Citation: Abdullahi, B. and Soba, G. M. (2025). “Gudummuwar Umaru Ɗanjuma Katsina wajen Faɗakar da Al’umma: Wasan Kulɓa na Ɓarna a Faifan Nazari.” in Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 03, No. 02, Pp. 152 – 159. www.doi.org/10.36349/djhs.2025.v03i02.019.
GUDUMMUWAR
UMARU ƊANJUMA KATSINA WAJEN FAƊAKAR DA AL’UMMA: WASAN KULƁA NA ƁARNA A FAIFAN NAZARI
Na
Bala
Abdullahi
Sashen
Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe, Jami’ar Jihar Kaduna, Kaduna
and
Galadima
Mubarak Soba
Department
of Hausa, Federal University Dustinma
Tsakure:
Ayyukan adabi
da dama sukan yi nuni da tsarin siyasa da zamantakewa da addini da falsafar
al’umma. Don haka, marubuta adabi kan bayyana manufarsu ta hanyoyi mabambanta
ta waɗannan
ayyuka na adabi. Wasan kwaikwaiyo dai wani muhimmin reshe ne daga cikin rassa
na adabi, kuma ta hanyar wasan kwaikwaiwo akan faɗakar da al’umma game da
wasu matsaloli ko halaye mara nagarta da ta yi wa al’umma ɗaurin
minti da nufin nusar da su domin a gyara gaba ɗaya.
Ta haka ne wannan maƙalar ta mayar da hankali game da rawar da
marubuta wasan kwaikwayo kamar Umaru Danjuma Katsina ke takawa don ganin
al’umma sun faɗaku game da wasu matsaloli da suka yi musu
katutu. Nazarin gundarin saƙon littafinsa na Kulɓa
Na Ɓarna
(wato Content Analysis) shi ne abin da ya yi jagora wajen fito da rawar da
marubuta wasan kwaikwayo ke takawa wajen faɗakar da al’umma game da
wasu illoli da ke damfare a cikin al’umma don su guje masu. Daga ƙarshe,
an ɗora
wannan bincike a kan ra’in gudunmuwar adabi ga al’umma domin nuni da gudummuwar
da marubuta adabi ke badawa wajen wayar wa al’umma kai.
Gabatarwa
Shi dai wasan
kwaikwayo ɗaya ne daga cikin rassa
uku na adabin Hausa. Sauran biyun su ne waƙa da kuma zube. Wasan
kwaikwayo abu ne mai daɗaɗɗen tarihi a duniya, kuma babu wani wanda zai bugi ƙirjinsa
ya ce ga haƙiƙanin lokaci ko ranar da aka farasai dai bayanin
da aka sani kawai shi ne, wannan ɓangaren adabi ne da ya daɗe
sosai. Wannan muƙala ta yi duba ne zuwa ga nau’in rubutaccen wasan
kwaikwayo ne, tare da bayyana gudummawar marubuta wasan kwaikwayo wajen faɗakar
da al’umma, da yi musu hannun-ka-mai-sanda don su guji aikata wani abu maras
kyau, da kuma riƙo da halaye da ɗabi’u
kyawawa. An ɗauki wani marubuci mai
suna: ‘Umaru Ɗanjuma Katsina da littafinsa na ‘Kulɓa Na Ɓarna’ a matsayin misali.
Ma’anar
Wasan Kwaikwayo
Masana da
manazarta da dama sun bayyana ma’anar wasan kwaikwayo ta fuskar rarrabe
ma’anonin kalmomin guda biyu, ‘wasa’ da kuma ‘kwaikwayo’. Wato dai kalmar wasa
ta ƙunshi
ma’anar aiwatar da wani abu wanda ba da gaske aka yi ba, don nishaɗantarwa
da motsa jiki. Ita kuwa kalmar ‘kwaikwayo’ na nuna yin wani abu don kwatanta
wani abu ta hanyar sauya kama kwatankwacin yadda wani yake yi, mutum ne ko
dabba. Ga dai abin da wasu masan suka ce kamar haka:
Umar
(1987:46-48) ya bayyana wasan kwaikwayo a matsayin kamance ko kwatanta wasu
halaye na ɓangarorin rayuwa ta sigar
wasa wato abin ya kasance ba gaskiya ba ne. A yayin da Price (1913) ya ce; ‘drama
is an imitation of past action through dialogue and other symbols’’. Wato
wasan kwaikwayo kamance ne aikin da ya gabata ta hanyar tattaunawa tsakanin
‘yan wasa da kuma yin nuni da wasu alamu.
Shi kuwa Ɗangambo
(1984:4), a littafinsa mai suna Rabe-raben Adabin Hausa Da
Muhimmancinsa Ga Rayuwar Hausawa, ya ce: “Wasan kwaikwayo kamar yadda
sunan ya nuna, wasa ne da ake gina shi a kan kwaikwayon wani labara ko wata
matsala da ake son nusarwa ga jama’a. Akan aiwatar da labarin ko matsalar cikin
yaƙini,
wato zahiri.”
Shi kuma
Malumfashi (1985:15), a kundin digirinsa na biyu mai taken “Asali Da
Bunƙasar Rubutaccen wasan Kwaikwayo Na Hausa”, ya bayyana wasan
kwaikwayo da cewa: “Koyi ne da yadda wani ko wasu ke yin wani abu. A wajen
koyin a iya samun canza kama ta magana ko na tufafi.
`Yar’aduwa,
(2007:5) kuwa, a littafinsa na Wasan Kwaikwayon Hausa: Nau’o’insa da
Sigoginsa, ya ce: “Ana amfani da ilimi ne domin tattara halayen mutane
a kuma gudanar das hi a cikin tsarin wasan kwaikwayo cikin annashuwa don cin ma
wata manufa.”
Shi kuwa
Sulaiman, (2013) cewa ya yi: “A tawa fahimtar, wasan kwaikwayo, kwaikwayon wani
abu ne ta fuskar wasa inda harhaɗuwar wasu ayyukan `yan
wasa kan samar da cikakken labari don isarwa ga al’umma. Wannan labara
mai ɗauke da wata manufa kan iya kasancewa ya faru
cikin al’umma ko kuma ƙirƙirarsa aka yi.”
A taƙaice,
wasan kwaikwayo wasa ne da ake ƙirƙira
don kwaikwayar wani al’amarin da ya faru, ko ake hasashen faruwarsa ta hanyar
sauya kama, don kwaɗaitarwa da jawo hankalin
al’umma, ko tsoratar da su a kan wani abu kan ɗabi’u
ko kuma al’adu ko yanayin sauyawar rayuwar don a nishaɗantar
ko a faɗakar
cikin wasa.
Ra’in
Bincike
Gusau (2015) a littifinsa na Mazhabobin Ra’i da
Tarke A Adabi da Al’adu na Hausawa ya kawo bayanai ga yadda adabi take
ba da gudummuwa ga al’umma wajen inganta rayuwarsu da zamantewa.Wannan hanya ta
nazarin gudunmuwar adabi ga al’umma tana mayar da hankali ne ga rawar da adabi
yake takawa a hali na zamantakewa. Haka zalika, tana duba yadda adabi yake
tafiya da al’adu da fasahohi na al’umma da suke daɗa inganta rukunonin rayuwa. Don
haka wannan maƙala ta zaƙulo wannan ra’i domin yin nuni da yadda wannan wasa na Kulɓa na Ɓarna ke yin nuni da hali na
zamantakewar al’umma kamar yadda marubucin ya nuna cikin littafin.
Taƙaitaccen Tarihin Marubucin Wasan ’’Kulɓa Na Ɓarna’’
An haifi
Alhaji Umaru Ɗanjuma Katsina a ranar 10 ga Afrilu, 1950
a cikin birnin Katsina, unguwar Ƙofar Soro da ke ƙaramar
Hukumar Katsina, ta Jihar Katsina. Mahaifinsa shi ne Muhammadu Ɗanjuma
(Tsohon ma'aikacin N.A), sai mahaifiyarsa Hajiya Hadiza Lanso.
Umaru Ɗanjuma
Katsina ya fara karatun boko matakin Firamare a Giɗaɗo
Primary School Katsina' a shekarar 1966 ya kuma kammala a shekarar 1972. Yaa ci
gaba da karutunsa na Sakandare a makarantar
'Goernment Secondary School Katsina' daga shekarar 1972 zuwa 1975. Haka zalika,
ya yi ta karatu har ya sami takardar shaida ta kammala karatu na 'West
African School Certificate' (WASC) a shekarar 1980. Daga nan sai ya tafi
makarantar horo kan fim da Talabijin da ke birnin Landan, inda a nan
ne ya sami takardar shaida ta Difloma kan Motion Picture da kuma Difloma kan wasan
kwaikwayo da ba da umarni.
Alhaji
Umaru Ɗanjuma Katsina ƙwararre ne a fagen
aikinsa, a karon farko ya zama ma'aikaci a matsayin ƙaramin jami’in al'adu a ma'aikatar
yaɗa
labarai ta Arewa ta tsakiya da take Kaduna daga shekarar 1975 zuwa 1978. Daga
baya, Umaru Ɗanjuma Katsina ya zama jami'in kula da al'adu,
cibiyar nazarin al'adun Najeriya reshen Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya. A
shekarar 1980 ya zama babban jami'in al'adu a wannan cibiyar. Haka kuma a
shekarar 1986 ne, aka mai da shi a matsayin mataimakin mai jan ragamar masu
aikin fasaha na wannan Jami'a ta ABU.
A tsakanin
shekarar 1989, Alhaji Umaru Ɗanjuma ya yi aiki a
matsayin darakta na al'adun jahar Katsina, daga nan sai ya ajiye aikin gwamnati
a shekarar 1991. Daga ƙarshe,
ya rasu a watan Oktoba shekarar 2021 a Asibitin Gwamnatin Tarraya da ke Katsina
bayan shekaru 71 da haihuwa. Ya rasu ya bar mata biyu da yara da dama. (21st Century
Chronicle)
Baiwar
Umaru Ɗanjuma Katsina
Babu shakka,
Umaru Ɗanjuma Katsina yana da baiwa mai tarin yawa, musamman a fagen
wasan kwaikwayo, kasancewarsa marubucin wasan kwaikwayo, kuma ɗan
dirama, wannan ya ba shi damar rubuta wasannin kwaikwayo na rediyo masu dogon
zango da dama, wanda daga bisani aka buga wasu daga ciki. Kaɗan
daga cikin rubuce-rubucensa da aka buga, sun haɗa da:
1. Kulɓa
Na Ɓarna
1&2
2. Ai Ga
Irinta Nan, NNPC, Zariya
3. Baƙin
Bature, NNPC, Zariya.
4. The Agony
of Justice, NNPC
Alhaji
Umaru Ɗanjuma Katsina ya shirya wasannin kwaikwayo da suka haɗa
da:
1. Goggo mai
Gyaɗa
2. Kishiya
3. 'Ya'yan
Zamani
4. Muna Ji
Muna Gani
5. Kowa Da
Zaninsa
6. Kaico
7.
Dattijo-Babawo
Kasancewarsa
gwani a ɓangaren wasan kwaikwayo, wannan ya sa ya taka
muhimmiyar rawa har a ɓangaren wasan kwaikwayo
na Talabijin da finafinai. Ga wasu daga cikinsu:
1. The Second
Circle Produced by Prof. Harry Higher
2. Magana Jari
Ce
3. Kasagi
4.
Tambari
5. Karambana
6. Queen Amina
7. Ruwan Bagaja
8. Ga fili-Ga
-doki
Bayan waɗannan,
Alhaji Umaru Ɗanjuma Katsina ya yi wasu shirye-shirye na
musamman da kamfanoni masu zaman kansu, kuma ya zama memba a ƙungiyoyi
daban -daban, tare da samun lambobin yabo daga kamfanonin shirya finafinai na
gida da na waje.
Tsokaci Kan
Wasan ‘’Kulɓa Na Ɓarna’’
Wasan dai an
gina shi ne a kan wata yarinya mai suna Zaliha wadda take ƙarƙashin
kulawar ƙanin mahaifinta mai suna Malam Inuwa da matarsa Mai Nakada
bayan rasuwar mahaifinta. A wannan hali ne take zaune a gidan kawunta da nufin
zai aurar da ita da zarar ta kammala makarantar Firamare, amma hakan bai yuwu
ba, domin ta samu shiga makarantar gaba da Firamare wato sakandare.
Zaliha ta
kasance tana da fara'a shi ya sa ma take da samari masu zuwa wajen ta kamar
su Ɗanlondon
da Ɗantakarda
a yayin da ta zo hutu a gidan kawunta Malan Inuwa. Kodayake, shi Ɗantakarda
shi ne tsayayye wanda ake tunanin za a haɗa su aure da Zaliha idan
ta kammala karatunta. Ɗantakardar nan kuwa yana da mahaifiya mai
suna Goggo wacce ba ta amince da soyayyar da take tsakaninsu ba, don ita a
tunaninta duk wata yarinya 'yar makarantar boko ba tagari ba ce. A wannan hali
ne ake ta tafiya kafin wani Alhajin birni mai suna Alhaji Ruwan Ido da
kawalinsa Zumuɗi suka ci karo da Zaliha a hanya, suka shiga
neman bayanai game da ita waɗanda suka jiɓinci
gidansu da mahaifinta da kuma makarantarsu.
Alhaji Ruwan
Ido dai ya yi nasara domin kuwa da Zaliha ta koma makarantarsu ta kwana, Alhaji
da Zumuɗi
sukan bi ta makarantar, suna ba da cin hanci ga Baba mai gadi don ya ba su
izinin shiga don su gana da Zaliha. Da yake wasu matan suna da alamar kwaɗayi
a tattare da su, Zaliha dai ta amince da su tare da amsar kuɗi
a hannunsu har ta faɗa musu duba da za su yi
don sauƙin
ganin ta idan Allah ya sa sun ƙara dawowa, domin da za
su tafi Alhaji da Zumuɗi sun yi mata alƙawari
da cewa za su dawo don su fita, su je su yi mata sayayya a shago.
Zaliha da
Alhaji Ruwan Ido suka shiga yin shagali domin kuwa yakan zo ya ɗauke
ta daga makaranta ba tare da izini ba, su je gidan shaƙatawarsa.
Hakan ya sa idon Zaliha ya buɗe da kuɗi
da shagali. Ba a jima ba, ai sai ta aika wa Ɗantakarda wasiƙa
da cewa ai kada ma ya ɓata lokacinsa don
jiranta, don kuwa ita babu abin da za ta yi da ƙaramin
ma'aikaci, ta ƙara mai da cewa, ai ita yanzu ta sami 'yanci ta
zama "Indifenda".
Da yake Allah
ba azzalumin kowa ba ne, ya bai wa Ɗantakarda wata yarinya
mai suna Amarya a matsayin mata, suna zaman jin daɗi
da mutunta juna. Bahaushe dai kan ce; ' Komai nisan jifa dai ƙasa
zai dawo'. Zaliha dai ta kasance da ciki, aka kuma kore ta daga makaranta, ta
dawo gidan Malan Inuwa da matarsa Mai Nakada su kuma suka zama abin tsegumi a
wajen al'umma. Shi kuma Alhaji Ruwan Ido da ya aikata wannan ɗanyan
aikin ya ƙaryata shi ya yi, har yake barazanar zai kai Malam
Inuwa ƙara wajen alƙali. Ganin hankalin iyayenta ya tashi ya
sa Zaliha ta gudu daga gida zuwa can wani gari ta haihu, amma yaron ya rasu.
Daga nan ne ta ga ba ta iya haɗa ido da Malan Inuwa, sai
kawai ta zarce da zaman kanta abinta a gidan Magajiya da sauran mata masu zaman
kansu, abokanan lalata irinsu Fulani da ita kanta Magajiyar.
A wannan hali
ne Zaliha ta haɗu da Ɗanlondon
tsohon saurayinta da Malam Inuwa ke tunanin irin su ne samarin da suke ɓata
yara mata. Ɗanlondon ya kasance yana zaune a garin da Zaliha
take karuwanci a matsayin malamin tarbiyya da jin daɗin
jama'a. Daga ƙarshe dai Ɗanlondon a matsayinsa na
malamin tarbiyya ya shiga yi wa Zaliha da sauran abokan aikinta nasiha don su
shiryu, su bar wannan karuwanci. Duk suka yi nadama, ya kuma sako Zaliha a gaba
ya mai da ita wajen Malam Inuwa, ya kuma nuna buƙatarsa na ganin cewa
an ɗaura
musa aure da shi da Zaliha. A nan ya yi wa Malam Inuwa habaici da cewa; "
Kulɓa
na ɓarna
ana cewa jaɓa". Wato shi da ake tunanin yana cikin irin
samarin nan masu ɓata yara mata sai ga shi,
shi ne sanadin shiriyan Zaliha.
Gudummawar Umaru Ɗanjuma Katsina Wajen Faɗakar Da Al’umma
Yin la’akari da ra’in gudummuwar adabi ga al’umma, wanda
ke mayar da hankali kacokan game da rawar da adabi yake takawa a
hali na zamantakewa, an duba yadda Umaru Danjuma Katsina wato
murubucin wasan kwaikwayo na Kulɓa Na Ɓarna ya
yi amfani da adabi don faɗakar da al’umma game da wasu matsaloli da suka kunno kai
da nufin samar da mafita. Dangane da muhimman abubuwa da Umaru Danjuma Katsina
ya taɓo, sun haɗa da:
· Alhazan Birni A
Wasan "Kulɓa Na Ɓarna"
Watau
Umaru Ɗanjuma Katsina, ya yi ƙoƙarin
nuna wa al'ummar iri mummunarɗabi'ar nan ta Alhazzan
birni na ɓata yara mata 'yan makaranta. Wani abu muhimmi da
ya kamata a yi la'akari da shi, shi ne idan ɓera na da sata, to
daddawa ma da warinta. A yayin da Alhaji Ruwan Ido da Zumuɗi
suka je ganin Zaliha a makaranta, da ta ga kuɗi kuma suka yi mata alƙawarin
fita da ita don su je su yi mata sayayya a kanti, ai kuma sai ta ƙara
amincewa da su har tana cewa;
Zaliha:"To na ji mutum ba
ya cewa ba ya son mutum ko da yaya yake" shf. 35
Da kuma inda
take cewa:
Zaliha:"To sai an jima, don
Allah idan ka je gidan Kalima ka ce ina gaishe ta, af, idan za ku zo ne goben
ku yi ƙoƙari ku bari sai Baturiya
ta fita sannan ku yi wa Baba mai gadi magana sai ya buɗe muku ƙofar. Shf.36
Alhaji Ruwan
Ido dai mun ga yadda ya yi amfani da kuɗi da dabaru don ganin ya
jawo hankalin Zaliha kamar shafi 35 inda yake ce mata:
Alhji:"Ita maganar zuwa
wurin iyaye duk ki manta da ita, ni yanzu abin da nake so da ke shi ne ki yarda
ki amince da ni. Ɗan'uwan ki ne, kuma ko da
ban aure ki ba, ki sani dai duk abin da na kashe maki ba zan tambaye ki
ba". Shf 35
Ai da jin haka
ya kamata Zaliha ta san inda shi Alhaji Ruwan Ido ya nufa domin kuwa ga dukkan
alamu ba da aure ya zo nemanta ba, amma saboda kwaɗayi
sai ta amince da wannan yaudara ta Alhaji. Shi kuma da ya ga ya samu shiga ai
sai batun zuwa a shaƙata.
· Cikin Shege
Marubucin ya
ci gaba da nuni da illolin da Alhazan birni ke yi wa yara 'yan makaranta ta
hanyar nuni da cewa Zaliha ta samu ciki kuma aka koro ta daga makaranta, ta
dawo gida, ta zama abin kunya ga iyayenta.
M.
Inuwa: Ciki? Haba ba sai in yanka kafira ba.
Mai-Nakada:
‘To,
sai dai ka kashe ta. Amman don ciki, ciki ne! ke Zaliha zo duk wannan kuka ki
bar shi. Ba yanzu ne lokacin kuka ba, sai an fara yi maki gori. Yamzu ki gaya
mana gaskiya’. Shf.59. A bi rubutun nan kal-kalma a yi gyara
A nan,
marubucin ya fito da illa mace ta yi cikin shege, wanda ƙyama
da horo wajen a kauce wa aukuwar wannan aiki, ya sa har al’umma suke tsangwamar
duk wata mace da ta ɗauko cikin shege. Illar
ba a nan ta tsaya ba, don takan gangara ta shafi sauran ɓangarorin
rayuwa. Marubucin ya yi nuni kan yadda rayuwar Zaliha ta kasance da yadda
karatunta ya zo ƙarshe, amma a sanadiyyar cikin da ta yi mata aka
kore ta. Wataƙila ta yiwu sanadin wannan karatu da al'umma da iyayenta da
kuma ita kanta sun ci moriyar ilimin da ta samu ta hanyar koyar da yara,
musamman ma duba da la'akari da ƙarancin yara mata masu
ilimin boko.
Da yake shi
Alhajin Birni ne ai tuni ya ƙaryata cewa shi ne ya yi
mata ciki tare da barazanar zai kai ƙara wajen alƙali
don ana so a ɓata masa suna. Watau a taƙaice
ya lalata mata rayuwa gaba ɗaya, tun daga neman
iliminta har zuwa mutuncinta da martabarta a idon maƙwabta.
A Bahaushiyar al'ada, mafi girman abin kunya da mace za ta aikata shi ne ta yi
cikin shege, domin ba ta da wata sauran ƙima a idon al'umma don
haka ma maganar aure bai taso ba, sai dai ta bar gari ta koma wani gari da ba a
san ta ba.
· Karuwanci Da illa Ga Yara
Mata
A sanadiyyar
cikin da Alhaji Ruwan Ido ya yi wa Zaliha ne ya sa ta shiga wannan ƙasƙanci
na karuwanci, bayan ta gudu ta bar iyayenta, inda a nan ne ta haɗu
da tsohon saurayin nan nata (Ɗanlondon), wanda shi ne ya yi ƙoƙarin
jan hankalinta tare da nuna mata illar wannan mummunar hanya da ta shiga, wadda
ke ƙunshe
da haɗura
da dama, kuma zai yi wuya a sami nagari da zai amince da auren karuwa. Misali:
Zaliha: To, Ɗanlondon, ni kaina ba da niyyar zaman kaina ma fito ba, Allah dai
ya ƙaddara da sai na yi.
Ɗanlondon: Kin gani fa ko ‘ya’ya kika haifa idan sun girma
sun sami muƙami ba su da ikon walawa. Ko me suke yi a
ce ai wane ɗan banza ne. Yanzu ina daɗin wannan aiki? Kuma yanzu kina nan kina zaman kanki sai ciwo ya
kama ki, ke ba ki da wani ɗan’uwa wanda za shi riƙa kula da ke. Ki je ki mutu kuma wurin jana’izarki sai ‘yan daudu
da ‘yan iskan gari…’ shf. 67
Da wannan
nasihar ce da Ɗanlondon ya yi wa Zaliha ne ya ja ra’ayinta,
wanda ya nuna mata illar karuwanci ga ‘ya’yan da za a iya samu da yadda
rayuwarsu za ta kasance a nan gaba. Ya lurar da ita kan makoma ta masu karuwaci,
sukan yi mummunan ƙarshe da mafi ƙasƙancin
mutane a al’umma su suke jagoranci wajen binne shi.
Saƙon Da Ke Tattare Da Wannan Wasa
A wasan Kulɓa
Na Ɓarna,
Umaru Ɗanjuma Katsina ya yi nuni da illolin da Alhazan birni ke yi
wa yara mata, kuma sai ya ƙara nuna cewa waɗanda
ake tunanin su ne ke ɓata yara mata su ne matasa,
duba da irin shigar da suke yi da askin banza da kuma irin sunaye na hofi da
ake kiran su. Idan muka leƙa cikin wasan "Kulɓa Na Ɓarna" ai za mu ga cewa
kawun Zaliha wato Malan Inuwa akwai wata rana da ya tarar da ita da Ɗanlondon
a ƙofar
gida da Zaliha a tsaye ga abin da ya ce:
"…ke
kama hanya ki shiga gida kada na ƙara ganin wani ƙato a ƙofar gidan nan, (Zaliha
ta shiga gida) kai kuma malan wuce ka tafi, nan ba ƙofar gidan karuwai ba ne. Haka kawai kuke taruwa ku zo kuna sanya
yara a muganyar hanya" shf. 8-9
Sai kuma Ɗanlondon
ya mayar da jawabi da cewa:
"Allah
ya ba ka haƙuri malam, idan ka raba mu a nan ai ba
zaka raba mu a makaranta ba, kuma ka san dai komai rashin kunyata ba zan zo
gaban gidanka ba, domin in nemi wata hanyar shegantaka da ɗiyarka, ko zan yi ba nan za mu haɗu ba. Manyan ma'aikata da manyan Alhazai su ke ɓata 'ya'yanku ba mu ɗalibai ba. Mu me ke gare
mu da za mu ba su ban da cika takarda da wasiƙa. Allah sarki ƘULƁA NA ƁARNA ANA cewa JAƁA, kuma Allah shi ba ka haƙuri. Idan ni ɗa ne ga iyayena ba za ka ƙara gani na a ƙofar gidanka ba".
Shf. 9
Wato da wannan
magana ta Ɗanlondon marubucin ya isar da saƙon
da ke cikin wasan, duk da dai malam Inuwa ya raba su a wannan lokacin ba zai
iya raba su ba a makaranta ba, kuma a tunanina duk wanda zai wanki ƙafa
zuwa gidan su budurwa to ko ma akwai rashin kunya to kaɗan
ne. Idan ka kwatanta haka da halayyar Alhaji Ruwan Ido, da yake da lalata ya
neme ta ai bai je gidansu ba gudun kar a gan su tare, kawai sai ya bi ta
makaranta inda daga nan ne suka shirya inda za su riƙa
haɗuwa.
Shi ko Ɗanlondon da aka yi masa kallon ɗan
iska shi ne ya zo gidan don ganin ta.
Har ila yau,
inda ya ce da Malan Inuwa Alhazai ne suke ɓata 'ya'yanku ba ɗalibai
ba, ya ƙara fito da hikimar da ke cikin maganar nan ta Kulɓa
na ɓarna
ana cewa jaɓa ce. Don ko ta faru da Ɗanlondon
wanda yake ɗalibi ne ɗan
makaranta ba shi da komai sai takardu, alhali waɗnda ke ɓarnar
su ne Alhazawa da ke gefe a manyan ma'aikatu kamar yadda wannan ya yi wa
Zaliha. Ya yi mata ɓarna, Ɗanlondon
da ake ganin shi ne lalatacce sai ga shi ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin
Zaliha ta dawo tafarki madaidaici ta hanyar yi mata nasiha da neman aurenta.
Lallai Kulɓa ce ke ɓarna, ana cewa jaɓa
Tsokaci Kan
Waɗannan Matsaloli A Yau
Ida muka kalli
wannan matsala ta masu hannu da shuni, Alhazai da irin illolin da suke wa yara
mata 'yan makaranta a yau sai dai du'a’i, domin kuwa idan mutum ya ga irin shaiɗancin
da ake yi a manyan makarantu (Jami'o'i) tsakanin Alhazai da 'yan mata abin da
ban takaici. Za ka tambayi kan ka, wai Alhazan ne ba su da imani? Ko ba su da
yara mata ne? A ɓangaren matan ko, shin
rashin tarbiyya ne? Ko sun fi ƙarfin iyayen su ne? Ko
iyayen sun san halin da 'ya'yansu suke ciki, amma sakaci ne? Domin babu yadda
za a yi iyaye su riƙa ganin abubuwan kuɗi, kamar suturu masu
tsada da takalma da jakunkuna masu tsada, amma ba za a iya tuhumar su daga ina
suka samo su ba. Ta yiwu wannan ne ya sa matsalar ta yi ta yaɗuwa
har zuwa yau. Taɓarɓarewar
tarbiyya ne ya kawo mu inda muke a yau, wanda ba mamaki lokacin da Umaru Ɗanjuma
Katsina ya rubuta wannan wasa a cikin shekarar1979, al'ummar gaba ɗaya
za su ƙyamaci Alhazan nan na ƙauye kuma iyayen na addu'a
ga 'ya'yansu a kowane lokaci don neman kariya daga waɗannan
miyagun Alhazai na birni. To amma, a yau da Allah ya kawo mu shekarar 2025,
wasu iyaye mata har roƙon Allah suke Allah ya haɗa
'ya'yansu da irin waɗannan Alhazai don kwaɗayi
da son abin duniya, musamman ma idan aka yi la'akari da irin ci gaban da aka
samu a fagen kiwon lafiya ksantuwar zubar da ciki ba komai ba ne mai wahala,
kuma idan yarinya ta tashi aure akwai magunguna na gargajiya da ake haɗawa
na musamman don 'yarsu ta kasance kamar ba ta taɓa sanin namiji ba.
Kammalawa
Marubuta wasan kwaikwayo ko shakka babu suna amfani
da fasaharsu wajen ganin al’’umma sun kuɓuta daga wasu matsaloli da kan iya kunno
kai a cikin al’umma. Umaru Danjuma Katsina dai ya taka rawar gani a wannan fage
musamman idan aka yi la’akari da wasanni daban-daban da ya rubuta ciki har da
wasan kwaikwayo na Kulɓa Na Ɓarna. Matsalar ɓata rayuwar mata ‘yan makaranta da Alhazai na birni ke yi
kamar yadda Umaru Danjuma Katsina ya nuna a wasan kwaikwayon Kulba Na Barna ya
ci gaba da aukuwa don kuwa idan aka ga yadda manyan motoci ke shiga da fita a
manyan makarantu kamar jami’o’i domin kwasan ‘yanmata domin lalata da su saboda
kuɗi da wasu abubuwa ƙyalƙyali kamar wayar hannu da makamantarsu.
Manazarta
Ahmad, U.B. (1985): “Nau’o’in Wasannin Kwaikwayon
Hausawa, Cibiyar Nazarin Al’adun Nijeriya, Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.
Ahmad, U.B.
(1985): Taɗonomy Of Hausa Drama,
Zaria: ABU Press Limited
Ɗangambo,
A. (1984): Rabe-Raben Adabin Hausa Da Muhimmancinsa Ga Rayuwar Hausawa. Kano:
Triumph. https://21stCenturychronicle.com
Katsina, U. D,
(1979), " Kulɓa Na Ɓarna".
Zariya: N.N.P.C
Malumfashi, A.
I. (1985): “Asali Da Bunƙasar Rubutaccen wasan Kwaikwayo Na Hausa” Kundin
Digiri Na Biyu, Sashen Nazarin Harsunsn Nijeriya Da Na Afrika, Zariya: Jami’ar
Ahmadu Bello.
Malumfashi,
I.A.M. (1990): “Madubi Ɗaya Fuska Biyu: Nazari Da Sharhi Kan
Rubutattun Wasannin Kwaikwayon Hausa”. Takardar da aka gabatar a Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Price, A.
(1913) The Theartre of Promiscuity: Comparatiɓe Study of the Dramatic
mWritings of Wole Soyinka and Howard Baker; Ph.D Thesis, School of English.
USA: Uniɓersity
of Leeds
Sulaiman, I.A
(2007): “Raha A Wasannin Ƙasimu Yero: Tarken Wasannin Karambana”
Kundin Digiri na Biyu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Da Na Afrika, Zariya:
Jami’ar Ahmadu Bello.
Sulaiman, I.A.
(2013): “Jirwaye Mai Kamar Wanka: Waiwayen Rabe-Raben Wasan Kwaikwayon Hausa”
Maƙala
a cikin Himma, Mijallar Nazarin Hausa, Juzu’I Na Huɗu, Fitowa ta Ɗaya, Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya, Katsina: Jami’ar Ummaru Musa `Yar’aduwa.
Umar, M.B.
(1987): Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Gargajiya,
Xiameng, S.
(2013): Rubutaccen Wasan Kwaikwayo A Rukunan Adabin Hausa: Haɓakarsa Da Muhimmancinsa. Kano: Gidan Dabino Publishers.
Yahaya I.Y da
wasu, (2003): Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare Na
1, Ibadan: Uniɓersity Press.
Yahaya, I.Y.
da wasu (1983): Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: Northern
Nigerian Publishing Company (NNPC).
Yahaya, I.Y.
(1988): Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zaria:
Northern Nigerian Publishing Company (NNPC).
`Yar’aduwa,
T.M. (2005) “Nazarin Littafin Kulɓa Na Ɓarna Na Ummaru Ɗanjuma Katsina” a cikin FAIS Journal Of
Humanities,
`Yar’aduwa, da
wasu (2007): Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakadare Na 3. Ibadan:
Univesity Press.
`Yar’aduwa,
T.M. (2007): Wasan Kwaikwayon Hausa: Nau’o’insa da Sigoginsa,
Kano: Benchmark Publishers Limited.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.