Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar'anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.
Tsira da amincin Allah su tabbata
ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari'a mai
sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
Akwai abubuwan da suke bata Azumi, su warware shi, allah Madaukakin Sarki ya ce: {Yanzu kam ku sadu da su (matanku), ku nemi abin da Allah ya rubuta muku, ku ci ku sha har sai farin zare ya bayyana muku daga bakin zare na al-fijr, sa'annan ku cika Azumin zuwa dare} [al-Baqarah: 183].
A cikin wannar Aya mai girma,
Allah ya ambaci ginshikan abubuwan da suke warware Azumi, a Sunna kuma Annabi
(saw) ya bayyana cikon sauran.
Abubuwan da suke warware Azumi
nau'uka ne guda bakwai:
Na farko: Jima'i:
Shi ne saduwa da mace ta hanyar
saka zakari cikin farji. Wannan shi ne mafi girman abubuwan da suke warware
Azumi, kuma shi ya fi girman zunubi. Duk lokacin da mai Azumi ya sadu da mace
to Azuminsa ya baci,
sawa'un Azumin farilla ne ko na nafila. Idan
da rana ne a watan Ramadhan, kuma Azumin wajibi ne a kansa, to wajibi ne sai ya
rama, kuma sai ya yi kaffara mai tsanani, ita ce: 'yanta baiwa mumina, idan
kuma bai samu ba, to sai ya yi Azumi wata biyu a jere, ba zai sha ko daya ba
sai da uzuri na Shari'a, kamar ranakun Eidi, da ranakun Tashreeq (ranakun 11,
12, 13 ga Zul-hijja),
ko wani uzuri na zahiri, kamar rashin lafiya
ko tafiya ba don yin dabara ma Shari'a ba. Idan ya sha rana daya ba tare da
uzuri ba, to dole zai sake tun daga farko, don dole ne sai an samu jerantawa.
Idan kuma ba zai iya yin Azumin
ba, to sai ya ciyar da miskinai sittin, kowane miskini zai ba shi rabin kilo da
gram goma na abinci, shinkafa ko masara d.s.
Ya tabbata wani mutum ya sadu da
matarsa da rana a watan Ramadhan, sai ya tambayi Annabi (saw) a kan haka, sai
ya ce:
«هَلْ تَجِدُ رَقَبَةً» قَالَ:
لاَ، قَالَ: «هَلْ تَسْتَطِيعُ صِيَامَ شَهْرَيْنِ» قَالَ: لاَ، قَالَ: «فَأَطْعِمْ
سِتِّينَ مِسْكِينًا»
[البخاري ,صحيح البخاري
,8/166]
(("Shin za ka samu
baiwa"? Ya ce: A'a. "Shin za ka iya Azumi wata biyu (a jere)"?
Ya ce: A'a. Ya ce: "To ka ciyar da miskinai sittin")). Bukhari
(6821), Muslim (1111).
Na biyu:
Fitowan maniyyi:
Idan mutum ya fitar da maniyyi
daga gare shi da gangan, imma saboda sunbantar mace, ko shafan jikinta, ko ta
wata hanyar daban, ta hanyar sha'awa to Azuminsa ya warware. Saboda wannan yana
cikin sha'awar da hakikanin Azumi ba ya tabbata sai da nisantarsa. Annabi ya
ce:
الصَّوْمُ لِي وَأَنَا أَجْزِي بِهِ، يَدَعُ
شَهْوَتَهُ وَأَكْلَهُ وَشُرْبَهُ مِنْ أَجْلِي،
[البخاري ,صحيح البخاري
,9/143]
((Zai bar abincinsa da abin shansa da biyan
sha'awarsa don ni)). Sahihul Bukhari (7492), Sahihu Muslim (1151).
Amma sunbantar mace da shafan
jikinta ba tare da maniyyi ya fito ba, ba ya karya Azumi, saboda abin da ya
tabbata daga A'isha (ra): tace
كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
«يُقَبِّلُ وَيُبَاشِرُ وَهُوَ صَائِمٌ، وَكَانَ أَمْلَكَكُمْ لِإِرْبِهِ»،
[البخاري ,صحيح البخاري
,3/30]
((Annabi (saw) ya kasance yana sunbantan
iyalinsa, yana runguma alhali yana Azumi, amma ya kasance ya fi ku rike
sha'awarsa)). Bukhari (1927), Muslim (1106).
Ya tabbata Umar bn Abi Salamah:
((ya tambayi Manzon Allah (saw):
أَيُقَبِّلُ الصَّائِمُ؟ فَقَالَ لَهُ رَسُولُ
اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «سَلْ هَذِهِ» لِأُمِّ سَلَمَةَ فَأَخْبَرَتْهُ،
أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَصْنَعُ ذَلِكَ، فَقَالَ: يَا
رَسُولَ اللهِ، قَدْ غَفَرَ اللهُ لَكَ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِكَ وَمَا تَأَخَّرَ،
فَقَالَ لَهُ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَمَا وَاللهِ، إِنِّي
لَأَتْقَاكُمْ لِلَّهِ، وَأَخْشَاكُمْ لَهُ»
[مسلم، صحيح مسلم، ٧٧٩/٢]
Shin mai Azumi zai sunbaci iyalinsa? Sai
Manzon Allah (saw) ya ce masa: "Tambayi wannar", yana nufin Ummu
Salamah, sai ta ba shi labarin cewa; Manzon Allah (saw) ya kasance yana aikata
hakan. Sai ya ce: Ya Manzon Allah, ai kai Allah ya gafarta maka abin da ya
gabata na zunubanka da na gaba, Sai Annabi (saw) ya ce: "Na rantse da
Allah na fi ku taqwa da tsoron Allah")). Muslim (1108).
Don haka idan mai Azumi yana jin
tsoron idan ya yi sunbantan zai fitar da maniyya, ko har hakan zai ja shi ga
saduwa da iyalin, saboda ba zai iya rike sha'awarsa ba, to a nan haramun ne a
kansa ya yi sunbantan, a babin "sadduz zari'a", wato toshe kofar
barna, da kuma kare Azuminsa daga baci.
Amma fitar da maniyyi saboda
mafarki, ko tunani ba tare da aiki ba, ba ya karya Azumi, saboda na mafarki ba
ya cikin zabin mutum, na tunani kuma Allah ya yi afuwa a kansa. Annabi (saw) ya
ce:
«إِنَّ اللَّهَ تَجَاوَزَ عَنْ
أُمَّتِي مَا حَدَّثَتْ بِهِ أَنْفُسَهَا، مَا لَمْ تَعْمَلْ أَوْ تَتَكَلَّمْ»
[البخاري، صحيح البخاري،
٤٦/٧]
((Allah ya yafe ma al'ummata abin
da ta raya a ranta matukar ba ta yi aiki da shi ko ta furta a magana ba)).
Bukhari (5269), Muslim (127).
Na uku: Cin abinci ko shan abin
sha:
Shi ne shigar da abinci ko abin
sha zuwa ciki, ta hanyar baki ko hanci, na dukkan nau'ukan abin ci ko sha.
Saboda fadin Allah:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ
الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ
{Ku ci ku sha har sai farin zare ya bayyana
muku daga bakin zare} [al-Baqarah: 183].
Duri ta hanci shi ma kamar ci da
sha ta baki ne, shi ya sa ya tabbata Annabi (saw) ya ce:
«بَالِغْ فِي الِاسْتِنْشَاقِ،
إِلَّا أَنْ تَكُونَ صَائِمًا»
[السجستاني، أبو داود، سنن أبي
داود، ٣٠٨/٢]
((Ka shaqa ruwa a hanci sosai, sai dai idan ka
kasance mai Azumi)). Abu Dawud (2366), Tirmiziy (788), Nasa'iy (87), Ibnu Majah
(407).
Amma shanshana wari ko kamshi ba
ya karya Azumi.
Na hudu: Abin da yake da ma'anar
ci da sha:
Misali karin jini, ko karin ruwa.
Idan aka yi wa mutum karin jini ko na ruwa to Azuminsa ya karye, saboda jini
shi ne abin da abinci yake samarwa a jikin mutum, haka karin ruwa, shi kuma
yana madadin abinci ne, duk da cewa; mutum ba abinci ya ci a zahiri ba. Don
haka za su dauki hukuncin ci da sha.
Amma allura ta magani, ba ta
karin ruwa ba, ba ta warware Azumi, ko da kuwa mutum ya ji dandano ko dacinta a
makokwaronsa. Ita allura ba ta warware Azumi, saboda ba a madadin abinci da
abin sha take ba, don haka ba za ta dauki hukuncin cin abinci ba.
Na biyar: Yin kaho:
Fitar da jini ta hanyar kaho yana
karya Azumi, saboda fadin Annabi (saw):
«أَفْطَرَ الْحَاجِمُ وَالْمَحْجُومُ»،
[السجستاني، أبو داود، سنن أبي
داود، ٣٠٨/٢]
((Mai yin kahon (wanzami) da wanda ake masa
kahon duka Azuminsu ya karye)). Abu Dawud (2367), Tirmiziy (774), Ibnu Majah
(1679).
Da wannan Malamai suke ganin jan
jini mai yawa a jikin mutum, wanda zai yi tasiri a jikin mutum, shi ma yana
karya Azumi, sai dai idan ya zama larura, to wajibi ne ya karya Azumin nasa,
daga baya sai ya rama.
Amma fitar da jini saboda habo,
ko tari, ko basir, ko ciwon rauni, ko cire hakori, jan jini kadan don yi test,
ko fitan jini saboda soka allura, duka ba sa karya Azumi, saboda ba kaho ba ne,
kuma ba sa tasiri a jiki kamar yadda kaho yake yi.
Na shida: Amai da gangan:
Shi ne fitar da abin da ke cikin
mutum na abinci ko abin sha ta hanyar baki. Saboda Annabi (saw) ya ce:
«مَنْ ذَرَعَهُ قَيْءٌ، وَهُوَ
صَائِمٌ، فَلَيْسَ عَلَيْهِ قَضَاءٌ، وَإِنْ اسْتَقَاءَ فَلْيَقْضِ»،
[السجستاني، أبو داود، سنن أبي
داود، ٣١٠/٢]
((Duk wanda amai ya rinjaye shi babu ramuko a
kansa, amma wanda ya nemo aman da gangan, to dole ya rama Azumin)). Abu Dawud
(2380), Tirmiziy (720), Ibnu Majah (1676).
Don haka duk wanda ya janyo amai
da gangan, to Azuminsa ya karye. Amma idan ba da gangan ba ne to Azuminsa bai
karye ba.
Na bakwai: Fitowan jinin haila ko
biki:
Fitowan jinin haila ko biki daga
mace yana karya mata Azumi, saboda fadin Annabi (saw) game da mace:
أَلَيْسَ إِذَا حَاضَتْ لَمْ تُصَلِّ وَلَمْ
تَصُمْ»
[البخاري، صحيح البخاري،
٦٨/١]
((Shin ba tana barin Sallah da Azumi ba idan
tana jinin haila?)). Bukhari (304) Muslim (79).
Don haka duk lokacin da mace ta
ga jini ya zo mata, na haila ko na biki to Azuminta ya baci, sawa'un a farkon
yini ne ko a karshensa, ko da kuwa kafin faduwar rana ne da minti daya. Amma
idan bai fara fitowa ba, har sai da rana ta fadi, to Azumin nata ya inganta.
Wadannan su ne abubuwan da suke
karya Azumi. Saboda haka haramun ne mai Azumi ya yi daya daga cikin wadannan
abubuwa, matukar Azumin nasa na wajibi ne, kamar Azumin Ramadhan, ko na
kaffara, ko na bakance, sai dai idan akwai uzuri na Shari'a da zai halasta masa
hakan, kamar tafiya ko rashin lafiya da makamancinsu. Saboda duk wanda ya fara
aiki na wajibi to dole ya karasa shi, ya cika shi, sai dai idan da uzuri.
Sa'annan duk wanda ya yi daya
daga wadannan abubuwa a tsakiyar rana a watan Ramadhan, ba tare da uzuri ba, to
dole ya yi kama baki, har rana ta fadi, don kiyaye alfarman watan, kuma ramuko
ya wajaba a kansa. Amma idan akwai uzuri to ramuko ne kawai ya wajaba a kansa.
Amma idan Azumin nafila ne, to ba
dole sai ya cika shi ba, ko da babu uzuri kuwa, amma ko shakka babu abin da ya
fi shi ne cikawan.
Ya ku 'yan'uwa, lallai wajibi ne
mu kiyaye aiyukan da'a, mu nisanci aiyukan sabon Allah, mu yi ibada ma Allah,
mu girmama wajibansa, kar mu yi wasa da su, mu sani abin da mutum zai yi na
ibada a halin rayuwarsa shi zai amfane shi a Duniya da Lahira, musamman a ranar
Lahira, ranar da mutum zai yi nadaman lokacinsa da ya bata a Duniya ba tare da
aikin da'a ma Allah da neman lada ba. Mu ribaci wannar ganima a rayuwarmu kafin
wucewar lokacinta; wannan wata mai albarka, da ma rayuwar gaba daya lokaci ne
na kasuwanci da Allah da neman riba, kar mu yi sakaci, kar mu gafala, duk wanda
ya yi sakaci zai yi hasara, kuma zai yi nadama a lokacin da ba za ta yi amfani
ba.
Allah ya karba mana Ibadunmu, ya
gafarta mana zunubanmu, ya taimake mu a kan kiyaye Azuminmu, ya nufe mu da
yawaita aiyukan da'a a cikin wannan wata, ya shiryar da mu hanya madaidaiciya.
Kuma Allah ya jikan iyayenmu, ya yaye mana matsaloli da fitintinu da suke damun
kasarmu, na kuncin rayuwa da rashin tsaro da aminci, ya ba mu shugabanni na
gari, masu tsoron Allah da kishin al'umma da tausayin talakawa.
Dr Aliyu Muh'd Sani (Hafizahullah)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.