Bello Sambo (2020). Kowa Ya Bar Gida. Muhalli, Sutura (Labaran Da Suka Samu Nasara a Gasar Gajerun Labarai a Kan Muhalli Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2020). Darma Digital Prints.
KOWA YA BAR GIDA
Na
Bello Sambo
Babban zauren taron na Event House, a cike y ke da
mahalarta, ta ko’ina ka duba jama’a ne, ya yin da a can saman dandamali kuma
manyan baƙi ne, da shugabannin taron a zaune. Daga bayansu kuwa wani babban
ƙyalle ne, da ke ɗauke da manyan rubutu kamar haka:
Barka da zuwa bikin bayar da takardar girmamawa ga
ƙungiyar Muhallinka Alfarmarka
Rana: Asabar 21,
ga Maris, 2020
Lokaci: Ƙarfe 10 na safe
Wuri: Ɗakin taro
na Event House
Shugabannin taron sun yi bayanai da dalilan shirya taron domin karramawar
ƙungiyar, haka manyan baƙi mahalarta taron, duk sun tofa albarkacin bakunansu.
A ƙarshe bayan jama’a da dama sun gama jawabai, sai aka kira shugaban ƙungiyar
Malam Hamza Sa’idu, kuma wanda ya ƙirƙiri ƙungiyar, da ya fito ya yi wa
mahalartan, bayanin dalilan da suka sa shi ya ƙirƙiri wannan ƙungiyar, da
aiyukanta suke da tarin fa’idoji da alfanu, ga al’ummar wannan gari.
A lokacin da malam Hamza, ya fito ya
hau dandalin taron, aka ba shi abin magana, sai aka ɗauki tafi raf!Raf!!Raf!!!
Bayan an natsu, sai ya yi gyaran murya sannan ya ce,
“Iyayen taro, da manyan baƙi da
sauran jama’a mahalarta maza da mata, ina ma ku sallama irin ta addinin
Musulunci.” Bayan an amsa, sai ya ci gaba, “ Haƙiƙa an yi man babbar tambaya da
aka buƙaci in fadi dalilan da suka sa na ƙirƙiri ƙungiyar MUHALLINKA
ALFARMARKA. Tabbas mun sani babu wani abu da ke faruwa ba tare da wani dalili
na fili, ko na ɓoye ba. Domin bayyana maku dalilin assasa wannan ƙungiyar zan ɗauke
ku zuwa shekaru uku baya.
Sunana Hamza Sa’idu, magidanci mai
mata ɗaya da yara biyu, ƙaramin ma’aikacin gwamnati ne ni. Ina zaune ne a gidan
haya, kasancewar ban da muhalli nawa na kaina. Sai dai a lokacin ina da fili da
nake gina nawa gidan, amma zamowa ta maras nauyin aljihu, da kuma matsalolin da
na riƙa fuskanta a gidajen haya, ya sa aikin ke tafiyar hawainiya, har ya ci
tsawon lokaci bai kammalu ba.
Na mallaki filin ne tun kafin
aurena, sakamakon shawarar da mahaifina ya ban, cewa a wannan lokaci matashi
kamata ya yi kafin ya yi aure, in da hali ya mallaki gidansa, in hakan bai samu
ba to a ƙalla ya mallaki ko fili ne, bayan ya yi auren sai ya ci gaba da aikin
ginin a hankali, domin ya kauce wa tarnaƙin gidan haya. Saboda haka sai wannan
shawarar ta zaburar da ni, na sayi fili a wata sabuwar unguwa da aka yanka
filaye. Bayan mallakar filin ne, wani aminina ya ban shawarar, in nemo wani
masanin ilimin gine-gine (wato building engineer), ya fitar man da taswirar
tsarin ginin da zan yi, dan in gina muhalli mai inganci. Ban yi wasa da wannan
shawarar tasa ba, domin muhimmancinta, na nemo wani injiniya, ya fitar man da
tsarin ginin (building plan), da zan yi mai inganci, daidai da tattalin
arzikina. Bayan ya fitar man ne na ci gaba da bin tsarin da ya fitar, saboda
ƙarancin walwalar kuɗi a tattare da ni, da matsalolin da na riƙa fuskanta daga
masu gidajen haya, sai ya zama aikin na tafiya a sannu, amma hakan bai dame ni
ba sosai, domin na san aikin na tafiya da inganci. Na fara wannan aikin bayan
aurena da shekaru biyu, amma sai da aikin ya lashe wasu shekaru uku, sannan ya
kai matakin yin rufi. A lokacin da na sayi filin nawa, ba wani gini a wajen,
amma a tsakanin waɗannan shekaru, duk kusan filayen da ke rukunin an gine su,
sun zama gidaje har mutane sun tare a cikinsu.
A tsakanin shekaru biyar da na yi da
aure, na zauna gidajen haya har guda biyar.
Gidan farko da na zauna haya, gidan
wata mace ce mai mita da yawan binbini. Takurawarta ta kai maƙura, ba ma yin
cikakken wata sai ta zo gidan, ta yi ta dube-duben bangwaye da daɓen gidan, wai
ta ga ko za mu kashe mata gida. Amma a haka za ta gama dube-duben ta tafi ba
tare da ta samu abun yin ƙorafi a kai ba. Sannan idan ya zamana saura kamar
wata biyu, kuɗin hayar da na bayar su ƙare, sai ta turo man dillalinta, wai ya
yi man tuni. Da kuma ya rage saura wata ɗaya, sai ta zo da kanta tunasar da ni
lokacin biyan kuɗi fa ya matso. Duk da cewa tun a farkon kama gidan, sai da aka
sanya wannan sharaɗin, a cikin takardar yarjejeniyar kama gidan, cewar da
lokaci ya yi zan biya kuɗi, ba ta son jinkiri, wai ba ta son a yi mata wasa da
biyan kuɗi. Na kuma amince a hakan, sai dai ga alamu hakan bai gamsar da ita
ba, dole sai ta yi tunasarwar take samun gamsuwa. Ga gidan ba wani wadatacce
ba, ɗakuna biyu ne kacal sai dan ƙaramin madafar abinci (kitching), da kewaye
(bayi), babu wadatar filin tsakar gida, amma a haka muke zaune cikin haƙuri,
tun da ba mu da shi, idan ma mun ce mu tashi mu canza wani, ba mu san shi kuma
wace irn matsalar za mu tarar a can ba, saboda masu hikimar zance sun ce,
“Sanin hali kan sa a ci maganin zama da mutum.” Sai mu ka ci maganin zama da ita.
Bayan na cika shekaru biyu a gidan,
zan sake biyan kuɗin shekara ta uku, aka samu akasin da ya jawo tashina daga
gidan. Nakuda ce ta taso wa matata abun ya zo da tangarɗar da har sai da aka
kwantar da ita asibiti, aka yi mata aiki aka fiddo jaririn, shi ma kuma ya zo
da matsalar da sai da aka kwantar da su. Duk ‘yan kuɗin da na tanada domin
wannan haihuwar sai da suka ƙare, ƙarshe dole ta sa na taɓa kuɗin hayar da zan
bayar, domin ceto lafiyar iyalaina, wacce a lokacin ta fiye man komai. Bayan
iyalina sun shafe kwanaki tara a asibiti, aka sallamo su, ‘yan kuɗin da suka
rage man, da gudummuwoyin da na samu daga ‘yan uwa da abokan arzuƙa, na harhaɗa
na sawo ragon suna, aka yi sunan yaron. Bayan mako wa’adin biyan kuɗi ya yi,
ban bayar ba saboda ban da su.
Da yammacin ranar sai ga Sadi,
dillalin Hajiya ya zo karɓar kuɗin haya, na faɗa masa ya gaya wa Hajiya dan
Allah ta yi haƙuri zan kawo mata, ta ɗan ƙara man lokaci, iyalina ce ta haihu
kuma abun ya zo da matsala, sai da aka kwantar da su asibiti, duka yau kwanansu
bakwai da sallamowa. Washegari misalin shida da rabi na ji ana bugo man gida
kamar za a ɓalle ƙyauren, cikin firgici na je, na ce, “kai! Wai waye ke bugo
mana gida da ƙarfi haka da sassafe?” Sai na ji an ce, “Ka buɗe mai gidan ce!”
Ina jin muryar nasan Hajiya ce mai
gidan, zuciyata a kiɗime na buɗe gidan, na ce, “Hajiya ke ce da sassafe haka?”
Ta bi ni da harara rai a ɓace, na basar na ce Hajiya ki shigo mana, ina kwa...
Ban ƙarasa ba ta ɗaga man hannu.
Ta ce, “dakata ba gaisuwarka ta
munafunci ni ke so ba! Da ban kwana ba za ka ganni ne? Ni maganar kuɗin haya ta
kawoni, ka ba ni kawai in juya.”
Na ce, “Hajiya ki yi haƙuri ai jiya
da malam Sadi dillali ya zo, na yi masa bayanin matsalar da ta same ni, bai faɗa
maki ba ne?”
Cikin faɗa ta ce, “Ya faɗa man, amma
ai wannan matsalarka ce, ina ruwana da ita!”
Na ce duk da nasan matsalata ce ba
taki ba, amma dai dan Allah Hajiya, ki yi haƙuri ki ƙara man lokaci, zan kawo
maki. Tun da muke tsawon shekaru biyu, kin sani ba ki taɓa samun matsala da ni
ba, wajen kula da gidanki, ko biyan kuɗi”
Sai ta yi tsaki ta ce,“To na ji
yaushe za ka hado man kudina?”
Na ce ki ban watanni biyu, insha
Allahu zan kawo maki zuwa lokacin.
Ta ce, “Tun da da dukiyar tsohonka
na gina gidan ba? Na baka mako ɗaya in ya cika baka haɗo man kuɗina ba, to ka
tattara kayanka ka bar man gida, in ba haka ba ko da hukuma zan haɗa ka, ka ji
na gaya maka!”
Sai ta juya ta tafi ba ko bankwana,
na yi tsaye ya yin da na bi ta da kallo. Na dawo cikin gida jikina a sanyaye,
matata da ke tsaye a tsakar gida tana jin duk sababin da Hajiyar ke yi, ta bi
ni da kallo idanunta cike da ƙwalla.
Duk wunin ranar haka muka zamo ba
wani cikakken kuzari a tattare da mu, saboda damuwar wulaƙancin da Hajiya ta yi
mana, da abun da zai faru a gaba. A cikin tsawon makon da Hajiya ta ɗibar man,
na kunkunga da ƙyar na samu na haɗa rabin kuɗin. A tunanina idan na bata za ta
haƙura, kafin in ida haɗo cikon, amma ina fafur ta ƙi yarda, daga ƙarshe ta ce
ta ban wata ɗaya na bar mata gidanta.
Kafin wa’adin da ta ba mu ya cika,
na samu wani gidan. Tsohuwa ce ke da gidan, kuma zaune take a ciki. Bayan mun
tare, muna murna mun samu gidan dattijuwar kirki, ashe abun ba haka ba ne,
farfar ɗin na baƙunta ne. Watanmu biyu a gidan, halayenta suka bayyana gare mu.
Haka kawai sai ta ce wai matata ta gyara mata ɗaki, kuma duk wasu aiyukanta,
sai ta ce ita za ta yi mata, wani lokacin ma sai ta ce wai ta ɗauko abayarta za
ta aike ta, ta sayo wa dabbobinta abinci. Kai tsurfa kala-kala! Tun muna bata
uzuri da martaba tsufanta, har muka fara gajiya.
Wata rana sai ta same ni ta ce wai
matata ba ta yi mata biyayya, ba ta gaida ta, kuma in ta sanya ta aiki, ba ta
yi sai ta ga dama. Na ce ta yi haƙuri akwai ajizanci na ɗan adam, amma zan mata
magana za ta gyara. Kai in taƙaice maku bayani, al’amuran tsohuwar nan sai ya
ƙara ta’azzara, har ta kai ni ƙarshe. Rannan sai ta ce wai ta aiki matata, ta
sayo mata goro, amma ta ƙi zuwa.
Na ce mata, “ goggo, ya kamata ki sani Zainab, matar aure ce, ba budurwa
ba, kuma zaman aure take yi, ba ‘yar aiki ba ce, ni kaina ban aikenta, duk abun
da za a yi ni ke fita in yo. Ya kamata duk abun da ki ke buƙata ki fita ki
sayo, ko ki ba yaro ya sayo maki.”
Sai ta ce, “Ikon Allah! Yanzu kai Hamza, ni ka ke gaya wa hakan, duk da
alfarmar da na yi maku na baku matsugunni a gidana?”
Na ce, “Goggo ai ba kyauta muke zaune ba, biyan ki muke.”
Bayan kwana biyu da faruwar hakan,
ta ban cikon kuɗina, ta ce na tattara tsiyata na bar mata gidanta.
Gida na uku da na zauna, duka watana
uku a cikinsa na tashi. Shi kuma dalilin tashin nawa, muna zaune ne da mai
gidan da iyalinsa. Sai ya kasance idan mun je masallaci da asuba mun dawo,
nakan zauna yin lazimi ƙofar gida, kuma sun san hakan, amma da sun zo sai su
rufe ƙofar da makulli, dole sai dai na zauna a ƙofar gidan har lokacin da suka
buɗe, ko kuma in ta bugawa har na tsawon lokaci, saboda ba su ba mu mabuɗi ba.
A haka muke zaman haƙuri.
Wata rana iyalina, ta je unguwa,
bayan tafiyarta sai ita ma matar mai gidan ta tafi unguwa, ta bar wa ɗansu
makulli, shi kuma sai ya kulle gidan ya yi tafiyarsa. Misalin biyar na maraice
na dawo sai na iske gidan a kulle, sai na kira shi ta waya, na ce ya zo ya buɗe
man gida, sai ya ce ba makulli a hannunsa. Ina nan zaune Ƙofar gida sai ga
matata ta dawo, nan muka ci gaba da tsayuwa a Ƙofar gidan, har uwar yaron ta
dawo, tana ganin gidan a kulle sai ta kira shi ta waya, yana zuwa ya sa makulli
ya buɗe gidan. Wannan abun ya ɓata man rai, sai na samu mai gidan na ce ya
kamata a ba mu makulli, saboda abun da ake mana a gidan nan baya dacewa, na
gaya masa duk abun da ya faru, amma madadin ya ɗauki mataki, sai kawai ya kawo
cikon kuɗina ya ce, in tashi in nemi wani gidan.
Daga nan na yanke ban ƙara zama
gidan haya tare da mai gidan. Na kama wani gida ni kaɗai sai dai yana
maƙwabtaka da na mai gidan. Lokacin da za mu koma gidan ne yayan matata ya sai
mata injin markaɗe, domin ta samu sana’ar yi. Allah cikin ikonsa da yake
unguwar babu injin sai kasuwa ta buɗe mata. Tana samun markaɗe sosai. Haka muka
zauna cikin natsuwa, komai na tafiya ba wani tashin hankali, har ma mun fara
mantawa da matsalolin da muka baro a baya. Bayan cikar mu wata bakwai a gidan,
sai matar mai gidan nan, ta sayo injin markaɗe. Amma saboda an saba da gidana,
sai ya zamana ba ta samun niƙan sosai. Sai ta faɗa wa mijinta, ya zo ya same ni
ya ce, matarsa ta sayi injin markaɗe, kuma gidana ma akwai injin. Na ce masa,
ai ba matsala kowa rabonsa ya ke ci. Sai ya ce a’a, wai matata ta daina tada
injinta, ko ta sayar da shi.
Maganar ta ɓata man rai, in ban da
raini, ya zai faɗa man haka? Sai na ba shi amsa da cewa, “ai Alhaji Nura, sai
dai matarka ta saida nata, domin ita ce ta sayo daga baya.”
Ya ce, Haka ma za ka ce?”
Na ce, “Ƙwarai kuwa.”
Ya ce, “To shikenan.”
Daga wannan lokacin, komai ya wuce,
muka ci gaba da gaisuwar mutunci. Ashe ni ban sani ba ta ciki na ciki. Da
lokacin biyan kuɗin haya ya yi, na kai masa, sai ya ce a’a wai ya ba ni wa’adi
in tashi, tun da ina baƙin ciki da ci gaban iyalinsa.
A haka na sake neman wani gidan
hayar na kama. Saboda irin wannan uzurawar ne, ya sa nake aikin ginina ka’in da
na’in, ba ƙaƙƙautawa, amma matsalar rashin hatiman nasara, sun ja aikin ya ƙi
kammaluwa da wuri. Duk wasu halastattun hanyoyi da zan bi in sanu ƙarin kuɗaɗen
shiga, dan aikin ya kammalu ina bi. Lokacin da na ga aikin ya kawo daidai rufi,
sai farin cikina ya ƙaru, domin na yanke shawarar da na rufe shi, zan gyara
wani ɓangare ne kawai in koma cikinsa, alabashi koda ina ciki ne, sai in
kammala sauran abun da ba a ida ba. Murnata ta koma ciki ne, a ranar wata
laraba da ba zan manta da ita ba, wacce ita ce ta zamo mabuɗin duk abun da ya
faru.
Al’amarin ya faro ne da misalin sha
biyun dare, ya yin da aka haɗa wani hadari mai duhu, haɗe da iska da walkiya,
da tsawa mai ƙarfi. Hadarin ya ci gaba da haɗuwa, yana mamaye sararin samaniya,
har na tsawon kusan mintuna arba’in, sannan aka kece da ruwa mai ƙarfi, haɗe da
iska da tsawa mai rikitarwa. Hausawa na cewa, ruwan dare gamagari.” Tabbas a
ranar an shimfiɗa ruwa na tsawon awoyi shida, sai shida da hamsin na safiya aka
ɗauke.
Da ƙarfe bakwai da rabi daidai,
wayata ta ɗauki ƙarar alamun shigowar kira. Ina dubawa, sai na ga ashe wani
aminina ne malam Haruna, cike da mamakin kiran nashi, da sanyin safiya na ɗaga
kiran. Abun da ya faɗa man, ya tada man hankali, ya dugunzuma ni. Ya faɗa man
cewa unguwar da nake ginin gidana, labari ya iske shi yanzu cewa ruwan da aka
yi, ya rusa gidaje da yawa tare da ambaliya, saboda haka ya kamata na je na ga
halin da nawa yake ciki, shi ma ga ya nan zai fito mun haɗu a can. Wata ƙara
cikina ya riƙa yi ƙululu!!! Cikin sanyin murya na ce, “Inna lillahi wa inna
ilaihi raji’un!” Na ce masa na gode yanzun nan zan tafi. Mai ɗakina da ta miƙe
tsaye cikin firgici, ya yin da ta ji ina sallallami, ta kalle ni a tsorace ta
ce,
“Abban Sultan, lafiya me ke faruwa?”
Na faɗa mata abun da malam Haruna ya
sanar da ni.
Ta ce, “Ya salam, innalillahi wa
inna ilaihi raji’un! Allah ya sa mu ji, kuma mu ga alkhairi.”
Na amsa da amin Ummar Sultan! Na ɗauki
makullin babur ɗina, na fita na tada, na nufi unguwar, zuciyata cike da
fargabar abun da zan tarar.
*************
Daga inda nake tsaye daga kan layir
da za ta sada ni da gidan nawa, ina iya hango irin yadda ruwan saman da aka
kwarara a daren jiya mai tsananin ƙarfi da iska, ya yi wa da dama daga ɗaukacin
gidajen layin. Ya yin da a bisa layin ba abin da idonka zai hango maka sai
ruwan da ke kwance, wanda ya malalu ko ina.
Zuciyata ta firgice, ya yin da idanuna suka hango man gidan da ke jingine
da nawa ta ɓangaren gabas a zube, duk da cewa daga inda nake tsaye ina iya
hango fuskar gidana ba abun da ta yi, amma hakan bai sa zuciyata samun natsuwa
ba. Sakamakon yadda na ga kusan ɗaukacin gidajen layin, sun samu nasu kason
gyaran ruwan. Ganin hakan ya sa zuciyata ta kasa samun yarda, da gamsuwar ba
abun da ya samu nawa.
Ina hangen da dama daga magidantan
layin cikin ruwan, suna ta ƙoƙarin tsamo kayayyakin amfaninsu, daga ciki, domin
kuɓutar da su daga salwanta. Haƙiƙa a wannan yanayi dole in ka ga yadda suke
hanƙoron kuɓutar da kayayyakin nasu, gami da irin halin da gidajensu ke ciki,
ka tausaya masu. Tun lokacin da na ɗauko hanya, zuwa ganin halin da nawa gidan
yake, babu abun da nake nanatawa sai, INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN. A
yanzu ma da nake tsaye, zuciyata cike da saƙe-saƙe, da wasi-wasin rashin sanin
takamaiman abin yi, ina ƙara nanata faɗarta.
Shin tsayawa zan yi, har sai ruwan
da ya mamaye layir ya janye, sannan in je in duba, ko kuwa ratsa ruwan kawai
zan yi, in dubo halin da gidan yake ciki? A irin yadda zuciyata ke cikin
taraddadi, bana jin zan iya jiran. Dan haka sai na duƙa, na naɗe ƙafafun
wandona yadda zan ji daɗin ratsa ruwan, to a daidai lokacin ne, na ji an dafa
kafaɗata ta baya.
A hankali na miƙe, tare da juyawa dan ganin wanda ya dafa ni, take na yi
tozali da aminina malam Haruna, wanda ya kira ni ta waya ya sanar da ni abun da
ke faruwa.
Malam Haruna, barka da zuwa na ce,
“Ka ga yadda ruwa ya maida layin ko?”
Ya ce, “E malam Hamza, na gani
wannan abu dai ba abun da za mu ce, sai Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.”
Na ce, “Gaskiya ne malam, muna fatan Allah ya sauƙaƙa mana al’amarin.”
Ya ce, “Amin, malam”. Muka yi shiru
jim, na ɗan lokaci. Sannan ya ce, “na ga gidan naka ma ga alamu ba abin da ya
yi?”
Na ce, “E to ba na ce ba, don ban kai ga dubawa ba, ina shirin ratsa ruwan dan zuwa
in dubo kenan, sai ga ka.”
Ya ce, “To, ai sai mu je mu duba
tare.”
Ya duƙa ya tattare ƙafafun wandonsa.
Muka ratsa ruwan, muka doshi gidan, a lokacin da bugun zuciyata ke ƙaruwa. Na
sa makulli na buɗe gidan, muka shiga, da dama daga magidantan da ke hanƙoron
tsamo kayansu, daga cikin ruwan, suka bi mu da kallo. Sai dai a wannan lokacin,
bana cikin yanayin tsayawa yin gaishe-gaishe da jaje, ba tare da na san halin
da nawa gidan ke ciki ba.
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!
Abin da muka samu kawunanmu, muna faɗa kenan, a lokacin da muka ga abun da ya
faru a cikin gidan. Bangon katangar gidan maƙwabcina ne, ya faɗo kan ginin ɗakunan
gidan, wanda hakan ya yi sanadiyar zubowar ɓangarori da dama na ɗakunan, tare
da karya lintarsu. Kasantuwar wannan taɓuwa da lintar ta yi, ya yi sanadin
tsagewar bangon arewa na gidan. Ganin wannan abu, ya sa na ji kamar kafafuna,
ba za su iya ɗauka ta ba, dan haka, sai na jingi na da bango, ya yin da
zuciyata ke cikin hargitsi da ɗimuwa, saboda babu wani magidanci, dake hanƙoran
gina muhallin da yake fatan tarewa a cikinsa, kuma ya gan shi cikin irin wannan
yanayi, ba tare da ya gigita ba, musamman ma ga irina mai ƙaramin ƙarfi, da na
shafe tsawon lokaci ina aikin. Tabbas wannan shi ne, ‘Ta leƙo ta koma.’ Ko kuma
in ce, ‘Murna ta koma ciki.’ Haka dai muka duba sauran sassan gidan, bayan mun
gama, na ƙiyasta a ƙalla gyaran wannan aikin, zai iya lashe kimanin naira dubu ɗari
uku, dan mayar da shi yadda yake.
Bayan mun fito na ce, “To ni yanzu
ina zan samu kuɗin da zan gyara gidan nan, cikin ƙanƙanin lokaci? Saboda barin
sa cikin wannan yanayin, na tsawon lokaci, zai iya jawo ƙarin wata matsalar, da
ta fi wannan.”
Malam Haruna, ya ce, “Malam Hamza, gyaran wannan matsalar kaɗai, ba ita ce
mafita ba”.
Na ce, “Malam, me kake nufi da
wannan maganar?”
Ya ce, “In ka lura matsalar da wannan layin yake ciki, har da ta rashin
fitar da ingantattun hanyoyin ruwa, za ka lura da hakan, in kai la’akari da
yadda ruwan ke kwance a kan layir, hakan kuma alama ce, me nuna ruwan bai da
wadatacciyar hanyar wucewa.”
Na ce, “Gaskiya ne, to yanzu me ye abun yi?”
Ya ce, “Ina da shawara.”
Na ce, ina sauraren ka malam.
Ya ce, “Me zai hana ku nemi bashin gyaran gida, da bankin bada lamuni na Federal
Mortgage Bank.”
Na kalle shi cike da mamaki, na ce, “Daman suna ba da bashin gyaran gidaje
ne ga ma’aikata, na yi tunanin bashin gidaje kawai suke bayarwa?”
Ya ce, “Ina, ai suna ba da tun daga naira dubu ɗari biyar, har zuwa miliyan
ɗaya, ga duk ma’aikacin da ya nemi hakan.”
Wata doguwar ajiyar zuciya na yi,
tare da jin wani daddaɗan sanyi ya ratsa zuciyata. Sai na samu kaina ina mai
cewa, ‘Alhamdulillah’ Na ce, “to malam, ya ake neman wannan bashin?”
Ya ce, “Yanzu kuwa zan baka bayanin,
duk yadda tsare-tsarensu yake.”
Na ce, To, ina saurarenka.”
Ya ce, “Kamar yadda yake a bisa tsari, bankin lamuni na Federal Mortgage
Bank, yana bayar da lamuni kan abun da ya shafi muhalli har kusan kalla huɗu,
akwai, tsarin bayar da gidajen kai tsaye bashi, wato (home loan), akwai kuma
tsarin da za a baka gidan matsayin haya, kuma ka mallake shi wato (rent to
own), akwai kuma tsarin bayar da bashin lamuni kuɗin gina gida da kanka, wato
(home construction loan), sai kuma akwai tsarin bayar da lamunin gyaran gida
wato (home renovetion loan), kuma wannan tsarin shi ne ya kamata ka ɗauka,
domin ka samu isassun kuɗin gyarawa da kammala gidanka.”
Na ce to malam ya ake bin shi wannan
tsarin har a samu kuɗin?
Ya ce, “ Da farko dai za ka fara
zuwa a buɗe maka asusun da zai tabbatar da kana ba da kason kuɗinka duk wata,
idan an buɗe za a baka ɗan littafi, wanda ke ɗauke da sunanka, da hotonka, da
ma’aikatarka, da ɓangaren da ka ke, da lambarka ta NHF, wacce take da matuƙar
muhimmanci wajen amsar lamunin, domin dole ne sai kana da ita. To idan ka samu
wannan littafin, sai ka nemi takardar neman bashin (form) a bankin. Idan ka
samu, sai ka bi duk ƙa’idojin da aka sharɗanta, ka cike, ka mayar. Daga nan sai
ka jira, idan an bi an tabbatar da ka cike kowace ƙa’ida, kuma abun da ka
buƙata bai zarce idan an kasa shi watanni sittin (60), a ɗauki kashi ɗaya cikin
uku na albashinka ba, idan kuma ya zarta, za su rage su baka abun da ya yi
daidai da abun da ke shigo maka a wata. In kuma aka samu wata matsala kamar, ba
ka cike wasu ƙa’idojin yanda ake buƙata ba, ko mutum biyun da suka tsaya maka
(guarantors), akwai wanda zai aje aiki, ƙasa da shekaru biyar da za ka biya
bashin, ko kuma matsayin albashinsa bai kai ya tsaya wa wanda ya buƙaci adadin
kuɗin da ka nema ba, za a kira ka, ka gyara. A ƙarƙashin wannan tsarin, za a ba
ka daga naira dubu ɗari biyar, har zuwa miliyan na gyaran gida. Sannan za ka
biya su ne cikin shekaru biyar, ko abun da ya rage daga shekarun aikinka. Da
zarar ka cike komai kan ƙa’ida, za ka jira zuwa wasu watanni, kafin takardar
(offer) amincewar ba ka lamunin ta fito.
Wannan jinkirin yana dangantuwa ne, da matsala ko rashin matsalar da
rukuninku ya samu, saboda suna tsara abun ne rukuni-rukuni (Batch), kowanne
mutum goma ne da suka buƙaci adadin kuɗi iri ɗaya, to in mutum ɗaya ya samu
matsala a rukunin, duka za a maido su har sai ya gyara a mayar. Bayan an baka
ofa komai ya ƙare, sai kawai jiran shigowar kuɗin da ka buƙata.”
Bayan malam Haruana ya gama yi man
bayanin tsarin banki ba da lamuni, sai na tambaye shi to ina zan zamu ita
takardar da za a buɗe man asusun? Ya faɗa man ai a bankin zan je na amso na
cike. Sannan ya ƙara man da shawarar ya kamata in zauna da mutanen layinmu, mu
tattauna yadda za mu gyara layin, mu fitar da hanyoyin ruwa, ta yadda ko a gaba
ba za mu sake fuskantar matsalar ambaliya ba, bare ta kai ga rushewar gidajenmu.
Na yi masa godiya muka yi bankwana.
Na yi amfani da shawarar aminina
malam Haruna, na bi duk ƙa’idoji na buɗe asusuna a federal mortgage bank, na
kuma samu fom na bashin gyaran muhalli, na cike na mayar. A lokacin da nake
bibiyar yadda zan samu lamunin ne, muka yi zama na musamman da maƙwabtana, muka
tatatauna matsalolin da suka haddasa mana wannan ambaliyar, da ta yi sanadiyar
jawo mana asara. A ƙarshe muka cimma matsayar haɗa kai, mu fitar da ingantattun
hanyoyin ruwa. Mun yarda cewar, matsalolin da wasunmu ke fuskanta a gidajen
haya, na matsi da takura ne, ke jawowa muke aikin gaggawa, domin mu tare a namu
gidajen, ba tare da la’akari da abun da ka je ya komo ba, wanda hakan ke koma
mana dana sani.
*****************
A ƙarshe mun gyara layinmu, mun
fitar da hanyoyin ruwa masu inganci, mun yi ciko, layin ya koma gwanin kyau.
Bayan watanni biyar, banki lamuni suka ban kuɗin da na nema, na kammala aikin
gidana muka tare cikin farin ciki.
Ire-iren matsalolin da na fuskanta
da waɗanda na ga wasu sun fuskanta, ya sa na yi tunanin bayar da tawa
gudummuwar, domin bai kamata abar abun ya ci gaba da faruwa a cikin al’ummarmu
ba. Da farko na fara ƙoƙarin yin aikin wayar wa al’umma kai ni ɗaya, sai na
fuskanci ba mai saurare na, ballantana ya yi amfani da shawarar da na bayar.
Wata rana muna tattauna matsalolin da mai ɗakina, sai ta ban shawarar in samu
wasu, masu irin wannan tunani, da kishin nawa, mu kafa ƙungiya, wataƙila hakan
zai fi tasiri, idan abun ya fito a ƙungiyance, domin al’umma sun fi girmama
hakan, kuma yin komai a ƙungiyancen, zai fi bada damar a cimma manufar da ake
fata.
Na yi amfani da shawararta, na tuntuɓi
wasu daga abokaina, da makwabtana, muka tattauna muhimmanci yin hakan, suka
amince. Daga nan muka kafa wannan ƙungiyar. Bayan kafuwar ƙungiyar, sai muka
duƙufa wajen ganin mun cimma ƙudurorin samar da ita. Muka ci gaba da wayar wa
da al’umma kai, a kan muhimmancin mallakar muhalli, tare da gina muhallai masu
inganci, da fitar da ingantattun hanyoyin ruwa, da samar da ingantattun
hanyoyin zubar da shara, domin kare kai daga ambaliyar ruwa, ko asarar dukiya,
da salwantar muhallai. Daga lokaci kuma zuwa lokaci, ƙungiyar tana shirya bita
dan ƙara wayar wa da al’umma kai, a kan abun da ya shafi muhallinsu, da irin
muhimmancin da muhalli mai inganci yake da shi. Cikin shekaru biyu da kafuwar
ƙungiyar, ta mamaye faɗin garin nan, domin a yanzu da nake baku wannan labari,
ƙungiyar na da mambobi dubu biyu da ɗari bakwai. Sannan akwai asusu na musamman
da ƙungiyar ta buɗe, wanda mu ‘ya’yanta zalla kawai, muke bada gudummuwoyinmu
na abun da ya sauwaƙ a, da kuɗin muke amfani wajen sayen kayayyakin aikin gayya,
kamar na gyaran kwatoci, da na kwasar shara, da kuma tone wasu magudanan ruwan,
da suka toshe na cikin unguwanni. To wannan dai shi ne dalilin da ya ja na kafa
wannan ƙungiya da kuma ayyukan da take yi.
Gaba ɗaya aka ɗauki tafi raf raf
raf!!! Bayan malam Hamza ya kammala jawabinsa, sai ya koma ya zauna. Mai
gabatarwa ya ce an ce daman waƙa a bakin mai ita tafi daɗi, yanzu mun ji abin
da ya yi sanadin samar da ƙungiyar MUHALLINKA ALFARMARKA, daga bakin
shugabanta. A yanzu za mu kira babban baƙonmu domin ya fito ya bayar da wannan
kambun girmamawar ga wannan ƙungiya. Jama’a suka sake tafawa, a lokacin da
baban baƙon, ke miƙa wa malam Hamza kambun ƙarramawar, wanda aka rubuta sunan
ƙungiyar da rubutu mai ruwan gwal.
Bayan kammala bikin ba da
kyaututtukan ne, aka rufe taron da addu’a, kowa ya nufi in da ya fito. Wani ɗan
jarida ya fara yi wa malam Hamza, tambayoyi;
Yallaɓai, me za ka ce game da wannan
karramawar da aka yi wa ƙungiyarka?
Ba abun da zan ce sai godiya ga
mahallincimu, domin da ikonsa ne da kuma iyawarsa, ƙungiyar ta taka wannan
matsayin.
Ana iya cewa, wannan nasarar ta samu
ne bisa ga jajircewarka?
Wannan nasarar ba tawa ba ce, kuma
ba ƙoƙari na ba ne, ta dukkan mambobin ƙungiyar ce, domin da jajircewa da
sadaukarwarsu ne, ƙungiyar ta kai inda take a yau.
A yanzu kana ganin ƙungiyar ta cimma
duk wasu ƙudurorin da aka kafata domin su?
Alhamdulillah! Mun cimma dai kashi
tamanin da biyar cikin ɗari.
To ranka ya daɗe mun gode.
Nima na gode.
ƘARSHE
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.