Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar'anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.
Tsira da amincin Allah su tabbata
ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari'a mai
sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
'Yan'uwa, wadannan kwanaki goman
karshe na Ramadhan da muke cikinsu, a cikinsu dare mai albarka yake, wato daren
Lailatul Qadr, daren da Allah ya yi baiwar falalolinsa ma wannar al'umma, kuma
ya fifita ta da su a kan sauran al'ummomi.
Daga cikin albarkan daren a
cikinsa aka saukar da Alkur'ani, a cikinsa ake raba dukkan lamari na kaddara
tabbatacce, ma'ana; a cikinsa Allah yake fayyace duk abin da zai afku a wannan
shekara, ya kaddara shi babu canji, daga "Lauhul Mahfuz" zuwa ga
Mala'iku marubuta, na kaddaran arziki, da ajali, da alheri da sharri har
karshe. Allah ya ce: {Lallai mu mun saukar da shi (Alkur'ani) a dare mai
albarka, lallai mun kasance masu gargadi. A cikinsa ake raba dukkan lamari na
kaddara tabbatacce} [al-Dukhan: 3-4].
Allah ya siffanta daren da
albarka, saboda falalarsa da yawan alheran da suke cikinsa.
Daga cikin albarkan wannan dare
na Lailatul Qadr yin ibada a cikinsa ya fi ibada a wata dubu. Allah ya ce: {Mu
mun saukar da shi ne (Alkur'ani) a cikin daren Lailatul Qadr. Me ya sanar da
kai Lailatul Qadr? Lailatul Qadr ya fi wata dubu. Mala'iku da Ruhi (Jibreel)
suna yawan sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu na kowane lamari aka kaddara.
Daren aminci ne har zuwa ketowan al-fijr} [al-Qadr: 1-5].
Al-Qadr ma'anarsa girma da daraja
da daukaka, ko kuma ma'anarsa ita ce: Kaddara abubuwa da Allah yake yi. An kira
daren da wannan suna ne saboda dare ne mai girma da daraja da daukaka, a
cikinsa Allah yake kaddara duk abin da zai faru a shekara.
Daren ya fi wata dubu, ma'ana; ya
fi su falala da daukaka da yawan lada, shi ya sa duk wanda ya yi Sallar dare a
cikinsa yana mai imani da neman lada to za a gafarta masa zunubansa da suka
gabata. Kamar yadda ya tabbata daga Annabi (saw) a Hadisin Abu Huraira (ra):
Bukhari (1901), Muslim (760).
Saboda girma da darajar wannan
dare Mala'iku, tare da shugabansu Mala'ika Jibreel (as) suna yawan saukowa,
suna saukowa da al'amuran da Allah ya kaddara.
Kuma dare ne wanda yake cike da
aminci ga Muminai, suna da aminci daga dukkan wani abin tsoro, saboda yawan
wadanda Allah yake 'yantawa daga wuta a cikin daren.
Lallai a cikin wannar Sura akwai
bayanin falaloli masu yawa na wannan dare, daga cikinsu:
Falala ta farko:
Allah ya saukar da Alkir'ani a
cikin daren, littafin da ya kasance shiriya ga mutane, kuma sa'ada gare su a
Duniya da Lahira.
Falala ta biyu:
Allah ya girmama sha'anin daren,
ta yadda ya yi tambaya a kansa, ya ce: {Me ya sanar da kai daren Lailatul
Qadr?}.
Falala ta uku:
Daren ya fi watanni dubu falala
da girman matsayi.
Falala ta hudu:
Mala'iku suna yawan sauka, su
kuma ba sa yawan sauka sai ga abu mai girma da matsayi da muhimmanci. Kai, har
Mala'ika Jebreel (as) shugaban Mala'iku shi ma yana sassaukowa, wanda hakan
yake nuna girman matsayin daren.
Falala ta biyar:
Daren aminci ne saboda yawan
kubutar bayi daga azaba da uquba, saboda bayi suna yawaita da'a da ibada ma
Allah a cikinsa.
Falala ta shida:
Allah ya saukar da Sura ta
musamman don bayanin girma da matsayi da daraja da albarka da falalar daren, da
alheran da ke cikinsa.
Daga cikin falalolin daren
Lailaitul Qadr, duk wanda ya yi Sallar dare a cikinsa yana mai imani da neman
lada to an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa, kamar yadda ya tabbata
daga Abu Huraira (ra), Annabi (saw) ya ce:
«مَنْ قَامَ لَيْلَةَ القَدْرِ
إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا، غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ،
[البخاري ,صحيح البخاري ,3/26]
((Duk wanda ya yi Sallar dare a daren Lailatul
Qadr, yana mai imani da neman lada to an gafarta masa abin da ya gabata na
zunubansa)). Bukhari (1901), Muslim (760).
Abin nufi; wanda zai samu gafaran
shi ne wanda ya yi Sallar dare a cikin daren yana mai Imani da Allah, tare da
yarda da ladan da Allah ya tanadar wa masu Sallar, kuma yana halin neman lada
da sakamako a wajensa.
Daren Lailatul Qadr a cikin watan
Ramadhan yake, kamar yadda Allah ya ce: {Mu mun saukar da shi ne (Alkur'ani) a
cikin daren Lailatul Qadr}. Kuma ya ce:
شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ
{Watan Ramadhan wanda aka saukar
da Alkur'ani a cikinsa shiriya ne ga mutane da bayanin shiriya da rarrabewa}.
Baqara (Aya: 185).
Don haka Daren Lailatul Qadr a
cikin watan Ramadhan yake, tun da saukar da Alkur'ani ya kasance ne a cikin
watan Ramadhan, a cikin daren Lailatul Qadr.
Daren Lailatul Qadr a cikin
kwanakin goman karshe na Ramadhan yake, shi ya sa Annabi (saw) ya ce:
«تَحَرَّوْا لَيْلَةَ القَدْرِ
فِي العَشْرِ الأَوَاخِرِ مِنْ رَمَضَانَ»
[البخاري ,صحيح البخاري
,3/47]
((Ku nemi daren Lailatul Qadr a kwanaki goman
karshe na Ramadhan)) Bukhari (2020), Muslim (1169).
Kuma a cikin kwanaki goman ma a
cikin wutri suke. Wato daren 21, 23, 25, 27, 29. Saboda fadin Annabi (saw):
((Ku nemi daren Lailatul Qadr a wutri, a kwanaki goman karshe na Ramadhan))
Bukhari (2017).
Kuma an fi tsammanin daren a
kwanaki bakwai na karshe, saboda ya tabbata daga Ibnu Umar (ra) ya ce: ((Wasu
mutane cikin Sahabban Annabi (saw) an nuna musu daren Lailatul Qadr a cikin
mafarki, a kwanakin bakwai na karshe, sai Annabi (saw) ya ce:
«أَرَى رُؤْيَاكُمْ قَدْ تَوَاطَأَتْ
فِي السَّبْعِ الأَوَاخِرِ، فَمَنْ كَانَ مُتَحَرِّيهَا فَلْيَتَحَرَّهَا فِي السَّبْعِ
الأَوَاخِرِ»
[البخاري ,صحيح البخاري
,3/46]
((Ina ganin mafarkin naku ya dace a cikin
kwanaki bakwai na karshe, don haka duk wanda zai nemi daren to ya nema a
kwanaki bakwai na karshe)) Bukhari (2015), Muslim (1165).
A cikin kwanaki bakwai din kuma
an fi tsammaninsa a cikin daren Ishirin da bakwai, saboda abin da ya tabbata
daga Ubayyi bn Ka'ab (ra) ya ce:
وَوَاللهِ إِنِّي لَأَعْلَمُ أَيُّ لَيْلَةٍ
هِيَ، هِيَ اللَّيْلَةُ الَّتِي أَمَرَنَا بِهَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ
وَسَلَّمَ بِقِيَامِهَا،
[مسلم، صحيح مسلم، ٥٢٥/١]
((Na rantse da Allah na san wane
dare ne (daren Lailatul Qadr), a sanina mai karfi shi ne daren da Manozn Allah
ya umurce mu da mu yi Sallah a cikinsa, shi ne daren Ishirin da bakwai)).
Muslim (762).
Amma Malamai sun rinjayar da
cewa; daren Lailatul Qadr yana canzawa, idan a wannan shekarar ta kasance a
daren ishirin da bakwai, to wata shekarar ta yiwu ta kasance a daren ishirin da
uku, ko da biyar ko da tara. Shi ya sa Annabi (saw) ya ce:
«التَمِسُوهَا فِي العَشْرِ الأَوَاخِرِ
مِنْ رَمَضَانَ لَيْلَةَ القَدْرِ، فِي تَاسِعَةٍ تَبْقَى، فِي سَابِعَةٍ تَبْقَى،
فِي خَامِسَةٍ تَبْقَى»
[البخاري، صحيح البخاري،
٤٧/٣]
((Ku nemi daren Lailatul Qadr a
cikin kwanaki goman karshe na Ramadhan, a kwanaki tara da suka rage, a kwanaki
bakwai da suka rage, a kwanaki biyar da suka rage)) Bukhari (2021).
Allah Madaukakin Sarki ya boye
sanin daren ne ga bayi don hikimarsa, da kuma rahmarsa ga bayi, don su dage da
Ibada cikin dukkannin kwanaki goma na karshen watan, sai aikinsu na Ibada ya
yawaita, ladansu ya yi yawa, su rabauta da yawan ibada; Sallah, Zikiri, Karatun
Alkur'ani da Addu'o'i a cikin daren, sai su kara samun kusaci da daukaka a
wajen Allah Madaukaki, su samu lada masu yawan gaske.
Kuma ya boye sanin daren ga
mutane don yin jarabawa ga bayi, don masu kasala su bayyana daga masu himma da
kokarin ibada. Don idan mutum yana neman abu to bai kamata ya zama mai kasala a
neman ba, kamata ya yi a ga yana da himma da kokari mai yawa wajen nemansa.
'Yan'uwa, a cikin daren Lailatul
Qadr Allah yana saukar da rahma, yana 'yanta bayi daga wuta, yana gafarta
zunubai, yana rabon falala da arziki da lada mai yawa a kan ibada a cikin
daren, ibada a daren ya fi ibada a wata dubu. Ku yi kokari wajen neman wannan
alheri da albarka mai yawa mai girman gaske. Kwanaki ne kadan, ku dage a
cikinsa kar ku yi kasala.
Allah ya karba mana Ibadunmu, ya
gafarta mana zunubanmu, ya taimake mu a kan kiyaye Azuminmu, ya nufe mu da
yawaita aiyukan da'a a cikin wannan wata, ya shiryar da mu hanya madaidaiciya.
Ya sa mu dace da daren Lailatul Qadr.
Kuma Allah ya jikan iyayenmu, ya
yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun kasarmu, na kuncin rayuwa da
rashin tsaro da aminci, ya ba mu shugabanni na gari, masu tsoron Allah da
kishin al'umma da tausayin talakawa.
Dr. Aliyu Muh'd Sani
(Hafizahullah)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.