𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wani malami ne a cikin audio clip yake cewa: Ƙa’idar tarawihi sai dole mutum ya yi tare da liman tun daga farko har ƙarshe, sannan ne zai samun ladanta. Har kuma ya janyo hadisin da ya ce: ‘Wanda ya tsaya har zuwa sallamar liman za a ba shi ladan tsayuwar dare.’ Mene ne gaskiyar wannan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam
Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.
Hadisin da ya yi
magana a kan hakan shi ne hadisin da Ahmad da As-haabus Sunan Al-Arba’ah suka
riwaito daga Abu-Zarr (Radiyal Laahu Anhu) cewa: Sahabbai sun roki Manzon
Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a daren da ya yi musu sallar
asham zuwa kusan rabin dare cewa, ya kara musu zuwa karshen daren. Sai shi kuma
ya amsa da cewa:
« إِنَّ
الرَّجُلَ إِذَا صَلَّى مَعَ الإِمَامِ حَتَّى يَنْصَرِفَ حُسِبَ لَهُ قِيَامُ
لَيْلَةٍ »
Shi mutum idan ya yi
sallah tare da liman har ya sallame ya juya za a lissafa masa tsayuwar dukkan
daren.
Wannan lafazin
riwayar An-Nasaa’iy (1372) da Ahmad (22030) da Abu-Daawud (1377) kenan. A cikin
Ahmad kuwa cewa ya yi: (إِذَا قَامَ) maimakon (إِذَا صَلَّى). Kusan haka ɗin shi ma Ibn Maajah
(1388) ya kawo, kuma ya cike da cewa:
« فَإِنَّهُ
يَعْدِلُ قِيَامَ لَيْلَةٍ »
Domin shi ana
daidaita shi da tsayuwar dukkan daren.
Shi kuma At-Tirmiziy
(811) da ya kawo lafazinsa cewa:
« إِنَّهُ
مَنْ قَامَ مَعَ الإِمَامِ حَتَّى يَنْصَرِفَ كُتِبَ لَهُ قِيَامُ لَيْلَةٍ »
Shi dai wanda ya
tsaya tare da liman har ya kammala ya juya, za a rubuta masa tsayuwar dukkan
dare guda.
Sai kuma ya bayyana
darajar hadisin, ya ce:
قَالَ
أَبُو عِيسَى هَذَا حَدِيثٌ حَسَنٌ صَحِيحٌ.
Abu-Isaa
(At-Tirmiziy) ya ce: Wannan hadisi ne kyakkyawa ingantacce.
Sannan da ya zo
bayanin matsayin hadisin a wurin malaman Fiqhu kuma, ya ce:
وَاخْتَارَ
ابْنُ الْمُبَارَكِ وَأَحْمَدُ وَإِسْحَاقُ الصَّلاَةَ مَعَ الإِمَامِ فِى شَهْرِ
رَمَضَانَ. وَاخْتَارَ الشَّافِعِىُّ أَنْ يُصَلِّىَ الرَّجُلُ وَحْدَهُ إِذَا
كَانَ قَارِئًا.
Ibn Al-Mubaarak da
Ahmad da Is’haaq sun zaɓi a yi sallar tare da
liman a cikin watan Ramadan. Shi kuma As-Shaafi’iy sai ya zaɓi mutum ya yi sallar
shi kaɗai idan dai shi ɗin makaranci
(alaramma) ne.
Asalin wannan maganar
kuwa ta auku ne kamar yadda hadisan suka nuna, a lokacin da Annabi (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi musu limancin sallar tarawihi har sau
uku: A daren 23 har zuwa kusan sulusin dare, a dare na 25 kuma zuwa rabin dare,
a dare na 27 kuma har zuwa kusan wayewar gari. (Jaami’ut Tirmiziy: 811).
A waɗansu riwayoyin ya
bayyana dalilin da ya sa bai cigaba da yi musu sallar na dukkan daren ba.
Al-Bukhaariy (lamba: 924) da Muslim (lamba: 1819) sun riwaito daga
Ummul-Mu’mineen A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) cewa: Manzon Allaah (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fita da tsakar dare ya yi sallah a masallaci, sai
waɗansu daga cikin
sahabbansa suka bi shi. Da gari ya waye suka bayar da labarin hakan, sai kuwa
mutane fiye da su suka taru suka yi sallah tare da shi a dare na biyu. Suka
sake bayar da labarin hakan, sai mutane suka sake taruwa da yawa a masallacin a
dare na uku, Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fito ya
yi musu limancin sallar. A dare na huɗu kuwa har sai da masallacin ya kasa ɗaukar adadin mutanen,
shi kuma bai fito ba sai a lokacin sallar Asubah. A bayan sallamar sallar ne
kuma ya ce musu:
« أَمَّا
بَعْدُ فَإِنَّهُ لَمْ يَخْفَ عَلَىَّ مَكَانُكُمْ ، لَكِنِّى خَشِيتُ أَنْ
تُفْرَضَ عَلَيْكُمْ فَتَعْجِزُوا عَنْهَا »
Bayan haka, ku sani
fa babu wani abu na al’amarinku da ya ɓoye mini. Sai dai ban fito ba ne domin na ji
tsoron kar a farlanta muku sallar daren, kuma ku zo ku kasa.
A wata riwayar Zayd
Bn Thaabit (Radiyal Laahu Anhu) kuma ya nuna gara dai su rika yin sallar a
gida, ya ce:
« مَا
زَالَ بِكُمْ صَنِيعُكُمْ حَتَّى ظَنَنْتُ أَنَّهُ سَيُكْتَبُ عَلَيْكُمْ،
فَعَلَيْكُمْ بِالصَّلاَةِ فِى بُيُوتِكُمْ، فَإِنَّ خَيْرَ صَلاَةِ الْمَرْءِ فِى
بَيْتِهِ، إِلاَّ الصَّلاَةَ الْمَكْتُوبَةَ »
Ba ku daina abin da
kuka rika yi ba har sai da na yi zaton za a wajabta muku. Don haka sai ku kula
da yin wannan sallar a cikin gidajenku. Domin mafificiyar sallar mutum ita ce a
cikin gidansa, sai dai ta farilla. (Sahih Al-Bukhaariy: 6113; Sahih Muslim:
1861).
Wannan ya nuna yin
sallar tarawih a gida ya fi yi a masallaci.
Don haka ba zai yiwu
a ce mutum ba zai samu ladan tarawihi ba sai in ya yi a masallaci tare da liman
har zuwa karshe. Tun da masallaci ba shi ne wurin yin wannan sallar na asali
ba.
Matukar abin da za a
ce dai shi ne: Ya halatta a yi ta a masallaci tare da liman saboda abin da
Khalifah Umar Bn Al-Khattaab (Radiyal Laahu Anhu) ya yi a zamanin halifancinsa,
inda ya tara jama’a a bayan Ubayy Bn Ka’ab (Radiyal Laahu Anhu), kuma da ya fito
a dare na-biyu ya gan su suna yi sai ya faɗi mashahuriyar maganarsa cewa:
نِعْمَ
الْبِدْعَةُ هَذِهِ ، وَالَّتِى يَنَامُونَ عَنْهَا أَفْضَلُ مِنَ الَّتِى
يَقُومُونَ .
Madalla da wannan
bidi’a. Amma wacce suke yin barci kafin su yi ta, ta fi wacce suke yin ta
yanzu.
Shi kuma mai riwaya
ya ce:
يُرِيدُ
آخِرَ اللَّيْلِ ، وَكَانَ النَّاسُ يَقُومُونَ أَوَّلَهُ .
Yana nufin karshen
dare ya fi alheri. A lokacin mutane a farkon dare suke yi. (Sahih Al-Bukhaariy:
2010).
Wannan ya nuna ba
dole ne yin sallar a masallaci tare da liman ba. Ko ba komai shi kansa
Sayyiduna Umar (Radiyal Laahu Anhu) a zamanin farko bai zama yana yin sallar
tare da su ba, a karshen dare yake yin sallarsa a gida, kamar yadda riwayoyin
suka nuna. Wa ya isa ya kuskurantar da wannan matsayin nasa a yau?
Idan kuma neman samun
ladan tsayuwar dukkan dare ne ya ɗauke hankalin wani, har yake kokarin wajabta
yin sallar a masallaci tare da liman, to bari mu saurari wannan hadisin kuma,
wanda Tameem Ad-Daariy (Radiyal Laahu Anhu) ya riwaito daga Annabi (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:
« مَنْ
قَرَأَ بِمِائَةِ آيَةٍ فِى لَيْلَةٍ كُتِبَ لَهُ قُنُوتُ لَيْلَةٍ »
Wanda ya yi karatu da
ayoyi ɗari a cikin dare
guda, za a rubuta masa qunutin dare guda. (Ahmad: 17421, da Ad-Daarimiy: 3514
suka riwaito shi, kuma Al-Albaaniy ya sahhaha shi a cikin As-Silsilatus
Saheehah: 644, da Saheeh Al-Jaami’i: 6468)
Ma’anar Qunutin dare
a nan shi ne: Tsawaita tsayuwar sallar dare. (An-Nihaayah: 4/183).
Daga nan ya fito fili
kenan cewa: Ko a gida mutum ya yi sallah yana iya samun irin ladan wanda ya
tsaya a masallaci har liman ya yi sallama. Ga kuma karin falalar sallar a
karshen dare.
A takaice dai, wanda
ya fita daga masallaci a bayan sallamar sallar Isha’i da manufar yin sallarsa
ta tarawihi ko tahajjud shi kaɗai ko tare da iyalinsa a karshen dare, ba za a hana shi
hakan ba. Kuma ba za a hana masa samun ladan tsayuwar dukkan dare ba, matukar
dai ya karanta abin da ya kai ayoyi ɗari a cikin sallarsa. Musamman dayake babu
wani nassi da ya nuna mustahabbancin haɗa sallar Isha’in da tarawihin, ta yadda
ficewar mai ficewa da waccan manufar zai zama makaruhi.
Maganar yin waɗansu raka’o’in
tarawihi tare da liman sannan mutum ya fita domin ya karisa sauran a gida a
karshen dare, kodayake ba mu san wani nassin da ya sunnata ko ya mustahabbantar
da hakan ba, amma kuma yin hakan ga wanda yake da manufar kammalawa a gida ba
wani makaruhi ko abin kyama ba ne. Domin tun da dai larura tana iya sanya mamu
ya rabu da limaminsa tun kafin sallamarsa daga sallar farilla, to ina kuma ga
rabuwarsa da shi a bayan yayi sallama daga sallar nafila?
Ba na ganin wani abin
kyama a nan, in sha Allah.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad
Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.