Ticker

6/recent/ticker-posts

Rashin Jini...

Ibrahim Mustapha Habibi (2020). Rashin Jini.... Muhalli, Sutura (Labaran Da Suka Samu Nasara a Gasar Gajerun Labarai a Kan Muhalli Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2020). Darma Digital Prints.

RASHIN JINI…

Na

Ibrahim Mustapha Habibi

Idan Ka Ji Gangami Da Labari

 “Ɗan Samari abin da nike so ka kiyaye a nan shi ne, idan har kana cin ƙasa to ka kiya yi ta suri, kuma ka fahimci cewa bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne,domin haka ka shafawa kanka ruwa a yi maka aski, idan ba haka ba kuwa za ka yi faɗuwar baƙar tasa, domin Idi Akwashe ya fi ƙarfinka” kai ba wai kai ƙaramin ƙwaro ba Akwashe ya fi ƙarfin duk wani ɗa a cikin zuri’arku. Babu wanda ya isa ya zamar mani matsala, saboda haka ka iya bakinka,ka bar maganar santocin unguwar nan da gidajena suka bi a kai, idan kana so ka rayu cikin salama”

Waɗannan maganganu na Alhaji Idi Akwashe ne suka sake dawowa a cikin ƙwaƙwalwata kamar yanzu ne tattaunawar ta faru.

Na runtse idanuwana a hankali tare da cije leɓena na ƙasa, na saki wata ajiyar zuciya. Na sake lafewa a reshen bishiyar da nake kwance, sakamakon motsi da wasu maganganu ƙasa-ƙasa da ake yi a ƙasan bishiyar wanda ban samu nasarar jin abin da ake cewa ba. Dama dai na samu ɗauki daga duhun dare kasantuwar babu hasken farin wata amma dai ban raba ɗaya biyu ba cewa waɗanda suka farmake ni ne a gida da zummar kawar da ni daga doron ƙasa.

Wani irin zafi tare da raɗaɗi ya ratsa jikina har cikin ƙwaƙwalwata sakamakon wani dutsi da na buga da ƙafata a lokacin da nake ta tiƙar gudu, ƙyas da na faɗo, Allah ya taimake ni na ƙara riƙe reshen da nake kwance gam tare da ɗauke numfashina. Zuciyata ta haskomani hoton duk abin da ya faru tamkar a mafarki.

Gudu direban motar ke ta shararawa kamar zai tashi sama,a gefe ɗaya kuma ƙarar horn haɗe da jiniya suna tashi, hakan ne ya sanya masu ababen hawa da ke kan titi suka yi ta sauka suna komawa gefe, suna ba motar jami’an kashe gobara waɗanda galibi aka fi sani da ‘yan kwana-kwana hanya domin su samu nasarar kai ɗauki a in da suka tunkara.

Babu rage gudu kuma babu ɗaga ƙafa direban ya haye wasu tagwayen tsalle-tsalle wato kabarin maitatsine da ke kan hanyar, har sai da motar ta ɗan tangaɗa a gefe kamar za ta faɗi, amma cikin kiyayewar Allah ta dawo daidai kan titin ba ta faɗi ba. Haka direban ya ƙara ba ta wuta ta yi wani irin ƙugi, sannan ya ƙara take motar ya wuce cikin matsanancin gudu,mutanen da ke tsaye a bakin titi duk suka bi motar da na mujiya tare da addu’ar Allah ya tsare.

Direban ya rage gudun motar lokacin da ya shiga wani shatale-tale da zai sa da shi da layin unguwar da ya tunkara domin kashe gobarar da ta tashi a wani gida. A hankali ya shigo layir saboda yanayin hanyar da ke cikin layir duk ta yi tudu da gangara sakamakon zaizayar ruwan sama kasantuwar gaba ɗaya layir babu wata magudanar ruwa kai ko ‘yar lambatu babu, abin da ya sanya ruwa ya ɓata wani kaso na layir.

Motar na ƙara matsawa gab da gidan da wutar gobarar ke ci, take labari ya sha bambam sakamakon wasu manyan gidaje guda uku iri ɗaya da a zahiri wani kaso na gidajen a kan layi yake wato an mamaye layir daga ɓangaren gidajen an cinye layir, daga nan layir ta matse abin da ya haddasa wa motar fire service ɗin kasa wucewa domin kai ɗauki saboda layir ta matse daga saitin gidajen da aka ci layi aka gina su, a ɗayan ɓangaren kuwa ramin masai wato soakaway ne na gidajen mutane da aka gina su a kan layir, waɗanda su ma sun taka muhimmiyar rawa wurin ƙara wa layir ƙunci.

Babu gwauro da marin da ba a kai ba amma sakamakon layir da aka cinye babbar motar fire service ba ta samu nasarar wucewa domin zuwa gidan da gobarar ke ci domin kai ɗauki ba. Direban ya buɗe motar ya fito ransa ɓace ya ƙura ma layir ido da a halin yanzu zai fi dacewa a kirata da lungu maimakon layi na ‘yan wasu daƙiƙu, sannan ya yi wani tsaki ya tayar da motar ya juya.

Mutane daga ko’ina sun himmatu domin kawo gudummuwa domin kashe gobarar da ta kama a gidan Malam Muntari wanda wutar har ta tsallaka gidan maƙwabtansa da ke jere da gidan,wajen babu abin da kake ji sai hayaniyar jama’ar da suka kawo ɗauki, ya yin da wutar ke ƙara sama kamar ana watsa mata fetur, a gefe guda sai koke-koken yara ƙanana da mata ake ji, wasu kuma ba su fita hayyacinsu ba, sun dai dage da sallallami.

Mutane sun yi rawar gani wajen kashe gobarar da ‘yan kwana-kwana ba su samu damar kashe wa ba sakamakon cin layir da aka yi, kuma sun nuna alhininsu ga abin da ya faru,ya yin da kowa bakinsa ke Allah-wadai da tofin allah-tsine ga cin layir unguwar da aka yi wato gidajen da aka gina su a kan layi da soakaway abin da ya zama musabbabin rashin samun nasarar daƙile gobarar da ta faru a unguwar tun farko. An samu nasarar kiran motar asibiti ta hanyar wani ma’aikacin jinya mutumin kirki Malam Ibrahim da ke nan unguwarmu, amma an samu cikas wurin ɗaukar majinyatan da suka samu ƙunar wuta sakamakon rashin yalwar hanyar da motar za ta biyo sai dai ta tsaya daga baya aka cicciɓi majinyatan aka saka su a motar, mahaifiyarmu ma sai dai aka tattallafota aka fice saitin gidajenmu sannan aka samu motar da za a kaita asibiti.

Ba wannan ne karo na farko da motar asibiti ke kasa zuwa wasu gidajen ba, saboda yadda Alhaji Idi Akwashe ya kwashe duk layir, amma bai taɓa fahimtar cewa ba daidai ba ne cin santoci da yake yi, kuma babu wanda ya taɓa tanka masa, amma da yardar Allah daga yau wannan shirun ya ƙare. Wannan shi ne abin da na sha alwashi duk da tsoransa da ake yi sakamakon rashin kirki da rashin tausayi, sannan yana taƙama da kuɗi domin gadara da biyan buƙatarsa, sannann mutum ne mai amfani da ‘yan daba domin su yi mashi maganin duk wanda ya zo bakin iyakar gonarsa, amma yau kam sai dai duk abin da zai faru ya faru, domin Akwashe ya zamar wa mutanen unguwarmu alaƙaƙai ba iya nan ba ma shi ne baƙin bunu.

 *** **** ***

Bai fi minti biyar da zamanmu ba sai ga wasu majinyata an shigo da su sun ƙone sosai, cikin gaggawa muka kama aka shiga da su abin gwanin ban tausayi. Jim kaɗan da shiga da su muka gaisa da ɗaya daga cikin waɗanda suka kawo su kasantuwar abokina ne, na san shi, na labarta masa abin da ya faru garemu da abin da nake shirin yi, shi ma ya ƙarfafa mani guiwa ya ce zai ba ni duk wani taimako. Nan yake faɗa mani cewa ‘yan uwan matar wansa ne, iska ne ya kaɗa manyan wayoyin wutar lantarki sakamakon gidansu na ƙarƙashin manyan turakun wutar lantarki sai tartsatsin wuta ya zubo abin da ya zama silar kamawar wuta a gidan suna cikin gidan wutar ta kama da ƙyar aka cece su, muka haɗe baki da cewa “akwai yiwuwar dama a yi da na sani a gidan da ke ƙarƙashin high tension wire”, yayan nasa ya fito yake sanar da mu matar gidan da ta fi ƙonewa ta rasu.

Fitowar wata ma’aikaciyar jinya ne ya kawo ƙarshen shirun da muka yi na alhinin mutuwar matar. Ta yi sallama, muka amsa a tare. “Don Allah wane ne Saifullahi?” ta faɗa tana yin ƙasa da idanuwanta. Cikin murya ƙasa-ƙasa na ce mata “gani nan” ta miƙo mani wata takarda ɗauke da sunayen wasu allurai da magunguna, ta ce “don Allah waɗannan kayayyakin ake so a kawo mana yanzu ake buƙatarsu” tana gama faɗar saƙon ta juya ta nufi cikin ɗakin da aka shigar da mahaifiyarmu da sauri.

Babu ɓata lokaci na sayo duk abin da aka rubuta na kawo kamar yadda aka buƙata.

Jim kaɗan ma’aikaciyar jinyar nan ta sake fitowa amma a wannan lokacin fuskarta ɗauke da annuri take sanar da ni cewa mahaifiyarmu ta farfaɗo, amma tana bukatar hutu kuma ba a yarjewa kowa shiga inda take ba. Na yi ajiyar zuciya bayan na katse saƙar zucin da nake yi, na yi wa Allah godiya.Wani ƙanina na kira na sanar da shi zan je gidan Alhaji Idi Akwashe domin yi wa tufkar hanci, saboda haka ya kula da mahaifiyarmu da duk abin da ake buƙata.

Na yi nasarar samun Akwashe gida mun tattauna amma ba cikin daɗin rai ba a ƙarshe muka rabu dutse hannun riga tare da yi mani barazana da gargaɗi, ya yin da na ce duk abin da ya iya ya yi. Duk da haka ban haƙura ba sai da na kai ƙorafi a hukumar kula da tsara birane dangane da yadda aka cinye layin mu da Akwashe ya yi, abin da ke barazana da lafiya da rayukan mutanen unguwarmu, sun karɓi ƙorafina sun yi iyakar ƙoƙarin su domin a yi sasanci abin ya ci tura, a ƙarshe dai suka yanke hukuncin tura mu kotu, kasantuwar na samu labarin Alhaji Akwashe ya ɗauki lauya, ni ma na shiga na fita na samu haɗuwa da abokina da muka haɗu asibiti wanda suka kawo marasa lafiyar da gidansu ke ƙarƙashin high tension line wato Aliyu Dabo kasantuwar shi lauya, kuma ya sha alwashin tsaya mani a shari’ar da za mu yi da Akwashe. Ana gobe za a fara shari’ar ne Akwashe ya aiko da ‘yan daba da zummar su kawar da ni daga doran ƙasa.

Da misalin ƙarfe uku na dare na ji an diro cikin harabar gidan da nake kwance na leƙa ta taga na gansu da makamai duk sun ɓoye fuskarsu, kafin su kai ga shigowa, Allah ya taimake ni na bi ta tagar baya, na kama katanga na dire sannan suka farga suka biyo ni, ga shi cikin dare babu hasken farin wata, har na samu na haye saman wata bishiya har Allah ya ƙaddara suka zo wurin suka duba amma ba su samu nasarar ganina ba.

Ƙarar kiran sallar assalatu da na ji ladani ya ambata, ya kawo ƙarshen dogon tunanin da na daɗe ina yi na abin da ya zama tushen al’amarin. Duk da jikina akwai tsami, na yi yunƙurin saukowa daga saman bishiyar, burina na iso gari ba tare da na haɗu da masu nemana ba, domin samun halin halartar kotu domin yau za a fara shari’armu da Idi Akwashe.

*** **** ****

 Walƙiya Alamun Hadari

Alƙali ya ƙarasa yanke hukuncin wata shari’ar ɓarayi, sannan mai karanto ƙara, ya karanto shari’armu, mai karanto shari’a ya ce “shari’a ta gaba ita ce shari’a da ta shafi cin santocin unguwa da Saifullahi Mustapha ya shigar yana ƙarar Alhaji Idi Akwashe, da zargin ya cinye masu layi, kuma hakan na barazana da lafiyarsu da dukiyoyinsu,ƙarewa da ƙarau matsugunninsu da rayuwarsu”.

Bayan mai karanto shari’ar ya gama,ya koma mazaunin sa, kaɗa kai da Idi Akwashe ya yi muka haɗa ido, cikin mamaki yake kallona a tsammaninsa an riga an shafe babina daga doron ƙasa tunda ya aika a kawar da ni, sai dai abin da ya mance “zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana mazuru ana shaho sai ya yi.

Farko lauyan wanda ake ƙara wato Alhaji Idi Akwashe shi ya fara gabatar da kansa ya ce “Sunana Barista Umar Faruk, lauya mai kare wanda ake ƙara Alhaji Idi Akwashe” ya ɗan jinkirta, sannan ya ci gaba da cewa “dangane da abin da ake zargin wanda ake ƙara, mai girma mai shari’a, wannan zance ne marar tushe saboda kuwa, ba haka nan aka gina gidajen ba, domin akwai takardar yarjejeniyar sayen duk filin da aka gina, sannan akwai takardun izinin gina gidajen da aka samu daga hukumar tsara birane, da duk wani abu da ake buƙata, saboda haka wanann zargi sam babu gaskiya a ciki, domin babu wata layi da aka ci aka yi gini a kai,ina roƙon wannan kotu da ta yi watsi da wannan shari’a domin hassada ce kawai da ganin ƙyashi ake nunawa ga wanda ake ƙara”.

Cikin murmushi lauyana ya miƙe tsaye,sannan ya fara tafiya a hankali ya tsaya,sannan ya ce “Sunana Barista Aliyu Dabo, lauyan mai ƙara wato Saifullahi Mustapha “surutu ƙasa-ƙasa ya fara cika kotun kafin kowa ya kama kansa.

Lauya Aliyu Dabo ya ce “maigirma mai shari’a ina so a ba ni dama na gabatar wa kotu da hujjoji da dalilai cewa wanda ake zargi ya aikata abin da ake tuhumarsa da shi ba ƙyashin sa ko hassadar sa ake yi ba, kamar yadda lauya ya ce”

Alƙali ya ce “eh an ba ka dama”

Ya ce “na gode mai shari’a”

Lauyan ya fara da cewa “maigirma mai shari’a ina ƙalubalantar ɗan uwana Barista Umar Faruk kan cewa da ya yi,wanda ake tuhuma bai aikata laifin da ake tuhumarsa da shi ba, ina so Barista ya tuna idan ya manta cewa ko da Alhaji Idi Akwashe ya samu takardar izinin gina gidaje daga hukuma ko hukumomin da ke da alhakin yin hakan,to gine-ginen da ya yi a unguwar ya saɓa wa tsari da ƙa’idar Hukumar tsara Birane Saboda a tsarin hukumar ga yadda ake so a gina gidaje a hukumance wato Resdential Layout,ya alla a unguwanni masu yawa ko cinkoson mutane wato High Density Areas ko unguwanni masu ƙarancin mutane inda babu cinkoson al’umma wato Low Density Areas, inda ke da nau’in gidaje irin GRA da Estate da Lowcost ko Quaters da sauransu”

Kotun ta yi tsit ba ka jin muryar kowa sai ta Barista Aliyu da ke ta zazzago ruwan hujjoji. Ya ɗan tsagaita sannan ya ci gaba da cewa “a hukumance ana fitar da filaye masu fadin mita 100x100 wanda a takun ƙafa a tsawo da faɗi yake kamawa ƙafa 335 a tsawo da faɗi, ko kuma mai faɗin mita 100x50 wato fili da a takun ƙafa tsawonsa ƙafa 335 faɗinsa kuma 167, sannan ana yanka fili mai faɗin mita 50x50, wanda a takun ƙafa tsawonsa da faɗinsa 167 ne, duk wani awo wanda ba wannan ba to awan ‘yan kasuwa ne waɗanda suke so fili ya yi masu auki wato masu yin awon igiya.

Sannan ana barin layi da faɗinta ya kai mita 15 daidai da ƙafa 50 a ƙalla a karon farko cikin mita 15 ɗin ne za a cire mita 1 wanda ya ke daidai da ƙafa 3 domin fitar da kwatar ruwa ta gidaje a kowane gefe, sannan a cire mita 1.5 wato ƙafa 5 a kowane ɓangare domin rufe bututun ruwa da turakun wutar lantarki, idan duk an yi hakan a ƙalla layi ƙaranci za ta kasance mita 10 wato ƙafa 35 na takun ƙafa, wanda asalin faɗin santocin unguwar ma sun fi haka saboda sabuwar unguwa ce,kuma Hukuma ce ta yanka filayen, amma Alhaji Akwashe duk ya kwashe santocin unguwar ya jefa su cikin gidajensa, unguwar ta koma rabi da rabi, wani wuri layi wani wuri lungu, mai girma mai shari’a wannan ya sanya motar jami’an kashe gobara ta kasa kai ɗauki kan lokaci a gidajen da aka yi gobara abin da ya zama sanadiyyar ƙaruwar gidan da gobarar ta ci daga ɗaya suka zama uku, wanda hakan ya zama barazana ga lafiya da dukiyoyi da rayukan mutanen da ke rayuwa a yankin”.

Barista Aliyu ya ci gaba da cewa “maigirma mai shari’a benen da Alhaji Akwashe ya yi a gidansa wanda yana kallon kusan duk wainar da ake toyawa a gidajen mutanen da ke gewaye da su,wanda hakan yana cutar da su,hakan kuwa ya saɓa wa ƙa’idar zamantakewa da tsarin Hukumar samar da gidaje da Hukumar tsara birane, domin kowane nau’i ko rukunin gidaje akwai fasalinsu da yadda ake tsara su, kamar yadda haramun ne a gina gidan ƙasa a rukunin gidaje wato Estate, haka bai halatta ba a gina gidan bene a tsakanin gidajen masu ƙaramin ƙarfi kamar yadda Akwashe ya yi duk da cewa filayen unguwar hukuma ce ta bayar da su a matsayi ramuwar gidajen ‘yan unguwar da gwamnati ta karɓa lokacin aikin hanya, saboda haka su asalin ‘yan unguwar suna da takardar haƙƙin mallaka shi kuwa Akwashe a hannun wasu ya saya shi ya sa yake da takardar yarjejeniyar saye,amma tsarin gidajen da ke akwai ba irin gidajen da ake yin bene ba ne saboda haka an karya doka an kuma saɓa ƙa’ida, saboda haka mai girma mai shari’a ina fatan wannan kotu mai alfarma da ta sanya a rushe wannan ginin benen.

Barista Aliyu ya ci gaba da cewa “maigirma mai shari’a baya ga waɗannan saɓa ƙa’ida da Akwashe ya yi, na cin santocin da ya yi ya haifar wa al’ummar unguwar matsaloli da suke shafar lafiyarsu da rayuwarsu kamar haka: cin santocin ya sabbaba lalacewar muhalli, muhalli ya koma marar kyau wanda a da ba haka ya ke ba, sannan ya cinye wuraren da za a fitar da magudanan ruwa abin da zai iya jaza ambaliyar ruwa daga yanzu zuwa kowane lokaci, kuma cinye santocin ya sanya babu kyakkyawar hanyar da ababen hawa za su shigo cikin unguwar abin da ya jaza motar jami’an kashe gobara kasa wuce wa domin kai ɗauki a gidan da aka yi gobara abin da ya sanya abin har ya ta’azzara a ƙarshe lafiya ta taɓu kuma aka yi asarar dukiya. Saboda haka mai girma mai shari’a da waɗannan dalilai nike kira da wannan kotu da ta yi nazarin hujjoji da dalilan da na kawo,ta yi hukunci bisa adalci a doron dokokin ƙasa.

Barista Aliyu ya yi godiya ya samu wuri ya zauna. Alƙali ya duƙar da kai ya ɗan daɗe yana rubutu sannan ya ɗago kansa, ya tambayi Barista Umar Faruk ko yana da wani abu da zai ce,cikin rashin ƙarfin jiki da kuzari ya tashi ya ce “ a’a ya mai shari’a”, Alƙali ya ci gaba da rubutu, sannan ya ce “ kotu ta kafa kwamiti domin ziyartar inda abin ya faru domin a kawo rahoto kafin yanke hukunci, kuma a tabbatar da gaskiya ko akasin abin da lauya ya faɗa.

Kwamitin ya ƙunshi wakili daga kotu da wakili daga hukumar tsara birane,sai kuma jami’in tsaro sai kuma lauyan mai ƙara da lauyan wanda ake ƙara. Saboda haka kotu ta ɗage sauraren wannan shari’a sai nan da makonni biyu masu zuwa,lokacin da kwamitin za su zo da cikakken rahoto,kuma a ranar za a yanke hukunci”

Alƙali ya fara tashi ya fice a hankali muka rufa masa baya tare da kaurewar hayaniya kowa na tofa albarkacin bakinsa. A bakin ƙofar kotu muka haɗu da Barista Aliyu muka gaisa cikin farin ciki daga nan muka bar harabar kotun.

**** **** ****

Rashin Sani Ya fi Dare Duhu

Kamar ana biki ko wani shagali a layinmu, mutane ne kashi-kashi musamman ma daga saitin gidan malam Muntari zuwa ƙofar gidanmu wanda su ne gidajen da gobarar ta shafa, ban san me ake tattaunawa ba, amma ina ƙarasawa wurin na fahimci suna bitar abin da ya faru a kotu ne da yadda shari’ar ta wakana da dama suna ganin tabbas a shari’ar nan walƙiya ce alamun hadari.

Bayan na gaishe da su malam Muntari da sauran wasu dattawan unguwar, sai malam Muntari ya ce mani “ku ne kuka san abubuwan da ke faruwa cikin ƙasa da ma al’amuran yau da kullum,tun kafin faruwar gobarar nan da watanni uku na nemi bashi a bankina domin yin wasu hidimomi, ban samu ba ga shi yanzu kuma ga abin da ya faru,wanda yanzu so nake na gyara ɓangarorin da wuta ta yi ɓarna,shi ne aka ce akwai wani banki da ke ba da rance domin gyaran gida nake so in ji ya abin yake”

Na yi ɗan murmushi sannan na cewa Malam Muntari “eh haka ne Malam”sannan na ci gaba da cewa “idan aka ce bashin gyaran gida bankin ke bayar wa kamar an tauye ayyukansa,domin ayyukan suna da yawa”

Malam Usman wanda tunda aka fara maganar bai ce kanzil ba, ya ce “to yanzu ina ganin abin da ya dace Saifullahi wuri za mu samu mu zauna ka yi mana gamsasshen bayani dangane da lamarin bankin nan idan mun ji yadda abin yake sai mutum ya tunkari tudun dafawa ya watsar da ‘yan rainin wayon bankunan nan da ke ja wa mutane rai, idan za su ba mutum bashi kamar za su ba shi kyauta”, malam Muntari ya ce kai muke saurare” ni kuwa na fara da cewa “ farko dai wannan banki ba wani sabon banki ba ne,hasali akwai shi a ƙasar nan tun kafin ‘yancin kai,sunan bankin Federal Mortgage Bank of Nigeria wato Bankin Bada Lamunin Gina Gidaje Na Ƙasa, an kafa shi ne a shekarar 1956 a lokacin ana kiransa Nigerian Building Society.Na ɗan jinkirta sannan na ci gaba da cewa, yana ayyuka da suka shafi muhalli da bada jingina da bada lamunin gina gidaje har a shekara ta 1973 aka canza masa suna zuwa bankin bada lamunin gina gidaje na ƙasa (FMBN).

 Haka bankin ya ci gaba da hidimar bada rancen gina gidaje da abin da ya shafi jingina da lamuni har zuwa shekara ta 1992 lokacin a ƙarƙashin doka ta ƙasa doka ta 3 ta gwamnatin tarayya wadda aka canja bayan dawowa mulkin siya sa da act no.3 of national assembly a ƙarƙashinta ne aka ƙirƙiro wani Asusun Adashen Gina Gidaje Na ƙasa ko ace Adashen Gata Na Gina Gidaje wato National Housing Fund Scheme, kuma a wannan tsari kowane ɗan ƙasa yana iya amfana da shi”

“Ta wace hanya ke nan?” cewar malam Usman “idan mutum ma’aikacin gwamati ne a Ƙaramar hukuma ko jiha ko tarayya,zai yi rijista da bankin,su kuma za su sanya shi tsarin aiwatarwa wato moblization,daga abin da yake samu na albashin sa za a ringa cirar kashi biyu da ɗigo biyar cikin ɗari 2.5%, idan mutum ya yi watanni 6 da fara aiki kuma yana zuba 2.5% zai iya neman bashi kuma za a ba shi,sannan ya yin biya ba a ɗaukar abin da ya wuce 1/3 na albashin mutum”

Malam Usman ya ce “Saifullahi akwai wasu tsare-tsare dangane da mallakar muhalli da bankin ya tanadar ga ‘yan ƙasa?” na ce “eh Malam”

Na farko dai akwai bashin asusun adashen gata na gina gidaje wato National Housing Fund Loan,a wannan tsarin mai ajiya zai samu gida a rukunin gidaje wato Estate wanda ɗan kwangila ko kuma shi bankin ya bada kuɗi aka gina,idan mai ajiya ya samu takardar nema ko gurbin amincewa, to bankin zai saya wa mai ajiya gida har ya biya a hankali ya danganta da yanayin gidan da kuɗin gidan saboda ya kasance yana ajiya a asusun.

Hanya ta biyu kuwa ita ce Bashin Gina Gidaje Na Keɓance,wanda ya shafi mutum ɗaya wato Individual Construction Loan wanda shi wannan idan mutum yana da filinsa wanda yana da takardar shaidar mallaka da takardar zanen gida da takardar ƙididdigar abin da zai kashe ya ida gidan idan ya fara ko ya gina gidan idan ba a fara ginawa ba kuma yana zubin adashen gata na asusun gina gidaje wanda yake da waɗannan zai iya neman bashi na kuɗi har naira miliyan 15, kuma banki zai ba shi kudin ya gina gidan da yake so, sai dai mutum zai sanya kashi goma cikin ɗari na kuɗin da yake nema 10% banki kuma zai sanya mashi kaso casa’in cikin ɗari 90%. Sannan zai iya ɗaukar tsawon shekaru 30 yana biyan wannan rance ko bashi, wanda hakan shi ne lokaci mafi tsawo na biyan kuɗin.

Sannan akwai bashin gina gidaje na ƙungiyoyin haɗa kai wato Cooperative Housing Loan duk ƙugiyar da suka yi rijista da FMBN suna iya neman rancen gina gida ga bankin bada lamunin gina gidaje ya ba su,misali,za su gabatar wa banki cewa suna da fili da zai gina gida kaza,kuma kowane gida zai ci kuɗi kaza,sai banki ya basu kuɗin su gina gidajen kuma ‘yan ƙungiya ne za a mallakawa wanda za a ringa biyan kuɗin a hankali gida ya zama mallakin kowane ɗan ƙungiya.

Sai kuma Bashin Gyaran Muhalli wato Home Renovation Loan, wanda shi a wannan tsari mai ajiya na iya neman kuɗi da suka kai har naira miliyan ɗaya domin gyara muhallinsa ya zama muhalli mai kyau wanda zai biya wannan miliyan ɗaya a cikin watanni 60 wato shekaru 5.

Na miƙe da zummar tafiya na ce “to Malam kun ji wannan shi ne abin da zan iya cewa dangane da bankin nan”.

 **** **** ****

Rashin Jini Rashin Tsagawa

Yau makonni biyu da alƙali ya sanya domin ci gaba da sauraren shari’armu sun cika, kuma a kotu kowa ya zo, ba tare da ɓata lokaci ba,alƙali ya nemi shugaban kwamitin da ya kafa domin binciko gaskiyar lamarin abin da lauya Aliyu ya gabatar. Shugaban kwamiti ya gabatar wa alƙali cikakken rahoton binciken da suka yi babu saɓani da abin da lauya ya gabatar.

Bayan alƙali ya ɗauki tsawon lokaci yana rubutu. Sai ya ɗago kansa ya ce “ wannan kotu ta gamsu da rahoton da kwamitin da ta kafa ya gabatar,saboda haka wannan kotu ta yanke hukunci tare da bada umurnin cewa duk soakway da ke waje da duk gine-ginen gidajen Alhaji Idi Akwashe da aka yi su a kan santoci a cire su duk santocin unguwar su kasance da faɗin mita 10, wato takun kafa 35, sannan a sauke benen cikin gidan,domin ba unguwar da ya halatta ba ne a yi benen, domin shi kaɗai ne a tsakiyar gidajen mutane.

Har alƙali ya gama karanto hukunci babu wanda ya yi ƙwaƙƙwaran motsi,na juya na kalli inda Alhaji Idi Akwashe yake ya duƙar da kansa ƙasa a cikin zuciyata na ji wani irin daɗi na ce “kowa ya ƙi ji ba ya ƙi gani ba, daman RASHIN JINI RASHIN TSAGAWA”

Alƙali ya ci gaba da cewa “ Manzon Allah SAW ya ce “Wanda ya yi imani da Allah da ranar tashin alƙiyama ya girmama maƙwabcinsa” girmama maƙwabci a nan na nufin kar a zalunce shi kar a cutar da shi. Saboda haka yin abin da zai cutar da maƙwabci rashin girmama shi ne,kuma rashin bin koyarwar manzon Allah (SAW) ne. Sannan Sa’id Ɗan Zaidu Ɗan Amru Ɗan Naufal ya ce “Manzon Allah (SAW) ya ce “Duk wanda ya ɗebi daidai da kamu guda na ƙasa za a ɗauro mashi ita daga ƙasa ta baƙwai ranar ƙiyama”. Alƙali ya ci gaba da cewa “kamu guda shi ne taku guda wato inci sha biyu a ma’aunin tape wato taku guda na ƙafa, saboda haka duk mai cin layi ya san abin da yake ci wa kansa,ba wai Idi Akwashe ba kawai, saboda haka kotu ta sake maida ‘yan kwamitin da ta kafa don su sanya ido su tabbatar an zartar da hukuncin da ta yanke.

*** **** ***

Kwamitan da kotu ta wakilta sun tsaya kai da fata har sai da aka zartar da abin da aka sanya su,yanzu unguwarmu santoci sun samu babu takura,duk masu soakway kan santoci sun cire shi, kowace irin mota tana iya wucewa a santocin babu takura. An sauke benen gidan Akwashe da duk gine-ginen gidajensa da ke kan layi, rayuwar ‘yan unguwarmu ta na ƙara daɗi, shi kuwa ya fara fuskantar ƙalubalen rayuwa,hasali ma ya tashi daga unguwar.

Su Malam Muntari da Malam Usman duk sun samu bashin gyaran gida daga bankin bada lamunin gina gidaje kowa ya gyara gidansa kamar ba ayi gobara ba,da suka zo yin fenti har da gidanmu suka haɗa kasantuwar kawunmu ya riga ya gyara gidanmu,wasu kuwa sun sayi gidaje sun huta da matsalar gidan haya.

Muna tsaye tare da wani abokina mai suna Salim wanda Mawaƙi ne wanda yana wurin lokacin da nake yi wa su Malam Muntari bayani akan banki,muna tattauna yadda muka samu nasarar shari’ar ya ce “amma fa Akwashe ya ji hukunci kamar Barcelona a hannun Bayern Munich,ashe daman RASHIN JINI RASHIN TSAGAWA” muka yi murmushi muka tafa.

Sai ya ce mani “ka ji sanarwar da gwamnatin jihar nan ta fitar?” na ce “a’a” ya ce “gwamna ya ce “duk wani mai gida a kan hanyar ruwa ko bakin tafki ko a ƙarƙashin manyan layukan wutar lantarki ko ƙarƙashin ƙarafunan sabis ko kusa da kamfanoni su tashi za a basu filaye a tallafa masu su gina gidaje domin kariyar lafiyarsu da dukiyoyinsu da rayukansu”, sannan ya ce “ matsalar ambaliyar ruwa ta yi yawa bisa ga rahotannin da suka samu tsakanin ƙungiyoyi da hukumomin da abin ya shafa, saboda haka ya ba da umarnin tona magudanan ruwa inda suka toshe da samar da su a uguwannin da babu su, sannan an hana gini da fito da soakway a kan santoci domin inganta muhalli sannan an hana yanka filaye ‘yan ƙuƙut, saboda ana samun sanƙarau a gidajen da suka matse babu wurin shaƙar nagartacciyar iska a lokacin zafi, sannan ya ja kunnen masu filaye da su daina haɗa kai da dillalai su na yanka fili ba bisa ƙa’idar gwamnati ba”, kai amma Allah ya saka masa da alkhairi, na ce “ƙorafin mu ya karɓu ke nan”

Haka ne “Dodon Idi Akwashe” ya ci gaba da yi mani kirari

“Gugar ƙarfe sha kwaramniya don talakawa,

Ɗan tsiron da Allah ke so ko babu ruwa zai tohu,

Kainuwa dashen Allah ba dashen mutane ba”

Na ce “ ya isa haka nan, yau kirari kake ji ina waƙar? Sai Salim ya kashe murya ya fara rero waƙa.

Ø Muhalli shi ne ginshiƙi,

Na farin cikin duk rayuwa.

Ø Wasu sun kira shi da sutura,

Wasu sun ce shi ne rayuwa.

Ø Idan gida na yalwace,

Za a zauna ba wata damuwa.

Ø Idan kuwa ya zam ƙuntace,

Za a rayu amma fa da damuwa.

Ø Idan ba magudanan ruwa,

Akwai matsala fa a unguwa.

Ø Matsalolin dai na da yawa,

Daga ciki ambaliyar ruwa.

Ø Idan santoci babu su,

Muhalli ba ya da karɓuwa.

Ø Gini in da bai dace ba,

Yana sa a rasa rayuwa.

Ø FMBN ya himmatu,

Domin ingantar rayuwa.

Ø Asusun NHF scheme,

Shi ne tushen janye damuwa.

Ø Bashi na gidaje ko kuɗi,

Domin rayuwar annashuwa.

Ø Individual loan ko estate,

Home renovation ba damuwa.

Ø NHF loan da cooperative,

Matakin inganta rayuwa.

Ø Rent-to-own system in ka duba,

Shi ma ai ya samu karɓuwa.

Kafin ya idar da waƙar na katse shi na ce wannan kabarta za ta fi daɗi idan an je studio, ya ce “to shi ke nan yanzu mene ne sabon labari?” Na ce “yanzu kuma masu cin iyakar maƙabarta da filin maƙabarta za a tunkara tunda an gama da masu cin santocin unguwa” ya ce “ina tare da kai har zuwa ƙarshen wannan taƙaddamar”.

  

Muhalli, Sutura

Post a Comment

0 Comments