Fatima Bello Bala (2020). Alakakai (Gidan Haya). Muhalli, Sutura (Labaran Da Suka Samu Nasara a Gasar Gajerun Labarai a Kan Muhalli Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2020). Darma Digital Prints.
ALAƘAƘAI (GIDAN HAYA)
Na
Fatima Bello Bala
Ko da
Jamilu ya shigo gidan ya ga yadda komai yake a hargitse sai ransa ya ƙara ɓaci.
Matarsa da ke gefe tana haɗa wutar murhu ya kalla kafin ya girgiza kai cike da
damuwa sannan ya shige ɗaki.
A
gidan haya suke wanda ya haɗa mabambantan ƙabilu kamar; Igbo da Yoruba da kuma
Hausawa. Duk da bambancin ɗabi'u da al'adu na mazauna gidan da kuma kasancewar
gidan ɗakuna takwas ya mallaka, hakan bai sa mai gidan ya yi banɗaki fiye da ɗaya
ba. Haka suke ta fama, matar wani na banɗaki mijin wata na bakin ƙofa yana
jira. Wani lokacin kuma sai shirgegen ƙato ya fito daga shi sai singileti da
gajeren wando ya bararraje a tsakar gida, ga matan mutane na zirga-zirga.
Rabi ta miƙe ta bi mai
gidanta Jamilu,
“Sannu da zuwa Abban Afnan.”
“Yauwa sannu.” Ya amsa a taƙaice.
“Ya jikin Jabir ɗin?”
“Jiki sai dai godiyar Allah.” Ta ƙarasa zancen
tana kallon inda Jabir yake kwance cikin mawuyacin hali.
Jabir yaro ne da bai fi shekara huɗu a duniya
ba. Shekaran jiya ya tashi da matsanancin zazzaɓi, amma ya jigata shi matuƙa.
“Ina sauran yaran suke?” Jamilu ya tambaya.
“Na
aiki Afnan gidan Baba Mairo, Yusuf da Ummi kuma ga su can cikin yaran Maman Ada
suna wasa.” Yana jin haka ya ɓata rai,
“Ba
na faɗa miki ba na son ki rinƙa bari suna cuɗanya da yaran nan ba? Yaran da ba
su da wata cikakkiyar tarbiyya.”
“Ka
yi haƙuri, ka san halin yara, kuma idan suka gane cewa ina hana yarana wasa da
nasu ai ba za su ji daɗi ba.”
“Kada Allah ya sa su
ji! Ni daɗin nake ji da kika bar su suke shiga cikinsu?”
Ganin sai ƙara hawa
yake kamar garin kwaki ya sa ta bar ɗakin. Abinci ta ɗauko ta kawo masa sannan
ta koma tsakar gida ta ci gaba da girkinta.
Jamilu babur mai ƙafa uku yake ja (keke
napep). Yara huɗu suka samu tare da matarsa Rabi, ga su a gidan haya kasancewar
ba su da ƙarfi, wani lokacin ma abinci gagarar su yake yi. Babbar 'yarsu ita ce
Safiya, sunan mahaifiyarsa ne da ita, suna kiran ta da Afnan, shekarunta
bakwai, sai Jabir da ke bin ta, sannan Yusuf, sai kuma autarsu Ummi wadda take
da shekara ɗaya da rabi.
Ranar wata Asabar Jamilu ya fita sana'arsa, bai
jima da fita ba keke napep ɗin nasa ya tsaya, da ƙyar ya sami wani ya taya shi
turawa suka isa wurin masu gyara. Ko da aka duba sai aka tabbatar masa da cewa
bulo-injin ne ya buga.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!”
Abin da kawai Jamilu ya
rinƙa maimatawa a cikin zuciyarsa, kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci yana
cikin damuwa.
Gefen wata bishiya da ke kusa da shi ya samu
ya zauna ya haɗe kai da gwiwa, ya rasa da wane zai fara. Ga yaronsa a gida ba
shi da lafiya ko kuɗin kai shi asibiti babu, ga kuɗin hayar gidan da yake ya
kusa ƙarewa har an ba shi notis, ga kuma gidan da mahaifiyarsa take ciki tun
satin da ya wuce ake ta damun sa da ya kawo kuɗin haya, kasancewar ita ma haya
ya kama mata, saboda ginin gidansu ya rushe kuma ba shi da halin yin sabo.
Shi ne babba a gidansu, manya a cikin ƙannensa
duk mata ne da ke gidan mazajensu, ragowar kuma yara ne ƙanana, don haka tilas ɗawainiyar
shi zai ɗauke ta.
Yana cikin wannan yanayin ne wayarsa ta fara
ihun neman agaji, ganin matarsa ce ke kira ya yi saurin ɗagawa.
“Jikin Jabir ya yi tsanani.” Shi ne abin da
kawai ta faɗa tana kuka.
“Subhanallah! Ga ni nan zuwa.” Ya katse wayar.
Kansa ya ji yana sara masa, ƙwaƙwalwarsa ta
cushe, ya rasa abin da zai fara yi. Yunƙurawa ya yi jiri na neman ɗaukarsa
kamar ɗan maye. A haka ya ba da
ajiyar babur ɗinsa ya tare abin hawa ya nufi gida.
Yana shiga gidan ɗakinsu ya nufa, ganin
yanayin Jabir ya ƙara dagula masa lissafi, kafin ya yi wani yunƙuri wayarsa ta ɗau
ruri, Balki ce ƙanwarsa. Yana ɗagawa ta shaida masa mahaifiyarsu ce babu
lafiya, rai a hannun Allah. Idanunsa suka ƙara yin jajir, ya kalli matarsa.
“Mama babu lafiya zan je yanzu in dawo.”
“Jabir ɗin fa?”
“Ba ni da kuɗin kai shi asibiti a halin yanzu,
ko mama tafiya zan yi na ga
halin da take ciki, amma ki yi haƙuri bari na dawo.”
Ko da ya je gidan sai ya tarar jikin mama ya
yi tsanani. Shiru ya yi don ya
rasa madafa a wannan gaɓar. Ganin kiran Rabi ya sa ya dafe kai ya tuna da ciwon
yaronsa. Tana kuka ta sanar da shi Jabir ya rasu.
“Innalillahi
wa'inna ilaihir raji'un!” Abin da ya furta ke nan a bayyane.
“Lafiya dai Yaya?”
Ƙanwarsa ta tambaya.
“Jabir ne ya rasu. Zan je gida.” Ya faɗa a
taƙaice ba tare da ya jira abin da za ta faɗa ba, ya tafi.
Sati ɗaya da rasuwar Jabir mai gidan da
suke ya matsa masa lamba a kan kuɗin haya. Tilas ya tattara kayansa ya bar
gidan, don ba shi da kuɗin da zai biya haya ko da na wata guda ne balle
shekara.
Yana zaune a gefen titi bai san inda zai nufa
ba, bai taɓa da-na-sanin rashin abin yi da muhalli irin yau ba.
A dalilin rashin bin shawarar da ya yi, shi
a dole aure yake so, ga shi babu sana'ar kirki kuma babu gida. Duk hangen da
ake yi masa da nuna masa muhimmancin muhalli amma ya yi biris. Yanzu ji yake
kamar ya sauwaƙe wa Rabi ya shiga duniya neman kuɗi.
Ya
sha ji ana cewa, 'Rayuwa kasada ce, sai an shiga an yi kutse ake samun nasara a
cikinta.'
Wannan saɗarar kawai ya
iya riƙewa, ya manta da mafi girman kasada shi ne ka rungumi abin da ba ka da
hannun ɗaukar sa. A hankali wani
zazzafan hawaye ya shiga silalowa daga idonsa. Bai damu da share su ba, domin
ya san kuka yanzu ya fara yi, tun da ya saya wa kansa shiga kasadar da ba zai
iya ba. Ya janyo igiyar wahala ya sagale wuyansa da ita. Saƙa da warwara yake,
amma ko kaɗan bai samo bakin zaren ba, ba shi da inda zai je, kamar yadda ba shi
da wanda zai kai wa kukansa ya share masa hawaye.
Kiran sallar azahar ne ya ankarar da shi daɗewar da ya yi
a wurin. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, yana share hawayen da ke kan
fuskarsa. A
hankali ya miƙe ya fara ajiye takunsa tamkar yaro mai tatata. Bai san inda zai nufa ba, yunwar cikinsa kaɗai
ta ishe shi.
A ɓangaren Rabi kuwa, tafiya take tana
tunanin makomarta a gidansu. Ba domin tana tunanin tarba mai kyau ba, haka ta
nufi gidan nasu da ke unguwar Arkillah cike da fargaba. Sallama ta yi ƙasa-ƙasa
kamar mai ciwon baki sannan ta shiga gidan. Aunty Lami da ke sharar tsakar gida
ta yi tsaye tana yi mata wani mugun kallo kafin ta ce, “Korarru! An sake korar ku ke nan? Tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alheri ba. Ke
kam Allah ya wadaran hali irin naki. To bara ki ji, ba a gidan nan ba, ku nan
kullum cikin yawon haya ba ku nan ba ku can, kuna ta gantali sai ka ce 'yan
gudun hijira.”
Ta san da ma za a rina,
sam Aunty Lami ba ta ƙaunar aurenta da Jamilu kasancewarsa talaka mai ƙaramin
ƙarfi. Har zuwa wannan lokacin ba ta ƙarasa shigowa gidan ba, haka zalika ba ta
fita ba, ta yi tsaye ƙyam ita da yaranta.
“Wai ke da wane ne haka Lami?” Umma ta faɗa
tana ƙoƙarin fitowa daga falo.
“Ni da wannan 'yar yawon hayar, an sake koro
su ta yo mana gida ita da yaran nan masu shegen ci.”
“Wai Rabi kike nufi?”
“Ita fa Umma, yo gidan nan ai da an ce korarru
ita ake nufi, domin babu gidan hayar da suka shiga suka shekara biyu ba tare da
an koro su ba.”
“Shi ne kike misalinta da 'yan gudun hijira…
Lami ai ko masu ‘yan
gudun hijira yanzu sun
tasar wa mallakar muhallinsu.”
Duk da zaman Afnan
yarinya ƙarama mai ƙananan shekaru, ta ji babu daɗi irin abin da ake yi wa
Amminsu.
“Umma ina wuni?” Rabi ta ce da Umma lokacin da
ta ƙarasa fitowa daga falon.
“Lafiya?” A gajarce.
Shiru Rabi ta yi ba ta
sake cewa uffan ba.
“Wai lafiya kika yi mana tsaye haka?” Umma ta sake wurga mata wannan
tambayar. Cikin rawar murya Rabi ta fara ajiye kalamanta, “Daman...”
“Daman
me?” Aunty Lami ta katse ta.
“Umma
na san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi, tun da kika gan su da kaya haka, to
fa koro su aka yi kamar yadda aka saba.”
“Wai
ke shi ke nan, haka za ki yi ta zama idan aka koro ku ki dawo gida ki zauna,
sai kuma an sami wani ki koma… ke a dole tantabara uwar aure?”
“Umma ba haka ba ne, ba
shi da kuɗi ne.”
“Ke dalla rufe mini baki, kullum zance ɗaya, babu! Ko ɓeran masallaci ba
zai faɗa muku babu ba… To ɗakin da kika saba zama Lami ta sanya kayanta a ciki,
sai dai ki je ɗakin ajiye kaya (store) ki gyara ki zauna.” Umma ta
ƙarasa zancen cike da rashin tausayi.
“To!”
Kawai Rabi ta furta game da share hawayen da suka cika kwarmin idonta, ta tuna
Innarta, da tana duniya ta san ko da hakan ya kasance da ita, to abin zai zo
mata da sauƙi.
Umma kishiyar
mahaifiyarta ce wadda yanzu shekararta shida da rasuwa. Ita kaɗai ce ga
mahaifiyarta. A baya babu irin azabar da Umma ba ta gana mata ba, sai da ta yi
aure ta bar gidan sannan ta sami sa'ida. Haka ma Aunty Lami ke ba ta wahala
tare da wulaƙanci iri-iri. A wurin mahaifinta kawai take jin sanyi, shi kuma
matafiyi ne; bai fiye zama a gari ba. Shi ya sa suke cin karensu babu babbaka,
sai dai sun manta Allah ba ya kwana kuma yana ji da ganin su.
Kamar wata ɓarauniya haka ta ja yaranta suka
wuce inda aka ce shi ne ɗakinsu. Cikin lokaci ƙanƙane ta gyara wajen tsaf suka
zauna ita da yaranta.
“Ammi me ya sa Umma da Mama Lami suka fiye
masifa?”
Kafin Rabi ta ce wani abu Yusuf ya karɓe da
cewa, “Idan na girma na yi kuɗi ba zan ba su ba, tun da suka sanya ki kuka.”
Sosai yaran suka ba ta mamaki, musamman Yusuf.
Ba ta yi tunanin suna fahimtar abubuwan da ke faruwa haka ba. Wata dariyar yaƙe
ta yi kafin ta ce da su, “Kin ga Afnan ki daina, babu kyau yin zancen wani ba
ya nan.” Sannan ta juya ta dubi Yusuf ta ce da shi, “Ba su ne suka sanya ni
kuka ba, wani ƙwaro ne ya faɗa mini a ido, kuma ku daina yawan surutu ba shi da
amfani. Ko kuna son maganarku ta ƙare ku zama kurame?”
“A'a Ammi" Suka faɗa a tare.
“Yauwa yaran kirki! To ku daina magana a kan duk abin da bai shafe ku
ba, kun ji ko?”
“To Ammi.”
****
“Sannu Mama! Ya ƙarfin jikin?” Jamilu ya furta
cikin sanyin murya.
“Da sauƙi. Ina Rabi da yaran?” Mama ta ƙarasa
zancen tana ɗan nishi saboda azabar ciwo, ga shi babu kuɗin zuwa asibiti, sai
'yan dabaru da harkar gargajiya ake ɗan yi mata.
“Na tura ta gidansu kafin mu ga abin da Allah
zaiyi.”
“To Allah ya kawo mana sauƙi… a yi ta haƙuri, kowa da kalar tashi
jarabawar.”
“To
Mama na gode.”
Sallama ya yi da Mamar
ya fito tsakar gida inda ya tarar su Hajara da Maryam a zaune. Kallonsu ya yi
cike da tausayin halin da suka tsinci kansu a ciki, ga su yara matasa amma
rashin wadata na neman mai da su tsofaffi; duka-duka shekarun Hajara goma sha
bakwai inda Maryam take da shekara goma sha huɗu. Su ne ƙananan ƙannensa
“Ni na tafi sai na dawo, a kula don Allah.”
“Allah ya kiyaye hanya ya kuma yi jagora,
Yaya.”
Ya amsa da amin sannan
ya fita.
“Yauwa malam Jamilu da ma kai
nake nema, ina ta zuwa muna saɓani.” Haruna mai haya ya faɗa.
“Allah sarki!” Jamilu ya ce da shi yana mai
addu'ar Allah ya ɗora shi a kansa.
“Game da mai gidan nan ne, ya yi ta damuna in
kawo masa kuɗin gida amma ina yi masa 'yan dabaru, wannan karon kam ya matsa
lamba, ya ce ko ku tashi ku ku ba da kuɗin haya.”
Shiru ne ya ɗan biyo
baya na wasu daƙiƙu kafin Jamilu ya numfasa, ya ce, “Ka ƙara yi mini uzuri malam
Haruna, wallahi sisin kwabo ba ni da shi yanzu, abubuwa sun taru sun yi mini
yawa. Ba sai na ce maka
komai ba, ka san halin rashin lafiyar da mahaifiyata take ciki.”
“Sanin hakan ne ya sa
nake ta ɗaga maka ƙafa ko a wancan lokacin, yanzu mai gidan ne ya takura ni.”
“Yanzu ya kake so na yi? Ban san inda zan kai mahaifiyata da ƙannena ba
idan har aka tashe su daga wannan gidan. Ka taimaka mana don Allah!”
“Ba
daga ni ba ne Jamilu, amma zan je na samu abin ce masa, idan ya gamsu ya bar ku
kun zauna shi ke nan, idan kuma bai yarda ba kada ka ga laifina.”
“To malam Haruna na gode.” Da haka suka yi
sallama.
Misalin ƙarfe takwas na
safiyar Laraba, Rabi ce kwance a ɗan karamin ɗakin da ta tare, yaranta na gefe
suna barci, ita kuwa sai tufka da warwara take yi. Jin bugun ƙofar ɗakin ya tsinke zaren
tunanin da take saƙawa.
“Wa
kike jira ya yi maki aikin gidan?” Aunty Lami ta furta cikin ɗaga murya.
“Yanzu
zan fito Aunty.” Rabi ta faɗa. In da sabo, to ta saba, domin tun da ta zo gidan
ita ce shara, wanke-wanke da girki. Sai dai ba ta gajiya wajen kai wa Allah
kukanta, kuma tana da yaƙinin wata rana komai zai zama labari. Tabbas ta ga ɗumbin
kuskure cikin auren wanda ba shi da aikin yi, domin kuwa sana'a da muhalli suna
daga cikin jin daɗin rayuwar mutum. Ga shi a dalilin rashinsu ita da yaranta
suna ganin taskun rayuwa. Hawayen da ya zubo mata, ta goge kafin ta fita
don yin aikin da ya zamar mata dole.
“Ko yaushe wahalarmu za ta ƙare? Ni dai na san
ina daga cikin jerin matan da suka zo duniya cikin rashin sa'a, da kuma dakon
soyayyar wahala. A da ina zaune da Jamilu ne saboda soyayya, amma a yau ina
zaune da shi ne saboda 'ya'yana.” Ta raya a zuciyarta.
“Ya Allah ka dubi maraicina! Ka kawo mana
haske a cikin rayuwarmu.” Ta faɗa a bayyane bayan ta share hawayen fuskarta.
****
“Lokacin da muke nuna maka cewa ka dakata da
auren nan sai ka tsaya da kanka, gani ka yi kamar muna yi maka baƙin ciki ne.
Yin aure mutum bai tsaya da ƙafafunsa ba tamkar baɗi ba rai ne, amma kai a dole
soyayya; aure kake so! Yanzu mene amfanin
haka? Kusan haihuwa huɗu amma duk a yawon gidan haya.”
Ali abokin Jamilu ya faɗa yana gyara zamansa
a kan bencin da suke zaune a ƙofar gidansu.
“Duk
wani kuskure na gano shi yanzu Ali, haƙiƙa na yi da-na-sani marar adadi, rashin
aikin yi ya zame mini ALAƘAƘAI a duniyata, sai dai hakan yana cikin ƙaddarata.
Don Allah ka ba ni shawara mene abin yi? Har ga Allah na fara tunanin sauwaƙe
wa matata igiyar aurena ko...”
Da sauri Ali ya katse
shi da cewa, “Ka yi hauka ne Jamilu? Ta ya ma wannan tunanin zai fara zuwar
maka? Matar da ta sadaukar da komai nata a kanka har kake tunanin saka mata da
saki? Idan har kana tunanin wannan ita ce mafita, tabbas ka yi kuskure.”
“To mene ne mafita Ali? Kaina ya toshe, tunanina ya tsaya, ba na
fahimtar komai a yanzu.”
“Ka
natsu Jamilu… duk yadda kake ganinka, to ka fi wasu… ka gode wa Allah.”
“To
Ali ina jin ka, yanzu mene ne abin yi?” Ya ƙarasa zancen cikin yanayi
na ban tausayi.
“Yanzu ina ga abu ɗaya za mu yi, akwai gidan
da zan je yin fenti jibi sai mu je tare, sai dai ban sani ba ko za ka iya yin
aikin fenti?”
“Me zai hana, zan iya mana, na ji daɗi sosai
Ali, Allah ya kai mu.”
“Daga nan sai mu ƙara da neman wani aikin
komai ƙanƙantarsa, ko da kuwa aikin ƙarfi ne, saboda zama hakan ba zai yiwu ba
sai da buga-buga.”
“Haka ne kam, to yanzu bayan fentin wane aiki kake tunanin za mu nema?”
“Za
ka iya yin leburanci?” Ali ya tambaye shi.
“Sosai
kuwa, yanzu ni ko aikin kwasar kashi ai zan iya, idan har zan rufa wa kaina da
ahalina asiri.” Cewar Jamilu.
“Ƙarshen
layin nan namu na ga ana yin wani babban gini, kamata ya yi gobe da safe ka zo
mu tafi mu gani ko Allah zai sa a dace. Sannan mu bazama neman aiki da
diploma ɗinka, ita ma ko za a sami nasara.”
“To Ali na gode sosai, Allah ya bar zumunci.”
“Amin!”
Daga haka suka yi
sallama.
****
Ƙarfe goma da rabi na dare wayarta da ke gefe
ta ɗauki ruri, ganin Abban Afnan ne ya sa ta ɗaga da sauri, cikin sanyin murya
ta gaishe shi. Amsawa ya yi game da
cewa, “Ammin Afnan don Allah ki yi haƙuri, kin ga ban dawo ba. Cin mutuncin
Umma da Aunty Lami yana sosa mini rai, shi ya sa kika ga ban dawo ba.”
Kanta
ne ya juya, tana jin tausayinsa na tsirgowa a zuciyarta. Shi talaka ne amma bai
rage ta da komai ba, ban da gidan da za su zauna. Ya tsaya mata a lokacin da ta
so shi! Ta tabbata da yana da dama zai shimfiɗa rayuwarsa ta taka ta bi ta
kansa. Sai dai so ba komai
ba ne, idan har babu kwanciyar hankali.
“Babu
komai, ka bari sai Baba ya dawo, in sha Allahu cikin satin nan zai dawo. Mun yi waya da shi,
amma ko su ba su sani ba. Idan yana nan duk wannan tijarar ba za su yi ta ba.”
Ta faɗa da muryarta mai sanyi.
“To Babu damuwa, Allah ya dawo da shi lafiya.
Ya yarana?”
“Amin! Yara sun yi barci. Ya jikin mama?”
“Jikin mama da sauƙi, an gode Allah.”
“Masha Allah, don Allah
ka gaishe ta.”
“Za ta ji!”
Sun ɗan taɓa hira kafin suka yi sallama tare
da katse kiran.
****
A hankali yake tuƙin motarsa, ganin ya wuce wani
mai kama da wanda yake nema ruwa a jallo ya sa ya dawo baya (reverse). Sam Jamilu bai gan shi
ba, ganin haka ya sa Alhaji Sani danƙara masa kira daidai lokacin da yake
fitowa daga motar.
Jamilu yana juyowa suka yi ido huɗu da Alhaji
Sani. Sai da 'ya'yan cikinsa suka motsa, tsaf ya san rashin mutunci irin nasa.
A hankali Jamilu ya ƙaraso wajensa jiki a sanyaye.
Cike da masifa ya fara magana, “Jamilu wane
irin ƙaramin mutum ne kai? Yau kimanin sati biyu babu kai babu kamanninka, baka kawo mini balas ɗin
kuɗina na napep ba… ka san halina sarai! Ban san wani abu asara ba. Ina ta tambayar abokan aikinka suna cewa ba
su san inda kake ba. Na aika gidanka an ce ka tashi. Saboda rashin gaskiya ya
yi maka katutu a zuciya ba ka sanar da ni ba, shi ne za ka gudar mini da keke?
To wallahi ba ka isa ba, hukuma ce za ta raba mu.” Ya ƙarasa yana zaro waya
daga aljihunsa.
“Ka
yi haƙuri Alhaji, ka san wannan ba halina ba ne, akasi aka samu.”
Nan dai Jamilu ya yi masa bayanin duk abin
da ya faru da shi. Amma fafur Alhaji Sani ya ce bai san zancen ba, sai ya ba
shi napep ɗinsa ko ya haɗa shi da hukuma.
Har
mutane sun fara taruwa, kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Da ƙyar aka samu
Alhaji Sani ya amince aka yi sulhu da yarjejeniyar zai kai masa kekensa idan ya
gyara. Nan kowa ya watse aka bar Jamilu, sam ƙafafunsa sun gagara ɗaukarsa.
Addu'a ya hau yi kan Allah ya dube shi ya kawo masa ɗauki. Takawa yake ba don
ya san inda yake jefa ƙafarsa ba, bai ankaro ba sai takawar birkin mota ya ji
da ƙarfi. Cike da masifa mai motar ya fito yana ɗura masa ashar, juyowar da
Jamilu zai yi suka haɗa ido. Mutuwar tsaye mai motar ya yi, cike da mamaki yake
kallon Jamilu tun daga ƙasa har sama.
“Jamilu
Adam!” Ya faɗa mamaki kwance a kan fuskarsa. Cikin rawar murya Jamilu ya furta,
“Muttaƙa
Hassan!”
Jamilu da Muttaƙa aminan juna ne, yanayin
aikin mahaifin Muttaƙa ya sa suka bar gari, tun lokacin ba su sake haɗuwa ba
sai yanzu, kusan shekara bakwai da rabuwarsu.
Yau cike take da farin
ciki kasancewar mahaifinta na hanyar dawowa, misalin ƙarfe biyu na rana Baban
su Rabi ya dawo daga tafiyar da ya yi ta wata da watanni. Cikin sa'a yana
shigowa ya ci karo da su Afnan a tsakar gida, suka rugo da gudu suna yi masa
oyoyo, kamar bai san komai ba, ya ce, “Yaushe kuka zo… Ina Amminku?”
Ganin ɗakin da suka nuna masa ne ya sauya masa
fara'ar fuskarsa a lokaci ɗaya, jan yaran ya yi suka isa har ɗakin, wanda hakan
ya yi daidai da fitowar Umma daga ɗakinta. Sosai hankalinta ya yi matuƙar tashi da ganin maigidanta. Nutsuwarta ta
tattaro kafin ta furta.
“Saukar
yaushe Alhaji… Wannan karon zuwan ba-zata aka yi mana?” Ta ƙarasa zancen tana
dariyar yaƙe.
Bai ce da ita uffan ba illa
mugun kallon da ya wurga mata tare da wucewa ɓangarensa.
Da misalin ƙarfe biyar na yamma, bayan Baba ya
huta ya ci abinci, ya kira Rabi ɗakinsa domin jin ƙarin bayani. Bayan ta zayyane masa
komai ya nisa, ya ce, “Yanzu ina shi Jamilun yake?”
“Gaskiya ban san inda yake ba a halin yanzu.”
“To
ki kira shi a waya ki ce ina son ganin sa. Ki yi haƙuri kin ji, in sha Allahu
komai zai daidaita.”
“To
Baba na gode sosai, Allah ya ja da rai.”
A ɓangaren su Muttaƙa
da Jamilu kuma, wani wajen suka samu da ba shi da hayaniya suka zauna, sai
hirar yaushe rabo ta ɓarke a tsakaninsu. Sosai Muttaƙa ya tausaya wa Jamilu
halin da yake ciki, kuma ya yi masa alƙawarin taimaka masa da dukkan ƙarfinsa.
“Ina ga ya kamata mu je mu fara kai mama asibiti yanzu kafin mu tunkari sauran
matsalolin.”
“Haka
ne Muttaƙa, na gode!”
Ko da suka je ƙofar gidan su Jamilu, abin da
suka gani ya gigita tunaninsu, ji ya yi kansa yana juyawa, addu'a ya hau yi
Allah ya sa mafarki yake yi ba da gaske ba ne. Wasu zafafan hawaye ne suke bin kuncinsa lokacin da
ya tabbatar da abin da yake gani ba mafarki ba ne.
“Wai
har sai yaushe rashin abin yi zai daina zama barazana ga farin cikina da na
ahalina?”
Tambayar da yake yi wa kansa ke nan amma ya
kasa samun amsarta.
Mahaifiyarsa
ce da ƙannensa a waje tare da kayansu ana wurgi da su, duk magiyar da suka
rinƙa yi masa bai sa ya saurare su ba, haka ya saka yaransa suna fatali da
kayan buƙatunsu. Ba Jamilu da jininsa ne aka yi wa wannan wulaƙanci ba, har
Muttaƙa da wasu maƙwabta sai da abin ya taɓa musu zuciya.
“Jamilu
ka daina kuka, Allah shi ne gatan bawa, sanya su mama a mota, da yardar Allah komai zai wuce…
Kai kuma ka jira ƙarshenka, idan tozarci abu ne mai kyau za ka gani.” Muttaƙa
ya furta yana kallon Alhaji Idi da ya sa ake watsi da kayan mutane.
A hasale Muttaƙa ya
fizgi mota kamar mai shirin tashi sama, bai tsaya ko'ina ba sai asibiti, saboda
sanadiyyar wannan abin ciwon Mama ya tashi sosai.
Baban Rabi sun zauna da Jamilu inda ya tambaye shi ina matsalar take. Ya sanar da shi komai
da ya faru, har da matsalar Mamarsa da korarta da aka yi ita ma. Ya tausaya
masa ƙwarai ya kuma ƙara da yi masa nasiha.
“Lallai mutum ba ya guje wa ƙaddararsa. Duk kuma abin da ka ga ya sami bawa, da
sanin Allah. Ka ƙara haƙuri ka gode masa a bisa ni'imar rai da lafiyar da ya ba
ka. Wata rana sai labari.”
Daga bisani ya yi masa
kyautar naira dubu ɗari tare da yi masa alƙawarin zai taimaka masa ya sami
aiki. Domin ya fahimci
babu wani abu da ya kai rashin abin yi tagayyara ɗan Adam. Godiya sosai ya yi
masa yana jin wani nauyin da ke saman kansa na ƙara raguwa.
Jamilu ya yi amfani da kuɗin da baban Rabi ya
ba shi ya je ya gyara wa Alhaji Sani keke napep ɗinsa game da kai masa abinsa
har gida, kamar yadda ya yi alƙawari. Sauran canjin kuma ya kama wa mahaifiyarsa hayar wani ɗan ƙaramin gida.
Muttaƙa
ya yi iya ƙokarinsa wajen nema wa Jamilu aiki a kamfanin babansa (Kamfanin gina
hanyoyi da magudanan ruwa). Kasancewar Muttaƙa abokinsa ne sai aka ba Jamilu
jami'i mai duba ayyuka, saboda a makaranta fannin gine-gine ya karanta. Haka
zalika ya mai da Jamilu mutum, wanda zai tsaya a kan ƙafafuwansa ba sai ya
dogara ga abin wani ba, sannan Baban Muttaƙa ya yi alƙawarin zai gyara wa
Jamilu gidan gadonsu da ya rushe. Wannan labarin sai ya ƙara zame wa Jamilu
kamar samuwar ruwa a sahara ne, ya rasa bakin da zai yi godiya, sai hawayen
farin ciki da ke sauka a kan fuskarsa.
“Haƙiƙa
kowa ya ce ƙaƙa-naka-yi, ya manta da Allah ne.”
Wannan azancin na Hausawa ya faɗo ransa.
Wataƙila a baya wahalhalun rayuwa sun mantar da shi Allah zai iya kawo masa
ƙarshen wahalarsa.
Astagfurillah! ya yi ta
nanatawa a bakinsa.
Ƙarfe tara daidai na safe Muttaƙa ne zaune a
ofis ɗinsa yana duba wasu takardu.
“Assalamu alaikum!”
“Wa'alaikas salam!” Muttaƙa ya amsa fuskarsa ɗauke
da murmushi. Sai da ya zauna kafin ya mai da dubansa ga amininsa, ya ce, “Ga
ni… sakatariyarka ta ce kana nemana.” Jamilu ya furta.
“Da ma mun yi magana da manajan bankin ba da lamunin mallakar muhalli (FMBN),
kasancewar kamfaninmu yana da rajista da su, ta yadda duk ma'aikatanmu za su
iya buɗe asusu a bankin. To yanzu na yi masa bayanin komai, don haka za mu tafi
can domin samun ƙarin bayani, daga nan sai mu ga yadda ya kamata a yi, don a
yanzu ba ni da wani buri da ya wuce na ga ka mallaki muhalli, Jamilu.”
Bai san lokacin da hawayen farin ciki suka zo
masa ba. “Haƙiƙa kai aboki ne nagari wanda kowa ke fatan samu a duniyarsa, ba
ni da isassun kalmomin yi maka godiya, sai dai ina yi maka fatan gamawa da
duniya lafiya.” Ya ƙarasa zancen yana goge hawayen fuskarsa.
“Haba daina mana, ba na so… yanzu tashi mu je
bankin.” Muttaƙa ya furta daidai lokacin da yake rufe fayil ɗin da ke hannunsa.
Kai tsaye bankin suka nufa, sosai manajan ya
yi musu tarba mai kyau. Bayan sun zauna a
ofis, Muttaƙa ya kalle shi ya ce, “Yauwa! Ahmad wannan abokina ne kuma
ma'aikacinmu ne, shi ma yana son ya ci gajiyar wannan bankin naku don ya
mallaki gidan kansa.” Ya ƙarasa zancen da murmushi kwance a fuskarsa.
“Masha
Allah! Muttaƙa na fahimta. Yanzu fom za mu ba shi ya cike… amma shekararsa nawa
da fara aiki?”
“Gaskiya
bai jima ba, cikin wata na biyu kawai yake.”
“Alal
haƙiƙa sai ma'aikaci ya yi wata shidda da fara aiki zai iya samun bashin kuɗi
ko gida. Don haka a shawarce ku bari idan ya cika wata shidda sai ku zo a yi
duk abin da ya kamata.”
“To
babu damuwa, godiya muke ƙwarai… Allah ya kai mu.” Muttaƙa ya faɗa game da
miƙewa tsaye. Sallama suka yi kana suka wuce.
A
mota Muttaƙa ya mai da dubansa ga Jamilu, ya ce, “Ina ga tun da abin ya kasance
haka sai a nema maka hayar wani gida ka zauna kai da iyalinka, don bai kamata a
ce ta yi wata da watanni a gidansu ba.”
“Kamar
ka shiga raina wallahi Muttaƙa, abin da nake tunani ke nan.”
Hakan
kuwa aka yi, bayan an kama gidan, Rabi da yaranta suka koma. Jamilu ya mai da
hankalinsa sosai a kan aikinsa. Ɓangaren mama kuwa jiki yana ta yin kyau, ciwo kamar
ba a yi ba.
BAYAN WATA BIYAR
Zaune
yake a kan kujerar zaman mutum biyu, sai kalle-kalle yake a falon. Ta yi kusan
minti biyu a tsaye tana kallonsa, murmushi kwance a kan fuskarta, ta furta,
“Abban Afnan wannan kalle-kallen na mene ne?”
Sai
da ya nisa tare da janyo ta jikinsa kafin ya ce, “Wallahi har yau mamaki nake
wai idan da rabo gidan nan zai zama mallakata, duk da a yanzu bai tabbata nawa
ba tun da ban gama biyan ba, amma wata nutsuwa da kwanciyar hankali nake ji
idan na tuna babu wanda zai tayar mini da hankali da sunan na biya kuɗin haya. Kai madalla da wannan
banki mai yin lamuni ga jama’a don mallakar muhalli. Haƙiƙa ba ƙaramin taimako
suke yi wa al'umma ba. Ga shi kuma baban su Muttaƙa ya gyara mana gidanmu na
gado har su Mama sun koma. Tabbas aikin yi da muhalli suna daga cikin jin daɗin
rayuwar ɗan Adam, haka zalika rashinsu zai zame wa mutum ALAƘAƘAI a rayuwarsa
da duniyarsa baki ɗaya. Babu abin da zance da mutane uku, wato mahaifinki,
Muttaƙa shi da mahaifinsa, sai fatan Allah ya saka masu da gidan aljanna.” Ya
ƙarasa zancen yana jin wani farin ciki tun daga ƙasan ruhi da zuciyarsa. Tabbas
mahuƙurci, mawadaci ne!
AlhamdulilLahi!
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.