Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar'anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.
Tsira da amincin Allah su tabbata
ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari'a mai
sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
Azumi yana da laduba masu yawa,
wadanda Azumi ba ya cika sai da su. Kuma wadannan laduba kashi biyu ne:
1) Laduba wajibai, wadanda wajibi
ne mai Azumi ya kiyaye su.
2) Laduba mustahabbai, wadanda ya
kamata mai Azumi ya kiyaye su.
Daga cikin laduban Azumi na
wajibi; ya wajaba a kan mai Azumi ya lazimci Ibadu na aiki da na magana, mafi
muhimmancinsu shi ne Sallolin farilla, su ne mafi girma a cikin rukunnan
Muslunci bayan Shahada guda biyu. Don haka wajibi ne mai Azumi ya kiyaye Sallolin
farilla, ya kiyaye su da sharudansu da wajibansu, ya yi su a Masallaci a cikin
jam'i, saboda hakan yana daga cikin aiyukan Taqwa, wadanda aka shar'anta Azumi,
aka farlanta shi saboda su. Don haka rashin kiyaye Sallah a cikin Azumi yana
kore Taqwa, kuma yana janyo wa mutum azabar Allah. Allah ya ce:
فَخَلَفَ مِن بَعْدِهِمْ خَلْفٌ أَضَاعُوا الصَّلَاةَ
وَاتَّبَعُوا الشَّهَوَاتِ فَسَوْفَ يَلْقَوْنَ غَيًّا
{Sai wasu suka zo a bayansu, suka
tozarta Sallah, suka bi abubuwan sha'awa, da sannu za su hadu da gayya (wani
kwari a Jahannama).
إِلَّا مَن تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا
فَأُولَٰئِكَ يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ وَلَا يُظْلَمُونَ شَيْئًا
Sai dai wanda ya tuba ya yi
imani, ya yi kyakkyawan aiki, wadannan su za su shiga Aljanna, kuma ba za a
zalunci kowa ba} [Maryam: 59 - 50].
Akan samu wasu masu Azumi suna
sakaci da Sallar Jam'i tare da wajabcinta a kansu. Saboda Allah ya yi umurni da
yin Sallah ne a cikin jam'i, wannan ya sa hatta makaho maras jagora Annabi
(saw) bai yi masa rangwamen rashin zuwa Sallar jam'i ba. Ya tabbata daga Abu
Huraira (ra) ya ce:
أَتَى النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
رَجُلٌ أَعْمَى، فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، إِنَّهُ لَيْسَ لِي قَائِدٌ يَقُودُنِي
إِلَى الْمَسْجِدِ، فَسَأَلَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنْ يُرَخِّصَ
لَهُ، فَيُصَلِّيَ فِي بَيْتِهِ، فَرَخَّصَ لَهُ، فَلَمَّا وَلَّى، دَعَاهُ، فَقَالَ:
«هَلْ تَسْمَعُ النِّدَاءَ بِالصَّلَاةِ؟» قَالَ: نَعَمْ، قَالَ: «فَأَجِبْ»
[مسلم، صحيح مسلم، ٤٥٢/١]
((Wani mutum makaho ya zo wajen Annabi (saw)
ya ce: Ya Manzon Allah, ba ni da jagora da zai kai ni Masallaci. Sai ya nemi
Annabi (saw) ya yi masa rangwame, yana yin Sallah a gidansa, sai Annabi (saw)
ya yi masa rangwame. Bayan ya juya ya tafi, sai ya kira shi, ya ce masa:
"Shin kana jin kiran Sallah"? Sai ya ce: Eh. Sai ya ce: "To ka
amsa")). Muslim (653).
Rashin halartar Sallar farilla
cikin jam'i yana sa mutum ya rasa falalar Sallar, Annabi (saw) ya ce:
«صَلاَةُ الجَمَاعَةِ تَفْضُلُ
صَلاَةَ الفَذِّ بِسَبْعٍ وَعِشْرِينَ دَرَجَةً»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٣١/١]
((Sallar jam'i ta fi Sallar mutum daya da
daraja ishirin da bakwai)) Bukhari (645), Muslim (649).
Kuma barin halartar jam'i sifa ce
ta Munafukai, bayan zai janyo wa mutum azabar Allah, zai sa ya yi kama da
Munafukai, kamar yadda ya tabbata daga Abu Huraira (ra): yace Manzon Allah (Saw) yace.
«لَيْسَ صَلاَةٌ أَثْقَلَ عَلَى المُنَافِقِينَ
مِنَ الفَجْرِ وَالعِشَاءِ، وَلَوْ يَعْلَمُونَ مَا فِيهِمَا لَأَتَوْهُمَا وَلَوْ
حَبْوًا، لَقَدْ هَمَمْتُ أَنْ آمُرَ المُؤَذِّنَ، فَيُقِيمَ، ثُمَّ آمُرَ رَجُلًا
يَؤُمُّ النَّاسَ، ثُمَّ آخُذَ شُعَلًا مِنْ نَارٍ، فَأُحَرِّقَ عَلَى مَنْ لاَ يَخْرُجُ
إِلَى الصَّلاَةِ بَعْدُ»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٣٢/١]
((Sallah mafi nauyi ga Munafukai
ita ce Sallar Isha'i da Sallar al-fijr, da a ce sun san abin da ke cikinsu na
lada da sun zo musu ko da da rarrafe ne. Hakika na yi nufin na sa a yi Sallah,
a tayar da Iqama, sai na umurci wani ya yi limanci, sai na tafi tare da wasu
mutane, a tare da su akwai damin itace, zuwa ga mutanen da ba sa zuwa Sallar
jam'i, don na kona musu gidajensu)). Bukhari (657), Muslim (651).
Saboda haka sakaci da Sallah, a
cikin jam'i yana daga cikin munanan aiyuka da suke hana cikan ladar Azumi, mai
sai mutum ya sha yunwa da kishirwan banza.
Daga cikin laduba na wajibi;
wajibi ne mai Azumi ya nisanci dukkan abin da Allah da Manzonsa (saw) suka
haramta na maganganu da aiyuka. Wajibi ne ya nisanci karya, wato ya fadi abin
da ba a yi ba ya ce an yi, ko ya fadi abin da aka yi amma bisa sabanin yadda
abin ya auku. Mafi girman karya kuma shi ne karya wa Allah da Manzonsa (saw),
kamar mutum ya danganta ma Allah halasta wani abu, ko haramtawa ba tare da
ilimi ba.
Allah ya ce:
وَلَا تَقُولُوا لِمَا تَصِفُ أَلْسِنَتُكُمُ
الْكَذِبَ هَٰذَا حَلَالٌ وَهَٰذَا حَرَامٌ لِّتَفْتَرُوا عَلَى اللَّهِ الْكَذِبَ
إِنَّ الَّذِينَ يَفْتَرُونَ عَلَى اللَّهِ الْكَذِبَ لَا يُفْلِحُونَ
{Kada ku fadi ga abin da harsunanku suke
siffantawa na karya, wannan halal ne wannan kuma haram ne, alhali karya kuke yi
ma Allah. Lallai wadanda suke kirkiran karya ma Allah ba za su rabauta ba.
مَتَاعٌ قَلِيلٌ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
Jin dadi ne kadan, sai kuma azaba
mai radadi} [al-Nahl: 116 - 117].
Ya tabbata daga Abu Huraira da
waninsa (ra) Annabi (saw) ya ce:
وَمَنْ كَذَبَ عَلَيَّ مُتَعَمِّدًا فَلْيَتَبَوَّأْ
مَقْعَدَهُ مِنَ النَّارِ»
[البخاري، صحيح البخاري،
٣٣/١]
((Duk wanda ya yi mini karya to
ya tanadi wajen zamansa a gidan wuta)) Bukhari (110), Muslim (3).
Kuma ya tabbata Annabi (saw) ya
ce:
وَإِنَّ الكَذِبَ يَهْدِي إِلَى الفُجُورِ،
وَإِنَّ الفُجُورَ يَهْدِي إِلَى النَّارِ، وَإِنَّ الرَّجُلَ لَيَكْذِبُ حَتَّى يُكْتَبَ
عِنْدَ اللَّهِ كَذَّابًا»
[البخاري، صحيح البخاري،
٢٥/٨]
((Ku nisanci karya, saboda karya tana
shiryarwa ga fajirci, lallai fajirci kuma yana shiryarwa zuwa ga wuta. Mutum ba
zai gushe ba yana karya, yana kirdadon yin karya face an rubuta shi a matsayin
makaryaci a wajen Allah)).Bukhari (6094), Muslim (2607).
Haka wajibi ne ya nisanci cin
naman mutane da gulmansu, ko da kuwa anbaton mutum da sifarsa wacce ba ya so a
kira shi da ita ce, kamar a ce masa gurgu, makaho, kuturu ta fiskar aibantawa,
ko abin da yake ki na halaye, kamar a kira shi da wawa, soko da sauransu.
Saboda Annabi (saw) ya yi bayanin giba da cewa shi ne:
«أَتَدْرُونَ مَا الْغِيبَةُ؟»
قَالُوا: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «ذِكْرُكَ أَخَاكَ بِمَا يَكْرَهُ» قِيلَ
أَفَرَأَيْتَ إِنْ كَانَ فِي أَخِي مَا أَقُولُ؟ قَالَ: «إِنْ كَانَ فِيهِ مَا تَقُولُ،
فَقَدِ اغْتَبْتَهُ، وَإِنْ لَمْ يَكُنْ فِيهِ فَقَدْ بَهَتَّهُ»
[مسلم، صحيح مسلم، ٢٠٠١/٤]
Annabi (Saw) yace. ko kunsan meye
giba? Sahabbai (Ra) Sukace Allah da Manzon sa Sune Masana. Sai Annabi (Saw)
yace.
((Ambaton dan'uwanka da abin da yake ki. Sai
aka ce masa: To idan ya kasance yana da wannan abin fa? Sai ya ce: idan yana da
shi to ka ci namansa, idan kuma ba shi da shi to ka yi masa kage)). Muslim
(2589).
Allah Madaukaki ya yi hani a kan
giba, har ya siffanta shi da mummunan kama, ya nuna giba ya yi kama da cin
naman mutum a zahiri bayan ya mutu. Allah ya ce: {Kar sashenku ya yi giban
sashe, yanzu dayanku zai so ya ci naman dan'uwansa bayan ya mutu? To ku kyamace
shi} [al-Hujraat: 12].
Haka kuma ya nisanci annamimanci
da hada fada, da yin batanci a kan mutum, wannan shi ma yana cikin manyan
laifuka. Annabi (saw) ya ce:
«لَا يَدْخُلُ الجَنَّةَ قَتَّاتٌ»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٧/٨]
((Annamimi ba zai shiga Aljanna
ba)) Bukhari (6056), Muslim (105).
Annamimnaci shi ne bata tsakanin
mutane, da haifar da fitina a tsakaninsu, mutum ya dauki magana daga wannan ya
kai ga wancan don ya bata tsakaninsu, ya haifar da gaba da kiyayya a
tsakaninsu.
Haka wajibi ne mutum ya nisanci
gisshu da cuta a cikin mu'amalar kasuwanci ko sana'a, saboda cuta yana daga
cikin manyan laifuka, Annabi (saw) ya ce:
مَنْ غَشَّ فَلَيْسَ مِنِّي»
[مسلم، صحيح مسلم، ٩٩/١]
((Wanda ya yi mana gisshu ba ya tare da mu))
Muslim (102).
Gisshu shi ne cuta da yaudara da
cin amana da rashin aminci a tsakanin mutane cikin mu'amala. Dukkan wanda cuta
ya zama hanyar abincinsa to ya sani haramun yake ci, wuta yake ci a cikinsa,
babu abin da zai kara masa sai nisa da Allah.
Haka kuma wajibi ne mai Azumi ya
nisanci kayan kade-kade da raye-raye da kayayyakin wasanni, da sauran abubuwa
da suke wannan layi, wadanda suke haramun ne, balle kuma a ce idan ya hadu da
sauti mai haifar da fitina da motsa sha'awa. Shi ya sa Annabi (saw) ya hada su
da zina, inda ya ce:
" لَيَكُونَنَّ مِنْ أُمَّتِي أَقْوَامٌ، يَسْتَحِلُّونَ
الحِرَ وَالحَرِيرَ، وَالخَمْرَ وَالمَعَازِفَ،
[البخاري، صحيح البخاري،
١٠٦/٧]
((Lallai wasu mutane za su
kasance a cikin al'ummata, suna halasta zina da hariri, da giya da kayan kida
da waka)). Bukhari (5590).
Duk wanda bai kiyaye wadannan
laduba ba, bai nisanci wadannan munanan aiyuka ba, to ko shakka babu zai iya
wayan gari ya yi kishirwan banza, da yunwan banza, kamar yadda Annabi (saw) ya
ce:
«مَنْ لَمْ يَدَعْ قَوْلَ الزُّورِ
وَالعَمَلَ بِهِ وَالجَهْلَ -[18]-، فَلَيْسَ لِلَّهِ حَاجَةٌ أَنْ يَدَعَ طَعَامَهُ
وَشَرَابَهُ»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٧/٨]
((Duk wanda bai bar fadin karya
da aiki da ita ba, da aikin jahilci to Allah ba ya bukatar ya bar cin abincinsa
da abin shansa)). Bukhari (6057).
An ruwaito daga Jabir (ra) ya ce:
(Idan kana Azumi to jinka ma ya yi Azumin, ganinka ya yi, harshenka ya yi, ya
kame daga karya da aiyukan haramun. Ka nisanci cutar da makwabci, ka lazimci
nitsuwa, kar Azuminka da shan ruwanka ya zama daidai).
Allah ya karba mana Ibadunmu, ya
gafarta mana zunubanmu, ya taimake mu a kan kiyaye Azuminmu, ya jikan iyayenmu,
ya yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun kasarmu, na kuncin rayuwa da
rashin tsaro da aminci, ya ba mu shugabanni na gari, masu kishin al'umma da
tausayin talakawa.
Dr Aliyu Muh'd Sani
(Hafizahullah)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.