Ticker

6/recent/ticker-posts

Fikihun Azumi Daga Makarantar Ibn Taimiyya (Kashi Na Biyu Da Na Uku)

FIQHUN AZUMI DAGA MAKARANTAR IBNU TAIMIYYA (2)

Malamai sun yi sabani a kan yin k'aho da tsaga da zane ga mai Azumi, wasu sun ce Azumin wanda aka yi masa k'ahon da na wanzamin ya baci, wasu sun ce; a'a, bai baci ba. Amma Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ya rinjayar da bacin Azumin wanda aka yi masa k'aho da na wanzamin, da kuma na wanda aka yi masa tsaga ko zane da aska a jikinsa.

Al-Imam Ibnul Qayyim da Ibnu Muflih sun hakaito hakan daga gare shi. Ibnul Qayyim ya ce:

الصواب الفطر بالحجامة والفصاد والتشريط وهو اختيار شيخنا أبي العباس بن تيمية

تهذيب السنن (6/ 368)

"Magana ta dadai; Azumi yana baci in an yi k'aho ko tsaga ko zane a jikin mai Azumi, kuma shi ne zabin Shehinmu Abul Abbas Ibnu Taimiyya".

Ga nan inda Shaikhul Islamin ya yi bayani kamar haka:

وَقَدْ بَيَّنَّا أَنَّ الْفِطْرَ بِالْحِجَامَةِ عَلَى وَفْقِ الْأُصُولِ وَالْقِيَاسِ

Mun yi bayanin cewa; k'aho kuma lallai

 yana karya Azumi bisa ka'idojin Shari'a da Qiyasi,

 وَأَنَّهُ مِنْ جِنْسِ الْفِطْرِ بِدَمِ الْحَيْضِ وَالِاسْتِقَاءَةِ وبالاستمناء.

" yana cikin jinsin bacin Azumi saboda jinin haila ne, da jawo amai, da jawo fitan maniyyi.

 وَإِذَا كَانَ كَذَلِكَ فَبِأَيِّ وَجْهٍ أَرَادَ إخْرَاجَ الدَّمِ أَفْطَرَ كَمَا أَنَّهُ بِأَيِّ وَجْهٍ أَخْرَجَ الْقَيْءَ أَفْطَرَ سَوَاءٌ جَذَبَ الْقَيْءَ بِإِدْخَالِ يَدِهِ أَوْ بِشَمِّ مَا يُقَيِّئُهُ أَوْ وَضَعَ يَدَهُ تَحْتَ بَطْنِهِ وَاسْتَخْرَجَ الْقَيْءَ فَتِلْكَ طُرُقٌ لِإِخْرَاجِ الْقَيْءِ وَهَذِهِ طُرُقٌ لِإِخْرَاجِ الدَّمِ وَلِهَذَا كَانَ خُرُوجُ الدَّمِ بِهَذَا وَهَذَا سَوَاءً فِي

[ابن تيمية ,مجموع الفتاوى ,25/257]

 In haka ne, ta kowace hanya idan mutum ya fitar da jini daga jikinsa to Azuminsa ya karye, kamar yadda ta kowace hanya in ya fitar da amai Azuminsa ya karye, sawa'un ya jawo aman ne ta hanyar sanya yatsa a baki, ko ya shanshana abin da zai jawo masa amai, ko ya sanya hanunsa a kasan cikinsa ya turo aman, wadancan su ne hanyoyin jawo amai. Wadannan kuma hanyoyin fitar da jini (k'aho, tsaga da zane), wadannan kuwa duka dadai suke a Babin Tsarki".

Shi ma wanzami mai yin k'ahon Azuminsa yana baci saboda yana zuk'an jinin da bakinsa. Ya ce:

وأما الحاجم فإنه يجتذب الهواء الذي في القارورة بامتصاصه والهواء يجتذب ما فيها من الدم فربما صعد مع الهواء شيء من الدم ودخل في حلقه وهو لا يشعر...

وأما الشارط فليس بحاجم وهذا المعنى منتف فيه فلا يفطر الشارط

مجموع الفتاوى (25/ 257 - 258)

"Amma shi wanzami mai yin k'aho, yana zuk'an iskan da yake cikin k'ahon nasa, ta hanyar tsotsa, da kuma iskan da yake zuk'an abin da ke cikinsa na jini, ta yiwu wani abu na jinin ya tafi da iskan da ya zuk'a ya shiga mak'ogwaronsa alhali bai sani ba…

Amma shi mai yi wa mutane tsaga ba kamar mai yin k'aho ba ne, shi ba a samun zuk'an jini da baki a tsaga, don haka shi Azuminsa ba ya baci".

Saboda haka, wanzami mai yin k'aho Azuminsa yana baci, amma mai yin tsaga da zane shi Azuminsa ba ya baci. Haka wanda aka yi masa daya daga cikin wadannan; k'aho, tsaga ko zane to Azuminsa ya baci.

Dr Aliyu Muh'd Sani  (Hafizahullah)

Fiqhun azumi daga makarantar ibnu taimiyya (3)

wanda ya yi "istimna'i" ya fitar da maniyyi da hanunsa ko da wani abun, azuminsa ya baci. a baya an yi ishara a kan wannan.

wanda maziyyi ya fito masa saboda kallon mace ko abin da ya yi kama da haka azuminsa bai baci ba. al-ba'aliy a cikin "ikhtiyaraatu shaikhil islam ibnu taimiyya" ya ce:

ولا يفطر بمذي سببه قبلة، أو لمس، أو تكرار نظر، وهو قول أبي حنيفة والشافعي، وبعض أصحابنا.

الاختيارات للبعلي (160)

"azuminsa ba zai karye ba saboda fitan maziyyi, imma saboda sunbanta ko shafan mace ko maimaita kallonta. wannan shi ne fadin abu hanifa da shafi'iy da wasu a cikin hanabila".

ibnu muflih ya ce:

وإن مذى بذلك أفطر أيضا، نص عليه "وم" واختار الآجري وأبو محمد الجوزي وأظن وشيخنا: لا يفطر، وهو أظهر "وهـ ش" عملا بالأصل، وقياسه على المني لا يصح، لظهور الفرق.

الفروع وتصحيح الفروع (5/ 10)

"in maziyyi ya fito masa saboda runguma to azuminsa ya baci...

amma shaihinmu (ibnu taimiyya) ya ce: azuminsa bai baci ba, kuma wannan shi ne mafi inganci (shi ne fadin abu hanifa da shafi'iy), saboda aiki da asali. amma yin kiyasin maziyyi a kan maniyyi abu ne da bai inganta ba, saboda akwai banbanci tsakaninsu".

saboda haka fitar da maniyyi da gangan yana karya azumi, amma fitan maziyyi saboda kallon mace ko magana da ita, ko wani abun daban ba ya karya azumi.

amma fa kar mu manta, akwai abubuwa da ba sa karya azumi amma kuma suna rage ladan azumin. don haka kar mu manta da babbar manufar azumi, wato samar da taqwa.

Dr aliyu muh'd sani (hafizahullah)

Fikihun Azumi


Post a Comment

0 Comments