Ticker

6/recent/ticker-posts

Kamaa-Dafìi Da Dafìi: Nazarin Alakarsu Da Bambancinsu

Citation: Bashir, A. and Mukoshy, J. I. (2025). “Kàmàa-Ɗàfìi da Ɗàfìi: Nazarin Alaƙarsu da Bambancinsu.” in Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 03, No. 02, Pp. 98 – 103. www.doi.org/10.36349/djhs.2025.v03i02.012.

KÀMÀA-ƊÀFÌI DA ƊÀFÌI: NAZARIN ALAƘARSU DA BAMBANCINSU

Na

Abdulahi Bashir

Department of Languages and Cultures, Federal University Gusau, Zamfara State

Da

Jamilu Ibrahim Mukoshy

Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto

Tsakure:

Wannan maƙala ta mayar da hankali ga nazari a kan kàmàa-ɗàfìi da ɗàfii, inda aka yi duba a kan alaƙarsu da bambancinsu. An lura cewa, akwai kamanci da bambanci dangane da siffofinsu da ayyukansu ta fuskar ilimin ƙirar kalma. A kan haka aka yi nazari a kan yadda ɗafi da kàmàa-ɗàfìi suka yi tarayya domin ana amfani da su a jikin tushen kalma don a faɗaɗa ma’anar kalma (ta fuskar jinsi da adadi) ko zuwa wasu azuzuwan kalmomin nahawun Hausa. An yi amfani da dabarun gudanar da bincike ta hanyar nazarin littattafai da maƙalu da mujallu da kundayen bincike wajen samar da bayanan da suka shafi kàmàa-ɗàfìi da ɗàfì ilimin ƙirar kalmar Hausa. Bugu da ƙari, an yi amfani da hanyar ɗora aiki ta Spencer da Lius (2012), inda aka bi salo da matakan da suka bi a aikinsu. Takardar ta samu nasarar bayar da ma’anar kàmàa-ɗàfìi da ɗafi tare da fito da siffofinsu da ayyukansu masu nuna alaƙa a tsakaninsu da ɗafi. Haka kuma, an kawo wasu bambance-bambancen da ake samu a tsakaninsu. A ƙarshe, takardar ta kammala da cewa lallai akwai kàmàa-ɗàfíì a Hausa, kuma akwai nau’o’i daban-daban da suka shafe shi a harshen Hausa. 

Muhimman Kalmomi: kàmàa-ɗàfìi, ɗàfìi, alaƙa da bambanci, ƙirar kalma, harshen Hausa

Gabatarwa

Ilimin ƙirar kalma ya kasance wani fage da ake nazarin kalmomi ta fuskar rarrabe su da bayaninsu daki-daki (Muhammad, 2019:9). Shi kuwa kàmáa-ɗàfíi, wata ƙwayar maana ce turkakkiya wadda ta kasance ita ba ɗafi ba kuma ba saiwa ba (Haspelmath, 2023). Haka kuma, kàmáa-ɗàfíi ƙwayar ma’ana ce da ba ta ɗauke da siffofin kalma na tsarin gaɓa-gaɓa (Gladday, 2024). Akwai wasu rukunin kalmomi waɗanda suka yi kama da cikkakiyar kalma, amma ba su iya cin gashin-kansu, har sai sun rataya da wasu kalmomi masu maƙwabtaka da su, kuma irin waɗannan ƙwayoyin ma’anasu ake kira da kàmáa-ɗàfii[1] (Spencer da Lius, 2012). Kàma-ɗàfi yana ƙunshe a cikin ilimin nahawu, kuma akwai ƙarancin ayyukan da suka yi bayani a kansa, musamman a harshen Hausa. Kàmáa-ɗàfíi ya kasance wata kalma da a da akan yi la’akari da ita a matsayin ɗafi cikin taron kalmomi (Sugayama da Hudson, 2006). A nan, za a iya cewa, kàmáa-ɗàfíi fassara ce ta wucin-gadi. Shi dai kàmáa-ɗàfíi yana ƙunshe ne da wasu siffofi da kuma tubalai biyu, watau dai abu ne mai kama da ɗàfíi sannan kuma yana kama da kalma. Har ila yau, kàmáa-ɗàfíi ƙwayar maana ce da take liƙe ko jingine da kalma a gefen hagu ko dama, ko kuma a tsakiya. A wasu wurare kuwa, kàmáa-ɗàfíi yakan jingina ne da kalmomi a cikin jumla ko a wani yanki na jumla, ta yadda sai ya dogara da wasu kalmomi ne, sannan za a samu ƙarin wata sabuwa kuma cikkakiyar kalma mai ɗauke da ma’ana.

Ma’anar Ɗafi da Nauoinsa a Hausa (Affixation)

Ɗafi yana ɗaya daga cikin rukunan hanyoyin ƙirar kalma kamar yadda masana suka yi bayanai a wurare daban-daban. Sannan kuma, ɗafi ya kasance ɗaya daga cikin manyan darusan ilimin ƙirar kalma, wanda za a iya cewa, yakan bayar da gudunmuwa wajen ƙirar kalmaomin Hausa. Domin kuwa, a koina aka yi maganar ilimin ƙirar kalma musamman dangane da jinsi da kuma adadi, to tabbas sai an ambaci ɗafi. Misali, akan yi amfani da ɗafi wajen yi wa saiwar kalma wani ƙari na musamman (kumbura) don fito da sabuwar maana. A nan, masana ilimin ƙirar kalma sun bayyana raayoyinsu dangane da maanar ɗafi a harshe. Daga cikin waɗannan malamai, akwai: Bagari (1986) da Zarruƙ (1996) da Abubakar (2001) da Sani (2002) da Fagge (2004) da Yaradua (2004) da Buhari (2011) Fagge (2013) da wasunsunsu. Akwai kuma wasu ‘yan kaɗan da suke ganin ɗafi iri biyu ne, watau kamar su: Skinner (1977) da Kraft & Kirk Greene (1973) da sauransu (Muhammad, 2018). Saboda haka, duk inda aka ci karo ɗafi zai iya shiga cikin waɗannan nau’o’i da aka kawo, musamman ta fuskar nazari.

Ma’anar Kàmàa-Ɗàfíì (Clitics)

Masana sun yi ƙoƙari sosai wajen bayyana raayoyinsu dangane da ma’anar kàmàa-ɗàfíìta sigogi daban-daban, musamman a fagen nazarin ilimin kimiyyar harshe da kuma ilimin ƙirar kalma. Irin waɗannan ra’ayoyi da masanan suka bayar, sun haskaka wa masu nazari hanyoyin nazarin ƙirar kalma da ƙwayar maana da sauransu. Inda aka bayyana kama-ɗafi a matsayin ƙwayar kalma turkakkiya wadda take ɗauke da siffofi ko sigogin ɗafi da ma kalma ita kanta. Kamar yadda akan iya samun kalma a cikin yankunan jumla, shi ma kama-ɗafi yakan iya zuwa cikin ɗaya daga cikin yankunan jumla na Hausa Zwicky (1977: 3) da Klavans (1995) da Anderson (2005) da Sugayama da Hudson (2006) da Spencer da Lius (2012) da Gladday (2024).

Bayan masana sun bayyana yadda kama-ɗafi yakan fito da sigoginsa tare da cikakkiyar kalma a jumla, sai dai a mafi yawan harsuna, kàmàa-ɗàfìi yakan bi tsarin musayar muhallin ƙwayoyin maana. Bugu da ƙari, kàmàa-ɗàfin nda aka jingina a ƙarshen gefen-dama na gurbin kalmar da aka baƙunta (Host), kamar dai yadda akesamu a ɗafa-goshi, to shi wannan shi ake kira kàmàa-ɗàfin ƙeya. Shi kuwa, kàmàa-ɗàfìnda akan jingina a ƙarshen-gefen hagu na gurbin kalmar da aka baƙunta (Host), akan kira shi da kàmàa-ɗàfin goshi. Bayan haka, akwai kàmàa-ɗàfìn tsakiya wanda akan saka shi a tsakiyar kalmar da aka taras ‘host’, kamar yadda yake faruwa ga ɗafa-ciki, sai dai ba kasafai hakan yake faruwa ba (Spencer & Lius, 2012). A aikin Zwicky (1977: 3) an bayyana ma’anar wasu muhimman kalmomi masu dangantaka da kama-ɗafi kamar haka:

i.        HOST: The word to which a clitic attaches

ii.      CLITIC: The item that attaches to a host word

iii.   CLITIC CLUSTER: A sequence of clitics

Fassarar Marubuta:

i.        GURBIN KALMA: Kalma ce da ake jingina mata kama-ɗafi

ii.      KAMA-ƊAFI: Wata ƙwayar kalma ce da akan jingina ta a jikin gurbin kalma

iii.   HARƊAƊƊEN KAMA-ƊAFI: Jerin kama-ɗafi ne masu zuwa a wurare daban-daban na jikin kalma kuma a lokaci guda.

Misali, a harshen Hausa ana samun harɗaɗɗen kàmàa-ɗàfíì, watau inda yakan fito a wurare biyu na kalma kamar haka:waɗánnan, waɗannàn, shâiska da sauransu.

Haƙiƙa waɗannan bayanai da aka yi a kan kàmàa-ɗàfíì sun nuna yadda kàmàa-ɗàfìn yakan fito da matsayi biyu, watau a matsayin ƙwayar maana, shi ya sa ma ya amsa sunan nasa na kàmàa-ɗàfíì. Domin kuwa shi dai ba ɗafi ne ba, kuma ba kalma ba. Sai dai yakan yi aiki a jikin tushen kalma. Bayan haka, bayanan sun ƙara ƙarfafa guiwar cewa, akwai kàmàa-ɗàfíì a Hausa, kuma yana da fuskoki guda biyu, watau yakan zo da sigar kalma, a wani lokaci kuma yakan zo da fasalin ɗafi ta fuskar ayyukansa a fannin ƙirar kalmomin wasu harsunan duniya.

Nau’o’in Kàmàa-Ɗáfíì

Kàmàa-Ɗàfíì yana da nau’o’i dangane da yadda yakan bayyana a tsakanin kalmomi, watau ko dai ya zo a farko ko a tsakiya ko kuma a ƙarshen kalma. Za a iya samun kama-ɗafi a cikin jumla ta fuskar ayyukansa a nahawu. Ga ire-iren kàmàa-ɗàfíì kamar haka:

a. Kàmàa-Ɗàfìn Goshi(Proclitics)

Kama-Ɗafin-Goshi (ProClitics): Wannan shi ne kama-ɗafin da ake maƙalawa a jikin saiwa ko tushen kalma da nufin samar da wata kalma cikakkiya kuma mai ma’ana. Ga Misalai: Maikano Na’Allah  Tasallah  Tabawa  Jabaka  sa-ɗaka  ɗangulbi wa? me? namu tasu  barmani anaruwa da sauransu. A don haka, za a iya cewa, kàmàa-ɗàfìn goshi ‘proclitic’ yana samuwa ne a sakamakon zuwan aikatau a matsayin ƙari, haka kuma, kàmàa-ɗàfìn ƙeya ‘enclitics’ yana bayyana ne a lokacin da aikatau ya motsa a dalilin kumbura ‘inflection’ (Kayne, 1990). Wannan ne ya ƙara tabbatar da cewa, akan iya samun kàmàa-ɗàfíì a farko (goshin kalma), ta hanyar gano saiwa ko asalin tushen kalmar da aka kawo don nuna misalai waɗanda za su gamsar da mai karatu ko nazari a cikin wani harshe da ake magana ko gudanar da bincike a kansa.

b. Kàma-Ɗáfin Tsakiya (Inter Clitics)

Shi dai Kama-Ɗafin-Tsakiya (Infixal Clitics), shi ne wanda ake iya samu na tsakiyar kalma ko tsakiyar jumla kamar haka:

Maja-sirdi  Maja-ruwa  Maje-karofi  Maje-ringim  Maka-wuya  Maga-wata 

Waɗansu (kàmàa-ɗàfíì a tsakanin ƙwayoyin kalma, watau a tsakiyar kalma).

Shiga-da-alwalarka (kàmàa-ɗàfíì a tsakanin kalmomi biyu).

Mota ta Ladi (kàmàa-ɗàfíì a tsakanin kalmomi biyu).

Ashirin da ɗaya (a tsakanin kalmomi biyu).

Yaa bayar da bashi (a tsakanin kalmomi, cikin yankin jumla)

Ba a tafi ba (a tsakanin kalmomi, cikin jumla).

Za ashiga aji = (a tsakanin kalmomi, cikin jumla) da sauransu.

Baya ga kàmàa-ɗàfin da ake samu a tsakanin wasu ƙwayoyin ma’ana (tsakiyar kalma), ko kuma a tsakanin kalmomi, watau a cikin jumla ko wani yanki nata.

c. Kàma-Ɗàfin Ƙeya (Enclitics)

Shi kuwa Kama-Ɗafin-Ƙeya (EnClitics), shi ne mai zuwa a ƙarshen kalma, inda ake liƙa ƙwayar maana a jikin wata kalma ta hanyar faɗaɗa ma’ana. Misali: Kwanona, korarsa, an aika wa, mene ne, Kande ce, idan da, lokacin da, wurin da, abin da, Uwani, Dubani, zuwa ga, maka, masa, mata da sauran ire-irensu. Idan aka lura, za a ga yadda kàmàa-ɗàfìn ƙeya yake zuwa a ƙarshen kalma, watau a gefen dama na gurbin kalmar ko kuma a ƙarshen wani yankin jumla da aka kawo, domin fito da ma'ana.

Alaƙar Ɗáfi da Kàmàa-Ɗáfìi

A wani lokaci, shi ɗafi tamkar kàmàa-ɗàfìi ne, domin kuwa, ba ya iya tsayuwa da ƙafarsa, saboda yana buƙatar wani abu da zai liƙu a jikinsa. Duk da cewa, kàmàa-ɗàfíì ba ɗafi ne ba a zahiri. Domin kuwa, shi ɗafi na asali akan ɗafa shi ne jikin saiwar kalmomin wani aji na nahawu kaɗai, watau kamar suna ko aikatau dangane da jinsi da kuma adadi. A yayin da shi ma kàmàa-ɗàfìi yakan yi aiki a nan, har ma a sauran ƙunshin kalmomin nahawu, watau, kamar a matsayin mahaɗi da nunau da mafayyaci da sauran makamantansu.

Kàmàa-Ɗàfìi da Ɗàfì suna da alaƙa ta sosai dangane da ƙirar kalma, musamman ta fuskar tsari da kuma dokokin ginin kalma a harshe. A nan, shi ma harshen Hausa ba a bar ba shi a baya ba wajen bin sahun sauran harsunan duniya game da yin amfani da wasu ƙwayoyin maana a fannin ƙirar kalma a Hausa. Ƙwayoyin ma’ana irin su ɗàfìi da kàmàa-ɗàfìi sukan taimaka sosai wajen samar da kalmomi tare da fito da ma’ana a cikin jumla. A don haka, a nan za a iya cewa, babbar alaƙar kàmàa-ɗàfìi da ɗafi musamman a fagen ilimin ƙirar kalma ita ce, dukkansu ƙwayoyin maana ne da akan yi amfani da su wajen samar da kalma ko fitar da ƙarin wata maana daga jikin kalma koa cikin jumla. Haka kuma, sigoginsu kusan iri ɗaya ne dangane da ayyukansu, domin kuwa, akan sami kàmàa-ɗàfin goshi da kàmàa-ɗàfin tsakiya da kuma na ƙeya kamar yadda abin yake ga ɗafi. Domin shi ma ɗafi yana da ɗafa-goshi da ɗafa-ciki da kuma ɗafa-ƙeya kamar yadda masana suka bayani a wurare daban-daban na ilimi.  

Bugu da ƙari, dukkansu suna aiki ne tare da tushen kalma wajen samar da cikakkiyar kalma ta fuskar jinsi da kuma adadi. Wani lokaci kuma, akan liƙa su ne a jikin kalma da nufin samar da wasu kalmomi, watau dai akan same su ne a fagen kumbura dakuma tsirar kalma,waɗanda suna cikin ginshiƙan ilimin ƙirar kalma a nahawu.Har ila yau, kàmàa-ɗàfìi da ɗàfìi ba su iya dogara da kansu har sai sun jingina da wata ƙwayar maana domin a samar da wata kalma mai maana. Duk da cewa, akan iya samun masu dogara da kansu, musamman masu gaɓa ɗaiɗai. Misali; ci da zo da ƙi da yi da sha da bi da ji da sauran makamantansu. A duk inda suka zo a harshen Hausa, to ana samun su ne a cikin rukunin ƙwayoyin maana (vocabulary items),akwai kuma masu aiki irin na nahawu (functional items). Watau dai tamkar yadda ake samun ta a cikin jumla, inda wasu jinsin kalmomi suke aiki na nahawu. Haka abin yake, ko da a cikin kalma. Kàmàa-ɗàfìi ya kasance a cikin masu rufaffen tsari (closed set system), wanda yana da wahala su sami wani ƙari a jikinsu, ko wata baƙuwar ƙwayar maana da za ta raɓu da su domin sake fito da wata sabuwar ma’ana ta daban.

Bambancin Kàma-Ɗàfi da Ɗáfi

Bayan an sami alaƙa a tsakanin ɗafi da kuma kàmà-ɗàfìi, har ila yau, akwai wasu ‘yan bambance-bambance da za a iya samu ta fuskar ƙirar kalma, waɗanda yawanci akan same su ne a yayin ƙirar kalma a harshe. Sannan, irin waɗannan bambance-bambance, sukan taimaka wajen tantancewa a tsakanin kàmàa-ɗàfìi da kuma ɗàafìi. Wannan ya nuna cewa, aikin da kowannensu yake yi daban, duk da cewa, a wani lokaci suna iya zuwa da siffofi iri ɗaya, musamman a gaɓar kalma. Kuma hakan ne yake daɗa tabbatar da cewa, KÀMÀ-ƊÀFÌI daban haka nan kuma ƊÀFÌI ma daban. Haka kuma, za a iya fahimtar alaƙar da take akwai a tsakanin kàmàa-ɗàfìi da kuma ɗàfìi, idan aka yi la’akari da waɗannan bayanaida suke cikin jadawali na I da ke ƙasa, kamar haka:

Jadawali na I: Misalan Siffofin Kàmà-Ɗàfìi da Ɗafi I

Siffofin Kàmà-Ɗàfìi

Siffofin Ɗafi

1.

Kàma-ɗàfi yana da ‘yancin zaɓen kalma, inda akan liƙa shi ko jingina shi.

Ɗàfìi bai da wannan ‘yancin, domin yakan yi aiki a jikin saiwar kalma.

2.

Kàmà-ɗáfìi yana da sassauƙar maana

ɗafi yana da sarƙaƙiya sosai

3.

Kàmà-ɗáfìi zai iya kasancewa cikin farfajiyar tsarin sauti.

Ɗàfìi bai cika shiga cikin farfajiyar dokokin tsarin sauti ba.

4.

Kàmà-ɗáfìi yana shiga cikin gamayyar tasrifi da tsarin sauti.

Ɗafi bai cika kasancewa cikin tsarin gamayyar tasrifi da tsarin sauti ba.

5.

Ana iya samun haɗaka a kàmà-ɗáfìi.

Babu wata haɗaka a ɗàfìi.

 

Har ila yau, an bayyana wani bambanci da ake samu a tsakanin ɗàfìi da kàmàa-ɗàfìi, inda ake liƙa ɗafi jikin saiwa, yayin da ake liƙa kàmà-ɗàfìi a jikin tushen kalma da kuma jingina shi a tsakanin kalmomin da ke cikin jumla. Ga misali a ƙasa:

Jadawali na II: Misalan Siffofin Kàmà-Ɗàfìi da Ɗafi II

 

Ɗàfìi

Saiwa

Ɗàfìi

Kalma

Kàmà-ɗàfìi

Tushen Kalma

Kàmà-ɗàfìi

Kalma

1.

Ma+

karanc+

-i

Makaranci

+

-‘Allah

-

Na’Allah

2.

ɗan+

Dog+

-o

Dogo

ɗan+

-gulbi

-

Ɗangulbi

3.

Ba+

Maguz+

-iya

Bamagujiya

-r/-s

Uwa+

-nì

Uwani

 

Waɗannan misalai da aka kawo, sun nuna yadda ɗàfìi yake aiki a jikin saiwa, a inda shi kuma kàmà-ɗàfìi yake aiki a jikin tushen kalma domin fitar da wata sabuwar ma’ana da ta dace da nahawun harshen Hausa.

Sakamakon Bincike

Wannan, bincike ya gano irin alaƙar da take akwai a tsakanin kàmàa-ɗàfíì da ɗafi, musamman dangane da irin aikin da suke yi ta fuskar ƙirar kalma a harshen Hausa.

Da farko, maƙalar ta yi ƙoƙarin yin bayani a kan ma’anoni da misalai da kuma nau’o’in kàmàa-ɗàfíì a harshen Hausa.

Haka kuma, binciken ya samu nasarar gano cewa, dukkansu akan iya jingina su jikin tushen kalma a fannin ƙirar kalmar Hausa.

Bayan haka, binciken ya gano cewa, shi ɗafi yakan raɓu da saiwa domin fitar da wata ma’ana da ta shafi kumburar kalma dangane da jinsi da kuma adadi.

Har ila yau, an gano yadda ake samun wasu bambance-bambance a tsakanin kàmàa-ɗàfíì da ɗafi, a inda ɗafi yakan haɗu da saiwa domin bayar da wata sabuwar ma’ana, yayin da shi kuwa kàmàa-ɗàfíì ba ya jinginuwa da saiwa, sai dai da gurbin kalma.

A ƙarshe an gano cewa, ɗafi yana zaɓar gurbin kalma, musamman a kan suna ko aikatau ko kuma sifa, a yayin da kàmàa-ɗàfíì ba ya da wannan ‘yancin na zaɓen kalmomi domin kuwa, ba ya iya dogara da kansa, sai dai yakan yi aiki a ko’ina cikin kalmomin nahawu.

Kammalawa

Haƙiƙa wannan maƙala ta yi bayani a kan alaƙa da bambancin da ake samu a tsakanin ɗàfì da kuma kàmàa-ɗàfíì, inda aka kawo bayanai dangane da ma’anoninsu. Sannan, maƙalar ta gano wuraren da sukan haɗu ta fuskar ƙirar kalma, watau tun daga matakin ƙwayar maana da saiwa da tushen kalma har zuwa ga yanayin ɗofanai da suke faruwa wajen samun canjin fasalin kalmomi a nahawun Hausa. Kuma, hakan yakan ba da dama wajen samun ƙaruwar baƙin kalmomi a taska ko rumbun kalmomin Hausa. Har ila yau, misalan da aka kawo sun ƙara ba da haske a kan cewa, lallai akwai kàmàa-ɗàfíì a Hausa, kuma akwai nau’o’i daban-daban da suka shafe shi a harshen Hausa. Bugu da ƙari, wannan bincike ya fito da inda suke da alaƙa ta fuskar aiki da kuma siga a nahawun Hausa, musamman a fagen ƙirar kalma. Bayan haka, an zayyano wasu daga cikin bambance-bambancen da ake samu tsakanin ɗàfì da kuma kàmàa-ɗàfìi na Hausa. Kuma da su ne ake iya gano tasiri ko ayyukan kàmàa-ɗàfìi a harshe, musamman ta fuskar ƙirar kalma da kuma ginin jumla. A ƙarshe, ana fatar, wannan maƙala za ta taimaka wajen warware matsalar da ake fuskanta ta fuskar nazari a kan ayyuka da siffofin ɗàfì da kuma kàmàa-ɗàfìi, musamman a harshen Hausa.

 

Manazarta

Abubakar, A. (2001). An Introductory Hausa Morphology. Maiduguri: University of Maiduguri.

Bagari, D.M. (1986). Bayanin Hausa: Jagora ga Mai Koyon Ilimin Bayanin Harshe. Rabat Maroco: Imprimerie Elmaarif Aljadida.

Fagge, U.U. (2004). The Status of Bound Morpheme MA- In Hausa. Algaita: Current Journal of Hausa Studies, Vol 1. No 3. pp 66-77.

Gladday, A.E. (2024). Cliticization in Obolo Language. In Implementation Strategies for the National Language Policy in Nigeria: The 35th Conference of the Linguistic Association of Nigeria (CLAN). Al-Qalam University, Katsina.

Haspelmath, M. (2023). Types of Clitics in the World’s Languages. In Linguistics Typology at the Crossroads. Anthropology Max Planck Institute for Evolutionary. 3-2 (2023). Pp 1-59. ISSN: 2785-0943.

Klavans, J.L. (1995). On Clitics and Cliticization: The Interaction of Morphology, Phonology and Syntax. New York: Garland Publishing.

Muhammad, I.A. (2018). Nazarin Ɗafi a Hausa. Kundin Digiri na Uku, Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto.

Muhammad, I.A. (2019). Ginshiƙin Ilimin Ƙirar Kalma A Hausa: Taƙaitaccen Tsokaci. Maƙalar da aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Jamiar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto.

Sani, M.A.Z. (2002). Alfiyyar Mu’azu Sani 1: Tsarin Sauti da Tasarifin Hausa. Benchmark Publishers Limited: Kano.

Spencer, A. & Luis, A.R. (2012). Clitics: An Introduction. Cambridge: University Press.

Sugayama, K. & Hudson, R. (2006). Word Grammar: New Perspectives on a Theory of Language Structure. London: MPG Books Limited.

Zwicky, A.M. (1977). On Clitics. Bloomington: Indiana University Linguistics Club.



[1]Kàmáa-ɗàfii wata ƙwayar ma’ana ce da ake liƙawa ko jinginawa a jikin tushen kalma. Haka kuma, abu ne da ya yi kama da ɗàfi dangane da sifa ko siga ko kuma aikinsa (Bayanin marubuta).

Dundaye Journal

Post a Comment

0 Comments