Ticker

6/recent/ticker-posts

DARUSAN RAMADHAN - Darasi na Goma Sha Shida: Fitar Da Zakka

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar'anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari'a mai sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.

Allah Madaukakin Sarki ya farlanta fitar da Zakka, har ya sanya shi cikin rukunnan Muslunci guda biyar, kamar yadda ya tabbata ta harshen Manzonsa (saw).

Fitar da Zakka da bayar da ita ga talakawa da wadanda suka cancance ta yana daga cikin manyan abubuwa da suke bayyana kyaun Shari'ar Muslunci, da kasancewarta babban hanya ta warware matsalolin rayuwar al'umma; matsalolin zamantakewa, matsalolin siyasa,  da matsalolin tattalin arziki da sauransu.

Allah ya ce:

وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ ۚ وَذَٰلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ

{Ba a umurce su da komai ba face su bauta ma Allah suna masu tsarkake Addini gare shi, suna masu karkata gare shi, kuma su tsayar da Sallah, su bayar da Zakka, wannan shi ne Addini tsayayye} [al-Bayyinah: 5].

Kuma Allah ya ce:

 ۚ وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ وَأَقْرِضُوا اللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا ۚ وَمَا تُقَدِّمُوا لِأَنفُسِكُم مِّنْ خَيْرٍ تَجِدُوهُ عِندَ اللَّهِ هُوَ خَيْرًا وَأَعْظَمَ أَجْرًا ۚ

{Ku tsayar da Sallah, ku bayar da Zakka, ku bai ma Allah rance, duk abin da kuka gabatar ma kawunanku za ku same shi a wajen Allah, shi ya fi alheri, kuma ya fi girman daraja} [al-Muzammil: 20].

Ayoyi a kan farlancin Zakka suna da yawa. Daga cikin Hadisai kuma akwai fadin Annabi (saw):

" بُنِيَ الإِسْلاَمُ عَلَى خَمْسٍ: شَهَادَةِ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلاَةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَالحَجِّ، وَصَوْمِ رَمَضَانَ "

[البخاري ,صحيح البخاري ,1/11]

((An gina Muslunci a kan abubuwa guda biyar; Shaidawa babu abin bauta sai Allah, kuma Annabi Muhammad ma'aikin Allah ne, da tsayar da Sallah, da ba da Zakka, da aikin Hajji, da Azumin watan Ramadhan)). Sahihul Bukhari (8), Sahihu Muslim (16).

Zakka tana daga cikin rukunnan Muslunci, ita ce mahadin Sallah a cikin nassoshin Shari'a. Musulmai gaba daya sun hadu a kan farlancinta, sun yi Ijma'i yankakke wanda babu shakka a cikinsa. Don haka duk wanda ya yi inkarin wajabcinta to hakika ya kafirta, za a nemi ya tuba, idan ya tuba, ya yarda da wajabcin Zakkar shi kenan, idan kuma ya ki tuba to za a kashe shi a matsayin kafiri, wanda ya yi ridda daga Muslunci. Ba za a yi masa wanka ba, ba za a suturce shi a likkafani ba, ba za a yi masa Sallah ba, ba za a yi masa addu'an neman rahma ba, ba za a bisne shi a makabartan Musulmai ba, kawai za a tona rami ne a can nesa a rufe shi, don kar warinsa ya dami mutane, 'yan'uwansa su cutu.

Haka duk wanda ya ki bayar da Zakka, ko ya rage abin da ya wajaba a kansa a cikinta alal hakika ya cancanci ukuba mai tsananin gaske.

Zakka tana wajaba ne a abubuwa guda hudu:

Na farko:

Abubuwan da suke fitowa a kasa na kayan gona:

Zakka tana wajaba a cikinsu saboda fadin Allah Madaukaki:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَنفِقُوا مِن طَيِّبَاتِ مَا كَسَبْتُمْ وَمِمَّا أَخْرَجْنَا لَكُم مِّنَ الْأَرْضِ وَلَا تَيَمَّمُوا الْخَبِيثَ مِنْهُ تُنفِقُونَ وَلَسْتُم بِآخِذِيهِ إِلَّا أَن تُغْمِضُوا فِيهِ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ غَنِيٌّ حَمِيدٌ 

{Ya ku wadanda suka yi imani, ku ciyar daga dadadan abin da kuka nema kuka samu, da kuma abin da muka fitar muku daga kasa} [al-Baqara: 267].

Kuma Allah ya ce:

وَآتُوا حَقَّهُ يَوْمَ حَصَادِهِ 

 {Ku ba da hakkinsa a ranar girbe shi} [al-An'am: 141].

Hakkin dukiya mafi girma shi ne Zakka. Annabi (saw) ya ce:

«فِيمَا سَقَتِ السَّمَاءُ وَالعُيُونُ أَوْ كَانَ عَثَرِيًّا العُشْرُ، وَمَا سُقِيَ بِالنَّضْحِ نِصْفُ العُشْرِ»

[البخاري، صحيح البخاري، ١٢٦/٢]

 ((A abin da ruwan sama ya shayar ko ya kasance ta idaniyar ruwa za a fitar da zakkar daya bisa goma, a abin da aka samu ta hanyar bayin ruwa za a fitar da rabin daya bisa goma)) Bukhari (1483).

Zakka ba ta wajaba har sai ya kai Nisabi, shi ne wusiki biyar, saboda fadin Annabi (saw):

«لَيْسَ فِيمَا دُونَ خَمْسَةِ أَوْسُقٍ صَدَقَةٌ، وَلَا فِيمَا دُونَ خَمْسِ ذَوْدٍ صَدَقَةٌ،

[مسلم، صحيح مسلم، ٦٧٣/٢]

 ((Babu Zakka a kayan gona ko 'ya'yan itatuwa har sai ya kai wuski biyar)). Muslim (979).

Wuski shi ne sa'i sittin (60) da sa'in Annabi (saw). Don haka Nisabi shi ne sa'in dari uku (300), wanda yake dadai da kilo dari shida da sha biyu (612), kowane sa'i kilo biyu da digo sha biyar (2.15).

Abin da za a fitar a ciki shi ne daya bisa goma, idan da ruwan sama aka shayar da shukan ba tare da wahala ba.

Ba a fitar da Zakka ga kayan marmari da ganyaye, kamar kankana, lemo, yakuwa da alayyaho da makamantansu, saboda Sayyidina Umar (ra) ya ce: (Babu Zakka a kayan marmari). Sayyidina Aliyu (ra) ya ce: (Babu Zakka a apple da abin da ya yi kama da shi).

Na biyu: Dabbobin Ni'ima:

Su ne rakuma, shanu, da tumaki da awaki, idan sun kasance sakakku, suna kiwo daga ciyawar da Allah ya tsirar, ba tare da aikin dan-adam ba, kuma an tanade su don tatsa, da haifuwa, idan sun kai nisabi Zakka ta wajaba a kansu.

Nisabin rakuma shi ne rakuma biyar (5), shanu talatin (30), tumaki da awaki arba'in (40). Amma idan daurarru ne, wadanda ake ciyar da su, kuma ba na kasuwanci ba ne babu Zakka a kansu. Amma idan na kasuwanci ne akwai Zakka a kansu.

Na uku: Kudi:

Su ne zinari da azurfa, a kowane yanayi suke. Allah ya ce:

 وَالَّذِينَ يَكْنِزُونَ الذَّهَبَ وَالْفِضَّةَ وَلَا يُنفِقُونَهَا فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَبَشِّرْهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ 

 {Wadanda suke taskance zinari da azurfa ba sa ciyar da su saboda Allah ka yi musu bushara da azaba mai radadi.

يَوْمَ يُحْمَىٰ عَلَيْهَا فِي نَارِ جَهَنَّمَ فَتُكْوَىٰ بِهَا جِبَاهُهُمْ وَجُنُوبُهُمْ وَظُهُورُهُمْ هَٰذَا مَا كَنَزْتُمْ لِأَنفُسِكُمْ فَذُوقُوا مَا كُنتُمْ تَكْنِزُونَ

Ranar da za a toye su a wutar jahanna, sai a yi lalas da su a goshin masu su, da gefen jikinsu, da bayansu, wannan shi ne abin da kuka taskance ma kawunanku, ku dandana abin da kuka kasance kuna taskancewa} [al-Taubah:  35].

Abin da ake nufi da taskance su shi ne rashin bayar da su saboda Allah, babba a ciki kuwa shi ne Zakka da Allah ya farlanta.

Ya tabbata Annabi (saw) ya ce:

«مَا مِنْ صَاحِبِ ذَهَبٍ وَلَا فِضَّةٍ، لَا يُؤَدِّي مِنْهَا حَقَّهَا، إِلَّا إِذَا كَانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ، صُفِّحَتْ لَهُ صَفَائِحُ مِنْ نَارٍ، فَأُحْمِيَ عَلَيْهَا فِي نَارِ جَهَنَّمَ، فَيُكْوَى بِهَا جَنْبُهُ وَجَبِينُهُ وَظَهْرُهُ، كُلَّمَا بَرَدَتْ أُعِيدَتْ لَهُ، فِي يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُ خَمْسِينَ أَلْفَ -[681]- سَنَةٍ، حَتَّى يُقْضَى بَيْنَ الْعِبَادِ،

[مسلم، صحيح مسلم، ٦٨٠/٢]

((Babu wani ma'abocin zinari da azurfa wanda ba ya bayar da hakkinsu face idan Ranar Kiyama ta kasance za narka su a fadada su kamar faranti na wuta, sai a toya su a wutar Jahannama, sai a yi masa lalas da su gefensa da goshinsa da bayansa, duk lokacin da ya yi sanyi sai a sake maimaitawa, a ranar da take kwatankwacin shekara dubu hamsin, har sai an yi hukunci tsakanin bayi)) Muslim (987).

Zakka tana wajaba a zinari da azurfa sawa'un an buga su sun zama kudi, ko kayan ado, saboda dalili bai banbance ba. Ya tabbata daga Abdullah bn Amr (ra) ya ce:

أَنَّ امْرَأَةً أَتَتْ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَمَعَهَا ابْنَةٌ لَهَا، وَفِي يَدِ ابْنَتِهَا مَسَكَتَانِ غَلِيظَتَانِ مِنْ ذَهَبٍ، فَقَالَ لَهَا: «أَتُعْطِينَ زَكَاةَ هَذَا؟»، قَالَتْ: لَا، قَالَ: «أَيَسُرُّكِ أَنْ يُسَوِّرَكِ اللَّهُ بِهِمَا يَوْمَ الْقِيَامَةِ سِوَارَيْنِ مِنْ نَارٍ؟»، قَالَ: فَخَلَعَتْهُمَا، فَأَلْقَتْهُمَا إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَقَالَتْ: هُمَا لِلَّهِ عَزَّ وَجَلَّ وَلِرَسُولِهِ

[السجستاني، أبو داود، سنن أبي داود، ٩٥/٢]

 ((Wata mata ta zo wajen Annabi (saw) da 'yarta a tare da ita, a hanunta akwai warwaro biyu na zinari masu kauri, sai Annabi (saw) ya ce: "Shin kina bayar da Zakkar wannan?" Sai ta ce: A'a. Sai ya ce: "Zai yi miki dadi a Ranar Kiyama Allah ya yi miki warwaro da su warwaro na wuta?". Ya ce: sai ta cire su, ta jefa su ga Annabi (saw), ta ce: Na bayar da su ga Allah da Manzonsa)). Abu Dawud (1563), Tirmiziy (637), Nasa'iy (2479).

Zakka ba ta wajaba a zinari har sai ya isa nisabi, shi ne Dinari ishirin (20), saboda Annabi (saw) ya ce:

وَلَيْسَ عَلَيْكَ شَيْءٌ - يَعْنِي - فِي الذَّهَبِ حَتَّى يَكُونَ لَكَ عِشْرُونَ دِينَارًا،

[السجستاني، أبو داود، سنن أبي داود، ١٠٠/٢]

 ((Babu komai a kanka na Zakkar zinari har sai kana da Dinari ishirin)) Abu Dawud (1573).

Dinarin da ake nufi shi ne wanda nauyinsa ya kai gram hudu da kwata, don haka nisabin zinari shi ne gram tamanin da biyar (85g).

Haka Zakka ba ta wajaba a azurfa har sai ya kai nisabi; shi ne uqiya biyar, saboda Annabi (saw) ya ce:

«لَيْسَ فِيمَا دُونَ خَمْسِ

[البخاري، صحيح البخاري، ١١٦/٢]

((Babu Zakka a kasa da uqiya biyar)). Bukhari (1447), Muslim (979).

Uqiya shi ne dirhami arba'in, don haka nisabin shi ne dirhami dari biyu (200), wanda yake daidai da gram dari biyar da casa'in da biyar (595g) na dirhami.

Zakka ta wajaba a kudi na takardu, saboda a yau su ne canjin zinari da azurfa, su suka maye gurbinbsu, don haka idan azurfa ya isa nisabi to Zakka ta wajaba.

Zakka tana wajaba a zinari da azurfa da takardun kudi sawa'un suna wajenka, ko kuma suna wajen mutane, kana binsu bashi. Saboda haka Zakka tana wajaba a bashin da kake bi. Idan bashin yana wajen mai wadata ne wanda zai iya biya, to mutum zai yi lissafi ya fitar da Zakka da shi, ko kuma ya jinkirta har sai ya karba, sai ya fitar masa, na tsawon shekarun da suka yi.

Amma idan kuma bashin yana hanun talaka ne, ko mai kin biyan bashi, wanda karban kudin daga wajensa yana da wahala, to babu Zakka a kan wannan bashi, har sai lokacin da mutum ya karba, sai ya fitar na shekarar da a cikinta ya karba, ban da sauran shekarun da suka gabata.

Na hudu: Kayan kasuwanci:

Su ne dukkan abin da aka tanada don neman kudi da kasuwanci da su; na gida, ko fili, ko dabbobi, ko abinci, ko motoci ko kayan shago da sauran dangogin dukiya. Sai mutum ya kimanta su a kowace shekara, sai ya fitar da Zakkarsu a karshen shekara, zai fitar da daya bisa hudun daya bisa goman kimar kayan, sawa'un kimar dadai yake da yadda ya sayi kayan, ko ya yi kasa da haka, ko ya fi haka.

Babu Zakka ga abin da mutum ya tanada don amfanin kansa, kamar abinci, ko kayan shimfida, ko gidan zama, ko motocin hawa, ko kayan sakawa, in ban da zinari da azurfa. Saboda Annabi (saw) ya ce:

«لَيْسَ عَلَى المُسْلِمِ فِي فَرَسِهِ وَغُلاَمِهِ صَدَقَةٌ»

[البخاري، صحيح البخاري، ١٢٠/٢]

((Babu Zakka a kan Musulmi a bawansa ko dokinsa)) Bukhari (1463), Muslim (982).

Haka babu Zakka ga abin da aka tanada don bayar da haya, kamar gidaje da filaye, da motoci da makamantansu, Zakkar tana wajaba ne a kudin da aka tara na hayan, idan sun shekara, sun kai nisabi.

Don haka 'yan'uwa wadanda suka mallaki nisabi, wajibi ne su gaggauta fitar da Zakkar dukiyarsu, su sauke wajibin da yake kansu, don su samu tsarki da albarka a cikin dukiyarsu, kuma su samu lada da tsira daga azaba da fushin Allah Madaukaki. Kuma wajibi ne mutum ya tsarkake niyya, ya sake ransa wajen ba da Zakkar, kar mutum ya bayar alhali ransa ba ya son bayarwan.

Wanda ya yi jinkiri bai fitar da Zakka ba, to ya ribaci wannan wata mai albarka, wata mai falala, watan kyauta, watan da talakawa suke cikin bukata zuwa ga abinci, suke bukatar sababbin tufafi don Eidi ma iyalan, suke bukatar yalwata abinci ma iyalansu a ranakun Eidi. Lallai duk wanda ya makara bai bayar da Zakka a kan lokacinta ba, to ya gaggauta ya bayarwa a wannan wata, la'alla ya samu falala saboda falalan watan.

Allah ya karba mana Ibadunmu, ya gafarta mana zunubanmu, ya taimake mu a kan kiyaye Azuminmu, ya nufe mu da yawaita aiyukan da'a a cikin wannan wata, ya shiryar da mu hanya madaidaiciya. Kuma Allah ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun kasarmu, na kuncin rayuwa da rashin tsaro da aminci, ya ba mu shugabanni na gari, masu tsoron Allah da kishin al'umma da tausayin talakawa.

Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)

Fitar Da Zakka

Post a Comment

0 Comments