𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Saurayi ne mai shekaru 19 ya tsinci kansa a cikin mummunan halin yin istimna’i har a cikin azumi. Ina hukuncin wannan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam
Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Istimnaa’i shi ne
mutum ya yi amfani da hannunsa ko wata na’ura a gabansa har ya biya buƙatarsa ta hanyar
fitar da maniyyi. Malamai sun saɓa wa juna a kan hukuncin wannan aikin, amma
maganar da ta fi bayyana a wurinmu ita ce maganar waɗanda suka ce: Shi
haram ne. Saboda maganar Allaah Ta’aala:
وَالَّذِينَ
هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ
(Muminai bayin Allaah
na-gari) su ne kuma waɗanda suke karewa ga
al’aurorinsu. (Suratul Muminina Aya ta 5)
إِلَّا
عَلَىٰ أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ
مَلُومِينَ
Sai dai ta hanyar
matan aurensu ko kuma kuyanginsu kawai, to lallai kam su (a nan) ba abaiban
zargi ba ne. (Suratul Muminina Aya ta 6)
فَمَنِ
ابْتَغَىٰ وَرَاءَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْعَادُونَ
Duk wanda kuma ya
nemi wata hanya a bayan haka, to waɗannan su ne masu ƙetare haddi. (Suratul
Muminina Aya ta 7).
Abu ne a fili kuwa
cewa: Amfani da hannu ko wata na’ura, kamar budurwar roba ko saurayin roba wasu
hanyoyi ne a bayan haka, watau a bayan aure ko amfani da kuyanga. Don haka ya
shiga ƙarƙashin ƙetare haddi.
Wannan shi ne asali.
Amma ko ya halatta ga
matasa waɗanda ba su da aure,
kuma suka ji tsoron faɗawa a cikin zina ko
luwaɗi da sauransu a ba su
fatawar cewa su riƙa aikata wannan?
Malamai sun nuna ba
kai-tsaye ba ne, har sai in an fara da gwada waɗansu matakan da shari’a ta kawo don
yin maganin matsalar kuma ba a samu nasara ba, kamar waɗannan:
1. Saurayi ya fara da
yin yaƙi da ransa, har ya fi ƙarfinta ya hana ta
aikata saɓo.
2. Ya yawaita yin
Isti’aazah: Neman Allaah ya tsare shi daga yaudara shaiɗan.
3. Ya yi ƙoƙarin zama mai khushu’i
da ƙanƙan da kai ga
Ubangijinsa a cikin sallah.
4. Ya yawaita yin
azumin nafila saboda Allaah, da neman kashe kaifin sha’awarsa.
5. Ya yawaita karatun
Alqur’ani da lura da ma’anoninsa da yin aiki da koyarwarsa.
6. Ya kula da
Zikirorin Safiya da Maraice da kwanciya barci da farkawa da sauransu.
7. Ya nisanci cin duk
abinci ko abin shan da aka san suna ƙara motsar da sha’awa.
8. Ya riƙa runtse ganinsa daga
kallon tsiraici a ko’ina, kamar waya da TV da sauransu.
9. Ya nisantar da
kansa daga cakuɗa da mata ko da
muharramansa ne, sai da larura.
10. Ya nisanci abokan
banza waɗanda za su ja shi, ko
su zuga shi ga saɓon Allaah.
11. Ya yawaita addu’a
da ƙanƙan da kai ga Allaah,
don ya kare shi daga wannan masifar.
Amma fa ya riƙa tunawa da maganar
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:
إِنْ
تَصْدُقِ اللهَ يَصْدُقْكَ
Idan ka gaskata
Allaah zai gaskata ka. (Sahih An-Nasaa’iy: 1845).
(A duba: Buluughul
Munaa Fee Hukmil Istimnaa’i na As-Shaikh Mas-huur Al-Salmaan (Hafizahul Laah)).
Sannan game da
hukuncin wanda ya aikata wannan mummunan aikin a cikin azumi, watau wanda ya yi
amfani da hannunsa ko wata na’ura kamar budurwar roba ko namijin roba ya fitar
da maniyyi daga gare shi, malamai sun saɓa wa juna:
1. Waɗansu malamai suna
ganin wanda ya yi hakan azuminsa ya ɓaci, saboda hadisin da Al-Imaam Al-Bukhaariy
da Al-Imaam Muslim suka riwaito mai cewa:
« يَتْرُكُ
طَعَامَهُ وَشَرَابَهُ وَشَهْوَتَهُ مِنْ أَجْلِى »
Yana barin abincinsa
da abin shansa da sha’awarsa saboda ni. (Sahih Al-Bukhaariy: 1894, Sahih
Muslim: 2763).
Suka ce: Wanda ya yi
amfani da hannunsa don fitar da maniyyi, bai bar sha’awarsa saboda Allaah ba.
Don haka, azuminsa ya ɓaci! (Tamaamul
Minnah: 2/154).
2. Wasu malaman kuma
suka ce: Azuminsa bai ɓaci ba, domin babu
wani dalili da ya nuna ɓacin azumin saboda
haka. Musamman ma dayake wasu daga cikin waɗanda suka zaɓi cewa azumin ya ɓaci, ba su kuma yarda
da cewa akwai kaffara a kansa ba. Suka ce: Domin abin da ya yi ba daidai ya ke
da jima’i ba! Jima’i ya fi kauri, don haka babu ƙiyasi a tsakaninsu!
Kamar haka, sai waɗannan malaman su ma
suka ce: A asali azumin mai istimna’i ma bai ɓaci ba, saboda jima’i ya fi istimna’in
kauri, kuma babu ƙiyasi a tsakaninsu! (Al-Awaayshah ya tattauna wannan mas’alar
a cikin Al-Mausuu’ah: 3/314-318).
Amma a kan hadisin da
waɗancan suka jawo, sun
bayar da martani da jawabai kamar haka:
1. Asalin hadisin a
cikin Sahih Al-Bukhaariy (1894) shi ne:
عَنْ
أَبِى هُرَيْرَةَ - رضى الله عنه - أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَآلِهِ وَسَلَّمَ - قَالَ « الصِّيَامُ جُنَّةٌ ، فَلاَ يَرْفُثْ وَلاَ يَجْهَلْ
، وَإِنِ امْرُؤٌ قَاتَلَهُ أَوْ شَاتَمَهُ فَلْيَقُلْ إِنِّى صَائِمٌ .
مَرَّتَيْنِ ، وَالَّذِى نَفْسِى بِيَدِهِ لَخُلُوفُ فَمِ الصَّائِمِ أَطْيَبُ
عِنْدَ اللَّهِ تَعَالَى مِنْ رِيحِ الْمِسْكِ ، يَتْرُكُ طَعَامَهُ وَشَرَابَهُ
وَشَهْوَتَهُ مِنْ أَجْلِى ، الصِّيَامُ لِى ، وَأَنَا أَجْزِى بِهِ ،
وَالْحَسَنَةُ بِعَشْرِ أَمْثَالِهَا »
Daga Abu-Hurairah
(Radiyal Laahu Anhu) cewa: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) ya ce: ‘Azumi garkuwa ne, (a ranar azumin ɗayanku) kar ya yi
batsa, kuma kar ya yi wauta. Idan kuma wani mutum ya nemi yin faɗa da shi, ko ya nemi
su zagi juna da shi, sai ya ce: Ni mai yin azumi ne. Na rantse da wanda
rayuwata ke ga hannunsa, sauyin bakin mai yin azumi ya fi ƙamshi a wurin Allaah
Ta’aala fiye da turaren miski: Yana barin
abincinsa da abin shansa da sha’awarsa saboda ni.
Azumi na wa ne, kuma ni nake bayar da sakayyarsa. Kuma kyakkyawan aiki guda
daidai da guda goma kwatankwacinsa ne.
Kalmar: Sha’awarsa a
cikin hadisin, saduwar jima’i da matarsa ake nufi, ba istimna’i ba. Ibn Hajr
Al-Asqalaaniy (Rahimahul Laah) ya kawo riwayoyin da suka bayyana haka a cikin
Fat-hul Baariy: 5/574-575, ya ce:
وَالْمُرَادُ
بِالشَّهْوَةِ فِي الْحَدِيثِ شَهْوَةُ الْجِمَاعِ لِعَطْفِهَا عَلَى الطَّعَامِ
وَالشَّرَابِ
Abin nufi da Sha’awa
a cikin Hadisin shi ne: Sha’awar jima’i, saboda an goya ta a kan abinci da abin
sha.
Sai ya cigaba da kawo
bayanai da riwayoyi a kan haka, har dai zuwa inda ya ce:
وَأَصْرَحُ
مِنْ ذَلِكَ مَا وَقَعَ عِنْدَ الْحَافِظِ سَمَوَيْهِ فِي فَوَائِدِهِ مِنْ
طَرِيقِ الْمُسَيَّبِ بْنِ رَافِعٍ عَنْ أَبِي صَالِحٍ: يَتْرُكُ شَهْوَتَهُ مِنَ
الطَّعَامِ وَالشَّرَابِ وَالْجِمَاعِ مِنْ أَجْلِي
Kuma abin da ya fi
fitar da wannan fassarar a fili shi ne abin da ya zo a wurin Al-Haafiz
Samawaihi a cikin littafinsa Al-Fawaa’id ta hanyar Al-Musayyib Bn Raafi’i, daga
Abu-Saalih cewa: Yana barin Sha’awarsa na abinci da abin sha da jima’i saboda
ni.
Don haka dai: Maganar
waɗannan malaman na ƙarshe ita ta fi a
fahimtarmu. Sannan kuma abin da ya wajaba ga wannan saurayin shi ne:
1. Ya tuba ga Allaah
Ta’aala tuba ta gaskiya a kan wannan laifin da ya yi.
2. Ya nemi Allaah
Ta’aala ya gafarta masa wannan ɗanyen aikin da ya aikata.
3. Ya yi nadama da baƙin ciki da da-na-sani
a kan wannan ɓarnar da ya tafka.
4. Kuma ya ɗaura niyyar cewa: Ba
zai sake komawa ga sake aikata wani irin laifin makamancin wannan ba, har zuwa ƙarshen rayuwarsa.
Muna taya shi da
addu’ar Allaah ya ƙara tsare masa al’aurarsa, ya kiyaye
shi har zuwa lokacin yin aurensa. Allaah ya taimake mu gaba ɗaya.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad
Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ƘARIN BAYANI
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.