Amrah A. Mashi (2023). Tun Ran Gini.... Ɗaukar Jinka (Labaran Da Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun Labarai Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2022). Kangiwa Multimedia and Communcation Company LTD
TUN
RAN GINI...
Na
Amrah
A Mashi
Tsayuwarshi
ya daidaita yana kallon ɗanshi Kabiru, hula a karkace
kana gani ka san babu mutunci. Matar
da ke gabanshi ta ce,
“Kada
mu yi haka da kai Ilu. Ka ce ba za ka iya ɗaukar
nauyinshi ba, ni na ce zan iya. Ka bar shi ya yi karatunshi don Allah, ilmi shi
ne jigon rayuwar ɗan Adam, don kai kanka da a ce ka yi shi da
yanzu ka wuce wannan rayuwar da kake cikinta ta duhun kai.”
Ya
mayar da dubanshi ga matarshi Safare, yana jin zafin kalaminta. Cike da tijara
ya ce,
“Safare
ni ne mai duhun kai?”
“To
idan ba duhun kai ba Ilu me zai sa ka kasa ɗaukar
nauyin karatun ɗanka? Ɗa ɗaya
tilo da Allah ya ba
ka? Wallahi ka dai ji kunya.” Kyakkyawan
mari Ilu ya ɗauke ta da shi, sannan ya ce,
“Ki
je gidanku na sake ki saki ɗaya. Kuma ban yarda ki tafi
da yarona ba. Boko dai ce
na ce ba zai yi ba, ina ruwan wani da wani, wai an ce da mahaukaci ka yi baƙo?”
Da
azama Kabiru ya rungume mahaifiyarshi yana sakin kuka. Bai so a ce saboda shi
iyayenshi sun rabu ba.
Tuni
Safare ke son barin gidan amma saboda makomar rayuwar Kabiru take zaman haƙuri. Zaman aure da Ilu ba ƙaramar jarabawar rayuwa ba ce. Don haka
yanzu sai ba ta wani damu ba. Ƙaramar
jaka ta shiga ɗaki ta haɗa
kayan sakawarta a ciki. Tana ji tana gani ta rabu da ɗanta
mai shekaru goma sha huɗu a duniya, yana kuka tana
kuka ta bar gidan.
Duk
son da Kabiru yake wa boko dolen shi ya haƙura.
Babu kuɗin
karatun. Don haka sai ya cire son karatun ma daga rayuwarshi kwata-kwata. Sai
dai dangana da boko ba shi ne ya zare masa ra’ayin neman kuɗi
ba. Gani yake kamar zafin talauci ne ya sanya mahaifinshi zama a cikin duhun
kai. Don haka sai ya ɗauki alwashin ba zai taɓa
yin rayuwa irin ta mahaifinshi ba. Ba zai zauna babu ilmi ba kuma ya yi rayuwar
talauci ba. Zai tashi ya nema da guminshi, zai yi kuɗi da
ƙarfinshi. Budurwa mai ƙwazo ko ba miji tana iya haihuwa.
Daga
cikin garadan makarantar allonsu akwai waɗanda
suke tafiya Legas (Lagos) neman kuɗi.
Kabiru ya ci alwashin yin ladabi ga ɗaya
daga cikin masu zuwa biɗa can Legas ɗin
don ya yi masa hanya shi ma ya tafi. Zai yi kuɗi,
zai fice daga duhun kai!
Wani gardi Idrisa ya faɗa masa matakan da
zai bi ya tafi, Kabiru ya ji daɗi ƙwarai, ya kuma sa a
ranshi kwanaki ƙalilan masu zuwa zai haɗa naira dubu bakwai
da ɗari biyar kuɗin mota, zai fara da kwana ƙarƙashin gada kafin
ranar da zai fara neman nashi.
Da
murna Ilu ya dawo gida, layin maular da suke ta aikin bi kullum yau ya zo
kansu. Tsohon ɗan majalisar jiha ya ba su kyautar naira dubu ɗari
biyar, suka raba kowa ya tashi da dubu ashirin. Hula karkace ya hakimce yana
sauraron shirin hantsi, da robar ɗanwake
a gabanshi. Kabiru na gefenshi yunwa kamar ta kar shi amma ko kallon inda yake
Ilu bai yi ba. A ƙarƙashin filonshi ya soka waɗancan
kuɗaɗen,
Kabiru na kallon su kuma su ya ci burin ya ɗauka
saboda gobe Laraba da yamma motar Legas ke tashi daga ƙauyensu.
Sai
da Ilu ya gama cinye ɗanwakensa tas ya lashe kwano
sannan ya miƙe domin wanke hannu.
Kwata-kwata ya manta da kuɗinshi da ke ƙarƙashin
matashin kai, da ba zai yarda ya bar su a wurin ba.
Daga
wanke hannun ma sai ya wuce banɗaki. Kabiru ya lalube kuɗin
nan tas.
Da
azama ya fice yana yi yana waige don kar baban nashi ya dawo bai samu damar
barin gidan ba.
Shi
kuwa Ilu ya ɗan ɗauki
lokaci a banɗakin kafin ya fito yana rera waƙar Ɗankwairo,
“Yaran Ɗankwairo
goma sha shidda,
an ka yi total anka
haɗa,
ya zama fayib sauzan
da sis handured nera...
fayib sauzan da sis handured nera...”
Bai ɗora
waƙar ba kasantuwar filonshi da ya gani ba
yadda ya bar shi ba. Rediyonsa a kwance setinta ma ya goce. Ya nufi filon ya ɗaga,
wayam!
“Tsiya
ta auku.”
Ya
faɗa
yana ɗora
hannu a ka.
“Kabiru!
Kabiru kana ina? Ka jiye mini tsinannen yaro? Fito mini da kuɗina
ko kuma wallahi yau hukuma ce za ta raba mu.”
Ya
nufi ɗakin
Kabirun babu kowa. Ya fito ya nufi ƙofar
gida amma babu ko ɗishi-ɗishin
Kabiru. Shi kam yau ya shiga ukku! Kuɗin
da ya ci burin fara neman auren wata sakin wawa ne da suka fara daidaita kansu.
Amma dai an yi lalataccen yaro ya faɗa a
bayyane.
Kabiru!
Tunda
nake a rayuwata ban taɓa ɗaukar
abin da ba nawa ba. Na samu kyakkyawar tarbiyya daga wurin mahaifiyata, na san
illar sata na kuma san makomar mai yin ta. Sai dai a yau, ba ni da wani zaɓin
da ya wuce in ɗauki na mahaifina. Ba zan ce ba a taɓa
halittar wata halitta mai mugun son abin duniyar Babana ba, sai dai zan iya
cewa tunda na yi wayo ban taɓa ganin mutum mai son kuɗinsa
ba. A kan kuɗi zai iya ɓatawa
da kowa. A kan kuɗii ya zaɓi
rabuwa da mahaifiyata. A kan kuɗi ya zaɓi
barin rayuwata ta tagayyara a bisa titi. Idan har ban ɗauki
waɗannan
kuɗaɗen
ba ba ni da wata hanya da zan iya samun kuɗin
tafiya Legas ɗin da nake son zuwa. Kuma idan na bari
wannan damar ta wuce ni shi kenan ba zan tafi tare da Idirisa ba, shi ne nake
da yaƙinin zai taimaka mini tunda shi ya saba
zuwa.
A
lokacin da zan ɗauki kuɗin
har sai da wani imani ya zo min, na ji tausayin Babana saboda wahalar bin layi
cikin rana da gumi da ya yi duk don ya samu kuɗin
nan amma ni ga ni nan daga zaune na ɗauke
su. Sai dai kuma, tun da nake da shi ban taɓa
ganin ya tausaya mini ba. Idan ciwo nake yi Innata ce, ta gama sayar da komai
nata duk domin farin cikina. Da kuɗinta
na yi karatun firamare har na kammala. Sakandare ce ta gagara saboda komai nata
ya ƙare tana masa maganar ya ce ba da
yawunsa ba ba kuma zai saka ko sisinsa ba. Da ta ce ta yarda za ta ci gaba da
buga-bugar nema don in yi karatun shi ne ya ce duka karatun nawa ne ma bai
yarda da shi ba.
Kai tsaye daga nan na wuce makarantar allonmu wurin su
Idirisa, na faɗa masa na haɗa kuɗin tafiyar amma ina neman alfarma, a wurinsa zan kwana
kafin tafiyar tamu gobe, ya kuma amince mini. Zuciyata ta rarrabu gida biyu,
wata na ba ni shawarar in je in yi bankwana da Innata in faɗa mata inda zan je,
wata zuciyar tana hana ni, don na san zai yi wuya ta bar ni in tafi, ni kuma na
riga na sa ma raina tafiyar nan don kuɗi nake son yi, kuɗi ba kuma na haram
ba, kuɗi zan nema da ƙarfi da gumina.
Sannan na tabbata wurin mahaifiyata ne wuri na farko da
Baba zai je nema na idan ya duba kuɗinsa babu.
A
wurin Idrisa na kwana. Washe gari da ƙarfe
biyu aka fara lodi a motarmu. Bayan la’asar ta tashi sai Birnin Ikko.
Kwananmu
biyu a hanya sannan muka isa. Ina da sauran kuɗi a
hannuna ban yi zaman yunwa a mota ba, Idrisa ma ni na saya masa fanke da lemu
sadda muka isa Lakwaja.
Isar
mu Ikko Idrisa ya ce mini ya gama nashi, kowa tasa ta fisshe sa, shi ma kanshi
kara shi ake a ɗakin wani abokin abokinshi.
Daga nan hankalina ya tashi, don ban san inda zan nufa ba. Ina kallo Idrisa ya
tafi ko waigena bai yi ba. A hankali nake takawa har na isa bakin tasha inda na
tarar kowa harkar gabansa yake yi.
Na
jima tsaye ina tunanin mafita sai kawai na ji an taɓa
ni. Ina waigawa na ga Idrisa ne ya kama hannuna kawai ba tare da ya ce komai ba
muka kama hanya. Babur ya tsayar mana guda ɗaya
muka hau mu biyu. Mun ɗan yi tafiya mai tsayi kafin
muka isa wata unguwa mai cike da bololi ga wani irin ɗoyi
da yake tashi kamar na mushe. Hancina a doɗe
haka muka sauka daga babur ɗin. Idirisa ya tambayi kuɗin
matashin ya ce dubu biyu. Ido na buɗe
ina tuna ‘yar tafiyar da muka yi wacce idan a garinmu ne ba zai wuce naira
tamanin ba amma wai har dubu biyu. Kallon da Idirisa ya yi min ne ya sa na gane
nufinsa. Na zaro kuɗin na miƙa masa sannan na bi bayan Idirisa sai ga
mu a gaban wasu gidaje ko in ce ɗakunan
kwali. A gaban wani mai lamba goma muka ƙarasa.
Rufe yake ɗakin sai da ya kira abokin nashi ya faɗa
masa shi ba ya nan ya je gida noman rani amma ainahin mai ɗakin
yana nan zai turo shi yanzu. Babu jimawa sai ga Jafaru ya zo muka gaisa da fara’arshi
ya buɗe
mana ɗakin
muka shiga.
Katifu
ne guda biyu irin na ‘yan makaranta sai tabarmi guda biyu, sannan daga gefe
akwai risho da tukunya sai ‘yan tarkacen kicin waɗanda
suka zama dole a buƙata.
Kwanakinmu
biyar a Legas Idirisa ya ce shi dai zai tafi wurin Oganshi inda ya saba karɓo
babur sojan haya. Har a wannan lokaci ban gama yanke ma kaina hukuncin aikin da
zan yi ba. Duka-duka shekaruna goma sha huɗu
ina cikin ta sha biyar, tuƙin
babur ya fi ƙarfina, ba kowa ba ne
zai yarda ya hau tunda ba girman jiki gare ni ba, ban ma iya babur ɗin
ba. Ban san me ya dace da ni ba sai na tambayi Jafaru bayan tafiyar Idirisa.
“Ban
so ka baro gidanku da ƙananun
shekarunka ba Kabiru. Dukkaninmu nan da ka gani ba mu zo nan ba har sai da muka
san ciwon kanmu. Zaman Legas ba zaman Katsina ko Kano ba ne. Gari ne na ka zo
na zo kuma kowa da ka gani a nan neman kuɗi ya
zo sannan kowa da ƙuduri
da halinsa. Ina gudun kada ka samu masu ha’intarka.”
Shiru na yi ina nazartar kalamansa, gaskiya ya faɗa min sai dai kuma
ta yaya zan iya nufar gida yanzu bayan burina bai cika ba? Da
wace fuskar ma zan iya tinkarar gidan Babana idan na koma ba tare da na yi kuɗi
ba? Zan yi su, duk da ƙananun
shekarun nawa. Na ba kaina amsa.
Jafaru
na da kirki sosai sannan ya tsayu da ƙafafuwansa
a Legas ɗin.
Shi da kanshi ya ba ni sana’ar yi, ina cikinta amma kai tsaye ba zan ce ga ta
ba, saboda ban san ko mene ne nake sayarwa ba. Abin dai da na sani shi ne, duk
waɗanda
yake saka ni ina kai wa waɗannan kayan to ba mutanen ƙwarai ba ne. Abu ɗan ƙarami a leda zan ba mutum amma ya ba ni
karancin kuɗi ya ba ni dubu ɗaya.
Ko
kaɗan
Jafaru ba shi da ƙeta,
yana biyana haƙƙina sannan ci da
shana duk a wurinsa suke.
Rana
guda na gane ashe kayan maye ne nake sayarwa, tun daga kan ƙwayoyi har zuwa tabar wiwi.
Kasantuwar
ba a samun tangarda daga gare ni ya sa a kullum nake ƙara samun shiga a wurin Jafaru. A ƙarshe ma sai ya sayo mini kayan wanki da
gyaran takalma har da kwando na ya ce ni ma in fara ƙoƙarin
tsayuwa da ƙafafuwana. Na ji daɗi
sosai sai dai daga zarar na fara tafiya mai yawa sai gajiya saboda ban saba ba.
Ga shi kuma irin wannan sana’ar ba irin wadda ake hawa abun hawa ba ce ba in
dai kana son samun abun kirki. Ranar farko da jan ido na dawo gida, kuma ina
shigowa na ɗauki kayan waccan ɗayar
sana’ar na bi duk inda na saba kai wa mutane na kai musu.
Tsawon
sati biyu amma na kasa sabawa da sana’ata, ga ciwon ƙafa da ya taso ni a gaba, ga kuma ciwon
kai wanda duk na san gajiya ce.
Na ɗauki
saƙon wasu na kai musu, kafin su sallame ni
sai na ji gudan yana faɗin,
“Na
jima ina neman hanyar da zan rage wa kaina gajiya na rasa ashe akwai sauƙaƙaƙƙiyar hanya ban sani ba.”
Wanda
na saba kai ma saƙon
ya ce
“Ai
tuni nake faɗa maka ka gwada tiramal (tramol) kai da
kanka za ka dawo harkar. Neman kuɗi za
ka yi da ƙarfinka ba tare da ka
gaji ba, sannan babu ɓacin rai babu ganda za ka
zama mai kuɗin kanka, idan ka je garinku ka ga yadda
kowa zai rinƙa russuna maka.”
‘Tiramal.’ Na
maimaita ma zuciyata. Sai kuwa na samu mafita. Ina barin wurin na kwance ledar
saƙon wani amma sai na ci karo da tabar
wiwi. Ba ita nake nema ba don haka sai na sake kwance wata ledar, a nan na ci
karo da kati huɗu na ƙwayar tiramal ɗin,
babu tunanin komai kawai na jefa ƙwaya
biyar a bakina na taune. Duk da wani irin mugun ɗaci
da gare shi amma a haka na daure sai da na taune sannan na bi da ruwa na kama hanyar
gida. Saƙon Jafaru na ba shi sannan na ɗauki
kwandon sana’ata na fice.
Tunda
na fita nake jin sauyin yanayi; komai nake jin yana kife mini, duniyar ma baki ɗaya
a baibai nake ganin ta, ga wani irin juyi da nake ji. Wuri na samu na zauna
inda babu kowa sannan na ɗauki sauran ƙwayar da ta rage a wancan katin na sha,
a tunanina shi zai kawar mini da wannan sauyin yanayin da nake ji. Cikin lokaci
kaɗan
barci ya yi awon gaba da ni. Tun wuraren la’asar ne na yi barcin amma sadda na
farka na fuskanci har gari ya sake wayewa, ga mamakina babu alamar ciwo ko gajiya a tattare da ni. Na ɗauki
kwandona na ƙara gaba ina jin
tabbas abin da ya dace da ni kenan in dai har ina son yin kuɗin
da na zo nema. Ba a hawa gini dole sai da matattakala.
Tun
daga wannan lokacin na dage da shan ƙwaya,
idan Jafaru ya aike ni sai in cire adadin da nake so in zuba kuɗinsa
in kai masa. A lokacin da ya gane abin da nake yi sosai ya nuna rashin jin daɗinsa,
ya rinƙa yi min faɗa saboda
tamkar ƙaninshi haka ya ɗauke
ni. Sai dai kuma aikin gama ya riga ya gama. A yadda nake ji na yanzu ba zan
iya komai ba idan ban sha ƙwayar
ba, ba ma tiramal ɗin kaɗai
ba har da wasu daga cikinsu wanda na ji ana kira da baliyan (vallium) duka sha
nake, kuma ba ƙaramin taimako suke
yi mini ba. Idan na sha ina samun kyakkyawar nutsuwa, sannan zan yi barci in
farka babu ko alamun gajiya, daga nan sai in shiga neman kuɗina
ka’in-da-na’in.
A
cikin shekaru biyu na yi kuɗin da nake muradi. Na sayi
babur da kuɗina na bayar ana yi mini haya saboda ni
ban iya ba kuɗin kawai ake kawo min. Sannan na sayi
nawa ɗakin
na zuba duk wani abu da ya dace duk da har yanzu ban rabu da Jafaru ba.
Na
tara kuɗi
sosai a Banki, don haka sai nake jin ya kamata na je gida yanzu ko don Innata.
Na yi kewar ta sosai kuma na san ba ƙaramin
tashin hankali ta shiga ba na rashi na. Shi kuwa Babana burina in gan shi, ba
wai don na yi kewar shi ba sai don kawai ina so ya ga irin ci gaban da na samu,
ya ga cewa ba dole sai ya tsayu a rayuwata ba ne zan yi kuɗi.
Na yi su, na yi kuɗi, na nema da ƙarfi da gumina.
Na iske Jafaru nake shaida masa ƙudurina, ya nuna jin daɗinsa sosai don da
ma ya jima yana so in je gida kamar yadda kowa yake yi amma ina turjewa ni fa
ba zan je ba har sai sadda na yi kuɗi.
A
hannun Jafaru na bar komai nawa, na zuba kayana sababbi a cikin jakar goyo
sannan na kama hanyar inda motocin garinmu suke tashi.
Kwanakinmu
biyu a mota muka isa ƙauyenmu.
Tunda muka shiga garin nake jin faɗuwar
gaba tare da taraddadin tinkarar mahaifana bayan tsawon shekaru biyu da na
shafe ba tare da sun san inda nake ba. A maimakon in fara zuwa gidan Babana sai
na ɗauki
hanyar gidan su innata, na zo mata da tarin tsaraba, ina son fara kai mata
doya, dankali da kuma ayabar da na zo mata da su.
Sadda
na je ba ƙaramin mamakin gani
na ta yi ba. Har shafa fuskata take yi tana al’ajabin ɗan
yaron nan nata mai shekaru goma sha huɗu ne
ya koma cikakken matashi mai jini a jika.
“Ka
tattara tsarabarka ka tafi da su Kabiru, ni ba zan karɓi
komai naka ba tunda duk tsayin lokacin nan kana can cikin kwanciyar hankali ba
tare da ka yi tunanin halin da nake ciki ba. Ka tafi kawai Kabiru ba na son
ganin ka.”
Hankalina
ya tashi, na gurfana a gabanta ina jin wasu irin hawaye masu zafi suna keto
min. Halittar da na fi so fiye da kowa a duniya ta kore ni daga wurinta, kuma
na sani tana da gaskiya, domin kuwa babu yaron kirkin da zai shafe tsawon
shekaru biyu ba tare da ya waiwayi gidansu ba.
“Ka
tashi ka tafi Kabiru!”
Ba
ni da wani zaɓin da ya wuce in tafin, sai dai na kasa ɗaga ƙafata domin barin gidan.
“Ki
yi haƙuri Innata ki yafe min. Zan tafi amma ki
bar kayan nan a wajenki. Zan ji daɗi
idan kika ci daga gumin gudan jininki. Wallahi ba da haram nake ci da sha ba.
Ba da haram na yi miki tsarabar nan ba. Aikin ƙarfi
nake yi, da gumina nake nema kuma da shi na sayo miki waɗannan.”
Daga
nan na juya na tafi ba tare da ko waiwayen kayan na yi ba.
Kai tsaye gidan Babana na wuce, ba tare da shakkun komai
ba na shige, don na san ko da Baba ya kore ni ina da makamin da zan kama shi da
shi, ina da kuɗi, ina da babban abin da yake so fiye da kowa da komai a
duniya. Idan
dai ƙashi na da tauri to kare bai da aikin
komai.
Ya
kore ni ɗin
da na je, sai dai ina zaro kuɗi na ajiye a gabanshi na ce
ban samu damar yi masa tsaraba ba amma ga wannan, sai na ga ya janyo ni a
jikinsa. Fuska cike da annuri yake shi mini albarka. Ba tare da ya tuhumi ina
na same su ba ko kuma ina na je duk tsayin shekarun nan ya ɗauke
kuɗin
ya soka aljihu. Daga nan sai na zama abun ƙauna
a gare shi, kamar dai yadda na yi tsammanin.
Satina
biyu a garinmu na fara shirin komawa Legas. Kusan kullum sai na je wurin Innata
amma tana kora ta, ta ƙi
saurare na ma balle na yi mata bayani. Idan ta gan ni tamkar wacce ta ga kashi.
Damuwar hakan ya sanya ni afa ‘yan Ƙwayoyina
wanda da zarar na sha nake jin komai ya wuce.
Ranar
da zan koma Legas ma sai da na je inda take na shaida mata zan tafi Legas. Ta ɗago
ta kalle ni da mamaki.
“Duk
tsayin lokacin nan Kabiru kana can da ma?”
Da
sauri na ɗaga mata kai.
Sai
kawai ta gyaɗa kai haɗe da
komawar ta ɗaki ta bar ni a nan. Na koma bakin ƙofar ɗakin
ina jaddada mata zan tafi.
“Allah
Ya tsare.”
Kawai
ta faɗa ba
ta ƙara da wani abu ba. Na sauke ajiyar
zuciya, na ji daɗin gajeriyar addu’ar nan
tata don haka da annurina na tafi. Mai tarko baya ɗaga
kara. Na fada a zuci.
Tunda
na koma Legas kusan kullum sai Baba ya kira ya maulaci kuɗi a
wurina, sai likafa ta buɗe masa, haka ya yi kyau, wai
an sayar da gonar raggo an sayo masa fura.
Ni
kuwa ba na jin komai nake yi masa aike, ko ba komai ya tabbatar wutsiyar raƙumi ta yi nisa da ƙasa.
Rayuwa ta ci gaba da tafiya shekaru na shuɗewa har na shekara
ashirin da takwas a duniya wanda har a wannan lokacin babu ruwan Innata da ni,
ko da na je ba ta ko kallon inda nake, amma hakan bai sanya ni fasa ziyartar ta
ba.
Shekaru goma sha uku ba nan ba ne, na ɗauki tsayin waɗannan shekarun ina
shan miyagun ƙwayoyi, wanda a gani na su ne ci
gaban rayuwata, idan babu tiramal tabbas babu ni! Sai
dai ban sani ba, ashe ciwo ci na yake ta ƙarƙashin ƙasa,
rayuwata gurɓata take yi ba tare da ni na ankare ba.
Kamar kullum ina zaune a ɗakina, Ghali ya zo
kawo min kuɗin wannan satin na sojan haya da yake yi da babur ɗina, ya tarar da ni
a ɓingire kasantuwar ciwon da ya buge ni, ina fitar da wani
irin kumfa daga bakina sannan idanuwana sun kafe ina wata irin jijjiga kamar
yadda masu farfaɗiya suke yi idan ta tasar musu. Hankalin Ghali ya tashi,
ya nemi Jafaru da duk waɗanda ya san ina hulɗa da su, amma kafin su zo har na
warware sai dai ciwon jiki da na gaɓoɓi.
Tun
daga wannan ranar kusan kullum sai wannan ciwon ya buge ni. Ya zamanto ba ni ma
iya fita neman kuɗin don kada ciwo ya same ni
a bakin hanya wani abun hawa ya kaɗe
ni. Ga wata irin muguwar rama da nake yi, babu wanda zai kalle ni bai tausaya
mini ba. Ban kuma fasa shan Ƙwayoyina
ba.
Na
fi shekara guda a cikin wannan halin, kuma ba yadda ba a yi da ni ba a kan in
koma gida a nema mini magani tunda dai a nan ɗin
muna ta zaryar asibiti amma an kasa gane ko wane irin ciwo ne yake damu na, ni
kuwa na ƙeƙashe
ido na ce babu inda zan tafi don kar in tafi jinya masu kula min da dukiyata su
rinƙa cutata.
A
lokacin da ciwon ya fara ci na ya cinye ne Idirisa ya sanar da iyayena. Duk da
fushin da Innata take yi da ni amma a haka ta daure suka kamo hanya ita da Baba
domin su tafi da ni.
Sai
dai suna zuwa ciwon ya tashi a gabansu, Baba ya ce babu inda zan tafi, hassada
ce daga mahassada, ya zo mini da tofi daga na sha asirin zai koma ga wanda ya
yi shi. Duk ba mu sani ba sharrin tiramal da sauran miyagun ƙwayoyin da nake sha ne.
Bayan
komawar su gida sai ciwon ya sake tashi. Babu shawara Inna ta zo ta koma gida
da ni. A ƙarshe duk wasu kuɗi
nawa suka ƙare wurin neman
magani. An sayar da babura da komai, har ɗakina,
an nemi magani sai dai babu nasara. Sai da muka ga wani likitan mahaukata ne ya
ba mu tabbacin miyagun ƙwayoyi
ne suka haddasa mini wannan ciwon, kuma ni da rabuwa da shi sai dai mutuwa.
Babana ya ga ishara, ya yi nadama mara amfani a lokacin
da ya tabbatar da shi ne silar komai, shi ya kashe mini rayuwa daga zaune, ya
shiga tsananin damuwa wanda daga ƙarshe har ciwon
zuciya ya kama shi, sai hawan jini, sai kuma mutuwar ɓaren jiki.
Jafaru
da yake ɗan
taimaka mini da aiken kuɗi shi ma na ji labarin NDLEA
sun kama shi.
A
yanzu haka fata nake mutuwa ta zo ta ɗauke
ni ko zan huta da wannan mummunar rayuwar. Kuma a haka neman Ƙwaya nake in sha, ko zan ɗan samu
sassauci a jiki da zuciyata. Ƙwaya ta bi jinina!
Ƙwaya ta nakasa mini rayuwa!
Ƙwaya ta zama silar gurɓacewar ƙuruciyata.
Ƙarshe.
Alhamdulillah.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.