Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar'anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.
Tsira da amincin Allah su tabbata
ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari'a mai
sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
'Yan'uwa, bayanin kashe-kashe
biyar na hukunce-hukuncen mutane a Azumi ya gabata, ga cigaba da kamar haka:
Kashi na shida:
Matafiyi sawa'un tafiyar mai
tsawo ce ko gajeruwa, tafiya ce mai bijirowa ko tafiya ce ta kullum, kamar ta
direbobin motocin haya, yana da zabin yin Azumi ko shan Azumin, matukar ba ya
yi tafiyar ce da niyyar yin dabara ma Shari'a ba, idan ya yi da niyyan haka ya
aikata haramun. Dalili a kan haka shi ne fadin Allah: {Duk wanda ya kasance
maras lafiya ko yana halin tafiya to ya kirga Azumin a wasu ranakun daban,
Allah yana so muku sauki ba ya so muku wahala}. [al-Baqarah (185)].
Ya tabbata daga Anas bn Malik
(ra) ya ce:
«كُنَّا نُسَافِرُ مَعَ النَّبِيِّ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَلَمْ يَعِبِ الصَّائِمُ عَلَى المُفْطِرِ، وَلاَ
المُفْطِرُ عَلَى الصَّائِمِ»
[البخاري، صحيح البخاري،
٣٤/٣]
((Mun kasance muna tafiya tare da Annabi
(saw), amma mai Azumi ba ya aibanta wa maras Azumi, maras Azumi ba ya aibanta
wa mai Azumi ba)) Bukhari (1947), Muslim (1118).
Abu Sa'eed al-Kudriy yana ba da
labarin Sahabbai sukan fita yaki tare da Annabi (saw), a cikinsu akwai mai
Azumi, akwai maras Azumi, sai ya ce:
يَرَوْنَ
أَنَّ مَنْ وَجَدَ قُوَّةً فَصَامَ، فَإِنَّ ذَلِكَ حَسَنٌ وَيَرَوْنَ أَنَّ مَنْ وَجَدَ
ضَعْفًا، فَأَفْطَرَ فَإِنَّ ذَلِكَ حَسَنٌ»
[مسلم،
صحيح مسلم، ٧٨٧/٢]
((suna ganin wanda ya samu karfin
yin Azumin sai ya yi to abu ne mai kyau,
wanda kuma ya samu raunin yin Azumin sai ya sha Azumin shi ma abu ne mai
kyau)). Muslim (1116).
Abin da ya fi dacewa ga dereban
motar haya wanda Azumi zai yi masa wahala shi ne; idan Azumin a lokacin zafi ne
to sai ya sha Azumin, sai ya rama a lokacin sanyi.
Abin da ya dace ga Matafiyi shi
ne ya yi abin da ya fi masa sauki, imma ya yi Azumin idan ba zai samu rauni ba,
ko kuma ya sha Azumin idan zai yi rauni. Idan kuma duka daya ne a gare shi to
abin da ya fi ya yi Azumin, saboda idan ya yi ya sauke nauyin da ke wuyansa,
kuma ya yi Azumi tare da mutane, zai fi samun nishadi, saboda hakan shi ne
aikin Annabi (saw), kamar yadda ya tabbata daga Abu al-Darda'i ya ce:
«خَرَجْنَا مَعَ رَسُولِ اللهِ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي شَهْرِ رَمَضَانَ فِي حَرٍّ شَدِيدٍ، حَتَّى إِنْ
كَانَ أَحَدُنَا لَيَضَعُ يَدَهُ عَلَى رَأْسِهِ مِنْ شِدَّةِ الْحَرِّ، وَمَا فِينَا
صَائِمٌ، إِلَّا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَعَبْدُ اللهِ بْنُ
رَوَاحَةَ»
[مسلم، صحيح مسلم، ٧٩٠/٢]
((Mun fita tare da Manzon Allah
(saw) a Ramadhan, a cikin tsananin zafi, har ya kai ga dayanmu yana dora
hanunsa a kansa saboda tsananin zafi. Alhali babu mai Azumi a cikinmu sai
Manzon Allah (saw) da Abdullahi bn Rawaha (ra))). Muslim (1122).
Kuma Annabi (saw) ya karya
Azuminsa don saukaka wa Sahabbansa, a lokacin da labari ya same shi cewa;
Azumin ya wahalar da mutane, kamar yadda ya tabbata daga Jabir (ra) ya ce:
أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ خَرَجَ عَامَ الْفَتْحِ إِلَى مَكَّةَ فِي رَمَضَانَ فَصَامَ حَتَّى بَلَغَ
كُرَاعَ الْغَمِيمِ، فَصَامَ النَّاسُ، ثُمَّ دَعَا بِقَدَحٍ مِنْ مَاءٍ فَرَفَعَهُ،
حَتَّى نَظَرَ النَّاسُ إِلَيْهِ، ثُمَّ شَرِبَ،
[مسلم، صحيح مسلم، ٧٨٥/٢]
((Manzon Allah (saw) ya fita zuwa
Makka a shekarar fathu Makka, sai ya dauki Azumi, har sai da ya isa wani waje
da ake kira KURA'U al-GAMEEM, kuma mutane suna Azumi, sai ya sa a kawo masa
kokon ruwa, sai ya daga shi sama, har mutane suka gani, sai ya sha)) Muslim
(1114).
Don haka Matafiyi idan Azumi zai
wahalar da shi to sai ya sha Azumin, kar ya ce zai yi Azumin, saboda Annabi
(saw) ya karya Azuminsa saboda Azumin ya yi wahala wa mutane, amma sai aka ba
shi labarin wasu ba sun yi Azumin, sai ya ce:
«أُولَئِكَ الْعُصَاةُ، أُولَئِكَ الْعُصَاةُ»
[مسلم، صحيح مسلم، ٧٨٥/٢]
((Wadannan su ne masu sabo,
wadannan su ne masu sabo)). Muslim (1114).
A wani Hadisin kuma ya ce:
«لَيْسَ مِنَ البِرِّ الصَّوْمُ
فِي السَّفَرِ»
[البخاري، صحيح البخاري،
٣٤/٣]
((Azumi a cikin tafiya ba ya
cikin da'a ma Allah)). Bukhari (1946), Muslim (1115).
Idan mutum ya taso daga wani gari
zai dawo garinsu, kuma ya sha Azumi saboda tafiya, sai ya iso garinsu da rana,
zai kame baki a wajen wasu Malamai, amma jamhurin Malamai sun tafi a kan ya
halasta gare shi ya ci, ya sha, sai dai bai kamata ya kasance a gaban mutane
ba.
Kashi na bakawai:
Maras lafiyan da ake fatan zai
warke, wannan yana da halaye uku:
Na farko: Idan Azumin ba zai
cutar da shi ba, kuma ba zai wahalar da shi ba to ya wajaba ya yi Azumi.
Na biyu: Idan Azumin zai wahalar
da shi, amma ba zai cutar da shi ba, wannan ya halasta gare shi ya sha Azumin,
sai ya rama idan ya samu sauki, saboda Ayar da ta gabata. Makruhi ne ya yi
Azumi matukar zai wahala, saboda ya samu rangwame daga Allah, Annabi (saw) ya
ce:
" إِنَّ اللهَ يُحِبُّ أَنْ تُؤْتَى رُخَصُهُ،
كَمَا يَكْرَهُ أَنْ تُؤْتَى مَعْصِيَتُهُ
[أحمد بن حنبل ,مسند أحمد ط الرسالة
,10/107]
((Lallai Allah yana so a yi aiki
da ramgwamensa kamar yadda yake kin a aikata sabonsa)). Ahmad (5866), Ibnu
Khuzaimah (2017), Ibnu Hibban (354).
Na uku: Idan Azumin zai cutar da
shi to ya wajaba ya sha Azumin, bai halasta ya yi Azumin ba. Saboda Allah ya
hana jefa kai cikin halaka, kuma Shari'a ba ta zo da wahalarwa ba.
To shi wannan maras lafiya zai yi
lissafin ranakun da ya sha Azumin, idan ya warke sai ya rama su.
Allah ya ba mu lafiya, ya karba
mana ibadunmu a cikin wannan wata mai albarka.
Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.