Citation: Baba Mohammed SHEHU (2024). Nason Addinin Musulunci A Cikin Surkullen Hausawa. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 12, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
NASON ADDININ MUSULUNCI A CIKIN SURKULLEN
HAUSAWA
Na
Baba Mohammed SHEHU
Tsakure
Wannan maƙala, nazari ne a kan
nason addinin Musulunci cikin surkullen Hausawa jiya da yau Bincike ne da ya
karkata ga sha’anin ire-iren surkulle da suka shafi rayuwar sauran jama’a, An
bayyana waɗansu muhimman lamurra ne na rayuwa kan yadda Hausawa ke amfani da kalmomin
surkulle da suka danganci zamantakewa a gargajiyance wanda hakan ya fito da
nason surkulle cikin addinin Musulunci a sarari. Yayin tattara bayanai, an yi
amfani da hanyoyin hirar baki da baki tare da jama’a Hausawa da kuma karantawa
daga rubutattun bayanai. An ɗora wanan binciken a kan ra’in An yi amfani da Ra’in
“Bazuwar Al’adu’’. Wasu masana na kiran sa da Diffusionism Theory of
Culture. Wannan ra’i yana bayyana yadda wata al’ada take tasowa , ta bazu zuwa wata
al’ummar da babu wannan al’adar. Binciken ya gano cewa, akwai ire-iren surkulle da Hausawa ke yi ba tare da
haɗawa da magani ba a fannonin rayuwa ta fusrkar mutuwa da takaba da fatalwa,
da shiga ɗaki da shiga banɗaki da makoki da neman tsari daga mutumin da
ake shakkarsa da kuma abin da ya shafi rayuwar lahira.
Fitattun Kalmomi: Addini, Naso, Musulunci, Surkulle, Tsari
1. 0 Gabatarwa
Wannan maƙala an yi ƙoƙari ne a bayyana yadda addinin Musulunci ya yi
naso cikin surkulle. An bayyana naso da cewa, bazuwar wasu abubuwa ne, ko
shigar wani abu a cikin wani bagire.CNHN (2006:357). Shi kuwa addinin Musulunci
shi ne addinin da Musulmi suke bi na bauta wa Allah shi kaɗai babu tarayya da
shi kuma Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Manzonsa
ne. CNHN (2006: 353-357).
Tattare da haka, an lura cewa, addinin
Musulunci addini ne da yake ta samun ci gaba cikin lamuran rayuwar al’umma.
Wannan kuwa ya haɗa har da lamuran da suka shafi ɓangarorin al’adun
Hausawa da suka haɗa da surkulle, magunguna, da sauransu. Wato dai, addinin
Musulunci yana iya shiga sassa daban-daban cikin al’amuran rayuwar Hausawa.
A ɗaya ɓangare kuma, shi ma lamarin surkulle ya fantsama a tsakanin
al’umma wanda ya sanya bazuwarsa zuwa ɓangarorin rayuwa da dama da suka
haɗa da tsibbu da Bori da sauran al’amuran rayuwa daban-daban. Binciken zai
mayar da hankali ne kan shigar addinin Musulunci cikin surkulle na gama-gari.
Wato za a bayyana yadda Musulunci ya yi naso cikin surkullen da Hausawa ke
aiwatarwa da suka jiɓanci sha’anin mutuwa da takaba da lamuran lahira da tsari
da sauransu. Sai dai za mayar da hankali kan surkulle wanda mutanen gari wanda
maza da mata tsofi masu tallar magani (‘yarmai ganye) ke yi.
Surkulle wani katafaren
lamari ne da Hausawa suka runguma, kuma suke yin sa, a rayuwarsu ta yau da
kullum. Wannan ya sa aka samu masana da suka bayyana fahimtarsu daban-daban kan
ma’anar surkullen. Da farko, an bayyana ma’anar surkulle da cewa:
Surkulle na kasancewa wasu
nau’uka na surutu, ko surutai da za a yi, a riƙa yin luguden kalmomi masu
sauti ɗaya, masu kama da juna ga ma’ana, da furuci, ana jujjuya suana
sassarƙar dasu, ana saƙar harrufa, ana ƙulle su yadda ake so, kamar
bakin da ke furta su a cikinsa aka halitta su.” (Bunza 2006:226).
A nan, za a ga cewa, an
bayyyan surkullen bisa yadda ake furta kalmominsa.
Sai dai kuma a cikin Longman Dictionary of
Contemporary English (1978:820), an bayyana surkulle a matsayin:
“Special words that someone uses in magic, or the art of saying these words.”
Fassarar mai bincike: Surkulle kalmomi ne na musamman da mutum kan yi amfani da
su yayin aiwatar da tsafi, ko dabarar bayyana kalmomin tsafin.
Bisa ga wani ra’ayin kuwa, an bayyana surkulle
da cewa, lafuza ne da ake furtawa na jahiliyya da Hausawa ke yi mai kama da
adu’a da suka ƙunshi sautuka marasa ma’ana waɗanda ake yin
amfani da su a matsayin mahaɗin magani wajen ɗiban magani, ko sarrafa shi.
(Gobir, 2012:261)
Haka nan, an bayyana
surkulle da cewa, wasu tarin kalmomi ne masu sauti kusan iri ɗaya da akan
furta domin biyan bukata a wajen mabuƙata ba tare da yin la’akari da ma’anar da
suka ƙunsa ba. (Almajir, 2009: 82). A nan, ke nan masu yin
surkulle sukan yi amfani da kalmomi ne waɗanda suke ba fitattu ba yayi furta
kalaman surkullen.
Haka nan, an bayyana cewa, surkulle shi ne yin
magani ta hanyar furta wasu addu’o’i marasa kan gado da ba su da ma’ana da kuma
maimaita faɗinsu. C.S.N.L. (2006: 413). A nan ma, ke nan masu yin surkulle na
amfani da kalmomi waɗanda suke ba fitattu ko sannanu ba.
A fahimtar wani masanin kuwa, cewa ya yi: Shi
surkulle abu ne da yake cike da wasu kalmomi, ko lafazuzzuka, waɗanda suke masu
wuyar furtawa, masu ƙarangiya tare kuma da rikitarwa, musamman
a ƙoƙarin fahimtar
ma’anoninsu da madosarsu. (Adamu, 2014:123).
Bisa ga fahimtar mai
bincike, surkulle furta kalmomi ne, ko lafuza da ake yi da baka masu wuyar
hardacewa da ake surka harsuna daban-daban yayin aiwatar da wata bukata kamar
sihiri, ko siddabaru, ko neman biyan wata bukata da ta danganci lamuran rayuwa.
Surkulle idan aka tantance,
ana iya duban surkukulle ya zuwa nau’o’i daban-daban. Tattare da haka, an
bayyana da cewa, ana iya kallon surkullen ya zuwa nau’i biyu. Akwai surkullen
gargajiya da kuma surkullen zamani. Surkulle na gargajiya shi ne wanda Bahaushe
ya gada tun gabannin saduwarsa da wani addini a doron ƙasa. Surkullen zamani kuma
shi ne wanda wani sashe daga cikin sassansa ya sami tasirin ko nason baƙuwar al’ada.
1.1 Asalin Surkulle
Masana da dama sun tufa
albarkacin bakinsu a kan abin da ya shafi asalin kalmar surkulle. Masanan sun
haɗa da Bunza, (2006) da Almajir, (2009) da Gobir, (2012) da sauransu. Abin
lura na farko shi ne, akwai ra’ayin da ke nuni da cewa, asalin kalmar surkulle
ta Hausa ce, mai ɗauke da tushe biyu, wato`sur’ da `ƙulle’. A nan, tushen `sur’
ya yi daidai da tushen kalmar surutu, wanda a fahimtar wasu, surkulle
kan ɗauki ma’anar surutu, sai kuma gaɓoɓin `ƙulle’, sun yi daidai
da ƙulli na magani da ake yi na
gargajiya warkarwa. (Bunza, 2006:226).
Wasu masana sun bayyana
cewa, asalin kalmar surkulle daga Larabci aka same ta, wato asalin surkulle
kalmomi ne na Larabci guda biyu, wato `surru’ manufa ɓoyayyen abu. Sannan
`kullu’ kuma ke nufin ga baki ɗaya. A nan, ke nan wannan ba ya rasa alaƙa da irin yadda tsarin
kalmar surkulle take saboda maganganu ne waɗanda mai furta su da wanda ake faɗa
wa ba lallai ba ne su iya fahimtar abin da suka ƙunsa. Don haka a nan, ke
nan dukkansu sirri ne, babu wanda ya sani. (Almajir, 2009:81)
A wani ra’ayi kuma an
bayyana da cewa, ita wannan kalma ta surkulle, ta samo asali ne daga al’ummar
Fulani ta dalili cuɗanya, ya sa Hausawa suka aro ta. Wato surkulle suna ne wanda
asali ake furta shi da `saraakule’ (ko surkulleji). Ita kuma kalmar saraakule,
suna ne wanda asali aka san Soninke da shi. Soninke kuwa, wata daɗaɗɗiyar ƙabila ce a Afirka ta Yamma,
wanda a halin yanzu take Jumhuriyyar Mali. Su waɗannan mutanen Soninke (ko
Saraakule), su suka kafa daular Ghana, wato abin nufi, su ne ƙabila mafi daɗewa a Afirka
ta Yamma. ( Shehu, 2002: 6-7).
Don haka, ya kasance su ne
suke yin sihiri ko ma’amala da sihirce-sihirce da ake yi a ƙasar, da kuma sanin dukkan
sirrin tsafe-tsafe. Ko da yake mafi yawancinsu sun karɓi addinin Musulunci. Sai
dai sun yi ƙaurin suna wajen yin
sihirce-sihirce. Wannan dalili ne ya sa sauran ƙabilun da ke zaune wurinsu
suke zuwa a yayin da suke so a yi musu wani taimako na biyan buƙatunsu.
Surkulle a wannan lokaci
wani ɓangare ne da suke amfani da shi a matsayin wani kadarko wajen saduwa
da iskoki. Wannan shi ne dalilin da ya sa wannan suna surkulle ya zama mai
ma’ana iri ɗaya da surkulle a tsakanin Fulani a ƙasar Mali (Melle) har zuwa
Arewacin Nijeriya. Cuɗanyar Fulani da Hausawa ya sanya Hausawa aron kalmar
surkulle. Hausawa sun are ta ne sai ta zama daban a bisa ƙirarta. Wato sai suka yi
mata kwaskwarima (gyaran fuska) ta zama surkulle. A bisa ga wannan ra’ayi ke
nan, yana nuna cewa, surkulle abu ne da ya zo tun kafin zuwan Musulunci ƙasar Hausa, wanda a yau
Bororo suke bi. Fulani makiyaya ko da yake musulmai ne, su ma suna yin surkulle
amma waɗanda suka fi ƙwarewa su ne Bororo. Daga cikinsu kuwa ”
Kitije” su suka fi kowaɗanne shahara wajen yin surkulle. (Shehu, 2012: 10-12)
A wata mahanga kuwa,
Almajir, (2009: 81) da ya ambato Ibrahim, (2002), an nuna cewa, asalin surkulle
ya samu ne ta dalilin masu bayar da magani na yin kore ga magani da suke
bayarwa.
Wato sukan yi amfani da
ayoyin Alƙur’ani, manufa sukan zaɓi
wata aya ta Alƙur’ani da ma’anarta ko
sautinta ya zo daidai da ma’ana, ko buƙatar da ake nema sai su yi amfani da harrufan
idan suka yi kama da wata magana ta Hausa. Daga haka sai aka ƙirƙiri kalmomin surkulle.
Surkulle a bisa ra’ayoyi da
aka ambata, ke nan ana iya cewa, abu ne da aka samo ta hanyar kitsa kalmomi
kuma ake yi a tsakanin al’ummomi daban-daban bisa waɗansu buƙatoci na rayuwa.
1.2 Surkullen Hausawa Jiya
da Yau
Surkulle dai al’ada ce mai
cin gashin kanta a cikin falsafar Bahaushe. Haka kuma kamar yadda kowace
al’umma ta duniya take da fuskoki na tsarin zamantakewa da kuma rayuwa
daban-daban, haka nan Hausawa ma suna da nasu al’adu na musamman. Haka nan,
suna da al’adu da ɗabi’u iri daban-daban. Daga cikin irin waɗannan al’adu
da ɗabi’u, surkulle yana da muhimmiyar rawa da yake takawa. Wato shi
surkulle wata al’ada ce tun da can ana yin sa, duk da cewa addinin Musulunci ya
yi tasiri. Haka kuma Bahaushe yakan fari wata al’ada ko ɗabi’a da nufin
inganta rayuwarsa to amma sai ya zamana a wani lokaci wannan al’adar
ko ɗabi’ar ta zama koma-baya yayin da aka samu wani sauyi da ci gaba na
zamani, musamman ma sauyi na addini. Sannan kuma abu ne da aka sani cewa, zuwan
Addinin Musulunci ya kawo sauye-sauye a cikin rayuwar Hausawa da al’adunsu.
Matsayin surkulle a cikin
al’adar Hausawa abu ne da yake da daraja a da. An lura cewa, kamar yadda
bokanci da sauran al’adu suka samu zama da gindinsu a da, tsakanin al’ummar
Hausawa , haka nan ga lamarin surkulle ya samu gindin zama. Wannan kuwa ya faru
ne saboda waɗanda jahilcin ilmin addinin Musulunci bai fita daga gare su ba.
Duk da cewa suna riƙo da addinin Musulunci amma ba su da wata wadatacciyar
wayewa ta addini, sai ya zama sukan karantar da mutane kalaman surkulle a
matsayin wata hanya ta samun ilmi na addini. Da haka surkulle ya ci gaba da
samun tasiri da ci gaba a zukatan Hausawa. Sannan daga haka aka samu cuɗanyar
kalaman addini suka shiga cikin sha’anin surkulle. Wato a wannan lokaci an ci
gaba da samun waɗanda suka amince da surkulle a matsayin hanyar koyon ilmi da
samun tarbiyya.
2. 0 Hanyoyin Tara Bayanai
Yayin gudanar da bincike na
ilmi, ana iya amfani da dabaru daban-daban domin a tara bayanai. Don haka, a
wannan bincike, an tattaro bayanai ta yin amfani da hanyoyi guda biyu. Da
farko, an yi hirarraki kai tsaye da jama’a daban-daban a ƙasar Kano; musamman a
garuruwan Wudi da Gaya da Kura da sauransu domin tattaro ire-iren surkulle
waɗanda ake jin cewa, addinin Misulunci zai iya naso a cikinsu, a samu biyan buƙatu da suka shafi tsari da
kariya da sauransu.
Haka nan, an yi amfani da
hanyar karance-karance. Tattare da wannan, an karanta wallafaffun littattafai
da kundayen bincike na matakan digiri daban-daban. Haka nan, an karanta muƙalu da jaridu da takardu da
aka gabatar a tarukan ƙara wa juna ilmi, masu da nasaba da wannan
bincike.
3.0 Ra’in Bincike
Ra’i wani awo ne na mizani
da akan yi amfani da shi ga aikin bincike na ilmi domin samar da haske kan wani
al’amari da ake iya gani. Wato wani ilmi ne wanda ke yin bayani game da lamari
da ba a tantance matsaya a kansa ba amma idan aka duba lamarin, ana iya ganin
haƙiƙanin gaskiyarsa a sarari.
Don haka, ra’i ma’auni ne wajen raba gardama a fagen ilmi ko bincike (Ado,
2019:126).
An yi amfani da Ra’in
“Bazuwar Al’adu’’. Wasu masana na kiran sa da Diffusionism Theory of
Culture. Wannan ra’i yana bayyana yadda wata al’ada take tasowa , ta bazu zuwa wata
al’ummar da babu wannan al’adar. Haka nan, ra’’in bazuwarr al’adu, ra’i ne mai
yin nuni da cewa, al’adun wata al’umma kan iya kwatanta al’adun al’ummomi biyu
saboda a gano dalilai da suka kawo bazuwar al’adun wata al’umma zuwa wata, ko
tasirin cuɗanyar al’adun wata al’umma cikin wata.
4. 0 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Hausawa
Wannan sashe kuma za a yi bayanin ire-iren
surkulle waɗanda addinin Musulunci ya yi naso a cikinsu, waɗanda ba su danganci
haɗawa da magani ba. Wato ɓangare ne da za a bayyana ire-iren surkulle da
suka shafi sauran al’amuran rayuwar jama'a waɗanda suke ba na ayyukan masu ba
da maganin gargajiya ba kamar bokaye da ‘yan tsibbu da maƙera maɗora da sauransu.
A ƙarkashin wannan kashi,
za a fito da ire-iren surkulle waɗanda addinin Musulunci ya yi naso da suka
shafi mutuwa da takaba da tattalin lahira da zaman makoki da kuma na fatalwa da
kuma tsari daga ire-iren mutanen da suke ba a yarda da su ba, ko don gudun ka
da su cutar.
Surkulle ya yi tasiri sosai kan waɗannan
al’amura da aka ambata a ƙasashen Kano da kuma Katsina. Waɗannan surkulle
sukan bambanta a waɗannan yankuna na Kano da Katsina, wato ya danganta daga
wuri zuwa wuri.
Ire-irern surkulle da addinin musulunci ya
yi naso a cikinsu sun haɗa da:
Addinin Musulunci ya yi tasiri sosai kan
waɗannan Surkulle, ko al’amura da za a ambata a ƙasashen Kano da kuma Katsina. Waɗannan surkulle sukan bambanta a
waɗannan yankuna na Kano da Katsina, wato ya danganta daga wuri zuwa wuri.
4.1. Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen Jin
Labarin Wani ya Mutu
Wannan surkulle ne da ake yi a sakamakon zuwan
addinin Musulunci ƙasar Hausa. Ga al’ada, lokacin da aka yi rasuwa,
namiji ko tamace, akan yi ƙoƙari a ga cewa,an yi wa
gawa sutura da kuma jana’iza, ba tare da ɓata lokaci ba. Haka kuma za a yi
hakann ta hanyar sanar wa jama’a ‘yan’uwa na kusa da na nesa. A tsarin addinin
Musulunci lokacin da aka sanar wa mutum wani ya rasu, akwai kalaman da aka
furta na addo’a. Addo’ar da ake yi ita ce:
……..Innaa Lillaahi wa innaa ilaihir
raji’uun
Ma’ana: Daga Allah muke kuma a gare Shi za mu
koma.
Wannan addo’a addinin Musulunci ne ya kwaɗaitar
da dukkan musulmi lokacin da ya gamu da wata masifa, ko ya ga wani abu mai tada
hankali, ya yi wannan addo’a da aka ambata. A hannu guda, akwai addu’a da ake
yi wadda surkulle ya yi naso a lokacin da aka sanar wa mutum cewa, ana gayyatar
sa jana’iza. Wato da zarar an faɗa wa mutum an yi mutuwa sai ya yi wanna addo’a
ta surkullr kamar haka:
Subuhaaka wa innii mayyitu,
In lookacii yaa arzama,
Sarikantun wa sarikaatun mautu,
Atiidu da Raƙiibu matambayaa
Ku yii masa tambayaa da sauƙii
Baa da raazanarwaa ba.
Wannan surkulle ana yin sa ne a yayin da aka
bayyana wa mutum cewa wani ya mutu wato in aka faɗa wa mutum ya zo jana’iza.
Haka kuma a wannan surkulle za a yi shi yayin da aka sanar wa mutum cewa, wani
ya mutu. Wannan Surkullen ya yi naso cikin addinin Musulunci saboda yana ƙunshe da kalmomin, ‘subuhaaka’ da `wa' da `innii' da kuma
`mayyitu' Kalmar `subuhakaa' an saƙala mata gaɓoɓi biyu
a ƙarshenta don a kauce wa faɗin `subhaanaka' ne.
`Wa' na nufin 'da', `innii'. ake nufi, sannan `mayyitu' kuma an shafe bakin
karshe na asalin kalmar mayyitun ta Larabci amma dai duka mai mutuwa ko mamaci
ake nufi. Haka kuma a jimlar 'in lookacii yaa arzama' ana nufin idan lokacin
mutuwa ta zo. Kalmar `sarikaatu' tana nufin ɗanɗano zafin mutuwa. A
dunkule surkullen yana nufin yi wa wanda aka ji labarin ya mutu addu'a da cewa
matambayan kabari su yi masa (ga shi mamaci) tambaya da sauƙi.
4. 2 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Wankan Gawa
Wannan surkulle ne da ake yi yayin da wani ya
mutu. Bisa al’adar addinin Musulunci, lokaci da aka ce wani ya rasu; namiji ko
tamace, yaro ko babba, akan yi masa wanka kafin a saka masa likkafani, a kai
shi kabari. Yayin da aka zo yi wa mamaci (gawa) wanka, a tsarin adddinin
Musulunci, mai yi wa gawa wanka ana so ya yi bismillah wato y ace: Bismillaahi,
sannan sai ya ƙuduri aniyar wanke gawar a zuciya. Akwai naso da
surkulle ya yi cikin niyyar fara wankan gawa. Surkulle da ake yi na wankan gawa
shi ne:
Bismillaahi, allaahumma
Suturhu, wa rufauhuu
Fii kabarin kabaraata
Har abadaa, bari mu
Wankee shi, kafin a wankee mu,
Ba mu san ranar Ƙauraa ba,
Ba mu san wanda zai wankee mu ba.
Wannan surkulle za a iya lura da waɗansu kalmomi
a cikinsa wato kalmomin ‘Bismillahi’ da ‘allaahummaa’ da ‘fii’ da kuma ‘Ƙabarin'. Waɗannan kalmomin aro ne daga harshen Larabci wanda bisa
ma' ana suna nufin: farawa da suna Allah, Wato an sami tsarmin Larabci a cikin
wannan surkulle.
Sannan kalmomin: `suturhu da rufauhu' kalmomi ne
da aka yi, musu ɓad da sau ne ta hanyar yi musu ɗafin ƙeya na 'hu' a ƙarshensu. Kalmar
‘suturhu’ tana nufin a yi wa mamaci sutura. Kalmar rufauhu a nan tana nufin a
rufa masa (mamaci) asiri ya samu tsari a lahira ko kuma a kwanciyar da zai a
kabarinsa. Haka kuma a jimlar ‘ba mu san raanar ƙauraa ba’ an yi amfani da aron ma'anar kalmar ƙaura da nufin ƙaura ta barin duniya.
Wato dai wannan surkulle ne da ya yi naso da ya zo a matsayin addu’a. Wato shi
ma addu'a ce ake yi wa mamaci ya samu tsira da zaman jin daɗi a kabari bayan ya
mutu. Abin da za a iya lura a wannan surkulle shi ne samuwar tasirin harshen
Larabci. Kalmomin “Bisimillaahi da Allahununa da kuma Suturhu” duka kalmomi ne
na Larabci aka surka da harshen Hausa.
4. 3 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Gama Wankan Gawa
Ga al’ada lokacin da mutum ya mutu, abu na farko
da akan yi wa gawa shi ne wanka. Idan aka gama wankan sai a saka
likkafani.Akwai surkulle da ake yi bayan gama wankan gawa.Wannan surkulle, ana
yin sa ne saboda neman rahama ga mamaci. Yayin da aka gama wanka kuma sai a ce:
Bisimillahi
Alluhudun hudan
Tafi dum
Wannan surkulle ne da ake yi bayan an gama wanke
gawa, ba shi da wata ma'ana. Sai dai kamar yadda na zanta da malama Sakina
Muktari a unguwar Gwale Jihar Kano, ranar 24 ga Nuwamba ta bayyana cewa, ana
yin surkullen ne domin kariya daga sharrin iskoki ka da su yi wa masu wankan
gawa wata illa. Sai dai a kalmar ana nufin kada mai wanka ta ji bugu na dundu a
bayanta. Wato kada aljani ya buge su kafin fita daga wurin wankan gawar.
4. 4 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Fitar da Gawad aga Gida
Wannan nau’in surkulle ne da ake yi yayin da aka
gama wankan gawa. Sai dai abin lura, surkulle bisa al’ada, akan yi shi ne bayan
an saka wa gawa likkafani. Tattaunawa da aka yi da malama Harira Muhammad a
garin Wudil , ranar 24 ga Oktoba, 2023 ta bayyana cewa, idan aka zo fita da
gawar ne za a yi surkullen kamar haka:
Kai duwa, kai duwaa-duwaa,
Baa ni wurii na wucee, wuceewaa,
Yaushe ka san ni, yau ne ka san ni,
Ka san sunaanaa? Naa san ka, naa
San `yaa' yanka. Inaa su duwai,
Inaa su Muusa da Isa ya jabbakaari,
Yaa, Rasuulallaahi shaafa' kainaa
Shafaa'atii, masa ceetoo, muu
Maa mu samuu.
Wannan surkulle ya yi naso cikin addinn
Musulunci a ta ɓangaren da aka yi maganar ‘yaa Rasuulullaahi shaafa kaina,
shafaaa’atii’ A sauran sassan suurkullen ya ƙunshi kalaman Hausa ne
zalla. Sannan surkulle ya fito maganar fitar da gawa daga gida zuwa yi mata
jana’iza (sallah) zuwa a kai ta kabari, surkullen ya, ƙunshi wata hikima ko dabara mai kama da hira tsakanin mutum biyu.
A matakin farko a surkullen ana magana ta hanyar ambaton suna `kaiduwaa
kaiduwaa'. Duwa ana nufin wai suna ne na mala'ika. `baa, ni wuriinaa na wucee'
wai da zarar an fadi haka sai kuma mai yin surkulle ya sake cewa, wuceewaa,
yaushe ka san ni, yau ne ka san ni ka san sunaanaa?' sai kuma a sake cewa
naa.san ka naa san `ya'yanku, inaa su duwai inaa su Muusa da Isaa. Wato ana
nuna an san kaiduwa da ‘ya'yansa da ma sauran manyan mutane annabawa.
Daga ƙarshe sai a ƙasara ambaton `yaa
Rasuulallaahi shaafa kainaa shafaa'atii,. yii masa ceetoo muu maa mu saamuu.
A wannan surkulle za a iya lura da cewa yana da
tasirin Larabci a cikinsa; a inda aka yi amfani da kalmomin `yaa' da
`rasuulallaahi' da kuma shafa’afii dukkansu na Larabci ne.
4. 5 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Kada Miji ko Mata Ta Yi Fatalwa
Fatalwa wani kamance ne na sake bayyanar mutumin
da ya mutu, da ke tsoratarwa. Zarabozo, (2002: 23). A Musulunci an yi maganar
fatalwa inda aka bayyana cewa, aljine da ke tare da mutum yakan sake fitowa da
kamannin mamaci. Akwai addo’a da akan yi ta fuskar addinin Musulunci da ake
kore fatalwar kamar haka:
A’uuzu billaahi minasshaɗaanirrjiim
A’uaazu bikalimaatillahittaamaatim
minsharri maakhalaƙ.
Wannan addo’a, akwai surkulle da ake yi
wandaya yi naso cikin addinin Musulunci da ya danganci lamarin takaba. Akan yi
wannan surkulle bisa manufa guda biyu. Wato surkulle ne da ke da amfani, ko
fa’ida a matsayin kada miji, ko matar ta da ta mutu ta dinga yin fatalwa ga
mijin, ko ga macen da aka mutu aka bar ta. Surkulle da ake yi shi ne:
Bisimillaahi inni nawai, fil katsar,
Tarnaƙin tirnaaƙa, dabalbalin
dabaibayin baƙin sa, taf ka ba ruwaa,
ka yi kwance, kwanciyar barcin har abadaa
baa da taasoowaa ba.
Wannan nau'i na surkulle yana nuni da ƙoƙarin yin shamaki tsakani mai yin takaba da
fatalwa, a lokacin da mijin mace ya mutu ya bar ta. Abin lura shi ne wannan
surkulle ma yana da nason addini a cikinsa. Za a ga inda aka fara da yin
‘bismillahl’, wato ma'anar wannan shi ne farawa da sunan maɗaukaki Allah.
4. 6 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Zaman Makoki
Zaman makoki shi ne zaman karɓan gaisuwa da
dangin mamaci ke yi na tsawon kwana uku. A bisa al’adar Bahaushe, duk wanda ya
mutu akan yi zama na wuni uku a matsayin zaman makoki. Akan fara zaman daga
ranar da aka yi jana'izar mamaci. Karatun surkulle da ake yi shi ne: Cikin
wannan surkulle, addinin Musulunci ya yi naso a ta ɓangaren da aka
Jingim maa jingim
Fankam kara fankam
Allah shi kaɗai yake
A gare shi ba wani
Sai shi.
Cikin wannan surkulle, addinin Musulunci
ya yi naso a ta ɓangaren da aka ce:
Allah shii kaɗai yake, a gare shi baa wani sai
shii.
A nan, ana ƙoƙari ne a kaɗaita Allah ne kai tsaye. Haka kuma wannan surkulle ne
da ake yi a daidai lokacin da aka fara zaman makoki (wato karɓar gaisuwa). A
wannan surkulle har wa yau, za a ga an maimaita ambaton kalmomin ‘jingim’ da
kuma ‘fankam’. Kalmar ‘jingim' tana nufin yawa, wato taron yawan mutanen da ke
zama a wurin karɓar gaisuwar mutuwa (ta'aziya) ne. Kalmar ‘fankam’ ita ma
ta ƙunshi makusanciyar manufa da kalmar ‘jingim’
wato tana nufin taruwar yawan jama'a masu zaman gaisuwa a wurin zaman makoki.
4. 7 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Shiga Takaba
Takaba wasu ayyanannun kwanaki ne da matar da
mijinta ya rasu ya bari ke killace kanta ta hanyar zama a gida har tsawon wata
huɗu da kwana goma. Shiga takaba a Musulunci abu ne da ba shi da wata
takamammiyar niyya. Sai dai akan ƙudurta ga zuciya cewa,
an shiga takabar da daga lokacin da mijin mace ya mutu. Akan ambaci sunan
Allah. Sai dai akwai surkulle da akan yin a fara yin takaba a tsarin al’adar
Hausawa. Surkulle da mata ke yi na shiga, ko fara takaba shi ne kamar haka:
Bismillaahi warkafun,
bi a'ala zugum
taalikai zugum-zugum
gidaa da shaiduu,
a nan zaa mu faara takabaa.
Wannan surkulle, yana nuni da addu’a ta musamman
domin shiga takaba da mata ke yi a da. Wannan karatu shi ma akwai nason
Musulunci a cikinsa. Wato ana ayyana niyyar shiga takaba ne ta hanyar wannan
surkulle. Jimlar, "bi a' alaa zugum taalikai zugum-zugum" na nuna
halin juyayin mutuwa ko mutumin da ya mutu ne, ambaton “a nan zaa mu faara
takaba” yana nuna shiga takaba ne kai tsaye.
4. 8 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Wankan Mai Takaba na Sati-Sati
Wannan surkulle ne da ake yi yayin da
Allaahumma innii waraa to janii
Bi ismika tirkaamaa tirkaa.
Wannan surkulle ya ƙunshi kalmomin da suka danganci addinin Musulunci a cikinsa inda
aka ce: ‘Allaahumma inni. Sai dai kuma an samu nason surkulle kalmar ‘wara’a’
ta yi kama da ta Filatanci mai ma’anar zuwa. ‘Allahumma’ na nufin ya Allah.
‘Bi’ na nufin da, ‘ismika’ kuma shi ne ‘sunanka’. Wato da sunan Allah. Kalmar
‘tirkaa’ ta yi kama da kalma mai ma’anar dukiyar gado da aka bari kafin a yi
rabon gadon, amma a nan tana nufin hoɓɓasan yin kwanaki bakwai na wankan,
ma’ana dukkan kwanakin ake nufi cewa an yi musu niya guda. Malam Ahmadu Barde
da aka zanta da shi a garin Kura ranar 2 ga Janairu,2023 ya bayyana cewa,yayin
da aka fara wankan kuma sai a ce:
Ilaahii zunubi algaya
Akalahuu wal lawaaya
Haka nan surkullen ne da ke da tasirin harshen
Larabci a cikinsa. Wato dukkan kalmomin da ke cikinsa, za a ga suna da tasirin
Larabci. Kalmar ‘ilaahi' na nufin Ubangijina, ‘zunubi’ na nufin laifuka da aka
aikata na haramci, ‘akalahuu’ aka cinye, ‘wa’ da, lawaaya kalma ce marar ma’ana
cikin wannan surkulle. A nan a wannan surkulle, ana neman gafara ne da kuɓuta
daga aikata kuskure yayin wankan.
4. 9 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Shiga Ɗaki Ga Mai Takaba
Wannan wata hanya ce da ake bi a sami kariya
daga sharrin iskoki. Wato surkulle ne da ake yi domin kare kai daga bugun
aljani. Bisa yadda al’ada ta nuna, mace mai takaba ana ganin cewa, ita ba ta da
cikakken tsarki ga jiki. Wannan ya sa akan yi surkulle saboda kariyar shafar
aljani yayin da mai takaba ta zo shiga ɗaki. A nan, mai takaba
za ta yi surkullen kamar haka:
Saahuuna maa'uuna,
kaucee daga nan,
zan wucee.
Wannan surkulle ba shi da wani tasirin
harshen Larabci a cikinsa. Wato kalmomin Hausa ce tsantsa ke ƙunshe cikin wannan surkulle. Kalmomin surkullen yawancinsu ba su
da wata ma’ana a cikinsu sai ɗan abin da ba a rasa ba. Misali a kalmar
‘kaucee’ ana nufin sanar da iskokin wannan gida da za a shiga da su ba da wuri
ana so a shiga gidan. Ana ambaton hakan ne kamar yadda na zanta da Bala Ɗantala da ke garin Gaya ranar 11ga Fabrairu, 2023 ya bayyana cewa,
akan yi wannan surkullen domin ka da a yi wa iskokin da ke gidan laifi bisa
tsarinsu na zaman gidan.
A kalmomi biyu na farko a surkullen suna da
tsarin gaɓoɓi iri ɗaya ne na buɗaɗɗun gaɓoɓi masu dogayen wasula a gaɓoɓi
biyu, na farkon kowace kalma (daga cikinsu). Kalmomin ‘saahuuna’ da ‘maa'ununa’
kalmomi ne na yabo da girmama iskokin da ke gidan da aka yi mutuwar.
4. 10 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Shiga Banɗaki
Wannan karatu na surkulle ne da ake yi yayin da
za a shiga banɗaki, lokacin da mutum; namiji ko mace za ta shiga sai ta yi
surkulle da za a bayyana nan gaba. Wani muhimmin abu dangane da wannan surkulle
shi ne ba sai lallai lokacin da za a biya buƙatar kama ruwa ba kaɗai
ake so a yi surkullen, akan so a yi shi ko da wankan yaro za a yi, ko wani abu
daban da bai shafi kama ruwa ba. Surkullen ana yin sa kamar haka:
Wa auli Rabbuka hattaa
Yaa tattaƙimu, yaa kai
Baawaa, raanar sakankanceewar;
ita cee ƙaala, yaa Faɗaa,
annabi Muusaa yaa faɗaa,
laabudda baa makawaa.
A wannan surkullen ma kamar a sauran ne, za a ga
akwai nason addninin Musulunci mai yawa a cikinsa. Wannan nau'i na surkulle ana
yin sa ne domin neman tsari daga gamuwa da aljani a banɗaki.
Kamar yadda ya gabata a wasu surkulle, wannan
surkulle shi ma yana da nason addini Musulunciu. Da farko,an yi amfani da aron
kalmomin Larabci a wannan surkullen. A jimlar ‘wa auli Rabbuka’ ana nufin
masoya ubangijinka har sai surkulle ya ci gaba da fito da labarin zuwan
alkiyama cewa babu tababa ranar za ta zo.
Mafi yawan waɗanda aka zanta da su a wannan
kashi mata ne. Don haka yawa-yawan surkulle da aka tattara suka kasance na
sha’anin mata. Wannan ya faru ne saboda a wannan ɓangare an fi mayar da
hankali kan sha’anin mutuwa, musamman kuma an fi mayar da hankali
kan ɓangaren takaba.
4.11 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Garar Lahira
Wannan surkulle ne da ake yi na neman tsari daga
sharrin garar lahira. A tsarin shari’ar addinin Musulunci, lokacin da mutum ya
mutu, akan saka masa likkafani. Daga nan kuma sa a yi masa jana’iza. Akwai
Surkulle da ake yi na neman tsari daga garar lahira kamar haka:
Asamakuu! Asamakuu !! Asamakuu!!!
Wannan surkulle ne da garar lahira za ta dinga
kiran wanda ya mutu a lokacin da aka saka shi a makara, za a kai kabari
Tattaunawa da aka yi da malama Goggo a garin Wudil ranar 23 ga Nuwamba 2022 ta
bayyana mini cewa, idan mamaci bai son irin amsar da zai faɗa ba, yayin da aka
saka shi cikin kabarinsa, sai wannan gara ta zo ta yi masa azaba. Irin amsar da
ake so a faɗa ita ce:
Alawajidaa! Alawajidaa!! Alawajidaa!!!
Idan mutum ya san wannan surkulle, kafin mutuwa,
ana sa rai yayin da mutum ya iya bayar da wannan amsa ta surkulle da aka
ambata. Wato surkulle ne da ake so mutum ya sani kafin ya mutu. A wannan
surkulle akwai nason addinin Musulunci sosai a cikinsa ta ɓangaren neman
tsari na wasu daga cikin ire-ren nau’ukan azaba na lahira. Sai dai kuma
kalmomin surkullen za a ga ba su da wata fitacciyar ma’ana.
4.12. Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Samun Kitsen Goro Ga Jiki
Goro wani nau’in ɗan itaciya ne da ake ci.
Bisa al’ada Bahaushe ya rungumi amfani da goro a lamuran rayuwa da suka haɗa da
bikin suna da bikin aure da a zaman yau da kullum. Bisa zantawa da aka yi da
Tabawa Tsamiya mai yawan cin goro, ranar 12 ga Satumba, 2023 a garin Doguwa,
Jihar Kano ta bayyana da cewa, a cikin goro da ake taunawa akwai wani kitse
wanda idan mutum yana cin, zai samu wannan kitsen shi ma amma sai yana yin
adu’ar surkullen zai sami kitsen ga jiki. Surkulle da ake yi na samun kitsen
goro ga jikin shi ne:
Bisimillahi, Bisimillaahi,
Mutuwas saraa, annuurus saraa,
Allah baa ni kitsen dooroo
Na ci.
Ko kuma akan ce:
Bisismillaahi, Bisimillaahi,
Ziryan zaraa, annuurus saraa,
Allah ba mu kitsen gooroo
Mu ci.
Wannan surkulle ana yin sa a lokacin da aka zo
saka goro a baki za a tauna. Kamar yadda aka zanta da ita malama Tabawa
Tsamiya, ta bayyana da cewa, idan mutum ya yi wannan adu’a ya tauna goro, zai
samu kitse na goro a jikinsa shi ma. Idan kuwa ya samu wannan kitsen goro ga
jiki, wutar lahira ba za ta ƙona shi ba. Wato
surkulle ne na tsari daga ƙunar wutar lahira. Wannan surkulle yana da nason
addininn Musulunci a cikinsa. Farko, an fara surkullen da sunan Allah wanda
addininn Musulunci ya yi umarnin kowane abu mai kyau da za a aikata, a fara yin
bismilah.
4.13 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkulle na
Tambayoyi da Ake yi wa Mamaci Lokacin da aka Ajiye shi Kafin a Wanke shi
Wannan naso ne da addinin Musulunci ya yi
a surkullen. Ɓangaren tambayoyi da ake yi wa mamaci. Hira da
aka yi da malama Furera Hassan a garin Kura, ranar 26 ga Nuwamba 2023 ta
bayyana cewa, Idan mutum ya mutu, ana ajiye shi a tsakar daki, a wannan wuri da
gawar take kwance mala'iku za su zo (da wata babbar kujera a hannu) su yi
tambayoyi ga wanda ya mutu idan ya san amsoshin tambayoyin da zasu yi masa, ya
tsira, idan kuwa bai sani ba daga nan waɗannan mala'iku za su dauka cewa
mamacin ba Musulmi ba ne, sai su buge shi da wannan babbar kujerar su kuma kai
shi ko su kai ta wuta. Ga yadda surkullen yake, kamar haka:
Tambaya Ta ɗaya:
Bawan Allah me kwanciyar tsakar ɗaki, miye
abu daya?
Amsa: Idan mamaci ya sani sai ya ce:
“Allah nee abu ɗaya”
Tambaya Ta biyu:
Baiwar Allah mee kyanciyar tsakar ɗaakii
miyee abu biyu?
Amsa: Idan ta sani sai ta ce:
Raanaa da wataa koo duuniyaa da laahiraa suu nee
abu biyu
Tambaya Ta uku.
Baiwar Allah mee kwanciyar tsakar ɗaakii
miyee abu uku?
Amsa: Idan ta sani sai ta ce:
Abu uku suu nee: Murhun tsakar gidaa, wanda akee
shirya wa macen da aka aurar domin ta yi girkii wa mijinta, ta saamu laadaa.
Tambaya ta Huɗu:
Baiwar Allah mee kwanciyar tsakar ɗaakii
miyee abu huɗu?
Amsa: idan ta sani sai ta ce:
Abu hudu su ne: gabas da yamma, kudu da arewa su
ne abu huɗu.
Tambaya Ta biyar:
“Baiwar Allah me kwanciyar tsakar ɗaki miye
abu biyar”.
Amsa: Abu biyar su ne:
Salloolii lookuta biyar, sallar asubaahii,
sallah azahar, sallar la'asar, sallar mangaribaa, da sallar liishaa. Suu nee
abu biyar.
Tambaya ta shida.
Baiwar Allah mee kwanciyar tsakar ɗaakii
miyee abu shida?
Amsa: Abu shida suu nee:
sama da ƙasa, gabas da yamma,
kudu da areewa. Suu nee abu shida”
Tambaya ta bakwai:
Baiwar Allah mee kwanciyar tsakar ɗaakii
miyee abu bakwai?
Amsa: sai a ce:
Abu bakwai su ne, saatii, ya maida saatii.
Junma'a, Asabar, Lahadii, Litinin, Talaataa, Laarabaa da Alhamis. Su ne abu
bakwa?
Tambaya Ta Takwas.
“Baiwar Allah mee kwanciyar tsakar ɗaakii
miyee abu takwas?”
Amsa:
Abu takwas suu nee: Ƙoofoofin gidan Aljanna guda takwas. Ko kuma da za a yi Bari, babu
rai shi ne abu takwas.
Tambaya Ta Tara:
Baiwar Allah mee kwanciyar tsakar ɗaakii
miyee abu tara?
Amsa:
Abu tare suu nee ɗa a cikin uwarsa, a haife
shi wataa tara da kwaanaa tara shii nee abu tara.
Tambaya Ta Goma:
Baiwar Allah me kwanciyar tsakar ɗaakii
miye abu goma?
Amsa:
Abu na goma shi ne La'ilaha Ilallaahu,
Mahammadarra Sulullaahi Sallallaahu alaihi wa sallama, ko salati ga Annabi sau
goma shi ne abu goma.
Waɗannan tambayoyi goma suna matsayin karantarwa
ce ta tauhidi, wato kadaita Allah. Mata tsofi suna bayar wa mata ko maza, da
nufin duk wanda, ko wadda ta san waɗannan amsoshi zai kuɓuta daga shiga wuta,
watau za a shiga Aljanna saboda ansan Allah da dukkan siffofinsa da kaɗaitarsa.
Hausawa kan ce, “Ba a yin rawa, ba juyi”, Bari
mu juya ga abin da addinin Musulunci ya yi nuni game da Tauhidi.
Ta ɓangaren addinin Musulunc, akwai ainihin tambayoyi da ake yi wa mamaci
akasin yadda masu surkulle na gama-gari suke riyawa, wato ga addinin Musulunci,
an nuna cewa, ana yi wa mamaci tambayoyin ne a cikin kabari, bayan an saka
mutum kabarinsa, sai mala’iku Munkaran da Nakirun su zo wa mutum su yi masa
waɗannan tambayoyi kamar haka:
Wane ne Ubangijinka? Meme ne addininka? Wanne ne
littafinka? Wane ne Annabinka? Wane ne ɗan uwanka?
Waɗannan tambayoyi (na sama) su ne wai daga
cikin tambayoyi da mala’iku suke yi cikin kabari.
4.14 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Neman Mutum a Duniya ko a Lahira
Idan ka nemi mutum a duniya ba ka gan shi ba,
idan ka je lahira ka gan shi. In ka ga dabba ta mace, ka ga dabar ta namiji. In
ka ga mutum a gidan duniya, in ka je lahira ka gan shi ka ga abu uku: jini uku
wata uku. Abu hudu kuma iddar aure ko aure ne na mazaje ba mai cike biyar sai
inna-nabi Abdullahi tsirar Allah ta tabbata agare shi.
Abu biyar su ne “sallah Azahar, La'asar,
Magariba, Lisha da Asubahi.
Wanda duk ya san wannan zai gamu da ɗan
uwansa a duniya ko lahira, wato ana nufin ɗan uwanka, akasin haka ba
zai ɓace maka ba muddin ka san wannan karatu.
4. 15 Nason Ire-Iren Surkulle a Lamari Lahira
Wannan sashe kuma zai Magana ka ire-iren
surkulle da ke nason addininbMusulunci a cikinsu. Lamarin surkulle a matsayinsa
bayan zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa. An lura
cewa, wani sashed aga cikin sassan surkulle ya sami naso har ya zuwa ga
sha’anin rayuwar lahira. Surkulle da za a bayyana sun haɗa da:
4.15. 1 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Zaman Kabari
Zaman kabari wata rayuwa da mamaci ke kasancewa
gabinnin a yi masa hisabi. Bisa tsari na addinin Musulunci, an bayyana cewa,
wannan rayuwa ta zaman kabari mutum dole ne sai kowa ya yi ta. Haka kuma an
bayyana mutum yana iya gamuwa zaman a jin daɗi, ko kuma zaman wahala. Wannan
kuwa ya danganta da irin ayyukan da ya aikata a zamansa na duniya. Akwai
surkulle da yake da nason addinin Musulunci a cikinsa na zaman kabari. Wannan
surkulle shi ne:
Inni nashidu shafi’alwara,
Shafii'unaa, nahaligunaa kulimnaa,
yauman hada, yauman Takasiru,
yauman nashara,
yauman Muharmmadunaa Musɗafaa,
Sallallaahu alaihi wa sallama.
Hira da aka yi da malam Ahmadu Barde, da ke
garin Kura Jihar Kano ranar 2 ga Janairu, 2023 ya bayyana cewa, wannan addu'a
ce da ake son mutum ya dinga yi a rayuwarsa, kafin ya mutu, watau idan mutum
yana yawan karanta wannan karatu ko addu’a ba zai gamu dawahala ko azabar zaman
kabari ba, in ya mutu.
4.15.2 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Mace ta Kuɓutar da Mijinta a Lahira
A nan, ana nufini lokacin da ake hawan Siraɗi,
mace mai biyayya ga mijinta, wacce take kuma bin umarnin Allah da Manzonsa za
ta samu damar ceton mijinta ta hanyar goyon mijin nata, ta yi gudu da shi ta
haye, ko tsallake Siraɗi. Mace mai aure za ta samu damar hakan ne idan tana
yawan karanta wannan karatu da mai nazari zai kawo nan gaba. Ba tare da an samu
wata tangarda ba matar za ta iya dauƙar mijin nata ta haye da
shi su shiga Aljanna tare. Wadda kuwa ba ta sanwannan karatun na surkulle ba,
za ta kasa ɗaukar, ko goyon mijin domin za ta ji nauyinsa tamkar nauyin
buhun ƙasa, ko tozali ɗari ne. Surkullen da za a
dinga karantawa shi ne kamar haka:
Ranar gudun kiyama,
ɗamar ɗamar na goye,
ka ce ma baraden,
ni ce nan ga goye abina
a rairayin Aljanna”.
A wannan surkulle za a ga cewa, ya ƙunshi kalamai da ken una lamarin addinin Musulunci. Inda aka ce,
‘Rairayin Aljanna a ƙarshen kalaman surkullen. Sai kuma a farkon
kalaman na farko, aka faro su da surkulle.
4. 15. 3 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Wasu Addu’o’i da ake so Mamaci ya Sani Yayin da yake Cikin Kabarinsa a Kwance
Karatun Surkulle na Shiga Aljanna
Wannan karatu ne da ake yin sa da tunanin cewa,
idan aka yi shi ya ɗauke wa mutum komai na zunubi, har ma komai da komai
dangane da abubuwa da suka shafi lamarin rashin ibada da sauran abubuwa.
Karatun surkullen shi ne kamar haka:
Allahu ilaihin Wahidun,
Jabbaru karirum da’imun
Fagfili kulli zunubana
war-hamna daral jannati,
aljannar janna gaba daya.
Wannan karatun surkulle shi ne wanda ake
samu ɗan ci gaba (watau) ya zama kamar dai surkulle ba surkulle ba ne
adu’a ce. Jimlar farko za a ga cewa, kalamai ne na addinin Musulunci. Wurin da
ya zama surkullen shi ne inda su masu yin surkulle suka ɗauka cewa, duk
wanda ya yi, ya kuma san wannan addu’a, to yanke kai tsaye zai shiga Aljanna
kuma komai yawan mutane watau ko mutane nawa ne za su tafi Aljanna
gaba ɗaya idan suka dimanci yin wannan karatu, walau maza ne ko mata, yara
ko manya, da makamantansu.
4.15. 4 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Jakin Lahira
Wannan surkulle ne wanda ake yi a lahira. Wato a
lahira wani jaki zai zo wa mamaci ɗauke da kayan azabar lahira iri
daban-daban, kamar macizai da kunami da sauran nau’ukan halittu masu
azabtarwaa. Wannan jakin lahirar idan ya zo, zai tsaya a gaban mutun, ya yi
masa tambaya. Idan mutum bai san amsar tambayar bas ai jakin ya juye masa
waɗannan kayan azabar. Karatun shi ne da farko, Jakin zai ce:
Mu jirkita, koo mu daakata?
Mutum idan ya sani sai ya ce:
Mu daakata hairan-hairan.
A hira da aka yi da malam Ahmadu Barde ranar 2
ga Janairu, 2023 a garin Kura, Jahar Kano ya bayyana cewa, wannan surkulle,
kalmar: "daakata'”da kuma “hairan-hairan” shi ne abin lura a wannan
surkulle. Faɗar 'hairan-hairan', shi yake hana jakin yi wa mamacin azaba. Don
haka hairan-hairan kalma ce mai nufin alheri a cikin tsarin Addinin Musulunci.
Haka nan, idan mutum bai san amsar 'hairan-hairan' ba sai jakin ya juye masa
macizai da kunami da yake ɗauke da su, su yi tą azabtar da shi.
4. 15. 5 Nason Addinin Musulunci Cikin surküllen
Tsohuwar Lahira Mai Babbar ƙwarya
Wannan surkulle yana nuna cewa, akwai wata
tsohuwa wadda take ɗauke da ƙwarya mai girman gaske.
Wannan tsohuwa, za ta zo wa mamaci lokacin da yake kwance cikin kabarinsa. Hira
da aka yi da malamaHassana Adam ranar 25 ga Nuwamba, 2023 a garin Wudil, Jahar
Kano ta bayyana cewa, da zarar an kai mutum kabarinsa an binne shi, wata mace
tsohuwa za ta zo masa da wata babbar ƙwarya a hannayenta domin
ta kwashe masa lada. Daga zuwanta, za ta faɗa wa wanda yake cikin kabarin wata
magana a matsayin tambaya, ko jawabi kamar haka:
Kalleene-kalleenaa.
Shi kuma wanda yake kabari sai ya amsa, ya ce:
Kalle'atun zuwainaa,
Kalle'atun Muhammadu.
'Idan aka yi haka, daga nan tsohuwar za ta tafi,
ba za ta samu damar kwashe wa mutumin ladansa ba da wannan babbar ƙwaryar. Haka nan kuma ba za ta ƙara dawowa ba.Mamaci sai
ya ci gaba da zama cikin kabarinsa ba da azaba ba.
4. 15.6 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Kunamar Lahira
Wannan surkulle, da ke nuna cewa wata kunama a
lahira za ta zo wa mamaci da nufin ta yi masa azaba. Idan ya iya, ko ya san
karatun surkulle da ake yina kunamar, ba za ta cutar da shi ba.Wannan surkullen
ga yadda ake bayar da shi kamar haka:
Na farko:
Ta daakira dak sandan dira naa dakaa.
Na biyu:
Mu kilfila, kilfil, Dandarin ta Maliki Shata
Hambali Maliki.
Ko kuma akan ce:
Dandarin dariyan dandarin ta Maliki?
Hira da aka yi da malama Sakina Muktari a Uguwar
Gwale cikin garin Kano, ranar24 ga Nuwamba, 2022 ta bayyana cewa, wannan
surkulle, wata kunama ce a lahira za ta zo wa mamaci da nufin ta yi masa azaba.
Idan ya iya, ko ya son karatun surkulle da ake yi wa kunamar tun a duniy, mutum
zai iya ba da amsa ga kunamar. Idan y aba da amsar daidai, kunamar ba za ta
cutar da shi ba.Wannan surkullen yana zuwa ne ta matakai biyu, kamar yadda ya
gabata a sama Na biyun akwai zaɓi wato shi na biyun ana yin sa tafuskoki biyu.
4.16 Nason Addinin Musulunci Cikin Surkullen
Ture Bangon Kabari a Lahira
Wannan ana nufin karatun surkulle wanda idan ba
a iya shi ba ko kuma ba a sanshì ba, bangon kudu da arewa gabas da yamina ne za
su hadu su matse wanda yakecikin kabari, ya ci gaba da zama cikin azaa. Idan
kuma ya san karatun shi ke nan,yatsira daga wannan nau'i na azaba. Addu'ar ita
ce: Mutum zai ce:
“Sabihi sahaha sa'adatu”
Sannan mala'iku sai su ce:
Mallam Sahaaboji to gayaa mana suunan kusheewa.
Daga nan kushewa za ta amsa, ta ce:
Yoo baa don sahaaboji nee ya gaya miki sunan
kusheewar ba da ina tunkuɗi awarzaki, to noonon da kika shaa a cikin uwarki maa
sai kin baa shi, To ammaa tunda mallam sahaaboji ne ya sanar da kee sunan
kusheewa a runkuɗi gabas, a runkuɗi yamma, a runkuɗi kudu a runkuɗi areewa a ba
ko sararin da zaa ki ji daɗin kwanciyar kusheewa,
A addinin Musulunci kuwa akwai abinda zai faru
ga mutum wanda aka saka cikin kabari da abinda zai cece shi daga azabar
matsewar bangon kabari. An samo hadisai waďanda suka yi magana game da haka:
“Daga Ahmad da Baihaƙi, daga A'ishatu cewa, daga Annabi (tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi), ya ce: “Lallai kabari yana hadewa ya matse Da a ce
mutumzai kuButa daga wannan matsewa,da Sa'adu dan Mư'azu zai kuButadaga wannan matsewa”(Al-Nasa'i).
Haka kuma a wani hadisi:
“An karɓo daga Abu Huraira (Amincin Allah ya
tabbata gare shi), daga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)
ya ce; Ya Allahl Ina neman tsari daga azabar kabari. Ina neman tsari daga
azabar wuta. Ina neman tsari da kariya a kan. shaiɗan da bala'insa”.
5. 0 Sakamakon Bincike
Wannan nazari, ya yi magana kan nason
addinin Musulunci cikin surkullen Hausawa. Wato an ware ire-iren surkulle
waɗanda ke da nason addinin Musulunci cikinsu. A ƙarashin wannan, binciken ya gano ire-iren surkulle waɗanda addinin
Musulunci ya yi naso a cikinsu. Cikin ire-iren waɗannan surkulle, binciken ya
gano irin nason da addini ya yi a surkullen farawa da kuma gama wankan gawa da
surkullen fitar da gawa da surkullen shiga ɗaki ga mai takaba da surkullel
neman tsari na shiga banɗaki da surkullen tsari daga fatalwa da surkullen fara
takaba da surkullen garar lahira da surkullen samun kitsen goro da sauransu.
6.0 Kammalawa
Wannan maƙala an bayyana yadda
addinin Mususulunci ya yi naso cikin surkulle kan abin da ya shafi al’amuran
rayuwar jama’a na duniya da na lahira. An bayyana ire-iren surkulle da ake samu
a fannonin rayuwa ta fuskar mutuwa da takaba da fatalwa, da shiga ɗaki da
shiga banɗaki da makoki da neman tsari daga mutumin da ake shakkasa da
sauransu.
Haka nan, an bayyana
ire-iren surkulle waɗanda suke na sauran rayuwa da ya haɗa da sha’ani wankan
gawa da tsarin shiga wuta a lahira da sauransu. Dukkan wɗannan surkulle ne
waɗanda suke ba na haɗawa da magani ba. Sannan yin hakan zai bai wa manazarta
damar binciko wasu dabaru, ko hanyoyi da masu surkulle ke bi su ƙirƙiri surkulle har ma su yi amfani da su a
matsayin tsari da kariya da samar da biyan buƙatu a gargajiyance.
Haka nan wannan maƙala ta fito da lamarin nan da Hausawa ke cewa, nishaɗi. Hakan ya
samu bisa yadda aka bayyana waɗansu daga cikin ire-iren surkulle da wannan maƙala ta zayyana.
7.0 Shawarwari
Ta yin la’akari da ire-iren bayanai da suka
gabata a wannan takarda, lamarin surkulle muhimman tubali ne na al’adar Hausawa
wanda ya kamata a laƙe masa. Don haka ne wannan takarda ta fito da
waɗannan muhimman shawarwari da suka haɗa da:
Abin la’akari na farko
shi ne an ce komai ka gani yana da ranarsa a tsarin rayuwa, musamman a hali
irin na zamantakewar yau da kullum. Al’ummar Hausawa a yau ta yi wa al’adar
surkulle biris kuma abu ne mai samar da fa’ida ta fuskar tsari da kariya da sauransu.
Haka kuma surkulle
kasancewarsa hanya mai karantar da Bahaushe yadda zai kiyaye abu da ka, a gwada
shi a baka ya (kuma) zauna a zuciya, don haka ya kamata a laƙe wa al’adar sosai.
Yana da muhimmanci a
kula cewa, masu ta’ammuli da surkulle su dinga yin la’akari da zamani da ake
ciki saboda su ma su dinga tafiya tare da zamani. Abin nufi, su ma kada zamani
ya tafi ya bar su.
Manazarta
Abdullahi, I. S. S. (2008). ‘‘Jiya Ba Yau Ba.
Waiwaye A Kan Al’adun Rayuiwar Hausawa Na Aure da Haihuwa da Mutuwa’’. Kundin
Digiri na Uku, Sashen Harshen Nijeriya. Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Abdulrahaman, M. A. (2017). “Mafarin Cuta A
Ma’aunin Al’ada”. Being a Paper Presented at the Intrenational Conference
organized by Centre for Research in Nigerian Languages and Folklore. Kano:
Bayero University.
Abdurra’uf, S. (1988). “Cutukan da Suka Shafi
Fatar Jiki da Magungunansu a Bahaushiyar Al’ada.” Kundin Digiri na Farko, Kano:
Jami’ar Bayero.
Adamu, M. T. (1992). “Siddabaru A Ƙasar Hausa: Yadda Yake da Yadda Ake Yin Sa”. Kundin Digiri na
Biyu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Adamu, M. T. (1998). Asalin Magungunan
Hausawa da Ire-Irensu. Kano: Ɗan Sarkin Kura Publishers.
Adamu, M. T. (2015).
Haihuwa Da Suna A Bahaushiyar Al’ada, Kano: Salma-A’aref Publishers.
Adamu, M. T. (2014). Siddabaru A Ƙasar Hausa.
Kano: Century Research Publishing Limited.
Ado, A. (2011). ‘‘Sana’ar Farauta a Ƙasar Hausa: Madubi Ce Ta Ƙyallaro Tushen Wasu
Sana’o’in Hausawa na Nijeriya’’. Takarda da aka gabatar a Taron Ƙara wa juna sani, Sashen Harsunan Nijeriya, Katsina: Jami’ar Umaru
Musa ‘Yar’adua.
Ado, A. (2017). Ra’o’in Bincike Kan
Al’adun Hausawa. Katsina: Kanki Classical Media Enterprises.
Ado, A. (2018). “ Al’adar Baiko Tsakanin Al’adu
Biyu: Hausawa da Misirawa ”. Cikin Kaduna Journal of HausaMulti
Disciplinary Studies. Vol. 1, No. 4. Department of Nigerian Languades and
Linguistis. Kaduna; State University.
Ado, A. (2019). Bincike na Kimiyya a
Hausa: Yadda Yake da Yadda Gudanar da Shi. Katsina: Goɓernment Printing
Press, Nagogo Road.
Almajir, T. S.
(2009).‘‘Surkulle: Yanaye-Yanayensa Da Muhimmancinsa Ga Rayuwar
Hausawa’’. In Himma Journal
of Contemporary Hausa Studies, vol. 1 no 1., Department of Nigerian
Languages, Katsina: Umaru Musa ‘Yar’adua University.
Bunza, A. M. (1990). ‘‘Hayaƙi Fidda Na Kogo (Nazarin Siddabaru da Sihirin Hausawa)’’. Kundin
Digiri na Biyu, Sashen Nazarin Harsunan Najeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Bunza, A. M. (1995)
‘‘Magungunan Hausa a Rubuce: Nazarin Ayyukan Malaman Tsibbu’’. Kundin Digiri na
Uku, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Bunza, A. M. (2004) ‘‘Ilmin
Tsibbu A ƘasarHausa Jiya Da Yau’’.
Takarda da aka gabatar a taron Ƙara Wa Juna Sani na Musamman.Kano: Cibiyar
Nazarin Harsunnan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Bunza, A. M. (2006). Gadon
Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Nigeria Limited.
CNHN (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Cibiyar Nazarin
Harsunan Nigeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
CNHN. H. A (2015). Maita
A Ƙasar Hausa: Jiya da Yau. Zaria: Ahmadu
Bello University Press Limited.
Dutse, M. A. S. (1990).
‘‘Nazari A Kan Magungunan Gargajiya Na Mata Hausawa Masu Ciki’’. Kundin Digiri
Na Farko, Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Ɗanhausa, A. M. (2017). ‘‘Mahanga Ta Magungunan Gargajiya Na
Afrika’’. Takarda aka Gabatar a Babban Taron Ƙara Wa Juna Sani na Ƙasa da Ƙasa, Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya da Hikimomin
Al’umma. Kano: Jami’ar Bayero.
Ɗanmaigoro, A. (2010). Magungunan Gargajiya Na Hausawa da Fulani.
Kaduna: El Abbas Printing and Media Concepts, No. 10, Gwari Road.
Gobir, Y. A (2012). “Tasirin Iskoki Ga Cutuka da
Magungunan Hausawa ”. Kundin Digi na Uku, Sashen Harsunan Nijeriya. Sokoto:
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Shehu, B. M. (2002) “ Surkullen Mata ”. Kundin
Digiri na Ɗaya, Sashen Nazarin Harsuna da Kimiyyarsu.
Jami’ar Maiduguri.
Zarabozo, J. M
(2002). The World of the Jinn and Deɓils. Lagos: H.I.I.P.H P.
O Box 1059 Oshodi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.