𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam Allah ya saka da alkhairi Allah ya biya da gidan aljanna tambayata malam mene ne hukuncin mai yanke zumunci Allah yabada ikon amsawa🙏
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
Wa'alaikum Salaam
Warahmatallahi Wabarkatahu
Hadisin Zubair dan
Mad'im Allah ya kara yarda a gareshi yace, Hakika Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam Ya ce: Mai yanke zumunci ba zai shiga aljanna ba. (Bukari da
Muslim).
Hadisin Abi Bakrata
Allah ya kara yadda a gareshi ya ce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya
ce: Babu wani zunubi wanda ya cancanta Allah ya gaggauta yi wa mai shi ukuba
tun daga nan duniya bayan wanda ya tanada a lahira kamar mai yanke zumunci
(Bukari).
Duk wanda ya yanke
Zumunci ga makusantansa raunana (wato Talakawa mabukata) ya kaurace musu, baya
sada Zumunci a garesu, baya kyautata musu, alhali yana da iko da wadatar da zai
taimaka musu, to wannan haramun ne shiga Aljanna a gareshi, sai dai in ya tuba
ga Allah, ya dawo ya kyautata musu.
Mai yanke Zumunci tun
daga duniya yan'uwansa baza su sami shakuwa da shi ba, kuma har ma wani lokacin
a rika mantawa da shi gaba ɗaya.
Ya zo a cikin Hadisi
daga Manzon Allah Salallahu Alaihi wasallam Ya ce: Wanda ya zamo yana da
yan'uwa mabukata baya kyautata musu, sai ya juyar da taimakonsa ga wasu daban
na nesa, to Allah ba zai karbi wannan aikin nasaba, ba zai yi duba agareshi
ranar Alkiyama ba. In kuma shi ma yazamo bashi da hali (wato shi ma mabukacinne)
to ya rika ziyartarsu yana karfafar halin da suke ciki Saboda fadinsa
Alaihissalam; Ku sadar da Zumunci ko da da Sallamane.
Sada zumunci yana da
tarin falala, wanda idan muka ɗauke falalar da za a samu a lahira, zamu ga cewa tun daga
duniya idan kaje ka sada zumunci ko da ziyarar abokin ka ne ko wani dan'uwanka
na jini, zakaji ka samu nutsuwa da nishadi, shi ma kuma zai ji dadi sosai.
Sada zumunci shi ne
kyautatawa da jinkai da bibiyar yan uwa (ma'abota zumunci), ta hanyar sadar da
dukkan alheri gare su, da kawar da dukkan sharri daga garesu gwargwadon iko.
Ziyartarsu da amsa
kira da gayyatarsu da taimaka musu da dukiya da tausasa magana gare su da kawar
da kai daga kura-kuransu da yi musu addu'ar alheri.
Hadisin Nana Aisha
Allah ya kara mata yarda tace, Sada zumunci yana rataye ne da Al-Arshi, yana
cewa: wanda ya sadar da ni to zan sadar da shi, wanda ya yanke ni to zan yanke
shi (Bukari da Muslim).
MA'ANA shi ne zai
sadar da shi da Rahmar Allah (SWT) ko ya yanke shi daga samun Rahama.
Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce: Ba Sadar da zumunci ba ne in anzo maka kaje,
in an baka ka bayar, in an girmamaka ka girmama, Sada Zumunci shi ne wanda ya
yanke maka ka Sadar masa ( wato Ka ziyarci wanda baya ziyartarka, ka bawa wanda
ya hanaka.)
Malamai sun bayyana
Sada zumunci a matsayin ɗaya daga cikin manyan
Alhairan da ake gaggauta bayar da lada akai, kamar yadda ya zo a cikin Hadisin
Manzon Rahama Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: Alherin da
ake gaggauta bayar da lada a kai shi ne Sadar da zumunci.
Abin da Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) yake kokarin nuna mana shi ne Musulmi ya kasance a
ko da yaushe mai tsananin kula da yan'uwansa na jini, dangi gami da yan'uwa na
ruhi, wato wadanda addini ya haɗa su.
Duk mai sada zumunci
zai kasance masoyi ne ga kowa, yan'uwa da sauran dangi za su so shi, ba don
yana ba su kuɗi ko wani abu ba,
amma kasancewar yana daga cikin waɗanda suke bibiyar lafiyarsu da kuma matukar
nuna tausayawa tare da jinkai gare su.
Ya Allah ka ba mu ikon
sada zumunci domin saduwa da dukkanin alkhairan da ke cikinsa na duniya da
lahira.
WALLAHU A'ALAM
✍
Auwal Zakari Ayagi
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ƘARIN BAYANI
MENE NE HUKUNCIN
MAI YANKE ZUMUNCI A MUSULUNCI, KUMA MENENE SAKAMAKONSA A DUNIYA DA LAHIRA?
TAMBAYA:
Assalamu alaikum. Malam, don
Allah ina neman ƙarin bayani kan hukuncin mutumin da yake yanke zumunci da
danginsa ko ƴan'uwansa.
Shin menene makomarsa a wurin Allah, kuma ta yaya ya kamata musulmi ya kasance
wajen sadar da zumunci koda ƴan'uwan ba sa nufinsa da alheri?
AMSA:
Haɗarin Yanke Zumunci Da
Falalar Sadar Da Shi
A cikin shari'ar Musulunci, yanke
zumunci (Qati'atur-Rahim) yana ɗaya
daga cikin manyan zunubai (Kaba'ir). Zumunci ba kawai ziyara ba ce; wani haƙƙi ne
na jini wanda Allah Ya umarci a kiyaye shi. Wanda ya yanke zumunci ya saba wa
umarnin Allah, kuma ya buɗe
wa kansa ƙofofin
tsinuwa da rashin albarka.
1. Tsinuwar Allah Ga Mai Yanke
Zumunci
Allah Madaukakin Sarki Ya bayyana
a cikin Alƙur'ani
cewa waɗanda suke
yanke zumunci sun cancanci tsinuwarSa, kuma zai toshe musu kunnuwa da idanu
daga ganin gaskiya.
Allah Madaukakin Sarki yana cewa:
فَهَلْ عَسَيْتُمْ إِن تَوَلَّيْتُمْ أَن تُفْسِدُوا
فِي الْأَرْضِ وَتُقَطِّعُوا أَرْحَامَكُمْ * أُولَٰئِكَ الَّذِينَ لَعَنَهُمُ اللَّهُ
فَأَصَمَّهُمْ وَأَعْمَىٰ أَبْصَارَهُمْ
Hausa: "To, shin kuna fãtan
idan kuka juya bãya, zaku yi barna a cikin ƙasa, kuma ku yanke zumunci tsakãninku? Waɗannan su ne waɗanda Allah Ya la'ance su,
saboda haka Ya kurantar da su, kuma Ya makantar da gannansu." (Suratu
Muhammad: 22-23).
2. Haramcin Shiga Aljanna
Babban hadarin da ke tattare da
mai yanke zumunci shi ne korar da za a yi masa daga shiga gidan ni'ima
(Aljanna). Wannan yana nuna cewa ko da mutum yana sallah da azumi, matuƙar
yana yanke zumunci da gangan, to akwai babban shinge tsakaninsa da Aljanna.
An karbo daga Jubair bin Mut'im
(R.A) cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
لَا يَدْخُلُ الْجَنَّةَ قَاطِعٌ
Hausa: "Mai yanke zumunci ba
zai shiga Aljanna ba." (Buhari da Muslim suka rawaito shi).
3. Gaggauta Ukuba A Nan Duniya
Mafi yawancin zunubai ana
jinkirta sakamakonsu ne har sai ranar Lahira, amma yanke zumunci da zalunci su
ne zunubai biyu da Allah Yake gaggauta wa mutum ukuba tun a nan duniya kafin
wadda take jiran sa a Lahira. Mai yanke zumunci zai ga kuncin rayuwa, rashin
albarkar dukiya, da kuma ƙiyayya daga mutane.
An karbo daga Abu Bakrata (R.A)
cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
مَا مِنْ ذَنْبٍ أَجْدَرُ أَنْ يُعَجِّلَ اللَّهُ
لِصَاحِبِهِ الْعُقُوبَةَ فِي الدُّنْيَا مَعَ مَا يَدَّخِرُ لَهُ فِي الْآخِرَةِ مِنَ
الْبَغْيِ وَقَطِيعَةِ الرَّحِمِ
Hausa: "Babu wani zunubi
wanda ya cancanci Allah Ya gaggauta wa mai shi uƙuba a nan duniya, tare da abin da Ya
adana masa a Lahira, kamar zalunci da yanke zumunci." (Tirmizi da Abu
Dauda).
4. Wanene "Mai Sadar Da
Zumunci" Na Gaskiya?
Mutane da yawa suna tsammanin
sadar da zumunci shi ne ka ziyarci wanda yake ziyartarka. Amma a mahangar
Musulunci, gwajin gaskiya na zumunci yana nan lokacin da ƴan'uwanka
suka yanke ka, kai kuma ka ƙi yarda ka yanke su.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
لَيْسَ الْوَاصِلُ بِالْمُكَافِئِ، وَلَكِنِ
الْوَاصِلُ الَّذِي إِذَا قُطِعَتْ رَحِمُهُ وَصَلَهَا
Hausa: "Mai sadar da zumunci
ba shi ne wanda yake saka alheri da irinsa ba (kana yi mini ina yi maka), a'a,
mai sadar da zumunci na gaskiya shi ne wanda idan aka yanke zumuncinsa, shi
kuma sai ya sadar da shi." (Buhari).
5. Falalar Sadar Da Zumunci
(Albarkar Rayuwa)
Idan mutum yana son Allah Ya buɗa masa hanyoyin samun
dukiya kuma Ya tsawaita masa rayuwa mai albarka, to hanyar ita ce sadar da
zumunci.
Daga Anas bin Malik (R.A) ya ce:
Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
مَنْ أَحَبَّ أَنْ يُبْسَطَ لَهُ فِي رِزْقِهِ،
وَيُنْسَأَ لَهُ فِي أَثَرِهِ، فَلْيَصِلْ رَحِمَهُ
Hausa: "Duk wanda yake son a
yalwata masa a cikin arzikinsa, kuma a jinkirta masa ajalinsa (tsawon rai), to
ya sadar da zumuncinsa." (Buhari da Muslim).
Kammalawa Da Shawara
Yanke zumunci yana jawo fushin
Allah da tsinuwa. Ya kamata kowane Musulmi ya bincika dangantakarsa da
iyayensa, yan'uwansa, da sauran danginsa. Ko da dangi suna da wahalar sha'ani,
ka yi haƙuri
da su don neman yardar Allah. Sadar da zumunci yana iya kasancewa ta hanyoyi da
dama:
• Ziyara:
Zuwa gida a gaishe su.
• Taimako: Ba
su abinci ko kuɗi idan
suna buƙata.
• Saduwa Ta
Waya: Kiran su don jin lafiyarsu.
• Tausasawa:
Yin magana mai daɗi da
kau da kai ga kura-kuransu.
Ya Allah Ka ba mu ikon sadar da
zumunci, Ka sanya albarka a cikin rayuwarmu, kuma Ka tsare mu daga tsinuwar
masu yanke zumunci.
WALLAHU A'ALAMU
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.