Bashir Adamu (2020). Baƙin Bunu…. Muhalli, Sutura (Labaran Da Suka Samu Nasara a Gasar Gajerun Labarai a Kan Muhalli Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2020). Darma Digital Prints.
BAƘIN BUNU…
Na
Bashir Adamu
15/7/2020 Babbar Kotun Jiha ta Ɗaya
“Duba da shedu da kuma hujojjin da masu ƙara suka gabatar wannan kotu mai daraja ta samu Alhaji
Musa wanda aka fi sani da (Kuɗi ƙasa) da laifin da ake zarginsa da aikatawa,
saboda haka kotu ta zartar mai da hukuncin ɗaurin shekaru goma a gidan kaso ba
tare da zaɓin biyan tara ba, haka kuma…”
Abin da na iya jiyo wa kenan daga bakin alƙalin, sai dai na farka na ganni
a gadon asibiti, kusa da ni ga wani jami’in gidan gyaran hali ya ƙura man ido
kamar yana tsoron kar na ɓace. A gefe guda kuma lauya na ne tare da Musa abokin
aiki na suke tattaunawa, na wurga kallo na ga saitin tagar gadon da nake kwance
na hango matata zaune a gindin wata bishiya da ke harabar ɗakin da aka kwantar
da ni ta yi tagumi, ƙaramin yarona Sadiƙ na ta faman wasan shi a gefenta.
Wata ajiyar zuciya na yi, sannan na
sake lumshe idona na nutsa a kogin tunanani, wai yau ni ne nan za a zartar wa
da hukuncin ɗauri? Wannan kuwa ba mafarki ba ne? Na ƙara buɗe ido na a hankali
domin tabbatar da ko dai a mafarki na ke amma duk abubuwan da na gani ɗazu
yanzu ma na sake ganinsu a zahiri, lallai ba mafarki ba ne. Zuciyata ta hasko
man farkon abin da nake ganin shi ne faruwar matsalar.
22/1/2019
Da ƙarfe 11:09 na safe
Ina zaune a ofishina ta shigo cikin
sigar rangwaɗa da murmushi a fuskarta tare da yin sallama irin ta wayayyun ‘yan
boko waɗanda addini bai ratsa ba, a tsarina ba a shigo wa ofishina kai tsaye,
sai mai taimaka man ya sanar da ni, amma na yi mamakin ganin ta haka, ba tare
da sanar da ni ba. Na ɗago a hankali na kalleta ban amsa mata sallamar ba, sai
dai kawai na ga hannuna na nuni gare ta da ta zauna.
‘Sunana Fatima amma an fi sanina da P.A sakamakon na taba zama P.A ta
tsohon kakakin majalissar dokoki ta ƙasar nan, yanzu kuma ina aiki da
ma’aikatar walwala da jin daɗin jama’a ta ƙasa a matsayin sakatariyar kuɗi, na zo
nan ne domin ka yi man hanya in karɓi bashin bankinku na gina gidaje, ina da kuɗin
da zan iya gina gida amma ina so ne na moru da wannan banki naku, sannan kuma
ba haka kawai za ka yi aikin ba, kai ma zaka samu rabonka a ciki. Nasan wata ƙila
kayi mamaki ta ina? Da farko ina son ka san cewa na san cewa kai ba zaka moru
gida ba ko kuɗin gyaran gida daga bankinku, duba da cewa kai ma’aikacin bankin
ne, wanda dokar da ta samar da bankin ta haramta maku haka.
Sannan kuma ni yanzu ina da sauran shekaru goma sha biyar a aiki ka ga zan
iya biyan kuɗin musamman saboda shekaru biyar ne dama mafi ƙarancin wa’adin,
sannan kuma na san cewa ba a bayar da ko sisi kafin a ba mutum wannan lamuni
illa iyaka dai ana buƙatar ya zuba kuɗi a asusun sa na tsarin samar da gidaje
na ƙasa a ƙalla watanni shida, wanda ni duk na cika wannan sharuɗɗa, amma kuma
ni zan biya ka kuɗi ƙasa ne kamar yadda ake kiranka in dai har ka yi man hanyar
samun gida a inda zan faɗa maka.’’
Hannu na ɗaga mata alamar ta tsaya, rigarta ta gyara ƙirjinta ya ɗan fito
fili ta duƙo gaf da ni ta ce, ‘‘ka sauraran ban gama ba’’ ƙamshin
turarenta ya daki hancina, na ji wani juyi a kaina tamkar ba a duniyar nake ba,
ban san sadda na fara jin shauƙin ta ba, kamar maganaɗisu ta ɗauke magana ta na
yi tsit ina kallonta.
‘‘Na san cewa, bankinku ya fito da tsarin bayar da miliyan ɗaya ne matsayin
kuɗin gyaran gida domin bai wa ma’aikata da dama damar amfanuwa da bankin naku,
domin ba kowa ne ke iya samun gida ba daga gareku, kuma kai ne babban darakatan
da ke kula da wannan ɓangare na raba bashin miliyan ɗayan. Na ga haka ne bayan
da na ziyarci shafinku, inda na ga an jero sunayen daraktocinku da ma sauran
ma’aikatanku, ganin sunanka kawai ya sa na aminta da cewa zaka iya yi man aikin
da nake buƙata, duba da cewa kafin ka dawo wannan bankin mun taɓa yin wata
harƙala da kai a lokacin kana aiki a hukumar sifiyo ta jiharku”.
Na ƙura mata ido ina so in tuno harƙalar da muka taɓa yi da ita, amma na
kasa, murmushi kawai ta yi ta duban ta ce, ‘‘kar ka wahalar da kan ka tuno harƙalar
zuwa gaba zan bayyana maka, amma ganin fuskata ba zai sa ka tuna ba, kuma ba
wannan maganar muke ba.’’
Kai tsaye na tambaye ta me kike so wai yanzu? sai faman jawabi kike kamar
ke ce babban darakatan wannan bankin, musamman yada kike zayyano wasu dokoki da
ƙa’idoji da suka shafi bankin.
‘‘So nake a ba ni
gida ɗaya
mai ɗaki
uku a rukunin gidaje na unguwar Samba da kuka gina a nan birnin Tarayya’’
Na kalleta a zuciyata
na ce,
anya wannan ba taɓaɓɓa
ba ce?
‘‘Da hankali na
ras, nasan tunanin da kake ila na haukace ko? To da hankalina zan maka bayanin
yadda tsarin zai kasance kai kawai bi za ka yi”
Na rangwanta mata
ne kawai saboda na ji
ta ambaci aikin da na yi
a hukumar Sifiyo wanda kuma ina da wani ɓoyayyen
sirri da ba ni so ya fito, amma sai wata dabara ta faɗo
man...
“Har yanzu bai tashi ba ne” wani ɗan siririn likita ne ya katse man
tunanina da muryarsa mai kama da an busa usur ɗin filin kwallo. Na buɗe ido na
a hanlkali ina kalon mutanen wajen ɗaya bayan ɗaya, na yunqura da niyyar tashi
sai na ji hannuna ɗaya ɗaure gam da ankwa, ban san sadda na koma na kwanta ba,
a daidai lokacin da likitan ya yunƙuro yana ƙoƙarin mayar da ni kar na tashi.
Haka na koma na kwanta ina bin duk wanda ke wajen da kallo ɗaya bayan ɗaya,
kamar wani wanda ya ɓata. Likitan ya dube ni cikin natsuwa ya ce, “Sannu
Alhaji, ai jikin naka ma da sauƙi, amma ka rage sanya abubuwa a zuciyarka,
domin kana iya samun bugun zuciya, kaga kuma hakan ba zai haifar ma da ɗa mai
ido ba”.
Ban ce masa kome ba sai saƙe-saƙe nake a zuciyata, haka na hango Musa tare
da lauyana sun nufo inda nike kai tsaye da alamar suma jira suke na tashi dama,
na yi kamar na sake runtse ido na amma sai naga na yi ido huɗu da matata wadda
ita ma ta lura da tashi na shi ya sa ta nufo inda nake, na kawar da kai na daga
kallonta cikin jin kunya da nadama, ko shakka babu matata tasha nusar da ni kan
abinda zai iya faruwa da ni musamman in ta ji irin wayar da nike a gida dangane
da wasu harƙaloli da nake ƙullawa, amma daidai da rana ɗaya ban taɓa nuna mata
cewar abinda take faɗa man yana shiga raina ba, asali ma ina mata kallon wata
wadda ta zama matsala a rayuwata saboda tsabagen sanya idonta ga harkoki na.
Mun kwashi shekaru kusan ashirin da ita, amma kullum bata taɓa gajiyawa ba
wajen nuna man soyayya da ƙauna, ni kuma in ban da tsana babu abinda ke ƙaruwa
nata a zuciyata, sau da yawa nasha yin tunanin ko dai hannu aka sa man na
tsanarta ne, duk wani abu da zata yi bai burgeni, duk ƙoƙarinta na kyautata man
ban gani, ni dai kawai barni da na fita waje na riƙa waya ta hirar waya da mata
a waje, duk yadda mace take a waje in tayi man magana zan bata kulawa ta
musamman, amma a gida kuwa da zaran na shiga zan murtuke fuska, abu kaɗan za a
yi man na fara bambami da hayaniya... “baban Sadiƙ sannu da jiki” muryar matata
ce ta ratsa kunnena cikin bazata, a karon farko tun bayan satin amaracinmu da
na ji muryarta ta ta yi daɗi kamar busar sarewa, ban iya amsawa ba sai dai ƙura
mata ido da na yi cikin nadama da kuma jimami.
Ko kafin na ce wani abu, Musa abokin aiki na ya fara magana, “sannu Master
(sunan da yake kirana da shi ke nan saboda ƙwarewata wajen iya tsara abubuwa),
kar ka damu mun gama magana da Lauya yanzu zamu ɗaukaka ƙara, saboda wannan
hukunci ba mu aminta da shi ba, kuma muna ganin akwai lauje cikin naxi”.
Lauyana Aliyu ya kalle ni yace, “Alhaji kasan duk abinda ya kamata ace mun yi
kan wannan kes ɗin mun yi shi, amma aka samu akasi, to wannan ba zai hana mu
samu nasara a kotun ɗaukaka ƙara ba, mun gama kome game da shirin mu na ɗaukaka
ƙara, saboda haka kar ka damu”.
Ba abinda na iya sai gyaɗa kai ba tare da na ce kome ba, idanuna rumtse
saboda ina matuƙar jin kunyar in buɗe su mu yi ido huɗu da matata.
Bayan tafiyar su Musa da Lauyana, sai likita ya bayar da umurnin a sallame ni
saboda ba wata damuwa a tare da ni, ban samu na yi wata doguwar magana da
matata ba, saboda ba na iya haɗa ido da ita a daidai wannan lokaci da ko a
safiyar ranar kafin a yanke man hukunci sai da muka yi faɗa kan in gyara ɗabi’una
duba da cewa shekaru na sun fara tafiya.
Jami’in gidan gyaran halin da ke tsare da ni ya buga waya ya buƙaci da aka
kawo mota domin tafiya da ni inda za a tsare ni kafin takardun ɗaukaka ƙara ta
su samu amincewa. Cikin mintina da ba su fi goma ba sai ga mota ta zo aka
kwance sarkar da aka ɗaure ni da ita na miƙe tsaye cikin girmamawa jami’in gidan
yarin ya kama hannuna kamar abokinsa muka fita daga ɗakin da aka kwantar dani
zuwa wajen motar da za ta tafi da ni. Matata na gani a kofar ɗakin tsaye tana
kallona hawaye na zuba daga idonta, ban tsaya wajenta ba kawai muka nufi cikin
motar kaina sadde a ƙasa. Mota ce ƙarama mai ƙirar shiga ba biya, aka buɗe man
gidan baya na shiga na zauna aka mayar aka rufe da kwaɗɗo, na buga tagumi na faɗa
cikin tunanin halin da na shiga.
*****
Maganganun Fatima P.A suka riƙa dawo man kamar sabbi.... “ kawai abin da
nake buƙata ka aminta da ba ni gidan saboda nasan zaka iya, kuma ma ai na cika
sharuɗɗa, sannan zan zuba adadin kuɗin da aka ƙayyade ga mai buƙatar gidan ya
zuba, sai dai fa da ka ji na ambaci gida mai ɗaki uku, kar kayi mamaki domin
nayi bincike shi kaɗai ne ya rage kuma yana nan kusa da wani makeken fili da
aka ware an ce wai kasuwa za a yi wajen da asibiti, to buƙatata a wannan filin
take, domin in aka ba ni gidan sai a ƙara shata man daga cikin filin da kuka ce
an ware domin yin asibiti da shaguna, duba da cewa gidan liƙe yake da filin a
wajen rubutawa nake son a ƙara man haka zan biya ko nawa ne kan wannan aikin”.
Cikin mamaki na ɗaga kaina na kalleta ina al’ajabin wannan abu nata ko
shakka babu wannan turo ta aka yi domin ba wanda ya san da wannan gidan sai
wasu tsirarun daga ma’aikatan kuma an ware wannan gida shi kaɗai ba a ba da shi
ba saboda wannan filin dama, suna kasafta yadda zasu samu wani kaso a cikin
filin domin samun kuɗaɗen kashe ƙwalama, kamar yadda suke kiran irin waɗannan
kuɗaɗen... “kar ka wahalar da kanka wajen tunanin ya aka yi na san da fili ko
kuma manufa ta tayin haka” muryarta ce ta katse ni daga tunanin da na fara,
taci gaba da cewa,
“kamar yadda na faɗa ma a baya ban
zo wajenka ba sai da nasan waye kai, lokacin da kana shugaba a hukumar Sifiyo
ta jihar ku, na san ka yi abinda ya fi wannan kuma ka wanye lafiya saboda
ƙwarewarka da kuma sakin hannunka ga jama’a musamman abokan aiki". lokacin
da kana Shugaba a hukumar Sifiyo ta jihar ku, nasan kayi abin da yafi wannan
kuma ka wanye lafiya saboda ƙwarewarka da kuma sakin hannunka ga jama’a
musamman abokan aiki".
Lokacin da ta tsaya da maganarta ta ƙura man ido kamar tana hangen wani abu
a cikin ido na, nima kuma sai na cigaba da kallonta ƙur naƙi ɗauke ido na daga
kanta har zuwa wasu ‘yan daƙiƙu, sannan na fara tunanin irin harƙalla da muka
yi lokacin ina shugaban hukumar Sifiyo ta jiha, ko shakka babu duk arziƙin da
na samu a rayuwa a wannan hukumar na same shi.
Duk da cewa a yanzu idan naje jihar tawa ta haihuwa ina ganin abubuwa da
yawa da suka kasance mu ne sanadin faruwarsu, kama daga cinkoson da ake fama da
shi a wasu titunan jihar, wanda hakan na da nasaba da yanka duk wani fili da ke
bakin hanya ko kuma ya shafi makarantu ko wasu wurare na gwamnati duk mun samu
haɗin kan gwamna mun yanka su tare da sayar da su ko ince ba da wa ga manyan
muƙarabban gwamnati, wanda yanzu nike ganin illar abun, domin akwai hanyoyin da
saboda wannan mugun aiki da muka yi ba zasu faɗaɗu ba.
Ba ma wannan ya fi damuna ba illa yadda muka yanka tare da bayar da duk
wasu filaye dake cikin rukunin gidajen da ba gwamnatin da na yi aiki a
ƙarƙashinta ta samar da su ba, sakamakon haka, aka rasa filayen asibiti da
masallaci da maƙabarta da ma kasuwa a rukunin gidajen, sai an yi tafiyayya
sannan aje, kuma abun ƙaddara nima a ɗaya daga cikin waɗannan unguwanni da muka
yi wa cin kashi nake da zama.
“kai nake sauraro, ka faɗa man yadda za a yi, kawai me zan bayar bayan kuɗin
da zan ajiye na mallakar gidan?” ki je sai gobe ki dawo zan tattauna da waɗanda
ke da hannun a wannan gida ɗayan da ya rage, in Allah ya yarda za a san yadda
za a yi. Mayar mata da magana kai tsaye ba tare da na ƙara ɗaga kai na kalleta
ba.
Bata ƙara cewa kome ba sai dai miƙewa ta yi, ta kallan cikin natsuwa tare
da yi man wani murmushi, sanna ta ɗaga ‘yan yatsun hannunta na dama ta kaɗa su
alamar bankwana, na bita da kallo kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa, tana
fita daga ofis ɗin na yi wata aciyar zuciya.....
*******
Alamar buɗewar kyauran motar da nake ciki ya tabbatar man da cewa an zo
gidan gyaran halin da za a ajiye ni, hankali na ya dawo jikina baki ɗaya,
jami’in da ya tsare ni a asibiti ne ya buɗe ƙofar tare da cewa, Alhaji bisimillah
fito an zo, ai ta dai haƙuri da rayuwa, kowane ɗan Adam bai wuce ƙaddararsa mu je
kanta a yi maka rijista”.
Haka na fito kamar ƙafafuwana ba za su iya ɗauka ta ba na bi bayan wannan
jami’i muka shiga cikin gidan, kai tsaye muka nufi wani ofishi, wanda a saman
ofishin naga an rubuta “Chief Worder” muka shiga ciki jami’in ya miƙa wa wanda
ke zaune a ofishin bayan ya duba takardar sai ya bani umurnin da in zauna, ya
fara magan da cewa, “Alhaji kamar yadda yake dokar gidana nan duk wanda aka
kawo kafin mu ba shi inda zai zauna sai ya faɗi mana laifin da ya yi aka kawo
shi a gidan nan..”
Na ɗago kai na na kalle shi na bayyana masa cewa, yau da gobe ce ta kawo ni
wannan gida naku ba wai dan ina so ba, na lura cewa amsar da na bashi bata
gamsar da shi ba, amma sai ya kyale kawai, ban kuma san dalilin sa na yin hakan
ba.
Wani jami’in ya kira ya ce masa a je a ba ni kaya da ɗaki, na bi bayan
jami’in ina kallon taswirar cikin gida, mutane na hanga cinkushe a cikin wasu
dogayen ɗakuna da na ga an nufi da ni gabana ya faɗi, na ji ciwon zuciyata ya
ƙara tasowa, saboda irin cinkushewar da ya yi. Kallon da wanda nake bi ya yi
man na san cewa ya farga da halin da nake ciki. “Alhaji ai wannan kaɗan ma ka
gani akwai ɗakin da a gidan nan asali an yi shi saboda mutum ashirin ne, amma
yanzu akwai sama da mutane ɗari da goma a cikinsa, ai matsalar muhalin nan ba
wai a gidajen cikin gari kawai ta tsaya ba, har a nan ma ya kamata irin
hukumominku su kawo ɗauki domin faɗaɗa yanayin zaman da ake a nan, duba da cewa
nan ɗin ma mutane ne ke zaune a ciki, kuma ita ƙaddara tana iya kawo kowa nan
kamar yadda ta kawo ka”
Na kalle shi kamar zan yi kuka na ce masa yanzu nima a cikinsu za a
ajiyeni? “ƙwarai kuwa, amma kai ɗakin da za a kai ka ba za ku wuce ku saba’in
ba, amma kuma in kana son a kai ka VIP to sai ka yi wani abu” cikin sauri na ce
masa ko nawa ne zan bada a kaini VIP ɗin. Ya yi murmushi yace, “ok biyoni muje
na kai ka sai na koma na sanar wa da oga, saboda shi za a ba kuɗin da za ka ba da
ɗin”.
Ɗakin da aka kira VIP, za a iya cewa mai kyau ne domin dai fallan ɗaya ne
wanda bai wuce girman ƙaramin falo ba, akwai gado biyu masu hawa biyu a cikinsa
sannan akwai wani koɗaɗɗen kafet shimfiɗe a tsakiyar ɗakin, kuma akwai kewaye a
cikin ɗakin, shi dama an ware shi ne musamman saboda manyan jami’an gwamnati ko
kuma waɗanda rikicin siya sa ya kawo gidan, a ɗakin na tarar da wani mutum ɗaya
wanda na san shi dama tun a cikin gari, shi ma dai kamar ni wata harƙallar ce
ta kawo sa a nan, amma shi ba a ma yanke masa hukunci ba.
Na zauna gefen gadon da aka ba ni na kalli zubin gadon, rabon da na kwanta
irin wannan gadon tun lokacin da na yi makarantar kwana, kusan shekaru talatin
da biyar da suka shuɗe, hawaye na ji na neman zubo man, amma dole na daure kar
su zubo, na ƙara matsawa bisa gadon na jingina da bango zuciyata na hasaso man
baya, kan abubuwan da suka faru har na samu kaina a wannan gida.
Na ƙara matsawa bisa gadon na jingina da bangon ina tunanin abubuwa kamar
yanzu suke faruwa, na tuna lokacin da shugaba jam’iyya ya kirani yake mai sanar
da ni cewa, sun yi magana da gwamna yana so a ba shi wani fili da ke cikin
rukunin gidajen Sulluɓawa zai gina gida, ko shakka babu wannan shi ne ɗan mabuɗin
duk wata matsala na faɗa.
Na tuna da lokacin da na je gidan sa kai masa taswirar filayen da ke cikin
rukunin gidajen, na same shi zaune a falonsa yana kallon labaran ƙasa. Bayan
mun gaisa na fara gabatar masa da sauran filayen da suka rage kamar haka; Ranka
ya daɗe wannan filin shi ne mafi girma an ware shi ne saboda a gina Islamiyya
da shaguna nan gaba, wannan kuma an ware shi ne domin gina asibiti da kuma kasuwa,
sai mita hamsin da ta zagaya gidajen baki ɗaya shi kuma an ware shi ne saboda
samun filayen wasanni ga yara da kuma shuka ciyawa tare da taimakawa wajen
samun iska da yanayi mai kyau, sai kuma sauran filaye da aka rage saboda
abubuwan daka iya tasowa nan gaba, kamar dai yadda dokar tsara birane ta
tanadar.
Bai ce kome ba sai da na gama sannan ya fara magana da cewa, “Ni yanzu
wannan filin da ka ce an ware saboda a gina Islamiyya shi za ka yanka man kuma
ka kawo man takardunsa, mun yi magana da sakataren gwamnati da shugaban
ma’aikata na gidan gwamnati duk su ma suna son filaye, sannan gwamna ya yi wa
‘yan jarida alƙawarin filaye kuma ya ce na sanar da kai su ma duk a nan za a
yankan masu, saboda haka kai kasan yadda zaka yanka filayen kowa ya samu kuma
kai ma ka fitar da kason ka.”
Ban tsaya yin musu ba ko gardama na aminta da maganar sa nace gobe in sha
Allah zamu zo da ma’aikatanmu a fara yanka filayen takardun filinka kuma zan
kawo su gobe in sah Allah.
Tun bayan fitowa ta daga gidan shugaban jam’iyya na fara tsare-tsaren yadda
zan samu filaye masu yawa a wannan aikin da za a yi.
Wanshekare muka fita da ma’aikatana muka fara aikin yanka duk wani fili da
ya rage a cikin rukunin gidajen Sulluɓawa, a wannan aiki sai da na samu filaye
takwas masu kyau bayan kuɗaɗen da na samu na alheri daga shugaban jam’iyya da
sauran muƙarabban gwamnatin da aka yanka wa filaye a wajen.
Sai dai ni kaina na san cewa fasalin unguwar ya sauya domin an matse
unguwar sosai za a yi gine-gine har wuraren da ba su da ce ba, kuma nasan cewa
yanka waɗanann filayen zai kawo wa unguwar matsalar ruwa sosai, domin akwai
wuraren da aka ware domin gina manyan rijiyoyi da za su ba unguwar ruwa, duk
mun yanke su yanzu sun zama gida.
Haka kuma, babu wani fili da za a iya gina Islamiyya ko Caji ofis ko wasu
abubuwa da ka iya taso a unguwa mai gidaje ɗari biyar yanzu kuma na samar da
filaye sama da ɗari biyu. Amma ba filin da za a gina shaguna ko kasuwa ko
asibiti, sai dai an fita nesa domin samo waɗannan abubuwa, wanda hakan ko
shakka babu zai iya haddasa asarar dukiya da rayuka a nan gaba. Ni dai ba
wannan ke gabana ba kawai ina duba abin da na samu ne a wannan huɗɗar....
“ƙarar buɗe ɗakin da muke ciki ne ta dawo da ni daga dogon tunanin da na
nausa, wani ɗan tsukakken mutum ne ya buɗe ɗakin tare da tsaya wa a ƙofar ɗakin
yana kallonmu. Ina Alhaji Musa ka zo ana son ganika kana da baƙi”, kamar na ce
ba zan fita ba saboda gajiyar da ke tare da ni kuma duka fa ban wuce awa ɗaya
ba da kawowa ba, na ɗaga kaina na kalle shi ba tare da na ce kome ba kawai na
tashi na nufi kofar ɗakin, gaba ya sani har muka isa dan tsukaken ɗaki wanda ke
da benji ɗaya a tsakiya sa. Taye take a tsakiyar ɗakin ta rungume hannu, kallo ɗaya
na yi mata na gane ta Fatima P.A ce.
Cikin zuciya ta na fara tunanin me kuma ya kawo wannan matar a nan? Kar dai
ace wani sherin ne kuma ya ta nufo ni da shi, gaskiya wannan matar ta sanya ni
tsaka mai wuya....
“Alhaji Musa ashe haka kuma abu ya kasance” siririyar muryarta ce ta karaɗe
ɗakin ba tare da na kalleta ba na zauan bisa bancin da ke tsakiyar ɗakin, a
zuciyata nace bari dai na nuna dakewa ga wannan mata, koda kau sau ɗayane a
rayuwata.
Wane abu kuma? Na mayar mata da ƙarfin zuciya, “abokin aikinka ne ya kirani
yake ceman wai an zartar ma da hukumncin ɗaurin shekara goma, ba tare da zabin
biyan tara ba”.. da na kashe Wa? Ko kuma da na aikata wane laifi? Da har za a
zartar man da wannan hukuncin? Shari’a ce yanzu alka fara na sanya lauyoyi na
su ɗaukaka ƙara kuma in sha Allah zuwa gobe ma na bar gidan nan, domin da zaran
an karɓi takardar ɗaukaka ƙarar za a bayar da beli na, sai kuma me?
Ta yi murmushi ta ce, “Allah ya baka haƙuri ni ba da wata manufa na zo ba
dama na zo ne domin samo hanyoyin da zaka fita daga wannan gida, saboda ba zan
manta da taimakon da ka yi man ba, wanda ya sa na mallaki gida, duk da cewa dai
kai ma ka fitar da kanka a lokacin amma dai in abokin huɗɗa ya shiga wani hali
akwai buƙatar a shiga cikin lamarin domin kawo masa agaji..”
“Lokaci ya yi malama kin san yanzu ba lokacin ziyara ba ne kawai dai an bar
ki ne”, wani ɗan tsukakken jami’in gyaran hali ne yake magana a ƙoƙarinsa na
shigowa cikin ɗakin. “a matsala ofisa hakan ma da ka yi man na gode, kuma na
isar ma da saƙon da na ke son isar wa.” Fatima ta mayar masa da martani tana
ƙoƙarin fice wa daga ɗakin.
Tun bayan da aka mayar da ni ɗaki ba abinda nae faman yi sai tunani, da
ƙyar na samu na yi sallah azahar da la’asar yanzu kuma da muka kammala sallar
magariba, na zauna kamar ina lazimi, amma ba abin da ke faɗo man a rai sai
tunanin yadda na shigar da Fatima har ta samu gidan da ta buƙata nima kuma na
samu rabona, na tuna cewa a lokacin babu sunan Fatima a waɗanda za a ba gidan
amma ta fiya kuɗi da ake buƙata tare da wasu ƙarin kuɗaɗe muka zare wani form
muka mayar da nata, bayan an bata gidan kuma ma kuje muka yi shige da fice
tsakaninmu da ma’aikata tsara birane da ke da alhakin yanka filaye da taswirar
wurare na bankinmu, aka ƙara matra fili mai girma daga cikin filin da aka ware
domin gina masallaci a rukunin gidajen.
Mu da muka yi aikin sai da muka tashi da wasu filaye masu girma a wajen,
wanda duk wannan abun shugaban mu bai sani ba mu kaɗai ke kidanmu muke rawarmu....
“ƙarar buga ƙofar ɗakin mu ce ta katse man wanna tunani na tashi na nufi baƙi
ƙofar ɗakin, wani ne sanye da kayan waɗanda aka tsare ya miƙo man wata roba ta
wata ‘yar kafa dake jikin kyauren. “ga abincinka” abin da ya faɗa ke nan kawai
ya juya. Na kalli abin da aka ce shi ne abinci na ina juya shi cikin takaici ko
almajirin gidana ba za a zuba mashi abinci a wannan robar ba, kuma abin da ke
ciki na gaza bambancewa tsakanin tsari da kuma tuwo, wasu hawaye masu zafi suka
zubo man a fuska, na yi tsaye na gaza matsawa ki’ina daga bakin ƙofar ɗakin.
Lallai na shiga matsala abin da na iya furtawa ke nan, na tuno da irin
tarin dukiyar da na mallaka amma wai nine aka yankewa hukunci ba tare da zaɓin
biyan tara ba. Na tuna ranar da aka kawo man sammaci ina zaune a gida wai ana
tuhumata da yanka filaye inda bai dace ba ta ɓarauniyar hanaya da amfani da
kujerata wajen raba filaye yadda bai kamata ba, wanda a cewar su wai hakan ya
haddasa asarar dukiyoyi da rayuka a unguwar Galadima da muka yamnka gab da
saukar gwamnatin da ta shuɗe.
A lokacin dariya na yi ina kallon abun matsayin shirme, na ɗauko wayata na
kira shugaban jam’iyya duba da cewa duk wasu abubuwa da shi muka shiryasu, amma
abin da ya ce man shi ne, “Musa kasan dai ba gwamnatinmu ba ce, kuma kafin mu
tafi sai da muka yi ma ƙoƙari muka sa ka koma aiki da gwamnatin tarayya, duk
domin mu tseratar da kai, yanzu wannan wutar kai ya kamata kasan yadda zaka
kashe ta”.
Duk da haka ban ɗauki abun da muhiummanci ba hakan ya sa na kira lauyana na
sanar da shi, amma ranar da aka fara zaman farko a kotun na fusknaci akwai
matsala, domin har sabon sakataren gwamnati da manyan jami’an gwamnati mai ci
sun halara wajen, na yi mamaki da cewa ni kaɗai ake tuhuma da laifi duk da cewa
ba ni kaɗai bane na kitsa abubuwa.
Lauyan masu gabatar da ƙara ya yi bayanin cewa ana tuhuma ta da laifin yin
amfani da ofishi na, na sanya mutane cikin matsala, ya bayyana cewa, yadda muka
shirya kutuguilar yanka filayen unguwar Galadima ta hanyar saida hanyoyin
magudanan ruwa da wasu filaye da aka ware domin gina wasu abubuwa, shi ya
haddasa matsalar da aka samu a yankin wanda ruwa ya gaza samun hanya har ya yi
wa talakwa ɓanna na rusa gidaje da asarori dama rasa rayuka.
Haka kuma ya gabatar da taswirar zanen unguwa na farko da yadda ya kamata a
ce an yanka ta, amma na yi amfani da ofis ɗina na yayyankawa yan uwa da abokan
arzuka filaye.
Ƙarshe ya bayyana cewa laifin da ake zargi na farko ya saba dokar aikin
gwamnati ta ƙasa sakin layi na takwas cikin ba. Laifi na biyu kuma cin amana ne
na ƙasa.
Duk ƙoƙarin da lauya na ya yi na kare ni amma abun ya ci tura sakamakon
hujojin da aka riƙa gabatarwa masu nuna cewa lallai na aikata wannan laifin.
Kafin yanke hukuncin sai da alƙalin ya ɗauki tsawon lokaci yana bayyana wa
mutane muhimmancin in suka ga an yanka filaye ba bisa ƙa’ida ba da su je kotu
su kai ƙara ba wai su tsayaba sai an samu matsala sannan a shiga taraddadi, ya
bayyana cewa ba wani mai hurumin yanka filaye ba bisa ƙa’ida ba koda gwamnati
ce ta yanka su to zaku iya kawo ƙararta sai a diba masalahar abun domin fitar
da mutane daga cikin matsala.......
“Wai Musa tsayuwar me kake a nan tun ɗazu? Ya kamata ace fa ka shigo daga ciki
ka zauna domin kana da hurumin da zaka sa a riƙa kawo ma abinci daga gida kamar
yadda ake yi man....” maganar abokin zaman ɗakina ne ta dawo da ni cikin hayaci
na, cikin rashin ƙwarin guiwa tare da nadama na nufo kan gadona hawaye na
kwararo man a ido, ina tunanin duk wannan halin da na shiga Fatima P.A tana da
masaniya kuma ita ce inji na faɗa wa ta a wannan hali, sai yanzu na tuno da
ita, harƙallar da muka yi da ita kuma ta faɗo man a rai kuru-kuru lallai ban
kyauta ba, abin da na cigaba da furtawa ke nan......
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.