Kabir Yusuf Anka (2020). Muhallinka Rayuwarka. Muhalli, Sutura (Labaran Da Suka Samu Nasara a Gasar Gajerun Labarai a Kan Muhalli Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2020). Darma Digital Prints.
MUHALLINKA RAYUWARKA
Na
Kabir Yusuf Anka
Unguwar Kwarin
Goga, unguwa ce da ta amsa sunan hargitsa-balle ta fuskar
fasali da tsarin gine-ginen awon igiya, haka yanayin zamantakewar unguwa zama
ne na baubawan burmi kowa bai san inda ya sa gaba ba, har da gidan karuwai a
unguwar.
Unguwa ce da ke fuskantar matsalar
rushe-rushen gine-gine a lokacin rani, da damina kuwa sai lahaula. Haka kurum
ba ruwa ba iska sai ka ga gini ya zube, ko ya zubo a kan na kusa, sun haɗu sun
yi rushe.
Yau ma an wayi gari da rushewar
gidaje guda huɗu da suke jingine da juna a unguwar. Rusau ɗin ya yi sanadiyyar
mutuwar mutane shida ciki har da mace mai ciki.
Duk lokacin da irin wannan ta afku za
ka ga yuyar jama'a, yara da manya sun yi dafifi a wurin domin kashe kwarkwatar
idonsu.
Aminu ƙaramin ma'aikaci a hukumar
ayyuka da gidaje na jiha da Malam Musa Ya'u (wanda suke kira Ɗanya'u) da Sale,
'yan haya ne a gidan Alhaji Sani da ke unguwar, duk suna wurin rusau ɗin gami
da sauran 'yan hayar unguwar, sannan akwai Alhaji Dauda Harka, ɗaya daga cikin
mamallaka gidajen hayar.
Rushe-rushen da ke faruwa yana bai wa
mutanen unguwar mamaki, ba damina ba, amma kawai sai ka ga gidaje na rushewa.
Sai dai, ko kaɗan shi Aminu ba ya
mamaki.
"Gaskiya wannan unguwa ba wajen
zama ba ce." Aminu ya faɗa da ƙarfi. Hankulan mutanen da ke kusa, suka
dawo gare shi.
"Me ya sa ka faɗi haka?"
Ɗanya'u ya tambaye shi, "Kuma kai ma ga shi mazaunin unguwar ne?"
"Saboda abubuwan da muke gani,
kuma suke cutar da mu."
"Mun ji, daina fargar jeji, ba mu
dalili." Cewar Sale.
Aminu ya nuna musu unguwar da
hannunsa.
"Da farko, kun ga dai yadda
unguwar take tudu da kwari, a wasu wuraren har da kwazazzabai."
Wasu suka kalla, wasu kuma suka amsa.
"E mun gani."
"To, ga waɗanda suke da masaniya
na kafuwar unguwar sun san asalin nan ɗin kwari ne, wato hanyar ruwa, kuma sun
san a shekarun da aka fara kafa unguwar, a lokacin gwamnati ta yi lebur da
wancan sashen."
Ya nuna gabashin unguwar.
"Gwamnati ta tsara da yin fasalin
gina rukunin gidaje ga al'umma masu buƙatar muhalli. A cikin tsari nata, nan
unguwar da muke wuri ne da za ta yi ƙaton kwarin magudanar ruwa da zai gangara
ya haɗu da can babban kwari, don haka gwamnatin ta fara kafa kwamitin tuntuɓar
masu gonaki da filaye don biyansu diyya.
"Da jin wannan labarin sai
dillallan filaye da gidaje 'yan awon igiya suka garzaya, suka nemi masu gonaki
da filaye, suna zuga su, wai zaluntar su gwamnati za ta yi, ta ƙwace musu
gonaki da filaye, don haka, su siyar musu, za su siya da daraja.
"Haka suka hau keken ɓera, suka
rinƙa siyar musu, ƙarshe unguwar ta koma hannunsu, suka yanka filaye a wurin da
bai kamata ba, kan magudanar ruwa."
"A matsayinmu na talakawa, 'yan
haya a wannan unguwa ya kake tsammanin za mu yi idan ba mu zauna a nan ɗin
ba?" Sale ya buƙata.
"Akwai unguwanni da yawa da za mu
iya mallakar muhalli, waɗanda gwamnati ta tsara, ta fitar da gine-gine cikin
fasali mai kyau, ga santoci wadatattu, ga magudanan ruwa, har da makarantu da
asibitoci."
"Kana ganin ire-irenmu za mu iya
mallakar gida a irin waɗannan unguwannin? Ko ka manta yadda muke ƙarma-ƙarmar
biyan kuɗin haya." Ɗanya'u ya tambaya.
Mutanen da ke wurin sai raba idanu
suke, suna ganin kamar almara Aminu yake gaya musu.
Aminu ya yi murmushi.
"E mana, akwai bankin ba da
lamuni da gwamnatin tarayya ta samar sukutum domin samawa al'ummar ƙasa
musamman marasa ƙarfi muhalli ingantacce. Ba irin muhallan wannan unguwar ba,
wadda na kira ba wajen zama ba..."
A wannan lokacin Alhaji Dauda Harka ya
sa baki.
"Kai saurara, duk iskancin
maganganun da kake yi ina jin ka, kana matsiyacinka, ɗan haya, ka zo, kana
kushe mana gidajen da muke taimakawa, mu gina wa mabuƙata."
"Ba kushewa na yi ba, gaskiya
nake faɗa." Ya nuna masa gidajen da suka rushe, "Kuma ga zahiri kana
gani."
"Gaskiyar banza. Yanzu mutanen
nan idan ba mu giggina musu gidajen haya masu sauƙi da rahusa ba a ina kake
tsammanin za su zauna?" Alhaji Dauda ya faɗa, yana kumfar baki.
"To kuma, sai aka ce ku gina musu
marasa inganci, tsukakku, a bigiren da rayuwarsu za ta zama cikin barazana da
ƙalubale?" Aminu ya faɗa.
Alhaji Dauda ya dubi yaronsa da ke
gefe, "Wannan a gidan wa yake haya?"
"A gidan Alhaji Sani
nake..." Aminu ya amsa.
"To ƙarshen zamanka ya zo a
gidan, kuma sai gidan haya ya gagareka a garin nan, babu unguwar da za ka je,
ka nemi gida ban sa an hana ka ba, ko an ba ka, sai na sa an tashe ka."
"Alhaji, ka yi duk abin da za ka
yi, amma ba zan daina nuna wa kaina da al'umma gaskiya ba. Sannan ka sha
kuruminka, fatana shi ne in mallaki muhallina, kuma in yi sanadin waɗanda muke
tare da su, su ma, su mallaka a unguwa mai tsari da fasali wanda masana masu
fasaha suka tsara, suka fitar. Tun farko sakaci na yi, amma yanzu na shiga
taitayina, an fahimtar ni, ina fatan mutanen da muke tare da su, su ma su
gane."
"To ni da kai mu zuba, wallahi ba
ka isa ka mallaki muhalli ba, sai dai bayan raina."
"Mu zuba ɗin, abu ne tsakanin
ƙarya da gaskiya."
"Za ka gani ne." Alhaji
Dauda ya faɗa cikin fushi, sannan ya wuce, 'yan korensa suka rufa masa baya.
Jama'ar da ke wurin suka raka su da
ido, sannan suka dawo da ganinsu ga Aminu. Wasu sun gamsu da nufin Aminun, amma
wasu sun rasa mene ne mafita.
"Ka yi ƙoƙari, amma ka jawowa
kanka matsala." Ɗanya'u ya ce da Aminu.
"Ba wata matsala da na jawo da ta
wuce wadda muke cikinta ni da kai da sauran jama'a."
"Kamar ya ya?"
"Rayuwar rashin muhalli
mana."
Suka kalli juna.
Masu aikin taimakon fito da kayayyaki
daga rusassun gine-ginen suka ci gaba. Masu tofa albarkacin bakinsu na yi.
*
Lokacin da su Ɗanya'u da Aminu suka
koma gida, sun tarar matan gidan a tsattsaye cirko-cirko suna ta cacar baki
suna faɗa da zage-zage.
Idan da sabo, sun saba da wannan, shi
ya sa kai tsaye ba su kula su ba, suka wuce cikin ɗakunansu.
Gida ne mai ɗakuna ashirin da ɗaya,
gefe da gefe, kwata ta ratsa tsakiyar gidan, kowanne ƙofar ɗaki akwai shirgin
tukwane, kejin kaji, tirken dabbobi da tsummokarai. Mutanen da ke gidan, maza
da mata da 'ya'yansu, sun fi hamsin.
Atine; matar Ɗanya'u dake inda ake faɗan
ta tsamo kanta, ta nufi ɗaki.
A cikin ɗakin akwai 'ya'yansu guda huɗu,
ƙanana 'yan shekara goma da takwas da biyu da rabi sai ɗan wata goma sha takwas
a zaune. Ɗanya'u yana tsaye a gefen gadon ƙarfe, Atine ta shigo.
"An mutu a rusau ɗin?"
"E, mutane shida ne suka
rasu."
"Wannan gidaje na unguwar nan
kamar da laka aka gina su, ba damina ba rani gidaje su yi ta rushewa, ni Atine
yau da gobe ta fi ƙarfin wasa, wata rana abin na iya zuwa kanmu."
"Wannan maganar ta ki, ta yi kama
da maganganun da Aminu ya faɗa, cewar unguwar nan ba wajen zama ba ce."
"Ai kuwa gaskiya ya faɗa."
"Ya za mu yi, talauci ya hana mu
mallakar namu."
"Uzurin nan da kuke jingina wa
talauci shi ke talauta zukatanku. Da ka tsara, ai da tuni ka mallaki gidan
kanka." Ta ce da shi.
"Da wanne kuɗi zan sayi gida,
bayan kin san sana'a ta, kin san samuna?"
"Su kuɗi ai adana su ake, a tara
su."
"Kina son ɓata min rai ne."
"Ko kaɗan, kawai ina son in nuna
maka yadda za ka tattala rayuwarka da tamu, ka mallaki muhalli, domin suttura
ne. Idan ka duba, ko halin da muke ciki a wannan gidan na rashin kwanciyar
hankalin kasa biyan kuɗin haya, ƙunci da takaici ai misali ne, kuma yana
damunka?"
"E, yana damu na, amma ba yadda
zan yi."
"Yadda za ka yi ɗin ake faɗa
maka, kana ƙi."
Ya miƙe, "Ba ƙi nake ba."
*
Alhaji Dauda ya nemi Alhaji Sani, bai
same shi ba, sai daga baya, suka haɗu.
"Na samu labarin abin da ya faru
tsakaninka da Aminu. Rawar kai ke damun shi." Cewar Alhaji Sani.
"Wa zai yi wa rawar kai, yana
ƙaramin ma'aikaci kuma ɗan haya?"
"Allah ya huci zuciyarka."
"Tashinsa nake so ka yi, daga
gidanka."
Alhaji Sani ya yi shiru.
"Ya ka yi shiru?"
"Gaskiya, ba shi da matsalar
biyan kuɗin haya, kafin lokaci ya yi yake biya, sannan duk gidan ya fi kowa
tsafta, yanzu idan na ce zan tashe shi, ban yi masa adalci ba."
"Za ka iya siyar min da
gidan?"
"Ba zan iya ba."
"To zan ƙulla masa abin da zai sa
ka tashe shi."
"Za ka iya yin hakan, ni kuma
idan abin ya kai matsayin in tashe shi, zan tashe shin."
"Hakan ya yi, nan da kwana biyu
zan aikata."
Suka tafi. Mintuna goma tsakani,
Alhaji Sani ya aika aka kirawo Aminu, bai fi mintuna goma ba shi ma ya zo.
Aminu ya gaishe shi cikin girmamawa.
"Zauna."
Aminu ya zauna.
"Shawara nake son ba ka. Ya
kamata ka guji shiga hurumin irin su Alhaji Dauda, ba don ba na son tashinka
ba, da yanzu na tashe ka daga gidana."
"Da ka yi wannan maganar sai na
ga, ya kamata in ba ka shawara Alhaji."
"Ina sauraronka." Alhaji
Sani ya amsa cikin mamaki.
"Bai kamata haka kawai saboda
raunannen dalili ku rinƙa tashin mutane daga gidajenku a lokacin da tashin na
iya zame musu shiga garari ba."
Ya girgiza kai.
"Lallai dole ku sami matsala da
Dauda. Ai mu a wurinmu 'yan haya kamar ɗaliban makarantar allo ne, wani lokacin
shiru kawai za mu ji mu kai tafka, wato mu tashi wanda muka ga dama, mu sa
wani, ko mu ƙara kuɗin haya yadda ranmu ke so, ba yadda za a yi da mu."
"Ka ga ai hakan bai dace ba.
Kawai don ina nema wa kaina mafita shi ne yake min bi-ta-da-ƙulli, to gaskiya
ba zan daina ba."
"Ai kuwa zan iya tashinka daga
gidana."
"Ba matsala, fatana in mallaki
nawa."
"Ai shikenan, na lura kai ɗan
kuka ne, mai ja wa uwarsa jifa, za ka iya tafiya."
Suka yi sallama.
*
Sa'ar da Aminu ya koma gida, ya yi
daidai da lokacin da Tani mai ƙosai ta yo jifa da faranti don samun Ɗanya'u, ba
ta same shi ba, ta kusa rushe wa Aminu kai, Allah ya kiyaye shi.
Ya koma gefe yana kallon abin da ke
faruwa. Faɗa ake tsakanin Tani da Ɗanya'u.
"Matsiyaci, duk gidan nan kai kaɗai
ne ɓutal, wanda sai an kai ruwa rana kafin ka iya biyan kuɗin haya, wallahi da
gidana ne, da tuni na daɗe da tashinka."
"Na ji ɗin, amma ni ban tara
'ya'ya da miji kwarata ba, masu bin ɗakuna da makwancin yara mata suna lalata
su."
Haka abin yake, don shi abin ya fi
shafa, 'ya'yansa mata 'yan shekaru sha shida da sha takwas da kuma sha huɗu
idan ana ruwan sama a zaure suke kwana, kuma an sha kama 'ya'yan Tani har da
mijinta suna kai musu hari.
"Allah tsine mai ƙarya?"
Tani, ta tsani a danganta 'ya'yanta ko mijinta da kwartancin, duk da ta san
suna yi.
"Wallahi wata rana sai na sa
hukuma ta kama su, ta yi musu hukuncin fyaɗe."
Takaici ya ƙule Aminu, ya saba ganin
haka a gidan nan, amma kullum abin ci gaba yake, ya sha gaya wa Ɗanya'u ya
daina shiga sabgar mata amma bai daina ba.
Ya isa gare shi.
"Wannan ba girmanku ba ne."
"Ka ga Aminu ka ƙyale ni, babu
wata 'yar iska a gidan nan da zan ɗaga wa ƙafa. Duk wacce ka ƙyale sai ta raina
ka."
Daga can Tani ta ɗago murya, "Kai
ne ɗan iska, mara mutunci."
Aminu ya ce, "Don Allah ka yi
haƙuri mu je waje."
Da ƙyar ya fita.
*
Alhaji Sani ya kira Alhaji Dauda ya
shaida masa yadda suka yi da Aminu.
Ran Alhaji Dauda ya ɓaci matuƙa, a
wayar ya ce.
"Wannan shi ne dalilin da ya sa
na ce ka tashe shi, yanzu ai shi ke nan, zan cika aikin da na ce zan yi."
"Ya yi."
*
Washegari da safe, Aminu da Ɗanya'u da
Saleh suka ratsa cikin unguwarsu suna ta faman tsallake-tsallaken kwatami.
Gabaɗaya faɗin santocin a ƙuntace
suke, ba su wuce ƙafa ashirin da biyar ba (25 feet), yadda aka jingina da
gicciye gine-ginen sam babu tunani, da yawan santocin motoci ba za su iya bin
su ba, don suna cike da shadda (soak-way) da ramukan tara ruwan ƙazanta da
kwatoci da suke malala a kan layir.
"Ku duba, ku gani, yanzu waɗannan
layuka ta ya mota za ta iya wucewa ta cikinsu?"
"To ai ba a yi su don wucewar
motoci ba." In ji Sale.
"Ka ga ai bai kamata ya zama haka
ba. Dubi yanda tun kafin mu je wurin da za mu, duk ruwan kwatami ya ɓata
mu."
"Rashin magudanan ruwa da waɗannan
ruwan ƙazantar za su rinƙa malala a ciki kenan." Sale ya faɗa.
Aminu ya ce, "Yawwa ɗan gari,
idan ka ɗauke guraben zuba shara, haƙiƙa magudanan ruwa wato kwatoci suna cikin
ginshiƙan samar da tsafta a kowacce unguwa, sannan suna rage hatsarin ambaliyar
ruwa musamman a lokacin mamakon ruwan sama.
"Amma dubi yadda muke cikin
rashin tsafta, unguwa kaca-kaca, hanyoyi duk a jagwalgwale, kun san irin
ambaliyar ruwan da muke fuskanta a damina..."
"Kuma ga mummunar asarar rayuka
da ta dukiya da ake tafkawa." In ji Sale.
"Ka manta yadda saboda rashin
hanya 'yan kwana-kwana ko jami'an ceton rai suke kasa shigowa da motocinsu don
ceton rayukan." Aminu ya faɗa.
Suka sha wata kwana, a daidai lokacin
an kwararo ruwan kashi ya malala kan layir, dole suka kauce ta gefe suna tsaki.
"Kalli don Allah, ku gani. Irin
abubuwan da muke magana kenan suna haifar ko jawo ɓarkewar cutuka kala-kala, a
rinƙa ɗora wa wani abu daban, ko a ce annoba, alhalin yanayinmu da
zamantakewarmu ce ta haifar da annobar."
Aminu ya ƙarashe zancen cikin damuwa.
Ɗanya'u ya nisa, "Sai yanzu na
gano dalilan da ya sa ababen hawa ba sa shigowa wannan unguwa tamu."
"Ƙwarai kuwa, hatta jami'an
lafiya da masu yin riga-kafi ƙaurace mana suke, saboda ba za su iya shigowa
ba."
Suka yi shiru, suna tafiya, har suka
bar unguwar, suka je inda suka nufa, wato unguwar da gwamnati ta tsara. Ga
kayan aikin gini nan an fara kawowa.
Suka tsaya, suna duba wajen. Aminu ne
yake nunnuna musu sassa na wajen.
"Duk nan da kuke gani an tsara
komai na gina gidaje a tsare, da santoci wadatattu da magudanan ruwa da
wadatattun ƙofar gida da wuraren dirakun wutar lantarki, kai komai an fitar har
da filin gina asibiti da makaranta."
"Allah mai iko." Cewar
Ɗanya'u.
Aminu ya kalle su.
"To maganar gaskiya, yanzu ya
kamata ku fahimci abubuwan da suke hana unguwarmu da ire-irensu samun kayan
more. Shin ta ya ya gwamnati za ta samu fili ko sararin shiga da motocinta masu
shimfiɗa bututun ruwan sha, ko na haƙa rijiyoyin tuƙa-tuƙa na zamani, ko
motocin kafa dirkokin wutar lantarki?
"Ina gwamnati za ta sami filin
gina asibiti ko makaranta ko maƙabarta? Yanzu ko koke-koke al'ummar irin wannan
unguwar tamu suka yi don a yi musu aiki, abin gagararta yake saboda an bar rini
tun ran zane..."
"Me ya sa zai gagare ta?"
Sale ya buƙata.
"Saboda idan za ta gina asibiti
ko makaranta sai ka ga iya kuɗin diyya na gine-ginen da za ta siya da rushewa
da gyara filin da tunanin yadda za a rinƙa shiga da kayan aiki ya isa a gina
katafaren asibitin a unguwannin da suke da tsari da sararin filin. Don haka
gwamnati ke gwammacewa ta gina a inda ba za ta biya diyya ba."
"Allah mai iko." Ɗanya'u ya
sake faɗa, Sale kuwa ajiyar zuciya ya yi.
"Wani abin kuma, gwamnati tana
yawan kashe kuɗi a unguwanni irin tamu, saboda cutuka da ke faruwa da ƙoƙarin
shawo kan annoba."
Suka ɗan yi shiru, kafin daga bisani
Ɗanya'u ya nisa, ya ce "Aminu, muna buƙatar ka ɗaura mu a layin da mu ma
za mu mallaki namu muhallin a unguwa mai tsari."
"Abin da nake ta ƙoƙarin yi ke
nan."
"To mu dai muna biye da
kai."
*
Rashin tsaro ya zama ruwan dare a
Kwarin Goga, don haka sace-sace, faɗan daba da rikicin wajen zuba shara ke
yawan faruwa.
Ka-zo-na-zo, da rashin sanin halin
kowa ke haifar da wannan al'amari.
A daren yau ma abin da ya faru kenan, ɓarayi
suka haura gidajen mutane suka yi sata. Bayan sun gudu, mutane suka taru a
wurin suna faɗin albarkacin bakinsu.
"Ɓarayin nan fa 'yan unguwar nan
ne." Cewar ɗaya.
"Ƙwarai, ai kowa ya sani, sau
nawa ana zuwa a kama manyan ɓarayi da 'yan fashi da masu satar mutane a unguwar
nan, ban da gidajen karuwai, na tabbatar akwai gidaje da yawa masu ɓoye masu
laifi."
"Na fara yarda da maganganun
Aminu, unguwar nan ba wurin zama ba ce, kawai mutum ya nemi mafita, ya nemi
unguwa mai tsari, ya koma."
"Gaskiya kam, kar a rayu a banza
a mutu a wofi, muhalli suttura ne..."
Duk hirar da suke yi, Aminu na gefe
yana jinsu. Aka gama abin da za a yi kowa ya kama gabansa.
Da safe misalin ƙarfe shida 'yansanda
da Alhaji Dauda da yaransa, suka iso ƙofar gidansu Aminu, a can bayan unguwar
suka ajiye motarsu.
Suka fito da shi, take mutane suka
cika wajen.
"Me na yi?" Aminu ya
tambaya.
Ɗansandan ya ce, "Idan muka je
ofis za ka ji."
"Ka gaya masa mana." Cewar
Alhaji Dauda.
"Hukumar 'yansanda da masu
gidajen unguwar nan suna zarginka da bai wa ɓata-gari maɓoya, hatta satar da
aka yi jiya ma ana zargin kai ka ɓoye ɓarayin."
Kowa ya yi shiru.
Wani saurayi ɗan shaye-shaye, dake
kwance a ƙofar gidan mai suna Falan-ɗaya ya taso cikin layi yana magana irin ta
'yan maye.
"Sori yallaɓai kun yi mistek,
wannan gayen fa e, ustaz ne ba ruwansa. To wai ma ina zai ɓoye su, ɗaki ɗaya fa
yake haya a gidan nan."
Alhaji Dauda ya ce, "Kai yi mana
shiru ko mu tafi da kai, kana cikin maye za ka kare mai laifi. Yallaɓai ku haɗa
da shi kawai."
"Yahaj zan buɗe aiki fa. Don
yaranka su Jagu ne suka yi satar jiya, duk na gansu, don ba ruwana ne, amma da
tun a jiyan zan ɓarar da su. Kuma a je a zo da su, idan na yi musu ƙarya."
Jikinsu ya yi sanyi.
"Alhaji ka gani, sharrinka ba zai
ba ka kariya ga yadda kuke cutar da al'umma a unguwar nan ba, kuma sharri ɗan
aike ne, yana dawowa wanda ya aike shi."
Cikin sanyin jiki suka bar wurin shi
da 'yansandan.
*
Kwanaki na gotawa, watanni na shiga,
har 'yan kwangilar da za su yi gini a unguwar da gwamnati ta fitar ta kusa da
Kwarin Goga suka fara gine-gine masu tsari da fasali.
Hakan ya tayar da hankulan su Alhaji
Dauda, suka fara zuga al'ummar Kwarin Goga wai gine-ginen sabuwar unguwar za su
ƙara haifar da toshe musu hanyoyin ruwa, su rinƙa samun ambaliya. Don haka su
kai shi ƙara, don a hana su yin ginin, su za su biya komai.
Wasu daga ciki suka tunzura, duk da su
Aminu da Ɗanya'u da Sale sun rinƙa wayar musu da kai cewar ba haka abin yake
ba, amma ba su ji ba. Suka kai ƙarar.
Aka sanar da Alhaji Mahmud halin da
ake ciki, na kai shi ƙara da mutanen unguwar Kwarin Goga suka yi.
Alhaji Mahmud ya ce "Hakan ya yi
kyau, ta hakan ma za su iya sanin suna zaune a matsugunnan da shari'a da tsarin
ƙasa ya haramta."
"Haka ne Alhaji, ka yi amfani da
ilimi." Cewar wanda ya kawo masa labarin.
Alhaji Mahmud ya sanar da lauyansa
halin da ake ciki.
A can ma gidan haya, Alhaji Sani ya
gaji da rashin biyan kuɗin hayar irin su Ɗanya'u da wasu 'yan haya uku, kai
tsaye, ya sa yaransa suka watso musu da kayansu waje, sannan ya kai Ɗanya'u
ƙara, saboda yana bin sa kuɗin shekara ɗaya da wata huɗu, tsawon lokaci bai
biya ba.
*
A ranar sauraron ƙarar, kotun ta cika.
Ƙarar farko da aka kira, ta Alhaji Sani ce da ya kawo Ɗanya'u.
"Alhaji Sani, mene ne ƙarar ka?"
"Ranka ya daɗe, ina ƙarar Malam
Musa Ya'u ne, ya zauna a gidana tsawon shekara ɗaya da wata huɗu bai biya ni kuɗin
haya ba."
Alƙali ya dubi Ɗanya'u.
"Malam Musa, ka ji abin
da Alhaji Sani ya faɗa, haka ne?"
"E haka ne ranka ya daɗe, amma ni ma
ina da magana."
"Yi maganarka."
"Mun yi zaman takaici da takura a
gidan Alhaji Sani na tsawon shekaru ashirin da takwas, kuma a cikin wannan
lokacin ana keta min haddin iyalina da 'ya'yana."
"Shi mai gidan ne ya keta maka
haddin?"
"A'a, 'yan hayar da muke tare
ne."
"Me ya sa ka zaɓi zaman gidan
haya na tsawon waɗannan shekaru ba ka gina naka muhallin ba?"
"Ba ni da kuɗi, ni talaka
ne."
"Ba ka da sana'a ne?"
"Ina da sana'a. Amma abin da nake
samu bai fi na abinci ba."
"Malam Musa idan har kana sana'a,
kuma kana da iyali ai ka san za ka hayayyafa ko?"
"Na sani."
"Idan haka ne ya kamata a ce ka
tsara yadda za ka mallaki muhallinka na kanka, domin muhallinka shi ne
sirrinka, shi ne mutuncinka, kuma shi ne rayuwarka. Yadda ka
mallaki matan da ka aura ta hanyar tara kuɗin aure da
hidindimu da kuɗin haya, haka ya kamata ka tara kuɗin siyen
muhallin da za ka rayu a ciki."
"Haka ne ranka ya daɗe, na yi nadamar hakan. Amma yanzu
babban takaicina shi ne,
bayan ƙarin kuɗin haya da yake yi mana
lokaci-lokaci, yanzu da ya tashi korar mu, ya sa aka watso mana kaya, bai ƙyale ni ba, ya kawo ni ƙara wai in biya shi tsohon bashin
kuɗin hayarsa."
"To ka ga duk waɗannan matsalolin
da ka zayyano rashin mallakar muhallin kanka ne ya jawo maka. Da naka ne, babu
mai tayar maka da hankali. Kuma mallakar muhallin nan yana da sauƙi, akwai
bankin bayar da lamuni da kawai za ka tuntuɓa, a yi maka bayani a sauƙaƙe cikin
Hausa, ka cike sharuɗɗa, cikin kwanciyar hankali sai ka mallaki
muhallinka."
"Batun mallakar muhalli, akwai
wanda muke zaune da shi, mai suna Aminu, ya fara jagorantarmu don cimma wannan
manufa, kuma mun yi nisa. Wannan lamari ya riske ni ne, ban shirya ba." Ya
marairaice. "A kan biyan bashin kuɗin hayar kuwa ina neman alfarma, wallahi ba ni
da kuɗi, yanzu ma, sai wani kango na nemi alfarma aka ba ni, muka sa kayanmu,
matana da 'ya'yana suka zauna, amma zan biya shi."
Alƙali
ya yi ɗan rubutu a littafin gabansa.
"To ka ɗauki lokacin da za ka iya
biyan kuɗin mu ji."
"A ba ni wata biyar."
"An ba ka."
Bayan an sallami Ɗanya'u, sai aka aka
karanto ƙara ta biyu, ƙarar da al'ummar unguwar Kwarin Goga suka kawo Alhaji
Mahmud.
Al'ummar suna ƙarar shi da cewar, yana
yin gine-ginen rukunin gidajen da za su tsare musu hanyoyin ruwa da kuma shige
da ficen.
Bayan saurare, alƙali ya fara karanto hukunci kamar haka:
"Bisa la'akari da tsarin fasali
ko taswirar filaye da ma'aikatar tsara birane ta jiha da kotu ta samu, ta gano
cewa dukkan gine-ginen da aka yi a unguwar Kwarin Goga an yi su ne ba bisa
tsari da fasali ba, asali ma wurin hanyar ruwa ne, kawai dillallan awon igiya
ne, suka sayar da filaye ba bisa ƙa'ida ba. A ƙarshe kuma kotu ta gano cewa wurin da Alhaji Mahmud ya fara gininsa shi ne
halastaccen filayen da gwamnati ta fitar, ta kuma sahale a yi gini. Don haka kotu, bisa dokar ƙasa ta bayar da notis na
watanni uku waɗanda suka yi gine-gine a kan magudanan ruwan Kwarin Goga, su
tashi domin a rushe
gine-ginen, a bi tsarin da ya kamata.
"Shi kuma Alhaji Mahmud ya je, ya
ci gaba da gininsa ba tare da barazana ba, sannan za a biya shi diyyar ginin da
aka rushe masa. Sannan kotu ta gano Alhaji Dauda a matsayin wanda ya zuga
jama'a suka rushe gine-ginen mutane, kotu ta bayar da oda a kamo shi."
Jama'ar suka fara
guna-guni, da 'yan maganganu.
"Zaluntarmu za a yi, gidajenmu sun fi shekara da
shekaru a wurin, amma a ce za a
rushe..."
Wani ma ya ce, "Kawai cin hanci ya bayar."
Alƙali ya dakatar da su, yana dubansu,
"Kotu ba ta yanke abu sai da hujjoji, ga lauyoyinku nan, idan hukuncin da
aka yanke ba haka yake ba, za su yi magana. Sannan ƙari a kan haka
shi ne."
Ya ɗauko taswirar tsarin (plan)
unguwar Kwarin Goga da wasu takardu ya miƙa wa lauyoyinsu.
"Wannan shi ne taswirar yadda
gwamnati ta tsara unguwanni a wannan jihar ciki har da unguwarku da takardun
filaye."
Suka fara duba fasalin. Alƙali ya ci gaba da
bayaninsa.
"Ya kamata ku san, muhalli babban
jigo ne ga rayuwar halittun Allah, don daga abinci sai muhalli a jerin buƙatu
na kowacce halitta. Amma mutane kan yi sakaci wajen nema da tsara wa kansu
muhalli mai inganci.
"Hukumar tsara birane (Ministry
of Land and Survey ) kan yanka rukunin filayen gidaje na unguwanni, masana'antu
da kuma kasuwanni. Ita kuma hukumar Tsara Gidaje (Housing and Cooperation) ita
ke tsara taswirar gine-ginen gidajen kwana na kowane rukunin gidajen da kuma
aikin gina su.
"Sannan ita hukumar ke tabbatar
da bin ƙa'idojin gini, da hanyoyi da magudanan ruwa da dirkokin wutar lantarki
da kuma bututun ruwan sha da sauransu. Kafin daga bisani ta cefanar da su ga
sauran mabuƙata ta hanyar bankin bayar da lamuni na gine-gine wato (Federal
Mortgage Bank).
"Kamar yadda shaidu suka
tabbatar, unguwarku da kuka gina, ba a kan tsari da fasali aka yi gine-ginen
ba, an yanka filaye ƙanana da ba su fi tsayin ƙafa arba'in da faɗin ƙafa
ashirin (40ft x 20ft) ba, sannan an yi muku gine-gine na ha'inci, hatta
santocinku ƙafa ashirin da biyar ne, kuma a kan layir kuke yin shadda
(soak-away) da ramukan tara ruwan ƙazantar da kuke korowa ta rariyar banɗaki,
maimakon ginin magudanar ruwa.
"Ga shi ana samun zaizaya da
yawan rushe-rushen gidaje a rani da damina saboda kun yi amfani da kayayyakin
gine-gine marasa inganci, ga asarar rayuka da dukiyoyi da ake yi. Ko ba haka ba
ne?"
"Haka ne." Suka amsa a
sanyaye, don maganganun sun ratsa su. Ya ci gaba.
"Don haka, kun ga idan an ƙi sharar masallaci, a yi ta kasuwa.
Ya kamata ku gyara."
Wasu suka gamsu, wasu kuma suka ƙi yarda.
Ana fitowa daga kotun wasu daga
mutanen unguwar suka ɗunguma, suka sami Aminu, suka bayyana masa gamsuwarsu da
duk jawaban da yake musu a baya, don alƙali ya ƙara tabbatar musu.
"Amma mene ne mafita?" Ɗaya
daga ciki, ya buƙata.
"Da farko, kamar yadda na sha faɗa,
akwai bankin bayar da lamunin mallakar gidaje, wanda yake shigewa duk wani ɗan
Najeriya tun daga ma'aikacin gwamnati zuwa ɗan kasuwa da masu aikin fasaha da
direbobin motocin haya da sauransu, musamman masu ƙananan ƙarfi irinmu wajen
mallakar muhalli.
"Bankin yana da tsarin asusun
adashin gina gidaje na ƙasa wato adashin gata, kowa a cikinmu ɗin nan tsakanin
ma'aikacin gwamnati da ɗan kasuwa musamman mai samun aƙalla dubu uku a wata,
zai zuba adashi a wannan asusu, zai ba da biyu da rabi 2,5% na misalin dubu
ukun wato adadin samunsa, ko na albashinsa. Yin hakan zai bai wa mutum damar ya
nemi rance na gina muhallinsa, ko na gyaran gida.
"Asusun da ke bai wa mai ajiya
damar mallakar gida a rukunin gidajen da ɗan kwangila ya gina ko kuma banki ya
ba da kuɗi aka gina. Idan kana wannan ajiyar da zarar ka samu dama da cika
ƙa'ida, kamar ma'aikacin gwamnati idan ya yi watanni shida yana ajiya, shi kuma
ɗan kasuwa ko sauran suka kai shekara suna ajiyar, bankin zai siya maka gida a
irin gidajen nan.
"Sannan idan ma a cikinmu akwai
mai fili musamman yankan gwamnati, mai takardar mallaka, kuma kana zuba adashi
a wannan asusu, za ka iya neman rancen kuɗi har miliyan goma sha biyar, bankin
ya ba ka ka gina gidan da kake so.
"Idan ma ƙungiya gare ku mai
rijista, wacce ta cike dukkan ƙa'idoji, kuma tana da asusu a wannan banki,
ƙungiyar za ta iya neman kuɗi ta gina wa 'ya'yan ƙungiyar gidaje a inda ya
dace.
"Akwai kuma tsarin gyaran gida,
yadda mai ajiya zai iya neman kuɗi naira miliyan ɗaya don gyaran gidansa, idan
ka samu canji ma har ka ƙara jari. Kuma wannan bashin yana iya kai har tsawon
shekaru biyar kafin ka biya, ko iya lokacin da kake so na ƙasa da shekaru biyar
ɗin - idan ma'aikaci ne, lokacinka na aiki bai gaza shekara biyar ɗin ba, ko
shekarun ka ba su kai sittin ba.
"Kuma ba kamar a baya ba, a yanzu
duk mai yin ajiya yana iya sanin me ya ajiye, idan ma'aikaci ne ya san me
ma'aikatarsa ta aika wa bankin, ya ji alert, ya ga balas. Da wayar hannunka za
ka danna lambobin *291# don ganin bayanan asusunka."
Ya ɗan yi shiru.
"Abin da kawai ake buƙata shi ne;
mutum ya yi rijista da reshen bankin da ke jiharsa ko ta yanar gizo. Kuma gabaɗaya
abin da ake cira shi ne 6%."
"Abin ba wahala, ga sauƙi."
Cewar Sale. "To wai ya aka yi yanzu ake sanin waɗannan damarmaki?"
"Ni dai zan iya cewa, saboda
ƙoƙarin daraktan bankin ne na yanzu, wato Arch. Ahmad Musa Ɗangiwa, domin
amfanar mutanenmu."
"Amma Allah ya saka masa da
alheri."
Suka amsa gabaɗaya, amin.
Cikin watanni, sai ga Aminu da Malam
Musa da Sale da sauran al'umma da suka gamsu da Aminu, sun mallaki ingantattun
gidaje a unguwar Alhaji Mahmud ya gina.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.