Ticker

6/recent/ticker-posts

A Dalilinsa Ne

Ahmed Adamu Yarma (2023). A Dalilinsa Ne. Ɗaukar Jinka (Labaran Da Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun Labarai Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2022). Kangiwa Multimedia and Communication Company LTD

A DALILINSA NE

Na

Ahmed Adamu Yarma

Shaye-shaye na ɗaya daga cikin munanan ɗabi’un da ke wargaza rayuwar al’umma, musamman a wannan zamanin da zaman banza ta zama sana’a. A wani ɓangare kuma gurɓatattun matasa ke mayar da ingantattun magungunan kayan maye ta hanyar amfani da su ba bisa ƙa’ida ba, domin samun kuzari wajen yin aikin ƙarfi, ko donkawai samun nishaɗi da holewa.

Tun bayan rasuwar mahaifina, kasancewar bani da kowa, ƙanin mahaifina Baffa Sale ya ɗauke ni, ya mayar dani gidansa. Ya kasance ba shi da wata sana’a sai shaye-shaye. Duk lokacin da ya dawo cikin maye sai ya hau matan gidan da duka, hakan ya sa duk matar da ya auro ba ta zama, saboda mummunar ɗabi’arsa. Har gidan ya zama daga ni sai shi kaɗai muke rayuwa a ciki.

A kwana a tashi ya zamana idan yaje ya yi shaye-shayensa ya dawo a buge abu kaɗan sai ya rufeni da duka har ta kai ga yana haiƙe mini da ƙarfi duk da bana so amma ba yadda na iya.

Wasu lokutan idan cin zarafi da takaicin rayuwar da nake ciki suka ishe ni, sai na kwaso ajiyayyun kayan mayensa da yake ajiyewa a gida nima na sha, ko ya rage mini raɗaɗi da baƙin cikin da na ke ciki. Har ta kai ga idan ya haiƙemini sai na sha ƙwaya sannan nake iya samun barci. Haka nayi ta zama da ƙanin mahaifina Baffa Sale ya mayar dani sa ɗaka ba kunya ba tsoron Allah.

Yau da gobe ya sa idona ya buɗe, kunya irin na ‘ya mace ta fice daga idona, na zama tantiriyar ‘yar ƙwaya, a haka nake zuwa makaranta, watarana in je a buge watarana a hayyacina. Babu wanda ya damu da ni balle rayuwata, ƙawayena duk suka gujeni, ba mai son raɓuwa dani. Na zama kamar ni ɗaya ce nake rayuwa a duniyar, kowa ya guje ni.

Babu wanda ya fahimceni, ya fahimci rayuwata, kamar Dokta Rufa’i, malaminmu ne dake ɗaukarmu darasin halayyar ɗan adam, shi kaɗai ne ya fahimci irin gurɓatacciyar rayuwar da na ke ciki, bai taɓa nuna mini ƙyama ko hantara ba, ya sha kirana yana mini nasiha akan irin rayuwar da na tsinci kaina a ciki, har ya fara fahimtar ba a son raina nake shaye-shaye ba, akwai dalilin da ya jefa ni cikin wannan mummunanr ɗabi’a, amma nakan kasa faɗa masa komai, saboda ina ga idan na faɗa masa na tona asirin gidanmu ne. Yayi iyakar ƙoƙarinsa domin yaga ya dawo dani kan layi, amma naƙi ba shi fuska har ta kai ga ɗalibai suka fara zargin ko yana sona ne, da ya fahimci mutane sun fara yiwa abun wata fassara sai ya saduda ya barni da halina, daga ƙarshe har ta kai ga an koreni daga makaranta.

A ranar da aka koreni daga makaranta ne, Baffa Sale ya dawo cikin dare a buge, ya zo zai haiƙe mini, cikin ɓacin rai na rarumi ɗaya daga cikin kwalaben shaye-shayensa na rusa masa a kansa, wanda hakan yayi sanadiyar tsiyayewar idonsa guda ɗaya, daga ranar na gudu na bar gidan na koma gararamba a gari a gari, lungu-lungu, kwararo-kwararo, rashin mafaɗi, rashin abun yi, da rashin muhalli ya ƙara dulmuya ni cikin shaye-shaye. Na cire rai daga kyakkaywar rayuwar duniya.

 Duniya ta yi mini duhu. Na rame na lalace, zazzaɓi mai tsananin zafi ya kama ni, jira kawai nake mai aukuwa ta auku!

A cikin wannan hali ne kamar daga sama, Allah ya kuma jefo mini Dokta Rufa’i. Kallo ɗaya na masa, na ji wani irin farin ciki ya lulluɓe ni, na ɗaga kai na kalle shi; farar fuskarsa ta zamto tamkar hasken farin wata a cikin duhuwar baƙin daji, a karo na farko naji zuciyata tayi fari fat, zazzaɓin dake jikina lokaci ɗaya naji ya fara sauka.

Dokta Rufa’i bai tsaya wata-wata ba, ya ɗauke ni, ya kai ni asibiti, sai da na shafe wata uku ina jinya a can, ya na ɗawainiya da ni ba dare ba rana. Bayan na murmure, na dawo hayyacina ne, ya ɗauke ni, ya kaini gidansa, inda yake zaune da mahaifiyarsa wanda ake kira Umma. Daga nan na ci gaba da zama tare da Umma, ta ɗauke ni tamkar ‘yar da ta haifa a cikinta.

Dokta kuwa ya ci gaba da kula da ni, ba tare da gajiya wa ba, kullum cikin ɗawainiya yake da ni. Nagode wa Allah da ya haɗa ni da waɗannan mutanen kirki. Har ta kai ga irin kulawan da Dokta yake bani ya fara kulle mini kai, na rasa wannan wane irin mutum ne? Na farko dai ni ba yar uwarsa ba, kuma bai taɓa nuna mini wani alamuna soyayya ba, balle in ce sona ya ke yi. Ya ma za a yi mutum mai mutunci irin sa ya so ni, ni da baffana ya lalata mini rayuwa tun ina ‘yar ƙarama, idona ya riga ya buɗe, har ta kai ga ba wani kayan maye da na taɓa gani a duniyan da ban taɓa sha ba.

Watarana, ina zaune tare da Umma, muna hira mai daɗi irin na ‘ya da uwa, Dokta Rufa’i ya shigo da takardu a hannunsa. Ya samu wuri ya zauna kusa da Umma, ya shaida mini cewa ya sama mini gurbin karatu a ƙasar Birtaniya. Farin ciki maras misaltuwa ya lulluɓe ni, na rasa ina zan sa kaina saboda murna, murnata ta koma ciki a lokacin da na ga Umma ta haɗa rai, nan take ƙwalla suka fara zuba daga idanunta. Dokta ya hau rarrashinta, ya kai ta ɗaki ya dawo wurina. Cikin sanyin jiki na ce masa na ga Umma kamar ba ta son tafiyata, in dai haka ne ni na haƙura.

Dokta ya yi murmushi ya girgiza kai yace mini, “Kansa’u yanzu kam ina ganin lokaci ya yi da ya kamata in miki bayani tunda za ki tafi karatu, na san kanki ya sha kullewa akan irin kulawar da nake ba ki. Ki sani ba ni ɗaya bane Umma ta haifa, mu biyu ne a wurinta, ni da ƙanwanta Farida.

Farida ta taso yarinya mai hankali da nutsuwa daidai gwargwado, sai dai kullum matsalarta ɗaya ce, Farida ta kasance irin mutanen nan ne masu sa abu a rai, idan ta sa abu a rai komai ƙanƙantarsa in ta rasa shi sai ta shiga tsananin damuwa maras misaltuwa. Ba tare da mun ankara ba ashe ta faɗa soyayya da wani yaro, kafin mu farga, soyayyar ta yi zurfi a zuciyarta. A daidai lokacin da mu ka ankara ne yaron ya yanke alaƙa da ita, ya bar zuwa wajenta sannan ya daina kiranta kwata-kwata, ashe mahaifansa ne suka tilasta masa auren wata daga cikin danginsa.

Tun da abun ya faru Farida ba ta sake jin ɗuriyarsa ba, sai kawai ta ji labarin yayi aure. Kamar yadda na faɗa miki Farida na da sanya abu a rai, tun da ta ji labarin auren, ta gagara jure rashinsa, ta zauna ba ci ba sha, daga ƙarshe abun yayi tsamarin har ta kai ga ta ɗura wa kanta magunguna da suka wuce kima (overdose) wanda hakan ya yi sanadiyar ajalinta.

Yau shekara biyu kenan da rasuwar Farida amma har yanzu Umma ba ta cire ta a rai ba, rashin Farida ya taɓa zuciyar Umma sosai, duk da tana ɓoye mini amma na jima da fahimtar hakan.”

Ya ɗaga kansa ya kalle ni, ido cikin ido ya cigaba da cewa, “cikin ikon Allah, tun ranar da na fara ganinki a jami’a na fahimci kuna matuƙar kama da Farida, kusan komanku ɗaya, musamman muryarku.

Daga nan ki ka shiga raina duk da kasancewarki ‘yar maye. Na yi bincike a kan ki na gano cewa ba ki da iyaye, a hannun lalataccen baffanki ki ke, daga nan na sha alwashin sai na dawo da ke hayyacinki, in son samu ne ma in dawo dake hannun mahaifiyata ki maye mata gurbin Faridanta.

Yanzu haka da kika ga ta shiga damuwa fargaba take kar ki tafi kamar yadda Farida ta tafi ta barta. Burin Farida ne a lokacin da take raye ta je Birtaniya karatu, shi ne na cika mata akanki. Don haka ki shirya nan ba da jima wa ba jirginku zai tashi.” Ban san lokacin da idanuna suka fara zubar da hawaye ba. Na tabbatar masa insha Allahu zan maye wa Umma gurbin Farida, ya ji daɗin jin haka. Na tashi na je wurin Umma na rarrashe ta, ita ma na tabbatar mata cewa ta ɗauka Faridarta tana nan raye, ba zan taɓa watsa mata ƙasa a ido ba.

Bayan kwanaki jirginmu ya tashi sai Birtaniya, na ɗau tsawon shekara shida ina karatu a can. Ba ni da burin da ya wuce in kammala karatuna na dawo gida Nijeriya in yi tozali da Umma, in kuma yi tozali da Dokta don tunda na tafi babu garin Allah da zai waye ba tare da nayi tunaninsa ba, tun ina ƙaryata kaina akan na kamu da sonsa, har na tabbatarwa kaina tabbas na kamu da tsananin sonsa.

Bayan na kammala karatuna ne, na dawo gida Najeriya. Na sa a raina yanzu ne lokacin da ya kamata in bayyanawa Dokta sirrin da ke cikin zuciyata, na tabbata yadda na sauya yanzu kam zai iya karɓar soyayyata. Ina shiga gidan na samu ba kowa a ciki, da na fito nayi tambaya ake shaida mini ai Dokta ya haɗu da tsautsayi wani mashayin matuƙi ya buge shi. Ban tsaya wata wata ba na garzaya asibitin, na samu Dokta a kwance shame-shame, jikinsa duk bendeji, ba ya iya ko magana, Umma na zaune a gefensa, tana ganina ta miƙe zumbur kamar wanda aka sokawa allura. Cikin gaggawa naje na sunkuya a gabansa cikin shessheƙar kuka, ya kalle ni daga sama har ƙasa ya ga yadda na sauya, duk da tsananin ciwon da yake fama da shi ya yi murmushin gamsuwa da jin daɗi.

Umma take shaida mini cewa, yau kwana uku kenan wani direba ya shawo kayan maye ya kaɗe Dokta yayin da ya zo tsallaka titi, a hakan ma abun yazo da sauƙi, don mashayin direban ma ya rasu.

Ban yi ƙasa a guiwa ba,na ɗauke shi na kai shi babban asibiti a ranar. Da yake ya riga da ya bugu ta ciki ba‘a ankara ba a ranar ya cika, yace ga garinku. Allah sarki Dokta! Ashe da rabon za mu sake haɗuwa! Rashin Dokta ya girgiza ni ba kaɗan ba, ku san zan iya cewa rasuwarsa ta fi taɓa mini zuciya sama da rashin iyayena!

Na ci gaba da zama da Umma, baiwar Allah, ta riƙe ni a matsayin ‘ya a lokacin da nake buƙatar uwa. Na maye mata gurbin ‘ya’yanta, muka zauna cikin aminci, na riƙe ta kamar uwar da ta tsuguna ta haife ni.

Tun dawo wa ta daga karatu, na samu aikin koyarwa a jami’a mallakar jiha. An so a riƙe ni a ƙasar waje, amma na ƙi yarda na zauna a can, ni da nake da Umma da Dokta, sai dai kash gashi daga dawowa ta Allah ya karɓi Dokta. Tasirin da Dokta yayi a rayuwata yasa na ƙuduri niyar ɗaurawa daga inda ya tsaya, na taimakon mutane musamman waɗanda su ka tsinci kansu a cikin irin jarrabawar da ta same ni.

Watarana ina gyaran takardun jarrabawan ɗalibai, sai na ci karo da takarda wani ɗalibi mai suna Kamilu Abdullahi, takardar cike take da abun mamaki, tambayoyi guda uku kacal nace su amsa a cikin biyar, amma Kamilu ya amsa duka, kai har abin da ban tambaye shi ba sai da ya rubuto, ya cika mini takardu da rubutun da ya wuce hankali. Na yi matuƙar mamaki da ganin takardan. Ban yarda ba, nace a raina duk yadda aka yi yaron nan satar amsa ya yi, amma duk da haka kansa na ja, don haka sai nasa a nemo mini shi.

Yana shigowa ofishina mamaki ya kama ni, kasancewar ba yadda nake siffanta shi a zuciyata haka na ganshi ba. Saurayin da ke tsaye a gabana kana ganinsa kaga ɗan ƙwaya, idanunsa jawur kamar garwashin wuta, bakinsa yayi fari fat bushe, yana sanye da wando ɗamamme kamar mai shirin yin kokuwa. Wannan riƙƙaƙen ɗan ƙwayar fa na tambayi kaina a cikin zuciyata.

Ya buɗe baki ya gaishe ni, warin wiwi ya daki hancina. Na kawar da kai gefe, na tambaye shi ya aka yi ya amsa tambayoyi biyar alhali nace a amsa uku kaɗai. Ya hau sosa kai, yana magana irin na bugaggu, “kawai naga…” Ya carke sannan ya cigaba.“Sun mini sauƙi ne, shi yasa na amsa duka.” Mamaki ya kama ni, na girgiza kai na masa ishara da ya zauna, sannan na ɗauko sabuwar takardan da ba komai a cikinta na miƙa masa haɗe da takardan tambayoyin jarrabawa, nace ya sake amsawa a gabana don in ƙure shi. Ya yi hamma ya yamutsa fuska sannan ya kama rubutu tiryan tiryan niko na zubawa sarautar Allah ido. Cikin abin da bai gaza minti talatin ba ya sake amsa dukkan tambayoyin, ya miƙo man takardan na kalla cikin mamaki. Yanzu kam na yarda da kansa ya rubuta ba satar amsa ya yi ba. Abin da ya ɗaure mini kai yanzu shi ne ya aka yi lalataceccen yaro irin wannan, wanda da ka ganshi kaga riƙaƙƙen ɗan ƙwaya amma yake da wannan baiwa.

Tun daga ranar na ja Kamilu a jiki, har muka saba duk inda ya ganni ko a buge ya ke zai taho da gudu ya karɓa mini jakata ya kai mini har cikin ofis. Watarana na kira shi ofishina, na ke tambayarsa akan abin da ya jima yana kulle mini kai game da shi, me yasa yake shaye-shaye alhali ya kasance ɗalibi mai fikira da hazaƙa. Nan take hawaye suka fara kwaranya daga cikin idanunsa, bayan na rarrashe shi, na kawo masa ruwan sanyi daga cikin firij.

Ya fara bani labarin dalilin da ya jefa shi cikin wannan ɗabi’a ta shaye-shaye.“Tun ina yaro na taso mai hazaƙa a makaranta. Kusan duk makarantar ba mai ƙoƙarina. Hedmastanmu ya sha zuwa wurin mahaifina yana ba shi shawari akan ya kula da karatuna sosai, ganin yadda nake da ƙoƙari. Babana bai taɓa ɗaukar abun da muhimmanci ba, kasancewar irin mutanen nan ne masu mataccen zuciya, ya tara mata har guda huɗu amma ba shi da takamammen sana’a sai sayar da ƙwaya a wata tsohuwar gindin bishiyar durumi dake tsakiyar ungunwanmu.

Gindin durumin majalisa ne da ya yi ƙaurin suna waje tara mutane yan zaman banza da caca da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi. Mahaifina shi ne Gardi a majalisan wato uban ‘yan caca, ya riga da ya kashe zuciyarsa da zaman wurin ba dare ba rana, bai damu da cinmu ba balle shanmu.

Kwata-kwata bai damu da baiwar da Allah ya mini na karatu ba, kullum damuwarsa shi ne mu ‘ya’yansa muje muyi dako ko aikin ƙarfi mu samo kuɗin da za mu kula da iyayenmu mata da ƙannen mu ƙanana.

Kasancewar ni nake ƙulla masa tabar wiwi kashi-kashi, yake kuma tura ni kasuwa in saro masa goro, yasa yau da gobe na fara son ɗanɗana-ɗanɗanon maye. Abokaina da muke dako da su, suka yi ta zuga ni akan in sato mana kayan maye a ɗakin mahaifina, domin mu sha, mu samu kuzarin yin aikin ƙarfin da gaske. A haka har suke rinjaye ni, na faɗa tsundum cikin wannan mummunar ɗabi’ar shaye-shaye, har ta kai ga ba na iya aikin komai in ban sha ba.

Baƙin cikin tsintar kaina a cikin wannan mummunar hali ya sa zuciyar mahaifiyata ta buga, daga ƙarshe ya yi sanadiyar ajalinta. Har tayi jinya ta koma zuwa ga mahallincinta a asibiti, mahaifinmu bai taɓa leƙo ta ba, balle ya sayi magani. Ba ta jima da rasuwa ba, jami’an yaƙi da sha da fataucin muggan ƙwayoyi suka yi caraf da shi, a yanzu haka da nake baki labari yana can yana girban abin da ya shuka a magarƙama.

Tunda na faɗa wannan mummunar ɗabi’a, duniya ta yi mini baƙi, na saduda da rayuwa, rayuwa kawai nake kamar dabba, aikin karfin ma yafara neman gagara ta, ya zamana banida aiki sai shaye-shaye da zaman banza, har ta kai ga na fara ɗauke ɗauke in na rasa kuɗin da zan sayi kayan maye.

Wata rana akayi rashin sa’a naje ƙwacen waya, aka kamani aka lakaɗa mi ni duka, daga ƙarshe aka miƙa ni hannun jami’an tsaro sai gidan yari. Kafin na ƙarasa wa’adina ne, wata ƙungiya wayar da kan matasa akan illolin shaye-shaye ta yi belin ire-ire na, ta ɗau nauyin jinyarmu da shirya mana darusan wayar dakai na tsawon lokaci, daga ƙarshe ta ba wasu jari daga cikinmu, irina masu son karatu ta samar mana guraben karatu a makarantu daban-daban.

A ɗan ƙanƙanin lokaci, na fara dawowa hayyacina, na fara karatu a jami’ar nan, haɗuwa da muggan abokai ya sa na ƙara komawa ruwa, duk da cewa na rage ba kamar can baya ba. Rashin tsayayyen uba da mafaɗi da talauci da muggan abokai ne suka ƙara jefani cikin wannan mummunar ɗabi’ar ta shaye-shaye.”

Kamilu na gama bani labarinsa, da yadda aka yi ya faɗa cikin wannan mummunar ɗabi’ar shaye-shaye, na jinjina kai cikin tausayi, gaskiya na yi matuƙar tausaya ma sa kasancewar yaro mai ilimi irin sa ya faɗa wannan jarrabawa, tabbas da ya samu mai ƙarfafa masa guiwa a karatu da bai faɗa cikin wannan mummunar ɗabi’a ta shaye-shaye.

Tun daga ranar na daɗa jansa a jiki, kasancewar labarin rayuwar mu kusan iri ɗaya ne, na mayar da shi tamkar ƙanina, a duk lokacin da na masa wani alheri naga farin ciki a fuskarsa sai na tuna da Dokta Rufa’i, sai na tuna da lokacin da yake ta faɗi tashi a kaina, hakan ya kan ƙaramin ƙarfin guiwa don ganin na ceto wannan saurayi mai fikira daga wannan mummunar ɗabi’a.

Sannu a hankali har ya watsar da shaye-shaye gaba ɗaya da taimakona da kuma taimakon Umma wanda ta ɗauke shi, shi ma tamkar ɗa.

Bayan ya kammala karatu ya kama aiki a babban asibiti jiha, ƙannensa da suke zaman banza, ya dawo dasu cikin hayyacinsu, wanda suke makaranta suka watsar ya mayar dasu, masu sana’a ya ƙara musu jari, iyayensu mata suka dawo cikin hayyacinsu duk a sanadin Kamilu wanda yanzu ya dawo kamili.

Tasirin da Dokta Rufa’i yayi a rayuwata yasa na buɗe Gidauniyar mai sunan Dokta Rufa’i foundation wanda ta bayar da muhimmanci akan zaƙulo mutanen da suka faɗa mummunar ɗabi’ar shaye-shaye, a ƙanƙanin lokaci muka ɗauki nauyin mutum arba’in. Da naje duba mutanen domin ƙarfafa musu guiwa da ba su shawarwari akan yadda za su daina wannan mummunar ɗabi’ar.

Kwatsam na hango wani dattijo rike da sandar makafi abun ya bani mamaki, shaye-shaye har da makafi? Da na matso kusa da shi sai naga ashe Baffa Sale ne ƙanin mahaifina, warin giya ya buleni, na kalli idon da na fasa masa naga baya gani. Gaba ɗaya ya rame, ya lalacewa, tsufa ta cimmasa ba abin da ya ke yi sai warin giya da zarni fitsari, na yi masa sannu, nan take ya gane muryata, “Kansa’u, dama kina raye? Na amsa masa, cikin tsana wata zuciyar tace in sa ayi waje da shi, tausayinsa ya kamani, yana kakkarwa, ya kuma ce,“nawa za’a bamu ne da aka kawomu nan wurin?” Hali zanen dutse, mai hali ba ya sauya halinsa. Na girgiza kai cikin takaici na ce masa, “In har ka bar shaye-shaye, ba abin da za ka nema ka rasa.

Da yake nasan halin kayana, in ya fahimci ba kuɗi za a ba shi ba guduwa zai yi. Sai na ɗau wasu ‘yan kuɗaɗe na bashi, ashe a hannu yake, yasan yadda yayi ya sulale. Bayan awanni aka zo aka gaya mana cewa ɗaya daga cikin mutanen da muka killace mota ta kaɗeshi, muna zuwa mu ka ga Baffa Sale ne, direban da ya kaɗeshi da mutanen dake wajen suka shaida mana cewa ya sha kayan maye ne ya yi tatul yana ta tangaɗi akan titi, direban bai Ankara ba ya kaɗeshi, na tsaya akan gawar na kalli Baffa Sale dake kwance jina-jina ɗaya idon ma ya fashe, na kalleshi na tuna tun lokacin da nayi wayo kullum a wahale yake a sanadiyar shaye-shaye da yake yi, yanzu yayi rayuwarsa a wahale ya tafi a wahale kenan Allah sarki Baffa Sale ƙarshensa kenan.

Bayan wani lokaci na ci gaba da rayuwata, daga Umma sai Kamilu su kaɗai ne dangina, lokaci ɗaya na kwanta rashin lafiya mai tsanani, Kamilu ya ɗaukeni ya kaini asibitinsu, da aka gwadani akace ina fama da ciwon ƙoda, dole sai an mini dashe. A karo na biyu kenan a rayuwata na cire tsammanin da rayuwa, ni da bani da kowa a duniyarnan wa zai bani ƙoda, ina kwance ga ciwo ga tunani ga zullumi, Kamilu da Umma suka zo suka zauna a gefena, Kamilu ya hau kwantar mini da hankali tare da ƙarfafa mini guiwa.

Daga ƙarshe ya tabbatar mini da cewa ya riga da ya gama cike takardu zai bani ɗaya daga cikin ƙodarsa, hawayen farin ciki suka kwaranyo daga idanuna, ashe tasirin da nayi a rayuwar Kamilu har ta kai ga zai iya bani ƙoda.

Allah sarki Dokta Rufa’i! A dalilinsa ne rayuwata, ta sauya na zama mutum, bayan rayuwata ta lalace. Allah sarki Kamilu! A dalilinsa ne yanzu zan cigaba da rayuwa, bayan na ɗebe tsammani.

Ɗaukar Jinka

Post a Comment

0 Comments