Ticker

6/recent/ticker-posts

Awon Igiya

Hafiz Adamu Koza (2020). Awon Igiya. Muhalli, Sutura (Labaran Da Suka Samu Nasara a Gasar Gajerun Labarai a Kan Muhalli Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2020). Darma Digital Prints.

AWON IGIYA!

Na

Hafiz Adamu Koza

Shekarar 2019.

 Kana shiga ofishin wani makeken hoto da ke sagale a jikin bango ne zai marabace ka. Su biyu ne a cikin hoton; wani matashi da ke tsakanin shekaru talatin zuwa talatin da biyar ne ya ɗan rusuna yana gaisawa da babban daraktan Bankin Ba Da Lamunin Mallakar Muhalli na Tarayyar Nijeriya, Arc Ahmad Musa Ɗangiwa. Daga gefe kuma kalanda ce mallakar kamfanin gina gidaje mai suna Jarlo International Limited. A kusa da kalandar akwai wani faffaɗan kambun karramawa na shi wannan kamfanin dai, wanda a jikinsa sunan Engr. Mahmood A. Sadiƙ shi ya fi kowanne rubutu haskawa.

 A kan kujera wadda ke kallon ƙofar ofishin, matashin da ke jikin hoton ne a zaune ya ƙura wa sikirin ɗin komfutar kan teburin da ke gabansa ido. Teburi ne mai faɗi da tsawo cike da tarkace na daga fayiloli da sauran abubuwa masu alaƙa da gine-gine. A hankali ya rausaya kansa baya tare da jingina shi da matashin kan kujerar, ya ɗauko fensiri ya riƙe yana jujjuyawa. A take zuciyarsa ta ɗauke shi zuwa shekarun baya, majigin rayuwarsa ya rinƙa zuguruftu a cikin kansa. Ya tuna shekarar 2006 wadda ta kasance mafi muni a rayuwarsa da ta ahalinsa.

Shekarar 1992.

 “Kama ka ja kar ka tsaya sai ka je ƙarshen iyaka... Ƙetare shegiyar ƙoramar can, cike ta zan yi.”

 “Ni fa aikin gwamnati nake yi amma kana ba ni umarni.”

 “Gwamnatin da sai bayan kwana talatin take baka abin da ba zai ishe ka kuskurar baki ba... tsakani ga Allah yaushe rabon da ka ci naman kaza?”

 “Wannan sirri na ne, ko ban ci kaza ba ai ina cin dafaffen wake; likita ya ce amfanin su ɗaya da nama.” Kafin ya ba da wannan amsar sai da ya riƙe gefen igiyar ya fara tafiya inda Alhaji Sade ya umarce shi da ya nufa. Yana tafiya zuciyarsa na tunanin maganar da Alhaji Sade ya yi.

 “... Gwamnati sai bayan kwana talatin take ba ka abin da ba zai ishe ka kuskurar baki ba...”

Ya ayyana a ransa lallai haka ne.

 “To amma akwai cuwa-cuwa ta yau da kullum, kamar dai wannan da nake yi a gonar Alhaji Sade, ko banza na sami wata ‘yar dubu uku zuwa huɗu... ba domin aikin gwamnatin ba, na san matsolon mutum irin wannan da ko mafarkinsa ba ya son a ƙaru da shi ba zai ba ni ƙarfanfanarsa ba... kodayake na san hakan da nake yi ba daidai ba ne...”

Yana zancen zucin ne ya ji muryar Alhaji Sade yana ba shi wani umarnin,

 “Nan ya yi... Ƙarshen iyaka na ce maka ai.” Ya ja ya tsaya, yana jiran umarni na gaba.

 “Oga Bala lokacin damina Baba yake ce mana ruwa ba a tarye mishi hanya, yau kuma ya ce a ja igiya a ƙetare ƙorama... sabon gida fa za a yi mana a nan mu dawo mu duka, wai inda muke ya yi matsatsi.”

Tun kafin ya ƙarasa zancensa, Oga Bala yake kallon sa ƙuri da ido.

 “Yaro ni ƙwararren ɗan safiyo ne kuma jami’in gwamnatin ƙaramar hukuma, amma ka ga yadda babanka, Alhaji Sade, yake bautar da ni saboda kawai ina son in rayu cikin jin daɗi... gidaje da dama a ƙaramar hukumar nan ni na auna su, kuma irin wannan awon na igiya da kake gani shi ɗin ne dai... idan na ƙi yin biyayya babu mai sake neman inda nake, hanyoyina na samu za su toshe in koma bara, ka ga kuwa ina amfanin baɗi ba rai...! Wai kai yaro mene ne sunanka?!”

A maimakon ya yi wa yaron sahihin jawabi wanda ya jiɓanci maganar da ya yi, mutumin da ke amsa sunan Oga Bala ya waske ya nufi wata maganar daban, a ƙarshe kuma ya ɓige da tambayar sunan yaro. Kafin ya ba da amsa, daga nesa Alhaji Sade ya ƙwalla kira,

 “Kai Mamuda zo nan ka riƙe mini wannan gefen in zo nan in ga yadda awon zai kama.”

Amsar Oga Bala ta samu, shi kuma Mamuda, yaro ɗan kimanin shekaru goma sha ɗaya, ya ruga da gudu ya nufi inda Alhaji Sade yake, ya bar Oga Bala da igiyar awon fili sototo.

 Bayan sun gama shata shandamemen filin da Alhaji Sade ya ƙuduri aniyar ginawa domin iyalinsa baki ɗaya su dawo da zama, sai kuma ya kira magini tare da zana mishi taswirar yadda yake so gidan ya kasance. Matansa uku, kowacce an kurta inda za a yi mata tafkeken ɗaki ciki-da-falo, duka ɗakunan an jere su daga gabashin gidan suna kallon yamma; ya ce uwargidansa za ta kama ɗakin da ke arewa, amarya kuma ta zauna a ɗakin da ke ƙarshen kudu, ta biyu kuwa a tsakiyarsu. Daga sukurwar kudu, inda aka ƙetare ƙorama, turakarsa zai gina a wurin, wadda zai yi wa shamaki domin asirtawa. Ya tsara ɗakuna guda biyu a ɓangaren arewacin gidan waɗanda za su kalli kudu, su kuma na yara ne; mata da maza kowanne jinsi da nasu. Yaranshi za su kai goma sha tara, mata sun fi maza yawa. Ɗansa na farko, Ibrahim (Iro), shi ma magidanci ne da yaransa huɗu. Mamuda yana daga cikin ƙananan ɗiyan Alhaji Sade, masu irin shekarunsa da ke rayuwa a gidan ne aka tanadar wa ɗakunan can guda biyu.

 Daga yammacin gidan ya shata wani fili ƙarami wanda za a yi banɗaki, yana kallon inda turakarsa take, a nan duk mazauna gidan za su rinƙa biyan buƙatunsu na larura. A tsarin Alhaji Sade, yin gwadala a gida ɓata lokaci ne da kuma almubazzaranci, amma dai ya tsara za a yi tanƙamemiyar rumfar kara a tsakar gida domin sararawa a lokacin bazara.

 Duk wannan tsari bai ɗauki tsawon lokaci ba aka kammala shi, kwanaki sittin da biyar kacal da farawa, yanzu ga shi har ana kwaramniyar tarewa. Alhaji Sade ya yanka filaye guda biyu ya ba ɗiyansa Ibrahim da Ɗanjuma, wanda zai yi wa biki kwanakin nan, su ma za su ja nasu ginin, yana son su kasance kamar da, zaman gandu.

 Ba su fi shekara ɗaya da tarewa ba mutane suka fara zuwa ana shata musu fili, da taimakon Oga Bala, suna saye su gina a matsayin muhalli. A irin wannan awo na igiya an sha samun cukumurɗa, a yi ta dambarwa saboda wani zai fara gini, sai kuma ga wani ya zo ya ce filinsa ne. Da ƙyar ake shawo kan rikicin. Alhaji Sade ya sha kwaramniya daga caji-ofis har gaban kuliya, a matsayinsa na wanda ya mallaki gonar da ake yankawa. A dafa a daga sai kalwa! A haka a haka dai cikin ƙanƙanen lokaci sai ga wuri ya fara bunƙasa, aka laƙaba wa unguwar sunan Sabon Fegi.

Shekarar 2006.

Ƙidayar kwanaki da makwanni da watanni da shekaru suna shuɗewa, unguwar Sabon Fegi a yau tana daga cikin unguwanni na gaba-gaba wajen rashin tsari da tsabta a lardin Kundumawa, hakan ya kasance ne sakamakon gidajen da aka gina a tsakanin shekaru goma sha huɗu zuwa wannan lokaci duk “Awon Igiya” ne. Kowace shekarar duniya suna fuskantar ambaliyar ruwa, kasancewar babbar ƙoramar nan da ta ratsa tsakiyar unguwar ita ma a cikin waɗannan shekaru ta ƙara zagwanyewa, ta fafare har ta haifi ‘ya’ya da jikoki da tattaɓa-kunne da ihihin! A wannan shekarar, cikin ɗumbin gidajen da ambaliyar ta rutsa da su har da na Alhaji Sade. Ruwan da aka tafka kamar da bakin ƙwarya ya yi tafiyar yaji da gidansa, ba gida kaɗai ba, hatta shi kansa a wannan ruwa ne ya cim ma ajalinsa.

 Mamuda, wanda a yanzu yana shekarar farko a karatunsa na NCE a Kwalejin Ilmi Ta Tarayya da ke birnin Katsina ya sami labarin mummunar ɓarnar da wannan ambaliya ta yi, kodayake an ɓoye mishi rasuwar mahaifin nasa, sai dai an ce ya garzayo gida domin ganin irin ta’adin da aka yi. Yana isowa garin ya iske mummunan labarin da ke nuna har kawo yanzu, kwana guda da wuni ana cigiyar gawar mahaifinsa da ta bi igiyar ruwa zuwa madatsar ruwa mai nisan kilomita huɗu daga inda suke.

… ƙetare shegiyar ƙoramar can, cike ta zan yi.

Muryar mahaifinsa ta yi zarya a cikin ƙwaƙwalwarsa a lokacin da yake ba Oga Bala umarni da suna shata filin gidan shekaru goma sha huɗu da suka gabata. Ya sake tuna firarsu shi da Oga Bala game da wannan ƙorama wadda a yau ta raba shi da mahaifinsa, gudan jininsa. Bai san lokacin da ya zube ƙasa ba yana hawayen takaicin abin da ya faru. Daga wancan lokacin zuwa yau duk shekara suna fama da ambaliyar ruwa, ga cututtuka da ke yi musu kisan mummuƙe ba tare da ƙiyasin waɗanda ake rasawa ba a kowace shekara.

Ya waiga ko’ina babu abinda yake gani sai ramukan ruwa da rusassun gidaje; mutane na rayuwa a fili babu suturar muhalli. Wayewarsa ta fara ɗarsa mishi tunanin babu mai laifi a wannan sabga sai gwamnati, domin kuwa an ce kai da kaya duk mallakar wuya ne. A ɗaya gefen kuma ya tuna boren da ‘yan unguwar suka yi a shekarar 2004, wai masu mulki suna takura musu da mitar unguwarsu ba ta da tsari, har ma wasu da ke unguwar a lokacin suna iƙirarin duk wanda ya sake takura musu, to a zaɓukan 2007 ba shi za su yi ba! Cikin gidajen da ruwa ya kacaccala har da na jagoran wancan bore da aka yi a 2004, yanzu kam ta tabbata cewar ba shi da nutsuwar da zai je rumfar zaɓe a shekara mai kamawa, tun da zai fara fafutukar sake muhalli.

 Lallai muhalli falala ne, muhalli arziƙi ne, muhalli shi ne ni’ima da jin daɗin rayuwa. Duk wanda ya mallaki nasa a taya shi murna, masu lalube kam a taya su da jaje! Ya tuna da wasu kalaman hikima da masanan falsafa, Winston Churchil da Socrates, suka yi game da muhalli;

“Idan muka tsara muhallinmu, shi kuma zai inganta mu!”

“Dubara mafi ƙololuwa da ake muradi tana cikin tsarawa da ƙayata muhalli.”

Da tunanin waɗannan kalamai ne Mamuda ya sha alwashin kawo sauyi a yadda ake tsara gidaje da unguwanni, tun daga matakin unguwarsu har jiharsa zuwa qasa baki ɗaya idan ya sami iko. Daga wannan lokaci ne fafutukarsa ta fara.

***** *****

 Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah, sannan an ce mahaƙurci mawadaci. Nema da noma da sa’a sun taimaka wa Mamuda ƙwarai a karatunsa da rayuwarsa. Tun bayan rasuwar mahaifinsu ya fuskanci cewar idan ba ya yi da gaske ba to karatunsa zai yanke, don haka ya fara hada-hadar kasuwanci a Kwalejin da yake karatu. Da farko ‘yar ƙaramar komfuta ya nema ya kuma je wurin wani daga cikin masu sana’ar ɗab’i a makarantar ya bayyana mishi halin da ya tsinci kansa, sannan ya buƙaci da ya ba shi dama duk lokacin da ba su da lakca ya rinƙa zuwa wurinsa yana koyon sana’a. Haka kuwa aka yi, da yake Mamuda haziƙi ne ba ta fannin karatu kawai ba, cikin ƙanƙanen lokaci ya sami karɓuwa wurin ubangidansa, domin yana da gaskiya ga kuma aiki tuƙuru. Mamuda bai biye wa sharholiyar ɗalibai takwarorinsa ba, duk abinda yake samu sai ya rinƙa aika wani kaso gida ana yi mishi noman rani; a shekarar ya noma kabeji mai yawan gaske. Kuɗin kabejin ya harhaɗa da wasu tanadinsa ya shiga fafutukar samun izinin buɗe shago na kansa a cikin Kwaleji. Ya yi sa’a kuwa aka ba shi dama. Da wannan sana’a ya ɗauki nauyin karatunsa na NCE kaf har ya gama.

 Ya san cewa zama zaunewa ne, yana kammalawa ya nemi gurbin karatu a Jami’ar Bayero Kano, inda suka ba shi damar karatu a fannin Injiniyan Muhalli (Bsc. Civil Engineering). Maƙasudin neman wannan karatu saboda ya cika burinsa na alwashin kawo sauyi a tsarin muhalli, musamman a unguwarsa wadda ana kallo ta zama tarkon mutuwa da asara ba tare da kulawa ba. Shagonsa na Kwaleji da wani makamancinsa da ya sake buɗewa a cikin garin Katsina suna taimakonsa ainun ga karatunsa, domin waɗanda ya ba amanar tafiyar da wuraren sun haifu!

 Tafiya sannu-sannu kwana nesa. Mamuda ya kammala karatunsa ya yi hidimar ƙasa ya amshi sakamako ya dawo garinsa da zama. Maimakon ya bazama neman aiki, sai ya saje da mazauna wurin ya fara noma da nema. Tsawon shekara guda yana ta tsare-tsaren matakan da zai bi wajen kawo gagarumin sauyi da ba a cika samun irinsa ba, yana ƙudurta cewa abinda ke ransa idan aka yi sa’a ya cim ma nasara, to zai zama tamkar ruwan dare mai game duniya. Shi dai ya aminta cewar shirin zaune ya fi na tsaye, don haka yake bin lamarin da taka-tsan-tsan, babu garaje, domin hau ne! A zaman shekarar da ya shuɗe cikin al’ummarsa ya yi nasarar sauya tunanin mutane da dama sun fara gane irin halin da rashin tsarin muhallinsu yake jefa su a ciki. Mafi akasarin waɗanda suka fahimce shi to matasa ne abokansa, domin bai yarda karatunsa ya yi masa shamaki da su ba; ya shige su ƙwarai ya kuma ci ribar janyo su a jikinsa. A yadda ya ɗarsa a ransa, tun da har aka ce matasa su ne ƙashin bayan al’umma, to fafutukarsa na buƙatarsu.

 Yunƙuri na farko da ya yi shi ne kafa ƙungiyar taimakon kai-da-kai wacce ta haɗa kowane rukuni na mutane, saboda an ce haɗin kai shi ne ƙarfi. Bai yarda ya zama shugaban gamayyar ba, sai dai a bayan fage shi ke tsara komai, wannan wata hikima ce da ya bar wa kansa sani. Ƙungiyar ta fara da ƙananan ayyukan sa-kai, inda suka rinƙa haƙo ƙasa daga wuri mai nisa suna ciccike ramukan da ruwa ya yi a tsakiyar gine-ginensu. Ya sani wannan ba zai yi magani ba, amma an ce gani ya kori ji, kuma jiki magayi ne. Idan ya ce musu aikin Baban Giwa suke yi ba za su yarda ba a yanzu, amma da zarar damina ta kama za su gani da kansu. Haka kuwa aka yi, damina tana kawo jiki, ruwa ya fara yawa, sai ga sababbin hanyoyin ruwa suna samuwa, inda ya rinƙa rarake wasu wuraren daban da inda aka yi mishi shinge. Hakan ya ta’azzara ambaliyar, domin ruwan ya rinƙa bi ta gefen ginin gidajensu. Rusau kuwa sai a yi shiru a wannan shekarar!

Amma cikin ikon Allah ba a sami asarar rayuka ba, domin tuni Mamuda ya yi shirin ko-ta-kwana ta yadda ambaliyar na farawa duk mazauna wuraren da aka tsammaci gininsu zai rushe suka koma gidajen yan uwa da abokan arzuƙa. Wannan shi ya nuna a fili mutanen unguwar Sabon Fegi sun amsa kiran taimakon junansu ba tare da jiran kowa ba.

 Wanka ƙarin kyau! Mamuda ya jagoranci wasu daga matasan unguwar suka kai kuka ga gwamnati da Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Nijeriya (NEMA) domin a kawo musu ɗauki. Cikin sauri kuwa kiran ya sami karɓuwa, gwamnati ta shigo, hukumomi suka garzayo. Faruwar hakan babbar nasara ce ga fafutukar da Mamuda ya ƙudurta.

***** *****

 Jajircewar da Mamuda ya nuna a wannan ambaliyar ruwa da ta zo da sabon salo a wannan shekarar ta janyo masa kwarjini da ƙima a idon mutanen unguwarsa har ma da hukumomin can da suka kawo musu ɗauki. Wasu daga hukumomin sun yi mishi tayin tafiya tare domin ayyukan jin-ƙai. Sannu a hankali himmarsa ta rinqa bayyana shi, duk wani muhimmin aiki idan ya taso a kowace hukuma da ya shiga sai ya nuna hazaƙa ta gani a yaba!

 Tunaninsa ya ba shi cewar har yanzu shi matashi ne, yana da sauran damarmaki a tsaye, don haka a cikin wannan yanayi ya nemi ci gaba da karatun digiri na biyu, inda ya jona da karatunsa na Civil Engineering da ya faro. Yana kammalawa sakamakonsa ya fito mai kyau, da ma tun gama digirinsa na farko ya shiga cikin Ƙungiyar Injiniyoyin Nijeriya, wato ‘Nigerian Society of Engineers’ a matsayin ‘member’, don haka sai ya rubuta takardun neman aiki zuwa ga kamfanoni da ofisoshin gwamnati masu alaƙa da tsarin muhalli da gine-gine. A cikin wurare biyar da ya aika buƙatarsa, kamfanoni guda biyu sun kiraye shi domin tantancewa, inda ya sami nasarar samun cike gurbi a matsayin ƙaramin ofisa a kamfanin gine-gine na Jarlo International Limited.

 Cikin ƙanƙanen lokaci likkafarsa ta rinƙa yin gaba, muƙaminsa ya rinƙa hauhawa a kamfanin Jarlo Intl. Ltd kamar yadda fulawar fanke take hawa. Rayuwarsa tana ba shi mamaki idan ya zauna yana tunani, yanzu ya tashi daga Mamuda Alhaji Sade ya koma Injiniya Mahmood A. Sadiq, lallai rayuwa birgimar hankaka ce, baƙi da fari.

 Yanzu da ya kammala gina kansa, sai ya dawo kan batun gina al’ummarsa afujajan. Hankalinsa kacokan ya koma kan yadda zai kawo ma rayuwar abokansa, ‘yan uwansa, wato mazauna unguwar Sabon Fegi ɗauki. Ya san asalin matsalar, a da mafarkin magance ta yake yi, yanzu kuma ya sami damar taka rawa domin tabbatar mafarkin a zahiri. Ƙungiyar taimakon kai-da-kai wadda ya kafa tun a shekarun baya ta zame mishi fandeshan na ɗora tubalin gyara matsalolin al’ummarsa.

 A ƙarshen shekarar 2018 kamfaninsu na Jarlo Intl. Ltd ya yi gangami domin karrama muhimman mutane da suke taka rawar gani wajen tallafawa da taimakon al’umma, cikin waɗanda aka ba kambun har da Eng. Mahmood A. Sadiƙ. An kwarzanta shi a matsayin matashi mai kishin al’umma da ƙoƙarin kawo sauyi a rayuwarsu. Wannan ya ba shi ƙwarin gwiwa ya ƙuduri aniyar aiwatar da wani babban motsi a farkon sabuwar shekarar 2019 domin tabbatar da matsayinsa na yadda aka zace shi.

Shekarar 2019.

 Da sauri ya ɗauke idonsa daga kan komfutar, ya ɗauko wata takardar zane-zane da fensiri da rula, ya fara jan layuka; cikin ƙanƙanen lokaci sai ga taswirar wata ‘yar ƙaramar tsararriyar unguwa ta bayyana a kan takardar. Ya ɗaga ta sama daidai idonsa ya yi murmushi, sannan ya naɗe ta ya miƙe tsaye ya nufi bakin ƙofar fita daga ofishin.

 Yana fita bai zame ko’ina ba sai wurin wani abokinsa da ya karanci zanen taswirar gidaje (architecture). Nan suka zauna ya fayyace mishi ƙudurinsa, sannan ya miƙa mishi taswirar unguwar da ya tsara domin gyara da shawarwari, sun rabu a cewar bayan kwanaki uku za su sake haɗuwa su tattauna.

 A cikin kwanaki ukun Injiniya Mahmood ya kammala duk wani shiri da tsare-tsaren cim ma manufar ƙudurinsa. Ranar da ya koma suka cinye tsawon wuni guda suna tattaunawa shi da abokin nashi. A ƙarshe suka tsayar da shawarar kiran taro na baki ɗayan mutanen unguwar Sabon Fegi, da sunan ƙungiyarsu ta taimakon kai-da-kai.

***** *****

 Mahalarta taron da ya iske tun gabanin zuwansa sun ƙarfafa shi, domin ya ga fuskokin manyan mutane magidanta, har da aminan mahaifinsa. Hakan ya sa ƙwalla ta cika mishi ido, ya so a ce mahaifinsa na daga cikin waɗanda za su shaida wannan aiki nashi.

 Bayan addu’ar buɗe taro Injiniya Mahmood ya miƙe tsaye cike da karsashi ya fara jefo wasu tambayoyi kai tsaye yana nuna waɗansu mutane a matsayin waɗanda za su ba shi amsa. Mutum na farko Limamin da ke jan salla a unguwar Sabon Fegi ya tambaya.

 “Gafarta Malam ya muka ji da rayuwa... Ina fatar ana ta yi wa ƙasa addu’a?” Malam ya amsa da, “Eh, ana yi Mamuda.”

 “To madalla! Allah ya amsa.” Ya waiwayi wani magidanci da ke can kusurwa a maƙale.

 “Malam Murtala bana wane shiri ka yi wa ambaliyar ruwa?”

 “Na bar wa Allah ikonsa. Yanzu ta abinci nake yi. Birkin masara ya tsinke...” Aka ɗan yi raha kafin Injiniya Mahmood ya sake kallon wani mutum mai kwarjini da alamun wadata ya ce da shi,

 “Alhaji na san Hajjin bana da ku za a sake yin ta, Allah dai ya amsa ibada...” Ya ɗan yi murmushin kulawa sannan ya ci gaba.

 “Irinku masu gidan Mahadi-ka-ture ai na san ruwa ba zai shafi gidajenku ba.”

 “Haba Mahmood! Abinda ya ci Doma ai ba zai bar Awai ba. ‘Yan uwana da abokaina suna cikin tashin hankali Wallahi ko barci da ƙyar nake yi. Da ina da iko, duk unguwar nan sai na yi musu gini irin nawa, ko ma fiye!”

Har cikin ransa ya ji daɗin wannan jawabi, ya kuma ba shi damar bayyana musu abinda ya zo musu da shi. Ya gyara tsayuwar farin gilashinsa, ya cije leɓe, ya fara magana da cewar,

 “Na farko dai ya kamata mu sani ambaliyar ruwa ba ta da magani a yanzu, saboda sabubbanta ba masu yankewa ba ne, kodayake haka, ana iya guje mata. Kafin mu kawo ga batun guje mata ɗin, bari mu fahimci sabubban da ake tsammanin suna janyo ta. Masana sun ce sauyin yanayi yana taka rawa wajen yawaitar ambaliyar ruwa. Shi wannan sauyin yanayi yana addabar duniya baki ɗaya. Mun kwana da sanin cewa yadda ake samun ruwa a yankunanmu yana sauyawa, wato ruwa na zuwa a makare ya kuma ɗauke da wuri. Shi kuma ruwan a kan kansa adadinsa ya ƙaru. A sauƙaƙe za mu ce lokutan samun ruwa sun ragu, ruwa ya ƙaru. Me zai faru? Amsar ita ce ambaliyar ruwa. Abu na biyu kuma shi ne ɗumamar yanayi.

Wannan ɗumamar yanayin tana haifar da zafi ga duniyarmu, sanadin haka sai tarin ruwan da ke cikin tsaunuka ya narke ya malalo cikin balbalin duniya har ya riski koguna da rafuka. Su kuma da sun tumbatsa sai su fashe su antaya cikin muhallan duk da suka raɓe su, daga wannan lokaci sai a yi ta tsitsitsi ɗin neman agaji; ruwa ya ɓalle! Misalin irin haka ga tsaunukan Futa-jalon nan da ɗumamar yanayi ke narkar da ruwan cikinsu. Abu na uku shi ne irin yadda muke gine-ginenmu babu tsari! ‘Yar kafar da za a bar wa ruwa ya wuce kowa ƙyashinta yake yi, shi kuma ruwa babu wanda zai tsare shi daga zuwa inda ya dumfara, don haka sai ya rinƙa shiga inda ba mu so.” Ya ɗan numfasa tare da kallon yanayin yadda mahalartan ke sauraronsa.

 “Kamar yadda na ce samuwar ambaliyar ruwa ba ta da magani, sai dai guje wa ta’adinta ba zai gagare mu ba. Misali ina da gida kusa da ƙorama, na tabbata ana yin mamakon ruwan sama, to a ruwa nake! Idan kuma na ɗan muskuɗa na bar wa ruwan hanyarsa kuna ganin zai bi ni har inda nake? Amsar ita ce a’a! Bahaushe ya ce wanda ya ja ruwa, shi ruwa ke duka. Ba tare da saƙar kwando ba, ina son in yi wa al’ummata tayin wani babban al’amari wanda kafin a fahimci alfanunsa sai an zurfafa tunani an kuma ɗauki rayuwa an koma da ita baya ana tuno irin wahalhalun da muke fuskanta a wannan unguwa ta Sabon Fegi.”

Da ya zo nan a jawabinsa sai ya ɗauko majigin bango da ya tanada, ya harhaɗa komai a nan take ya haska wa mahalarta taron taswirar unguwar da suka tsara shi da abokinsa. Rukunin gidaje ne mai tsari irin na zamani; gidaje ne bungalo masu ƙunshe da ɗakuna biyu, wasu kuma uku. An fitar da hanyoyin ababen hawa da na magudanan ruwa da turakun lantarki, a tsakiyar unguwar an yi wata ‘yar ƙaramar kasuwa da rumfuna jejjere. Majigin ya nuna hatta yadda hada-hadar kasuwanci ke gudana a tsakanin jama’ar wurin. A can gefe kuma ga wani ɗan fili an ware inda aka haska yadda yara ke wasanni cikin nishaɗi. Unguwar ta tsaru kai ka ce a birnin Paris kake.

 Bayan Injiniya Mahmood ya gama nuna wannan majigi ne sai ya yi wa al’ummar da ke wurin bayanin cewar mafarkinsa shi ne duk ‘yan unguwar Sabon Fegi kowane magidanci ya mallaki ɗaya daga cikin gidajen da ke wannan majigi. Ƙusƙus ta kaure a tsakanin mutanen, shi dai har yanzu yana tsaye, bai karaya ba. Wani mutum mai ruwan gajiyayyu ya miƙe tsaye ya ce,

 “Mamuda kafin yanzu ba mu san cewa ka raina mu ba, amma yau ta fito fili. Ni da ke leburanci ina ciyar da iyalina da ƙyar ko kyauta ka ba ni wancan gidan idan ya ƙara awa ɗaya a wurina to nauyin kasuwa ya yi. Na ji daɗi da ka ce mafarki kake yi, to ka farka...!”

 “Na yi alƙawarin ni da kai za mu fara mallakar gida a wannan rukuni.” Injiniya Mahmood ya katse hanzarin mutumin yana murmushi. Sannan ya ci gaba da magana.

 “An ce zuciyar mutum birninsa. Yadda Malam Isa ya sare wa duniya haka bai kamata mu rayu a haka ba. Mu ne za mu fara taimakon kanmu kafin wani ya shigo daga baya da nufin taimakonmu. Kamar yadda na yi alƙawarin samar wa Malam Isa gida a wancan rukuni idan ya tabbata, wanda kuma na san zai tabbata, to zan cika shi da yardar Allah. Idan mun yi sadaukarwa, mun taimaki juna, mun tuna da wahalar da muke sha a kowace shekara, mun yi mafarkin yankewar ɗawainiyarmu, to shan ruwa ya fi wahala a kan mallakar gida a wannan unguwa da na nuna muku. Abinda nake so ku sani shi ne, akwai wani tsari na Bankin Ba Da Lamunin Mallakar Muhalli na Tarayya mai suna National Cooperative Housing Development Scheme (NHDS).

Wannan tsari yana ba ‘yan ƙungiyoyi damar mallakar muhalli idan sun cika sharuɗɗa, na san mu ma ƙungiyarmu ta sa-kai da muka samar tun tsawon lokaci za ta iya cike sharuɗɗan. Yana daga cikin fannin da na sani kuma nake da ido a kansa, don haka kafin in zo nan sai da na tabbatar cewar ba zai ɗauke mu dogon lokaci ba kafin mu cim ma nasara. Abinda nake buƙata kawai goyon baya daga gare ku.” Ya rausaya kansa kaɗan sannan ya ci gaba.

 “Za mu nemi agaji da tallafi daga hukumomi da gwamnatoci da masu hannu-da-shuni domin samar da wannan unguwa ta yadda abinda za mu sadaukar na aljihunmu ba zai gagare mu ba. Har wa yau, daga cikinmu dole masu ƙarfi su taimaki marassa shi. Misali mun san cewa kamar Malam Isa idan aka ce ya rinƙa ajiye wani abu a cikin Asusun Samar da Gidaje na Ƙasa (NHF) da za mu buɗe nan gaba to zai takura, yana da muhimmanci masu ƙarfi a cikinmu su sadaukar da wani abu daga samunsu domin shiga kafaɗar irin waɗannan mutane. Na sani masu iyali da yawa za su ce shin ina za su kai sauran iyalansu idan aka ce ga gida mai ɗakuna biyu ko uku, to wannan ba zai zama damuwa ba.

Muna iya sake bitar taswirar ni da abokina da sauran masanan da za mu sanyo a sabgar domin ya yi daidai da buƙatar kowa ba tare da an tsauwala ba. A ƙarshe ina mai ƙara tunatar da mu irin wahalhalun da muke sha, don haka ina roƙonmu da mu amshi wannan dama mu yi amfani da ita domin inganta muhallinmu yana daga cikin wajibi a kawunanmu. Ina buƙatar amincewarku kafin in ci gaba da tsare-tsaren yadda za mu samar da wannan unguwa.”

Malam Isa da aka yi wa alƙawari shi ya fara miƙewa, sannu a hankali mahalarta taron suka rinƙa tashi domin mubaya’a. ‘Yan tsiraru ne suka rage a zaune. Da ma Injiniya Mahmood ya kwana da sanin ba zai iya gamsar da kowa ba, adadin ma da ya samu sun ba shi mamaki ƙwarai da gaske.

 Da yake ana farkon shekarar 2019 ne, watanni biyu cur ya shuɗe yana ta kwaramniyar yadda za su cim ma nasara. Ya fuskanci ƙalubale waɗanda a wasu lokutan suna karya mishi gwiwa, amma da ya tuna inda ya faro, sai ya ƙara zage dantse. Ya sani an ce ba a kama zomo daga zaune, don haka yana ɗaukar kowane ƙalubale a matsayin nasara. Farkon abinda ya fara yi shi ne jagorantar buɗe wa kowanne daga cikin waɗanda ke tare da shi asusun ajiya a NHF, inda za su rinƙa ajiye kaso 2.5 na abinda suke samu a kowanne wata. Hakan shi zai ba su damar samun lamuni daga FMBN ba tare da jinkiri ba.

Daga nan kuma sai ya rinƙa tunkarar hukumomin ba da agaji da gwamnatoci da masu hannu-da-shuni yana bayyana musu manufarsa da ƙudurinsa na sauya rayuwar mutanen unguwarsa. Mutane da dama suna ganin kamar tarar aradu ce kawai Injiniya Mahmood yake yi, sai dai a cikin wata na huɗu da fara wannan tsare-tsare nasara sai ƙara kusanto shi take yi.

Kamfanin da yake aiki na Jarlo Intl. Ltd suna ba shi duk wani goyon baya da gudummowa a fafutukar da yake sha. Sun ɗauka cewa aiki ne yake rage musu na yunƙurin da suke yi domin samar wa al’umma muhalli ingantacce. Ta ɓangaren FMBN ma ba ta sauya zane ba, suna taimakonsa da duk wani bayani da ya je nema domin ɗorewar muradinsa.

 Haƙuri mai ci da rabo! A cikin wata na bakwai har sun kammala duk abinda ya dace, an samar da ingantaccen wuri da ya cika dukkanin ƙa’idar da FMBN yake kallo kafin ‘yan ƙungiya su amfana da gina rukunin gidaje na ƙashin kansu. A ɗaya gefen kuma ba a sami gafcewar kuɗaɗen ajiya da kowannensu ke sanyawa a cikin asusun NHF ba, ana taimakon duk wanda aka ga ba zai iya biya a wani wata ba saboda yanayin rayuwa.

 Mafarkin Injiniya Mahmood yana gab da cika, domin har an fara share wuri da taimakon wasu hukumomin agaji da kuma abinda ɗaiɗaikun mutane ke tallafawa da shi.

Shekarar 2020.

 A farkon shekarar 2020 Bankin Ba Da Lamunin Mallakar Muhalli na Tarayya suka amince da buƙatar ƙungiyar su Injiniya Mahmood na bai wa duk ɗan ƙungiyar lamunin kuɗaɗen da zai gina gida a wannan rukunin gidaje mai ƙunshe da gidaje ɗari biyu da goma sha uku. A farkon watan Fabrairu aka aza harsashin gina wannan rukunin gidaje da aka ba sunan Sabon Fegi Estate, kamfanin Jarlo Intl Ltd inda Injiniya Mahmood ke aiki su ne masu gina gidajen.

Aiki ya yi nisa kwatsam sai ga annobar ƙwayar cutar korona ta tsayar da kowace irin harka a duniya. A watan Maris Nijeriya ta shiga jerin ƙasashen da suka hana duk wani motsi, hakan ya sa aikin Sabon Fegi Estate ya tsaya cak. Sai dai yanzu da lamurra suka fara daidaita, a watan Agustan da ya gabata an sake dawowa gadan-gadan ana ci gaba da aiki. Injiniya Mahmood ya sha alwashin a watan Maris na sabuwar shekarar 2021 za a yi bikin buɗe wannan rukunin gidaje wanda aka tsara cewar babban daraktan FMBN, Arch. Ahmad Musa Ɗangiwa zai jagoranta.

Muhalli, Sutura

Post a Comment

0 Comments