Ticker

6/recent/ticker-posts

Kufcewar Salo

Bamai Dabuwa (2020). Kufcewar Salo. Muhalli, Sutura (Labaran Da Suka Samu Nasara a Gasar Gajerun Labarai a Kan Muhalli Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2020). Darma Digital Prints.

KUFCEWAR SALO

Na

Bamai Dabuwa

Duk da kasancewar da yammaci ne amma ko kaɗan babu sauki daga azababben zafin ranar da ke ƙoƙarin babbaka mutane, wanda ya haifar da ɗumamar yanayin da ba za ka iya bambance tsakanin rana da inuwa ba. Irin yanayin nan ne da Hausawa ke kira rana zafi inuwa ƙuna. Garin cike yake da tafka-tafkan bishiyoyin da ya kamata a ce sun samar da sassanyar iska gami da mafaka ga al'ummar yankin, amma sai ya kasance tamkar ana guma shinkafa. Babu ɗaya daga cikin ganye ko reshe na dukkan bishiyoyin da ke kaɗawa, kamar dai tsayayyen ƙarfen MTN.

Gari ne madaidaici, mai tarin al'umma kuma fitacce, ba don noma, albarkar ƙasa ko kasuwancin da ke gudana a cikinsa ba. Sai don ibtala'in cututtuka da mace-macen da ke wakana, wanda ya zarta na adadin rayukan mutanen da aka rasa a sanadiyyar ta'addancin boko haram ko na tantirai a yankin Zamfara. Al'amarin kullum sake damalmalewa yake, adadin mutanen da ake rasawa da majinyata na hauhawa fiye da kima musamman a wannan loto na damina.

A cikin sati ɗaya kawai kimanin mutum hamsin suka rasa ransu, ya yin da majinyatan da aka kwantar a asibiti suka doshi ɗari biyu, bayan wanda suke zuwa ganin likita a rubuta musu magani su koma gida. Akwai ƙarancin wayewa sosai ta fuskar ilmi musamman na zamani a garin, tsirarun da suka yi karatun ba a cikinsa suke zaune ba.

Saleh Muhammad Bello, matashi ne ɗan kimanin shekaru ashirin da takwas. Ɗalibi a jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi aji uku. Yana karanta Architecture. Zaune yake tare da iyayensa a garin Dutsen jihar Jigawa, wanda asalinsu 'yan Birkita Wake ne wacce ke a ƙaramar hukumar Birniwa duk a jihar ta Jigawa daga ƙarshenta ta arewa maso gabas, iyaka da jihar Yobe. Ganin gida da dangi ne ya kawo su sakamakon hutun da ake sanadiyyar cutar Covid-19 (Corona). A 'yan kwanakin da suke zaune ne Saleh ya fahimci halin da al'ummar suke ciki na annoba da kuma yadda hukuma ta yi watsi da al'amarinsu.

Cikin tsirarun kalmomi ya zayyana halin da al'ummar ke ciki ya watsa a shafinsa na facebook, wanda a ranar da ya saki rubutun hukumar lafiya ta jihar suka tuntuɓe shi inda shi kuma ya ƙara musu bayani tare da tabbatar musu da al'amarin.

Kashegari da sassafe sai ga motoci ƙirar Hilux farare kimanin su uku jiki an rubuta NCDC sun shigo garin cike da likitoci sanye da wasu kalar riguna da suka rufe jikinsu tun daga sama har ƙasa, hatta fuska da kansu killace suke. PHC (Primary Health Care) manaja na ƙaramar hukumar ne ya musu iso shi ma sanye da irin nasu kayan. Saleh shi ne mutumin da suka buƙaci gani kafin daga bisani su nausa asibitin bayan shi ma sun ba shi kalar nasu kayan ya saka. A asibitin ne suka riƙa zagayawa suna duba marasa lafiyar da musu tambayoyi haɗe da ɗaukar jininsu ɗayan bayan ɗaya. Bayan sun kammala ne suka sanarwa da PHC manaja ɗin da Saleh cewa za su koma da samples ɗin can Dutse gwaji da umarnin killace marasa lafiyar don suna zargin Corona ce ta shigo garin ba a farga ba.

Kwanaki biyu da tafiyarsu sakamakon ya fito. Amma ga mamakinsu, babu mutum ɗaya da ke ɗauke da cutar ta korona. Abu ɗaya duk sakamakon ke gwadawa, shi ne zazzaɓin cizon sauro sai typhoid. Wannan ne ya sa gwamnati ta samar da ingantattun magunguna da isassun likitoci a garin don shawo kan matsalar kyauta. Sai dai, hakan bai hana masu lafiyar kamuwa ba, wanda suka warke ma sai ka ga bayan sati sun kuma kamuwa a karo na biyu.

A wannan gaɓar ne lissafin da yawa ya kwance, ya yin da wasu ke tunanin ko sihiri aka yi wa garin, wasu kuma suka aminta cewa saɓo da tulin zunuban da suke aikatawa ne sila. Daga ɓangaren Saleh kuwa bai gamsu da ko ɗaya daga cikin biyun ba. Nasa tunanin da fahimta kan al'amarin daban ne.

"Rashin tsari da bin ƙa'idar gine-gine da magudanan ruwa ne ummul'aba'isin jinya da mace-macen da ke faruwa a garin Birkita Waken jihar Jigawa."

Saƙon da ya wallafa kenan a shafinsa na facebook wanda ya ja hankalin mutane da dama, sai dai mafi akasari ba su fahimta ba inda cikin ɗaurewar kai suke tambayarsa.

"Ta yaya?"

 ***

Jirkice yake bisa wata gajiyayyiyar darduma, wacce kala da gashi-gashin da take da shi na sabunta suka kokkoɗe da tujewa saboda tsabar shekarun da ta shafe. Duƙun-duƙun take da datti, ta yi baƙiƙirin. Amma wani abun mamaki game da ita shi ne da za ka kwanta bilayi da fararen kaya, sumul za ka tashi ba tare da ka kwashi daidai da ƙwayar zarra na kazanta a tare da ita ba. Dardumar shimfiɗe take bisa wani dakalin ƙasa mai faɗi. Inda shi kuma dattijon da ke kanta ya tayar da kai da hannunsa bisa filo.

Dattijo ne fari kuma dogo siririyi. Duk da cewar yana a kwance ne, hakan bai hana ka ganin yadda ƙaton tumbinsa ya kwanta a ƙasa ba. Yana da matuƙar wahala samun dogon mutum ƙyamurmuri da tulin tumbi kamarsa saboda ya saɓa da tsari ko zubin halittar ire-irensa. Idan kuwa aka samu to cikin biyu akwai ɗaya. Ko dai a sanadin rashin lafiya ko kuma a baya an kwanƙwaɗi barasa. Sai dai, babu ko ɗaya cikin biyun a al'amarin wannan dattijon.

Lafiyarsa lau, hasalima da za ku kasa tsere da shi zai iya ba ka ruwa duk da cewar ya doshi shekaru saba'in. Kawai irin masu kuɗin ƙauyen nan ne da idan suka samu dama sai su buɗe baki suna ta caccakawa ciki duk abin da suka ga dama da sunan jin daɗi. Sanye yake cikin fararen kaya malum-malum. Tulin rawanin da ya tanke kansa da shi kamar wani huhun goro ne zai hana ka ganin tarin furfurar da ta cika masa kai. Shi ne dagacin garin.

A gefensa daga can ƙasa, wasu dattijan ne su biyu a dama da hauni sun sa shi a gaba bisa taburma.

"Wakili ina aka kwana maganar kuɗin sadaka da na ce a haɗa?"

Cewar dagacin kansa a sama, idonsa a rufe.

"Ranka ya daɗe, na sanar da duk masu unguwanni. Suna harhaɗawa."

Cewar wanda ke daga ɓangarensa na dama.

"Da kyau! Ka ga gobe talata kasuwar Biriniwa idan aka haɗa sai a je ko saniya a siyo, juma'a sai a yanka wajen sadaka." Cewar dagacin a karo na biyu.

"Gaskiya ne ranka... Wa alaikumussalam"

Wannan karon na haunin ne ya amsa kafin daga bisani sallamar da aka musu ta katsar da shi, inda ya amsa ba tare da ƙarasa waccan maganar ba.

"Ranka ya daɗe ina kwana!"

Cewar wanda ya yi sallamar, bayan ya zube bisa gwiwowinsa a gaban dagacin. Bayan sun gaisa ne ya ɗora da magana.

"Rankayadaɗe sunana Saleh, ni ɗan gidan Alhaji Muhammadu ne jikan malamin jeji Bello. Na zo da wani muhimmin batu ne kan abubuwan da suke faruwa na mace-mace da jinya a wannan gari. Da albishirin cewa in sha Allah komai zai zo ƙarshe. Kwanaki biyu da suka wuce, na dora wani rubutu a dandalin sada zumunta na Facebook, ɗaya daga cikin sabbin kafafen sadarwa na zamani, cewa rashin tsari da bin ƙa'idar gine-gine da magudanan ruwa ne ke assasa jinya da mace-macen da ake a wannan gari..."

"A'a yaro! Allah dai."

Dagacin ne ya katse shi, bayan ya gyara zama yana fuskantarsa.

"Haka ne, amma Allah ɗin ne da kansa a cikin suratul Ra'ad, aya ta goma sha ɗaya ya ce

 " ۗ إِنَّ اللَّهَ لَا يُغَيِّرُ مَا بِقَوْمٍ حَتَّىٰ يُغَيِّرُوا مَا بِأَنفُسِهِمْ ۗ "

Cewa shi Allah ba ya canja yanayi ko halin da mutane suke ciki har sai sun gyara da kansu. Sannan mantawa ka yi, kamar na ce in sha Allahu ma wanda ya cika ma'ana da nufin ƙarashen ayar."

"Ina sauraronka yaro, ci gaba."

"Bayan na ɗora wannan rubutu ne na samu kira daga ma'aikatar lafiya, inda suka min wasu tambayoyi na amsa musu a taƙaice. Daren jiya suka kuma kirana, inda suka shaida min cewa kwamishinan lafiya da na muhalli za su zo ranar laraba ƙarƙashin wakilci da umarnin mai girma gwamna, don ji da ganewa idanunsu ta yadda aka yi ibtala'in da ke afkuwa yake da alaƙa da gine-gine ko magudanan ruwa. Duk da cewar za ka samu labarin zuwansu daga masarauta ko ƙaramar hukuma, ina ganin akwai buƙatar na sanar da kai ni ma, domin garinka ne. Babu shakka kowa ya yi yaƙi aka ce sarki ya taya."

"Da kyau yaro! Allah ya maka albarka. Allah ya kawo su lafiya."

Wannan karon wakilin dagacin ne ya yi magana cike da zumuɗi.

"Wakili, an ce fa ta yaro kyau take ba ta ƙarƙo. Bai kamata ka hau zancen yaro karami ka zauna ba. Tun farko ya kamata ka fahimta akwai yarinta sosai a cikin maganganunsa. Ta yaya ma za a ce gine-gine ke haddasa mana mace-mace da jinya. Ta ina ma suka haɗu. A duk wanda suka mutu ɗin akwai wanda gini ya danne ne da za a ce gini ne ko kwamishina ƙaramin mutum ne da har za su saurare shi. Haba!"

Cewar dagacin a fusace.

"Ranka ya daɗe shi ne fa yaron da ake cewa ya yi silar da yanzu kyauta ake bayar da magani a asibitunmu. Kuma tun daga Dutsi ma'aikatan lafiya suka zo suna duba lafiyarmu a dalilinsa."

Wakilin ya ce da shi cikin sanyin murya.

"Ko shi ne ma dai kam, ai ya kamata ka duba wannan maganar kuma. Kar ka bari yaro ƙarami ya caje ka mana da wayonka."

"Yawan shekaru ba shi ne wayo ba ai ranka ya daɗe. Sannan kamar yadda ya faɗa, babu shakka garinka ne. Idan har ya iya gamsar da mutanen da ke birni kuma masu ilmi har suke shirin zuwa don taimaka mana, me zai hana ba za mu ba shi dama ba. Na farko ba kai ne ka gayyato su ba bare ka yi fargabar abin kunya. Na biyu ina jin tsoro kar baƙin nan su zo mu yi banza da su saƙo ya iske hakimi mu shiga uku." In ji Wakilin.

"Ka ce wani abu kam. Amma dai ni da ban ci kasuwa ba, rumfa ai ba ta faɗa min ba. Duk da haka za mu bayar da haɗin kai da duk gudunmowar da ta dace. Ko ba komai ni ma zan so na ji ta yadda gine-gine da magudanan ruwa suka zamo silar wannan matsalar ta mu. Yaro ka je, Allah ya kai mu ranar da lafiya."

Da wannan Sale ya tashi ya bar su, jikinsa a sanyaye, zuciyarsa kuma cike da takaici da mamaki.

  ***

Rumfuna ne aka samar irin na zamani kimanin su huɗu daga kowacce kusurwa, maƙil da mutane mabambanta a shekaru da jinsi. Ɗaya daga cikin rumfunan daga gabas ta bambanta da sauran ta fuskar kwalliya da ƙawa. Saɓanin sauran, ita kujerun da ke ƙarƙashinta manya ne kuma masu taushi. Kana ba sai an faɗa maka ba, kana kai dubanka izuwa mutanen da ke ƙarƙashin za ka tabbatar da cewa mutane ne na musamman kuma muhimmai.

Ba kawai don yadda suka kece raini da ƙure adakar kwalliya ba, jami'an tsaron da ke zarya da ba su kulawa kaɗai ma ya wadace ka ba su girma. Sannan tsarin da aka bi wajen shirya kujerun ya sha bambam da sauran rumfunan, sakamakon tazarar da aka bayar na kimanin taku uku zuwa huɗu na sawu a tsakanin kujera da kujera. Sannan babu mutum ɗaya ciki da ba ya sanye da camfu (face mask) a fuskarsa.

Kodayake wannan tsari da shirin ne aka bi wajen jera kujerun da ke a sauran tantin ma, amma sai mutanen suka cushe su waje guda, idan ma akwai tazarar za ka iske mutane sama da biyu sun cike tsakanin. Da alama ba ruwansu da wata Corona, amma kuma wani abin mamaki sh ne zai yi wahala ka samu mutum ɗaya cikinsu da ba ya sanye da face mask ɗin. Ƙila ko sun ɗauka wani abin burgewa ne sanya shi ɗin oho.

A tsakiyar rumfunan daga yamma, wani dogon benci ne tsayayye, ɗauke da abin magana, inda ya ranƙwafo daidai saitin bakin duk wanda ya fuskance shi. Don naɗa da miƙa magana ga jibga-jibgan amsakuwwar da aka samar a kowacce kusurwa wa sauraron al'uma. Duk da cewar babu inda aka jona wata waya da za ta taimaka wajen sadarwa ko harba magana daga jikinta zuwa amsakuwwowin, amma a hakan maganar ke isar musu suna fitarwa. Wannan fasahar ba ƙaramin tafiya da tunanin mutanen Birkita Wake ta yi ba.

" Yauwa! Duba da lokaci da kasancewar akwai abubuwa manya na aiki da ke a gaban musamman manyan baƙin da suka zo don kawo mana ɗauki, bayan buɗe taro da addu'a, ina ganin zai fi mana kyau idan muka nausa ga agenda ta gaba. Wanda ita ce ta kawo mu wannan wuri. Sai dai, kafin nan zan so na yi kira ga jama'a da a taƙaita surutu da sauraro. Bayan haka ne nake kira ga Saleh Muhammd Bello, ɗalibi kana masani a kan abin da ya shafi gini da zane-zane daga jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke garin Bauchi, don ya faɗaɗa da fayyace mana yadda aka yi gini da magudanan ruwa ke da nasaba da ibtala'in da ake fama da shi a wannan gari. Malam Saleh bismillah." Cewar mutumin da alamu ke gwada ɗan jarida ne.

Sanye yake cikin doguwar riga fara da baƙar hula a kansa. Isar sa wajen kedawuya ya fara magana da cewa:

"Masu girma kwamishinan lafiya da na muhalli, maigirman shugaban ƙaramar hukumar Birniwa, ɗan majalisar jiha mai wakiltar Biriniwa, masu girma iyayen ƙasa, hakimin Birniwa da Diginsa, sauran baƙi da al'umar wannan gari na Birkita Wake assalamu alaikum. Kimanin shekaru masu yawa, wannan gari ke fama da annoba ta cututtuka da mace-mace . Wani ƙaulin ma aka ce tun farkon samuwarsa, babu shekarar da za ta zo ta wuce ba tare da an samu matsala ba musamman da damina. Mutane suna ta mutuwa, adadin mutanen da ake kwantarwa a asibiti da wanda kullum ke kamuwa da jinya sai hauhawa yake kamar wani farashi.

 Gwamnati da ma'aikatan lafiya suna bakin ƙoƙarinsu amma abin da ya ci tura. Ba don babu magani ko sihirin da dayawa suke cewa an yi wa garin ba ne, sai don wani abu da marubuta ke kira da kufcewar salo wanda a gwarance ake nufi da an bar jaki ana dukan taiki. Dayawan mutane suna ganin kamar babu wata alaƙa tsakanin cutar malaria ko typhoid da tsarin gini ko muhallinmu, alhalin sun manta inda ake samu ko abubuwan da ke haifar da cututtukan. Wanda na tabbata idan da za a bi diddigin ababen da ke haifar da su da daƙile su, to da yardar Allah komai zai zama tarihi ne.

Domin waccan hanyar da ake bi na bayar da magani tamkar a kashe maciji ne ba a sare kansa ba. Malaria cuta ce da a kimiyyance aka tabbatar da cewa ta macen sauro ke haddasa ta, wacce da turanci ake kiranta da female anopheles mosquito. Wannan ya sa bahaushe da ya tashi haulayir da jinyar ya kira ta da zazzaɓin cizon sauro. Wato daga nan za mu fahimta cewa sauro ne ke haddasa mana wannan zazzaɓin, shi kuma sauro babu inda yake rayuwa da hayayyafa sai a wajen da kwata ko tsayayyen ruwa yake.

Maigirma kwamishinan lafiya, da a ce za ka ratsa cikin wannan gari da ƙafa, ko ka ɗaga kanka zuwa kowanne kusurwa, za ka iske kwata a kowanne ɓangare kore shar. Babu wani lungu ko saƙon da za ka bi ba ka iske kwata ba, wani sa'in ma a cikin gidaje za ka tarar da kwata. Dangane da ruwan da muke sha kuwa, babu wani burtsate ko kan famfon da za ka iske ba kwancaccen ruwa mai datti a gindinsa, a wasu wuraren ma ga burtsatsen ga kuma shaddar kashi a kusa. Ba mu san cewa ruwan kashi da na kwatan muke sha ba.

Don Allah ta yaya ne typhoid ba za ta kama mu ba, alhalin ruwan shanmu ya gurɓata!"

Shiru ya yi na ɗan wasu daƙiƙai tare da share gumin da karyo masa a fuska ta hanyar amfani da hankicin da ya ciro a aljihunsa. Kafin daga bisani ya mayar da hankicin ya ci gaba.

"Babu wani takamammen hanyar da ruwan sama ko wanda muka yi wanka da wanki zai wuce, saboda da inda ya dace inda bai dace ba, gini kawai muke. Akwai lungunan da da za ka bi, kana cikin tafiya za ka tsinci kanka a tsakar gidan mutane. Sai ka tarar da gida ruwa ya kwanta a baya ko gabansa, a hankali yana nasawa cikinsa.

Domin a yadda muka ɗauka, gida shi ne kawai ka tayar da soro ka rufe ka shiga. Ba mu san cewa za ka iya yin gida ka shiga amma kullum ya saka rashin lafiya ba. Ba a bin tsari wajen yanka filaye da fitar da tituna yadda ya kamata, kasancewar idan ka buƙaci gida dagaci kawai za ka samu, shi kuma ya haɗa ka da yaransa su sara maka fili kafcece, gwargwadon kyautatawarka gare shi. Daga ƙarshe rankuyadaɗe, ina mai sanar da ku cewa matuƙar ba tsari da gyara wajen fitar da titi, magudanan ruwa da cika ƙa'idar fitar da filaye yadda ya kamata aka yi ba, to ba za a shawo kan wannan matsala ba.

Da wannan ne nake kira ga gwamnati da ta taimaka ta kawo mana agajin da ya kamata cikin gaggawa wannan gari tun kafin mu ƙare. Na gode."

Tafi da sowar da mutane suka kaure ne ya cika wajen, wanda sai da aka ɗauki daƙiƙai kafin mai magana na farko ya isa wajen maganar.

"Madalla da wannan yaro mai tarin ilmi da basira. Abu na gaba shi ne jin ta bakin wakilan mai girma gwamna kuma kwamishinonin lafiya da muhalli. Sai dai, duba da lokaci kwamishinan lafiya ne zai yi jawabi a madadin su biyun. Rankayadaɗe bismillah."

"Mai girma kwamishina, shugaban ƙaramar hukumar Birniwa, ɗan majalisar jiha mai wakiltar Biriniwa, iyayena iyayen ƙasa hakimai da al'uma baki ɗaya ina mana maraba. Mun saurari bayani mai gamsarwa, babu shakka babu ƙarya ko kuskure dangane da abubuwan da aka faɗa. Ba surutu zan ja mu da shi ba, ba kuma zan mayar da mu baya ba ne.

Albishir zan muku al'umar wannan gari da cewa kayanku ya tsinke a gindin kaba, domin duk matsalolin da kuke fuskanta da maganinsu suna a ƙarƙashin ofishina da na abokin aikina ne. Ina mai ba ku tabbacin cewa za mu miƙa kukanku ga mai girma gwamna, kana mu ma za mu yi bakin ƙoƙari a ƙarƙashin ikonmu. In sha Allah ba za mu bari ku ƙare ba malam Saleh, domin taƙamar gwamnati mutanenta. Idan aka ce babu kowa, wa za mu mulka to? Don haka a dakace mu, alheri na nan zuwa da izinin Allah. Madalla."

Bayan kwamishinan ya kammala ne aka gayyaci shugaban ƙaramar hukumar, inda ya yi jawabin godiya musamman ga baƙi da fatan isa gida lafiya.

"A madadin ma'aikatar yaɗa labarai ta jihar Jigawa da kuma ofishin yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Birniwa ni Sunusi A. Doro nake kira ga shugaban malamai kuma limamin juma'a na babban masallacin wannan ƙaramar hukuma da ya rufe mana taro da addu'a."

Bayan Sati Biyu

Makonnin biyu da waccan taro, gwamnatin jihar Jigawa ta fitar da sanarwar sabbin ayyuka a gidan rediyo ciki har da titunan cikin garin Birkita Wake (Township Road).

"Ranka ya daɗe wata shawara ce nake tafe da ita dangane da diyyar (Compensation) da gwamnati za ta rabawa mutanen da aiki ya biyo ta gidajensu aka rushe don su gina sabo ko gyara da su buɗe asusu ko zuba adashen gata a bankin bayar da lamuni na gidaje don su gina masa gida mai kyau irin na zamani."

Cewar Saleh ya yin da ya kai ziyara fadar dagacin.

"To fa! Kai fa yaron nan kana da rigima. Me ya haɗa mu 'yan ƙauye da wani adashen gata ko banki kuma, idan dai ba so kake ka damfare mu ba don kawai ka ji za a rabawa mutane kuɗi." Cewar dagacin yana tsattsare shi da idanu.

"Ranka ya daɗe ka saurari yaron nan. Ko don irin cigaban da ya kawo mana a wannan gari." Wannan loton Wakili ne ya yi magana.

"Da wannan don wannan kam Wakili, wai an aika tsohon banza biko. Ina jiye mana damfara ne."

"Ranka ya daɗe babu maganar damfara a nan, shawara ce kawai na kawo don taimakawa mutane. Idan har ta yi ba sai a watsar da ita." Cewar Saleh cike da takaici.

"To ai na ji kana maganar banki ne, mu da ba ma'aikata ba me ya haɗa mu da banki?"

"Ajiya ko wata sabga da banki ba lallai sai ma'aikaci ba. Kana shi wannan bankin da nake magana a kansa ba kamar saura ba ne, an samar da shi ne don taimakawa ma'aikata da 'yan kasuwa wajen mallakar muhalli yadda suke so a duk inda suke so. Sannan ba a keɓe ko iyakance ba, duk ɗan Nijeriya ɗin da a ƙalla samunsa ya kai ₦7000 ko ya haura za su iya masa rijista a matsayin ɗan kasuwa ko mai dogaro da kai."

Hannu ya zira cikin aljihunsa ya zaro wani ɗan ƙaramin littafi, kafin daga bisani ya dora da cewa.

"Yanu misali kamar ni da ba ma'aikacin gwamnati ba ne, na yi rijista tare da su. Su ne ma suka mallaka min wannan littafin da ake kira da passbook. A cikinsa ne ake shigar da bayanan ajiyar da nake duk wata. Littafi ne mai muhimmancin gaske, wanda a tare da shi akwai suna da hotona a jiki. Bari ka gani."

Ya ce da dagacin a lokacin da yake ƙoƙarin buɗe littafin.

"Kana akwai taƙaitattun bayanai dangane da shi wannan bankin wanda suke jaddada cewa ba lallai sai ma'aikaci ba, kana ba a ware jinsi ko yare ba. Mace ko namiji duk za su iya cin gajiyarsa. Shi ya sa a takensu ma suke cewa Everyone Deserves A Home wai kowa ya cancanci muhalli.

Abu ɗaya da ake buƙata daga mutumin da ke son rijista ko ya yi rijista da su shi ne duk watan duniya zai riƙa ajiye kaso biyu da rabi (2.5%) cikin ɗari na samunsa. Misali idan mutum ma'aikaci ne, yana ɗaukar albashin ₦40000 duk wata zai riƙa ajiye ₦1000 kenan, haka ne ma ɗan kasuwar da ke samun dubu ɗari duk wata zai ajiye dubu biyu da ɗari biyar kacal.

Wannan kuɗin da yake tarawa duk wata ne idan ya taru za a yi amfani da shi wajen gina masa muhalli. Idan ma mutum yana sauri ne kuma kuɗin da ya ajiye bai kai ya gina masa gidan da yake so da shi ba, bankin yana iya arawa mutum kuɗin da zai gina ko gyara gidansa. Wannan ya sa ake kiran hakan da adashen gata, domin babu wanda zai matsa maka matuƙar za ka ci gaba da ajiye kaso biyu da rabin abin da kake samu ɗin."

"Me zai faru idan na fara ajiya a bankin kuma na mutu ko kuma matsalar rayuwa ta taso na buƙaci kuɗi, shin za su dawo min da kuɗina ne ko na yi asararsu kenan?" Dagacin ne ya tambaya. Da alama ya fara gamsuwa.

"Za ka iya cire kuɗinka a duk lokacin da ka so, kana idan mutuwa ta riski mutum ma bankin zai mayar da kuɗin wa magadansa. Yana ma daga cikin tsarinsu mayarwa da duk mutumin da ya kai shekaru sittin zuwa sama kuɗinsa."

"Na gane, wannan shawarar na karɓe ta. Za ka yi wa mutanen gari wannan bayanin a masallacin juma'a idan Allah ya kai mu. Allah ya maka albarka yaro, babu shakka zuwanka wannan gari alheri ne a gare mu."

Da wannan suka yi sallama. Bayan Saleh ya kama hanya da nufin tafiya ne kuma ya juyo da cewa.

"Ranka ya daɗe, da a ce za ka daina kwanciya da zarar ka ci abinci da ka samu sauƙin tumbin nan naka."

Bai saurari amsar da zai ba shi ba ya tafi.

Tun bayan da aka samar da fitar da tituna, magudanan ruwa da nelayi famfuna da ƙazanta da karɓar tsarin bankin lamuni da mutanen Birkita Wake suka yi, matsalar da suka fuskanta a baya ta zamo tarihi. Kana an samu canji sosai ta fuskar mu'amala da zamantakewa ta mutanen garin. Ya yin da suka zaɓi tura yaransu makaranta da dauƙar dawainiyarsu.

A ɓangaren dagacin garin kuwa sam bai ji daɗin al'amarin ba domin takunkumin da ƙaramar hukuma ta saka masa. inda bai isa ya yanka ko bayar da fili ba tare da saninta ba. Duk lokacin da za a fitar ko yanka fili a garin sai an sanar da ƙaramar hukumar. Ita ce za ta aiko ma'aikacinta (surveyor) ya zo ya fitar kana ta bugawa mutum takarda.

Ƙarshe.

Muhalli, Sutura

Post a Comment

0 Comments