Ticker

6/recent/ticker-posts

Kuskuren Dr. Gumi a Mas'alar "Muwalatin" Kafirai

Kamar yadda na faɗa jiya, duk mai bibiyar Dr. Gumi a mas'alolin Addini, ya san akwai mas'aloli da yawa da a kan kuskure yake, ya fahimce su a juye. Saboda manhajinsa na ilmi ba mai kyau ba ne, gurɓatacce ne.

Daga cikin mas'aloli masu hatsari, waɗanda Dr. Gumi ya fahimce su a karkace, ko ka ce: a juye, ya mai da sama ya koma ƙasa, ƙasan kuma ya mai da shi sama (upside down) akwai mas'alar "Muwalatin" kafirai. Wato ƙawance da kafirai da jiɓintarsu da nuna musu soyayya, da taimakonsu.

Alal haƙiƙa Ayoyi masu yawa sun zo suna hana Musulmai yin "Muwalati" ga kafirai, har suka yi hukunci da cewa; duk wanda ya jiɓince su, ya nuna musu soyayayya to shi ma ya shiga cikinsu, ya zama kafiri.

To, kamar kullum a kowace mas'ala, mutane suna rabuwa gida uku;

- Masu tsanani da guluwwi,

- Masu sakaci,

- Ƴan tsakiya, waɗanda suke kan hanya madaidaiciya.

To, masu sakaci su ne masu cewa; "Muwalati" ga kafirai ba shi da wata matsala. Ya halasta mutum musulmi ya ƙaunaci kafirai, ya so su, a sake ba ƙaidi. Waɗannan su ne ƴan Boko Aƙida (ƴan daɗi arna), da kuma Sufaye, masu cewa; kowane mai Addini, wa Allah yake bautawa.

Sai kuma masu guluwwi, waɗanda suke ɗaukar Ayoyin a sake, suke kafirta duk wani mai alaƙa da kafiri. Waɗannan su ne masu guluwwi wajen kafirta Musulmai, daga cikinsu ake samun ƙungiyoyin ta'addanci, masu ɗaukar makami a kan Musulmai.

Wannar mas'ala ta son kafirai, ko mu'amala da kafirai, tana daga cikin manyan shubuhohin ƙungiyoyin ta'addanci, inda suke kafirta Musulmai; shugabannin ƙasashe da talakawansu, saboda alaƙa da Amerka da Turai.

Amma su kuma kashi na uku, su ne waɗanda suka tsaya a tsakiya, suka fahimci Ayoyin bisa yadda Salaf magabata suka fahimce su.

Waɗannan, da suka kalli gamayyar Ayoyin "Muwalati" ga kafirai, kuma suka duba fassarorin Salaf gare su, sai suka samu Salaf suna kasa "Muwalatin" kashi biyu:

Ibnul Jauziy ya ce:

قوله تعالى: { وَمَنْ يَتَوَلَّهُمْ مِنْكُمْ فَإِنَّهُ مِنْهُمْ } فيه قولان:

أحدهما: من يتولهم في الدين، فإنه منهم في الكفر.

والثاني: من يتولهم في العهد فإنه منهم في مخالفة الأمر".

زاد المسير (١/ ٥٥٨)

Ma'ana; "Muwalatin" kafirai nau'i biyu ne cikin maganganun Salaf:

- Akwai na kafirci.

- Akwai kuma na saɓon Allah, wanda bai kai kafirci ba.

Ga bayaninsu kamar haka:

1- Soyayya wa kafirai da jiɓintarsu saboda Addininsu. Wannan shi ne kafirci. Ibnu Jarir ya ce:

القول في تأويل قوله: {لا يَتَّخِذِ الْمُؤْمِنُونَ الْكَافِرِينَ أَوْلِيَاءَ مِنْ دُونِ الْمُؤْمِنِينَ وَمَنْ يَفْعَلْ ذَلِكَ فَلَيْسَ مِنَ اللَّهِ فِي شَيْءٍ إِلا أَنْ تَتَّقُوا مِنْهُمْ تُقَاةً}...

"ومعنى ذلك: لا تتخذوا، أيها المؤمنون، الكفارَ ظهرًا وأنصارًا توالونهم على دينهم".

تفسير الطبري (٦/ ٣١٣)

Sai ya nuna cewa; Ayar tana hani ne a kan "Muwalati" ga kafirai a kan Addininsu.

Sai ya ruwaito:

عن السدي: "لا يتخذ المؤمنون الكافرين" إلى"إلا أن تتقوا منهم تقاة"، أما "أولياء" فيواليهم في دينهم، ويظهرهم على عورة المؤمنين، فمن فعل هذا فهو مشرك".

تفسير الطبري (٦/ ٣١٤)

Daga Suddiy, ya ce:

Amma wanda ya ƙaunaci kafirai, saboda Addininsu, ya tona asirin Muminai, wannan kam Mushriki ne.

Amma idan kafiran su suke da ƙarfi, Musulmai ba su da ƙarfi, to idan sun tilasta wa Musulmi, ko kuma yana jin tsoronsu, saboda su suke da karfi da iko, to a wannan hali mutum ba shi da laifi. Sai ya nuna musu ƙauna da taimako gwargwadon abin da zai ture sharrinsu daga gare shi. Ibnu Jarir ya ruwaito:

عن ابن عباس قوله: "لا يتخذ المؤمنون الكافرين أولياء من دون المؤمنين"، قال: نهى الله سبحانه المؤمنين أن يُلاطفوا الكفار أو يتخذوهم وليجةً من دون المؤمنين، إلا أن يكون الكفارُ عليهم ظاهرين، فيظهرون لهم اللُّطف، ويخالفونهم في الدين".

تفسير الطبري (٦/ ٣١٣)

Daga Ibnu Abbas (ra), ya ce:

Allah ya hana a riƙi kafirai abin ƙauna, sai dai idan kafiran sun kasance masu ƙarfi, ana tsoron ta'addancinsu, to sai a lallaɓe su, a nuna ana tare da su, amma a Addini kam sai a saɓa musu.

Haka ya ruwaito:

عن السدي: "...إلا أن يتقي تقاةً، فهو يظهر الولاية لهم في دينهم، والبراءةَ من المؤمنين".

تفسير الطبري (٦/ ٣١٤)

Haka Shaikh al-Shanƙiɗiy ya faɗa, inda ya banbance "Muwalati" da ƙaunar kafirai bisa zaɓi, daga ƙaunarsu idan sun tilasta wa mutane. Inda ya ce:

"وبين في موضع آخر: أن محل ذلك فيما إذا لم تكن الموالاة بسبب خوف، وتقية، وإن كانت بسبب ذلك فصاحبها معذور، وهو قوله تعالى: {لا يَتَّخِذِ الْمُؤْمِنُونَ الْكَافِرِينَ أَوْلِيَاءَ مِنْ دُونِ الْمُؤْمِنِينَ وَمَنْ يَفْعَلْ ذَلِكَ فَلَيْسَ مِنَ اللَّهِ فِي شَيْءٍ إِلَّا أَنْ تَتَّقُوا مِنْهُمْ تُقَاةً} فهذه الآية الكريمة فيها بيان لكل الآيات القاضية بمنع موالاة الكفار مطلقاً، وإيضاح لأن محل ذلك في حالة الاختيار، وأما عند الخوف والتقية فيرخص في موالاتهم، بقدر المداراة التي يكتفي بها شرهم، ويشترط في ذلك سلامة الباطن من تلك الموالاة.

ومن يأتي الأمور على اضطرار *** فليس كمثل آتيها اختيارا

ويفهم من ظواهر هذه الآيات أن من تولى الكفار عمداً اختياراً رغبة فيهم أنه كافر مثلهم".

أضواء البيان (٢/ ١٣٣)

A wani wajen kuma ya ce:

"وقد قدمنا أنه (جل وعلا) بَيَّنَ أن الذي يتولى الكفار اختياراً رَغْبَة فيهم وفي دينهم أنه منهم، كما تقدم في قوله: {وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُمْ فَإِنَّهُ مِنْهُمْ إِنَّ اللَّهَ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ} [المائدة: الآية ٥١]".

العذب النمير (٥/ ٢١٨)

Ka ga sai ya sharɗanta abubuwa biyu, kafin "Muwalati" ga kafirai ya zama kafirci:

1) Muwalati da taimakon kafiran da ƙaunarsu ta kasance ne bisa zaɓi.

2) Ta kasance saboda ƙaunarsu ne, da son Addininsu da kwaɗayinsa.

To in dai an rasa waɗannan abubuwa biyu, to wanda ya yi soyayya da taimako da "Muwalati" ga kafirai ba zai kafirta ba.

2- Soyayya ga kafirai, da yi musu "Muwalati", da taimakonsu, saboda wata buƙata ta duniya (ba saboda Addininsu ba). Wannan ya kasu kashi biyu:

A- Taimakonsu a kan Musulmai saboda wata buƙata ta duniya, kamar a wajen yaƙi, ko leƙen asiri, ko tona asirin Musulmai. Kuma ya yi hakan ne bisa zaɓi, ba tare da an tilasta shi ba. Wannan babban zunubi ne, mai girma, amma bai kai kafirci ba.

Ƙissar Haɗib bn Abi Balta'ah (ra) dalili ne a kan wannan.

B- Soyayya ga kafirai, da yi musu "Muwalati", saboda dangantaka, ko abota ko zumunci, ko mu'amala ta hulɗoɗin duniya da kasuwanci da sauransu. Wannan halas ne, babu laifi. Ibnu Jarir ya ruwaito:

عن مجاهد في قوله: "لا يتخذ المؤمنون الكافرين أولياء من دون المؤمنين"، إلا مصانعةً في الدنيا ومُخالقة".

تفسير الطبري (٦/ ٣١٥)

Daga Mujahid:

Wato sai dai saboda lallaɓa su a mu'amala ta duniya - ba ta Addini ba -, tare da saɓa musu a lamarin Addini.

Kuma ya ruwaito:

عن قتادة قوله: "لا يتخذ المؤمنون الكافرين أولياء من دون المؤمنين إلا أن تتقوا منهم تقيَّة"، نهى الله المؤمنين أن يوادّوا الكفار أو يتولَّوْهم دون المؤمنين. وقال الله:"إلا أن تتقوا منهم تقيَّة"، الرحم من المشركين، من غير أن يتولوهم في دينهم، إلا أن يَصل رحمًا له في المشركين".

Daga Ƙatada:

Sai dai son kafirai da taimakonsu, saboda dangantaka da zumunci, amma ban da a lamarin Addininsu.

Ya ruwaito:

عن الحسن في قوله: "إلا أن تتقوا منهم تقاة"، قال: صاحبهم في الدنيا معروفًا، الرحم وغيره. فأما في الدّين فلا".

تفسير الطبري (٦/ ٣١٦)

Daga Alhassan, ya nuna cewa:

Ka zauna da kafirai a lamarin duniya bisa kyautatawa, kamar zumunci da waninsa, amma a lamarin Addini kam a'a.

Saboda haka, ashe kenan, bisa fahimtar Salaf, ba kowane "Muwalati" ga kafirai, da nuna musu so da ƙauna ne yake zama kafirci ba.

- Akwai na kafirci; shi ne idan mutum ya yi don yana son Addininsu.

Kamar yadda muke gani, a duk shekara ƴan Shi'a, har coci suke zuwa suna taya kiristoci yin Addininsu.

- Akwai kuma wanda bai kai kafirci ba, aikin saɓo ne mai girma, wato taimakon kafirai a kan Musulmai, don abin duniya, ba don son Addininsu ba, ko don Addinin nasu ya ɗaukaka.

- Akwai kuma na halas. Shi ne yin mu'amala da kafirai, da yin hulɗoɗi da su, imma saboda zumunci, ko zamantakewa da makwabtaka, da kyautata musu. Wannan ya sa ya halasta ka auri bayahudiya ko kirista, alhali dole a samu soyayya a tsakani.

Saboda haka, irin hulɗa da ƙawance da Saudiyya take yi da Amerka da Turai, yana nau'i na uku ne, hulɗa ce ta kasuwanci da ƙawance, da hulɗar difilomasiyya, da sauran alaƙoƙi da ƙawance don cimma maslaha na tsakani.

Kuma idan mun kyautata wa Iran zato, sai mu ce: irin wannan "Muwalatin" take yi wa kafiran Rasha da China. Sai dai idan an samu taimakon kafiran, don yaƙar Musulmai, kamar yadda Iran take yi, ta taimaki Amerka a Iraq, ta taimaki Rasha da Basshar Asad a Syria, a kan yaƙar Musulmai. To wannan ya shiga kashi na biyu.

To saboda haka, sai mu yi tambaya, mu tambayi Dr. Gumi, ta yaya aikin Saudiyya zai zama kafirci, amma ita Iran nata ya zama Muslunci?

Haba Dr.!

Da wane irin ma'auni kake awu ne?!

A takaice, ya bayyana cewa: wannan hukunci da Dr. Gumi ya yi a kan Saudiyya da wasu ƙasashen Larabawa, ya yi ne bisa Manhajin masu guluwwi a kafirtawa, irin ƙungiyoyin boko haram da sauransu.

Allah ya shirya.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments