Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsokaci Game Da Littafin Malam Zalimu

Daga

Mus'ab Alfindiki Ph.D.
Sa'adatu Rimi College of Education Kano
+2348033971311

1.1 Tarihin Ado Ahmad Gidan Dabino

An haifi Ado Ahmad a shekara ta 1964 a garin Xanbagina da ke Qaramar Hukumar Dawakin Kudu. Ya girma a Unguwar Zangon Barebari a cikin birnin Kano. Ya fara karatun allo, (Alqur’ani) a makarantar Malam Rabi’u a Unguwar Zangon Barebari, a shekarar 1968 da karatun littattafai na Islamiyya a makarantar marigayi Sheikh Tijjani na ‘yanmota, (1971). Bai sami damar yin karatun boko yana qarami ba, sai da ya girma sannan ya sami shiga makarantar ilmin manya ta Masallaci (Adult Evening Classes) Kano a shekara ta 1984 zuwa 1986. Ya yi makarantar sakandare ta dare (G.S.S. Warure Evening Session), Kano a shekara ta 1987 zuwa 1990. Ya shiga Jami’ar Bayero inda ya sami takardar shaidar Difloma Qwarewa a kan yaxa labarai, wato (Professional Diploma in Mass Communication) a Sashen Koyar da Aikin Jarida, a shekara ta 2004 zuwa 2005.

Ya rubuta littattafai da aka buga su kamar haka: In Da So Da Qauna 1-2 da Masoyan Zamani 1-2 da Duniya Sai Sannu da Kaico! Da Malam Zalimu (wasan kwaikwayo) da Ina Mafita (wasan kwaikwayo) da Daqiqa Talatin (wasan kwaikwayo) da Mata da ShayeShayen Kayan MayeIna Mafita? da Sarkin Ban Kano, Alhaji Dr. Mukhtar Adnan (Tarihi), wanda suka rubuta da Sani Yusuf Ayagi. An kuma fassara wasu daga cikin littattafansa guda biyu daga harshen Hausa zuwa Ingilishi: The Soul of My Hear (Fassarar In Da So Da Qauna) da Nemesis (Fassarar Masoyan Zamani). Ya gabatar da muqalu da dama a tarurrukan qara wa juna sani a cikin Nijeriya da qasashen waje. Wasu daga cikin takardun nasa an buga su a cikin mujallun ilmi. Yana yin rubuce-rubuce a cikin jaridu da mujallun Hausa. Tare da shi aka kafa wasu qungiyoyi, kamar Qungiyar Marubuta ta Nijeriya Reshen jihar Kano, (ANA) a shekara 1992, kuma ya riqe shugabancinta na tsawon shekara uku. Shi ne mai gabatar da shirin Alqalami Ya Fi Takobi, a gidan rediyon Freedom Kano da kuma shirin Duniyar Masoya a gidan rediyon Shukura FM da ke Damagaram, qasar Nijar. Harkar rubuce-rubuce da kuma wallafa ta ba shi damar zuwa qasashe fiye da goma sha biyar a Afirika, sannan kuma a qasashen Turan ya sami zuwa London da Faransa da Italiya da kuma Jamus. Ya zama zakaran gasar rubutun wasan kwaikwayo ta shekarar 2009 ta tunawa da marigayi Injiniya Mohammed Bashir Qaraye, a Abuja, Nijeriya. (Ya shiga gasar da littafin Malam Zalimu).

Ya sami takardun yabo da dama daga jami’o’i da qungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi da gwamnati, saboda gudummuwa iri-iri da yake bayarwa waxanda suka shafi harshen Hausa da adabi da al’adu ta fannin rubuce-rubuce da shirin finafinai da aikin jarida da harkokin qungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi da kuma gwamnati. A ranar 24 ga watan Nuwamba na shekarar 2011 ya sami takardar yabo daga Inuwar Jama’ar Kano, (Kano Forum) cikin mutane goma sha xaya da aka yaba da su a jihar Kano wajen bayar da gudummuwa game da ci gaban al’umma.

Shi ne marubuci xaya daga cikin littattafan da wannan aiki zai nazarta mai suna Malam Zalimu. Littafin ya kalli yadda yanayin malamai a qasar Hausa yake kasancewa wato wasu masu gaskiya ne da imani da tsoron Allah da tausayi da kuma dattaku, wasu kuwaa masu yaudara ne da zalunci da qin gaskiya da halayya irin ta vatarwa. Waxansu daga cikin ‘yan masu wasa su ne: Malam Zalimu, Tanimu, Laminde, Sauda, Malam Dangana, Hajara, Maigari da kuma Alhaji Qailula da sauransu.

1.2 Malam Zalimu

Wannan wasa an gina shi ne a kan koyar da darussa daban-daban na zamantakewar yau da kullum, domin koyar da halaye nagari da nisantar munanan halaye. Daga cikin waxanan halaye akwai kishi tsakanin mata abokan zama wanda yake kai wasunsu ga shiga malamai da bokaye da nufin cutarwa wanda a qarshe abin yake komawa kansu su afka cikin da-nasani. Har wa yau an nuna irin nasarar da mata masu haquri da tsare haqqin aure suke samu a gidajansu ba tare da bin boka ko malami ba. Allah yake kare su da ga dukkan sharri.

A nan za a ga cewa wasu matan kan nuna zafin kishi ga abokan zamansu har su riqa iqirarin ganin bayansu ko kawo qarshen zamansu a gidajen aurensu, wasu matan kan bi ta qarqashin qasa ne, wato su shiga malamai da bokaye don cimma burinsu, wasu kuwa kan yi amfani ne da kissa da kisisina da gulma da sauransu wajen lalata zaman kishiyoyinsu a gidajen, sai dai hakan kan yi tasiri ne kawai na xan wani lokaci wanda ba ma tabbas yin tasirin nasa kuma daga qarshe abin ya komo kansu ko waninsu. Ga malamai kuwa an nuna matsananciyar gaba da ganin qyashi da ke afkuwa a tsakaninsu saboda abin duniya wanda har ya kai su ga jifan juna da asirai da nufin tagayyara junansu wanda ba wata nasara a kan hakan. Duk da cewa malamai jagorori ne na al’umma akan sami marasa tsoron Allah masu haddasa fitina, da kuma yin amfani da damarsu su cutar da jama’ar da suka fi qarfi ko kwaxayi da nuna qyashi ga waninsu. An fito da malamai masu tsoron Allah da gargaxin mutane a kan aikata munanan halaye. Masu kyautata mu’amalarsu da taimakon juna sannan da yin haquri ga jama’a sannan da koyar da mutane kyawawan halaye da nuna musu su nisanci munana domin samun tsira a duniya da lahira gaba xaya.

An nuna ma’aikata a wannan qasa, akwai masu tsayawa a kan gaskiya da riqon amana da kuma riqo da ibada, da kuma masu cin hanci da rashawa a ayyukansu. Su bi dukiyar jama’a su cinye su kuma gina kansu da yaransu da dukiyar da ba ta halali ba, su kuma cutar da jama’a ta hanyar yi musu wasa da hankali ko yawo da hankali. A qarshe wannan ya fito da zalunci irin na wasu mutane da kuma qarshen su. Littafin ya yi nuni cikin tsawatarwa tare da jawo hankalin al’umma a kan cewa dukkan gaba da gabanta a rayuwa ta duniya. Shi ya sa Bahaushe ke cewa in za ka gina ramin mugunta gina shi gajere, sannan komai na da iyaka duk bunqasarsa ikon Allah ne kaxai ba ya qarewa.

A cikin littafin Malam Zalimu (2009) na Ado Ahmad Gidan Dabino, an kawo irin wannan nasiha inda Saude ta tafi gidan Malam Dangana domin ya haukatar da kishiyarta, shi kuma ya yi mata nasiha da cewa:

Malam Dangana: Ke yanzu za ki so wata ta haukatar da ke ko wani na ki?

Saude: (Ta girgiza kai) Ba zan so ba malam.

Malam Dangana: Idan har ba za ki so ba, don me kike son ki aikata wannan mummunan aiki ga wata?

Saude: (Ta vata rai, ta kau da kai) To na ji malam, sai an jima zan je in yi shawara.

Malam Dangana: Abin da ya kamata ki yi ke nan ki sake shawara. Da dai addu’a kika ce in yi miki domin ki sami fahimtar juna da ita, kada ku dinga yin tashin hankali, to zan iya yin wannan da gaggawa. (shafi 5-6).

 Idan aka yi la’akari da tattaunawar Malam Danagana da Saude, sai a ga kyakkyawar nasiha ce ya ba Saude. Ita Saude burinta shi ne haukatar da kishiyarta, saboda ta vata mata rai. Wannan abu ne da ake yi ta hanyar mugun aiki wanda ba wanda ke so a yi masa. A kan haka ne Malam Dangana ya yi mata nasiha domin ta canza ra’ayinta domin ko ita ba za ta so a yi mata kamar yadda ta faxa da bakinta ba. Abin da ke qunshe cikin hirar tasu faxakarwa ce ta fuskar nasiha domin, ta sauya tunani. A maimakon wannan mugun aikin, ta nemi addu’a don gyara tsakaninta da kishiyarta.

Idan aka yi duba da yadda rayuwa take a zahiri sai a ga cewa ana samun mata masu irin wannan tunani na cutar da abokan zamansu, kamar yadda Saude ta qudurta yi. Akwai matan aure masu shiga Bokaye da malaman tsibbu da nufin a cutar da kishiyoyinsu, ko a kashe su, ko a sa musu wata cuta ko rashin jituwa da miji da sauransu. Idan irin waxannan mata suka karanta wannan bayani na Malam Dangana zai iya zama nasiha gare su, su fahimci ba cutarwar ce ke da muhimmanci ba domin, su kansu ba za su so a yi musu hakan ba. Abin da ya fi shi ne neman gyaran zama tsakaninsu, su zauna lafiya, su fahimci juna, a daina fitina da tashin hankali.

Bayan wannan a shafi na 7 zuwa 8 an nuna yadda Laminde amaryar Saude suke tattaunawa da qawarta Amina inda take mata nasiha a kan miqa lamari ga Allah a maimakon mugun zama da kishiyata. Ga yadda hirarsu ta gudana:

Laminde: Amma matar nan ta dame ni da masifa.

Amina: Laminde ki rabu da ita kawai ki ci gaba da gaya wa Allah. Zai yi miki magani. Idan kin lura duk sauran kishiyoyinta da ta kora ai rashin dogara da Allah ne da suke yi, ban da jefe-jefen juna da asirai babu abin da suke yi.

Laminde: In Allah ya yarda, zan ci gaba da yin addu’a. (Shafi:7-8).

 Laminde kishiyar Saude ce. Ita Saude halinta shi ne biyar bokaye da miyagun malamai domin, cutar da kishiyoyinta. Tashin hankalin Saude ne ya ishi abokiyar zamanta Laminde har ta koka wa Amina. Ita kuwa Amina kasancewarta mai dogaro ga Allah, sai ta yi wa Laminde nasiha kyakkyawa. Ta ja hankalinta da ta riqa kai kokenta ga Allah domin shi ne maganin komai. Ta lurar da ita da ta nisanci abin da ake yi na jifa ko mugun aiki tsakanin kishiyoyi. Wannan ne ya sa Saude ta yi nasara kan sauran kishiyoyinta domin, ba su dogara ga Allah.

A zamatakewa ta zahiri, matar da ta dogara ga Allah, ta tsare yawan addu’a, musamman safe da yamma, Allah kan kare ta daga sharri kowane iri. Akwai kishiyoyi waxanda su kuma biyar bokaye suke yi domin, neman biyan buqatunsu. Matar da aikin bokanta ya fi qarfi, yawanci ita take galaba kan saura domin ba wurin Allah suka mai da lamarinsu ba. Haka ne ya sa Saude ta yi nasara kan sauran abokan zamanta masu yawa.

 Ke nan bayanin Amina wata nasiha ce ga kiyoshi kan cewa, su miqa lamurransu ga Allah, su riqa addu’a, su nisanci miyagun ayyuka tsakaninsu. Wannan ita ce hanyar nasara a gare su.

a cikin littafin Malam Zalimu (2009) na Ado Gidan Dabino an kawao irin wannan wa’azi inda Laminde take mayar wa da Saude martani kan irin rikicin zamantakewa na aure tsakanin kishiya da kishiya. Ga abin da take cewa: 

Laminde: wanda duk ya dogara ga Allah ba zai tave ko ya tozarta ba, Allah yana tare da masu haquri da gaskiya a kowane lokaci. (shafi: 3).

Laminde da Saude duk matan Tanimu ne, kuma kullum ba a raba su da cacar baki. Saude tana da halayya irin ta mata ‘yan duniya ga raini ga abokiyar zamanta. Ita kuwa Laminde tana da sifa irin ta waxanda suka yi makaranta kafin aurensu da kuma tarbiyya, hakan ne ya sa sau da yawa ba ta biye wa Saude idan tana takalarta da rigima. Idan aka yi la’akari da maganar Laminde da ta yi wa Saude a nan sai a ga wa’azi ne. Ita Saude burinta shi ne ta ga Laminde ba ta gidan Tanimu, watau dai burinta shi ne ta ga ranar da auren Laminde da Tanimu zai rabu, ta huta da zama da kishiya. Ita kuwa Laminde ta yi mata wa’azi ne da nufin ta canza ra’ayinta. Take kuma nuna mata fatan da take yi mata na ta ga ta tozarta, ba za ta tava gani ba domin ita ta dogara da Allah ne a kan komai nata. Nan ta qafa hujjar da faxar Allah yana tare da masu haquri, masu gaskiya koyaushe.

Idan aka yi duba da yadda rayuwa take a zahiri, za a ga cewa akwai zaman kiyoshi mai cike da rikici da rashin zaman lafiya. Irin wannan zama na sa wata kishiya ta yi qoqarin ganin ta wulaqanta abokiyar zamanta. Idan irin waxannan mata suka karanta irin wannan bayani na Laminde sai ya zama wa’azi ne gare su, su fahimci cewa lamarin duniya dogara ga Allah shi ne maganin duk wani mai son ganin ya tozarta wani. Dogara ga Allah ne mafita ga duk wani makirci na wani. Allah yana nan tare da wanda ya dogara gare shi, ya zama mai haquri, kuma mai gaskiya. Ke nan mutum ya dogara ga Allah sannan ya sa haquri ta tsaya ga gaskiya shi ne magani duniya.

Haka kuma a cikin wannan littafin a shafi na 5, an sami fitowar wa’azi ga mata irin waxanda suke zuwa neman taimako daga wajen malamai a kan biyan buqatunsu, nan ne aka nuna yadda malan za su dinga qarfafar matam da suke zuwa wajensu ta hanyar aiwatar ko gabatar da buqatunsu na alheri sama da na sharri ta hanyar wa’azi. Misali: 

Malam Dangana: (Ya zazzano idan ya buxe baki) wa’iyazu billahi, ai wannan ba aikina ba ne, gaskiya ni ba zan iya haukatar da wani ba, domin yin haka ba tsarin Musulunci ne ba. kina sa ne da cewa Annabi (S.A.W) ya ce, ‘Imanin xayanku ba ya cika har sai ya so wa xan‘uwansa abin da yake so wa kansa. Ke yanzu za ki so wata ta haukatar dake ko wani naki? (Shafi: 5).

Malam Dangana mutum ne da Allah ya azurta shi da ilimi na addini da kuma sanin laqani irin na almajirta. Hakan ne ya sa jama’a kan nemi ya riqa sa su a cikin addu’o’i da roqon Allah da yake yawan yi a kan buqatunsu da nufin ko a sami dacen biyan buqata. Saude ta je wajensa da buqatar neman maganin da za ta haukatar da kishiyarta Laminde. A hirar ta su za a ga wa’azi aka yi wa mutane ta bakin Malam Dangana cewa bai kamata xan Adam ya zama tunaninsa na ya cutar da xan Adam irinsa ba ne domin ya cimma wata manufa tasa. Nan take kuma aka nuna yadda malamai za su dinga tsame kansa daga cikin masu yin taimakon a yi cutarwa ga wani tare da kuma jan hankalin wanda yake niyyar gudanar da mummunar aniyar da ya kula, ya kuma canza tunani daga mummunan tunani zuwa kyakkyawan tunani don samun qarshe mai kyau. Idan aka yi duba a rayuwar yau, za a ga cewa ana samun mata masu irin wannan tunani na Saude na cutarwa ga abokan zamansu (kishiyoyi).

Idan irin waxannan mata masu irin wannan munmunan tunani suka ci karo da irin wannan bayani na Malam Dangana aka kuma ci sa a suka karanta da idon basira sai ya zama wa’aza ne a gare su. Wannan gavar na iya yin tasiri gare su ganin yadda malamin ya kafa hujja da hadisin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata gare shi. A nan kuma an nuna yadda ake son malamai su zama masu gina kyakkyawar al’umma ta hanyar bayar da kyakkyawar shawara tsakaninsu da masu bijiro musu da neman taimako na buqatu iri-iri.

Littafin Malam Zalimu Na Ado Ahmad Gidan Dabino

Post a Comment

0 Comments