Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Tsarin Rubuta Gajeren Sako da Hausa a Kafafen Sadarwa na Zamani

Citation: Kulumbu, M. S. U (2025). “Nazarin Tsarin Rubuta Gajeren Saƙo da Hausa a Kafafen Sadarwa na Zamani.” In Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 03, No. 02, Pp. 13 – 19. www.doi.org/10.36349/djhs.2025.v03i02.002.

NAZARIN TSARIN RUBUTA GAJEREN SAƘO DA HAUSA A KAFAFEN SADARWA NA ZAMANI

Na

Muhammad Sani Umar Kulumbu

School of Languages, A. D. R ufa’i College of Education, Legal and General Studies, Misau, Bauchi State

Tsakure:

Wannan takardar ta yi nazari ne akan tsarin rubutun Hausa da ake yi a kafafen sadarwa na zamani da suka samar da sabon salon rubutun Hausa da ake rubuta kalmomi a taƙaice ta hanyar gajarta rubutun saƙo a kafafen sadarwa na zamani da aka yi nazarinsu a wannan aikin. Manufar nazarin shi ne na ya ilimantar da maabota waɗannan kafafe yadda ya kamata a bi ƙaidojin rubutun Hausa da amfani da harufan da Hausa take da su domin gyara rubutun da ake yi a irin waɗannan kafafe na sadarwar zamani. An nazarci wasu saƙonni da aka rubuta da Hausa a shafukan fezbuk (Facebook) da wasAf (WhatsApp) wanda sakamakon nazarin ya nuna yadda ake amfani da wani irin salon rubutun Ingilishi wanda ya saɓa ƙaidojin rubutun Hausa da take da su. An yi amfani da rain Alamomin Rayuwar Alumma na mazhabar Saussure (1978) wanda ya jagoranci nazarin da aka yi. Daga ƙarshe an kawo shawarwarin yadda za a yi rubutun Hausa ta amfani da harufan Hausa masu ƙugiya da masu goyo waɗanda Hausa take da su a tsarin rubutunta.

Muhimman kalmomi: amfani, tsari, kafafe, shafuka da salo

Gabatarwa

Kafafen sada zumunta na zamani waɗanda ake rubuta gajeren saƙo a shafukan fezbuk  (Facebook) da was’Af (WhatsApp) a Hausa sun kawo wani irin sauyi da kuma ƙalubale na saɓa ƙa’idojin rubutun Hausa da aka san da su bisa al’ada a rubutun yau da kullum. Nazari ya gano cewa rin wannan ƙalubale na saɓa ƙa’idar rubutu ya samu ne saboda masu amfani da waɗannan kafafe wajen aika rubutaccen saƙo da yawansu ba Hausawa ba ne ko kuma da wasunsu ba masu ilimin harshen Hausa ba ne watau ba su da ilmi ko sanin ƙa’idojin rubutun Hausa. Wasu kuma suna rubutu na isa ko ganin dama da nuna gwaninta. Wannan nazari ne da ya duba irin sabon salon rubutun Hausa da kuma matsalolin da ake fuskanta a waɗannan shafukan da ake bi a aika da rubutun Hausa. Nazarin zai iya taimakawa ma’abota kafafen sadarwa na zamani wajen amfani da sabuwar hanyar rubutun da kuma bin tsarin ƙa’idojin rubutun Hausa da yadda ya kamata a yi amfani da harufan Hausa a rubutun saƙonnin da Hausa.

Saussure (1978:23) ya bayyana cewa dole rubutu ya kasance; za a iya karantawa kuma ya bayar da fassarar tubalan da aka gina shi rubutun a kai da suka danganta da sauti da ma’ana da zanen alamau a harshen rubutu. Ana amfani da rubutun Hausa a bisa doron nazarin al’ada da adabi da harshe a kan shimfiɗaɗɗen tsari da ƙa’idojin da aka aminta da su. Wannan bincike ya karfafa yin amfani da tsarin da aka ɗora Hausa a kai wajen daidaita sahun bin ƙa’idojin daidaitacciyar hanyar rubuta Hausa a kowane irin farfajiya domin isar da rubutaccen saƙo. Rashin bin ire-iren waɗannan ƙa’idoji ne yake kawo daƙusher harshe. Ɗaya daga cikin dalilan durƙushewar harshe kuwa shi ne na rashin daidaituwar tsarin ƙa’idojin rubutu da masu amfani da harshen za su yi a rubuce-rubucen adabi da al’adunsu domin bayyanar da kansu ga duniya.

Dalili da Manufar Bincike

Dalilin gudanar da wannan aikin shi ne nazartar tsarin rubutun gejerun saƙonni da ake rubutawa da Hausa kamar yadda ake yi a wasu harsuna misali Ingilishi a kafafen sadarwa da Hausa take cin gajiyarsu a yanzu. Nazarin ya kalli yadda aka aro tsarin rubutun Ingilishi wanda ake amfani da shi a Hausa wajen aikawa da rubutaccen saƙo a waɗannan kafafen sadarwa na zamani da aka duba a wannan takarda. Manufar takardar ita ce na fito da yadda ya kamata Hausa ta ci moriyar sabon salon rubuta gajeren saƙo da kalmomin Hausa da ake da su a harshen. Takardar ta ƙarfafa yadda za a samar wa tsarin muhalli a rubutun Hausa da aka runguma a yau. Hakan zai bunƙasa hanyar rubutun Hausa da harshen Hausa da masu amfani da Hausa wajen tinƙaho da harshen wajen gogayya da sauran harsuna da suke da tsarin rubutun da ya ɗaukaka daraja da matsayinsu a yau a duniya. 

Ra’in Bincike

An gina wannan aikin ne a kan ra’in nazarin harshe, musamman abin da ya shafi alamomin rayuwar al’umma. Gusau (2015:54) ya bayyana cewa alamomin rayuwar al’umma masu matuƙar muhimmanci waɗanda suka shafi zamantakewar al’ummar ta fuskar sadarwa ta harshen rubutu. An danganta wannan aiki ne da mazhabar wani masanin kimiyyar harshe Saussure (1978). Wannan mazhaba ta danganci nazarin ma’anar saƙo musamman ta hanyoyin rubuce-rubuce da zane-zane ko hotuna domin isar da wani darasi ko faɗakarwa a al’umma. A wannan takarda an lura da cewa, ire-iren waɗannan abubuwan da suka shafi hanyoyin isar da saƙo sun yi daidai da wannan bincike da aka yi a nan a kan yadda ake amfani da harshe (ta rubutu) wajen isar da saƙo a rubuce ga al’umma ta waɗannan kafafen sadarwa na zamani irin su fezbuk da watsaf.

Bitar Ayyukan Magabata

An duba abin da masana magabata suka ruwaito dangane da rubutun Hausa kamar yadda aka yi bita a wannan nazari kamar haka:

A cikin littafin Institute of Education (1979) an bi sawun haifuwar boko a rubutun Hausa da zayyana haruffan Hausa da ƙa’idojin rubutu waɗanda ya kamata a yi amfani da su a rubutun Hausa a kowane matakin na rubutun Hausa.

Yahaya (1988) an nazarci tarihin hanyoyin da aka bi na rubuta Hausa ne tare da bayanin ire-iren gudunmawar da aka bayar wajen samar da ɗimbin littattafan da aka wallafa…, da hanyoyin sadarwa kamar jarida da mujalloli na Hausa.

Appolonia da Salami (2000) aiki ne da ya duba tsarin rubutu a wasu harsunan Nijeriya a littafinsu: Orthographies of Nigerian Languages a inda suka nazarci hanyayon da ake bi wajen rubutu a harsunan da suka bibiya cikinsu kuwa har da harshen Hausa.

Sa’id (2006) an kalli wasu ɓangarori na ƙa’idojin rubutun Hausa da bitar yunƙurin samar da ingantacciyar hanyar rubuta Hausa aka yi a aikin. An faro tun daga aikin Bargery (1934) sai aikin kwaminti daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa na 1951 da na 1972 da kuma tarukan shekarar 1980 a Zaria da Yamai ta ƙasar Nijar a ƙoƙarin daidaita rubutun Hausa.

Wurma (2005) aiki ne da ya bayyana muhimmancin harshen Hausa da irin ci gabansa da ma’anar daidaitacciyar Hausa. An yi tsokaci a kan karin harshe da daidaiatcciyar Hausa da bambancin daidaitacciyar Hausa da sauran kare-karen harshen Hausa da ake da su. Aikin ya faɗaɗa bayani game da ƙa’idojin daidaitacciyar Hausa.

Adamu (2004) bayanin irin ci gaban da harshen Hausa ta samu ne lokacin da fasahar sadarwar zamani ta kwamfuta ta shigo Hausa, musamman a fagen ɗab’i da wallafe-wallafe cikin Hausa. An yi bitar ƙoƙarin da aka yi na samar wa Hausa haruffanta (fonts) a kwamfuta domin rubuta Hausa da haruffan Hausa zalla. An samar da haruffa na Rabiat da Daneji da na su Abdalla da Hausa Latin domin marubuta a Hausa ta hanyar amfani da kwamfuta da sauran kafafen sadarwa na intanet da ake amfani da su a Hausa.

Amfani (2024) aiki ne da aka an ambaci irin ci gaban da Hausa ta samu ta fuskar ƙa’idojin rubutun Hausa tun daga shekaru 1912 har zuwa tarurrukan shekarun 1970s da aka gudanar a wurare daban-daban a ƙoƙarin samar da daidaitacciyar ƙa’idar rubuta Hausa a ciki da wajen Nijeriya.

Samuwar Shafukan Sadarwa na Zamani a Hausa

Akwai kafafen sadarwa na zamani da ake ƙulla zumunta a Hausa kamar su wayar salula da ake aika gajeren saƙo na sms/mms ta GSM da shafin Facebook da na WhatsApp da wannan aiki ya bibiya domin ganin yadda ake rubuta saƙo a tsarin gajarta rubutun Hausa da masu amfani da Hausar suke yi kamar yadda aka kawo a wannan takarda.

Fezbuk (Facebook)

An samar da wannan kafar sadarwa ta fezbuk (Facebook) ne a shekarar 2003 da manufar sada zumunta ga ‘yan uwa da abokan hulɗa daga nesa da na kusa ta hanyar hira da gaisuwa da aika saƙonni: a rubuce da hotuna da sauti da bidiyo (Sani: 2015). Da tafiya ta yi nisa, sai abin ya shafi kowa a duk al’amura na rayuwa. Kusan duk rayuwa a yau, ta ɗamfara kan irin wannan kafa wajen samun labarai. Kai hatta su kafafen yaɗa labarai na murya (radio) da hoto ko bidiyo (talabijin) da gidajen jarida ko mujallu suna da shafukan facebook domin isa ga ma’abotansu.

Was’Af (WhatsApp)

Ana sadarwa da shafin WhatsApp ta hanyar aika saƙonni: a rubuce, da hotuna, da bidiyo, da murya. Kafafen yaɗa labarai kamar su: rediyo da talabijin da jarid da mujallu duk suna amfani da hanyar WhatsApp domin sadar da masu bibiyarsu a kodayaushe kai tsaye ko ajiye saƙo. WhatsApp kafa ce ta sadarwa, wadda mutane biyu ko fiye da haka suke iya hira mai tsawo (Chatting) ko kuma aikawa da hotuna ko bidiyo kan batutuwa daban-daban da ya shafi al’amuransu.

Tsarin Rubuta Gajeren Saƙo ta hanyar Taƙaitawa a Kafafen Sadarwa na Zamani

Hausawa sun kwaikwayi irin salon rubuta gajerun saƙo ne daga wasu harsuna na duniya kamar Ingilishi inda ake da salon rubutun taƙaita kalma a Ingilishi da yake zuwa a sigogi kamar guda uku:

(i)- Abbreviation da

(ii)- Acronym da kuma

(iii)- Initialization. 

Rubutun Hausa a Shafukan Fezbuk (Facebook) da na Was’af (WhatsApp)

Crystal (2006:42) yana mai cewa: “Abubuwan da irin wannan tsarin rubutun saƙo ta hanyar taƙaita rubutu ya ƙunsa sune inda ake amfani da gwauron harafi ko lambar ƙidaya da alamar rubutu domin wakiltar rukunan kalmomi ko yankin jimla ko ganga ko wata magana da take da nasaba da wani aiki ko motsi”, Ana amfani da alamomin rubutu kamar su aya da alamar tambaya ko motsin rai domin kyautata rubutu da fito da ma’ana sosai a fili. Waɗannan alamomin rubutu da haruffa da lamba su ne manyan tubalan gina rubutu a salon taƙaitawa da ake amfani da su a shafukan da kafafen sadarwa na zamani ya samar a Hausa.

Ga yadda ake amfani da irin wannan salon rubutun taƙaitawa da ta ginu a kan waɗannan abubuwa na rubutu a kafafen sadarwa da ake amfani da su a rubutun Hausa kamar haka;

1. Alamomin rubutu

Akwai alamomin rubutu da ake yin amfani da su wajen nuna taƙaitawa rubututaccen saƙo ta rubutun Hausa kamar su alamar ayar tambaya ko ta motsin rai ko alamar zarce ko karan-ɗori wajen domin taƙaita rubuta dogon zance ko kuma tsarin rubutun da marubuci ya zaɓar wa kansa. Ana amfani da wasu alamomin rubutu da ake samu da sauƙi yanzu a kan wayoyin hannu ko na’urar kwamfuta da masu amfani da su suke sarrafawa a matsayin kalmomin rubuta saƙo a rubutunsu. Misalin alamomi irin su: @, $, %, &, (), !, ?

Misali a wannan rubutaccen gajeren saƙo a taƙaice: mu/su n ms zw wrn d msln ƙrf 6?

Ma’ana: mu ko su ne masu zuwa wurin da misalin ƙarfe shida ɗin? A nan an samu yin amfani da alamomi a matsayin kalma da kuma lamba domin a isar da saƙo. Haka kuma an taƙaita rubutun wasu kalmomi da aka yi amfani da baƙi ba wasali a gaban su.

…z sm shgr d kɗ ksw

Ma’ana: za a samu masu shigar da kuɗi kasuwa

2. Haruffa

Ana amfani da haruffa domin wakiltar wasu kalmomi ko gungun kalmomi rubuta saƙonni ta harshen taƙaitawa da a batun wasali a kan gaɓa.

Misali a wannan saƙo kamar haka: mn tfy zw USA yau  byn slr asb d ƙrf 6

ma’ana: mun tashi zuwa Ƙasar Amurka a yau bayan sallar asubahi da ƙarfe shida.

Yyk d yr

Ma’ana: ya ya kuke da yaran

3. Lamba

Lamba tana nufin alƙalamin ƙidaya a inda Sa’id (2006:301) ya ce ana amfani da alamar lamba wadda ta ke wakiltar wani abu da ba harafi ba a salon rubutun taƙaitawa a Hausa. Misali a wannan saƙo kamar haka: z tr 10k d krf 8 kbw mai hwr.

Ma’ana: za a turo naira dubu goma da ƙarfe takwas ki bai wa mai haihuwar.

Dalilan Rubuta Gajerun Kalmomi a Shafukan Fezbuk da na Watsaf

Cryatal (2006; 55) ya ce: reduction saɓe time and money if intelligibility is not loss. Daga cikin dalilan da wannan nazari ya gano da yake haifar da wannan tsarin rubutun gajerun kalmomin saƙo ta hanyar taƙaitawa sun kasu kamar kasha uku a harshen taƙaita rubutu domin samun lokaci da tattalin kuɗin sadarwa muddin za a fahimci saƙon da aka rubuta kamar haka:

1, Sauƙi

A Skinner an fssara ma’anar sauƙi da cewa wani abu ne marar wuya da ba sai an wahala wajen sarrafa shi ba (1976:165). Watau a nan za a fahimci kalmar sauƙi tana bayar da damar samar da abu da ba zai wahalar ba. A irin wannan tsarin rubutun taƙaitawa, yana samar da sauƙin rubuta saƙo ga masu amfani da hanyar a shafukan sadarwa na zamani wajen isar da saƙonninsu ga waɗanda suka nufa dominsu.

2. Sarari

Skinner (1976:170) an kawo ma’anar sarari da cewa wuri ko sarari ko fili da za a yi wani abu kamar ajiya ko zama ko rubutu. Rubutun taƙaitawa yana bayar da damar samun sararin rubuta saƙonni da yawa a shafukan sada zumunta da ake amfani da su a aika da rubutaccen saƙo a taƙaice a cikinsu.

3. Lokaci

An samu ma’anar lokaci a Skinner (1976: 190) da cewa: wata dama ta gudanar da wani abu a ƙayyadadden lokaci. A rubutun taƙaitawa ana samun damar bayar da isasshen lokaci wajen rubuta abubuwa da yawa cikin lokaci ƙanƙani da mutum yake so ya rubuta saƙonni masu yawa da haruffa ƙalilan.

Yadda ya kamata a Rubuta Kalmomin Hausa a waɗannan Shafuka na Sadarwa

Babu shakka samuwar kafafen sadarwa na zamani ya kawo wani irin sauyi a rayuwar Bahaushe musamman ta fuskar sadarwa. An samu shigowa da karɓuwar sabon salon rubuta saƙonni a shafukan sadarwa da ake amfani da su. Rubutun Hausa ya ari hanyar rubutun taƙaitawa irin na Ingilishi a inda ake amfani da harufa da wasu alamomin rubutu a matsayin kalmomin rubuta saƙo. Hakan ta bayar da dama ga masu rubuta saƙonni da Hausa aron tsarin rubutun Ingilishi gaba-gaɗi domin isar da saƙonsu ta hanyar rubutun Hausa. Duk da aron hakan, akwai wasu harufa ko sautin da ake samu a Ingilishi da babu su a rubutun Hausa. Domin haka wannan takarda take ƙoƙarin nuƙusar da marubuta saƙonni a waɗannan kafafen sadarwa na zamani da yi la’akari da ire-iren abubuwan da Hausa take da su waɗanda babu a Ingilishi domin a tafi tare da zamanin da ake ciki. Kamata ya yi a rubuta f a gurbin p haka ma kalmomi ko harufa masu ƙugiya da Hausa take da su ne za a yi amfani da su kamar a rubutun daɗi ba dadi ba ko ɗaci ba daci ba da sauran ier-iren waɗannan. Haka ya kamata a yi rubutun a waɗannan kafafen sadarwa tun da Hausa tana da yalwa da wadatar kalmomi da harufan da za a iya amfani da su a fagen sadarwar rubutu kamar yadda wannan takarda ta yi nazari. Amfani da haruffan Hausa da ake samu a na’urorin rubutu na zamani ne zai bayar da armashin rubutun Hausa a waɗannan kafafen sadarwa na zamani da ake magana wannan nazari.

Sakamakon Bincike

Ire-iren matsaloli da suka bararraje a fagen rubutun Hausa a shafukan sadarwa na sada zumunta na zamani kamar yadda nazari ya binciko kuma aka kawo misalai a wannan takarda bai hana a tafi da wannan tsari na rubutun gajeren saƙo da aka taƙaita rubutun ba. Rubutun taƙaitawan sabon samfurin rubutu ne da zamani ya taho da shi a kowane harshe da ba a bar Hausa a baya ba. A nazarin an gano cewa rashin bin ƙa’idojin rubutun Hausa ne yake haifar da illoli da ruɗanin a kasa fahimtar saƙon da aka rubuta da rubutun Hausa kuma sukekawo saɓanin fahimta a waɗannan shafuka da suke jawo abubuwa kamar haka:

1- A kasa gane abin da aka rubuta na tambaya ko umurni aka bayar a saƙon?

 Misali: haka ake yi (?). ana tambaya ne

haka ake yi A wajen koyarwa (umurni)

a yi haka Ana bayar da umurni

2- Sauya ma’anar saƙon (inda aka samu kalma mai harshen damo)

ya ci duka Ya cinye duk

ya ci duka Ya bugu (a jikinsa)

3- Wahalar karanta abin da aka rubuta a saƙon

abinduba wane An harhaɗa kalmomi a jimlar maimakon: abin dubawa ne

Shawarwari

A wannan nazari ne ake ganin za iya magance ire-iren matsalolin da aka bijiro ta hanyar  horaswa ko ilmantar da masu mu’amala da kafafen sada zumunta na  zamani da:

1- Su fahimci muhimmancin bin ƙa’idojin rubutun Hausa.

2- Yadda za a riƙa amfani da daidaitacciyar hanyar rubuta harufa ko kalmomin Hausa a kowane lokaci a kowane irin rubutu da ake yi.

3- A kauce wa rubutun gaggawa duk da ƙarancin lokaci da ƙarancin filin rubutu a waɗannan kafafen sadarwa da ake amfani da su.

4- A bai wa kowane harafi ko lamba mai wakiltar kalma muhallinsa kamar baƙi  ko wasali ko lambar ƙidaya domin a fito da manufa da ma’anar saƙon abin da aka rubuta da rubutun Hausa.

Kammalawa

Samuwar rubutun Hausa a ire-iren waɗannan shafuka na sadarwar zamani wajen aika saƙonni a ko da yaushe ya kawo gagarumin sauyi a tsarin rubutun Hausa da ake yi yau. An kuma dubi abubuwan da ke tasowa a yi amfani da wannan salo na taƙaita rubuta saƙonni a irin waɗannan kafafe na sada zumunta na zamani. Daga cikin dalilan da aka yi nazari sun haɗa da ƙarancin wurin rubuta saƙo da kuma isasshen lokacin rubuta saƙon. Duk da haka nazari ya gano cewa wannan hanyar gajarta rubutu ta taƙaitawar rubuta kalmomi da sahen jimla da jimla ta samar da wani yanayi na ƙara ilimi wajen zurfafa tunani da nuna ƙwarewa da son burgewa tsakanin ma’abota tsarin. Nazarin ya fito da irin matsalolin da ake ganin masana da kwararru za su yi duba a al’amarin saboda a daidaita sahun tafiyar inganta rubutun Hausa a kowane bigire na rubutu da Hausa.

Manazarta

Adamu, U. A. (2004). Hausa and Information and Communication Technologies (ICTs). 6th Hausa International Conference, Kano: CSNL, BUK.

Amfani, A. H. (2024). Standard Hausa Orthography: Some Residual Issues. In Generative Approach to African Linguistics and Literary Studies. A Festschrift to Prof .M. Munkaila, Bedu, A. and Usman, B (Eds). Maiduguri: UPL

Appolonia, U.O. da Salami, O. S. (2000). Orthographies of Nigerian Languages. Ibadan: UPP.

Bargery, G. P. (1934). A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary. London: OUP

Crystal, D. (2006). Language and the Internet. Cambridge: CUP

Crystal, D. (2008). Txtng: The gr8 db8. Oxford: Oxford University Press.

Gusau, S. M. (2015). Mazhabobin Ra’i da Tarke a Adabi da Al’adu na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited.

Institute of Education A.B.U. Zaria (1979). Karatu da Rubutu a Harshen Hausa. Thomas Nelson (Nig.) Ltd.

Sani, U. (2015). Saɓa Ƙa’idojin Rubutun Hausa a Facebook. Unpublished B. A. Project, UDUS. 

Saussure, Ferdinand de. (1978). Course in General Linguistics, New York: Fontana/

Collins. Trans. from the French (Cours de linguistique g´en´erale, 1972 [1916]) by Wade Baskin.

Sa’id, B. (2004). Ƙa’idojin Rubutun Hausa: Jagora ga Marubuta. Kano: Benchmarks Publishers Ltd.

Sa’id M. (ed) (2006). Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero. Kano: CSNL, BUK.

Skinner, N. (1976). Ƙamus na Turanci da Hausa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.

Wurma, A. G. (2005). Daidaitacciyar Hausa Da Ƙa’idojin Rubutunta. Kaduna: Olatunde R. Publishing Works.

Yahaya, I. Y. (1988). Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-ruubuce cikin Hausa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.

Dundaye Journal

Post a Comment

0 Comments