Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar'anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.
Tsira da amincin Allah su tabbata
ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari'a mai
sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
Azumi yana da Sunnoni
Mustahabbai, wadanda ya kamata mai Azumi ya kiyaye su, don ya samu cikakke lada
a kan Azuminsa, daga cikinsu:
Yin Sahur yana daga cikin
sunnonin Azumi, shi ne mutum ya ci abinci a karshen dare kafin al-fijr. Annabi
(saw) ya yi umurni da haka inda ya ce:
«تَسَحَّرُوا فَإِنَّ فِي السَّحُورِ
بَرَكَةً»
[البخاري ,صحيح البخاري
,3/29]
((Ku yi sahur, saboda akwai
albarka a cikin sahur)). Bukhari (1923), Muslim (1095).
Haka Annabi (saw) ya bayyana
cewa; Sahur ne abin da ya raba Azumin Musulmai da na Ahlul Kitabi, inda ya ce:
«فَصْلُ مَا بَيْنَ صِيَامِنَا
وَصِيَامِ أَهْلِ الْكِتَابِ، أَكْلَةُ السَّحَرِ»
[مسلم، صحيح مسلم، ٧٧٠/٢]
((Banbancin Azuminmu da na Ahlul
Kitabi shi ne cin abincin sahur)). Muslim (1096).
Don haka ake so mai Azumi ya yi
sahur da duk abin da ya samu, ko da ruwa ne ko dabino.
Kuma yana daga cikin abin da ake
so shi ne a jinkirta sahur din, ya kasance a kusa da ketowan alfijr. Shi ya sa
Allah ya ce:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ
الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ
{Ku ci ku sha har sai farin zare ya bayyana
muku daga bakin zare} [al-Baqarah: 183].
Ma'ana har sai hasken al-fijr ya
bayyana daga duhun dare.
Saboda haka ba gwaninta ba ne
mutum ya ki yin sahur, har ya zo yana bugan kirjin cewa; shi ba ya yin sahur.
Daga cikin Mustahabban Azumi
akwai gaggauta buda baki, da zaran an tabbatar da faduwar rana to sai a
gaggauta yin buda baki, saboda Annabi (saw) ya ce:
«لاَ يَزَالُ النَّاسُ بِخَيْرٍ مَا عَجَّلُوا
الفِطْرَ»
[البخاري، صحيح البخاري،
٣٦/٣]
((Mutane ba za su gushe suna tare
da alheri ba matukar sun gaggauta buda baki)) Bukhari (1957), Muslim (1098).
An so mutum ya yi bude baki da
zaran rana ta fadi, ko da da ruwa ne ko dabino. Ya tabbata daga Anas (ra) ya
ce:
«كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُفْطِرُ عَلَى رُطَبَاتٍ قَبْلَ أَنْ يُصَلِّيَ، فَإِنْ
لَمْ تَكُنْ رُطَبَاتٌ، فَعَلَى تَمَرَاتٍ، فَإِنْ لَمْ تَكُنْ حَسَا حَسَوَاتٍ مِنْ
مَاءٍ»
[السجستاني، أبو داود، سنن أبي
داود، ٣٠٦/٢]
((Annabi (saw) ya kasance yana
yin buda baki kafin ya yi Sallah, yana cin danyen dabino, idan bai samu danye
ba sai ya yi da busasshen dabino, idan bai samu ba sai ya kurbi ruwa)). Abu
Dawud (2356), Tirmiziy (696).
Kuma lokacin buda baki lokacin
amsa addu'a ne, don haka ake so mutum ya yi kokari wajen yin addu'o'i da rokon
Allah biyan bukatunsa na alheri. Annabi (saw) ya ce:
«إِنَّ لِلصَّائِمِ عِنْدَ فِطْرِهِ لَدَعْوَةً
مَا تُرَدُّ»
[ابن ماجه، سنن ابن ماجه،
٥٥٧/١]
((Lallai mai Azumi yana da addu'a a lokacin
buda bakinsa, wacce ba za a mayar da ita ba)). Ibnu Majah (1753).
Daga cikin addu'an da aka ruwaito
daga Annabi (saw) akwai fadinsa:
«ذَهَبَ الظَّمَأُ وَابْتَلَّتِ
الْعُرُوقُ، وَثَبَتَ الْأَجْرُ إِنْ شَاءَ اللَّهُ»
[السجستاني، أبو داود، سنن أبي
داود، ٣٠٦/٢]
Ma'ana; kishirwa ya tafi,
jijiyoyi sun jika, lada ya tabbata insha Allahu.
Abu Dawud (2357).
Daga cikin Sunnonin Azumi da
ladubansa ana son yawaita karatun Alkur'ani da zikiri da addu'o'i da rokon
Allah da Sallah da sadaka. Ya tabbata Annabi (saw) ya ce:
ثَلاَثٌ لاَ تُرَدُّ دَعْوَتُهُمْ، الإِمَامُ
العَادِلُ، وَالصَّائِمُ حِينَ يُفْطِرُ، وَدَعْوَةُ الْمَظْلُومِ يَرْفَعُهَا فَوْقَ
الغَمَامِ، وَتُفَتَّحُ لَهَا أَبْوَابُ السَّمَاءِ، وَيَقُولُ الرَّبُّ عَزَّ وَجَلَّ:
وَعِزَّتِي لأَنْصُرَنَّكِ وَلَوْ بَعْدَ حِينٍ.
[الترمذي، محمد بن عيسى، سنن
الترمذي ت بشار، ٢٥٣/٤]
((Mutane uku ba a mayar da
addu'arsu, mai Azumi har sai ya yi buda baki, adalin shugaba, addu'ar wanda aka
zalunta, Allah zai daga ta a saman gajimare, sai a bude mata kofofin sama, sai
Ubangiji ya ce: na rantse da girmana da buwayata zan taimake ka ko da bayan
wani lokaci ne)) Tirmiziy (2526), Ibnu Majah (1752).
Kuma Annabi (saw) ya kasance mai
yawan kyauta a Ramadhan, kamar yadda ya tabbata daga Ibnu Abbas (ra) ya ce:
«كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَجْوَدَ النَّاسِ بِالخَيْرِ، وَأَجْوَدُ مَا يَكُونُ فِي شَهْرِ
رَمَضَانَ، لِأَنَّ جِبْرِيلَ كَانَ يَلْقَاهُ فِي كُلِّ لَيْلَةٍ فِي شَهْرِ رَمَضَانَ،
حَتَّى يَنْسَلِخَ يَعْرِضُ عَلَيْهِ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
القُرْآنَ، فَإِذَا لَقِيَهُ جِبْرِيلُ كَانَ أَجْوَدَ بِالخَيْرِ مِنَ الرِّيحِ المُرْسَلَةِ»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٨٦/٦]
((Annabi (saw) ya kasance ya fi
kowa kyauta, kuma kyautansa ya fi yawa a Ramadhan, saboda Jibril ya kasance
yana haduwa da shi a kowane dare a watan Ramadhan har ya kare, Manzon Allah
(saw) yana karanta masa Alkur'ani, idan Jibril ya hadu da shi ya kasance mafi
kyauta fiye da iska mai kadawa)). Bukhari (4997), Muslim (2308).
Daga cikin laduban Azumi ana so
mai Azumi ya halarto da girman ni'imar Allah gare shi, ta yadda ya datar da shi
ga yin Azumin, ya saukaka masa shi, kuma ya cika masa Azumin, saboda akwai
mutane da yawa wadanda suka rasa wannar daman, imma saboda ajali ya riske su,
ko rashin lafiya, ko gazawa, ko sun bata daga hanya, don haka mai Azumi ya gode
ma Allah a kan ni'imar Azumi, wacce kofa ce ta samun alherai masu yawa, na
samun falalan ibadu, da gafaran zunubai da daukakar daraja a gidan Aljanna.
Don haka bayi ku lazimci laduban
Azumi don rabauta, ku nisanci sabuba masu tauye Azumi su hana samun ladansa, ko
cikarsa.
Allah ya karba mana Ibadunmu, ya
gafarta mana zunubanmu, ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu
da suke damun kasarmu.
Dr Aliyu Muh'd Sani
(Hafizahullah)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.