Ticker

6/recent/ticker-posts

Dr. Gumi Da Kanzagi Wa Iran

Duk wanda ya san Dr. Gumi ba zai yi mamakin maganarsa ta kafirta shugabannin Larabawa, da musluntar da shugabannin Iran ba. Saboda shi Dr. Gumi - duk da a galibin yanayi ina kyautata masa zato - ina yi masa uzuri da rashin sani ko ƙaracin ilimi a fagage masu yawa. A wani ɓangaren kuma, ina zarginsa da rashin adalci, musamman a siyasar gabas ta tsakiya. Ai kowa ya san irin abin da ya bayyana na karamci da Iran ta yi masa, a shekarar da suka gayyace shi wajen wani taro nasu. Da kuma abin da ya faru da shi a Saudiyya, a bara, inda aka hana shi shiga ƙasar, a lokacin aikin Hajji. Wannan ya sa shugabannin Iran suka zama waliyyai a wajensa, na ƙasashen Larabawa kuma kafirai.

To yanzu ko ba komai, wannan kafirta Sarakunan Larabawa da yake yi, yana musluntar da shugabannin Iran, babban uzuri ne ga Saudiyya, bisa hana shi shiga ƙasarta da ta yi.

Bayan haka, shi Dr. Gumi, alamu sun nuna bai san miye Shi'a ba. Saboda yana nuna babban laifin Shi'a shi ne zagin Sahabbai. Alhali Shi'a suna da Aƙidu na shirka da kafirci da zindiƙanci da munafurci, waɗanda suke ƙunshe a cikin Aƙidar Imama,  wacce ita ce jigon Addininsu, wacce da ita suka banbanta da sauran Musulmai.

A cikin Aƙidar Imama, akwai guluwwi a haƙƙin Imamai, da ba su matsayin Allah, na bauta da sanin gaibi, da daidaita su da Allah a Rububiyya, da sauran Siffofinsa, na tasarrufi a cikin halitta da ilimi, da sauransu.

Da kuma Aƙidunsu game da Annabta, na daidaita Imama da Annabta, da fifita Imamai a kan dukkan Annabawa, in ka cire Annabi (saw).

Da sauran Aƙidu na kafirci da zindiƙanci, da ƙin Allah da Manzonsa (saw).

Mutane da yawa ba su san waɗannan ba, hatta da yawan Malamai. Sai aka ɗauka zagin Sahabbai kawai shi ne laifin Shi'a.

To, ko shi zagin Sahabban da ƴan Shi'a suke yi ba ƙaramin abu ba ne. Zagin da ƴan Shi'a suke yi wa Sahabbai zindiƙanci ne. Wato Munafurci ne, irin Munafurcin Munafukan zamanin Annabi (saw).

Saboda zagin da ƴan Shi'a suke yi wa Sahabbai, zagi ne na rushe musu Addininsu da adalcinsu. Shi ya sa a ruwayoyinsu aka ruwaito cewa; Sahabbai sun yi ridda, saboda sun juya baya wa Wilayar Imamai, ba su zaɓi Sayyidina Aliyu (ra) a matsayin khalifa ba. Don haka Sahabbai ba adilai ba ne, fasiƙai ne, riddaddu.

To, abin nufi fa, shi ne; ba za a ƙarɓi komai na Addini a wajen waɗannan Sahabban ba. Saboda ba a ƙarɓan Addini a wajen kafiri murtaddi.

Bisa wannan, dukkan Alƙur'ani da Sahabbai suka naƙalto daga Annabi (saw), da dukkan Hadisai da suka ruwaito daga Annabi (saw), da dukkan Fiƙhun da suka ruwaito daga Annabi (saw), kai, da duk wani abu na Addini da Sahabbai suka ruwaito daga Annabi (saw), ba abin karɓa ba ne, abin jefawa a bola ne!

SubhanalLahi!

Toh, me ya saura a Addinin kuma?!

Wannan kuwa ba ƙaramin zindiƙanci mai rushe Addini ba ne!

Idan aka bi ta ƴan Shi'a, duka wannan Addini da muke yi ɓatacce ne lalatacce, saboda munafukai kafirai murtaddai ne suka ruwaito, wato Sahabbai, alhali ba a karɓan Addini ta hayar kafirai.

Wannan ya sa Imam al-Ɗahawiy ya ce:

"وحبهم دين وإيمان وإحسان، وبغضهم كفر ونفاق وطغيان".

العقيدة الطحاوية

"Son Sahabbai, Addini ne, Imani ne, Ihsani ne. Ƙinsu kuma kafirci ne, munafurci ne, ƙetare iyakar Muslunci ne".

Ma'ana; ƙiyayyar da Rafidha suke yi wa Sahabbai, suke zaginsu, suke aibanta su, suke cewa; sun yi ridda, saboda ba su bai wa Sayyidina Aliyu (ra) khalifanci a bayan Annabi (saw) ba, wannan zagi da kafirtawa da suke yi wa Sahabbai kafirci ne, munafurci ne, irin munafurcin munafukan zamanin Annabi (saw).

Ba za kanfahimci haka ba, sai ka san wannan magana ta Abu Zur'ah al-Raziy, inda ya ce:

"إذا رأيت الرجل ينتقص أحدا من أصحاب رسول الله - صلى الله عليه وسلم - فاعلم أنه زنديق؛ وذلك أن الرسول - صلى الله عليه وسلم - حق، والقرآن حق، وما جاء به حق، وإنما أدى إلينا ذلك كله الصحابة، وهؤلاء يريدون أن يجرحوا شهودنا؛ ليبطلوا الكتاب والسنة، والجرح بهم أولى، وهم زنادقة".

الكفاية للخطيب البغدادي (ص: ٩٧)

"Idan ka ga mutum yana sukar wani daga cikin Sahabban Manzon Allah (saw) to ka sani shi zindiƙi ne. Domin kuwa Manzon Allah (saw) gaskiya ne, Alƙurani gaskiya ne, duka abin da ya zo da shi gaskiya ne. Duka wannan Sahabbai ne suka isar mana da su. Su kuma waɗannan mutane (ƴan Shi'a) suna son su tozarta shaidunmu ne, domin su ɓata Alƙur'ani da Sunnah. Alhali su suka cancanci a tozarta su, kuma su zindiƙai ne".

Kamar dai yadda aka ruwaito daga Imam Malik inda ya ce:

"إنما هؤلاء أقوام أرادوا القدح في النبي صلى الله عليه وسلم، فلم يمكنهم ذلك، فقدحوا في أصحابه؛ حتى يقال: رجل سوء، ولو كان رجلًا صالحًا لكان أصحابه صالحين".

الصارم المسلول (ص: ٥٨٠)

"Waɗannan fa mutane ne kawai da suke son sukar Annabi (saw), amma ba za su iya ba, sai suka soki Sahabbansa, don a ce: Shi ma mutumin banza ne, saboda da a ce: ya kasance mutumin kirki, to da dole sahabbansa ma su zamo mutanen kirki".

Dole fa ka fahimci cewa; idan aka rushe Sahabbai, to Wallahi ko ka ƙi, ko ka so, dole a rushe Addinin Muslunci. Saboda babu yadda za a yi mu karɓi Addini ta hannun kafirai. Rushe Muslunci kuwa shi ne asalin tushen da aka kafa Addinin Shi'anci a kansa, tun da sanyi safiya, lokacin da Munafuki ya kafa Addinin na Shi'a, wato Bayahude Abdullahi ɗan Saba'i.

Wannan ya sa tun tuni Malaman Muslunci suka yi hukunci wa ƴan Shi'a cewa; su kafirai ne.

Daga cikinsu akwai Imamu Malik, Imamin Mazhabarmu ta Malkiyya, inda ya ce:

"الذي يشتم أصحاب النبي (ص) ليس له سهم - أو قال: نصيب - في الإسلام".

السنة للخلال (٣/ ٤٩٣)

"Wanda yake zagin Sahabban Annabi (saw) ba shi da kaso - ko cewa ya yi: rabo - a cikin Muslunci".

An karanta Ayar (محمد رسول الله) har ƙarshe a gaban Imamu Malik, sai ya ce:

"من أصبح في قلبه غيظ على أحد من أصحاب رسول الله (ص) فقد أصابته هذه الآية".

 حلية الأولياء (٦/ ٣٢٧)

"Duk wanda ya wayi gari a zuciyarsa akwai fushi da Sahabban Manzon Allah (saw) to wannar Ayar ta hau kansa".

Ma'ana, babu masu jin haushin Sahabbai sai kafirai. Saboda a cikin Ayar Allah ya ce:

{ليغيظ بهم الكفار}.

Saboda haka babu wani ɗan Malikiyya na gaskiya, ko Ahlus Sunna na gaskiya da zai ɗauki Rafidha ƴan Shi'a a matsayin Musulman da ba zindiƙai masu nufin rusa Muslunci ba. Su zindiƙai munafukai ne, suna cikin al'ummar Musulmai kamar Munafukai a zamanin Annabi (saw).

Su fa ƴan Shi'a Munafukai ne, babu yadda za a yi ka gane gaskiyar Musluncinsu, saboda suna da wata Aƙida mai suna "Taƙiyya". Wato a tsakanin sauran Musulmai sai su ɓoye ainihin Aƙidunsu, ba za su bayyana ba, sai a tsakanin su ya su.

To don Allah, mai wannar Aƙida ta "Taƙiyya", ta yaya za ka gane gaskiyarsa a komai ma?!

Babu yadda za ka gane.

Kuma wani abu mai hatsari da suke kansa, shi ne matsayarsu game da Ahlus Sunna (wanda ba ɗan Shi'a ba), wato wanda suke kira "Nasibiy". Jininka halas ne a wajensu. Jira kawai suke yi su samu dama. A duk lokacin da suka samu dama sai sun yayyanka Ahlus Sunna, da sunan su "Nasibawa" ne, maƙiya Ahlul baiti.

Kuma suna nan kan wani alkawari da suka ɗauka, cewa; sai sun ɗauki fansar jinin Imam Hussaini (ra) a kan Ahlus Sunna, saboda Ahlus Sunna "Nasibawa" ne, makasa Hussaini (ra). Wannan ya sa da suka samu dama a Syria da Iraq, suka sha jinin Ahlus Sunna iya yadda suke so.

Sa'annan kuma, Khomainy ya yi musu wata Wasiyya, cewa; suna gamawa da Iraq su koma kan ƙasashen Gulf, su mamaye su, su mayar da su ƙarƙashin gomnatinsu ta Shi'a da take Iran.

Saboda haka, ni a yi sanina, duk cikin al'ummar Musulmi, babu ƙungiya mai zagon ƙasa wa Muslunci, mai kuma mungun nufi a kan Musulmai kamar Rafidha ƴan Shi'a. Kusan dukkan ƙungiyoyin "Baɗiniyya", masu rushe Addini daga ƴan Shi'a suke, wato suna fitowa ne daga masu ƙaryar son Ahlul Baiti. Tun daga kan Saba'iyya, masu allantar da Sayyidina Aliyu (ra), har kan "Ubaidiyyun", masu allantar da al-Hakim bilLah, da kuma su "Isma'iliyya", "Nusairiyya", "Duruz", "Baha'iyya" har kan "Ithna Ashariyya", da sauransu, dukansu ƴan Shi'a ne, amma manufarsu da aiyukansu su ne rushe ainihin Addinin Muslunci.

Shi ya sa Alƙur'aninsu daban, Hadisansu daban. Salon Addininsu daban, duka saboda ba su yarda da Sahabbai ba, ba sa karɓan Addini daga gare su.

Saboda haka, ku faɗa wa Dr. Gumi cewa; zagin Sahabbai ba ƙaramin laifi ba ne, da shi ake rushe Addini. Babu mai zagin Sahabbai sai zindiƙi, munafuki irin munafukan zamanin Annabi (saw).

✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani (hafizahullah).

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments