Ticker

6/recent/ticker-posts

Laifin Wa?

Bilkisu Muhammad Garkuwa (2020). Laifin Wa?. Muhalli, Sutura (Labaran Da Suka Samu Nasara a Gasar Gajerun Labarai a Kan Muhalli Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2020). Darma Digital Prints.

LAIFIN WA?

Na

Bilkisu Muhammad Garkuwa

 “Ko ka biya ni bashi na ko in yi maka rashin mutunci.... tun yaushe nake lallaɓa ka sai ka ce kyauta za ka ba ni!”

Cikin matuƙar hasala wanda ake yi wa faɗan ya mayar da amsa.

 “Yo wa ya hana ka yin rashin mutuncin? Ka yi ka gama in dai rashin mutunci ne ba wanda ban gani ba, shekara ta goma sha takwas ina waɗari a gidajen haya, saboda haka naka wasa ne. Kuma kuɗi ban ce na cinye ba, kawai na ce sai na samu, idan kuma babu zan ba ka, ɗauki a cikin aljihuna.”

Shiru mutumin ya yi cike da jin haushi yake kallon malam Bello. takaici ne ya hana shi magana. Ya bar wajen a fusace kamar kububuwa. Taɓe baki Malam Bello ya yi cikin ƙwafa ya ce,

“Aikin kawai! Mutane ba uzuri a rayuwarsu. Duka ma yaushe na ci bashin na biya kuɗin haya? Ko sati ba a rufa ba amma don ci da zuci ya zo yana kumfar baki zai tara mini jama'a kamar wanda na cinye biliyan, alhali dubu biyu da ɗari biyar ne kacal.”

Malam Sani da ke gefensa ya kalle shi da mamaki.

“To wai ma da ka raina kuɗin me ya hana ka ba shi abin sa?” Sai da malam Bello ya ja dogon tsaki ya ce,

“To ina na gansu? Ka san hasarar da na yi kuwa? Kuɗin hayar wata uku na biya na baro wancan ƙabarin gidan.” Cikin mamaki malam Sani ya ce ban gane ƙabarin gida ba. Jinjina kai Malam Bello ya yi,

“Yo ƙabari mana malam Sani, wutar gidan ce daga soro ta lalace, an yi an yi mai gidan ya gyara ya ƙi, a ƙarshe dai dalilin wannan wayar da ta faɗo jikin ƙofa, ruwan saman da aka yi a ran nan, yara uku; biyu ƴan gidan ɗaya ɗan maƙwaɓta suka taɓa ƙofar duk suka mutu, saboda tsabar rashin imani da aka faɗo wa mai gidan sai cewa ya yi wai ai da ma ya ce mu tashi mun ƙi tashi, ka ji rashin imani, to idan mun tashi ina za mu?” Kama baki Malam Sani ya yi cike da mamaki.

 “Gaskiya dai laifinku ne, amma yanzu da kuka ga uwar bari ai kun tashi.”

 “Ka ji ka da wani zance, to idan mun tashi ina za mu? Ka san kuwa me ake kira da yawon gidan haya? Kafin ka samu sai ka kusa zautuwa, shi kansa dillalin neman na silifas yake, kuɗin in ka lissafa sai ka ga sun ishe ka biyan sadakin bazawara.”

 “Allah ya yi mana magani. Yanzu a wacce unguwar ka tare?” Dariya malam Bello ya yi.

 “Ka san ba na yin nesa da wajen gadina, ina can baya lungun kwata...” Da sauri malam Sani ya katse shi.

 “Lungun kwata gidan ƴan son banza?”

 “Yauwa! Nan fa… nan muka kama haya.”

 “Malam Bello ai wannan saki-na-dafe ka yi, ka baro tsiya ka koma wa tashin hankali, da darajarka me zai kai ka wannan gidan?”

 “a a dakata, duk wannan surutan da kake ji shaci-faɗi ne, kuma nan ɗin ai ya fi sauƙin kuɗi...”

 “Laifin naka ne, wanda bai ji bari ba, ya ji hoho!” Bakinsa ya taɓe ya miƙe daga kishingiɗar da ya yi.

 “Kana da matsala wani zubin, ga sauƙi wa zai tarkatarwa kansa tsada? kana kallon yadda haya ya zama jidali a cikin garin nan, da me mutum zai ji ne don Allah? Ai sara ake ana duban bakin gatari, ka gan ni nan tarawa nake ina ƙuƙutawa in samu in yi aure ko na huta da sunan aminin gauro.”

Takaici ne ya ƙume malam Sani, ya yi shiru da bakinsa ya kasa magana. Cikin ko-in-kula malam Bello ya cigaba da magana.

 “Kai dai kawai Allah kawo mana agaji, addu'a ta ɗaya Allah ya kawo mini hanyar da zan mallaki gida na ƙashin kaina, gida nake so na gani-kashe-ni.”

 “In ka so mallaka za ka samu mana.”

Kar kace hula malam Bello ya yi.

 “Kai ba ka rabo da so-ki-burutsu. a ina zan samu?”

 “Ba zancen so-ki-burutsu, da gaske sai dai matsalar a yadda nake gani fa sai ka na da hanya, musamman kai da kake da madafa, ma'ana ka ga gadi kake, wataƙil firinsifal ya dafa maka ka samu a bankin ba da lamuni...”

 “Kai-Kai-kai saurara, arrrr! Kada ka kawo mini zancen nan a mafita, abinda aka ce ba na talaka, sai na masu ƙumbar susa? Wane kiyashi in ji ɗan giwa! Bari ka ga ma in tashi in tafi, Allah ba mu alheri.”

Da ido malam Sani ya bi shi, da ko yana mamakin halinsa duk da ba yau suka saba ba. Kai tsaye tsohon kekensa ya hau ya wuce gidansa.

Cikin lungun nasu ya shigo ganin yana tangal-tangal kamar zai faɗa ƙatuwar kwatar da ta raba gidaje biyun da ke jere a cikin lungun ya sa shi sauka yana kakkauce fuska don wani irin wari ne mai ta da hankali yake fitowa daga kwatar. Cikin mita a ransa ya shige gidan da yake haya. Yana shiga ya ga matan gidan sun yi sororo suna kallonsa cikin tsegumi. Shigarsa ɗakin ya ji shewar wasu mata, zama ya yi yana mamakin ko meye gamun shi da su. Lami ce matarsa ta shigo fuskarta a haɗe, cikin faɗa ta ce,

 “Yanzu dai malam idan ba neman rigima ba mai ka dawo yi? Kana sane dai gidan nan ba kamar wancan ba ne, ka ga yanzu shigowar ka haka suka ya da mini da maganar wai ga ka nan kullum a tafe. Gaskiya ka daina zuwa don ba za ka janyo mini hayagaga ba!” Cike da mamaki yake kallonta.

 “Kina nufin in daina zuwa cin abincin ranan? Ban da masifa su biya haya in biya sannan a kafa mini sharaɗi kan wasu...”

 “Gaskiya ka bar zuwa, tun da nake zama gidan haya ban taɓa ganin munafukai sama da wannan gidan ba, komai naka a kan idonsu. Ka yi wa Allah malam ka daina zuwa, in dai abincin rana ne zan rinƙa ba Fa'iza ta kai maka, ko ni na rufe zani na kai.”

 “To, wata sabuwa... shi kenan yanzu dai zuba mini in ci, daga gobe Fa'izan ta fara kai mani tun da abin haka ne.” Cikin ƙunƙuni ta fice.

 Bayan ya gama cin abincin ya fito. Fitarsa daga ɗaki matan gidan dukkan idanuwansu suka yo kansa, da ƙyar ya samu ya kai bakin ƙofa, cikin lalura idonsa ya sauka kan wata mace da ke zaune ba riga a jikinta, ta kuwa watsa masa harara da sauri ya kau da kansa, dogon tsakinta ya jiyo har da rakiyar baƙar magana.

 “Aikin kenan kullum a cikin zirga-zirga don jaraba.”

Lungun ya biyo da kekensa, cikin rashin sa'a wani yaro ya yo jifa, da sauri ya kauce ƙaton dutsen ya faɗa kwata hakan ya sa ruwan kwatar fallatsuwa a jikin kayansa. Cikin takaici ya kai duba kan yaron da ya ruga a guje yana ƙyalkyala dariya. Kallon kayan jikinsa ya yi cike da takaici, wani magidanci da ke zaune kan dakali ya ce,

 “Sai haƙuri! Ka san yadda lungun namu yake.” Gyaɗa kansa kawai ya yi ya wuce yana tunanin yadda zai yi ya yi sallah alhali kwatar ta ɓata kayan, ga Lami ta hana shi shiga cikin gidan wai sai dare.

 Kwanci tashi watansu uku cikin gidan ‘yan son banza. A cikin wata ukun nan ya ziyarci ofis ɗin ƴan sanda sau huɗu saboda faɗan da ake yi da matarsa Lami, tuni ya ƙosa ya rasa yadda zai yi ya bar gidan nan don ya gaji.

 Cikin dare gobara ta kama gidan da ke kusa da su, hakan ta sa suka tashi cikin kiɗima da tashin hankali, kan ka ce kwabo wutar ta laso nasu gidan, ba shiri duk mutanen gidan suka yi ta kansu. Duk irin yawan jama'a da lungun ke da su, kasancewar lungu ne cikin lungu, hakan bai hana wutar laso gidajen da ke kusa da su ba. Ɗauki ba irin wanda ba a kawo ba, amma kamar ana ƙara mata fetur. An kira kwana-kwana sun zo, sai dai ba yadda suka iya don daga inda motar su ta iya tsayawa zuwa inda gidan yake ba ƙaramar tafiya ba ce, ga babu yadda za a yi motar ta iya shiga ciki saboda ko mutum biyu ba su isa sun jero kan lungun sun yi tafiya ba, balle mota.

Duk wata dabara an yi, an kasa shawo kan wutar, sai da ƙyar Allah ya taimaka ruwan sama ya sauko, da kuma agajin mutanen unguwa da wasu ruwa da aka yi ta ɗebowa aka samu wutar ta mutu, bayan gidaje huɗu da ta lashe, an yi dai arziƙi ba a yi asarar rai ba, sai ta dukiya. Yana jin ɗaya daga cikin ma'aikatan kwana-kwana na faɗin, kamata ya yi Gwamnati ta rushe unguwar gaba ɗaya don ba ta da tsari. Haka dai suka tattara suka bar layin don da ma ya gaji, ya kama haya a Layin Gangare.

 A ranar da suka tare ya fahimci akwai matsala sai dai ba shi da yadda zai yi. Shigowarsu unguwar ya iske ‘yan daba riƙe da manyan sanduna, wai suna wasan gangi, uwa-uba gidan da ya tare kusa da babban kango ne wanda a nan ‘yan dabar ke taruwa su yi dabdalarsu. Babu abinda ya ɗaga masa hankali sama da warin abubuwan bugarwa kala-kala. Cikin alhini Lami ta ce,

 “Malam anya kuwa za a haifi ɗa mai ido nan kuwa? Ka ga fa kana da asma.” Jinjina kai ya yi.

 “To, ya zan yi Lami… Mu zauna amma dole zan binciki wani gidan.”

 Satinsu ɗaya da dawowa, washegari da safe, yana wanka duk a takure yake, yana ta alla-alla ya yi ya gama ya fice, saboda banɗakin ba wata wadatacciyar ƙofar rufe shi sai wani langa-langa da a ke karawa, shi ma iyakarsa rabin bakin ƙofar sai dai ka yi buƙatarka a tsugunne don kana miƙewa za ku haɗa ido da mutanen gidan da jiki a bayyane, ba iya wannan ne kaɗai ya sa shi saurin ba, har da mugun warin da ke tashi a banɗakin saboda rashin kula da tsabta.

 

‘Yan sanda ne suka kawo wa kangon farmakin da suke kawowa lokaci-lokaci, zuwansu ya sa ‘yan dabar tarwatsewa da gudun ceton rai. Yana tsaka da wankan ɗaya daga cikin ‘yan shaye-shayen ne ya shigo gidan a guje, bai yi wata-wata ba ganin mata a tsakar gidan ya sa ya faɗa cikin banɗakin. Malam Bello na wanke fuskarsa ya ji ƙarar bige langa-langar an yi ciki, cikin tashin hankali ya buɗe ido ruwan sabulu ya shigar masa ido, azabar zafin da ya ji ne ya sa ya rufe idon, da sauri ya wawuri riga don suturta jikinsa, cikin rashin haƙuri ya sake bude idon ya daure rigar a jikinsa.

Ɗan shaye-shayen can karshen banɗakin ya shige yana raba ido, da sauri Malam Bello ya saka wando. Kan ɗan shaye-shayen ya yi da mugun haushi ya kai masa duka, kokawa sosai suka fara, cikin rashin sa’a santsi ya kwashi malam Bello ya faɗi, bai ji wani wahala ba ya tashi ya ƙara kai masa duka, a guje ya fice yana zage-zage. Yana fita ‘yan sandan suka kama shi.

Cikin kunya malam Bello ya fito daga shi sai wando, matan gidan sun yi cirko-cirko a tsakar gidan, ba abinda suke kallo sai jikinsa da wandonsa da ya kwaso dauɗar banɗakin, takaici ne ya sa ya koma banɗakin yana mitar halin matan gidan haya. Wani ruwan sabo Lami ta kai masa, ya yi sabon wanka ya fito, duk da hakan ba su bar wajen ba suna nan suna ta tsegumi da ƙananan maganganu, yana fitowa su ka hau ce masa "barka barka…! an yi arziƙi dai." bai amsa musu ba ya shige ɗaki, yana shiga Lami ta biyo bayansa.

 “Haba maigida suna maka barka amma ba wacce…” Cikin hasala ya katse ta.

 “Ban da rashin kunya suna kallona ba riga amma sun ware ido ba wacce ta yi ƙoƙarin barin wajen, ashe da a ce a kan wani ne hakan ta faru ke ma haka za ki saki idon kina kallonsa? Me ake da gidan haya! haba don kawai ana zaune gida ɗaya sai a ce muharraman juna ne ban da hauka?" Ya ƙarasa da jan tsaki, jikinsa sai rawa yake sosai. Allah kaɗai ya san irin baƙin cikin da ya ji, shi takaicinsa ma Allah ya sa lokacin da ɗan shaye-shayen ya shigo ba su gan shi a haka ba, cikin saƙe-saƙe ya fice daga gidan. A daren nan mazan gidan suka zauna har ya dawo wai suna masa barka da arziƙi matansu sun ba su labari, sama-sama ya amsa ya shige ransa ɓace yana jin takaici.

 Sace-sace a unguwar kamar hauka don duk ƴan tukwanen Lami an sace, haka ma kekensa sai tashi ya yi babu shi, ya ji takaicin sace keken nan. Tun daga lokacin ya tsani unguwar, da ƙunci yake shigowa da takaici yake fita. Matan gidan da sun gan shi sai su fara dariya ƙasa-ƙasa, hakan ya janyo ƙananan gulmace-gulmace har ta kai ana musayar yawu tsakanin Lami da matan gida.

 Al'amarin ƴan shaye-shayen nan sai ƙaruwa yake, yanzu abin har da rigingimu a tsakaninsu don cikin faɗan nasu har wani suka cire wa kunne, ranar ƴansanda suka dire a layin sun kama wasu daga cikinsu wasu sun tsere.

 Zaune yake jugum saboda dokar da ƴansanda suka sa wa unguwar na bayan sallar isha'i kada su ga kowa a waje, zama Lami ta yi.

 “Malam wai mene ne duk ka bi ka takura wa kanka, ga ka nan sai raguwa kake kamar ana ɗiban ka?" Cikin takaici ya ce,

 “Ba dole ba, a ce wai cikin unguwarku ba ka da zaman lafiya, kullum cikin ɗari-ɗari, unguwa sai ka ce filin yaƙi; kullum da abin da zai je ya dawo."

 "Sai haƙuri malam! Wata rana sai labari." Shiru ya yi yana ƙissima yadda zai tashi cikin gaggawa.

 

 Kwana biyu faɗan ya yi sauƙi, washegari da asuba suka tashi da ganin gawa a bakin kangon da ke jingine da su. Gawar riƙaƙƙen ɗan dabar da ya yi ƙaurin suna. Tashin hankali! Ranar unguwar kamar ta tsinke da ‘yansanda don ‘yan dabar nan hayaniya suka yi ta yi suna faɗa sosai, hakan ta sa aka kori kowa gidansu. Ranar bai fita wajen aikinsa ba don fur aka hana su fita har yamma ‘yansanda ne danƙare a wajen. Cikin satin ya tashi daga unguwar ya koma unguwar Gadar Yan Tsaki.

 

 Wannan karon ya dage a kan ba zai ƙara zama a gidajen da mutane suke da yawa ba ko kuma unguwar ƴan daba da kuma cikin lungu. Gidan da ya kama bakin titi ne daɗin-daɗawa su biyu ne kacal daga shi sai matar gidan wacce take fita aiki kullum sai babban ɗanta namiji, shi da Lami sun yi farin ciki sosai.

 Ba su fi sati ba suka fara fuskantar wasu abubuwa daga wajen ɗan maigidan mai suna Sadauki, don tun safe mamansa na fita abokansa suke zuwa su ƙure rediyo yana jin sauti, waƙoƙin da suke ji irin na banza wanda kunnuwanka ba za su so jin waɗannan munanan kalaman ba a gaban ƴaƴa, ga shi da yaren Hausa suke waƙar. Idn suna yi ba sa kashewa ko da lokacin sallah ya yi, Lami sai dai ta duba yanayi kawai ta yi salla. Abokansa sam ba su da tarbiyya, don har fitowa suke tsakar gidan suna iface-iface sai dai Lami ta koma ɗaki ko su shige banɗaki malam Bello ya yi ta jira su daɗe kafin su fito, ya rasa yadda zai yi, don tuni ya fara ƙosawa, Lami kullum sai ta yi masa ƙorafi.

Rannan da ya gaji ya faɗa wa mamansa, rufe ido ta yi ta shafa wa idonta toka a kan ba mai takura wa yaronta a gidan ubansa, dole suka kawo ido suka zuba masa, don ranar da ya kai ƙarar Sadauki yini ya yi da abokansa suna zage-zage wai sai sun daki hancin munafiki, ba yadda suka iya haka suka haƙura.

 Ranar wata asabar ne, Lami ta bar Fa'iza a gida a kan za ta je kasuwa ta dawo, bayan ta dawo ne ta iske Fa'iza cikin yanayi na taimako, ba sunan wanda take furtawa sai Sadauki. Kafin ta kai ta asibiti rai ya yi halinsa. "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun." kawai take furtawa. Ko da malam ya dawo ya kai ƙara Sadauki ya gudu.

Ƙiri-ƙiri haka aka nemi Sadauki aka rasa, wai don har suka bar unguwar bai dawo ba, a karshe ma aka ce ya gudu can Ikko. Fa'iza ƙanwar Lami ce mahaifinsu ɗaya, daga can garinsu aka kawo musu ita saboda su har yau Allah bai ba su haihuwa ba duk da shekarun da suka kwashe da aure.

 Cikin alhini suka koma sabuwar unguwar da take kan titi, don ko wata biyu ba su yi ba aka shafa musu jan fenti a kan su tashi za a yi titi a wajen, ba su tashi ba har sai da mota ta zo sannan suka tattara suka koma gidan bene mai ɗauke da mata goma sha ɗaya. Wohoho! Gidan tun da suka tare ake raba raini, idan iyaye mata ba su yi ba, yara za su yi iyayen su shiga ciki, gidan saboda bala'insu sun yi ƙaurin sunan rashin mutunci ga rashin tarbiyya, yaro ƙarami za ka ji yana ashar ɗin da za ka rasa a ina aka ƙirƙiro ta. Farkon zuwan Lami akwai alhinin rasuwar Fa'iza, hakan tasa ba ta shiga shirginsu, hakan ya sa suka sa ta a gaba wai ta fiya girman kai. Tun tana kau da kai har abun ya ishe ta ta fara damuwa, hakan ya sa ta ƙara kame kanta. Ba ta tsira ba, don abun nasu ma hauhawa ya yi tamkar tiri, shi ma kansa malam Bello bai tsira ba don tun da suka tare sai can dare yake dawowa.

 Kasa jure cin mutuncin su Lami ta yi, hakan ya sa ta fara biye musu, cikin tsautsayi abin ya zame musu faɗa har aka cire wa Lami tsiron gashi guda ɗaya, bayan dukan tsiya da ta sha don har kwanciya ta yi a asibiti.

 

Daga nan ba su koma gidan ba suka koma Ramin ƙasa. A nan ne fa Lami ta haifi ‘ya’ya uku Najib, da Nana A'isha, sai ƙaramarsu Asiya, sosai suke zaune lafiya da mutanen gidan sai abinda ba a rasa ba babban takaicinsu ɗaya gidan gab yake da ƙaton rami sannan gefensu ƙananan ƙwatoci ne.

***** *****

 Cikin tashin hankali suka tsirawa ruwan ido, wasu daga cikin yaran wajen har sun fara kuka. A cikinsu matasan aka samu wanda ya yi ƙarfin halin kiran ƴan kwana-kwana. Tuni labari ya zagaye unguwar cikin tashin hankali da koke-koke Lami ban da kuka da da-na-sani ba abinda take. Malam Bello zugudum ya yi ransa na ƙuna, shi kaɗai ya san irin baƙin cikin da yake ji, suna cikin wannan halin taraddadin ƴan kwana-kwana suka zo, ko da su ka cirosu dukkansu babu mai rai. "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun." ita ce kalmar da Malam Bello ke nanatawa. Labari ba inda bai je ba har gidajen rediyo, saboda sauran biyun matasa ne ɗaya yana karatun gaba da sakandire, ɗayan kuma ɗan ƙwallo ne da ya yi suna a unguwar. Cikin jimami mahaifiyar Malam Bello ta zo daga ƙauye.

 

 Kwana uku da rasuwarsu ne, ana zaman makoki hayaƙi na tashi daga cikin ramin wanda da ma hakan al'adarsu ce ƙone bolar cikin ramin, hayaƙin na damun mutanen unguwar sai dai ba su da yadda za su yi don yin maganar tamkar janyo wa kanka wani sabon tashin hankalin ne. Mahaifiyar malam Bello Inna, kasa jure wa shaƙar mummunan hayaƙin ta yi saboda lalurarta ta asma, don ita ma tana da shi. Yamma na yi cutar ta tashi, shi kansa ya san dalilin wannan hayaƙin ne don shi ma ya fara jin alamar tasa tana ƙoƙarin tashi, da sauri ya kai ta asibitin da ke can bayansu.

 

 Sun ba ta taimakon gaggawa saboda tana matuƙar buƙatar hakan shi ma suka kwantar da shi. Cikin kulawa likitan yake kallon malam Bello, ya girgiza kansa ya ce,

 “Malam Bello, hakan ba zai yiwu ba, tund a mun yi iya yin mu mun samu ta sauka sai ka mai da ita gida." Ƙara lafe murya malam Bello ya yi fuskarsa cike da nuna zallar alhini ya ce,

 "Don Allah likita ka bari ta ƙara kwana a nan har yanzu hayaƙin bai gama ci ba, tana komawa ciwon zai dawo ni kaina duk ranar da aka kunna wutar a makaranta nake kwana saboda na tsira da lafiyata." girgiza kai ya yi.

 “Tuntuni Malam Bello na faɗa maka na ce ka samu unguwa mai kyau ka zauna ka ga kai ba kowanne waje ne ya dace da kai ba."

 "Hmmm na ga rayuwa likita, na ga masifa duk a dalilin gidan haya, ka gan ni nan masifun da na gani ba za su lissafu ba. Nan ɗin ne kawai aka samu na kwarari shekaru a cikinsa ƙalau, shi ma ga shi abinda ya faru daga ƙarshe ka ga ɗana sukutum na rasa ga Nana can ita ma ba sauƙi daga faɗa wa cikin wannan kwatar ni ba lafiya ga Inna ma. Kai wannan duniya ta yi mini zafi! Ina zan saka kaina ni Mamman, gida haya!" Cikin tausayawa likita ya girgiza kai.

 "Sai haƙuri malam Bello, amma gaskiya wannan unguwar ba wajen zama ba ne, ko dan lafiyarku, duk unguwannin da suke zagaye da mu unguwar ku sun fi kowa yawan lalurar amai da gudawa da kuma cutar cizon sauro, saboda rashin tsabtataccen muhalli, uwa-uba wannan ramin, Allah ya kyauta, ita kuma Nana In-shaa-Allah za ta warke saboda mun mata allurai, amma da ba ku kawo ta da wuri ba to gaskiya da Allah kaɗai ya san me zai faru, shawarata ka je ka nemi gida a Bankin Ba da Lamuni mana, ko kafi son ka yi ta yawo daga nan zuwa can kuma duk kanwar ja ce, ba wani waje da za a je ba a dace ba?" Malam Bello kamar ya fashe da kuka ya ce,

 "Ka san wannan harka ce ta masu kuɗi ni kuma da gadi ma nake ina ni ina zuwa wannan bankin ?" Ware ido likita ya yi,

 "Wa ya ce maka sai mai kuɗi? Wannan banki na kowa da kowa ne, ma'ana in dai kana da cikakken aikin yi wanda za ka iya biyansu, to tabbas su kuma za su taimake ka." Da mamaki ya ce,

 "Likita da gaske kake?"

Tabbatar masa ya yi, cikin farin ciki ya yarda da shawararsa.

 Washegari aka sallame su, bayan sun dawo ya kuma samu wani mummunan labarin wani malam Sanusi wanda shi kaɗai ne yake iya wuce cikin layin da mashin, tsautsayi ya shigo garin kauce wa yara masu guje-guje ya faɗa ramin dai-dai ruwan ciki da ƴaƴansa uku da ya ɗauko su daga makaranta, kafin a zo a ciro su rai ya yi halinsa, tashin hankalinsu ya ƙaru, cikin sati ɗaya an rasa mutum bakwai. Labarin mutuwar ya yaɗu sosai, har sai da chiyaman ɗin yankin ya ji, nan hukumar kula da gidaje ta ba da sanarwar gidajen nasu ba a kan tsari yake ba, su tashi. Fur suka yi ƴan unguwar a kan ba za su tashi ba.

 Malam Bello tuni ya fara binciken yadda zai cike duk wani tsari na neman tallafin Bankin Ba Da Lamuni. Cikin nasara ya bi dukkan tsarin, cikin jin daɗi ya yi wa wasu da yawa bayanin abun musamman ƴan layin da suka ƙeƙesa kasa a kan ba mai tashinsu, wasu da yawa sun bi tsarin don da ma sun gaji da ɗauki ɗai-ɗai da ruwan ramin nan ke musu.

***** *****

 Kiran sallah ne ya farkar da shi daga barcin da yake shararawa, da sauri ya tashi. Fitowarsa daga ɗaki ya fahimci an yi ruwan sama, saboda jikar da gidan ya yi, har a lokacin ma akwai yayyafi kaɗan-kaɗan.

Bayan sun idar da Sallah a kan hanyarsa ta dawowa ya fahimci ba ƙaramin ruwa aka yi ba, murmushi ya yi haɗe da hamdala. Shekara da shekaru, duk damina ba su taɓa barcin kirki ba, ashe laifinsu ne. Da a ce sun yi abinda ya dace tabbas da sun yi barci mai cike da daɗi. Yanzu kam ya gode wa Allah ya kuma gode wa Bankin Ba Da lLmuni, ban da shi da Allah ne kaɗai ya san me zai faru da shi a gaba.

Alhamdulillah.

Muhalli, Sutura

Post a Comment

0 Comments