FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR
IBNU TAIMIYYA (4)
Kowa ya sani, saduwa (jima'i) da rana da gangan a watan Ramadhan yana bata Azumin mutum, kuma yana wajabta ramuko da kaffara. To amma idan mutum ya sadu da iyali kusan Asubahi fa, yana zaton da sauran lokaci ashe bai sani ba tun tuni Alfijir ya keto, ko kuma ya manta ya sadu da iyalinsa da rana tsaka, BISA MANTUWA, me ya wajaba a kansa?
To Malamai sun yi sabani a
kan haka, daga cikin Malaman Salaf akwai wadanda suka ce: BABU RAMUKO A KANSA,
BALLE KAFFARA.
Wannan shi ne abin da
Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ya rinjayar, kuma shi ne zabinsa kamar yadda
Almajirinsa Ibnu Muflih ya fada a cikin "Al-Furu'u" (5/ 41).
Shaikhul Islami ya ce:
وهذا
القول أصح الأقوال وأشبهها بأصول الشريعة ودلالة الكتاب والسنة وهو قياس أصول أحمد
وغيره فإن الله رفع المؤاخذة عن الناسي والمخطئ. وهذا مخطئ وقد أباح الله الأكل
والوطء حتى يتبين الخيط الأبيض من الخيط الأسود من الفجر واستحب تأخير السحور ومن
فعل ما ندب إليه وأبيح له لم يفرط فهذا أولى بالعذر من الناسي.
مجموع
الفتاوى (25/ 264)
"Wannar fahimta ta fi
sauran inganci, kuma ta fi dacewa da ka'idojin Shari'a da dalilan Alkur'ani da
Sunna, kuma kiyasi ne bisa ka'idojin Imam Ahmad da waninsa cikin Malamai.
Saboda Allah ba zai kama mai mantuwa da mai kuskure ba. Wannan kuwa mai kuskure
ne, Allah ya halasta masa ci da saduwa da iyali har sai farin zare ya bayyana
daga bakin zare na Alfijir (sai hasken Alfijir ya bayyana daga duhun dare),
kuma an sunnanta jinkirta Suhur, don haka duk wanda ya aikata abin da aka
sunnanta masa ko aka halasta masa ba tare da sakaci ba, to wannan shi ya fi
cancantar uzuri fiye da mai mantuwa".
Saboda haka, duk wanda ya yi
saduwa (jima'i) da rana, wato tsakanin fitowan Alfijir har zuwa faduwar rana,
da gangan, da saninsa, Azuminsa ya baci. Kuma ramuko da kaffara sun wajaba a
kansa.
Amma wanda hakan ya faru da
shi, cikin mantuwa, ko cikin rashin sanin ketowan Alfijir, to babu komai a
kansa, kawai zai cigaba da Azuminsa ne, babu ramuko a kansa balle kaffara.
Alal hakika duk wanda ya
fahimci Shari'a a dunkulenta, bisa ka'idojinta da gamayyar dalilan Shari'a zai
ga cewa; lallai wannar fahimta ita ce mafi inganci kuma mafi karfin dalilai.
Dr Aliyu Muh'd Sani
(Hafizahullah)
FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR
IBNU TAIMIYYA (5)
Malamai sun yi sabani a kan
Mai Azumi idan ya ci abinci ko ya sha abin sha da rana a watan Ramadhana a
halin mantuwa ko kuskure. Sawa'un wanda ya manta ya ci ko ya sha, ko wanda yana
ta ci da sha bisa zaton Alfijir bai keto ba, alhali tun tuni Alfijir ya keto.
Wasu Malaman sun ce:
Azuminsa ya baci, sai ya yi ramuko.
Wasu kuma sun ce: Azuminsa
yana nan bai baci ba, don haka babu ramuko a kansa.
Wannan shi ne fahimtar da
Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ya zaba, saboda karfin dalilansu da dacewarsa ga
kiyasi, Al-Imam Ibnul Qayyim da Allama Ibnu Muflih sun hakaito haka daga gare
shi. Duba:
إعلام
الموقعين (3/ 244)، الفروع (5/ 39)
Shaikhul Islami Ibnu
Taimiyya ya ce:
والذين
قالوا: لا يفطر في الجميع قالوا: حجتنا أقوى ودلالة الكتاب والسنة على قولنا أظهر؛
فإن الله قال: {ربنا لا تؤاخذنا إن نسينا أو أخطأنا} فجمع بين النسيان والخطأ؛
ولأن من فعل المحظورات الحج والصلاة مخطئا كمن فعلها ناسيا وقد ثبت في الصحيح أنهم
أفطروا على عهد النبي صلى الله عليه وسلم ثم طلعت الشمس ولم يذكروا في الحديث أنهم
أمروا بالقضاء ولكن هشام بن عروة قال: لا بد من القضاء وأبوه أعلم منه وكان يقول:
لا قضاء عليهم. وثبت في الصحيحين أن طائفة من الصحابة {كانوا يأكلون حتى يظهر
لأحدهم الخيط الأبيض من الخيط الأسود وقال النبي صلى الله عليه وسلم لأحدهم: إن
وسادك لعريض إنما ذلك بياض النهار وسواد الليل} ولم ينقل أنه أمرهم بقضاء وهؤلاء
جهلوا الحكم فكانوا مخطئين. وثبت عن عمر بن الخطاب أنه أفطر ثم تبين النهار فقال:
لا نقضي فإنا لم نتجانف لإثم. وروي عنه أنه قال: نقضي؛ ولكن إسناد الأول أثبت وصح
عنه أنه قال: الخطب يسير. فتأول ذلك من تأوله على أنه أراد خفة أمر القضاء لكن
اللفظ لا يدل على ذلك. وفي الجملة فهذا القول أقوى أثرا ونظرا وأشبه بدلالة الكتاب
والسنة والقياس وبه يظهر أن القياس في الناسي أنه لا يفطر والأصل الذي دل عليه الكتاب
والسنة أن من فعل محظورا ناسيا لم يكن قد فعل منهيا عنه؛ فلا يبطل بذلك شيء من
العبادات ولا فرق بين الوطء وغيره سواء كان في إحرام أو صيام.
مجموع
الفتاوى (20/ 572 - 573)
"Wadanda suka ce:
Azumin mutum ba zai baci ba, a dukkan halayen mantuwa da kuskure, sawa'un a
lokacin fitowan Alfijir ko lokacin faduwar rana, suka ce: Hujjarmu ta fi karfi,
kuma dalilan Alkur'ani da Sunna suna nuni a kan haka. Saboda Allah ya tabbatar
a cikin Ayar Baqara cewa; ba zai kama masu mantuwa da kuskure da laifi ba, a
cikin Ayar sai ya hada mantuwa da kuskure. Saboda aikata laifi a aikin Hajji da
Sallah a halin kuskure dadai yake da wanda ya aikata cikin mantuwa. Kuma ya
tabbata a Hadisi ingantacce; Sahabbai sun sha ruwa a zamanin Annabi (saw) sai
rana ta bayyana, kuma babu wanda ya umurce su da ramuko. Haka ya tabbata a
Hadisi ingantacce; wasu daga cikin Sahabbai sun kasance suna ci da sha har sai
farin zare ya banbanta daga bakin zare, bayan Alfijir ya fito har gari ya yi
haske sosai, amma Annabi (saw) bai umurce su da ramuko ba, saboda wadannan
jahilai ne masu kuskure. Haka ya tabbata daga Umar bn Khaddab (ra) ya sha ruwa
sai rana ta bayyana, sai ya ce: babu ramuko a kanmu, saboda ba mu da zunubi.
A dunkule; wannan fahimta
ita ta fi karfi ta hanyar Hadisi da kafa hujja da nazari kuma ta fi dacewa da
dalilan Alkur'ani da Sunna da Kiyasi. Da shi zai bayyana cewa; abin da yake
kiyasi game da mai mantuwa shi ne; Azuminsa bai baci ba, saboda ka'idar da
Alkur'ani da Sunna suka yi nuni a kanta ita ce: duk wanda ya aikata abin da aka
yi hani a kansa cikin mantuwa to bai aikata laifi, don haka ibadarsa ba za ta
baci ba, kuma babu banbanci tsakanin saduwa da iyali da waninsa na ci da sha,
sawa'un a cikin Haramin Hajji ne ko Azumi".
Saboda haka, duk abin da aka
yi bisa kuskure ko mantuwa a cikin Azumi, na ci ko sha ba ya bata Azumi, ko da
kuwa saduwa da iyali ne, kamar yadda ya gaba a jiya.
Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)
FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR
IBNU TAIMIYYA (6)
Mutane sun kasu kashi biyu
wajen karya Azuminsu:
1- Akwai mai ganganci.
Wannan dole ya rama Azumin da ya karya, in kuma saduwa ne (jima'i) dole ya yi
kaffara bayan ya yi ramuko.
2- Akwai mai kuskure, ko
mantuwa, ko rashin sani (jahilin da bai san hukunci ba ko bai san yadda ake yi
ba). Wannan babu ramuko in ya karya Azuminsa bisa kuskure, ko mantuwa ko rashin
sani balle kuma kaffara.
Wasu Malaman sun
banbanta tsakanin mai manyuwa da jahili maras sani wajen karya Azumi. Al-Imam
Ibnul Qayyim ya ce:
قستم
الجاهل على الناسي في عدة مسائل وفرقتم بينهما في مسائل أخر، ففرقتم بينهما فيمن
نسي أنه صائم فأكل أو شرب لم يبطل صومه، ولو جهل فظن وجود الليل فأكل أو شرب فسد
صومه، مع أن الشريعة تعذر الجاهل كما تعذر الناسي أو أعظم؟ كما عذر النبي -صلى
الله عليه وسلم- المسيء في صلاته بجهله بوجوب الطمأنينة فلم يأمره بإعادة ما مضى...
وعذر
عدي بن حاتم بأكله في رمضان حين تبين له الخيطان اللذان جعلهما تحت وسادته ولم
يأمره بالإعادة
إعلام
الموقعين (3/ 10)
"Kun yi kiyasin jahili
maras sani a kan mai mantuwa a mas'aloli da yawa, amma sai kuma kuka raba
tsakaninsu a wasu mas'alolin, sai kuka raba tsakaninsu a mas'alar mai Azumi
idan ya manta ya ci abinci ko ya sha abin sha, kuka ce: Azuminsa bai baci ba,
amma sai kuka ce: idan bai sani ba, sai ya yi zaton akwai sauran dare, sai ya
ci ko ya sha Azuminsa ya baci, alhali Shari'a tana yin uzuri ga jahili kamar
yadda take yi wa mai mantuwa ko ma fiye da haka, kamar yadda Annabi (saw) ya yi
uzuri ga wanda ya munana Sallarsa saboda ya jahilci wajabcin nitsuwa a cikin
Sallah, sai bai umurce shi da ramukon Sallolinsa na baya ba...
Haka kuma Annabi (saw) ya yi
uzuri ga Adiyyi bn Hatim (ra) a kan cin abinci da ya yi a Ramadhan har sai da
gari ya waye wartal, har sai da ya iya banbance tsakanin farin zare daga bakin
zare, wadanda ya sanya su a karkashin filonsa, amma Annabi (saw) bai umurce shi
da ramuko ba".
Saboda haka jahili mai halin
rashin sani dadai yake da mai kuskure ko mantuwa a wajen karya Azumi, duka babu
ramuko a kansu. Wannan shi ne zabin Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya kamar yadda
Almajirinsa Al-Imam Ibnul Qayyim ya hakaito inda ya ce:
تناقضوا
كلهم في جعل الناسي في الصوم أولى بالعذر من الجاهل، ففطروا الجاهل دون الناسي،
وسوى شيخنا بينهما، وقال: الجاهل أولى بعدم الفطر من الناسي
إعلام
الموقعين (5/ 506)
"Masu Qiyasi gaba
dayansu sun yi tufka da warwara ta yadda suka sanya mai mantuwa a Azumi shi ya
fi cancantar uzuri feye da jahili mai rashin sani, sai suka ce: Azumin jahili
ya baci, amma in mai mantuwa ne Azuminsa bai baci ba. Amma Shehinmu (Ibnu Taimiyya)
ya daidaita tsakaninsu, ya ce: Jahili shi ya fi cancantar a ce: Azuminsa bai
baci ba fiye da mai mantuwa".
Saboda haka duk wanda ya
karya Azuminsa saboda mantuwa ko kuskure ko rashin sani to babu ramuko ko
kaffara a kansa, kawai zai ci gaba da Azuminsa ne, Azuminsa yana nan bai baci
ba. A kan haka Shaikhul Islami ya ce:
قد
ثبت بدلالة الكتاب والسنة أن من فعل محظورا مخطئا أو ناسيا لم يؤاخذه الله بذلك
وحينئذ يكون بمنزلة من لم يفعله فلا يكون عليه إثم ومن لا إثم عليه لم يكن عاصيا
ولا مرتكبا لما نهي عنه وحينئذ فيكون قد فعل ما أمر به ولم يفعل ما نهي عنه. ومثل
هذا لا يبطل عبادته إنما يبطل العبادات إذا لم يفعل ما أمر به أو فعل ما حظر عليه.
مجموع
الفتاوى (25/ 226)
"Ya tabbata da dalilan
Alkur'ani da Sunna cewa; duk wanda ya aikata wani abu da aka hana a halin
kuskure ko mantuwa to Allah ba zai kama shi a kan haka ba, a wannan halin zai
zama kamar bai aikata laifin ba, don haka babu zunubi a kansa, duk wanda babu
zunubi a kansa kuwa to shi ba mai sabo ba ne, ko bai zama wanda ya aikata abin
da aka hana ba. To a wannan lokaci sai ya kasance ya aikata abin da aka umurce
shi, bai aikata abin da aka hana shi ba. Irin wannan kuwa ibadarsa ba ta baci,
kawai ibada tana baci ne ne idan mutum bai aikata abin da aka umurce shi ya
aikata ba, ko kuma in ya aikata abin da aka hana shi aikatawa".
Lallai wannar ka'ida ce ta
Shari'a mai girma wajen hukunci wa mutane da aiyukansu, rashin sanin irin
wannar ka'ida ne yake jefa jahilai da masu guluwwi cikin kuskure wajen
hukuncinsu ga mutane ko a kan aiyukansu.
Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.