Ticker

6/recent/ticker-posts

Littattafan Hausa Na Sayarwa

Masu buƙatar waɗannan littattafai suna iya tuntuɓa:

WhatsApp: 08133529736

Email: abuubaidasani5@gmail.com

JERIN LITTATTAFAN DA MUKE DA SU
Littattafan Hausa Na Sayarwa

Aure a Ƙunshiyar Karin Magana

Littafi: Aure a Ƙunshiyar Karin Magana

Adadin Shafuka: 208

Tsokaci: Wannan littafin ya kawo al'adun aure daban-daban na Hausa daga madubin karin magana. Ya shafi zamantakewar aure da taurarin gidan aure kamar ango da amarya da uwar miji da kishiya da sauransu.

Cimakar Hausawa

Littafi: Cimakar Hausawa

Adadin Shafuka: 418

Tsokaci: Wannan littafin ya kawo bayanai game da abinci, tun daga kan ma'ana har zuwa tushen abincin Hausawa. Haka kuma, ya dubi muhimman batutuwa da suke da alaƙa da abinci, kamar batun "yunwa" da sauransu. Ya kawo bayanai game da nau'ukan abincin Hausawa na gargajiya da na zamani sama da ɗari biyu (200). Ya kuma kawo tsokaci dangane da tasirin zamani a kan abincin Hausawa.

Damfara a Duniyar Intanet

Littafi: Damfara a Duniyar Intanet

Adadin Shafuka: 256

Tsokaci: Wannan littafin ya kawo bayanai game da nau'ukan damfara daban-daban musamman waɗanda ake yi a zamanin yau da taimakon intanet da na'urori. Waɗanda suke hawa kan intanet (musamman masu kasuwanci a kan intanet) sun fi fuskantar barazanar faɗawa homar 'yan damfarar zamani. Littafin ya kawo bayanai game da matakan kare kai daga faɗawa tarkon 'yan damfara.

Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Littafi: Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Adadin Shafuka: 635

Tsokaci: Wannan littafin ya kawo tarihin Aminu Ladan Abubakar (ALAn Waƙa) a faɗaɗe. Ya kuma kawo jerin waƙoƙinsa a ƙarƙashin rukunoni daban-daban. Sun haɗa da waƙoƙin faɗakarwa da na siyasa da na soyayya da na sauransu.

Fasihiya Binta Labaran (Fati Nijar Da Waƙoƙinta)

Littafi: Fasihiya Binta Labaran (Fati Nijar Da Waƙoƙinta)

Adadin Shafuka: 355

Tsokaci: Wannan littafi ya kawo tarihin Hajiya Fati Nijar. Haka kuma, ya kawo jerin waƙoƙin fasihiyar a ƙarƙashin rukunoni daban-daban. Sun haɗa da waƙoƙin siyasa da na soyayya da na sarauta da sauransu.

Hausa Da Hausawa a Duniyar Intanet

Littafi: Hausa Da Hausawa a Duniyar Intanet

Adadin Shafuka: 171

Tsokaci: Wannan littafin ya kawo bayanai game da yaɗuwa da bunƙasar adabi da harshe da al'adun Hausawa a cikin duniyar intanet. Haka kuma, ya kawo ƙalubale da hakan yake haifarwa ta fuskoki daban-daban tare da tattauna hanyoyin shawo kansu.

Hausa Names and Naming Traditions

Littafi: Hausa Names and Naming Traditions 

Adadin Shafuka: 316

Tsokaci: Wannan littafin ya kasance fassara da faɗaɗawa na littafin Hausa mai suna "Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa Da Maƙwabtansu)." Littafin ya kawo bayanai game da suna da tarihin samuwar suna a duniya. Haka kuma, ya kawo bayanai masu faɗi game da sunayen Hausawa, ciki har da dalilan samuwar sunayen da ma'anoninsu. Bugu da ƙari, littafin ya tattauna sunayen Fulani da Barebare a ƙoƙarinsa na bayanin sunayen da Hausawa suka ara daga waɗannan maƙwabta nasu. Littafin ba fassara ba ne kawai, an faɗaɗa bayanan da aka kawo a cikin takwaransa na Hausa.

Sunayen Hausawa

Littafi: Sunayen Hausawa

Adadin Shafuka: 140

Tsokaci: Littafin ya kawo bayanai game da suna da tarihin samuwar suna a duniya. Haka kuma, ya kawo bayanai masu faɗi game da sunayen Hausawa, ciki har da dalilan samuwar sunayen da ma'anoninsu. Bugu da ƙari, littafin ya tattauna sunayen Fulani da Barebare a ƙoƙarinsa na bayanin sunayen da Hausawa suka ara daga waɗannan maƙwabta nasu. An fassara wannan littafin cikin harshen Ingilishi. Littafin Ingilishin yana da suna "Hausa Names and Naming Traditions." 

Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa'idojin Rubutun Hausa

Littafi: Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa'idojin Rubutun Hausa

Adadin Shafuka: 171

Tsokaci: Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya waƙe ƙa'idojin rubutun Hausa, tun daga kan baƙaƙe da wasulla, har zuwa ƙa'idojin haɗawa da raba rubutun Hausa. Marubuta wannan littafin sun yi tahamisin littafin Farfesa.

Waƙoƙin Hausa na Gargajiya

Littafi: Waƙoƙin Hausa na Gargajiya

Adadin Shafuka: 237

Tsokaci: Wannan littafi ya kawo bayani game da waƙoƙin gargajiya tun daga kan bitar tarihin samuwarsu, har zuwa amfani daban-daban na waƙoƙin gargajiya ga Hausawa. Haka kuma, littafin ya kawo misalai a ƙarƙashin rukunonin waƙoƙin gargajiya daban-daban. A ciki har da waƙoƙin reno da na cikin tatsuniyoyi da na bara da na roƙon ruwa da na ayyuka (daɓe da daka da niƙa) da sauransu.

Littafi: Wasanni a Ƙasar Hausa

Adadin Shafuka: 591

Tsokaci: Wannan littafin ya kawo bayanai game da wasannin gargajiya na Hausawa. An kawo rabe-raben wasannin ta fuskoki daban-daban. Daga nan an tattauna misalan wasanni ɗari biyu da goma sha huɗu (214). Bugu da ƙari, an tattauna tasirin zamani a kan wasannin.

Wasannin Kwaikwayo na Hausawa (WAEC Text)

Littafi: Wasannin Kwaikwayo na Hausawa (WAEC Text)

Adadin Shafuka: 176

Tsokaci: Wannan littafin ya kawo bayanai da misalan wasannin kwaikwayo na gargajiya na Hausawa. Sun haɗa da wasannin tashe da wasu daga cikin wasannin dandali. WAEC ta zaɓi littafin tare da sanya shi a cikin manhajar karatu.












Post a Comment

0 Comments