London. Oɗford
University press.
C.S.N.L. (2006) “Ƙamusun Hausa” Ahmadu Bello University Press, Zaria.
Tijjani, S. A (2011) Jigon Faɗakarwa da Ban dariya cikin waƙoƙin Tashe.
Algaita Journal of current Research in Hausa Studies. Department of Nigerian
Languages and Linguistics. Bayero University Kano, vol 2, No 1, series vii.
Ahmad. M.S. (1976) Waƙoƙin Sa’adu Zungur, Zaria.Ahmadu Bello University Press.
(2007) Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa [Sabon
Tsari]. K.D.G.
Publishers Kano.
Yahaya, A. B. (1997) Jigom nazarin waƙa. Kaduna. Fisbas Media Services.
OxfordAdvanced Learner’s Dictionary (2015) New
York, OxfordUniversity Press.
Ahmad, M. S. (1968) Waƙoƙin Sa’adu Zungur, Zaria, NNPC
Buhari, I. (1426/2005) “Sahih Buhari”
Darul kutbul Ilmiyya Bairut Lubnan.
Muslim, I. (1425/2004) “Sahih Muslim”
Maktabatu Nizaru Masɗafal Baz.
Abu Dawud, I. (1424/2003) “Sunan Abu Dawud”
Darul Fikr.
Tirmizi, I. (1430/2009) “Sunan Tirmizi”
Darul Fikr.
Ibn Majah, I. (1432/2011) “Sunan Ibn
Majah” Maktabatu Nizarul Musɗafal Baz.
Naisaburi H. (2003) “Almustadraku alal
Sahihaini” Maktabatu Sham’iyya. Lebenon.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.