Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar'anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.
Tsira da amincin Allah su tabbata
ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari'a mai
sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
Bayani a kan kashi na bakwai ya
gabata, ga cigaba kamar haka:
Kashi na takwas:
Mace mai haila: haramun ne mace mai jinin
al'ada ta yi Azumi, kuma ko ta yi bai inganta ba, saboda Annabi (saw) ya ce:
مَا رَأَيْتُ مِنْ نَاقِصَاتِ عَقْلٍ وَدِينٍ
أَذْهَبَ لِلُبِّ الرَّجُلِ الحَازِمِ مِنْ إِحْدَاكُنَّ»، قُلْنَ: وَمَا نُقْصَانُ
دِينِنَا وَعَقْلِنَا يَا رَسُولَ اللَّهِ؟ قَالَ: «أَلَيْسَ شَهَادَةُ المَرْأَةِ
مِثْلَ نِصْفِ شَهَادَةِ الرَّجُلِ» قُلْنَ: بَلَى، قَالَ: «فَذَلِكِ مِنْ نُقْصَانِ
عَقْلِهَا، أَلَيْسَ إِذَا حَاضَتْ لَمْ تُصَلِّ وَلَمْ تَصُمْ» قُلْنَ: بَلَى، قَالَ:
«فَذَلِكِ مِنْ نُقْصَانِ دِينِهَا»
[البخاري ,صحيح البخاري
,1/68]
((Ban ga masu tauyayyen hankali da Addini mai
jan hankalin tsayayyen namiji kamar daya daga cikinku ba". Sai suka ce:
Menene tawayan hankali da Addinin namu ya Manzon Allah? Sai ya ce: "Shin
shaidar mace ba rabin na namiji ba ne?" suka ce: Eh haka ne. Ya ce:
"To wannan shi ne tawayan hankalinsu. Kuma shin ba tana barin Sallah da
Azumi ba idan tana jinin haila?", suka ce: Eh tana bari. Ya ce: "To
wannan shi ne tawayan Addininsu")). Bukhari (304) Muslim (79).
Idan jinin haila ya zo wa mace
alhali tana Azumi, ko da kusa da faduwar rana ce da minti daya, to Azuminta na
wannan rana ya baci, ramuko ya kama ta, sai dai idan Azumin nafila ne,
ramukonsa ba wajibi ba ne.
Haka idan ta yi tsarki daga haila
da rana a Ramadhan ba ta da Azumin wannan rana. Amma shin za ta kame baki? Amsa
a kan haka ya gabata a bayanin hukuncin matafiyin da ya dawo gida da rana.
Jamhurin Malamai sun tafi a kan cewa; ba wajibi ba ne.
Idan kuma ta yi tsarki cikin
dare, ko da kafin al-fijr da minti daya ne to Azumi ya wajaba a kanta. Za ta
dauki Azumi ko da ba ta samu daman yin wanka ba, sai bayan fitowan al-fijr.
Hukuncinta kamar hukuncin mai janaba ne, ya tabbata daga A'isha (ra) ta ce:
«أَشْهَدُ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِنْ كَانَ لَيُصْبِحُ جُنُبًا مِنْ جِمَاعٍ غَيْرِ
احْتِلاَمٍ، ثُمَّ يَصُومُهُ»،
[البخاري ,صحيح البخاري
,3/31]
((Annabi (saw) ya kasance yana
wayan gari yana mai janaba, saboda saduwa da iyali, kuma ya dauki Azumi)).
Bukhari (1931) Muslim (1109).
Mai jinin haila wajibi ne ta rama
Azumin ranakun da ba ta yi Azumi ba saboda zuwan jinin, an tambayi A'isha (ra):
Me ya sa mai haila take rama Azumi, amma ba ta rama Sallah? Sai ta ce:
«كَانَتْ إِحْدَانَا تَحِيضُ
عَلَى عَهْدِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، ثُمَّ لَا تُؤْمَرُ بِقَضَاءٍ»
[مسلم، صحيح مسلم، ٢٦٥/١]
((Hakan yana faruwa da mu sai a
umurce mu da mu rama Azumi, amma ba a umurtanmu da rama Sallah)). Muslim (335).
Mai jinin biki hukuncinta kamar
mai jinin haila ne, cikin dukkan hukunce-hukunce da suka gabata.
Kashi na tara:
Mace mai shayarwa: idan mace ta
kasance mai shayarwa ko mai ciki, sai ta ji tsoron za ta cutu idan ta yi
Azumin, ko kuma dan nata zai cutu, to ya halasta ta sha Azumin, saboda Hadisin
Anas bn Malik (ra), Annabi (saw) ya ce:
إِنَّ اللَّهَ تَعَالَى وَضَعَ عَنِ الْمُسَافِرِ
الصَّوْمَ، وَشَطْرَ الصَّلاَةِ،
[الترمذي، محمد بن عيسى، سنن
الترمذي ت بشار، ٨٦/٢]
((Allah ya dauke wa mai Matafiyi
rabin Sallah, ya dauke Azumi wa matafiyi da mai ciki da mai shayarwa)). Abu
Dawud (2408), Tirmiziy (715), Nasa'iy (2275), Ibnu Majah (1667).
Don haka ya halasta ta sha Azumi,
kuma wajibi ne ta rama ranakun da ta sha.
Kashi na goma:
Mabukaci zuwa ga shan Azumi:
wanda ya bukaci shan Azumi saboda wata larura, kamar tsamar da wanda ya nitse a
ruwa, ko kubutar da wanda gobara ta ritsa da shi, ko wanda gini ya rushe a
kansa, ko wanda ya makale a sama, ko ya fada rijiya, ko taimakon masu hatsarin
mota da makamantan haka, idan ya zama ba zai iya kubutar da dayan wadannan ba
har sai ya ci abinci ko shan ruwa, don ya samu karfin jiki to ya halasta ya sha
Azumin, ya ma wajaba, don kubutar da wanda ya fada cikin halaka wajibi ne. Kuma
ya wajaba ya rama Azumin.
Haka sojojin Muslunci da suke
wajen Jihadi saboda Allah, wajen yakar abokan gaban Musulmai, ya halasta su sha
Azumi don su samu karfin yin Jihadi, kuma za su rama. Saboda Hadisin da ya
abbata daga Abu Sa'eed (ra) ya ce:
سَافَرْنَا مَعَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِلَى مَكَّةَ وَنَحْنُ صِيَامٌ، قَالَ: فَنَزَلْنَا مَنْزِلًا،
فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّكُمْ قَدْ دَنَوْتُمْ
مِنْ عَدُوِّكُمْ، وَالْفِطْرُ أَقْوَى لَكُمْ» فَكَانَتْ رُخْصَةً، فَمِنَّا مَنْ
صَامَ، وَمِنَّا مَنْ أَفْطَرَ، ثُمَّ نَزَلْنَا مَنْزِلًا آخَرَ، فَقَالَ: «إِنَّكُمْ
مُصَبِّحُو عَدُوِّكُمْ، وَالْفِطْرُ أَقْوَى لَكُمْ، فَأَفْطِرُوا» وَكَانَتْ عَزْمَةً،
فَأَفْطَرْنَا،
[مسلم، صحيح مسلم، ٧٨٩/٢]
((Mun yi tafiya tare da Manzon Allah (saw)
zuwa Makka, alhali muna Azumi, sai muka sauka a wani wajen, sai Manzon Allah
(saw) ya ce: "Hakika kuna kusa da abokan gabanku, shan Azumi zai ba ku
karfin jiki", wannan rangwame ne, a cikinmu akwai wadanda suka yi Azumi,
akwai kuma wadanda suka sha Azumin. Sai muka sake sauka a wani wajen, sai
Manzon Allah (saw) ya ce: "Lallai za ku dirar ma abokan gabanku da safe,
shan Azumi zai ba ku karfin jiki, don haka ku sha Azumi", wannan sai ya
zama umurni na dole, sai duka muka sha Azumin)). Muslim (1120).
Wannan Hadisi yana nuni ga cewa;
samun karfin yakar abokan gaba shi ma sababi ne mai cin gashin kansa da zai sa
a sha Azumi, ba dole sai da sababin tafiya ba.
Dukkan wanda ya halasta ya sha
Azumi cikin wadanda ambatonsu ya gabata to wajibi ne ya rama Azumin kwanakin da
ya sha Azumin Ramadhan. Wanda ya sha watan gaba dayansa, zai rama watan. Idan
watan kwana talatin ya yi Azumi talatin zai rama, haka idan ishirin da tara ya
yi.
Ana so mutum ya gaggauta rama
Azumin Ramadhan da yake kansa, kar ya jinkirta shi har watan Sha'aban idan ba
tare da uzuri ba. Ya tabbata daga A'isha (ra) ta ce:
«كَانَ يَكُونُ عَلَيَّ الصَّوْمُ مِنْ رَمَضَانَ،
فَمَا أَسْتَطِيعُ أَنْ أَقْضِيَ إِلَّا فِي شَعْبَانَ»،
[البخاري، صحيح البخاري،
٣٥/٣]
((Azumin Ramadhan yakan kasance a
kaina, amma ba na iya ramawa har sai a Sha'aban, saboda shagaltuwa da hidima wa
Manzon Allah (saw))). Bukhari (1950), Muslim (1146).
قَالَ يَحْيَى: الشُّغْلُ مِنَ النَّبِيِّ أَوْ
بِالنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
Amma idan uzurin bai gushe ba,
har mutuwa ta riske shi, to babu komai a kansa. Amma idan sakaci ya yi,
danginsa sai su rama masa, saboda ya tabbata Annabi (saw) ya ce:
«مَنْ مَاتَ وَعَلَيْهِ صِيَامٌ
صَامَ عَنْهُ وَلِيُّهُ»،
[البخاري، صحيح البخاري،
٣٥/٣]
((Duk wanda ya mutu akwai Azumi a
kansa majibintansa su rama masa)). Bukhari (1952) Muslim (1147).
Wadannan su ne kashe-kashen
mutane a cikin Azumi, Shari'a ta zo da hukuncin kowa gwargwadon yanayi da halin
da yake ciki, saboda rahma da hikima da suke cikin Shari'ar Allah Mai hikima da
rahma. Don haka sai mu gode wa Allah a kan haka, mu roke shi
tabbatuwa a kan bin Shari'arsa da yi masa da'a
don neman yardarsa.
Allah ya karba mana, ya gafarta
mana zunubanmu, ya jikan iyayenmu, ya kyautata karshenmu, ya ba mu zaman
lafiya, ya yi mana maganin matsalolin tattalin arziki da na tsaro da muke fama
da su a kasarmu.
Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.