Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar'anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.
Tsira da amincin Allah su tabbata
ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari'a mai
sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
Abu ne sananne Alkur'ani maganar
Allah ne, littafinsa ne da ya saukar wa Manzonsa a matsayin shiriya ga bayi a
rayuwarsu gaba daya, ta bangaren Addini da Ibada da bangaren harkokin
rayuwarsu. Shi ne mafificin littafin Allah, wanda ya saukar da shi ga mafificin
Manzonsa (saw), ga al'umma mafi falala. Littafi ne wanda ya kunshi bayani, da
shiriya, da haske, da rahma da albarka da waraka.
Littafi ne wanda Allah ya umurce
mu mu karanta shi, mu yi tadabburinsa, mu fahimce shi, mu dauki ilimomin da
suke cikinsa, mu yi aiki da shiriyoyinsa da umurni da hanin da ke cikinsa.
Alkur'ani littafi ne mai girma,
Allah ya siffanta shi da siffofi masu yawa, kuma masu girma, wadanda suke nuni
a kan wajabcin girmama Alkur'ani, da yin ladabi wajen karanta shi, da nisantar
wasa da wargi ko shagala wajen karanta shi. Saboda haka Malamai suka yi bayanin
laduba na karanta Alkur'ani, wadanda za su sa mai karantawa ya yi tadabburin
Alkur'anin, ya fahimci abin da yake karantawa, har ya samu falalan Alkur'anin
wajen karanta shi, na samun natsuwa a zuciya, da warakar shubuhohi, da waraka a
gangar jiki.
Daga cikin laduban karanta
Alkur'ani, wajibi ne mutum ya yi niyya, kuma ya yi ikhlasi a cikin niyyar tasa,
ya yi niyyar yin ibada ma Allah, da neman yardarsa, saboda karatun Alkur'ani
ibada ce mai girma, ibada kuma ba ta karbuwa sai da ikhlasi. Shi ya sa Annabi
(saw) ya ce: ((Ku karanta Alkur'ani, ku nemi yardar Allah, kafin wasu mutane su
zo, suna saita shi kamar saita masu, suna gaggauta samun sakamakonsa ba sa
jinkirta shi)). Ahmad (14855).
Ma'anar suna gaggauta sakamakonsa
shi ne suna neman abin duniya da shi, na dukiya ko daukaka. Saboda haka wajibi
ne mutum ya tsarkake karatunsa na Alkur'ani daga dukkan abin da zai bata masa
ikhlasi.
Daga cikin laduban karatun
Alkur'ani mutum ya karanta Alkur'ani yana mai tara hankalinsa a kansa, yana
tadabburinsa, yana kallon ma'anoninsa, yana fahimtarsu, yana lura da su, yana
kaskantar da kai ga ma'anonin maganar Allah, yana jin cewa; Allah yana magana
ne da shi kai tsaye, saboda Alkur'ani maganar Allah ne.
Daga cikin laduban karatun
Alkur'ani ana so mutum idan zai yi karatun ya yi tsarki, saboda hakan yana
cikin girmama maganar Allah. Kar mutum ya karanta Alkur'ani alhali yana da
janaba har sai ya yi wanka, ko taimama idan ba zai iya amfani da ruwan ba, a dalilin
rashin lafiya ko rashin ruwan. Amma mai janaba zai iya ambaton Allah, ya yi
addu'a ya roke shi da addu'o'i na Alkur'ani.
Daga cikin laduban karatun
Alkur'ani ana so kar mutum ya yi karatu a wuraren kazanta, ko wuraren da ba za
a saurara ma Alkur'anin ba, kamar wuraren hayaniya, saboda a cikin hakan akwai
wulakanta Alkur'anin. Don haka bai halasta ya karanta shi a bayan gida wurin
tsuguno ba, ko kan bola.
Daga cikin laduban karatun
Alkur'ani ana so mutum ya yi "Isti'aza", ya ce: {A'uzu billahi minash
shaidaninr rajeem}. Saboda Allah ya yi umurni da haka, inda ya ce: {Idan za ka
karanta Alkur'ani to ka nemi tsari da Allah daga shaidan jifaffe} [al-Nahli:
98].
Zai yi haka ne don kar shaidan ya
hana shi karatun, ko ya shagaltar da shi.
Haka ana so ya yi
"basmala" ya ce: {Bismillahir rahmanir raheem} a farkon kowace sura,
in ban da Suratu al-Taubah.
Daga cikin laduban karatun
Alkur'ani ana so mutum ya rera sautinsa, saboda ya tabbata Annabi (saw) ya ce:
((Allah bai saurari wani abu ba kamar yadda ya saurari wani Annabi mai dadin
murya, yana rera Alkur'ani, yana bayyana shi)). Bukhari (7544), Muslim (792).
Daga cikin laduban karatun
Alkur'ani ana so mutum ya yi tartilinsa, wato ya karanta shi bisa ka'idojin
Tajwidi. Allah ya ce: {Ka karanta Alkur'ani karantawa mai kyau} [al-Muzammil:
4].
Don haka ana so ya karanta shi a
nitse, ba tare da sauri ba, tare da kiyaye ka'idojin karatu, da tsayar da
harufansa da lafuzansa, don hakan zai sa mutum yin tadabburin ma'anoninsa.
Daga cikin laduban karatun
Alkur'ani ana so mutum idan ya zo kan Ayoyin Sujada to ya tsaya ya yi sujuda,
sai ya yi kabbara ya yi sujadan, ya yi tasbihi a cikinsa, sai ya dago ba tare
da kabbara ba.
Lallai wannan wata na Ramadhan
watan karatun Alkur'ani ne, ya kamata Mumini ya dage da yawaita karatun
Alkur'ani a cikinsa, kuma ya lazimci wadannan laduba, don ya samu amfani da
fa'idan karatun, ya samu albarkar Alkur'ani da rahmar da ke cikinsa, kuma don
ya zama cikin wadanda Alkur'ani ceta a ranar Kiyama.
Allah ya karba mana Ibadunmu, ya
gafarta mana zunubanmu, ya taimake mu a kan kiyaye Azuminmu, ya nufe mu da
yawaita karatun Alkur'ani a cikin wannan wata, ya shiryar da mu hanya
madaidaiciya. Kuma Allah ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu
da suke damun kasarmu, na kuncin rayuwa da rashin tsaro da aminci, ya ba mu
shugabanni na gari, masu kishin al'umma da tausayin talakawa.
✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.