Ticker

6/recent/ticker-posts

Labarina

Binta Rabiu Spikin (2020). Labarina. Muhalli, Sutura (Labaran Da Suka Samu Nasara a Gasar Gajerun Labarai a Kan Muhalli Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2020). Darma Digital Prints.

LABARINA

Na

Binta Rabiu Spikin

FARKON AL’AMARI

 20 GA WATAN AUGUSTA 2020- ƘARFE 10:30 NA SAFE

Farida ta fito daga gidanta tana taku a hankali cikin nutsuwa. A gefen gidan, motarta ce ƙirar Honda ‘yar ƙaramar mai ƙofa ɗaya. Cikin nutsuwa ta isa ga motar ta buɗe ta ɗan russuna ta gaida wasu magidanta da suke zaune a gefen motar. Kowannensu ya amsa gaisuwar cikin basarwa da ji-ji da kai. Tana lura da yadda hankalinsu duk yake kan Alhaji Baballe, wanda shi ma a lokacin yake fitowa daga tangamemen gidansa, yana kashingiɗe a bayan mota, ya yin da direba ke tuƙa shi. Dukkansu suka ruɗe da gaishe-gaishen “A dawo lafiya” da kuma “Allah ya kiyaye ka.” Ko kallon kirki ba su samu ba daga Alhajin, ya wuce abinsa cikin isa da ƙasaita. Farida ta yi murmushin takaici sannan ta shiga motar, ta tuƙa ta tafi.

Tana isa ofis ta ajiye motar a wajen adana motoci, ta gaisa da masu gadi da sauran mutanen da ke harabar. Tana isa ofis ɗinTA, sallama kawai ta yi don ta tarar abokiyar aikinta Maryam, ta riga ta zuwa. Ta jefar da jakarta a kan kujera sannan ta saki wani huci. Maryam da ke rubutu da na’ura mai kwakwalwa (computer) ta ɗago ido ta kalli Farida sannan ta ce, “Lafiya dai Farida? Yau kuma wane ne ya taɓo min ke?”

“Ke dai bari Maryama”. Farida ta amsa mata.Wai sai yaushe ne mace za ta yi daraja a cikin al’ummarmu? Yanzu don Allah don na mallaki gidan kai na shi kenan sai a yi ta nuna min halin ko-in-kula da ƙyaliya alhalin duk abin da ake so na kare mutunci, ina ƙoƙarin kwatantawa?

Maryam ta taso ta zo inda Farida ke tsaye ta ɗan dafa kafaɗarta ta ce, “Haba Farida! Sau nawa za mu yi maganar nan ne? Ta yaya za ki bari wasu mutanen unguwa suna ɓata maki rai kullum? Na sha faɗa miki fa, hassada ce kawai ba wani abu ba. Wai shin ma, me suka yi miki yau ɗin?”

Farida ta sauke numfashi sannan ta ce, “Yau ma kamar kullum, na fito zan taho wurin aiki, na same su suna zaman gefen hanyar da suka ɗora wa kansu duk safiya. Saboda zaman tare na ɗan russuna na gaishe su. Amma yan talikan nan ba ki ga irin kallon banzan da suka yi min ba. Kuma na san abin da kallon yake nufi… wato suna kira na da mace mai zaman kanta a fakaice, ba tare da sun furta ba…”

Maryam ta katse ta, “To mene ne a ciki Farida? Kowa fa da yadda Allah ya tsara masa rayuwa. Amma idan irin abubuwan da suke yi miki sun dame ki, ki koma gidan wani ɗan uwanku mana. Kin san mu Hausawa ba kasafai muke son mu ga mace na zaune a gida ba miji ba, sannan auren da kika yi niyyar yi bai yiwu ba.

Farida ta ja dogon numfashi ta ce, “Kina zaton akwai matar da take jin daɗin zama ita kaɗai ba a ƙarƙashin inuwar miji ba? Kin ga, je ki ƙarasa ayyukan da ke gabanki ni ma ki bar ni in yi aikina. Amma ba na nadamar mallakar gidan kai na. Hasali, hakan da na yi shi ne tushen farin ciki ne. Domin muhalli na daga cikin ni’imomin rayuwar duniya.”

Maryam ta yi tagumi sannan ta tambayi Farida, “Shin Farida ta yaya kina ma’aikaciya, a yanayin da muke ciki, kafin albashi ma ya zo har mun kashe shi, amma ke har kika mallaki gidan kanki, a unguwa mai kyau da tsari, kuma na ga ba wata sana’a kike yi ba bayan wannan aikin naki?”

Farida ta yi murmushi sannan ta ce,Ana yawan yi min wannan tambayar. Amsata kullum ita ce Allah ya saka wa bankin bayar da lamuni na ƙasa wato Federal Mortgage Bank da alheri. Lokacin ina aiki da ma’aikatar ilimi suka zo suka kawo mana tsari wanda za ya ba mu damar mallakar gidajenmu na ƙashin kanmu. Da kamar in ƙi shiga to kuma sai Allah ya taimake ni na shiga ɗin. Yanzu kam na fi kowa murna da tsarin”.

Maryam ta sauke numfashi sannan ta tambayi Farida, “Wannan wane irin tsari ne?” Farida ta numfasa sannan ta shiga kogon tunani…

GAM-DA-KATAR

4 GA WATAN DISAMBA, 1992 (Shekaru 28 baya) ƘARFE 11:00 NA SAFE

Farida da sauran abokan aikinta sun fito daga wani muhimmin taro da aka yi a ɗakin taro na ma’aikatar ilmin jiha, kowannensu da takardunsa a hannu. Malam Sammani wanda suke ma’aikata ɗaya da Farida da kuma Malama Ruƙayya, wadda ta zo daga gamammiyar ƙungiyar malamai suna tattaunawa a kan wannan bita da bankin bayar da lamuni ya shirya wa ma’aikatan ma’aikatar ilimi domin wayar musu da kai don su samu cin moriyar shirin bankin na sama wa ma’aikata muhalli. Bisa dukkan alamu, bitar ta ƙayatar da mahalartan matuƙa. Farida ta tambayi Malam Sammani, “Malam Sammani, ni fa sai ka yi min ƙarin bayani.

Malam Sammani ya yi murmushi sannan ya kalli malama Ruƙayya, kafin daga bisani ya maida kallonsa ga Farida sannan ya ce, “Malama Ruƙayya, kin ga mutuniyar ko, za ta yi mana halin nata na ruɗewa, tsakani da Allah mene ne abin rashin fahimta a nan?”

Ruƙayya ta yi dariya ta ce,Ni ma dai yau ina tare da Farida Malam. Don Allah muna son ƙarin bayani”.

Malam Sammani ya ce, To ku saurare ni ku ji. Shi dai wannan banki na bayar da lamuni a ƙasar nan yake, kuma yana da ressa a kowace jaha. Abin da ake buƙata daga kowane mutum ma’aikaci ko mai sana’a shi ne ya zama yana ajiye kaso biyu da rabi cikin ɗari (2.5%) kacal na abin da yake samu na albashinsa a asusun bankin, wato kamar dai adashin gata, domin a wannan tsarin mutum zai iya mallakar muhalli. Bari in maku misali gwari-gwari. Wanda yake samun naira dubu biyu a wata abin da ake buƙata ya saka a asusun kowane wata bai wuce naira tamanin ba. In har mutum ya yi wata shida yana ajiye wannan kuɗin, to zai iya cin moriyar shirin ya mallaki muhalli”

Farida da Ruƙayya suka tafa, sannan Farida ta ce, “To in don wannan ne mun yarda. Waɗannan takardun da suka cika mana hannu da su fa?”

Sammani ya ba ta amsa, “Waɗannan takardun fom ne. Da su za a yi muku rijista. Kowannenmu za ya je ya cike shi wato ya faɗi dukkan abin da suka buƙaci ya faɗa a kan fam ɗin, sannan a mayar da su bankin. Ma’aikatan bankin za su ba wa kowannenmu lamba, alamar mutum ya yi rijista kenan.”

Ruƙayya ta ce, “Ai ni na fahimci wannan daga laccar da aka yi mana. Amma ban gane batun fam na biyu da suka ce za su ba mu ba. A nan dai ba su haɗo mana da shi ba”.

Sammani ya yi dariya sannan ya ce, “Ku matsalata da ku ita ce, idan ana jawabi ba kwa mayar da hankali, koma wa gefe kuke yi kuna tauna cingam kuna ƙus-ƙus. Sai an gama ku dame ni da tambayoyin da tuni an amsa su a wajen taron.”

Ruƙayya da Farida suka sake fashewa da dariya suka tafa, sannan cikin dariyar dai Farida take magana, “malam Sammani namu, ai ba a raba mata da ƙus-ƙus. Kuma mun san ko ba mu gane ba za ka yi mana ƙarin bayani”.

Ruƙayya ta ƙara masa bayani, “Kuma Farida ta fi gane naka bayanin, ka dai san halin mutuniyar taka.”

Sammani ya amsa masu, “Ba wani wayo da za ku yi min fa! Zan dai yi muku ƙarin bayani, don na saba. Amma na ga yadda za ku yi, ranar da aka tura ku bita ba tare da ni ba. Shi wannan da aka ba mu yanzu sunan sa Form NHF 1, shi ne na ɗaya. Sai an cike shi an mayar bankin sannan a ba da wanda kike tambaya wato form NHF 2, shi kuma don amfanin ma’aikatarmu ne, tun da ma’aikata ce za ta yi mana shaidar cewa muna yi mata aiki. Wanda za a bai wa damar ya cike duka takardun guda biyu shi kaɗai, shi ne wanda yake ba ma’aikacin gwamnati ba, wato kamar ɗan kasuwa ko mai yin wata sana’a tasa ta ƙashin kansa, kuma yana son shiga tsarin. Da wannan takarda ta biyu wato Form NHF 2 Bankin Bayar da Lamuni yake amfani ya ba wa kowane mutum lamba. Ita wannan lamba ta kowa daban ce”.

Farida ta sake tambaya, “Lamba kaɗai za su ba mu?”

“Bayan lamba, za su ba ki wani ɗan littafi wanda da shi ne ma’aikatarki za ta dinga rubuta adadin kuɗin da aka cire a albashinki duk wata aka saka miki a asusun banki”. Sammani ya amsa mata. “Idan ba ku manta ba, na faɗa muku kashi biyu da rabi ne, cikin ɗari wato 2.5%. shi kenan kin shiga tsarin. Daga wannan lokaci kuma ba sauran wani ka-ce-na-ce, duk wata za a cire kaso biyu da rabi cikin ɗari na albashinki a saka a asusun bankin. Da ma’aikatarki da su bankin da ke kanki, za ku san nawa ne jumlar da aka cire miki, a wata nawa tun da kina da wannan littafin da na yi muku bayani”

Ruƙayya ta ce, “Shi ma wanda ba ma’aikaci ba, dole ne sai ya saka kuɗi duk wata?’

Sammani ya amsa,sosai kuwa. Kuma na san abin da ya sa kika yi wannan tambayar. Wato ko da kin yi aure, kuma kishiyarki ba ta aiki, sai ki saka ta a tsarin, don ba kya son ki yi ke kaɗai ko?”

Farida ta yi dariya “oh! Ni jikar mutum biyu! Ni nan da kake gani na, ni ce gugan ƙarfe sha kwaramiya. Ko mata nawa za ka kawo bayan ka aure ni, ba abin da zai ɗaga min hankali. Me jiya ta yi, balle yau?”

Ruƙayya ta kalle su kawai tana dariya, ta ce, “Gaskiya a harkar nan Farida ke kaɗai kika yi gam-da-katar. Ga samun lamunin gida, ga malam Sammaninki yana biye da ke kamar ya haɗiye ki don ƙauna. Allah ya kai mu ranar daurin aure mu sha shagali”.

Sammani ya ce, “Ai don ta daɗe tana sanyin jiki ne. Ai da tuni ba wannan maganar ake yi ba”.

Farida ta yi dariya sannan ta ba su amsa, “Gaskiya Ruƙayya kin yanke ni. Ai malam Sammani ne ya yi gam-da-katar ɗin, don sai an yi kwana biyu ana bitar nan, kuma ko ba komai kullum zai ga kwalliyata da kyakkyawar fuskar nan tawa, ga ƙamshin turare mai sanyaya rai. Ina laifi….

Duk suka buɗe baki suna kallonta, ita kuwa ta yi gaba abin ta, ya yin da Malam Sammani ya bi ta da kallo. Ya numfasa, sannan ya ce, “Farida gaskiya ta faɗa. Har ba na son kwanakin nan biyu su ƙare. Ya Allah ka mallaka min wannan baiwa taka, ka sa ta zama matar aurena”.

*******

20 GA WATAN AUGUSTA 2020 4:30 NA YAMMA

IYALI NA GARI, TUSHEN FARIN CIKI

Da yamma, bayan Farida ta gama girki, sai ta yi sallar la’asar. Ta daɗe a zaune tana karatun Ƙur’ani da addu’o’i, daga bisani ta tashi ta koma kan kujera, ta kunna talbijin tana kallon shirin girke-girke. Haƙiƙa gidanta yana da matuƙar tsari. Gida ne a cikin jerin gidajen da bankin lamuni ya gina wa ma’aikata. Yana da ɗakuna uku, kowane da banɗakinsa, da kuma falo wadatacce. A cikin falon akwai wurin dafa abinci (Kitchen) na zamani, da kuma ɗakin ajiye-ajiye (Store) daga waje akwai madaidaicin fili, wanda ya isa Farida ta ajiye motarta, haka nan a baya ma akwai ɗan ƙaramin fili, inda take kiwon kifi. Abin sha’awa, unguwar tasu akwai ruwa da kuma wuta, sannan ga layin a tsare da kwalbati wadda ta bi gefe da gefe har bakin babban titi. Haƙiƙa dukkan mazauna unguwar sun more da unguwa.

Aliyu da Usman matasa ‘yan shekara sha huɗu da sha uku, suka yi sallama suka shigo sanye da kayan makarantar Islamiyya a jikinsu, ƙannensu mata su uku suka shigo a bayansu. Kowannensu ya gaishe da Farida sannan suka je suka tuɓe kayan makaranta, suka zubo abinci suka fara ci, haɗe da hira. Bayan sun gama cin abincin Maryam ta ɗebe kwanukan ta tafi ta wanke su ta adana a ma’ajiyarsu, sannan ta dawo falon ta zauna. A haka har aka kira sallar magriba. Gaba ɗaya suka tashi don yin sallah, sannan suka ɗora da tilawar Alƙurani har aka kira sallar isha. Sai bayan sun idar da sallar isha sannan suka dawo falon suka ci gaba da hira. Cikin hikima da nuna kulawa Farida ke tambayar ‘ya’yanta game da karatunsu kuma tana gamsuwa da irin amsoshin da ta samu daga kowannensu. Sai da dare ya ɗan fara nisa sannan suka tafi suka kwanta. Aliyu ne ya faɗa wa Farida kalmar da ta tsunduma ta a kogin tunani. Domin da ya tashi tafiya ɗakinsu don ya kwanta, sai ya zo kusa da Farida ya durƙusa, sannan ya ce, “Mama mun gode bisa kulawarki gare mu. Allah ya ba mu tsawon rai, ya sa za mu yi ɗawainiyar da za ta hutar da ke a lokacin tsufanki”. Farida ta nisa kawai tana murmushi, ta ce, “Aliyu kenan! To amin. Amma ni yanzu wa nake da shi wanda ya fi ku? Allah dai ya ba mu tsawon rai mai amfani. Allah ya yi muku albarka. Ka je ka kwanta ko? Don kada ka makara sallar asuba”.

Cikin fara’a Aliyu ya tashi ya nufi ɗakinsu. Ita ma Farida ta miƙe, ta kashe fitilu, ta bi dukkan ƙofofi ta kulle, tare da yin addu’a. Sannan ta shiga ɗakinta. Maryam ta yi shimfiɗa a ƙasa. Ita kuma Farida ta je banɗaki ta wanke fuskar ta, ta ɗauro alwala, ta ɗan tsaya a jikin madubi ta goggoge fuska sannan ta saka rigar bacci, ta yi addu’a ta shafa, ta kashe fitila ta bi lafiyar gado ta kwanta. Sai dai kuma a yau bacci ya ƙaurace wa idanunta. Sai juye-juye take yi tana tunanin rayuwarta.

6 GA WATAN YULI, 1980 ZUWA YAU

MUHALLINKA GARKUWARKA

Farida ‘ya ɗaya ce tilo a wurin mahaifiyarta Halima wadda ake yi wa laƙabi da Gwaggo Dubu, mace mai fara’a da son mutane. Kafin rasuwarta, ba irin gatan da Farida ba ta gani ba na iyaye da kakanni. Kuma da yake mahaifinta yana da hali, ba ta rasa komai ba tun tasowarta har lokacin aure. Mahaifiyarta ta rasu tana da shekara takwas, shi ne riƙonta ya koma hannun Gwaggo Maimuna, wadda ita ce kishiyar mahaifiyarta. Bayan rasuwar Gwaggo Dubu, Alhaji Iro, mahaifin su Farida, bai sake auren wata matar ba. ‘Ya’yan gwaggo Maimuna su shida ne, mata biyu maza huɗu. Daidai gwargwado tana bai wa Farida kulawa, amma da yake Farida ce ‘yar fari a wurin mahaifinta, sai ya kasance yana matuƙar sonta. Wannan soyayya da yake nuna mata ita ce sanadiyyar kishin da gwaggo Maimuna take yi da ita, duk da tana matuƙar ƙoƙarin boyewa amma sai da Farida ta fahimta. Wata ƙila shi ne dalilin da ya sa Faridan tana gama makarantar sakandare, da shekaru goma sha takwas gwaggo ta azalzala sai dai a yi mata aure.

An aurar da ita ga ɗan ƙanin Babanta wanda suke kira Yaya Mansur kuma cikin ƙanƙanin lokaci suka haifi ‘ya’ya har biyar, domin Farida ba ta yaye, sai da wani cikin. Sai dai fa auren ana yin sa ne kawai, domin Farida da mijinta Mansur, kullum a cikin tashin hankali suke tamkar suna ganin hanjin juna.

Wannan ya samo asali saboda tarbiyyarsu ta bambanta, duk da kasancewar su ‘yan uwan juna. Shi ma Mansur ɗan fari ne kamar Farida, amma shi an sangarta shi fiye da ƙima. Ko kaɗan iyayensa ba sa ganin laifinsa. To kuma da yake ana son Farida ta yi zaman auren, kuma Babanta ne babba, daɗin daɗawa kuma Gwaggo Maimuna ba ta son auren ta koma zaman gida, ba a taɓa ba wa Farida dama ta bayyana laifin mijinta ko a ji ta bakinta ba. Kullum wani abu ya faru Mansur ne da gaskiya. A haka suka haifi yaran nan biyar. Saboda sangarta kuma Yaya Mansur sam bai san wahalar ‘ya’yansa ba.

Farida na sana’ar ɗinki, Allah ya sa mata albarka a ciki, don haka Mansur ya sakar mata dukkan ɗawainiyar gida. Iyakaci ya kawo abinci, amma su kuɗin cefane ko sabulun wanka da wanki, kuɗin makarantar yara, harkar lafiya, kai komai yana wuyan Farida. Kuma duk an san irin wannan mugun zama da suke yi, ba wanda ya taɓa ƙoƙarin kiran Mansur don a yi masa faɗa. Sai dai mahaifin Farida yana ƙoƙarin kyautata mata, kuma yana taimakonta da kuɗi da kayan masarufi, wasu lokutan ma har da suttura.

A haka suka haifi ‘ya’yan biyar. Sai dai cikin rashin sa’a, a kan ɗan ƙaramin saɓani Mansur ya saki Farida, sakin wulaƙanci, domin saki uku ya danƙara mata a lokaci guda. Abu mafi muni da ya faru a sha’anin sakin shi ne korar da Mansur ya yi wa Farida daga ita har ‘ya’yanta daga gidansa. Babban ɗanta a lokacin shekararsa takwas, ragowar kuma haka suke tafi-in-bi-ka, har da mai shekara guda. Cikin ɓacin rai Farida ta kwashi tawagar ‘ya’ya ta tafi gidansu, ashe wasa farin girki, domin Gwaggo Maimuna cewa ta yi ba ta san zancen ba, ba za ta zauna da Farida da gayyar wannan ‘ya’ya ba. Sai dai a san na yi.

Duk da irin son da mahaifin Farida yake yi mata, a ɗaya ɓangaren yana shakkar matarsa da ‘ya’yanta. Haka mahaifin Farida da ita kanta Faridan suka yi ta jele, tsakanin dangi, don dai a san yadda za a yi da Farida da ‘ya’yanta. Yinin ranar nan sur, ba wanda ya ci wani abincin arziki a cikinsa, ana ta yawan mayar da yadda aka yi. Sai daga baya, da ƙyar aka samu aka rarrashi gwaggo Maimuna ta bar Farida da ‘ya’yanta su zauna a gidanta. Alhaji Talle, mahaifin Mansur, ya ji ɓacin rai sosai na faruwar wannan lamari, har ma ya so a bar Faridan ta zauna a gidansa tare da ‘ya’yanta, amma Alhaji Iro mahaifin Farida ya ƙi, domin matarsa Zulai, mahaifiyar Mansur na ɗaya daga cikin masu iza wutar rikici tsakanin ma’auratan. Daga ƙarshe dai haka aka haƙura, Farida ta tare a gidansu. Shi kuwa isasshen, wato Mansur, ai barin garin ma ya yi abinsa, yana ganin ya saki Farida, ya rabu da matsala. A wannan zama da Farida ta yi a gidansu, ta koyi darussa da dama, babban cikin darussan kuwa, shi ne muhimmancin mallakar muhalli, domin shi muhalli garkuwa ne ga ɗan Adam.

Daga farko, kamar lamarin zai yi kyau, domin Farida tana taka tsantsan. Duk abin da ta san zai ɓata wa Gwaggo Maimuna rai, ba ta yin sa. Kacokam ta karɓe aikin gidan duk da ga ‘ya’yan ita gwaggon, ‘yanmata, amma saboda gata su ba sa yin komai sai dai su ci su kwanta. Sai fa idan lokacin makaranta ya yi, su tafi domin dukkansu suna zuwa jami’a ne.

Saboda a ɗauke mata hankali daga duk wata damuwa, sai mahaifin Farida ya saka ta a wata Islamiyya ɓangaren matan aure, kafin lokacin sake ɗaukar ɗalibai a jami’a. Wannan karatu shi ne matsalar da Farida ta fara samu ta farko, domin karatun bai kwanta a ran Gwaggo Maimuna ba. Duk da kasancewar kullum kafin Farida ta fita sai ta tashi da wuri, ta yi shara, ta yi wanke-wanke, kana ta shirya ‘ya’yan ta su tafi makaranta. Waɗanda ba su isa zuwa makaranta ba su biyu ne take barin su a gidan. Amma waɗannan yara tamkar an bar wa Gwaggo rainon makaranta guda cike da yara. Kullum Farida ta fita ta dawo, sai an ce mata ga abin da ‘ya’yan ta suka yi. Sannu-sannu abin ya faskara, tilas Farida take tura yaranta maƙwabta, gidan wani yayanta, ɗan ƙanin Babanta, kuma ƙanin mijin da suka rabu, Mansur, don a samu zaman lafiya.

Wannan abu yana matuƙar damun Farida kuma tun daga wannan lokaci take ta addu’ar Allah ya mallaka mata muhallinta na kanta, domin dai shi ne garkuwarta da yaranta. Sai dai kuma ta ina za ta fara? Ɗinki dai, da yake shi ne sana’ar da ta iya ya gagara yiwuwa a gidansu. Don ɗakin da suke ma ba wadatar wurin da har za ta kafa keken ɗinki. Sai dai duk da haka, tana karɓar ɗinkin ƙananan yara, da su gyaran tsummokara, da ɗinkin manyan ma idan ya samu, sai ta shiga gidan Yaya Sabuwa (inda take kai ajiyar yarantakenan) ta yi, idan ta samu lokaci. Da ɗan abin da take samu take kun ji-kun jin yara, sai ɗan abin da Babanta ya ba ta.

Da yake Allah ma ji roƙon bawa ne, a makarantar da take zuwa akwai ɓangaren boko, wato ɓangaren yara kenan. A zuwan da take yi yau da gobe suka saba da wani malami na ɓangaren yara, sannu a hankali ya fahimci natsuwa irin ta Farida da kaifin ƙwaƙwalwa, don haka lokacin da aka tashi ɗaukar malamai na sa-kai, sai ya yi mata tayi. Bayan ta yi shawara da mahaifinta, ta samu amincewarsa, kawai sai ta fara aikin koyarwa. Duk da abin da ake ba ta a matsayin malamar sa-kai ba mai yawa ba ne, amma dai tana jin ɗaɗin aikin ƙwarai da gaske, sannan ta yi banki tana tara ɗan abin da ya sauwaƙa. Daga baya ma ta shiga adashin malaman makarantar.

A haka ta rarrafa ta ɗan tara kuɗi ta sayi fam (takardar neman gurbin shiga makaranta) kuma cikin taimakon Allah ta samu dacewa aka ɗauke ta a matsayin ɗaliba a Kwalejin Horar da Malamai.

Mansur kuwa, tsohon mijinta, sai da ta kwashe wata huɗu a gida, sannan ma ya dawo gari. A lokacin maganar sakin ta ɗan yi sanyi. Duk da haka, ya sha faɗa daga mutane da dama a cikin dangi.

Da yake bai san ciwon kansa ba ko a jikinsa, a haka har maganar ta wuce. Kuma don rashin kunya, haka zai ɗebi su biskit da alawa ya tafi gidan su Farida wai ya zo ganin ‘ya’yansa. Mahaifin Farida Alhaji Iro bai taɓa hana Mansur zuwa wurin ‘ya’yansa ba, shi ne dai kunyar kansa ta sa sai ya daidaici lokacin da ba ya gida sannan ya je. Haka aka ci gaba da rayuwa. Sai da ya ga Farida ta soma samun sauyin rayuwa, wato ba ta tagayyara ba, domin dai ga karatu tana yi, ga sana’a tana ɗan taɓawa, kuma ba ta saki aikinta na koyarwa ba, kurum yarjejeniya aka yi aka tsara mata lokutanta na shiga aji, don kada su ci karo da lokacin zuwanta makaranta. Kuma ƙarin abin burgewa shi ne, daga inda take aiki zuwa kwalejin da take karatu ba nisa sosai, ko da ƙafa ana iya zuwa.

Haka nan tsakanin gidansu da makarantar da take koyarwa ba nisa sosai. Sai a lokacin ne Mansur ya so ya tayar da balli marar tushe, wai shi dole sai Farida ta koma gidansa, wai shi saki ɗaya ya yi mata. A wannan karon ne kaɗai Alhaji Iro mahaifin Farida ya fito ƙiri-ƙiri ya goyi bayan ‘yarsa domin cewa ya yi, “Ko saki ɗayan ka yi mata, ai ta gama idda, kuma ba za ta koma gidanka ba sai dai idan ba na numfashi”. Mahaifinsa kuwa Alhaji Talle cewa ya yi “Ko saki ɗayan ka yi mata, tun da har ka furta mana cewar saki uku ka yi mata, to saki ukun ne. Kada ka sake zuwa min nan da irin wannan shiriritar”.

A haka dai ya gaji da binbininsa ya ƙyale ta. A haka ta ci gaba da gudanar da rayuwarta cikin nasara. A makarantar da take ta haɗu da Sammani, wanda shi ne mutumin da ya taimake ta har ta kai ga mallakar gidanta na kanta, da taimakon Bankin Bayar da Lamuni na Nijeriya.

Sammani matashi ne wanda yake da matsakaitan shekaru. Matarsa ɗaya da ‘ya’ya uku, malamin makaranta ne, kuma ya zo kwalejin ne domin ƙaro ilimi, sai dai shi karatun digiri zai yi, ba kamar Farida ba da take neman takardar shaidar zama malamar makaranta. A hankali soyayya mai ƙarfi ta ƙullu a tsakaninsu, kuma suna da niyyar aure. Abin da ya yi musu cikas kurum rashin kuɗi, tun da ba wani albashin a zo a gani ne da shi ba.

Sai dai suna ta shiri tare da tsimi da tanadi don ganin cikar wannan buri nasu. Kusan kullum suna tare. Ban da soyayya har da aminci a tsakaninsu, don haka duk irin ɗawainiyar da ke wuyan Farida Sammani ya sani, ya san matsalolinta, musamman na tsohon mijinta, da matar Babanta da kuma ‘yan uwanta waɗanda suke uba ɗaya. Bakin gwargwado Sammani na taimakonta da shawarwari da kuma abin da ya sauwaƙa, duk da ba wani mawadaci ba ne. A haka ta kammala karatunta. Sammani kuma ya taimaka mata ta samu koyarwa a makarantar gwamnati maimakon aikin da take yi na sa-kai. A haka ta yi ta samun ci gaba, da ƙarin girma har Allah ya taimake ta, bayan an yi zaɓe, sabon shugaban ƙaramar Hukumar su ya kasance abokin Sammani, kuma ta dalilinsa da ita da Sammanin suka samu aiki a ma’aikatar ilimi.

A ma’aikatar ilimin ne suka samu damar zuwa taron bita da Bankin Bayar da Lamuni suka bayar don su taimaki ma’aikata su samu sauƙi wajen mallakar muhallinsu. Tun daga lokacin Sammani da Farida suka tabbatar matsalarsu ta zo ƙarshe. Sun shirya cewar Farida za ta shiga tsarinsu, su samu ta mallaki gida, sai ta tare da ‘ya’yanta. Shi kenan ta huta da zama da kishiya, sun kuma huta da maganganun jama’a, domin a tsawon shekara shida da suka yi tare, ba irin surutun da ba a yi musu ba. Inda Allah ya taimaki Farida shi ne, shi dai Sammani ba ya zuwa gidansu zance, iyakacinsu waya, sai dai ko su haɗu a makaranta ko wurin aiki. Sannan kullum Babanta ya yi mata maganar aure sai ta rushe da kuka, ta ce ita ba ta samu miji ba.

Da yake ba magana take ɗauko masa ba, shi ya sa bai takura ba. Wannan burin nasu da shi take kwana take tashi. Komai na Farida yana tafiya cikin nasara da sa’a. Kwatsam! Sai mahaifinta ya rasu ba tare da ya yi wata doguwar jiyya ba. Wannan mutuwa ta gigita rayuwar Farida har sai da ta kwanta ciwo. Da taimakon Allah da yawan adduo’i ta samu kanta. Sai dai wani sabon shafin ya buɗe mata na rashin tabbas. Ba abin da yake ɗaga mata hankali illa rashin muhalli. Duk da ta shiga tsarin Bankin Bayar da Lamuni na mallakar muhalli, akwai sharaɗi, sai mutum ya yi wata shida yana ajiya a asusun kafin ya iya mallakar muhalli. Ita kuwa watana huɗu kenan da ta fara ajiya a asusun. Haka Farida ta ci gaba da addu’a a kan mallakar muhalli.

Tashin hankali, wanda ba a sa maka rana, domin kwanan mahaifinsu arba’in da mutuwa, Gwaggo Maimuna da ‘ya’yanta suka faro maganar rabon gado. Inda Gwaggo Maimuna ta ce ai bai hallata ba mutum ya mutu a bar shi da nauyi a ka. Ƙarara suka nuna suna son a sayar da gidan domin Farida da ‘ya’yanta su fita daga gidan. Aka juya ƙaura-wambai amma matar nan ta ƙeƙasa ƙasa ta ce dole a yi rabon gado. A wannan karon ma Sammani ne ya kawo wa Farida ɗauki, domin shi ya yi ta shige da fice har Allah ya taimaki Farida ta mallaki muhallinta na kanta, da taimakon Bankin Bayar da Lamuni.

 Duk shige da ficen da take tsakanin wurin aikinta da bankin Gwaggo Maimuna da ‘ya’yanta ba su san abin da ake ciki ba. Sai da aka kammmala sannan ta faɗa wa Gwaggo Maimuna cewar ta sayi gida za ta tashi sati mai zuwa. Nan kuma Gwaggon ta hau borin kunya. Daga baya kuma ta yi ta yawo da zancen, tana cewa Farida ta zaɓi ta yi zaman kanta. Aka yi ta tsegumi da ƙananun maganganu, Farida ta toshe kunnenta. Sannan Sammani ya sake ba ta goyon baya domin a wannan lokacin ya zo wurin dangin mahaifinta ya gabatar da kansa a matsayin mijin da yake son auren ta. Aka yi murna sosai. Nan da nan aka shiga shirye-shirye.

An shirya cewar Farida za ta tare a gidanta ranar laraba, sai a ɗaura musu aure ranar Juma’a. Ta ga gata sosai daga wurin dangin mahaifinta da ma mahaifiyarta, duk da su ba a nan suke ba, suna wani gari, amma wasunsu sun zo, haka nan sun kawo gudummawa.

Ta tare a gidanta cikin farin ciki. Gidan madaidaici ne mai ɗakuna uku da falo, ga wadatar tsakar gida, inda zai iya kasancewa wurin ajiye mota. Ita da yaranta da kuma dangin mahaifiyarta da suka zo suna gyaran gida da gyaran jikin amarya, domin jibi ne ɗaurin aure. Washegari alhamis aka tashi da mummunan labarin rasuwar Sammani, wanda ciwon ciki ya turnuƙe shi cikin dare. Kafin a kai shi asibiti ya cika.

Wannan shi ne labarin Farida. Shi ya sa ta kasa aure, domin ta tsorata da abubuwan da suka faru da ita. Amma tana addu’a Allah ya kawo mata miji nagari. Abubuwa da dama sun faru bayan rasuwar Sammani. Daga cikinsu akwai ƙarin girma da ta samu a wurin aiki, da motar da ta saya, da kuma sabon bazawarin da ta samu, wanda take fatan ya zamar mata mijin aure.

Alhamdulillah!!!

Muhalli, Sutura

Post a Comment

0 Comments