Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar'anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.
Tsira da amincin Allah su tabbata
ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari'a mai
sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
Abubuwa masu karya Azumi da suka
gabata, idan ka cire Jinin Haila da na Biki, - wato su ne saduwa da mace
(Jima'i), fitar da maniyyi, ci da sha, abin da yake da ma'anarsu, kaho, janyo
amai – ba sa karya Azumi sai da sharuda guda uku:
Na farko: Mutum ya zama yana sane
da cewa suna karya Azumi. Amma idan ya zama ya jahilci cewa; suna karya Azumi
to Azuminsa bai karye ba. Saboda hukuncin yana faduwa bisa jahilci. Allah ya
ce: {Ya Ubangijinmu kar ka kama mu da abin da muka manta ko muka yi kuskure}
[al-Baqarah: 286]. Ya tabbata a Hadisi Allah ya ce: ((Na yi)). Muslim (126).
Haka kuma Allah ya ce: {Babu
laifi a kanku a abin da kuka yi kuskure, sai dai kuna da laifi ne a abin da
zuciyarku ta yi gangancinsa} [al-Ahzab: 5].
Don haka duk wanda ya kasance
jahili ya aikata wani abu mai karya Azumi cikin rashin sani da kuskure to
Azuminsa bai karye ba, sawa'un ya jahilci hukuncin ne, kamar ya yi zaton wannan
abu ba ya karya Azumi, sai ya aikata shi, ko kuma lokacin ya jahilta bai san
lokacin ya yi ba, kamar ya yi zaton al-fijr bai fito ba, sai ya ci abinci,
alhali ya keto, ko ya yi zaton rana ta fadi, sai ya aikata daya daga cikin
wadancan abubuwa, alhali rana ba ta fadi ba, to wannan Azuminsa bai karye ba,
saboda ya tabbata Sahabi Adiyyi bn Hatim (ra) a lokacin da Ayar: {Ku ci ku sha
har sai farin zare ya bayyana muku daga bakin zare} [al-Baqarah: 183] ta sauka,
kawai sai ya dauki zare guda biyu, daya baki daya fari, sai ya ajiye a kasan
filonsa, jim kadan sai ya duba su, yana ta cin abincinsa, har sai da ya iya
banbance tsakaninsu, bayan gari ya yi haske, a lokacin tukun ya dena cin
abinci. Sai da safe ya tafi wajen Manzon Allah (saw) ya ba shi labarin abin da
ya yi, sai Annabi (saw) ya ce: ((Lallai filonka yana da fadi in dai har farin
zare da bakin za su kasance a karkashinsa. Ai abin da ake nufi kawai shi ne,
hasken yini da duhun dare)). Bukhari (4509, 4510), Muslim (1090).
To ka ga a nan Adiyyi ya ci
abinci bayan fitowan alfijir, amma Annabi (saw) bai umurce shi da ramuko ba,
saboda bai san hukuncin yadda ya kamata ba.
Ya tabbata daga Asma'u bnt
Abbubakar (ra) ta ce: ((Mun yi buda baki a zamanin Annabi (saw) a ranar da aka
yi gajimare, sai daga baya rana ta fito)). Bukhari (1959).
Asma'u ba ta fadi cewa; Annabi
(saw) ya umurce su da rama Azumin ranar ba, ba su san lokaci bai yi ba suka yi
buda baki. Da a ce ya umurce su da ramuko da an ruwaito.
Sai dai da zaran an fahimci rana
ba ta fadi ba, to sai a kame baki, har sai ranar ta fadi.
Haka wanda ya ci abinci bayan
fitowan al-fijr, yana zaton bai fito ba, sai daga baya ya bayyana masa cewa;
al-fijr ya fito to Azuminsa ya inganta, kuma babu ramuko a kansa, saboda bai
san lokaci ya yi ba.
Kuma Allah ya halasta wa mutum ya
yi ta ci da sha, da Jima'i, har sai al-fijr ya keto, ba a ramuko ga abin da aka
ba da izni a kansa. Amma da zaran mutum ya san cewa; lokacin ya yi to sai ya
kame daga cin ko shan.
Sharadi na biyu: Ya kasance mutum
yana tune ba mai mantuwa ba. Idan ya aikata daya daga cikin abubuwan da suka
gabata cikin mantuwa, to shi ma Azuminsa bai baci ba. Saboda Ayar Suratu
al-Baqarah da ta gabata.
Kuma ya tabbata daga Abu Huraira
(ra), daga Annabi (saw) ya ce: ((Duk wanda ya manta ya ci ko ya sha alhali yana
Azumi to ya cika Azuminsa, kawai Allah ne ya ciyar da shi ya shayar da shi)).
Bukhari (1933), Muslim (1155).
Sai Annabi (saw) ya yi umurni da
cika Azumin, wannan kuwa dalili ne a kan Azumin bai baci ba. Jingina ciyar da
shi da shayar da shi ga Allah shi yake nuna Allah ba zai kama shi a kan haka
ba. Amma duk lokacin da mutum ya tuna sai ya kame ya dena ci, ya tofar da na
bakinsa, saboda uzurin nasa ya kauce.
Sharadi na Uku: Ya kasance bisa
zabinsa da nufinsa ya aikata dayan wadancan abubuwa ba tilasta shi aka yi ba.
Idan tilasta shi aka yi to Azuminsa bai baci ba, don haka babu ramuko a kansa,
saboda Allah ya dauke hukunci a kan wanda ya kafirta bisa tilastawa, alhali
zuciyarsa tana nitse da imani, inda Allah ya ce: {Duk wanda ya kafirce da Allah
bayan imaninsa, sai dai wanda aka tilasta, alhali zuciyarsa tana nitse da
imani, amma wanda ya sake zuciyarsa ga kafirci to akwai fushin daga Allah a
kansu, kuma suna da azaba mai girma} [al-Nahl: 106].
Idan Allah ya dauke hukuncin
kafirci daga wanda aka tilasta to wanda aka tilasta a kan abin da bai kai
kafirci ba shi ya fi cancanta a dauke masa hukuncin.
Idan miji ya tilasta wa matarsa
ya sadu da ita alhali tana Azumi, to Azuminta bai baci ba, kuma babu ramuko a
kanta. Shi kuma bai halasta ya tilasta mata saduwa da ita ba, alhali tana
Azumi, sai dai idan Azumin nafila ne ba tare da izninsa ba, alhali yana gari,
to a wannan shi ba abin zargi ba ne, yana da uzuri.
Idan kura ko garin mai nika ko
wani abu ya shiga cikin mai Azumi ba tare da nufinsa ba, ko ya yi kurkuran baki
ko shaqa ruwa a hanci, amma sai ya wuce ya shiga cikinsa, ba da nufi ba,
Azuminsa bai baci ba, kuma babu ramuko a kansa.
Saka kwalli, ko saka magani a ido
ba ya karya Azumi, ko da mutum ya ji dandanonsa a makokwaronsa, saboda wannan
ba abinci ko abin sha ba ne, ba kuma abin da yake ma'anarsu ba ne. Haka Azumi
ba ya baci don an diga magani a kunne, ko saka magani a rauni, ko da an ji
dandanonsa a makokwaro.
Haka Azumi ba ya baci idan mai
girki ya dandana a harshensa don jin gishiri, matukar bai hadiye ba. Haka Azumi
ba ya baci idan an shanshana turare, kuma ba ya baci idan an kurkure baki, ko
shaqa ruwa a hanci, sai dai kar mutum ya shaqa ruwan sosai, don kar ya wuce ya
shiga cikinsa. Annabi (saw) ya ce: ((Ka shaqa ruwa a hanci sosai, sai dai idan
ka kasance mai Azumi)). Abu Dawud (2366), Tirmiziy (788), Nasa'iy (87), Ibnu
Majah (407).
Haka yin aswaki ba ya karya
Azumi, kai, Sunna ne ma yin aswaki da rana. Amir bn Rabee'a (ra) ya ce: ((Na ga
Annabi (saw) sau ba iyaka, yana yin aswaki alhali yana Azumi)) Abu Dawud
(2364), Tirmiziy (725).
Don haka amfani da aswaki shi ya
fi a kan yin amfani da makilin da brush.
Babu laifi ga mai Azumi ya yi
abin da zai saukaka masa tsananin zafi da kishirwa, kamar jika jiki da ruwa da
makamancin haka, kamar yadda aka ruwaito hakan daga wasu Sahabbai.
Saboda haka wajibi ne bawa ya san
hukunce-hukuncen Ibada da yake yi ma Allah, don ya yi ibada kamar yadda Allah
yake so, kuma ya yarda da ita.
Allah ya karba mana Ibadunmu, ya
gafarta mana zunubanmu, ya taimake mu a kan kiyaye Azuminmu, ya nufe mu da
yawaita aiyukan da'a a cikin wannan wata, ya shiryar da mu hanya madaidaiciya.
Kuma Allah ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun
kasarmu, na kuncin rayuwa da rashin tsaro da aminci, ya ba mu shugabanni na
gari, masu tsoron Allah da kishin al'umma da tausayin talakawa.
✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.