Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar'anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.
Tsira da amincin Allah su tabbata
ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari'a mai
sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
Alal hakika Ibada da Allah ya
umurce mu da yinta, kuma ya halicce mu don ita tana da hikimomi masu yawan
gaske, da fa'idoji masu amfani na zahiri da na ma'ana, saboda Allah Madaukaki
mai ilmi ne, kuma mai hikima ne, don haka ya zama akwai hikima cikin halittarsa
da Shari'arsa; na umurni da hani, da ibadu da ya wajabta ma bayi.
Shar'anta Azumi, da farlanta
Azumin Ramadhan yana da hikimomin masu yawa, wadanda suka sa Azumin ya zama
cikin Rukunan Muslunci.
Azumi ibada ce da take kusatar da
bawa ga Ubangijinsa, ta hanyar hana ransa abubuwan da take so na abinci da abin
sha da biyan sha'awarsa ta saduwa, saboda abin da Ubangijinsa yake so, a cikin
haka gaskiyar imaninsa yake bayyana, da cikar bautarsa ga Ubangijinsa, da
karfin soyayyarsa gare shi. Saboda mutum ba ya barin abin da yake so sai saboda
abin so wanda ya fi wancan girma. Shi Mumini a lokacin da ya san ana samun
yardar Allah a Azumi, sai ya fifita samun yardar Allah a kan abin da ransa yake
so, sai ya bar abin da ransa yake so don ya aikata abin da Allah yake so.
Daga cikin hikimomin farlanta
Azumin, shi sababi ne na samun Taqwa da tsoron Allah, Allah ya ce:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ
الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ
{Ya ku wadanda suka yi Imani, an
wajabta muku Azumi kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suka gabace ku,
don ku samu tsoron Allah} [al-Baqara: 183].
Saboda haka ne mai Azumi aka
umurce shi da aikata aiyukan da'a, da nesantar sabo da aiyukan zunubi, Annabi
(saw) ya ce:
«مَنْ لَمْ يَدَعْ قَوْلَ الزُّورِ
وَالعَمَلَ بِهِ وَالجَهْلَ -[18]-، فَلَيْسَ لِلَّهِ حَاجَةٌ أَنْ يَدَعَ طَعَامَهُ
وَشَرَابَهُ»
[البخاري ,صحيح البخاري
,8/17
((Duk wanda bai bar fadin karya
da aiki da ita ba, da aikin jahilci to Allah ba ya bukatar ya bar cin abincinsa
da abin shansa)). Bukhari (6057).
Shi Mumini mai Azumi, da zaran ya
yi tunanin aikata sabo sai ya tuna cewa; yana Azumi, sai ya bari, shi ya sa
Annabi (saw) ya umurci mai Azumi, idan wani ya zage shi, ko ya neme shi da
fada, to ya ce: ni mai Azumi ne.
Daga cikin hikimar farlanta
Azumi, tunanin mutum da zuciyarsa za su shagala da amboton Allah da tuna Allah,
saboda ta rabu da abubuwan sha'awa da suke dauke hankali, na ci da sha da
saduwa, wadanda suke makantar da zuciya, shi ya sa Annabi (saw) ya koyar da
sassauta cin abinci, inda ya ce:
مَا مَلأَ آدَمِيٌّ وِعَاءً شَرًّا مِنْ بَطْنٍ.
بِحَسْبِ ابْنِ آدَمَ أُكُلاَتٌ يُقِمْنَ صُلْبَهُ، فَإِنْ كَانَ لاَ مَحَالَةَ فَثُلُثٌ
لِطَعَامِهِ وَثُلُثٌ لِشَرَابِهِ وَثُلُثٌ لِنَفَسِهِ.
[الترمذي، محمد بن عيسى، سنن
الترمذي ت بشار، ١٦٨/٤]
((Dan'adam bai cika mazubi mafi sharri kamar
cikinsa ba. 'Yan lomomi sun ishi dan'adam wadanda za su tsayar masa da bayansa,
idan ya zama dole to ya kasa cikin kashi uku, daya na abincinsa, daya na abin
shansa, daya na numfashinsa)). Tirmiziy (2380), Ibnu Majah (3349).
Daga cikin hikimar farlanta
Azumi, mawadaci zai san girman ni'imar Allah a kansa, ta yadda ya wadata shi da
abinci da abin sha da aure, alhali da yawa sun rasa wannar ni'ima. Don haka sai
ya gode ma Allah a kan wannar ni'ima, kuma zai tuna 'yan'uwansa talakawa
wadanda suke kwana cikin yunwa, sai ya taimaka musu da sadaka da kyauta, ya ba
su abinci da abin sha da tufafi. Wannan ya sa Annabi (saw)
: «كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَجْوَدَ النَّاسِ بِالخَيْرِ، وَأَجْوَدُ مَا يَكُونُ فِي شَهْرِ
رَمَضَانَ، لِأَنَّ جِبْرِيلَ كَانَ يَلْقَاهُ فِي كُلِّ لَيْلَةٍ فِي شَهْرِ رَمَضَانَ،
حَتَّى يَنْسَلِخَ يَعْرِضُ عَلَيْهِ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
القُرْآنَ، فَإِذَا لَقِيَهُ جِبْرِيلُ كَانَ أَجْوَدَ بِالخَيْرِ مِنَ الرِّيحِ المُرْسَلَةِ»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٨٦/٦]
ya fi kyauta a Ramadhan fiye da
kowane lokaci, ya fi yin kyautan a lokacin da Jibril (as) yake haduwa da shi
suna darasin Alkur'ani, kamar yadda ya tabbata a Hadisin Ibnu Abbas, duba
Bukhari (4997), Muslim (2308).
Daga cikin hikimar farlanta
Azumi, hanyoyin jini a jikin mutum suna kuntacewa saboda yunwa da kishirwa, sai
hanyoyin gudanar Shaidan a jikin mutum su kuntace, saboda yana gudana ne a
magudanan jini, kamar yadda ya tabbata daga Annabi (saw) ya ce:
فَإِنَّ الشَّيْطَانَ يَجْرِي مِنَ ابْنِ آدَمَ
مَجْرَى الدَّمِ
[البخاري، صحيح البخاري،
٥٠/٣]
((Lallai Shaidan yana gudana a jikin mutum ta
magudanan jini)) Bukhari (2039), Muslim (2174).
sai Azumi ya toshe hanyoyin
wasiwasin Shaidan, ya tare wa mutum hanyoyin motsa sha'awa da tunzuran fushi.
Shi ya sa Annabi (saw) ya ce:
«يَا مَعْشَرَ الشَّبَابِ مَنِ
اسْتَطَاعَ مِنْكُمُ البَاءَةَ فَلْيَتَزَوَّجْ، وَمَنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَعَلَيْهِ
بِالصَّوْمِ فَإِنَّهُ لَهُ وِجَاءٌ»
[البخاري، صحيح البخاري، ٣/٧]
((Ya ku matasa, wanda ya samu ikon aure to ya
yi, saboda yana rintse ido, kuma yana kare farji. Idan kuma bai samu iko ba to
ya lazimci Azumi, don makari ne gare shi)). Bukhari (5065) da Muslim (1400).
Azumi yana da fa'idoji masu yawa,
ta bangaren kiwon lafiya, da kuma bangaren samun karfin rai, da karfin zuciya
da samun tarbiyya ta juriya, da iya hadiye fushi, da kuma tarbiyya a kan
nisantar girman kai da saukin hali, don yawan cin abinci da koshi da yawan
saduwa, yana haifar da munanan dabi'u na alfahari da jiji da kai da girman kai
wa mutane.
Don haka zuciya da rai suna
bukatar ibadu da za su tsarkake su, su sa su zama bayin Allah masu taushi da
kankan da kai ma Allah Madaukaki, Azumi kuma yana daga cikin manyan Ibadu masu
samar da wannar tarbiyya, da tsarkake zukata da gyaran halaye.
Allah ya karba mana Ibadunmu, ya
gafarta mana zunubanmu, ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu
da suke damun kasarmu.
Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.