Citation: Nasir Usman NASIR (2023). Gudummawar Ƙungiyoyin ‘Yan Kasuwa Wajen Bunƙasa Kasuwancin Hausawa A Kano. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 11, Number 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
GUDUMMAWAR ƘUNGIYOYIN ‘YAN KASUWA WAJEN BUNƘASA KASUWANCIN HAUSAWA A
KANO
Na
Nasir Usman NASIR
Tsakure
Wannan takarda ta yi duba ne kan ƙungiyoyin ‘yan
kasuwa a Kano tare da yin bincike da zaƙulo wasu muhimman
abubuwa daga gare su ta yadda suke gudanar da al’amura da kuma irin rawar da ƙungiya ke takawa
wajen tafiyar da harkokin kasuwanci, musamman a wannan zamani da muke ciki. Kaɗan daga cikin muhimman al’amuran da suke gudanarwa sun haɗa da: Warware yunƙurin ɓoye kaya da ayyukan jin ƙai da sasanta rikici da
hukumomi da daidaita farashi da samar da ingantattun kaya da sauransu. Yayin
tattaro bayanai na wannan bincike, an tattauna da shuwagabannin ƙungiyoyin ‘yan
kasuwa da su waɗanda ake jagoranta da direbobi masu dako da kuma karance-karance. A ƙarshe, sakamakon
binciken ya gano rawar da ƙungiya take takawa, musamman wajen kare haƙƙoƙin ’ya’yan ƙungiya da kawo wa
kasuwanci ci gaba.
1.0 Gabatarwa
Ƙungiya ta kasance taro ne na mutane daban-daban da suka haɗu a kan wata manufa iri ɗaya domin su cimma wasu buƙatunsu. Wannan ya sa yawancin
al’umomi na duniya suke da wasu ƙungiyoyi na ɓangarori da dama da suke amfani da su domin ganin sun sauƙaƙa harkokinsu don samun ci gaba a
rayuwa. Haka kuma, su waɗannan ƙungiyoyi akan same su a ɓangarori da dama. Misali, ma’aikatan gwamnati da ‘yan kasuwa da ‘yan ƙwadago da ɗalibai da sauransu. Ana kafa waɗannan ƙungiyoyi ba don komai ba, sai don a magance wasu
matsaloli da ka iya tasowa da kuma kawo ci gaba. Ƙungiyoyi sukan taimaka domin a gudu
tare a tsira tare. Al’umar Hausawa ba a bar su a baya ba, kasancewar su ma suna
da nasu tsare-tsaren da suke amfani da su na ƙungiyoyi tun a gargajiyance.
Bahaushe mutum ne wanda bai yarda da zaman kashe wando
ba. A kullum yana ƙoƙarin ya ga cewa, ya samu na kansa. Wannan ya sa yake gudanar da sana’a,
domin ya samu abin da zai rufa wa kansa asiri. Daga cikin sana’o’in kuwa akwai,
noma da kiwo da fatauci da saƙa da fawa da ƙira da sauransu. Sana’o’in ba haka nan suke kara zube ba,
domin Bahaushe mutum ne da al’adarsa ta yarda da tsari irin na shugabanci.
Wannan ya sa tun a gargajiyar Bahaushe za a iske da yawa daga cikin sana’o’insa
na gargajiya suna da tsarin ƙungiyoyi da shugabanninsu. Sai dai a wancan lokacin,
Sarkin gari ne yawanci ke naɗa sarakunan waɗannan sana’o’i. Waɗannan masu jagorancin suna tafiyar da ayyukansu kasancewar suna samun haɗin kai da taimakon juna da samun kyakkyawar fahimta a
tsakaninsu, musamman masu sana’a iri ɗaya. Wannan takarda zata yi ƙoƙarin fito da irin rawar da ƙungiyoyin ‘yan Kasuwa suke takawa wajen gudanar da
harkokinsu na Kasuwanci.
2.0 Ma’anar Ƙungiya
Masana da manazarta sun yi tsokaci kan ma’anar ƙungiya. Waɗannan masana da manazarta sun haɗa da:
Bargery (1934) yana da ra’ayin cewa, “ƙungiya ita ce taron
jama’a domin ayyukan ci gaba”. Shi kuma Alkasim, (2000) yana da ra’ayin cewa, “ƙungiya haɗin kan al’umma ne da suka yarda kan wani abu don ci
gabansu”. A yayin da CNHN (2006, sh. 286) ke ganin cewar “Ƙungiya shi ne taron jama’a waɗanda suka haɗa kansu don cin ma wata manufa”. Ta ɓangaren Abubakar (2017) kuwa, yana ganin, “Ƙungiya na iya kafuwa ne a lokacin da
mutum biyu ko fiye suka haɗa kai kuma suka amince su yi aiki tare domin samarwa kansu ci gaba”.
A dunƙule za a iya cewa, ƙungiya ta kasance taro ne na mutane daban-daban da suka haɗu a kan wata manufa iri ɗaya domin su cim ma wasu buƙatu ko muradunsu na rayuwa.
3.0 Ma’anar Kasuwanci
Alhassan da wasu (1987) suna cewa, “A saya a sayar shi ne kasuwanci, wato a nan
mutum ya fitar da kuɗinsa ya sayi kadara, sannan
wani lokaci ya fitar da wannan kadara ya sayar shi ne kasuwanci”. A CNHN (2006) cewa aka ya yi, “kasuwanci,
sana’ar saye da sayarwa a kasuwa”. A daidai lokacin da Umar (2009) a
nasa ra’ayin cewa ya yi, “kasuwanci wata hanyar hulɗa ce ta saye da sayarwa tsakanin jama’a”.
Idan aka yi la’akari da ƙunshiyar waɗannan ma’anoni da magabata suka bayar kan kasuwanci, za a
fahimci suna da dangantaka da kasuwanci da saye da sayarwa. Babu wanda ya yi
magana kan samun ribar abin da aka sayar ko mayar da kuɗi ko kuma faɗuwar abin da aka sayar.
Da wannan nake ganin akwai giɓi da waɗannan magabata suka bari kan ma’anar
kasuwanci. A taƙaice dai muna iya cewa, kasuwanci hanya ce ta saye da sayarwa tsakanin
mutane wadda ake gudanarwa a kasuwa ko a
wani wurin na daban da nufin samun riba, sai dai a wasu lokutan akan mayar da
kuɗi ko kuma a faɗi.
4.0 Gudunmawar Ƙungiyoyin ‘Yan Kasuwa Wajen Bunƙasa Kasuwancin Hausawa
Ƙungiyoyin ’yan kasuwa suna matuƙar taka rawar gani wajen bunƙasa kasuwanci da tattalin arziki ga
su kansu ‘yan kasuwa da ma sauran al’umma baki ɗaya.
4.1 Warware
Rikici da Jami’an Hukuma
Ana samun irin waɗannan matsaloli tsakanin jami’an hukumar ‘yan sanda ko kwastam. Ɓangaren kwastam, ana
samun kayayyakin da ake kawowa daga ƙasashen waje. Misali, kayan da ake sayarwa a Kasuwar
Kwari da Singa da Famsenta da kuma Ƙofar Wambai. Waɗannan Kasuwanni da aka ambata mafi yawancin kayayyakinsu daga ƙasashen waje ake shigo
da su. Ana samun rikici tsakanin jami’an Kwastam da masu waɗannan kaya musamman idan jami’an suka riƙe musu kayansu,
kasancewar wasu ta ɓarauniyar hanya suke bi, wasu kuma ta hanyar da ta dace. Amma duk yadda
suka yi ana samun rikici tsakaninsu. A irin wannan hali, ƙungiyoyin ‘yan waɗannan Kasuwanni kan yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin an sasanta
matsalar domin a sakar musu kayan. Haka idan aka koma kan jami’an ‘yan sanda,
su ma ana samun rikici da su. Duk wasu kayayyaki da za a wuce da su sai an ba
su wani abu ko da mutum yana da shaidar
gaskiya a kan kayansa. Ƙungiya kan yi iya ƙoƙarinta wajen ganin sun sasanta kansu da waɗannan jami’ai.[1]
4.2 Warware Yunƙurin Ɓoye Kaya
A wasu lokutan ‘yan kasuwa na da ƙudurin ɓoye wasu kayan da suka fuskanci sun yi ƙaranci kuma ana da buƙatar su. Misali, ‘yan
kasuwar Dawanau suna da wannan hali na ɓoye kayan abinci musamman bayan an samu amfanin gona. Amfanin gona da ake
nufi a nan sun haɗa da gero da dawa da wake da masara.
Wasu ‘yan kasuwar kan sayi kayan da aka noma su ɓoye su a wani wuri na musamman har sai lokacin da aka
fuskanci kayan sun fara yankewa kafin su fitar da su. A irin wannan yanayi, ƙungiya kan taka wa masu
irin waɗannan ƙuduri birki ta hanyar wa’azantarwa
da su fitar da waɗannan kayayyaki domin a sayarwa masu
buƙata. Ko da yake ƙungiya ba ƙaramar wahala take sha ba wajen warware irin waɗannan matsaloli kasancewar wasu ‘yan ƙungiyar na da irin
wannan hali na ɓoye kaya.[2]
4.3 Daidaita
Farashi
Ƙungiya tana da hurumin daidaita farashin kayayyakin da ake sayarwa a
kasuwanni. Maimakon ta bari kowa ya sayar da abu yadda ya ga dama. Rashin
tsayar da farashin kayayyaki kan haifar wa ƙungiya matsala. Wannan ya sa take
taka rawa wajen ganin ta tsayar da farashin kayayyaki. Yin hakan na sa a ƙarshe masu saye su
yabawa waɗannan ƙungiyoyi domin rawar da suka taka
wajen ganin an sassauta musu wajen sayan kaya ta hanyar samun daidaitaccen
farashi.[3]
4.4 Kare Zalunci
da Almundahana a Kasuwanci
Ana samun ‘yan kasuwar da suke da wannan mummunan hali. A
wasu lokutan ‘yan kasuwa na tsallake wasu dokoki na ƙungiya. Misali, hana ɓoye kaya bayan wani lokaci a fitar da shi a sayar da
tsada, ko kuma sayar da kayayyakin da suka lalace. Wani lokaci, sayar da kayan
sata da makamantansu. A irin wannan yanayi, ƙungiya tana iya ƙoƙarinta domin ta ga cewa ta rage waɗannan ha’incin. Misali, ‘yan ƙungiyar Kasuwar Famsenta na taka
rawa wajen rage irin wannan zalunci, musamman idan aka sayar wa mutum wayar
sata. Haka Kasuwar Kantin Kwari ana samun wasu ɓata garin ‘yan Kasuwa da suke sayar wa mutane kaya kamar
atamfa ko yadi ko shadda wacce ta kasance dameji ce. Daga baya idan wanda ya
saya ya gane zai iya dawo da kayan wurin wanda ya saya. Idan ya ƙi yarda har maganar ta
je wajen ƙungiya, za ta saka baki (ƙungiya) ta kuma hukunta wanda ya sayar da kayan musamman
idan ta fahimci akwai son zuciya a ciki. Har wa yau, ‘yan kasuwar dawanau suna
da halin ɓoye kaya. Bayan wani lokaci sai su
fitar domin su sayar da kayayyakin da tsada. Ƙungiyar tana ƙoƙari wajen dakatar da masu irin
wannan ɗabi’a. Tana kuma hukunta duk wadda
ta kama ta hanyar cin tara mai yawa.[4]
4.5 Samar da
Ingantattun Kaya
Ƙungiya tana da matuƙar amfani wajen ganin ta wadata kasuwanni da kayayyaki, musamman waɗanda mutane ke buƙata sosai. Misali, ƙungiyar ‘yan Kasuwar Na’ibawa da ‘Yan Kaba na taka rawa ƙwarai wajen samar da
kayan marmari da kayan miya. Ƙungiyar na’ibawa tana ba wa kowanne ɗan kasuwa dama ya kawo kawane nau’in kayan marmari da
yake so. Haka, ƙungiyar ‘yan Kasuwar Kwari da Ƙofar Wambai da Famsenta da Singa, suna ƙoƙarin samar da kaya ga mabuƙata duk da cewa mafi
yawan kayayyakinsu a ƙasar waje ake samu. Waɗannan ƙungiyoyi suna da Kamfanonin da suka daidaita kansu wajen sayan kaya a
wajensu ta yadda kowane ɗan ƙungiya ka iya saya ba tare da wata matsala ba. Ƙungiyar ‘yan Kasuwar Unguwa uku ‘yan
awaki tana iya ƙoƙarinta wajen ganin an samar da dabbobi ba tare da yankewa ba. Haka kuma, a
ko da yaushe ƙungiyar kan dubi irin dabbobin da ‘ya’yanta suke saukewa a kasuwarsu domin
tabbatar da lafiyarsu da kuma tsabtace sana’arsu.[5]
4.6 Ayyukan Jin Ƙai
Gudanar da wasu ayyuka ga al’umma domin a ciyar da ƙasa gaba na daga cikin
abubuwan da ya shafi ayyukan jin ƙai. Ƙungiyoyin ‘yan kasuwar da suka bunƙasa suka samu ɗaukaka sosai kan yi wasu ayyukan da ake kyautata zato ko
ake sa ran gwamnati ce ya kamata ta yi. Daga cikin ƙungiyoyin ‘yan kasuwar da aka
nazarta, an fahimci cewa ƙungiyar ‘yan kasuwar Kantin Kwari suna da wata gidauniya
da suka kafa. Manufar kafa wannan gidauniya ita ce, taimaka wa marayu da
zawarawa, da ba su tallafi da koya musu ƙananan sana’o’i domin su riƙe kansu. Wannan gidauniya ta haɗa kai da hukumar hisba, inda suke tallafa wa zawarawa
wajen aurar da su da kuma koya musu ƙananan sana’o’i kamar ɗinki da fenti da yadda ake sabulu da turaren wuta da na
ruwa da sauransu. Haka suna taimaka wa marayu ta hanyar saka su a makaranta da ɗaukar ɗawainiyar karatun nasu.
Baya ga wannan, ƙungiyoyin ‘yan kasuwa na koya wa matasa yadda ake gudanar
da kasuwanci, inda suke zama yaran shaguna daga nan su ma su samu damar tsayawa
da ƙafafunsu. Har wa yau, suna samar wa matasa aikin yi ta hanyar ba su ayyuka
a cikin kasuwanninsu kamar shara da gadin kasuwa. Misali, ƙungiyar ‘yan Kasuwar Famsenta ba su
dogara da hukumomin Kasuwa kaɗai ba, sun ƙaro ma’aikatan da suke musu gadin kasuwa. Wannan gadin kamar wata hanya ce
ta tallafawa jama’a da samar musu aikin yi.
Har ila yau, ƙungiyoyin ‘yan kasuwa suna gudanar da aikin gayya. Ma’ana
suna ware wani lokaci da suke gudanar da share-sharen tituna da magudanar ruwa
da wajen zubar da shara (bola) da makamantansu. Haka kuma, ƙungiyoyin ‘yan kasuwa
suna ziyartar asibitoci da kuma ɗaukar nauyin bayar da magani ga marasa galihu.
4.7 Tarbiyya
Koyar da hali na gari ko kuma wani tafarki da akan ɗora mutum a kan ta domin samun madogara da girmama na
gaba dangane da tafiyar da harkokin yau da kullum shi ne tarbiyya. Wannan yana
daga cikin muhimman abubuwan da wasu ƙungiyoyin ‘yan kasuwa kan koyar ga al’ummar da take
shugabanta. Ita ƙungiya tana da wasu dokoki da sharuɗɗa da ta gindaya wa duk wani ɗanta. Misalin wasu hanyoyin tarbiyyantarwa a waɗannan ƙungiyoyi akwai rashin yarda da sata da sanya sutura marar kyau da rufe shaguna da zarar an kira
salla da makamantansu.
4.8 Haɗa Zumunci
Zumunci na nufin kyakkyawar dangantaka ta jini ko ta aure
ko kuma ta abota tsakanin mutum da mutum. Daga cikin manufofin kafa ƙungiya akwai neman goyon
baya ko haɗin kai. Wannan ya haifar da zumunci
musamman ga ‘yan ƙungiya ɗaya. A wani ɓangaren kuma, idan ƙungiya ta taimaka wa wani mai saye sakamakon wata
almundahana ko zalunci da ɗan ƙungiyarta ya yi masa hakan na iya samar da zumunci tsakanin wanda aka
taimaka da masu jagorantar ƙungiya.
5.0 Sakamakon Bincike
Wannan bincike ya gano wasu muhimman abubuwa game da ƙungiyoyin ‘yan kasuwa.
Daga ciki kuwa akwai taimakawa su kansu ‘ya’yan ƙungiya da kuma sauran al’umma waɗanda suke da alaƙa da ‘yan kasuwa ta fuskar sayayya da makamantansu. A taƙaice binciken ya gano
lallai ƙungiyoyin ‘yan kasuwa suna taka rawar gani wajen bunƙasa kasuwanci ga al’ummar Hausawa da
ma wasu na daban. A ƙarshe, nazarin ya gano rawar da ƙungiya take takawa wajen tafiyar da ayyukansu musamman
wajen kare haƙƙoƙin ’ya’yan ƙungiya da kawo wa kasuwanci ci gaba. Misali, shugabannin ƙungiya suna iya ƙoƙarinsu wajen kare ’ya’yansu daga faɗawa wani halin da zai jawo masu asarar dukiya daga wasu
hukumomi kamar Kwastam ko soja ko ’yansanda.
6.0 Kammalawa
Wannan takarda ta yi tsokaci ne kan rawar da ƙungiyoyin ‘yan kasuwa
suke takawa wajen bunƙasa kasuwancin Hausawa. Takardar ta fito da irin taimakawa da ƙungiya take yi domin a
gudu tare a tsira tare domin kaucewa faɗawa karayar tattalin arziki da kuma biyan buƙatunsu. Baya ga nan, lura da abin da
ke cikin takardar ta nuna cewa ashe gudanar da kowane abu a ƙungiyance yana da matuƙar muhimmanci saɓanin gudanar da abu akasin haka. Aiwatar da kasuwanci a ƙungiyance yakan sa a
gudu tare a tsira tare ba tare da an cutar da wani ɗan kasuwa ba. Wannan ya nuna ashe ƙungiya ta kowane ɓangare tana da muhimmanci ƙwarai musamman idan ana kiyaye
dokokinta sau da ƙafa.
Manazarta
Abubakar, M. (2017). Tasirin ƙungiyoyin zaɓi-sonka ga al’ummar Hausawa, keɓaɓɓen nazari a jihar Kaduna. ƊKundin Digiri Na Farkoɗ. Sashen Nazarin Harsuna da Kimiyya. Jami’ar Jihar Kaduna.
Alhassan, B. S, da Abubakar, A, da Zarruƙ, R.M. (1987). Sabuwar hanyar nazarin Hausa, littafi na biyu. University Press.
Alkasim, H. K. (2000). Gudunmawar ƙungiyoyin marubuta littattafai ga
raya adabin Hausawa. ƊKundin Digiri Na Farkoɗ. Sashen Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu
Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Bargery, G.P. (1934). A
Hausa-English dictionary and English-Hausa Ɓocabulary. Ahmadu Bello University Press.
CNHN (2006). Ƙamusun Hausa. Jami’ar Bayero.
Umar G. G. (2009). Bukukuwan
Hausawa. Ol-faith Prints.
Rataye I: Jerin sunayen waɗanda aka yi hira da su.
|
SUNA |
UNGUWA |
SHEKARUN HAIHUWA |
KASUWANCI |
MATSAYI |
WURIN DA AKA YI HIRA |
RANAR DA AKA YI HIRA |
|
Yusuf Aliyu |
Hotoro |
60 |
Kasuwancin Awaki |
Wakilin Sarkin Kasuwa |
Kasuwar Unguwa Uku `Yan awaki |
23 ga Watan Maris, 2019 |
|
Sammani Adamu El-Smart |
Jambulo |
38 |
Kasuwancin Sutura |
Tsohon Chairman |
Babban Shagon El-Smart Kantin Ƙwari |
12 ga Mayu, 2019 |
|
Salihu Idriss |
Goron dutse |
39 |
Kasuwancin Sutura |
Member |
Kantin Ƙwari |
5 ga Mayu, 2019 |
|
Abdul-Aziz Ɗalha Musa |
Haɗeja Road, Kano |
50 |
Kayan Abinci |
Chairman |
Kasuwar Singa |
15 ga Yuni, 2019 |
|
Hamza Abubakar |
Sabuwar gandu |
32 |
Gyaran Waya |
Tsohon Mataimakin Chairman |
Shagonsa da ke Famsanta |
13 ga Maris, 2019 |
|
Hussaini Magaji |
Gama Briget |
29 |
Waya |
Member |
Shagonsa da ke Famsanta |
15 ga Yuni, 2019 |
|
Abdullahi Ahmed Muhammad (Brother) |
Sheka |
45 |
Kayan Marmari |
Tsohon Chairman |
Rumfarsa da ke kasuwar Na’ibawa `yan lemo |
23 ga Maris, 2019 |
|
Haruna Auwal |
Waliri layin Tsangaya |
42 |
Kayan Marmari |
Member |
A teburinsa da ke kasuwar Na’ibawa `yan lemo |
14 ga Mayu, 2019 |
|
Ɗayyib Sani |
Shagari kwatas |
33 |
Kayan marmari |
Member |
A teburinsa da ke kasuwar Na’ibawa ‘yan lemo |
14 ga watan Mayu, 20019 |
|
Ɗanjummai Musa |
Yadakurya |
37 |
Kayan miya |
Chaiman na `yan Tattasai |
Rumfarsa da ke kasuwar `yan kaba |
15 ga Mayu, 2019 |
|
Shu’aibu Salisu |
Dawanau Temporary |
38 |
Kayan Awu |
Secretary |
Rumfarsa da ke kasuwar Dawanau `yan awu |
29 ga Mayu, 2019 |
[1]Hira da Sammani Adamu El-smart. Tsohon shugaban Kantin Kwari. Ranar
12-05-2019 da Abdul’aziz Dalha Musa,
shugaban kasuwar Singa, ranar 15-6-2019 da kuma Hussaini Magaji da ke Famsanta,
ranar 13-5-2019.
[2]Hira da Shu’aibu Salisu, sakataren ƙungiyar kasuwar Dawanau, ranar 29-5-2019.
[3]Hira da Abdul’aziz Dalha shugaban ƙungiyar kasuwar Singa, ranar 15-6-2019.
[4] Hira da Hamza Bukar da ke famsanta, tsohon shugaban ƙungiyar Famsanta, ranar
13-3-2019).
[5] Hira da Abdullahi Ahmad Muhammad , mamba a kasuwar Famsanta, ranar
23-3-2019 da Yusuf Aliyu, wakilin sarkin Kasuwar ‘yan awaki, ranar 11-7-2019.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.