Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar'anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.
Tsira da amincin Allah su tabbata
ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari'a mai
sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
'Yan'uwa kwanaki goman karshe na
Ramadhan sun shiga, a cikinsu akwai alherai masu yawa, da falaloli masu yawa
wadanda Allah ya kebance su da kwanakin.
Daga cikin kebantattun falaloli
na wadannan kwanaki Annabi (saw) ya kasance yana kokari da damaran yin ibada
fiye da yadda yake yi a sauran kwanakin watan, ya tabbata daga A'isha (ra) ta
ce:
«كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَجْتَهِدُ فِي الْعَشْرِ الْأَوَاخِرِ، مَا لَا يَجْتَهِدُ
فِي غَيْرِهِ»
[مسلم ,صحيح مسلم ,2/832]
((Manzon Allah (saw) yana dagewa
da Ibada a kwanaki goman karshe dagewan da ba ya yin irinsa a waninsu)) Muslim
(1175).
Kuma ya tabbata ta ce:
«كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا دَخَلَ العَشْرُ شَدَّ مِئْزَرَهُ، وَأَحْيَا لَيْلَهُ، وَأَيْقَظَ
أَهْلَهُ»
[البخاري، صحيح البخاري،
٤٧/٣]
((Idan goman karshe sun shiga
Annabi (saw) ya kasance yana daura damara, yana raya darensa, yana tayar da
iyalansa daga bacci)) Bukhari (2024) Muslim (1174).
A cikin wadannan Hadisai akwai
bayanin falalolin wadannan kwanaki goma na karshen Ramadhan, saboda Annabi
(saw) ya fi dagewa da Ibada a cikinsu fiye da sauran kwanakin watan, wannan
kuwa ya kunshi dagewa a kan aikata dukkan nau'o'in ibada; na Sallah, karatun
Alkur'a, zikiri, sadaka da sauransu, saboda Annabi (saw) ya kasance yana
nisantar iyalinsa, don ya samu cikakken lokaci na ibada da zikiri, kuma ya
kasance yana raya darensa gaba dayansa da Sallah, da karatun Alkur'ani da
ambaton Allah da zuciya da harshe da gabobi, saboda darajar wadannan kwanaki,
da kuma neman daren Lailatu Qadr, wacce duk wanda ya yi Sallan dare a cikinta,
yana mai imani da neman lada to an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa,
kamar yadda ya tabbata daga Abu Huraira (ra),
Annabi (saw) y ace:
«مَنْ قَامَ لَيْلَةَ القَدْرِ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا،
غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ، وَمَنْ صَامَ رَمَضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا
غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ»
[البخاري، صحيح البخاري،
٢٦/٣]
((Duk wanda yay i Sallar dare a
daren Lailatul Qadr, yana mai imani da neman lada to an gafarta masa abin da ya
gabata na zunubansa)). Bukhari (1901), Muslim (760).
Daga cikin abin da yake nuna
falalar wadannan kwanaki Annabi (saw) ya kasance yana tayar da iyalansa daga
bacci, don su tashi su yi Sallah da zikiri, don su ribaci wadannan darare masu
albarka, saboda dama ce a rayuwa, ganima ce daga Allah, bai kamata Mumini mai
hankali ya yi sakaci har wannar dama ta kubuce masa shi da iyalansa ba, saboda
darare ne kirgaggu, ta yiwu a cikinsu bawa ya yi gamon katar, wanda zai zamo
sanadin samun rabo gare shi a Duniya da Lahira.
Lallai yana daga cikin hasara mai
girma ka ga mutane masu yawa suna bata lokaci a cikin wadannan kwanaki, a kan
abin da ba shi da amfani, su kwana suna bata dare a wasanni da kallace –
kallace, amma idan lokacin Sallar dare ta yi sai su yi bacci, ko kuma su cigaba
da wasanninsu, sai su rasa alherin da a shekara sau daya kawai ake samunsa. Duk
wannan yana daga cikin wasan da Shaidan yake yi da bayi, yake toshe musu hanyar
alherai.
Mai hankali ba zai yi wasa har
Shaidan ya hana masa samun alherai da falaloli da suke cikin wadannan kwanaki
ba.
Daga cikin falalolin wadannan
kwanaki akwai yin I'itikafi, saboda Annabi (saw) ya kasance yana yin I'itikafi
a cikinsu.
I'itikafi shi ne lazimtar
Masallaci don shagaltuwa da Ibada kadai. I'itikafi yana daga cikin Sunnoni da
suka zo a cikin Alkur'ani da Sunnar Annabi (saw), Allah ya ce:
وَلَا تُبَاشِرُوهُنَّ وَأَنتُمْ عَاكِفُونَ
فِي الْمَسَاجِدِ
{Kada ku sadu da su (matanku) alhali kuna
I'itikafi a Masallatai} [al-Baqarah: 187].
Annabi (saw) ya yi I'itikafi,
Sahabbansa sun yi a bayansa, ya tabbata daga A'isha (ra) ta ce:
«أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ
عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، كَانَ يَعْتَكِفُ العَشْرَ الأَوَاخِرَ مِنْ رَمَضَانَ حَتَّى
تَوَفَّاهُ اللَّهُ، ثُمَّ اعْتَكَفَ أَزْوَاجُهُ مِنْ بَعْدِهِ»
[البخاري ,صحيح البخاري
,3/47]
((Lallai Annabi (saw) ya kasance yana yin
I'itikafi a goman karshe na Ramadhan, har ya rasu. Sa'annan matansa sun yi
I'itikafi a bayansa)) Bukhari (2026), Muslim (1172).
Manufar I'itikafi ita ce mutum ya
yanke daga komai don ya shagaltu da Ibada kadai a Masallaci, don neman falalar
Allah da ladansa, da kuma neman dacewa da daren Lailatul Qadr. Saboda haka ake
so mai I'itikafi ya shagala da zikiri, da karatun Alkur'ani, da nafilfili na
Sallah, kuma ya kamata ya nisanci duk abin da ibada ba, da abin da bai shafe
shi ba, na surutu a kan lamarin Duniya. Babu laifi idan ya yi magana a kan
abubuwan da akwai Maslaha a cikinsu, ko akwai bukata.
Ya tabbata daga Safiyya (ra) ta
ce:
كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ مُعْتَكِفًا فَأَتَيْتُهُ أَزُورُهُ لَيْلًا، فَحَدَّثْتُهُ ثُمَّ قُمْتُ
فَانْقَلَبْتُ، فَقَامَ مَعِي لِيَقْلِبَنِي،
[البخاري ,صحيح البخاري
,4/124]
((Annabi (saw) ya kasance yana
yana I'itikafi sai na zo na ziyarce shi da daddare, na yi magana da shi, sai na
koma gidana, sai Annabi (saw) ya tashi tare da ni don ya mayar da ni)) Bukhari
(3281), Muslim (2175).
Haramun ne mai I'itikafi ya sadu
da iyali, da yin abin da suke gabanninsa; sunbanta, shafa da sha'awa da
sauransu, saboda fadin Allah:
وَلَا تُبَاشِرُوهُنَّ وَأَنتُمْ عَاكِفُونَ
فِي الْمَسَاجِدِ
{Kada ku sadu da su (matanku) alhali kuna
I'itikafi a Masallatai} [al-Baqarah: 187].
Amma fitan mai I'itikafi daga
Masallaci ya kasu kashi uku:
Na farko: Fitan da ya zama dole:
Kamar fita zuwa bayan gida, don
biyan bukata, wankan janaba, Alola, ko fita don cin abinci. Idan ya zama babu
bayan gida a Masallacin, kuma babu wanda zai kawo masa abinci da zai ci, to
babu laifi ya fita, saboda ya zama dole.
Amma idan zai yiwu a kawo masa
abinci ya ci a Masallacin, kuma a Masallacin akwai bayan gida da zai shiga ya
biya bukatansa, to babu bukatar ya fita.
Na biyu: Fita saboda aikin da'a:
Kamar fita saboda gai da maras
lafiya, ko halartar Sallar jana'iza da makamancinsu, to wannan ba zai fita ba,
sai dai idan ya shardanta hakan tun lokacin fara I'itikafin, don haka babu
laifi.
Na uku: Fita ga abin da ya saba
ma I'itikafin:
Kamar fita don yin kasuwanci, ko
don saduwa da iyali; Jima'i da abin da ke da alaka da shi, to wannan bai
halasta ba, ko da kuwa ya shardanta hakan, saboda yana kore manufar I'itikafin.
Daga cikin kebantattun falaloli
na wadannan kwanaki, a cikinsu daren Lailatul Qadr take, daren da ya fi wata
dubu.
Don haka ya ku 'yan'uwa, ku
kiyaye darajan wadannan kwanaki, ku dage da ibada a cikinsu, ku nemi daren
Lailatul Qadr. Lallai wadannan kwanaki suna da tsada, kar ka sake ka yi
asaransu.
Allah ya karba mana Ibadunmu, ya
gafarta mana zunubanmu, ya taimake mu a kan kiyaye Azuminmu, ya nufe mu da
yawaita aiyukan da'a a cikin wannan wata, ya shiryar da mu hanya madaidaiciya.
Ka sa mu dace da daren Lailatul Qadr.
Kuma Allah ya jikan iyayenmu, ya
yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun kasarmu, na kuncin rayuwa da
rashin tsaro da aminci, ya ba mu shugabanni na gari, masu tsoron Allah da
kishin al'umma da tausayin talakawa.
Dr Aliyu Muh'd Sani
(Hafizahullah)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.