Citation: Torankawa, M. U. (2025). “Karin Magana a Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai.” In Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 03, No. 02, Pp. 160 – 166. www.doi.org/10.36349/djhs.2025.v03i02.020.
KARIN MAGANA A WAƘOƘIN
ALHAJI MUSA ƊANBA’U
GIDAN BUWAI
Na
Malami, Umar
Torankawa
Sashen Gudanar Da
Shirye-shirye, Rima Television Sokoto
Tsakure:
Sunan wannan maƙala
shi ne karin magana a cikin waƙoƙin Alhaji Musa Danba'u Gidan Buwai.
Manufar maƙala
ita ce nazari da sharhi kan yadda Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai yake sarrafa karin magana a cikin
wakokinsa don a fito da baiwa da hikimomi da zalaƙar harshe da Allah ya ba shi wadda yake
amfani da su wajen shirya waƙoƙinsa. An bi hanyoyi guda biyu wajen
binciken, wato yin hira da iyalansa da abokan hulɗarsa
musamman waɗanda suke
taimaka masa wajen gudanar da sana’arsa ta waƙa, da kuma nazarin waƙoƙin. An
dora aikin ne bisa ga littafin Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau mai taken Jagoran
Nazarin Waƙar
Baka. Bayan nazarin waƙoƙin. Sakamakon ya nuna akwai karin magana a cikin waƙoƙin
nasa.
Gabatarwa
Waƙar baka, waƙa ce da galibi mawaƙan kan shirya nan take ba tare
da wani tanadi na musamman ba. Duk da cewa wasu mawaƙan kan shirya waƙoƙinsu a gida kafin su je inda za su aiwatar da su. Galibi
wasu nan take suke shirya waƙoƙin, kuma hikimomi da azanci da
basirar waƙar da
salailan sukan zo musu ne a lokacin da suke rera waƙoƙin. Alhaji Musa Ɗanba’u
Gidan Buwai ɗaya ne daga cikin shahararrun
mawaƙan baka a ƙasar Hausa, waɗanda Allah ya ba hikima da fasaha, da azanci wajen gudanar
da waƙa. An kalli mafi yawa daga cikin
waƙoƙinsa, kuma aka yi ƙoƙari aka fito da karin magana a
ciki. Kamar kowane nazari akan sami tsari na musamman da ya
kamata a gabatar kafin
gudanar da shi, wannan maƙala an dubi waƙoƙin Alhaji
Musa Ɗanba’u ta hanyar nazarin karin magana da
suke ɗauke dasu da kuma nuna misalai daga wasu ɗiyan waƙoƙinsa tare da yin sharhi dai-dai gwargwado. An
kasa wannan aikin
maƙala zuwa matakai guda huɗu
kamar haka:- Mataki
na farko kuwa shi ne gabatar wa ga aikin gaba ɗaya
sai mataki na biyu inda aka yi waiwaye akan tarihinsa da kuma yadda ya fara waƙa da mastayinsa a cikin mawaƙan baka na Hausa. Mataki na uku
ya ƙunshi bayanai akan karin magana
da yadda Alhaji Musa Ɗanba’u
Gidan Buwai ke sarrafa shi a cikin waƙoƙinsa tare da kawo misalai daga
cikin ɗiyan waƙoƙin da kuma yin sharhi dai-dai gwagwado. Mataki na huɗu kuwa shi ne kammalawa.
Asalin Alhaji Musa Ɗanba’u
Gidan Buwai Da Haihuwarsa
Mahaifin Musa Ɗanba'u bisa asali shi mutumin ƙasar ƙwargaba ne
da take cikin yankin ƙaramar
Hukumar Mulkin Wurno ta Jihar Sakkwato, Nijeriya. Sunansa kuwa Abdullahi Mai-Ɗan-Jaki ko kuma yadda waɗansu
suke kiran sa da Audu Jikan Liman. Wato Mahaifin Abdullahi, Liman Muhammadu ne
ya yo ƙaura daga can ya dawo Gidan Buwai da
zama. Abdullahi makaɗin goge ne, amma haye ya yi domin kuwa bai gaji kiɗa
daga iyayensa ba. Hasali ma, mahaifin Abdullahi, Liman Muhammadu, malami ne
wanda ya kafa makarantar ilmi, sannan ga shi liman. Shi kansa Abdullahi,
mahaifin Musa, malami ne har kuma ya fara limanci, sai ya saki, ya kama
harakar kiɗan goge. (Gusau 2016: 10).
Mahaifiyar Musa Ɗanba'u kuwa
sunanta Aminatu, amma an fi kiran ta da Umma, ita kuma haifaffiyar garin Gidan
Buwai ce, kuma mahaifinta wato Malam Musa na ɗaya
daga cikin malaman garin Gidan Buwai.
An sami riwayoyi
mabambanta dangane da shekarar haihuwarsa[1],
inda a riwayoyin an ambato cewa an haifi Musa Ɗanba'u Gidan Buwai a shekarar 1955 da
shekarar 1958, da
kuma 1962.
A cewar Gusau
(2016: 10-11) wanda kuma wannan takarda ta fi dogara gare shi, an haifi Musa Ɗanba'u ne a shekara ta 1958 wato
lokacin yunwar muɗa a ƙasar Hausa, a garin Gidan Buwai
ta gundumar Rara da ke ƙaramar
hukumar Raɓa a Jihar Sakkwato. Kamar yadda
Shehin Malami Sa'idu Muhammad Gusau ya kawo a Littafinsa
Sunan da aka raɗa masa shi ne Musa kamar yadda Musulunci ya aminta ga duk yaron
da aka haifa, kuma ya cika sati. Baya ga sunan yanka, Musa na da sunan laƙabi, wato Ɗanba’u[2].
Da yake Musa ya
girma a gidan karatu bai sha wahala ba wajen neman ilimi don kuwa ya fara
karatu ne a wurin kakansa, Liman Muhammadu.
Daga bisani ya
koma wurin mahaifinsa Abdullahi ya ci gaba, inda a nan ne ya sami sauke Alƙu'ani, kuma ya ci gaba da
karatun sani, na littattafan fiƙihu
irin su Ahalari da Ishimawi da Risala da kuma ƙari
da littattafan hadisai irin su Muwaɗɗa da Buhari da sauransu.
Kamar yadda ake sanya kowane yaro makarantar boko in ya kai mizanin shiga
musamman lokacin da ya yi shekara shida zuwa bakwai, shi ma Musa Ɗanba'u an sa shi makarantar boko, sai dai ba don
mahaifinsa yana da sha'awar ya yi karatun ba, ya yi hakan ne kawai don cika
umurnin masu gari. Bayan da tafiya ta fara sai ya fahimci akwai waɗansu
matsaloli da suka dabaibaye harakokin gudanar da aikace-aikacen gida da na
gonaki, sanadiyyar zuwan Musa Ɗanba'u
makarantar boko[3],
kuma shi Abdullahi mahaifin Musa ba mazauni wuri ɗaya
ba ne, wannan ne ya haifar da aka cire Musa Ɗanba'u daga makarantar boko a lokacin yana aji uku na
firamare, daga nan ne bokonsa ya tsaya.(Torankawa, 2025: 31).
Musa Ɗanba'u ya kasance mutun managarci wajen
nema wa kansa sana'ar da zai dogara da ita domin tallafa wa ga sha'anin gudanar
da harkokin rayuwarsa na yau da kullum, a irin wannan ƙwazo ne ya yi sana'o'i kamar sana'ar taula wato sayar da
ruwa a birnin Kano da sana'ar kayan gwangwani, wadda ya sami ɗaukaka
a cikinta a wancan lokacin, inda sai da ya kai yana yi wa motar Roka lodi shi
kaɗai. Wannan
sana'a ta kayan gwangwani sana'a ce da akasari jama'ar Gidan Buwai suke yi a
lokacin, kuma sun sami shahara a cikinta. Haka kuma ya kasance manomi.
Musa Ɗanba'u ya fara koyon kiɗa da waƙa
ne cikin mutane biyar da suka zauna tare da wani makaɗin ganga mai suna Bawa Mai Ganga, kuma sun yi yawace-yawacen
kiɗa tare da shi. Daga wannan
tafiya ce Musa Ɗanba'u ya
fara waƙoƙin kokawa da noma, inda ya ci
gaba da gudanar da waƙoƙin ta yin rangadi musamman a
garuruwan da ke zagaye da Gidan Buwai har ma da waɗansu da ba zagaye da garinsu ba, wato kamar irin su Acida da
Wurno da Kware da Gande da Gwadabawa da Illela da Gada musamman a ranakun da
kasuwanninsu,
ke ci. A irin wannan ne ya haifar da zaman Musa Ɗanba'u a garin Acida da Illela, inda a halin yanzu iyalansa
da yaransa wato ƙungiyarsa
kusan dukkansu suna zaune ne a garin Illela.
Bayan waƙoƙin kokawa da noma, Musa Ɗanba'u ya yi waƙoƙi ga rukunoni na
mutane da yawa na
siyasa da na sarauta da na kishin ƙasa da na
faɗakarwa wato waƙoƙin wayar da kan jama'a da sauransu.
Daga lokacin daya fara waƙa, shi ne
ya zama jagoran ƙungiyar waƙarsa, kuma a yawancin lokuta shi yake fara ƙulla waƙa. ƙungiyar waƙar Alhaji
Musa Ɗanba’u ta ƙunshi 'yan amshi da makaɗa
da kuma sauran masu taimakawa wajen gudanar da kiɗa.
Alhaji Musa Ɗanba’u ya
auri mata guda shida a lokuta mabamtanta. zuwa rasuwarsa ya bar mata uku da
suka yi masa wanka, wato takaba da kuma 'ya'ya goma shatara (19), goma (10)
maza, tara (9) kuwa mata ne.
Allah ya yi wa Alhaji Musa Ɗanba'u
rasuwa ranar Talata 7/04/2015 jin kaɗan bayan an
sanar da cewa Muhammadu Buhari ya ci zaɓe, ranar
Talata 31/03/2015. A lokacin Alhaji Musa Ɗanba'u
ya shiga aka yi murnar cin zaɓe da shi inda ƙura
ta turnuƙe, ya faɗi,
aka kai shi asibiti. Mako ɗaya yana jinya, Allah ya karɓi
ransa. Allah ya gafarta masa, ya jiƙansa.
(Gusau 2016: 12).
Karin Magana
"Karin
magana wata dabara ce ta dunƙule
magana mai yawa a cikin zance ko 'yan kalmomi kaɗan,
cikin hikima. Ya
ƙara da cewa karin magana,
yawanci yana da ɓari biyu: ɓari na farko, yana yin jimlataccen bayani ko furuci na wata
manufa, ɓari na biyu kuwa, yana yin
sharhi ko ƙarin
bayani, kan abin da ɓari na farko ya faɗa".
(Ɗangambo, 1984:36). Karin magana
wata tsararriyar magana ce wadda take a gajarce wadda take bayar da ma'ana
gamsasshiya mai faɗi da yalwa idan an bayyana". (Gusau, 1986:1). Karin magana
wata 'yar gajeriyar jimla ce ta hikima; wadda ta ƙunshi
ma'ana mai yawa in za a tsaya a yi bayaninta. Kuma yakan ƙara wa salon magana daɗi da armashi, yakan nuna gwanintar iya maganar mai magana,
kuma ya sa mai sauraron maganar rashin ƙosawa
da zancen da ake gaya masa". (Muhammad, 2005:59). Shi kuwa 'Yar'aduwa, (2007:79-84)
cewa ya yi "Karin
magana wata 'yar jimla ce gajeriya da mai magana zai faɗa ta hikima, amma kuma ta ƙunshi ma'ana mai yawa idan an tashi yin sharhinta.
A taƙaice dai ana iya cewa karin
magana wata tsararriyar
jimla ce gajeriya da takan zo a dunƙule,
kuma mai tattare da hikima da yalwa a lokacin da ake son bayyana ko sharhi
game da abin
da ta ƙunsa.
Makaɗan baka na Hausa suna amfani da
wannan dabara ta karin magana don nuna gwaninta da naƙaltar harshe da kuma yabo ga
uwayen gidansu
ko kushewa abokan
gabar uwayen gidansu ta hanyar yi musu habaici da shaguɓe ko gugar zana. Alhaji Musa Ɗanba'u na daga cikin makaɗan baka da yake yin karin magana a cikin waƙoƙinsa kamar yadda aka gani a ɗiyan
waƙoƙinsa,
kamar haka:-
Karin Magana na Yabo
Yabo na nufin
ambaton kalmomi na sambarka da nufin nuna amincewa hali ko ɗabi’u kyawawa na wani mutum ko dabba ko wani abu. Awaƙoƙin baka ana yi wa mutun yabo ta nuna halayensa kyawawa ko
siffanta shi da wasu ɗabi’u ko ayyuka waɗanda za su ƙaramasa
kwarjini da martaba a idon mutane. (Gusau, 2002: 29).
Yabo na cikin
muhimman turakun waƙoƙin baka wanda mawaƙi yake yi domin Ɗaukaka uban gidansa, Makaɗan baka da dama suna ɗaukar wani Karin Magana su naɗe yabo ga uban gidansu a cikinsa wanda sai an fasa Karin
maganar sai a ga an yabi gwarzon da kalmomin masu dangata shi da addini ko
baiwa ko kyauta ko asali mai kyau ko makamantantan waɗannan abubuwa. Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai ya yi irin wannan yabo ta hanyar kawo
Karin Magana ga wasu uwayen gidansa domin ya ƙara ɗauakaka su, ya nuna kyakkyawan
matsayinsu ga duniya. Ga misali a cikin wasu daga ɗiyan waƙoɗinsa kamar haka:-
Waƙar
Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko
Gwamnan jihar Sakkwato mai taken "Gwamnan Mun Yi Mun ƙare" Musa Ɗanba'u
ya zo da dabarar amfani
da karin magana ya yabi gwarzon nasa kamar haka:-
In rana ta ɓullo
hannu ba ya ruhe ta,
Alu
ka ƙara shiri lokacinka ne ɗan Garba,
Baba ka ƙara
matsawa mu karya 'yan DPP,
Kai dai Alu ka ƙara
matsawa mu karya 'yan DPP.
(Alhaji
Musa Ɗanba’u Gidan Buwai: Waƙa"Gwamna
mun yi mun ƙare")
A wannan ɗan waƙa
mawaƙin ya zo da karin maganar Hausawa
a layi na farko da yake cewa in rana ta ɓullo, tafin
hannu ba ya rufe ta. Wato in lokacin abu ya yi ba mai iya hana shi, yana nufin
lokacin ubangidansa ne, 'yan adawa su yi haƙuri ba su iyawa, wato a nan yana nufin ubangidansa shi ne
rana da hannu ba ya iya rufewa. Hannu kuwa na nufi dandazo magabta wato ‘yan
adawa da suke kai kawo na ganin sun ga bayan uban gidansa, to amma ba su iyawa
saboda kwarjininsa da ɗakakarsa tamkar haske rana ne da tafin hannu ba zai taɓa
rufe shi ba.
Haka kum a ɗan waƙar da ke biye Ɗanba'u ya ambaci wani karin magana kamar haka:-
'Yan adawa ku yi haƙuri
da ikon Allah,
Tun da kun san in lokacin mutum ya kama,
Karo da shi ba daɗi,
Hasadar
da sukai ma Aliyu ta zama taki.
(Alhaji
Musa Ɗanba’u Gidan Buwai: Waƙar "Gwamnan
Mun Yi Mun ƙare")
A layi na huɗu kuwa ya daɗa fito da karin magana da cewa “Hasadar da su kai ma Aliyu ta zama taki”, abin nufi a nan she ne
hasada ga mai rabo taki ce, wato hasadar da suke wa ubangidansa ta zame masa
taki domin kullum sai daɗa samun nasara yake yi a cikin tafiyarsa ta siyasa.
A wata waƙa da ya yi
wa mataimakin gwamna Mukhtari Shagari mai taken "Ɗan Sadauki Aikinka ya yi Kyawo" Ɗanba'u ya zo da irin wannan dabara ta karin magana, kamar
haka:-
Jagora: Zakaran da Allah yac ce ya zan cara,
Ko ana yin mazuru ana shaho,
'Yan Amshi: Babu halin da zai sa ya bar carar.
(Alhaji
Musa Ɗanba’u Gidan Buwai: Waƙar "Ɗan sadauki aikinka ya yi kyawo")
Wannan ɗan waƙa mawaƙin ya yi amfani da karin magana da Hausawa suke cewa
zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana muzura ana shaho sai ya yi.Wato yana
mai da jawabi ne irin na ɗan waƙar da ya
gabata na nuna irin ɗaukaka da kwarjinin da Allah ya yi wa ubangidansa ta ba
shi nasara a kan abokan gaba, da kuma yi wa 'yan adawa hannunka mai sanda da su
yi haƙuri da ikon Allah.
Karin Magana na Kushewa
Kushewa na nufin
ambaton kalmomi masu nuna kada daraja ko muruwa ga abokan gaba musamman ta
amfani da ɗaya daga cikin zantukan magana
na azanci, wato habaici[4] a wuri
aiwatar da Karin Magana, da nufin nuna hali ko ɗabi’u
marar kyau ta hanyar sakayawa, ba tare da ambaton suna ba. Makaɗa da mawaƙa
na amfani da wannan dabara ta azanci don nuna gwaninta da ƙwarewa wajen nakasa daraja ko
muruwa ta abokokin adawarsu ko abokan adawar uwayen gidansu, kamar yadda ya
fito daga cinkin misalan Karin Magana a cikin wasu daga ɗiyan waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai kamar haka:-
A
wannan waƙa ta Gwamna Wamakko mai taken"Mai Ban Tsoro
Magatakarda Wamakko" Alhaji Musa Ɗanba'u
ya yi karin magana inda
yake ce wa:-
In ka ji ƙi-gudu sa-gudu ab bai zoba,
Ranar zaɓen ka ɗan Barade na Wamakko,
Waɗansu maza har Yamen suna gudu.
(Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai: Waƙar
"Mai ban
tsoro magatakarda wamakko")
Makaɗin ya zo da karin magana na habaici ne mai ɗauke
da kalmar in a farko, a layi na farko
inda ya ce In ka ji ƙi-gudu sa-gudu ab bai zoba, wato yana nufin duk aka ji mutum ya ce ba ya gudu abin
guda ne bai gani ba don ga wasu sun yi karo da gwarzonsa, wato 'yan adawa sun
gudu har sun kai Yamen saboda tsoron ubangidansa. A nan ya yi amfani da wannan
dabara ta Karin
Magana na habaici don ya kushe
abokan hamaya da kuma nuna rashin dauriya da ‘yan adawa ke da shi.
Haka ya ƙara kawo karin magana a wannan ɗan
waƙa da ke tafe kamar haka.
Jagora: Iyakacin guguwa duk ta ɗau
yayi,
Tana
ganin dutsi dole tab bar shi,
'Yan Amshi: Don
babu damar ta miƙa ta ɗauko shi.
(Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai: Waƙar"Ɗan sadauki
aikinka ya yi kyawo")
Ɗanba’u ya zo da wannan karin magana ne
mai ɗauke da sigar habaici don ya zolayi abokan gaba da ɗaga
darajar ubangidansa inda ya kira “yan adawa da sunan yayi da iskarda guguwa kan
iya hurcewa da su, amma fa ga ubangidansa ya yi abuntarwa[5]
da cewa dutsi ne da iskar guguwa ba za ta ɗaukar
shi ba saboda ƙarfin da
yake da shi a fagen siyasa.
Wannan waƙa ta DPN
mai taken"Alheri Yanzu Kowa Buƙatatai
Ya Kai" Ɗanba'u
Gidan Buwai ya yi amfani da wannan dabarar ta karin magana a cikin wannan ɗan
waƙa kamar haka:-
Jagora: Mi ar ranar kilinge,
Ga harakar duniya,
Ko ga shi cikin gida,
'Yan Amshi: Kyalla shurewa takai,
Jagora: Yanzu ko ga shi cikin gida,
'Yan Amshi: Kyalla shurewa takai.
(Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai: Waƙar"DPN ta yi dai-dai da ‘yan Nijeiya")
A nan mawaƙin ya yi
karin magana ne ta hanyar yi wa abokan gabar ubangidansa arashi ne da ke nuna
rashin amfaninsu ga jama'a, kuma raggo maras takaɓus
ko yin takar-takar. Hausawa na cewa kilinge kana gida aka mushe, wato yuƙa ce maras kai wada ake amfani da ita wajen wasa yuƙa, ko kuma a ce ya yi ƙoƙarin Kushe
su ta hanyar nuna irin rauni abokan adawar ta kwatantasu da kilinge wato wuƙar da ba ta da ɓota. Wato bai iya gudanar da komi a
harakar al’umma balantan a ba shi jagorantarsu.
Har wa yau makaɗin ya zo da karin magana a cikin wannan waƙa ta Sarkin Musulmi Macciɗo mai
taken"Gwauron Giwa Jikan Hasan Ɗan Amadu" da
cewa:-
Yaro: Ɗanba'u mai kiɗa,
Mamaki ɗai
nikai,
Mamakin duniya,
Ni ko duniya,
Ina jin tsoron ki,
Ka ga harakar 'yanAdam,
Tana ban mamaki,
Wasu sun ce,
An hana ni waƙa nan Sakkwato,
ƙarya ƙaryar ƙasa,
Zancen banza,
Don ƙarya
ba magana ba,
Wasu sun ce,
An hana ni waƙa,
Nan Sakkwato,
Ni ko na gaya masu,
Kura ko
bata ci,
Kare nasaunan ta,
Yanzu ko da ba ni waƙa,
ƙafata
ta tsaya,
Tun da duk Najeriya,
Wani mai kyauta da naira,
ƙasar
nan na sani,
Wani mai kyauta da mota,
ƙasar
nan na sani,
Ko ba Najeriya ba,
Musa in tsallake,
In tahi Nijar,
Mu iskikke,
Tanja Mamadu.
(Alhaji
Musa Ɗanba’u Gidan Buwai: Waƙar "Gwauron Giwa Jikan Hasan Ɗan Amadu")
A wannan ɗan waƙa Alhaji
Musa Ɗanba'u Gidan Buwai ya yi amfani da
karin magana mai nuna habaici don
a layi na sha bakwai da na ashirin inda ya yi shaguɓe, ta hanyar kushewa ga
abokan sana'arsa ta waƙa ko
magabta don ya nuna cewa ko ba ya waƙa
ya fi ƙarfinsu. Ya siffanta kansa da kura su
kuwa abokan gaba ya siffanta su da kare wanda an san yadda yake tsoron kura, da
kuma nuna cewa ya kafu a wajen waƙa saboda ya
san mutane masu karimcin ba da kyautar kuɗaɗe
da motoci a ciki da wajen ƙasarnan
wato ya kan tsalaka maƙwatan ƙasa irun su Nijar da sauransu.
Kammalawa
A wannan maƙala an
fahinci yadda Alhaji Musa Ɗanba’u
Gidan Buwai ya yi amfani da dabaru da hikimomi daban-daban ya saka karin magana
a cikin jerin waƙoƙinsa mabam-banta da ya yi saboda isar da saƙon da ke ciki. A maƙalar
an ga yadda karin magana ke ƙawata waƙoƙin baka na
Hausa don yin armashi wajen rerawa da kuma samar da nishaɗi
ga masu sauraro ba tare da gajiyawa ba ko ƙosawa. Haka
kuma an nuna yabo da kambama uwayen gidansa ko kushe wa da nakasa abokan adawar
uwayen gidansa.
Manazarta
Bala, da wasu,
(1993). "Alhaji Musa Ɗanba'u
Gidan Buwai Da Waƙoƙinsa" Kundin Digiri Na
Farko. Sakkwato: Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Ɗangambo, A. (1982). Rabe-RabenAdabin Hausa Da Muhimmancinsa
GaRayuwar Hausawa. Kano: Maɗaba'ar Trumph.
Garba, M. (1998).
"Azancin Magana A Waƙoƙin Makaɗan Baka". Kundin Digiri Na Biyu. Kano: Jami'ar Bayero
Gusau, S. M.
(2002). Sarkin Taushi Salihu Jankiɗi. Nazari da Ratayen Wasu Waƙoƙinsa Baraka Publishers Limited,
Kaduna.
Gusau, S. M.
(2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers
Limited.
Gusau, S. M.
(2016). Makaɗa
Da Mawaƙan Hausa, Littafi
Na Biyu. Kano:
Century Research and Publishing Limited.
Hirabri, S. (2017). “Zambo Da Habaici A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji
Musa Ɗanba'u Gidan Buwai”. Kundin Digiri Na Farko.
Sakkwato: Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Muhammad, Y. M. (2005), Adabin Hausa
Zaria:
Ahmadu University Press Ltd, Nigeria.
Shagari, B.M. (2011). "Waƙoƙin Jam'iyyar PDP Na Alhaji Musa Ɗanba'u Gidan Buwai". Kundin Digiri
Na Farko. Sakkwato: Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Torankawa, M.U (2025). "Nazarin Azanci A Cikin Waƙoƙin Alhaji
Musa Ɗanba’u Gidan Buwai " Kundin Digiri
na Biyu. Sakkwato:
Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Yahya, A.B.
(2016). Salo Asirin Waƙa. Sokoto: Guaranty Printers.
‘Yar’aduwa, T. M.
da Junadu, I. (2007), Harshe da Adabin
Hausa a Kammale Don Manyan Makarantun Sakandare. Printed by Nazarth Prees
Ltd Ibadan.
Hira
|
Suna |
Muhallin da aka tattauna |
Shekaru |
Ranar da aka tattauna |
|
Alhaji Shehu
Wazirin Musa Ɗanaba’u
Gidan Buwai |
A Garin Illela ƙaramar hukumar Illela Jihar
Sakkwato |
55 |
13/o5 2023 |
[1]Don }ari bayani, a dubi Bala da wasu, 1993. daShagari,
2011: 17 da Gusau, 2016: 11 da kuma Hirabri,
2017: 25 da Torankawa 2025: 28-29
[2] Don }arin bayani a dubi Shagari,
2011:16-17
da Gusau,
2016:10 da Torankawa 2025: 30
[3] Hira da Alhaji Shehu Gidan
Buwai Wazirin Musa [anba’u kuma ]an’wansa na jinni ranar littinin 13/05/2025
[4] Habaici wasu kalmomi ne da ake fa]a a fakaice don a ɓata wa wani mutum rai ba tare da an bayyana mutumin da ake nufi }uru-}uru ba. Habaici ya fi zambo sau}i domin akwai sakaya zance a cikinsa wato ba a fitowa fili }arara a yi wa mutum shi, kuma ba a fa]in wata fitacciyar siffar mutum ko wani fitaccen halinsa. habaici riga ce duk wanda ya sa za ta shige shi. (Gusau, 2002:37)
[5]
Don ƙarin bayani a dubi (Yahya, 2016: 13) ko ([angambo, 2007: 46)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.