Citation: Abubakar, I.. (2025). “Hausa a Potiskum: Nazari ta Fuskar Kirar Kalma.” in Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 03, No. 02, Pp. 64 – 71. www.doi.org/10.36349/djhs.2025.v03i02.008.
HAUSA A POTISKUM:
NAZARI TA FUSKAR KIRAR KALMA
Na
Ishaku Abubakar
Department of
Hausa,
Umar Suleiman College of Education Gashu’a, Yobe State
Tsakure:
Kamar yadda taken yan nuna “Hausa
a Potiskum: Nazari ta fuskar kimiyyar harshe” takarda ta bayyana yadda
al’ummoin Potiskum suke tasrifin kalmomin Hausa. Sannan, takarda ta yi amfani
da tattaunawa/hira da lurar gani da ido da yanar-gizo da rubutattun bayanai a
matsayin hanyoyin tattara bayanai. Baya ga haka, ta yi amfani da Aronoff, M.
(1976) Ra’in Gina Kalma daga Kalma (Word Based Theory). Sakamakon bincike ya
nuna al’ummomin Potiskum suna amfani da shafe sauti da ɗafa goshi da ɗafa
ciki da ɗafa ƙeya a
matsayin hanoyin ginin kalma.
Gabatarwa
Potiskum
gari ne kuma xaya daga cikin qananan hukumomi goma sha bakwai na Jihar Yobe,
sauransu sun haxa da Bade, Bursali da Fune da Fika da Karasuwa da Nguru da
Gaidam da Gujba da Jakusko da Tarmuwa da Yunusari da Yusufari da Machina da
sauransu. Baya ga haka, Potiskum gari ne da yake da ximbin tarihi na makarantu,
malamai, kasuwanci na amfanin gona da dabbobi, sana’o’i kamar noma da qira
kamar faifan settelite da bodin trailer da sauransu kana yana qumshe da harsuna
kamar Ngizimawa, Karai-Karai, Bolewa da ma sauran qabilu mazauna garin kamar Ngamawa
da Inyamurai, Yarabawa, Hausawa, Baburawa, Kilba, Jukun da sauransu. Haka nan, sanannen abu ne cewa
duk lokacin da harshe ya bar gida ko qasarsa, sai ya samu sauye-sauye. Saboda
haka, harshen Hausa a Potiskum bai zamo bare ba. Gusau (2008: Sh. 1-45) ya bayyana cewa “ƙasar Hausa ta ƙunshi garuruwa manya da ƙanana da Hausawa suke zama wanda
shi ne ya kasance farfajiyarsu. Daga ciki akwai Kano da Sakkwato da Gobir da
Zamafara da Katsina da sauransu. Ajayi da Crowder (1971:Sh.15) sun ƙara da cewa “ƙabilu da suke makwabtaka da ƙasar Hausa sun haxa da Bere-bari, Jukun, Angas, Gwari, Nupe,
Basa, Borgu, Garama, Zarma, Adarawa da sauransu”. NNPC (1979) ta nuna cewa ƙasar Hausa ta ƙunshi Sakkwato da Zamfara da
Katsina da makamantasu, sannan maƙwabta
sun haxa da Nupe da Borgu da Garaama da Adarawa da sauransu (Abubakar, 2024).
Masana da manazarta sun yi
rubuce-rubuce da nazarce-nazarce da dama a kan ƙirar kalma wanda kowa da ɓangaren
da ya duba. Sai dai duk rubuce-rubuce da nazarce-nazarce da suka yi, ba su taɓo Hausa a Potiskum ta fuskar ḱirar kalma ba. Saboda haka, wannan takarda wani yunḱuri ne na fito ko bayyana yadda
al’ummomin Potiakum suke tasrifin kalmomin Hausa. Wannan takarda babu shakka
tana da matuƙar
muhimmanci musamman ga ɗaliban nazarin harsuna da
ainihin masu magana da harshen Karai-Karai da Ngizim da Bole musamman waɗanda suke jin Hausa kan yadda suke tasrifin kalmomin Hausa
sakamakon hulɗa ko cuɗanya da Hausa. Sannan binciken zai bayyanar da ainihin masu
magana da harsunan cigaba ko koma baya da aka samu a harshensu. Baya da haka,
gudunmawa ce a fagen ilmi. Sannan, hanya ce ta adana rubutaccen bayanai a kan
harshen Hausa a Potiskum. Bugu da ƙari,
ana nuna matsayi da ƙarfin
Hausa a harsunan Chadi.
Manufar Bincike
Sananne ne cewa babu wani aiki
ko bincike da za a gudanar da ba shi da matsala balle manufa. A nan, manufar
wannan takarda ita ce fito ko bayyana yadda harsunan Potiskum suke tasrifin
kalmomin Hausa
Hanyoyin Gudanar da Bincike
Hanyoyin gudanar da bincike ya
shafi ko danganci wurare ko kafofi ko mutane da za a tuntuɓa ko amfani da su wajen gudanar da bincike. A nan, an
gudanar da wannan bincike ta hanyar tattaunawa/hira da lurar gani da ido da
yanar-gizo da amfani da ɗakunan karatu. A wannan bincike,
maza da mata daga cikin Karai-Karai da Ngizimawa da Bolewa kana da Hausawa da
Kilba da sauransu mazauna Potiskum da kewaye. Sannan, bincike ya keɓanta ga Potiskum da kewaye.
Ra’in Bincike
Wannan bincike ya yi amfani da
Aronoff, M. (1976) – Ra’in Gina Kalma daga Kalma (Word Based Theory). Aronoff, M (1976) ya nuna cewa
hanyoyin gina kalma su shafi gundarin kalma. Sannan sabuwar kalma ta kasance ta
hanyar amfani da sananniyar doka. Kalma
ta kasance tana da nasaba da sauran ɓangarorinta. Baya da haka,
kalmomi su kasance sanannu kuma samammu da sauransu. Daga cikin waɗanda suka bunƙasa
ko ƙarfafa ra’in akwai Scalise (1984) da Abubakar (2001) Baba (2017) da
sauransu. Duba ga ra’in, ya dace a ɗora shi a kan wannan bincike. Dalilin amfani da wanan ra’i
shi ne yana bayani kan ginin kalma daga tushen wata kalma.
Dalilai da suka kawo Bunƙasar Harshen Hausa a Potiskum da
Kewaye
Babu shakka duk lokacin da aka
ce harshe ko wani abu ya ci gaba ko bunƙasa
a wani wuri, akwai dalilai da suka haifar ko jawo hakan. Daga cikin dalilai
akwai:
1. Rashin ƙyamar Baƙo
Wannan shi ne dalili na farko
kuma babba daga cikin dalilai da suka kawo bunƙasar Hausa a Potiskum a matsayin harshen mu’amala domin bincike ya nuna cewa kasancewar al’ummomin (Bolewa da Karai-Karai da Ngizimawa) ba sa ƙyamar baƙo, wato suna karɓar baƙi
hannu bibiyu tare da ba su masauki da gona a kuma taru a noma masu da ba su
rumfa a kasuwa don su yi kasuwanci da ba su fili (ɗebi da kan ka) don su gina gida, kai da riƙe su tamkar ‘ya ‘ya da ba su aure, har
takai-ta-kawo ga waɗanda ma ba su da ɗakin baƙo
a gidajensu sukan cire ‘ya’yansu
daga cikin ɗakunansu su bai wa baƙi, su kuma yaran su tafi wurin
abokansu su kwana (tattaunawa da Isah Hassan).
Idan aka duba wannan dalili, za
a fahimci cewa tabbas wannan haka yake, kuma ko a yau za ka samu Hausawa da
yawan gaske da suka mallaki gidaje da gonaki da rumfuna a kasuwa duk da sauyin
zamani da aka samu. Ke nan, za a iya cewa waɗannan
al’ummomi sun yi fice da suna wajen karɓar baƙi wadda ta-kai-ta-kawo ga waɗanda ma ba su da ɗakin baƙi a gidajensu sukan fitar da ‘ya‘yansu daga cikin ɗakunansu su bai wa baƙi
su zauna. Haƙiƙa, waɗannan al’ummomi za a iya cewa sun kai ƙoli wajen mutunci da wayewa da
kyakkyawar ɗabi’a ko al’ada ta karɓar mutumin da ba ka san shi ba ta kowace fuska amma ka ɗauke shi tamkar ɗa. Babu shakka, wannan ɗabi’a ko hali shi ne babbar kafa da ta buɗe ƙofar
bunƙasar Hausa a Potiskum a matsayin
harshen mu’amala.
2. Kasuwanci
Wannan shi ma yana ɗaya daga cikin manyan dalilai da suka haifar ko kawo bunƙasar Hausa a matsyin harshen mu’amala a Potiskum. Kasuwanci yana nufin sana’ar saye da sayarwa. A nan, Hausawa sun zo ƙasar (Potiskum) don kasuwanci,
sannan harshen kasuwanci ko saye da sayarwa shi ne Hausa. Ke nan, sai mutum
yana jin Hausa kafin ya saya ko ya sayar da kayansa. Sannu a hankali sai
harshen ya zamo shi ne harshen mu’amala
Saboda haka, idan aka yi
la’akari da wannan dalili, shi ma za a fahimci cewa kasuwanci yana daga cikin
manyan dalilai na bunƙasar
Hausa a Potiskum, sannan harshen gudanar da kasuwancin shi ne Hausa. Ke nan,
dole Hausa ta cigaba tare da bunƙasa.
3. Ajiye Harshe a Gefe ɗaya
Wani dalilin da ya haifar da
Hausa a matsayin harshen mu’amala a Potiskum shi ne kowace al’umma ta amince ta
ajiye harshenta a gefe ɗaya don a yi magana da harshe ɗaya domin samun ci gaba mai ɗorewa
ko a ce don ci gaban al’umma. Sakamakon haka idan ana magana da Hausa sai wani
ya kasance yana magana da harshensa na uwa, wannan ya nuna rashin waye ko ƙauyancinsa a fili (tattaunawa da
Usman Adamu).
Idan aka duba wannan dalili shi
ma, za a ga cewa wannan kusan haka yake, domin duk wanda ya kasance ana magana
da Hausa shi kuma yana magana da harshensa na uwa, ana masa ganin baƙauye ne ko kuma bai waye ba.
Wannan dalilin sannu a hankali Hausa ta samu ƙofar mamaye ko game garin da kewaye. Mamayar sai ta zama
kamar juyin-juya hali ko a ce wutar daji, idan ta taso Allah kaɗai ya san inda za ta tsaya.
4. Koyar da Hausa a Makarantu a
Matsayin Kwas
Babu shakka wannan shi ma yana ɗaya daga cikin dalilai. Ma’ana koyar da Hausa da ake yi a
makarantu a hukumance a matsayin kwas shi ya haifar tare da bunƙasarta a Potiskum da ma kewaye
gaba ɗaya wanda a ƙarƙashin wannan an samu litattafai na karatu da jaridu. Saboda
haka, babu shakka dole Hausa ta ci gaba, sannan da kasancwarta harshen bai ɗaya a Arewacin Nijeriya shi ma ya ƙara bunƙasarta a Potiskum.
Duba ga wannan dalili, za a iya
cewa wannan babu shakka haka yake domin duk harshen da ya kasance ana koyar da
shi a makarantu, tilas ya ci gaba da kuma yin tasiri a zukatan al’ummomin da
kuma kan harsunan da suke wurin. Alal misali, Ingilishi ko Turanci baƙon harshe ne amma sakamakon
koyar da shi a makarantu dole ya yi tasiri a zukata da kuma kan harsunan wurin
domin zai yi wuya ga wanda ya yi karatun boko ko na zamani ya yi magana da
harshensa na uwa ba tare da ya surka da Ingilishi ba, ina kuma ga harshen Hausa
da ya kasance shi ne harshen bai ɗaya a Arewacin Nijeriya.
5. Aure
Wani dalili da ya haifar da
Hausa a matsayin harshen mu’amala a Potiskum shi ne auratayya tsakanin harsuna
wato al’ummar Hausawa da al’ummomin Potiskum. Alal misali Bahaushe ya auri wata
daga cikin al’ummomin kamar Bakarkariya ko Baboliya ko Bangizimiya, yaro ko
yarinya da za a haifa zai yi wuya ya tashi da harshen uwa sai dai Hausa
(Tattaunawa da Alh. Muhammad Talba Shua da Alh. Zubairu Umar). Idan kuma
al’ummomin suka auri bahaushiya kai tsaye yaro ko yarinya da za a haifa zai
tashi da harshen Hausa, sakamakon uwar Bahaushiya ce. To, yanzu su ma iyayen da
Hausa suke magana, ina kuma ga yara.
La’akari ga wannan dalilin shi
ma, za a iya cewa tabbas wannan iƙrari
ko bayani haka yake domin Hausa ta kasance ita ce harshe na bai ɗaya, sannan, idan aka samu aurarraki tsakanin al’ummomi
mabambanta, lallai sai wani ya ajiye harshensa kafin a samu fahimtar juna da
isar da saɗo ko sadarwa a tsakanin al’umma.
Baya da haka, wani abin da yake faruwa shi ne akasari ‘ya ‘ya sun fi tashi da
harshen uwa domin tana gida tare da su kowane lokaci. Dogaro da wannan dalili
shi ya sa yawanci ‘ya ‘ya suke tashi da harshen uwa, amma mai gida ba shi da
lokacin da zai zauna a gida har ya koya wa yara harshensu.
6. Koyar da Addinin Musulunci da
Karatun Boko
Kusan za a iya cewa Hausawa su
suka kawo Addinin Musulunci ga al’ummomin Potiskum, sannan wannan koyarwa da
Hausa ake yi tare da fassara abin da Allah ya ce da Annabi (SAW) ya ce.
(tattaunawa da Bukar Ahmadu Bulakos) Ke nan, wajibi ne Hausa ta bunƙasa ta ma zama abin da ba a yi
tsammani ba.
Idan aka duba wannan dalilin shi
ma, za a fahimci cewa malamai masu karantar da addini da wa’azi duk Hausawa ne
sannan da Hausa suke fassara ko yin bayani.
Babu shakka dole Hausa ta ci gaba, kai ko da ma wane harshe ne dole ya
bunƙasa da kuma ci gaba.
7. Baya da haka, wani dalilin a
hira da Usman Adamu ya nuna cewa al’ummomin ba sa son magana da harshensu na
uwa domin alama ce ta nuna rashin wayewa da ƙauyanci a fili. Ma’ana.
kowa yana magana da Hausa amma kai ka kasance kana magana da harshenka
(Karai-Karai ko Ngizimanci ko Bolanci). Babu shakka wannan ya nuna ko fito da
rashin wayewa da kuma ƙauyancinsa
a fili.
Wannan dalilin shi ma idan aka
yi nazarinsa, kusan za a iya cewa haka yake. Ƙauyanci ko rashin wayewa ce a gare su idan ana magana da
Hausa sai wani kuma yana magana da harshensa na uwa har ma ana masa ganin kamar
bai daɗe da shigowa gari ba.
8. Har wa yau, wani dalilin shi ne
na rashin rubuce-rubuce ko fassare-fassare da harshen uwa. A nan, samun
rubuce-rubuce da harsunan wurin abin nema ne. Misali adabobi da al’adu da
bayani a kan harshen da harshen sai dai da wani harshe daban kamar Hausa ko
Ingilishi, amma idan ka duba za a ga cewa akwai rubuce-rubuce da yawa a kan
harshen Hausa da Hausa (tattaunawa da Usman Adamu).
Duba ga wannan dalilin shi ma,
za a fahimci cewa akwai rubuce-rubuce masu ɗimbin
yawa a kan harshentaHausa da Hausa kama tun daga adabobi da al’adunta da
harshen saɓanin harsunan Potiskum. Sannan
da kasancewa na rashin son magana da harshen uwa na ganin alama ce ta nuna
rashin wayewa da ƙauyanci a
fili. Saboda haka, waɗannan dalilai su ma sun ƙara buɗe ƙofar
bunƙasar Hausa a Potiskum a matsayin
harshen mu’amala.
9. Almajirci
Wannan shi ma yana ɗaya daga cikin dalilai da suka haifar da Hausa a matsayin
harshen mu’amala a Potiskum da kewaye. Almajirai da masu neman ilmin Alqur’ani
sun zo ko kwararo gabashin Nijeriya inda wasu suka yi zango ko sauka a Potiskum
wasu kuma suka wuce Damaturu da Geidam da Maiduguri da sauran wurare na
gabashin Nijeriya don karatun Alqur’ani. A nan, sakamakon zamansu don karatun
Alƙur’ani
Hausa ta bunƙasa matuƙa a Potiskum.
Duba ga wannan dalili da aka
kawo a sama, za a iya cewa wannan haka yake, sannan dole ta ci gaba da bunƙasa wadda za ta ma iya mamaye
Arewacin Nijeriya gaba ɗaya.
10. Siyasa
Wannan shi ma wani dalili ne na
kasancewar Hausa a matsayin harshen mu’amala a Potiskum. Siyasa kama tun daga
siyasar NEPU da NPN har zuwa yau PDP da APC, Hausawa sun zo garin Potiskum
sakamakon kamfe wadda wasu ta kasance sanadiyar zamansu a garin wadda a wannan
dalilin Hausawa sun ƙaru da
yawan gaske.
Daga ƙarshe, duk waɗannan dalilai da aka kawo a sama kamar rashin ƙyamar baƙo da kasuwanci da koyar da Hausa
a makarantu da rashin rubuce-rubuce da harshen uwa da siyasa da almajirci da ƙauyanci ko rashin wayewa da kai
da ma waɗanda ba a kawo ba, babu shakka
sun isa a matsayin shaida ko hujjoji na bunƙasar Hausa a Potiskum da kewaye a matsayin harshen mu’amala. Duba ga garin ba ya daga cikin garuruwan Hausa balle
makwabtanta kamar yadda Ajayi da Crowder (1971) da Gusau (2008) suka nuna ko
kawo (Abubakar,2025).
Nazari
ta Fuskar Ƙirar
Kalma
Ƙirar kalma ko ginin kalma kamar
yadda wasu suke kira yana ɗaya daga cikin manya ko ginshiḱan kimiyyar harshe. A taḱaice shi ne ginshiḱi na biyu a fannin, sauran sun
haɗa da tsarin sauti da ginin jumla
da ma’ana. Sani (2009:25) ya bayyana ginin kalma da hanya ce ta samar da wata
kalma daga saiwarta. Haka nan, Abubakar (2001:1-5) ya nuna cewa nazarin ginin
kalma ya shafi samar da kalma ta ɓangarori biyu da hanyoyi. Ɓangarorin sun ƙunshi kumbura da tsira (lexical
morphology da inflectional morphology. Sannan hanyoyin sun haɗa da ɗafi da nannage da kwaskwarima da
sauransu. Sai dai Fagge (2012) da Ayodele (2001:78-80) da Mathews (1993) sun
bayyana ginin kalma da nazari ne na tsarin kalma. Shi kuwa Bello (2024) ya nuna
cewa ilimin ginin kalma yana bayyana canje-canje da ake samu tsakanin kalmomi
ta hanya kumbura da tsira da harɗantawa domin samar da sabuwar
kalma. A wannan gaɓa, za a iya bayyana ḱirar kalma ya shafi samar da
wata kalma ta daban daga tushenta. Daga cikin hanyoyi da al’ummomin Potiskum
suke gina kalmominsu akwai: shafe baƙi
ko gaɓa da ɗafa goshi da ɗafa ciki da ɗafa ƙeya.
Shafe Baƙi ko Gaɓa (Deletion of
consonants/syllable)
Shafe baƙi ko gaɓa yana nufin cire ko shafe wani sauti ko wata gaɓa a kalma daga farko, tsakiya ko ƙarshenta. Kaɗan daga cikin misalai akwai:
|
Hausar Potiskum |
Daidaitacciyar Hausa |
|
aihùwaa |
haihùwaa |
|
àsaarà |
hàsaarà |
|
icèe |
itàacee |
|
koomii |
koomai |
Duba ga misalai da
aka kawo a (Ai-iv), a misali na (Ai-ii), za a ga cewa an samu shafewar baƙi ko gaɓa a farkon kalma. Alal misali kalmar haihùwaa da hàsaarà.
A nan, a Hausar Potiskum baƙin
farko na kalmomin aka shafe don a samar da wata kalma. Kalmar da aka samar ita
ce aihùwaa da kuma àsaaràa. Sannan, a misali na (Aiii), gaɓa ta biyu aka shafe, kalmar da aka samar ita ce icèe
wadda a Hausa icèe yana nufin tilo sannan itàace shi ne
jam’i saɓanin Hausar Potiskum wadda itàacee
yana nufin tilo sannan itatuwàa yana nufin jam’i. Sai dai, a
misali na (Aiv), wasalin /a/ na gaɓa ta biyu buɗaɗɗiya aka shafe wadda kalmar da
aka samar ita ce koomii saɓanin koomai na
Daidaitacciyar Hausa. Kodayake, hanyoyin gina kalmomi sanannu ne a wurin masana
da manazarta ginin kalma.
Dafa goshi (Prefixation)
Ɗafa goshi yana nufin liƙa wa ko ƙara wa saiwar kalma wani abu
wato baƙi ko gaɓa a farkon tushen kalma domin a samar da wata kalma ta
daban. Saboda haka, a Hausar Potiskum ana amfani da ɗafa goshin /gwaa/ +naa ta zama gwanaa. Kodayake, ɗafin ya sanya kalmar ta koma gamayyar tasrifi da tsarin
sauti kamar yadda za a iya gani a misalin. Haka nan, wannan ya fi samuwa ko
faruwa daga cikin wasu Karai-Karai da Ngizimawa da Bolewa har da Hausawa inda
suke faɗin gwanaa maimakon gonaa
na Daidaitacciyar Hausa. Misali:
Hausar Potiskum
|
Saiwa |
Ɗafi |
Kalma |
Daidaitacciyar
Hausa |
|
gon |
+waa |
gwaanaa |
goonaa |
Daba ga misali da aka kawo a
(Bi), za a ga cewa an samu gamayyar tasrifi da tsarin sauti inda aka samu ɗafin /+waa/ wadda ya nashe wasalin gaɓa ta farko na kalmar goonaa. A nan, wannan za a iya cewa
wata babbar shaida ce na irin nau’in Hausar al’ummomin Potikum inda musamman
wasu daga cikin Karai-Karai da Ngizimawa da Bolewa da ma Hausawa suke furta gwanaa
da rubutawa maimakon gonoaa na Daidaitacciyar Hausa. Ka ga a nan, an
samu gamayyar tasrifi da tsarin sauti. Kodayake, ana iya jin kalmar a wasu
wurare na Arewa maso gabashin Nijeriya kamar yankin Biu da Gwoza da Madagali,
wannan tasiri ne na karin harshe ko Hausar wuri, A gefe ɗaya, wannan bincike yana ƙoƙarin fito
da irin nau’in Hausar Potiskum ce, ba Hausar
sauran wurare ba, kowane yanki da nasu irin nau’in
Hausar, kuma babu shakka in dai za a gudanar da bincike, lallai a samu bambanci
duk da kasancewar ana iya tarayya a kan wasu kalmomi ko wani haka. Haka nan,
idan aka yi nazari, za a fahimci cewa a Aronoff (1976) hakan doka ce.
Ɗafa ciki (Infixation)
Kamar yadda suna
ya nuna, ƙarawa ko
liƙawa tushen kalma wani abu (sauti
ko gaɓa) a tsakiya don a samar da wata
kalma (Abubakar,2001:1). Shi kuwa Sani (2011:38) ya bayyana shi da saƙala wasali; inda ya nuna cewa
yin amfani da wasali a wurin da yake babu shi a kalma tun asali. A fahimta ta, ɗafa ciki yana nufin sanya wani sauti ko gaɓa a tsakiyar kalma domin a samar da wata kalma ta
daban. A nan, a Hausar Potiskum su ma
suna amfani da ɗafa ciki wajen gina kalma ga
misali:
Saiwa Ɗafi
i. shuug / +waa/
Hausar Potiskum
shuwàagàbannii
Daidaitacciyar Hausa
shuugàbannii
Duba ga misali da aka kawo a (Ci), za a ga cewa an samar da kalma ta
hanyar ɗafa ciki da ɗafa ƙeya.
Kodayake, kalmar ba ta taƙaita
ga Hausar Potiskum ba ana iya jin kalmar a wasu wurare. Sai dai a wannan gaɓa ana ƙoƙarin bayyana yadda harsunan suke
tasrifin kalmomin Hausa.
Ɗafa ƙeya (Suffixation)
Fagge (2004:8) da
Abubakar (2001:1) sun nuna cewa ɗafa ƙeya yana nufin ƙarawa ko liƙawa wani abu a ƙarshen tushen kalma don samar ko
gina wata kalma. Ke nan za a iya cewa ɗafa ƙeya yana nufin ɗosana ko ƙara
wa saiwar kalma sauti ko gaɓa a ƙarshe don a samar da wata kalma
ta daban. A nan, a Hausar Potiskum ana amfani da ɗafa
ƙeya wajen samar da wasu kalmomi.
Kaɗan daga cikin misalai akwai:
Hausar Potiskum
|
Saiwa |
Ɗafi |
Kalma |
Daidaitacciyar Hausa |
|
abok |
+ anee |
àbookàanee |
àbòokai |
|
masallat |
+ yyaa |
masallatayyàa |
màsàllàatai |
|
yaƙ |
+ unaa |
yaaƙùnaa |
yàaƙee-yàaƙee |
|
fat |
+ uka/naa |
fatuka / fatuunaa |
fatuu |
La’akari da misalai da aka kawo
a sama (Di-iv), a misali na (Di), an yi amfani da ɗafin /+anee/ don a samar da wata kalma wato abok+anee
maimakon àbòokai na Daidaitacciyar Hausa. A misali na (Dii), an samu ɗafa ƙeyar
/+yyaa/ a kalmar masallatayyaa maimakon masallaatai na
Daidaitacciyar Hausa. Haka nan a misali na (Diii) an samu ɗafin /+unaa) a kalmar yaaƙùnaa maimakon yàaƙe-yàaƙe na Daidaitacciyar Hausa.
Daga ƙarshe, idan aka la’akari ga misalai da aka kawo tun daga (Ai-iv) har zuwa
(Di-iv), za a fahimci cewa an bayyana yadda Hausar Potiskum take ta fuskar ƙirar kalma. Sai dai faɗin shuwàagabanni da àsaaràa da icèe a wannan gaɓar, za a iya cewa bai taƙaita ga Hausar al’ummomin
Potiskum ba domin kalma ce da za a iya cewa gama-gari wadda ana iya jin ta a
wasu wurare. Duk da haka, wannan shi ne asalin yadda al’ummar Potiskum suke tasrifin kalmomin Hausa.
Sakamakon Bincike
Babu shakka duk lokacin da aka
gudanar da bincike lallai a samu sakamako. Saboda haka, sakamakon wannan
bincike ya haɗa da:
i.
Shafe baƙi ko
gaɓa a farko ko ƙarshen
kalma wajen tasrifin kalmomin Hausa.
ii.
Haka nan, sakamakon bincike
ya nuna akwai ɗafa
goshi wajen tasrifin kalmomin Hausa a Potiskum.
iii.
Har wa yau, sakamakon
bincike ya nuna akwai ɗafa
ciki wajen samar da kalmomi a Hausa Potiskum.
iv.
Daga ƙarshe,
sakamako ya nuna akwai ɗafa
ƙeya
a matsayin hanyoyin gina kalmomin Hausa a Potiskum.
Kammalawa
A kammalawa, kamar yadda bayanai
da suka gabata, masana da manazarta sun bayyana ƙirar kalma da samar da wata kalma daga tushenta. Sannan,
shafe baƙi da ɗafa goshi da ɗafa ciki da ɗafa ƙeya
sun kasance matsayin hanyoyi da al’ummomin
Potiskum suke tasrifin kalmomin Hausa. Baya ga haka, takarda ta yi amfani da
tattaunawa ko hira da lurar gani da ido da yanar gizo da amfani da ɗakunan karatu da sauransu a matsayin hanyoyin tattara
bayanai. Sannnan, ta yi amfani da Aronoff, M (1976) Ra’in Gina Kalma daga Kalma
(Word Based Theory). Har wa yau, binciken ya kasance gudunmawa ce a fagen ilmi
kana hanya ce ta adana rubutaccen bayanai a kan harsunan Potiskum tare da nuna
matsayi da ƙarfin
Hausa a harsunan Chadi.
Manazarta
Abubakar,
A. (2001). Introductory Hausa morphology.:
Faculty of Arts, University of Maiduguri. P. xii-xiii.
Abubakar,
I (2025). Nazarin Hausa a Potiskum ta fuskar kimiyyar harshe. Kudin digiri na
uku, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa Yar Adua. Katsina
Abubakar,
I. (2024). Hausa a Potiskum: Nazari ta fuskar ma’ana. cikin Abubakar. A. da
wasu (editoci) cikin Gaɗau Journal of Arts and
Humanities.
Vol. 6 No.1 Shafi. 132-141.
Ajayi,
J.F. & Crowder, M. (1971). History of
West Africa. Longman Group Limited. P.15-17.
Aronoff,
M. (1976). Word formation in generative
grammar. The MIT Press
Ayodele,
A. (2001). Morphology: An introduction. (1991). The English
Compendium. TIMIgrafik Production. P.32.
Baba,
A.T. (2005). Hausa spoken as a second
language in Jos/Bukur Nigeria: Background and Form. Faculty of Arts. Shafi. 20-25.
Bello,
M.Z (2024). Jagoran nazarin ginin kalma a Hausa. UMYU Pres Limited.
Shafi. 14.
Fagge, U.U (2004).
An introduction to Hausa morphology. Gidan Dabino Publishers. Shafi. 8.
Fagge, U.U.
(2012). Hausa language and Linguistic.
Ahmadu Bello University Press Limited.
Gusau,
S.M. (2008). Waƙoƙin
baka a ƙasar Hausa. Benchmark Publishers Limited
Mathews,
P.H. (1993). Morphology: An introduction to the theory of words structure.
Cambridge University Press. P.78-80.
Northern
Nigerian Publishing Company Limited, (1979). Hausawa da makwabtansu. Reprinted. Northern Nigerian Publishing
Company Limited. Gaskiya Building. www.nnpchausa.com
Sani,
M.A.Z. (2009). Siffofin daidaitacciyar
Hausa. Benchmark Publishers Limited. Shafi. 25-26.
Scalise,
S. (1984). Generative morphology.
Holland. Foris Publication.
Sunayen waɗanda
aka tattauna da su
|
S/N |
Suna |
Addireshi |
Matsayi |
Shk |
Lokaci |
Rana |
|
1. |
Alh. Ahmed Gindas |
Min. of Housing DTR. |
Tech. officer |
57 |
5:00pm |
20-01-2025 |
|
2. |
Ahmadu Garba |
Masallacin Danja |
Sch teacher |
53 |
4:15pm |
20-01-2025 |
|
3. |
Alh. Ibrahim H. Tambari |
ADP – Pot. Zonal Office |
Chief LSO |
56 |
4:00pm |
22-01-2025 |
|
4. |
Ali Alhaji Ali Galadima |
Sarkin Baburawa |
S/Baburawa |
50 |
5:00pm |
22-01-2025 |
|
5. |
Alh. Ayuba Maidede |
Layin palace |
Xan kasuwa |
59 |
4:00pm |
22-01-2025 |
|
6. |
Hauwa Moh’d Chana |
GDSS Mamudo |
V/Principal |
50 |
4:30pm |
22-02-2025 |
|
7. |
Laraba Ibrahim |
Kusa da S/layi Pri. Sch. |
Matar aure |
56 |
4:30pm |
25-02-2025 |
|
8. |
Mohammed Shehu |
GDSS Potiskum |
Class teacher |
40 |
4:45pm |
25-02-2025 |
|
9. |
Adamu Audu |
GDJSS Sabon Layi |
V/Principal |
47 |
5:00pm |
02-03-2025 |
|
10. |
Usman Adamu |
Yobe State University |
HOD Geo. |
55 |
2:00pm |
04-03-2025 |
|
11. |
Isa Hassan |
Masallacin Musa Kamba |
Staff Audit |
54 |
4:00pm |
04-03-2025 |
|
12. |
Bukar Ahmadu Bulakos |
Fika GSS Potiskum |
V/Principal. |
50 |
5:00pm |
04-07-2025 |
|
13. |
Yusuf Suleiman |
Tudun Wada |
Xan kasuwa |
45 |
4:00pm |
06-07-2025 |
|
14. |
Hassan Maina |
Gidan Marayun Deputy |
Mai gadi |
65 |
5:00pm |
06-07-2025 |
|
15. |
Malam Zannan Khalili |
Halilu Mai Yadi residence, opposite FCE |
Lecturer |
40 |
4:30pm |
08-08-2025 |
|
16. |
Ibrahim Babe |
Unguwar Bolewa |
Staff NPS |
52 |
4:35pm |
09-08-2025 |
|
17. |
Alhaji Abdullahi Daki |
Liman Abdullahi Street, Un/Bolewa |
Retired NCS |
60 |
4:45pm |
09-08-2023 |
|
18. |
Mohammed Bello |
FCE (T) Potiskum |
EO Voc. |
55 |
11:30pm |
11-08-2025 |
|
19. |
Rebecca Simon Marcus |
FCE (T) Potiskum |
HOD |
60 |
12:30pm |
11-08-2025 |
|
20. |
Alhaji Zubairu Umar |
Babbar kasuwa Potiskum |
Xan kasuwa |
60 |
11:00pm |
19-08-2025 |
|
21. |
Alhaji Mohammed Dafa |
Layin EYN hurch |
Retiree |
61 |
4:00pm |
21-08-2025 |
|
22. |
Habu Bomai |
Board of Internal revenue Damaturu |
Director |
57 |
4:30pm |
24-08-2025 |
|
23. |
Abubakar Moh’d Daya |
H M B Damaturu |
DFS |
57 |
5:00pm |
24-08-2025 |
|
24. |
Mohammed Talba Shuwa |
District Head of Nangere |
Hakimin Nan |
53 |
4:30pm |
26/08/2025 |
|
25. |
Habibu Umar |
Savannah
Street B/ummi |
Xan kasuwa |
42 |
10:00am |
26-08-2025 |
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.